Author : Billyn Abdull Category : African Stories & Novels
buƙatar sanda za'a sanar da wa ya samu ace suna kusa da shi. Hakan zai bashi ƙarfin gwiwar amsa daga abinda ƙaddara zatazo da shi.
Tunda shugaban zaɓe ya fara magana kusan a lokaci guda numfashin biliyoyin al'ammar ƙasar ya tsaya cak.
_“A bisa sakamakon da aka tattara, ɗan takarar AGS Party, Honourable Yusuf Shu’aibu Tafida… ya lashe zaɓen shugaban ƙasa.”_
“Ya arrahim!”.
Hajiya Zainab ta faɗa tana mai fashewa da kukan farin ciki tare da miƙewa ta rungume Janar da ke kusa da ita kamar yayi sumar zaune. Sai da ta sake furta, “Alhamdulillah Daddyn Deen! Alhamdullahi!. ALLAH ya baka, ALLAH ya cika maka burinka, ALLAH ya baka wannan ne don ka gyara gaskiya!”.
A hankali Janar ɗin ya lumshe ido, zuciyarsa cike da wani nauyi mai girman gaske, nauyin da yake jin tamkar ya ɗauka daga yanzu nan har zuwa shekaru da yawa. Lokacin da ya buɗe ido sai kawai ya zame yay sujida, ganin haka itama ta bishi, hakama yaran da gaba ɗaya suka kacame da ambaton Alhmdllh duk sai suka bisu....
★★★
A gidan Mammah ma lokaci guda falon yay wani irin shiru na sakan, kafin su Yaya Ma'aruff su kacame da ambaton kalmar Alhamdullah. Sai da suka ga Mammah ta tafi sujida sannan suma duk suka bita har su Ruky. Mammah ta jima bata ɗago ba saboda hawayen da suke zubar mata. Koba komai tana ji a ranta nesa tazo kusa in sha ALLAHU. Sai da ta goge hawayen tas sannan ta ɗago tana murmurshi. Su dai su Yaya Ja'afar na mamakin yanda Mammah ke son janar ya samu kujerar nan, amma basu taɓa tambaya ba, yanzu ma kuma basu tambayar ba. Kawai suna ganin da Yaya Imran na son shi ne dai. Kuma Dada ma sanda yana nan yana girmama al'amarinsa matsayin ogansa......
<<%>><★><<%>>
Shima dai a ɓangaren Daddy Imran tamkar Janar ana sanarwa yi yay tamkar ha suma a zaune. Duk ihun da Khalifa da Asma'u keyi baima jisu ba sai da Ammie data zuba masa ido tana murmushi ta kama hannunsa ta matsa a cikin nata. Wani nannauyan numfashi ya kawo hawaye na cika masa ido. Ya kalli Ammie dake lallonsa cikin ido tana murmushi, dan duk da bai taɓa fitowa ya sanar mata shirinsa tsakaninsa da Janar ba tana tsintar wasu abubuwan nasu ta waya idan suna yi. Yau kam ko kunyar yara baiji ba ya jawota jikinsa ya rungumeta, a haka cikin dabara ya share hawayen da suka cika masa ido. Kafin ya saketa ya tafi sujida shima. Sai suma duk suka bishi, yana ɗagowa yayma su Asma'u alamar suzo gareshi, suma su biyun ya haɗasu ya rungume dan auta barci yake.
Sai da ya sake su suna masa congratulations yana gyaɗa musu kai da ɗaukar waya dan bakinsa ma ji yay ya masa nauyi. Kai tsaye layin janar ya kira duk da baida tabbacin samu, dan yasan a yanzu duk wani masoyinsa abinda yake ƙoƙarin yi kenan...
Tabbas hasashen Daddy Imran akan Janar haka ne, dan wayoyine keta rige-rigen shigowa wayar sa a dai-dai wannan lokacin, sai dai ta yayansa kawai ya ɗaga sai ga ta Imran ma. Sunan da ya gani yasa zuciyarsa ta tsaya na ɗan daƙiƙai. (Imran....) Sai yaga sunan na koma masa bibbiyu tamkar haɗe da sunan Haysam. Sai da ya lumshe idanu ya sake buɗewa sannan ya ɗaga yana kaiwa kunnensa. Daga sallama abu na biyu da Daddy Imran ya furta shine,
“Sir… mun yi nasara Alhamdullah. Subahanal-lah. Allahu-akbar. ALLAH ya tabbatar da alkairi, mulki jarabawa ce mai girma, ina roƙon UBANGIJI ya dubi tsarkin zuciyarka, da ƙyaƙyƙyawan fatanmu da ƙyaƙyƙyawan zaton da muke maka yay riƙo da hannayenka wajen baka damar sauke nauyin al'ummar wannan ƙasa gwargwadon iko. Duk wanda zai kasance da kai a cikin wannan sha'anin mulkin in har bazarana ne shi ga sauke hakkokin mutane koda wanene ALLAH ya tauyeshi ta inda zai rasa ƙarfin iya yin komai. UBANGIJI ya zama gatanka, bangon jinginarka, mafakarka, damu baki ɗaya. Once again, Congratulations, Sir.”
“Thanks you Imran. Amin ya rabbi Jazakallahu khairan. Imran ka san wannan nasara ba tawa ba ce. Tawa da taka ce. Ta Haysam ce. Ta gaskiya ce.”
Hawaye ne suka cika idanun Daddy Imran daga can, muryarsa na rawa ya ce, “Na gode, Sir… na gode da bama wannan YAƘIN daraja da kake yi.”
“Yaƙin Haysam yaƙinmu ne ƙasa gaba ɗaya, wanda bai sani bane ko bai fahimta bane kawai keja da baya. Ka shirya, dan tun gobe idan ALLAH ya kaimu nake so ka fara haɗa min duk bayanan shari’ar Haysam tun daga farkon ranar da aka fara har ƙarshe. Ba zan shiga gidan gwamnati ba tare da na duba gaskiya ba. Lokaci ya yi da za mu dawo masa da mutuncinsa tare da namu muma Imran. Dan haka kwana ɗaya kawai zanyi da shiga gidan gwamnati Haysam ya fito in sha ALLAHU”.
Daddy Imran ya gyaɗa kai, hawayen da yake ta riƙewa tun ɗazun na sauka masa. Muryarsa ta shaƙe a cikin maƙoshinsa dake kai-kawo da nauyin shekaru takwas na zafi ya furta, “Sir! Sai nake jin kamar ina mafarki ne irin wanda na sabayi. Dan ALLAH idan barci nake kada ku tada ni”.
“Ba barci kake ba Imrana. Gaskiya bata da lokacin jira. Dole tun a yau mu tunawa kammu akwai wani mutum da ba zamu bari ya cigaba da kwana cikin duhu ba bayan ALLAH ya bamu wannan AMANAR, maza kaje, jeka ka fara shirin fitowar gwarzon haziƙin jarumin soja mai gaskiya da kwatanta gaskiya akan kowace gaskiya duk ƙarfinta.”
“Thanks you Sir! Thanks yo...”
Daddy Imran ya kasa ƙarasawa saboda yanayin da yake ciki misaltashi sai UBANGIJI. Ji yake tamkar zai faɗi sai da ma Ammie ta riƙeshi suka zauna ta miƙa mashi ruwa. Dama ta kora su Asma'u suje suci abincin dan kaf ɗinsu yau babu wani abincin kirki a cikinsu saboda uban gayya bai ci ba hankalinsa nakan television yini guda.
Tambayar da Ammie ta jefa masa a karo na farko game da al'amarin yasa Daddy Imran kallonta cikin ido. Wani sassanyan murmushi ya sakar mata, batare da ya buɗe mata ba a dunƙule ya furta, “Akwai wani mutum guda dake bina bashi Hafsat, bashin adalci, bashin ƙauna, bashin zuminci.
Kuma lokaci ya yi da zan biyashi koda da kwatantawa ne.”
“ALLAH ya cika maka wannan buri Daddyn Khalifa”.
“UBANGIJINA ya cika min sai dai tabbatarwa”. Ya faɗa cikin salon raɗa da rungumeta a jikinsa.....
=============
★PRISON★
A kwanakin farko na kawo television ɗin ɗakinsa bai maida hankali akan zaman kallonta ba, dan lissafinsa nakan haɗa kalaman vistor ɗinsa da musu fashin baƙi a farashin mutane masu hangen nesa da basu raina bincike irinsa. Abu uku kawai da aka turke tvn da ita ne ya fara tasirin jan hankalinsa gareta dole. Sun saka mata security ta yanda bata kasuwa, bai iya rage volum, bai canja tasha daga ukun nan kacal duk da kuwa akwai remote. Duk da basu sakata da ƙara mai takura ba kasancewar sa mutum mara san damuwa da hayaniya sai da ta fakurashi a kwanakin farkon. Sai daga baya daya fahimci an kawota ne garesa dan tai masa irin wannan takurar ai sai ya dake ya ajiye komai gefe har a kwana na huɗu ya maida hankali a kallon fashin baƙin masana akan taron campaign ɗin da aka rufe, a bazata yaci karo da na Janar Yusuf Shu'aibu Tafida ne a gaba. Duk da bawai akan Janar ɗin masu fashin baƙin ke tattaunawar ba, suna tattaunawa ne akan mabiyan ɗan takara, inda daga ƙarshe suke faɗin alƙaluma na sake nuna tsohon Janar dake gaba wajen tara masoya a duk jahar da yaje. Wannan shine karo na farko daya fara bama tvn hankalinsa, daga ranar kuma ya cigaba da bibiyar komai daki-daki, har hakan ya bashi damar fara tantance kowace fuska dake tare da Janar Yusuf dama sauran ƴan takara tun daga na shugaban ƙasa har zuwa shugabannin jihohi. A haka aka gangaro har ranar zaɓe, duk yanda abubuwan ke gudana nan ma yana biye, sai ta kai har ƙirga ƙuri'u ya bibiya. Sai dai a yau da aka tashi da jiran faɗar sakamako ya yini da ciwon kai saboda matsawa kansa da ayyukan ƙwaƙwalwa da yay a cikin satin nan gaba ɗaya. Dan haka bai wani maida hankali ba sosai ga television ɗin, bayan ma ya idar da sallar isha'i yay zaman fara karatun Alkur'ani ne, kasancewar tvn ba kasuwa take ba, ba rage ƙara take ba a bazata bayanin shigaban hukumar zaɓe ya shiga cikin kunnensa.
Cak harshensa ya tsaya dai-dai da bugun zuciya na sakanni, kafin ya iya ɗago manyan idanunsa zuwa kan tvn ya saukesu akan fuskar ɗan jaridar dake maimaita kalmar.........✍️
KIƊA A RUWA 2
29
..........“Wow! Congratulations, Her Excellency General Yusuf Tafida.”
Dada bai motsa ba. Bai yi murmushi ba. Bai yi mamaki ba.
Sai dai zuciyarsa ta furta abu guda ɗaya dai-dai da lumshewar idanunsa a hankali (Wata rana gaskiya za ta dawo da kanta. In dai har zuciya bata manta da UBANGIJI da masu gaskiyar ba) sai kuma a hankali ya ajiye Alkur'anin ya zame zuwa sujuda. Ya jima kafin ya ɗago ya sake ɗaga hannu yana ambaton, “Subahanal-lah! Allahu-akbar!”. Akan tausasan laɓɓansa
Bai ce ya damu da samuwar shugabancin Janar Tafida domin ya fita anan ba, amma tabbas ya damu da addu'ar ƙasar nan tasamu mai kishin ƙasa kamar Janar da yakema ƙyaƙyƙyawan fata akowane motsinsa, ta samu shugaba mafi alkairi, yana ji kuma a ransa ogansa kuma yaya koma uba shine zaɓin ALLAHn da suke fata da roƙa in sha ALLAHU. Sake juyawa yay yana kallon tvn a karo na biyu, dan duk da sanarwar dare ce wasu wajajen har al'umma sun fara bikin murna, sauke numfashi mai nauyi yayi, zuciyarsa tana ƙonewa irin ƙonawar da MAZAN FAMA kawai ke iya fuskanta a lokacin da suke iya hango HASKEN MASU GASKIYA......
÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷
★ONE WEEK LATER★
Sati guda kenan da bayyana sakamakon zaɓe. Janar da ubannin gidansa dama talakawan ƙasa da suka zaɓesa sun sha shagulgulan biki tako wane ɓangare. Idan ka cire sauran mabiya sauran jam'iyyu dake cikin takaici da baƙin cikin rashin samun nasara. Sai dai abinda mu talakawa da muke a wannan yanayin basu fahimta ba. Su waɗan can manyan da suke so tuni sun ƙulle da Janar ɗin anata farin cikin samun nasara. Sai a kafafen media ne kawai suke suka da nuna rashin jin daɗi. Duk da kuwa da yawansu har cikin zuciyarsu suna jin rashin daɗin, amma suna shanyewa saboda a hakan ma dai da ai dasu za'aci gwamnatin tunda dama duk tafiyar ɗaya ce a baɗini, a zahiri ne ake daban-daban.
A lokacin da nan ake faman bidirin farin ciki ga sabon shugaban ƙasa janar Yusuf ba haka bane ba. Duk da bai kai ga tarewa a gidan Gwamnati ba aikin suke ta ƙarƙashin ƙasa shi da Daddy Imran da Haydar Galadima (Faro).
Dan a yanzu haka a yau Janar Tafida ya gama ganawa da kwamitin miƙa mulki da sukai zaman meeting da tunda aka ci zaɓen nan shi suketa zamanyi saboda tsare-tsare musamman ƴan jam'iyya da kowa ke ganin lokacin fanshe wahalarsa tayi za'a bashi muƙamin da yake buƙata. Suna fitowa daga meeting ɗin aka ɗaukeshi zuwa gida. Tun ma kan ya ƙarasa shigewa falon sashensa ta baya kasancewar gidan bashi cike yake da dangi sati guda kenan ya ciro wayarsa a aljihu ya fara neman layin Daddy Imran.
Bugu biyu Imran ya ɗaga, dan a lokacin shima suna tare da Faro ne a wani guesthouse ɗinsa da in har zasuyi magana akan Dada can suke zuwa.
A nutse Daddy Imran yay sallama tare da gaishe da Janar. Daga nan ya amsa masa sai dai Daddy Imran baya jinsa sosai sakamakon matsalar rashin network da kowa ya sani ƙasar na fuskanta. Hakan ne yasa Janar ɗin faɗin, “Ka na ji Imran?”.
“I’m here, Sir.”
“Yauwa ina fatan kun kammala dukkan abinda muke buƙata?”.
“Yes sir! Yanzu haka ma ina tare da Haydar anan guesthouse ɗina. Ga komai daya dace a hannunmu ko abu guda bana tunanin mun bari yayi saura. Hatta da sabbin bayanai akan Ojo Dabo ya zo da su a daren jiya, sune kawai nake ganin zanyi ƙoƙarin tabbatarwa dan nima akwai wasu a hannuna”.
“Babu lokaci Imran, inaga ku ajiye sabbin bayanan Ojo yanzu a hannunku, muyi amfani da tsoffin dake wajenka zasu wadatar. Dan wannan aikin shine farko da nake son na gabatar a ƙarƙashin mulkina a ranar dana taka ƙafata a gidan gwamnati in sha ALLAHU washe gari sake nazarin shari’ar Haysam Abdul-rasheed Shehu zai tabbata. Babu wani aiki da zan gabatar na tabbatar da godiyata ga ALLAH sai in fara da wannan. Dan haka ku kasance cikin shiri kawai”.
Daga can Daddy Imran ya runtse ido yana sakin wani wadataccen murmushi mai faɗi da armashi, dan yana jin kamar an buɗe wata ƙofa da ta rufe a zuciyarsa da ƙwaƙwalwa a shekaru takwas da suka gabata, ƙofar dawowa, ƙofar adalci, ƙofar fansa.
Cike da wata irin muryar shauƙi ya furta, “Sir! Umarninka kawai muke jira a wannan gaɓar”.
Murmushi mai faɗi shima Janar ya saki, tare da faɗin, “Imran… ka shirya abinda na tambaye ka?”.
“Na shirya Ranka ya daɗe. Na dawo da kowace takarda, kowace sanarwa, kwafe-kwafen shari’a, rahotanni, bincike, duk wani abu na shekaru takwas ya kammala a cikin kundi guda ɗaya. Kundin da saka hannunka kawai yake buƙata da umarni yayewar baƙin labulen daya rufe min gani da jin Zak-Shadow. KIƊA A RUWA MAI TADA HANKALIN DODONNI.”
“Good Imran. Lokaci ya yi da zan sa hannu wajen dawo da gaskiya. Lokaci yayi da The two shadows zasu sake bayyana a inuwa ɗaya. Amma…” ya ɗan yi shiru, sai kuma ya cigaba da faɗin “......ba za mu je tare da kararrawa ba.”
Daddy Imran ya fahimta. Aikin da aka basu ba na kan titi ba ne. Yana cikin inuwa, cikin sirri kamar yadda azzalumai ke yin wasan su. Tamkar yana a gaban Janar ya ƙame jikinsa waje guda irin aƙidar sojoji da girmamawarsu, sannan ya sara masa da Salute na girmamawa mai harsuna da yawa har Janar na iya jin ƙarar bugawar ƙafafunsu shi da Faro da shima ya miƙe ya ƙame. A tare suka furta, “Yes, Sir. I'll handle it quietly”.
Daga can shima Salute ɗinsu Janar yayi yana wani shegen murmushi mai matuƙar bayyana tsantsar makamancin farin cikin da yake a cikin zuciyarsa. Daga haka ya yanke wayar. Ba ajiyeta yayi ba, sake lalubo wata number yayi. Lambobi ne da ba kowa ke da su ba, lambobin da suka tsaya tsayin shekaru biyu babu wanda ya kira shi da su. Badan bai isa ba, sai dan shiri irin na masu makirci dake da dama a hannu. Sai dai yau shi zai kira, kiran da dole a ɗauka masa kuma a risina masa, dan wannan kiran ya zama dole ga masu amsawar..
A bazata kiran tsohon Janar ya shiga wayar babban hafsan tsaro da zai hau aiki tare da shi a sabuwar gwamnatinsa. Kiran daya saka General a ƙaulani, firgici, ruɗani duk da bai san takamaiman dalilin sa ba. Amma shi ya san jiya ba yau bace, ko giyar waye yasha bai isa hana kansa amsa wannan kiran ba a yanzu. Cike da rawar jiki kuwa ya amsa, cike da girmamawa da risinawa da ƙanƙan da murya ya fara gaishe da tsohon Janar ogansa a gun aiki, sabon shugaban kasar sa mai jiran gado kuma a yanzu.
Janar Yusuf Shu'aibu Tafida yay wani murmushi mai ma'anoni da yawa yana mai jinjina kai. Lallai ƙasa ta lalace, lalacewar da mutane sun koma girmama kujerun iko sama da girman daraja da kimar ɗan adamtaka da UBANGIJI yayi ma bayinsa. Bai ja tunaninsa da nisa ba ya fara magana ba daɗi, ba sirri mai nauyi, amma da umarni.
“Ina bukatar sashin ku ya fara nazarin batun jami’in SOJA da aka jefa cikin gidan maza shekaru takwas da suka wuce. Ba tare da hayaniya ba.”
Cikin matuƙar bugawar zuciya Genaral ya furta, “Sir! Zak-Shadow?”.
“Eh. Na san akwai ɗan hazo. Ina so ku share min hanyar ganin shi cikin sirri kafin na shiga ofis.”
Yawu mai matuƙar kauri Genaral ya haɗiya jininsa na tsitstsinkewa, a take zufa ta jiƙe jikinsa sharaf. Ya kasa magana har sai da Janar Yusuf yay gyaran murya irin ta manyan da umarni kawai suke badawa sau ɗaya tak.
Kamar wanda aka farkar a suma General ya amsa da sauri har harshensa na sarƙewa. “Za’a yi, Ranka ya daɗe. Amma wannan… zai bugi wasu mutane.”
“Ai dama so nake ya buge sun da bulala mai zafi da dafi. Dan lokaci yayi da zasu ji su kuma sani. Gaskiya ba ta tsorata da MAKIRCI ko ƘARFIN IKO. Gaskiya ce take tsoron TUGGU