Author : Billyn Abdull Category : African Stories & Novels
koda MAKIRCI yayi nasarar ƁOYETA.”
General ya kaɗa kai kamar tsohon ƙadangare dan ya kasa magana ma. Sai sake wanke masa jiki zufa take dan tabbas a wannan gaɓar yana a tsaka mai wuya ne.....
<<%>>★<<%>>
PRISON
*8:30pm* aka samu baƙuncin jami’an tsaro na musamman, dole a kirasu jami'an dana musamman, domin ko sun iso ba tare da hayaniya ba balle yanayin rububi. A nutsensu suke cikin Uniform. Kai tsaye kuma sun nema ganin shugaban prison ɗin ne ta hanyar bama securitys ɗin dake kula da shiga da fitar kowa takarda.
KIƊA A RUWA 2
30
.........Isowarsu ɓangaren da Dada yake ya tabbatar min da lallai ba wannan jami'an bane ainahin vistors ɗin, dan a ƙofar wajen suka samu wanda akaima rakkiyar. Bayan sun ƙame tare da salute ɗinsa ɗaya ya matsa yana sanar da ogan nasu cikin magana ƙasa-ƙasa. Kansa kawai ya jinjina batare da yin magana ba, kuma ba'a ganin fuskarsa dan ya saka norse mask ga eyeglass, sannan kansa da hula p-cap data sake ɓoye ainahinsa. Yana sanye cikin ƙananun kaya daga sama har ƙasa baƙaƙe.
Har cikin ainahin ɗakin ganawar securitys ɗin sukai masa rakkiya, dan shi kaɗai ya shiga banda jami'an sa. Koda suka nuna masa kujerar zama bai zauna ba, yana daga tsaye kawai a cikin dakin yana jiran shigowar wanda zuciyarsa ke bugawa saboda tsoron abin da zai gani, tsawon shekaru biyar har da wattani huɗu a kai bai ga Zak-Shadow koda daga nesa ba. Mintina kaɗan da suka kasance masu nauyi na cika wanda yake begen gani da ƙagauta ya iso.
Cak numfashinsa yaso tsayawa sakamakon bayyanar mazan fama, sosai ya rame fiye da wancan ganin da yay masa na shekarun baya. Duk da lokaci-lokaci ana masa aski hakan bai hana gashin saje taruwa a farar fuskarsa ba da kansa. Fata kam tayi haske da kwanciya saboda zaman waje guda. Sai dai baza'ace akwai laushi na jin daɗi ba. Yanda yake kallonsa haka shima Dada ke kallon nasa, dan duk da ya rufe fuska a kallo ɗaya ya gane wanene, dan ko cikin rububi manta wannan halittar ta gabansa sai dai ɗimuwa a lokacin magagin mutuwa amma ba a cikin hayyaci ba.
A karo na farko baƙon ya ɗan murmusa da ƙoƙarin danne abinda ke yunƙuro masa. Sai kuma ya kai hannu a hankali ya zare glasses ɗin idanunsa. A tare idanuwa nasu suka haɗu a cikin na juna. Imran ya kasa motsi. Haka shima Dadan bai motsa ba, dan kai tsaye zuciyarsa yake kallo a zahiri.
Fin sakan talatin suna a haka kafin Dada ya saki wani ɗan murmushi da lumshe idanu ya buɗesu a lokaci guda, a hankali ya cigaba da takowa har inda Imran yake. Har yanzu nutsatstsiyar fuskar nan tasa da murmushin nan nashi na ƙasaita, ya motsa lips kamar mai son raɗa ya furta, “Ranka ya daɗe, soja… har yanzu baka daina kuka da ido ba?”.
Kauda kai Daddy Imran yayi yana haɗiye hawayen da basu ƙaraso cikin idanunsa ba, amma da yake Zak-Shadow ɗin nasa Zak-Shadow ne shi har ya karantosu daga ƙirjinsa.
Wata ƴar ƙaramar dariya Dada ya saki da kaiwa zaune, ƙafarsa ɗaya kan ɗaya hannayensa da yau babu handcuffs harɗe a ƙirjinsa ya sake faɗin, “Sit mana my Boss”.
Yanzu kam shima murmushi Daddy Imran yayi, sai kuma ya gyara kujera ya zauna irin zaman Dadan suna kallon juna tamkar wani saurayi da budurwa.
“Na yi missing naka sosai, Zak...” kalma mafi nauyi da girma dake riƙe da zuciyar Imran ta fito daga bakinsa. Sai kuma hawaye suka cika masa idanu.
“Idan ka cigaba da wannan kukan, how many missions za ka gama?. Kalleni da ƙyau ina raye, kuma ina cikin ƙoshin lafiya mi kake buƙata bayan hakan daga UBANGIJI? Ko sai na tashi mun gwada ƙarfi ne?”.
Dariya sosai Daddy Imran keyi cikin hawaye, dan ya fahimci yau raha Zak.. ɗinsa ke ji. Kai tsaye ya ce, “Kai dai ba zaka canza ba.”
“Zama da kai ne Imran, kwana biyu sai nake jin matsanancin kewar ka. Ashe kana gab da ni ne shiyyasa.”
“Duk randa muka zama a nesa da juna lallai ƙasa ta bizne idanun wani a cikinmu ne ko mu duka. Sai dai ni nafi fatan fara tafiya na barka dan nasan bazan iya ɗauka ba idan kai ne ka barni”.
Idanu sosai Dada ya zuba masa. Dan haka shiru ya biyo baya, irin shirun nan mai cike da abubuwan da bazasu faɗu ba. Tsohon lokaci kafin Daddy Imran ya katse yanayin nasu ta hanyar miƙa masa briefcase daya shigo da ita.
“New President Yusuf Tafida… ya buƙaci nazarin shari’arka tun daga farko har ƙarshe. Sai dai ba yau za mu faɗi komai ba. Amma daga yau ɗin game ya fara dawowa.”
Cak numfashin Dada ya tsaya ba ƴan sakanni, ya kuma zuba ma Imran ido tamkar zai haɗiyo shi da su, “Sabon shugaban ƙasa, zai iya zama yana da alaƙar huɗɗa da waɗanda suka karyar da ni fa Imran, sai dai maybe shima bai sani ba.”
“Miyasa kai wannan tunanin? Dama ce fa tazo mana daga UBANGIJI. Kafa san wanene Janar”.
“Tabbas nasan Janar, sani na nagarta da mazantaka. Ba kuma bana farin ciki da damar bane, ina ganin kamar yazo da gaggawa ne, gaggawar da zasu iya kaishi ƙasa da ita a kaina, dan yazo musu da bazatar abinda ba shi suke hasashe ba a kansa. Dole ya zama mai zaɓi biyu a lokacin da ya bayyana musu ainahin fuskarsa a kaina. Saboda a tsarinsu babu wani shugaban ƙasa da zai kasance baya abota da su. Koda sun ɓoye masa waccan fuskar tasu a yanzu inada tabbacin zasu bayyana masa ita ya sansu ya san aikinsu. Matsalar kuma idan har yana son gaskiya, to sai ya tabbatar min da hakan da aikin shi. Ba da kalamai ba. Dan kar ya kasance na amince na fita ya zama yana cikinsu bazan ƙyalesa ba koda shine Abdul-rasheed Shehu Isa Kobi”.
Daddy Imran ya fahimci hangen Dada, dan haka ya sauke numfashi mai nauyi yana jinjina kansa da faɗin, “Haysam na yarda da ku kai da Janar da Faro. In sha ALLAHU Janar bazai bamu kunya ba, yanda muka fara da shi zamu ƙare a tare koda sai bayan babu ran mu ne NASARA zata bayyana. Na tabbatar shima kamar mu ya ke, idan gaskiya tana gona, zai haƙo ƙasa ya nemota da kansa.”
Dada yayi murmushin mai zafi fiye da bala’in da yake hangowa da ƙurar da zata tashi. “Shike nan Imran! ka gaya masa, idan yana neman gaskiya, kada ya zo da haske. Duk wanda yake neman ƙasar nan, sai dai ya biyo duhun dare. Ni zan fara jiranku daga yau. Ku dinga tuna kuma zan dawo da gudunmawata. Game on.... again.” yay furucin ƙarshe da wani salo yana kashema Imran ido ɗaya da yin alamar harba bindiga da yatsu biyu.
Dariya Imran ya kece da ita, irin dariyar da shi kansa yasan ya jima baiyi ta ba. Kai koda kwatance baya kawota a zuciyarsa balle ma fuskarsa. Shima Dadan kallonsa yake yana wani shegen murmushi mai bayyana haƙwara, kai daka gansu kasan ƙara'in farin ciki ne na tsahon shekaru ke fidda kansa tun daga ƙasan zuciya har zuwa fuskokinsu. Sai dai Imran yasan minene ma'anar murmushi irin wannan a fuskar Zak-Shadow ɗinsa. Ya tabbatar zafin daya jure cikin wannan duhu na tsawon shekaru takwas da wata huɗu, sakamakon wannan murmushin idan ya fito ƙasa za ta sake girgiza......
<%><%><%><%>
“Malam Almu maganar ciwo ai ta wuce wasa, kuma ta kori komai a rayuwa. Dan haka babu batun neman alfarma zuwa gida daga garemu. Ka shirya kawai abinka ga kuɗin mota. Wannan kuma sai kai amfani da shi wajen kaita asibiti, ALLAH ya bata lafiya yasa kaffara ne. Zaka wuce yau ne ko sai zuwa gobe? Dan muma zamuje airport ne ɗaukar Bilal yau zai dawo”.
“Kai kai Masha ALLAH. Yau Alhaji Bilal zai dawo ashe? To bari na jira ya dawo tukkuna ai kamar zai fi”.
Kai tsaye Mammah dake saurarensu ta ce “A'a Malama Almu ban goya bayan haka ba, kaje dai tunda zaka dawo ai. Itama Innarka na buƙatar ka, kuma tana buƙatar a kaita asibiti. Ina ga ma idan kaga jikin babu daɗi sosai kawai ka ɗakkota zuwa goben ku taho nan a kaita asibiti zai fi”.
Godiya maigadi yake jerama Mammah dasu Yaya Ja'afar har hawaye na cika masa idanu. Yana tausayi da mamakin alkairan bayin ALLAHn nan, shiyyasa a lokuta da dama idan ya tuna dalilinsa na zaman gidan nan tare da su sai yaji zuciyarsa na karaya akan ƙudirinsa. Haka ya miƙe yana shartar hawayen da shi kaɗai yasan dalilinsu ya fita...
A gurguje maigadi ya shirya tare da damƙa gate a hannun sabon driver kamar yanda su Ja'afar suka ce masa. Ya wuce ya tafi yana ayyana wa a ransa ai bazai wuce jibi ba, idan har zuwa kwana uku bai dawo ba to bazai wuce safiyar kwana na huɗu ba in sha ALLAHU. Dan babu wani ciwo da Innarsa keyi kamar yanda ya faɗa, ogansa ne ya bashi umarnin zuwa ya sameshi da gaggawa a yau.
Saboda shi Innarsa ma ta jima da rasuwa, a hannun kishiyar uwa ya tashi, azabar data bashi da wahala ta maida shi yanda yake a yau, sai dai a gidan Mammah sanin mutum cikakke sukai masa mai nagarta sakamakon ɓoye ainahin wanene shi da yayi a garesu....
Tofa, wata sabuwa maigadi🤔🤐🏃🏼♀️.
÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷
★DUBAI★
Duk yanda su Hajiya Hasiba suka so tafiya India bincike akan Adeel bai yiwu ba. Dan kuwa randa ta samesa da dabarun zuwa India business a ranar yace mata ya kammala shirin tafiyarsu. Ta jira har su dawo sai taje. Kota sanar masa business ɗin da kamfanin da zasuyi koma miye a kawo mata shi. Jin haka yasa ta saurin cewa ba damuwa suje ɗin kawai su dawo tayi nata uzirin daga bayan.
Shirin nashi bai bata tsoro ba sai da ya tabbatar mata harda su Nabeeha za'a. Ta tambayesa ba'asi yace hankalinsa zaifi kwanciya idan tana acan tare da shi. Dan karma ya barta anan wani abu ya faru. Duk da kuwa yana da ƙarfin ikon sakawa a bibiyar masa ita duk inda ta shiga a cikin ƙasar. Amma baya buƙatar hakan, dan bayan abokinsa ɗaya jal babu wanda yasan yana bibiya ko son auren Nabeeha.
Abinka da sai yanda akai da kai, dole suka hau shirin tahowa. Sai dai ran Nabeeha da Ismat fal farin ciki. Hakama Mamawo, dan koba komai itama akwai nata shirin data barma tata zuciyar game da Adeel ɗin, tana ganin kuma zuwansu ƙasar tasu ce zai iya cika cikin sauƙi saɓanin anan da wasu dalilai zasu iya hanata. Amima da Raihana ko basu so wannan tafiya ba. Dan harga ALLAH su daɗin zaman Dubai suke ji, har basa son tuna zuwa ƙasar haihuwarsu. Shiyyasa ma suke matuƙar jin haushin Nabeeha da taƙi bada haɗin kai bori ya hau. Dan wlhy da a cikinsu Adeel ya nuna yana son wata hohoho da wani labarin ake ba wannan ba ma..........✍️
31
........Sun iso cikin dare. Kasancewar a babban birnin suka sauka yay bucking hamshaƙin hotel na gani na faɗa da yafi kowane hotel tsari da ƙayatarwa. Su kuwa gidan Hajiya Hasiba suka sauka. Dan tun a can ya nuna musu baya son asan tafiyarsu ɗaya da shi har ya kammala aikin nasa su koma.
Ba laifi gidan babba ne sai dai ba ƙato ba. Six bedrooms ne. Sai faluka guda uku. Akwai na baƙi da bedroom ɗaya, sai falon ƙasa shima da bedrooms 2, sai upstairs da falo da 3 bedrooms shi kuma. Akwai kitchen a ƙasa. Sai can gate akwai ɗakin maigadi. Shi kaɗaine kuma a gidan da matarsa da yaransu biyu. Kasancewar idan suna nan itace ke musu aiki. Dan haka tun suna can ta sanarma maigadin zuwansu. Haka matar ta yini yau tana ƙalƙale gidan, da yamma mai musu abinci tazo tai musu, sai da ta shirya komai a dinning sannan ta wuce dan dama ba'a nan take kwana ba.
Tun kan Hajiya Hasiba ta shiga siyasa tana da kuɗi, dan kuwa tako wace hanya nemansu akeyi. Alaƙarta da manyan ƙasar musamman first lady ya sake armasa dukiyarta da sanin manyan mutane da ake harkokin da basai ance komai ba (🥱🤭🤫), ko wannan gidan ƙyautarsa aka bata sukutum kamar juye alalar gwangwani a plate 🥱🤣. A yanzu kuma ga Adeel ya ida jiƙeta.
Duk da ba wata gajiya ce a tare da su ba kowa sai wayyo-wayyo yake yi. Duk suka zube a falon ƙasa suna sauke numfashi, maigadi da matarsa nata kai-kawon shiga musu da kaya da jera musu sannu. Da ƙyar suka iya tashi bayan wani lokaci suka haye sama su duka. Dan duk can suke da ɗakunan barci har Mamawo ɗin ma daba wani zama take sosai a ƙasar ba. Wanka suka fara gabatarwa sannan suka nema abinci. Suna kammala ci kowa ya nema makwanci. Basu tashi farkawa ba a washe garin ma sai ƙarfe kusan sha biyu. Haka sukai wanka suka sakko ƙasa neman abinci. Sunko samu Joy ta kammala komai har na rana, aiko suka far masa da ci sai da kowa yay ƙat.
Wajen ƙarfe uku Nabeeha tace tana son zuwa gidanta ɗakko wani abu. Aiko daga Mamawo har Momyn tasu suka hayayyaƙo mata da masifa. Da farko shiru tai musu, sai daga baya ta saka musu kuka. Jikinsu ne kuma yay sanyi, dan haka Momyn tata tace ta shirya amma su Ismat ne zasu rakata su dawo tare, amma yau yamma tayi ta bari sai gobe. Bata musa ba tace ta yarda.......
<<%>><<%>><<%>>
Kamar kullum yau ma a dai-dai lokacin da aka saba tashinsu islamiyya aka tashe su. Kasancewar Yaya Mu'azz ne ya kawosu sun tabbatar bazai zauna zaman jiransu ba kamar driver har zuwa yanzu. Sai dai zai dawo ya ɗauke su. Su duka zukatansu cike suke da zumuɗin komawa gida saboda Uncle Bilal, dan ba ƙaramar kewarsa sukai a watannin nan da baya nan ba. Sune farko fitowa a aji, ajin nasu kuwa daga shi sai na ƴan sauka, duk da suma dai gab suke da kaiwa sittin ɗin in sha ALLAHU.
Hayaniyar dake tashi a ajin ƴan saukar ne ya daki kunnuwan su Nimrah da suka fara fitowa, kallon juna sukai ita da Ruky, sai kuma suka nufi ajin da sauri dan ganewa idanunsu abinda ke faruwa. Gaba ɗaya ajin ya hargitse da ɗaliban ƴammata da samarin cikinsa, dan kuwa sun girmi su Nimrah su zasu iya kaiwa sha bakwai ne. Yanda suka dunƙule waje guda suna jefe-jefen takalmansu yasa Nimrah data kutso kai cikinsu kallon abinda suke jifar. Abin takaici abin mamaki ba komai bane sai mage. Wata baƙar mage ce da jariran ƴaƴanta biyu, ɗaya fari tas ɗaya baƙi da kwalliyar golden a jikinsa. Mai kwalliyar golden ɗin na kwance kansa da jini alamar wani ne ya jefesa, farin kuwa ya maƙale jikin uwar da itama har an jimata ciwo sai wani irin nishin kuka take. Ai bama tasan ta zabura inda magen take ba jikinta na rawa.
Ihu ƴan ajin suka fara mata da kiran karta je ba mage bace aljana ce ko wata mayyar ta rikiɗa tunda ance mayu na zama mage, amma kota kansu batabi ba ta ƙarasa. Hannu ta saka ta ɗauki magen ta rungume, tare da ɗaukar farar itama dake jaririya abin sha'awa, tana kai hannu zata taɓa golden ɗin dake kwance a ƙasa kawai cikin ƴan ajin wani ya wulwulo dutsina har biyu. Ai ko ɗayan ya sauka akan magen babba ɗaya akan Nimrah.
Juyowa Imam yay yana hararar Ruky da tai maganar. Kafin yace wani abu cikin sake lanjarewa Nimrah ta ce, “Dan ALLAH Yaya. ALLAH su Afry ma naso ko?”. Ta juya tana kallon su Aheel. Magiya suma suka fara. Sai lokacin Mu'azz daya ɗan juyo ya hararesu ya sake maida kansa ga titi sannan yay magana. “Ku yaran nan kun cika nemarwa mutane hanyar kashe kuɗi. Ga asarar salla a jam'i da kuka jawo mana. Wai kun manta yau Uncle Bilal zai dawo ne”
Su dai basu kula faɗansa ba suka cigaba da maguyarsu duk da ransu cike yake da farin cikin batun dawowar Uncle Bilal da zaiyi a daren nan. Sai da yay ƙwafa sannan ya rage gudun motar. Canja hanya yay zuwa inda yasan ana saya musu ice-cream ɗin da suke so. Basu wani jima ba suka iso. Har zasu fito ya hararesu yana faɗin, “Ina zaku bimu da uniform a jiki ace satoku mukayi, ke kuma ga rauni a kai”.
“Abinda ba'a ganin ciwon na rufe da hijjab. Dan ALLAH ka barmu muje”. Nimrah ce mai maganar cikin tura baki. Mu'azz zai ƙara magana Imam ya ce, “Barsu dan ALLAH Bro. Muje, muna sake tauye lokacin salla ne kawai a wannan surutun”.
Ba yanda Mu'azz ya iya yayi gaba suka bishi, Ruky harda masa gwalo. Su Imam na gaba riƙe da hannayen su Abees, su kuma suna biye da su,