Author : Billyn Abdull Category : African Stories & Novels
jikin Mammah da nasa. Ya ɗan sauke ajiyar zuciya daga cikin ƙirjinsa, shi ba abin ya motsa ba ko sanar mata ba Mammah da take tunani bace girma yay tangal-tangal. To mima ya kaishi wannan gangancin, ai gara ya barta kawai yanda ƙafarta ta kawota ta fitar da ita, ko shi zuwa anjima idan tayi barci ya sulale yabar mata ɗakin. Dan da yasan ma suna shigowa kwana irin haka da bai kawo kansa ba shi kam... Tunaninsa ya tsaya cak, saboda yanda ta juyo gaba ɗayanta yana fuskantar sa. Yanda ta sake ƙanƙamesa dole ya lumshe idanunsa dake cike da son yin barci yana ɗan cizar lips. Sai da ta gama mutsu-mutsunta dan kanta ta nutsu tana sake mamuƙeshi sannan ya saki numfashin daya riƙe a cikin ƙirjinsa. A haka ya fara jin saukar ɗumin numfashinta a hankali cikin jikinsa. Tun yana saurarenta har shima barcin yay awon gaba da shi batare da ya farga ba, dan ya gaji matuƙa, ga magunguna da yake sha na saka shi barci dama. Ga hayaniyar daya sha yau tasu da yawan magana da aka saka shi.....
Ƙarfe uku dai-dai ya farka, sabo da tashi sallar dare yasa komai nauyin barcin da yake ciki idan lokacin yayi sai ya farka. Idanunsa ya buɗe a hankali, tare da karanto addu'ar tashi barci a saman lips ɗinsa. Ya motsa hannunsa da nufin kunna lamp yaji ya masa nauyi, ya ɗan laluba da ɗayan sai yaji mutum. Abinda ya faru a farkon dare ne ya faɗo masa. Ya ɗan cije lips ɗinsa kaɗan yana kai hannun ƙasan pillow, ALLAH ya taimake sa ya samo wayarsa. Dannata yay screen ɗin ya kawo haske, kai tsaye hasken ya faɗa kan kyakkyawar black beauty face ɗinta. Cikakkiyar girar ido da eyelashes da suka dace da girman idanunta, hancinta dake zaune ɗaram a fuskar tata da madaidaicin bakin tsiwa mai pink da baƙi. Cike da kame kai irin na manyan jarumai da nutsuwa ya janye idanun kai kace baiga komai ba ma. Sai ma zameta ya shiga yi a hankali daga jikinsa data kanainaye dan gaba ɗayanta a rabin jikin nasa take, yanda har ya gyara mata kwanciya ya ja bargon ya rufa mata bata ko motsa ba sai ma filon daya saka mata a madadinsa ta sake kanainayewa ya sashi fahimtar tana da nauyin barci, sannan ta saba da wannan rungume filon shiyyasa shima ta masa ɗaurin goro batare data fahimci shi ba filon nata bane ba.
Bedroom slippers ɗinsa ya saka ya fice a ɗakin dan gwara salin alin ya bar mata ɗakin ya koma inda ya baro ya ƙarasa daren kada a tafka abin kunya. Ko'a mafarki bazai so ta buɗe ido ta ganshi ba balle tasan abinda ya faru.....
★Itama saboda da tashi sallar asuba ya saka ta farkawa a kiran sallar farko. Duk da suma Mammah ta horesu da tashi sallar dare tun basu kai hakan ba. Yau ma dan alluran da doctor yay mata ne sukai tasiri wajen ƙara nauyin barcinta yasa har bata farka ba a lokacin da sukan tashin. Cikin lalube take kiran sunan Mammah, sai dai jin shiru da jin gadon empty sai ita kadai yasa ta buɗe idon. Dama tasan da wuya Mammah takai yanzu a gado bata sauka ba, dan ita in har ta tashi sallar ta ta dare bata sake komawa gado kuma sai in barcin rana.
Nimrah na buɗe ido ta maida ta rufe saboda ganin duhu. “Mammah baki kunna fitila ba? Wayyo duhu ba ƙyau”. Tayi maganar ne da mirginawa gefen gadon cikin lalube ta taɓa makunnar lamp. A take kuwa ɗakin ya gauraye da haske, sannan ta buɗe idanun. Ɗaki dai shiru babu alamar Mammah a ciki, dan haka ta shiga waige-waige, sai kuma ta zubama inda alamun kwanciyar mutum ta nuna idanu. Ta ɗauke ta maida toilet, sai dai tsin babu alamar motsin ruwa a nan ma, dan haka ta sauka a gadon gaba ɗaya. Kamar yanda suka saba gyara gado da sun farka yasa ta janye blanket ɗin da filos tahau ƙoƙarin gyarawa. Ta kammala tana maida filoluwan idannunta suka sauka akan baƙin agogon dake a side drawer, mai ƙyau da tsada da tambarin sunan mawaad Company. Daga gani kasan an saye shi da kuɗi masu nauyi.
Bata kawo komai a ranta ba ta ɗauke idanun nata ta ƙarasa aikinta. Tunanin Mammah na bayin yasa ta fice abinta zuwa ɗakinsu.
Ta samu suma su Biebah duk sun tashi, dan daga ita har Ruƙayya akan sallaya ma suke. Ruky na Sallah Biebah na karatun Alkur'ani. Sai ita ma ta wuce bayi abinta. Da yake sheɗan sheɗan ne sai da ta kabbara salla ya tuna mata a hannun data ga agogon nan da rana. Sai ko da ƙirjinta ya buga, da ƙyar ta iya ture tunanin a ranta ta cigaba da sallarta. Suna idarwa kuma suka hau tilawar Alkur'ani dan yau akwai tahfiz akwai kuma amsar hadda. Wannan ya sake mantar da ita batun agogo na wucin gadi.........✍️
56
..........8:30am suka fito cikin shirin tahfiz, Mammah ce kawai a falon zaune tana shan shayi. Su Kulu sun gyara ko'ina tsaff sai ƙamshi ke tashi kamar me, dan zuwa yanzu ƙamshin turaren SHUWA INCENSE AND MORE +234 704 229 3387. Suna da turare wuta da khumra kaloli har uku: black humra, white humra, brown humra. Akwai oil perfume da kullacham da genine da Turare kabasa kaloli uku shima. white, black, and brown. Akwai man kitso, da kayan gyaran jiki masu gyara fata da sanyata laushi da santsi kiyita glowing abinki hajjaju. Sun gama kama gidan tako ina. yanda Nimrah da Ruky ke faman tuttura baki gaba yasa Mammah faɗin, “Oh oh mi akama Autaras ɗin Mammah? Kuzo naji”.
Inda take duk suka nufa, yayinda Biebah ke faɗin, “Yo Mammah miza'ai musu, halin ne ya motsa makarantar ce basa son zuwa”.
Rungumesu Mammah tayi tana faɗin, “Su dai basu ce ba Biebah, zasuje makarantar su ko?”. Tai maganar tana taɓa wuyan Nimrah. “Kinga babu ma zazzaɓin”.
Sake langaɓe mata sukai suna shagwaɓar su, dai-dai nan Mu'azz da Ammar da suka fara sakkowa daga stairscase, cike da neman tsokana Mu'azz ya kalli su Nimrah da suka tashi daga jikin Mammah zasu je dinning ke faɗin. “Tunda kaga Zakanya da Damisa na kumbura yau akwai ɗaukar magana a makaranta kenan.”
Ammar dake dariya ya ce, “Kada ka musu sharri”.
“Hummm ALLAH Uncle baku fahimce su bane, duk randa yaran nan basa son zuwa makaranta ka kula sai sun ɗakko magana. Kuma zaka ce nina faɗa maka. Kai dai kabar wayarka a kusa da kai kawai, dan nasan za'a kiraka, bare ma kwana biyu basu tafka ta'asar ba”.
Hararasa kawai su Nimrah sukai basu ce komai ba, Mammah dake hararar Mu'azz itama ta ce, “Kar ku kulashi kunji ƴan albarka. Maza kuje ku karya kar ku makara.”
Gwalo suka masa suna matsawa suka gaida Uncle Ammar dake musu dariya. Dai-dai nan suma su Ayyan suka shigo da gudu cikin nasu shirin. Afrah ta faɗa jikin Nimrah. Sosai bakin Nimrah ya washe da farin ciki, ta ɗauketa suka wuce Dinning dan Biebah da Mu'azz har sun ƙarasa. Yanda suka cika falon da uban surutun su sai ka ɗauka wata gayya ce guda. Mammah da Ammar na daga falo suna tasu hirar. A haka su Yaya Ja'afar suka shigo falon tare da su Shariffa. Cikin girmamawa duk suka gaida Mammah, ta amsa musu da kulawa tana tambayar ya jiki-jiki. Su duka kunya ta hana su amsawa sai murmushi da sukai suna duƙar da kawuna. Sai ga Bilal shima ya sakko, yanda yake ɓata fuska yasa Yaya Ma'aruff tambayarsa lafiya?. Sashen Dining ya harara da faɗin,
“Wlhy yaran nan sun hana ni barci Yaya”.
Shima su Nimrah dake kwasar dariyar abinda Ayyan yake yi ya kalla. Sai kuma ya dawo da kallonsa kan Bilal ɗin yana faɗin, “Ai kai ke ɗaure musu ƙugu dama idan sana wani abun. Sai ka bari su tafi ka koma? Dada fa?”.
“Inaga yana barci shi ma, tunda muka dawo massalaci ya sake shigewa. Yauwa Mammah yaran nan fa kwana biyun nan basa fita sallar asuba wlhy. Dan yanzu haka Dayyan baiyi ko salla ba”.
Tsaki Ammar yayi, cikin takaici ya ce, “Shiyyasa na baro masa ɗakin, nafa tada shi yafi sau uku amma yaƙi tashi. Sai kace wanda yasha wani abu. Ni dai Mammah yau kisa a gyara musu ɗakin baƙi su koma gaskiya”.
Caraf Biebah dake isowa wajen ta ce, “ALLAH nima ƙorafina kenan Yaya. Ita waccan sai latse-latsen wayar banza, ta dameni da charting da dare da dariya.”
Ja'afar da sai yanzu yay magana cikin takaici ya kalla Mammah shima. “To wai tunda sun gaishe mu su koma gida mana? Idan shi Babban ya gama makaranta su kananun fa?”.
Rasa ma abin cewa Mammah tayi, dan gani take taron dangi suke neman yi mata ita kam. Cikin sa'a takun sakkowar Dada ta saka wani bai sake magana ba, sai ma maida hankali sukayi ga stairscase ɗin. Su ko su Nimrah da hankalinsu ba nan ma yake ba sun cigaba da surutun su ne. Dan kusan yana step ɗin ƙarshe Ruky ta taso da gudu da abu a hannu, Nimrah na binta alamar koma miye nata ne Rukyn ta ɗauka. Tsabar kuma basu da man kai ta wajen stairscase ɗin suka yi. Ai ko kaɗan ya rage Ruky taci karo da shi, yay gyaran muryar data ratsa kunnuwansu. Ai ko cak ta tsaya tana zaro idanu, haka ma Nimrah dake bayanta sai da taji zuciyarta ta buga. Lokaci ɗaya falon yin tsitt, dan har su Abees sai da suka nutsu.....
Sosai ya zuba musu idanunsa da suka saka su duƙar da kawuna ƙasa. Cikin ƙarfin hali Ruky ta ce, “Dada mun tuba, ALLAH bamu san ka taho ba ne”.
Maimakon tankawa kallonsu kawai yake. Duk sai suka sake firgicewa, Nimrah ta sake ɓoyewa a bayan Ruky kamar wata munafuka. Sai da yaja fin minti ɗaya idanunsa na ladabtar da su kafin ya furta, “Dama ya dace mata suna guje-guje?”.
Kawuna suka shiga girgizawa da sauri. Yanda suke yi ɗin ya bama kowa dariya, sai dai babu mai zarrar yinta a fili inba Mammah ba. Ita kuma murmushi kawai tayi ta ɗauke kanta. Ƙasa-ƙasa Ammar ya furta, “Aiki gamai ƙareka. A kallo kawai Ninah da Ruky sun nutsu dole nayi sadaka idan na fita”.
Mintsininsa Bilal yayi, ya rufe baki yana buge masa hannu. Ya Ma'aruff kam gefe ya kauda ido yana murmurshi bayan sun kalla juna da Twinyn sa Ja'afar.
Shima bai sake ce musu komai ba ya ƙaraso falon, hakan ya saka su Lailah sake nutsuwa kawunansu a ƙasa na girmamawa. Zaune ya kai a kujerar kusa data Mammah, sai kuma ya kalla su Aheel da sukai tsuru-tsuru, to iyayen daba sun nutsu bare su. Hannu ya miƙa musu, babu musu kuwa suka nufe shi su duka ukun. A mamakin kowa kansu ya shiga shafawa fuskarsa na sassautawa duk da ba murmurshi yake ba. Suma yaran sai suka fara gaida shi, duk da ganin jiya kawai sukai masa da alama kamaninsa da iyayensu da yake ya tasirantu a zukatansu.
Ya gaisa da su Ma'aruff duka bayan sun dawo sallar asuba. Amma hakan bai hana su sake gaishes hi ba a yanzu. Suma su Shariffa suka gaishe shi da Biebah. Sai lokacin su Nimrah suka ƙaraso suma suka gaida shi. Biebah yay ma umarnin kawo masa coffee, ta amsa tana nufar kitchen. Bata wani jima ba ta dawo, table taja gabansa tana ajiye masa ƙaramin tray ɗin data ɗora cup ɗin, dai-dai su Nimrah sun kammala tattare kwanikan dining suma. Sun dawo falon da nufin ficewa Mammah ta dawo da batun da su sun ma manta sun fara, dan tasan halinsu zasu iya zagayewa su gayama Dadan nasu.
“Ina roƙonku ku bisu a hankali, kuyi haƙuri kuma da su, kofa ba komai ƴan uwanku ne, da wannan ƙorafin ai inaga kuyi jihadin gyara musu ɗabi'un nasu na banza cikin hikima zai fi ko”.
Kamar Biebah zatai kuka ta ce, “Wlhy Mammah ko mazan zasu canja banda macen. Bata da mutunci fa, da nai mata magana jiya da daddare zatai live da kayan barci catai min wai bata son takura naji da matsalolin gaba na. Shiyyasa na bar mata ɗakin na koma ɗakin su Ninah na kwana”.
Caraf Nimrah ta ce, “Lah Small Mom dama kece? Nifa na zata ita finga fiyau ɗin ce ta shigo mana. ALLAH kaɗan ya rage ban faɗo da ke ba a gadon, kuma da har na ayyana haka a raina naga ban gama fita daga kamun UBANGIJI ba ina zazzaɓi sai na wuce ɗakin Mammah abina acan na kwana nima.”
Dariya su Bilal sukayi saboda (Finga fiyau data kira Hanoon). Yayinda Dada ya kusa ƙone lips da coffee jin taɓargazar da tsuntsuwar yarinyar nan ke neman yi masa, tunda in kowa bai san a ɗakin Mammah ya kwana ba ai ita Mammah ta sani. Sarai Mammah taji mi Nimrah ta faɗa, amma ta basar dan koda ta ɗan kalli Dada ta gefen ido ta lura sai da ya ɗago nasa idanun ya kalla Nimrah ɗin, kafin itama ya saci kallonta.
Ke Biebah da baki san miya faru ba ta amshe zancen Nimrah da faɗin, “Haba naso inyi magana da kika shigo da asuba kina ƙanshin turaren daban sani ba, sai kuma na tuna sanda muka tashi baƙya nan. Kice kaɗan ya rage nasha ƙasa. Ina arziƙi an jeho uwa, dole na fara kwana da fitila indai na shiga ɗakin ku kuwa”.
Ammar da Mu'azz da su Lailah na dariya ƙasa-ƙasa, Dada na ayyana dole ya sallama turaren daya saka a daren jiya kuwa a gidan nan. To Biebah taji ƙamshi ai bashi ba sake saka wannan turare balle ta fahimci daga shi yake.
Ja'afar ne ya katse zancen da faɗin, “Mammah a bar zancen sai an jima. Ku kuma kuwuce kada ku makara”.
Mammah ma ta fahimci dole zancen ya tsaya iya nan kada a kama wani layin, sai dai a ranta tana jinjina hukun UBANGIJI, dan ikonsa ne ya haɗa waccan haɗuwar ta daren jiya a ɗakinta..........✍️
Gaskiya ya kamata a ƙara gasama Nimrah baki karta ɓaro aiki wataran da shegen surutun nan nata😂
Yanda suka kallesa suka watsar ya saka shi jin zafi, amma dan kar abokansa daya tabbatar suna kallonsu su fahimta sai ya sake faɗin, “Bai kamata ace kyawawa kamarku wayayyu suna wannan halin ba. Baƙyau wulaƙanci fa”.
Kallonsa Ruky tai cike da harara da taɓe baki ta ce, “Ka bari sai ka koyi sallama tukunna ka mana wa'azi”.
“Oh sorry! Nayi kuskure. Assalamu alaikum ƙyawawa”.
Yanzun ma Ruky ce kawai ta amsa masa. Nimrah kam ko kallonsa bata sake yi ba dama. Shi su duka birgeshi suke, dan harga ALLAH baya iya tantance wama yake so. Sai dai yanda Nimrah ta watsar da lamarinsa ya sashi zuba mata idanu da faɗin, “I really like your style Baby. Kiyi komai ba komai kin isa ne.”
Karon farko taja tsoki, batare data tanka masan ba dai ta miƙe tana Kama hannun Ruky da itama ta watsa masa harara. Shi ko ɗan iskan sama, sai kawai ya riƙo hannun nasu dake cikin na juna yana neman rungumesu su duka. Hummm babbar bala'i kenan, ai kawai saukar yatsun hannun Ruky biyar yaji akan kyakkyawar farar fuskarsa, bai gama dawowa a hayyacinsa ba Nimrah ta saka gwiwar ƙafarta ta daki gabansa...
Wata irin gigitacciyar ƙara data amsa wajen gaba ɗaya ya fasa yana sakin fuskarsa ya damƙe gaban wandonsa. Ƙafin ma sauran ɗaliban dake wajen suzo kansu ya zube a wajen a sume. Ko'a kwalar rigar su Ruky, dan saima nuna shi da Nimrah tai da yatsa tana faɗin, “Sha-sha-shan banza bunsuru ka ɗauka mu ƴan gidan gala ne. Wannan kaɗan ne daga tunatar dakai tarbiyyar daka rasa. Shege, halan gidanku ba mata ne, miyyasa bakaje ka rungumi gyatunarka ba ai itama mace ce zaka samu biyan buƙatar abinda kake nema......”
“Shike nan kun kashe shi”.
Cewar ɗaya daga cikin abokansa da yay jarumtar taɓa hancinsa da yatsa, da kai kunne ƙirjinsa ya tabbatar zuciyarsa bata bugawa. Maimakon yaran nan su razana kai tsaye Ruky ta ce, “Ai an rage mugun iri”. Taja hannun Nimrah suka bar wajen hankali kwance.
Tuni wajen ya kacame da hayaniyar ɗalibai, wasu kuma suka garzaya sanarma malamai dan abin ya tayar musu da hankali bana wasa ba......
★✨★✨★✨★✨★
A dai-dai wannan lokacin da waccan cakwakiyar ke faruwa a makaranta anan Daddy Imran ne bisa hanya sun dawo daga wani waje shi da Dada. Shi da kansa yake driving, ta gefensa Dada na zaune ya baza takardu a jikinsa da laptop yana aiki. Yanda motar tai shiru zaka fahimci aikin mai muhimmanci ne. Dan shima Imran ya maida hankalinsa ne kawai ga tuƙinsa, lokaci-lokaci yakan kalla Dadan ya maida kansa ga titin. Sai dai a yanzu koda ya kallesan sai ya ɗauke kansa da faɗin, “Kana buƙatar hutu fa haka nan, dan ka samu nutsuwar fuskantar tattaunawar anjima da shugaban ƙasa. Ga su Dabo sun matsu su ganka suma”.
Ɗan mitsilin murmushin gefen baki ya saki, batare daya daina abinda yake ba ya bama Imran ɗin amsa bayan shuɗewar minti ɗaya.
“Basu san na tsufa ba suke zumuɗin gani na”.
Dariya Imran yayi har yana ɗan dukan streeng. Sai da yay mai isarsa sannan ya ce, “Kaga ko bazan bama tsoho ɗiyata ba, ka lallaɓa matarka ta dawo ka huta wannan shaye-shayen shayi da lomon shamin da kanwa kullum.”
Dada bai bashi