Author : Billyn Abdull Category : African Stories & Novels
kaga fa kana ƙoƙarin bani mamaki.” Ya yi murmushi mai ɗan kaifi, ba na farin ciki ba, na jarumin da ya saba da iya riƙe nauyin abu a zuciya da ƙwaƙwalwa batare daya bari abokin gaba ya fahimci lagonsa ba. Cikin halin ko in kula ya cigaba da da ɗin, “Ka zo nan kana min barazana da dorinar ƙarya, ka ce ku ne ƙasa, ku ne haske, ku ne gwamnati. Amma duk da wannan ƙarfin ikon naku kuma kuka zaɓi ɓoye fuska kamar masu tsoron haske a gaban ZAKIN dake ɓoye cikin keji?. Gaskiya ban yarda da wannan ƙarfin ikon naku mai kama dana ƴan wasan kwaikwayo ba, ya kamata ku koma ku canja shiri.”
Ya ɗan sake matsawa gaban tebirin sosai yana sassauta murya kamar mai son yin raɗa idanunsa na sake shiga cikin na baƙon, sai dai muryar tasa ta cika da nauyin, da ƙarfi irin na masu izzar ƙarfin zuciya da jarumtar ƙwarai dake jinsu ko a ɗaure su ba masu risinawa wawaye bane.
“Ɗan aike!. Ka manta da abu ɗaya.”
Shiru ya mamaye ɗakin. Baƙon ya tsaya tamkar an dasa shi a wajen yana kallon Zak-Shadow da jin ƙaguwar son barin wajen dan wani irin firgitashi al'amarinsa keyi, dauriya kawai yake da dannewa saboda sanin akwai camara a jikinsa dake ɗaukar komai. Kai tsaye kuma duk abinda suke tattaunawa ƴan ƙungiya ma na kallonsu........✍️
21
........Tunaninsa ya katse sakamakon cigaban kalaman Zak-Shadow masu zafi da sanya zuciya raɗaɗi.
“Idan kaje ka sanar da iyayen gidanka saƙo daga ni Haysam Abdul-rasheed Shehu. Ku na mallakar gwamnati, amma ba kwa mallakar ƘASA. Ku na mallakar masu muƙami, amma ba kwa mallakar mutanen da suke amsa sunan KASAR. Ka sanar musu. Idan suna tunanin zasu sarrafa ni kamar karnukan su… to su sake tunani tun kafin lokaci ya ƙure musu. Ka faɗa musu. Wannan ba ƙarshen wasan ba bane, farkon rugujewar su ne, domin kuwa yanzu ne za'a FARA WASA na GASKIYA. Ka faɗa musu. Wanda yake da cikakken iko ba ya zuwa ya gaya wa wanda yake tsoro barazana. Domin wannan zuwan naku tabbatar min yay da kun MATSORATA ne, kuma ni abin tsoronku ne. Na ji ƙamshin wannan tsoron naku tun shigowarka nan. Ka faɗa musu. Idan kun kasance da ikon da kuke ikirari… ku kasheni kawai zai fi muku sauƙi da samun cikar burin ku cikin salama” ya ɗan yi dariyar da ta sake tsokano zuciyar bako. Batare da bashi damar cewa komai ba ya cigaba da faɗin,
“Ka faɗa musu. In har kukai sakacin ƙin kasheni da ɗaukar zantukana cika baki, to ku shirya… ku shirya wasan da muka fara ba lissafin saƙar zaren ginin gidan GIZO-GIZO ba. Ka faɗa musu. Shi wannan filin da suke cika bakin samarwa domin ƙwallon ƙafa, da jinin da zasu jiƙa ƙasar domin ta tausasa. Ni ne zan samar da filin WASAN, sannan na jiƙa ƙasar da jinin jikinku. A maimakon buga wasan ƙwallo na ɗaura muku sarƙar mata a ƙafafuwa ku zagaye filin da takun RAWAR ƘOROSO. Ka faɗa musu. Ni nake tsara gangar da masu kiɗanta, kuma tabbas in sha ALLAHU sune zasu taka wannan rawar fa. Ka tafi ka faɗa musu. Na gane kun TSORATA. Sannan wannan SAƘON daka kawo zai zama kuskurenku na farko. Na biyun zai biyo bayan fitowata daga nan. Ka faɗa musu. Idan har iyayensu sun haifesu da alfaharin igiyar aure, kamar yanda ni Haysam Abdul-rasheed Shehu Kobi A'isha da Abdul-rasheed suka haifeni da wannan alfaharin ku rubuta kalamaina ku ajiye da yaƙini a saman dutse. Sannan ku shirya.”
Ya turo kujerar ya tashi a hankali yana sakin murmurshin ƙasaita tamkar sarki ya miƙe daga gadon mulkinsa. Ya zubama agogon hannunsa idanu na sakanni tare da sake sakin murmushi mai ma'anoni da yawa sannan ya fara takun dake nuna alamar barin wajen. Da sauri shima baƙon ya kalla agogon nashi mai ɗauke da camara saboda kallon da Zak-Shadow yay ma agogon ya tabbatar ɗayan biyu ne, ko dai ya fahimci camara ɗin ce ko ya tsargu....
Dada da yay takun da bai gaza biyar ba ya tsaya cak, tare da juyowa a hankali, idanunsa suka sauka a kan mutumin. Fuska ta bogi, amma mugunta ta gaskiya.... Murmushi ya sake saki da ɗan taɓe baki. Cikin salon isar da saƙon ƙarshe a inda yake da tabbacin masu aiken na kallonsa yanda ya dace domin idanunsa kam a kan agogon mutumin ya furta,
“Ni bana kare gwamnati. Bana kare hukumar soji. Bana kare kujerun ƴan mulkin mallaka. Amma ku sani. Na kare ƙasa. Na kare mutanen ƙasa. Na kare gaskiya duk da ƙarfin ikon UBANGIJI mai IZZA da cikar mulki na gaskiya. Wannan kuma… Shine abinda kuke tsoro. Zan ƙara tabbar muku, idan har kuka bar Haysam Abdul-rasheed Shehu a raye, zai cigaba da tabbatar muku wannan tsoron a cikin ZUKATA. Bance zan iya komai ba, amma bazan taɓa raina kaina a gaban ALADU irin ku ba”. Ya ɗan yi shiru yana murmurshi mai ciwo, dan kowace kalma yana fitar da ita ne daga zuciyarsa kamar takobi mai kaifin gayawa jini ya wuce.
Baƙo da zuciyarsa ke dukan uku-uku cike da ƙarfin hali ya ɗan taɓe baki, numfashinsa dake fita da rawa ya fisgo da ƙyar dan neman ƙwace masa yake. A karo na farko ya ji wani abu ya motsa masa a ƙirji, ba tsoro bane kawai, ba kuma bakin ciki bane kawai. Bayyanan nen rauni ne dake tuna masa, shima fa ɗan ƙasa ne tamkar Zak-Shadow, yana da dangi a ciki ba iyalai kawai ba, yana da ƙarfin ikon kiranta tushe ba son tara dukiya da ƙarfin ikon son mulki kawai ba....
Dada daya gama fahimtar raunin nasa dake son bayyana ya juya zai fita abinsa yana murmurshi, sai kuma ya sake tsayawa tare da juyowa a lokaci guda. Da tabbatar wa ya ce, “Ya kamata na sake jaddada muku domin fita hakki. Kar ku barni a nan domin in gani daga shirin shirin ku. Idan kukai wannan sakacin zan zauna in rubuta yadda zan rushe ku daga cikin ɗakin nan da wawancin ku ke sakaku kallonsa keji”. Ya kammala da murya mai sanyi, amma mai ɗauke da tabbataccen iƙirari.
“Kuna da duhu. Ni kuma ina da hasken da yake huda duhun nan naku. Saƙo na ƙarshe, duk wanda ya sake zuwa inda nake da saƙon ku, zan bashi amsar da zai maido muku. Sai dai GAWARSA ce zata dawo da amsar da gangar jikinsa ba BABU RUHI....”
Ya saki murmushi tare da salute da yatsa ɗaya kacal sannan ya juya abinsa cikin takun nan nasa da wanda basu fahimcesa ba ke kallon na izgili da izza. Ƙofar ya buɗe ya fita ba tare da ko waiwaye ba yabar baƙo da rawar zuciya da jiƙewar gumi, ga shi ya gagara koda motsi a wajen tamkar wanda gangar jikinsa ta mutu ta barshi da fitar numfashi kawai........
<%><%><%><%>
Cike da nutsuwa take haɗa masa abincin karin a gabansa, duk da kuwa tana daga tsaye ne shi a zaune kan ɗaya daga kujerun daning ɗin. Ya zuba mata idanunsa na girma fuskarsa da murmurshi. Sai da ta kammala zata matsa ya riƙo hannunta. Kallonsa tayi itama a karo na farko, sai dai fuskarta ita sam babu walwala alamar akwai abinda ke damunta ko ranta a ɓace yake.
“Juwairiyya mike damunki ne wai?”.
Yanda yay maganar cikin taushin murya yana sake tsatstsareta da idanu ya sata sunkiyar da kanta. Sai dai batace komai ba. Numfashi ya ja ya fesar tare da sake matsa hannunta cikin nashi, ya buɗe baki zai magana kenan takun fitowar wani daga cikin yaran ya sashi yin shiru yana sakar mata hannun. Itama matsawa tai kaɗan dan mai fitowar har ya bayyana. Ba kowa bane face Abdul-rasheed da suke kira Imam saboda sunan aboki, amini kuma mahaifi gasu Dada da yaci. Imam shine babban ɗanta a gidan, sa'anni suke shi da Mu'azz koma muce ya girmesa da kusan 2years. Yarone nutsatstse yana tsananin kama da Uncle Nasiru, akwai mai bi masa Halimatus'sa'adiyya. Sai Bintu sa'ar su Nimrah, itama dai ƙawarsu ce dan ƙiriniyarsu ɗaya da ita, idan suka haɗu sam basa jin bari musamman idan an samu hutun makaranta sukan haɗu anan ko gidan Mammah ko gidan Daddy Imran. Adam da Sadiq sune ƙananu a gidan, dan Hajiya Zuwairah ta haifesu ne ma kusa-da-kusa sakamakon gwanne data samu, ta haifi Adam da wata uku ta sake samun cikin Sadiq, hakan yasa tsiransu nasu ba yawa.
“Abba ina kwana? Ummu Ina kwana?”.
Imam ya faɗa yana mai kaiwa duƙe. Hannu Uncle Nasiru ya miƙa masa alamar suyi musabaha yana murmurshi, yayinda Hajiya Zuwairah ta amsa masa da kulawa. Fuskar Imam da murmurshi ya bama Abban hannu kamar yanda yake masa kullum. Dai-dai lokacin Sadiyya da Bintu ke fitowa suma dan ɗakinsu ɗaya.
Abba ya ce, “Abdul-Rasheed kaifa abokina ne ba suruki ba”. Murmurshi Imam yayi kamar yanda ya saba a duk sanda Abban nasu ya faɗi haka. Hakama Hajiya Zuwairah na tayashi. Imam na kaiwa zaune a kujera shima su Bintu suka ƙaraso dining ɗin, cikin girmamawa suka gaida Abban sannan Ummu da Yaya Imam. Duk sun amsa musu da kulawa, Ummu ta kalli Sadiyya tana faɗin, “Halimatu taso min su Adam suzo suyi kari, dan yanzu haka ma basu tashi ba balle batun tafiya Tahafiz, ni narasa miyasa kukafi ɗaukar tafiya boko da muhimmanci a rayuwarku fiye da islamiyya”.
Sadiyya data zama budurwa sosai tai ƴar dariya da faɗin, “Ummu itama islamiyya muna so ALLAH, baga Yaya Imam nan ba har jami'a fannin Islamic ya zaɓa”.
“To ai shi dama yana son karatun addini ba irinku ba. Dan magajin mai sunan nashi ne da Haysam.”
Hajiya Zuwairah ta bata amsa. Murmurshi Uncle Nasiru yayi, zuciyarsa na tuno masa amininsa kuma ɗan uwa Abdul-rasheed, tare da jin raunin zuciya na gagara taka kowacce irin rawa akan al'amarin babban ɗa na ƙwarai irin Haysam.
KIƊA A RUWA 2
22
.........“Wlhy Abba zasu aika kada ka amince da daɗin bakinta. Idan ba haka ba nima sai dai a maida ni makarantar su Asma'u ai ƙawaye basu ƙawaye ba”.
Caraf Adam yace, “Muma haka Abba”.
Dariya kowa ya sanya. Abba ya shafa kan Adam da Sadiq. “Kenan dai na gane a gidan nan kowa yana jealous da Mamana kawai”.
“A da alama kam”.
Cewar Ummu tana murmushi. Itako Bintu tayi kicin-kicin da fuska alamar jin haushi. Sai da Ummu ta lallasheta sannan ta yarda ta zuba abinci. Daga haka suka nutsu suka fara karyawa babu mai magana. Sai da suka kammala kowa ya miƙe dan zuwa yay shirin Tahafiz har Imam. A lokacin ne Uncle Nasiru ya sake kallon Hajiya Zuwairah dake gyara gurin duk da su Bintu duk sun kwashe kwanikan sun kai kitchen.
“Zamu iya magana yanzu?”.
Kallonsa ta ɗanyi, sai kuma ta tura baki kama ƴar yarinya. Dariya yayi yana haɗe hannayensa da faɗin, “To ni dai duk ma laifin da nayi ayi haƙuri ai min afuwa. Amma dan ALLAH a sanar min damuwa kada zuciyata ta sake kumbura.”
Kanta ta sunkuyar kawai batare da tayi murmushi data saba yi ba a duk sanda yay irin wannan maganar, sai kuma ta ɗan sauke numfashi cike da nutsuwa ta ce, “Abban Jiddah akan maganar jiya da kaƙi sauraren Jiddah akai ne. Bayan kuma ni da kai duk munji abinda Ismat ta faɗa fa. Yanzu dan ALLAH sai ka bari ɓacin rai ya rinjayeka barin yaran nan a cikin tarkon musiba? Kana jin fa abinda ke faruwa; a tunaninka watarana mahaifiyarsu bazata ci galaba akansu ba musamman ma Nabeeha dake ɗauke da igiyoyin aure a kanta! Nasan Nabeeha mai laifi ce a gareka, dan babu izninka babu na mijinta ta koma wata ƙasa da zama bayan ana cikin damuwa da halin da mijinta ke ciki, amma abinda zamu kalla ko tana da laifi wani kaso ne a ciki Hajiya Hasiba nada wani, saboda tana da tasiri ƙwarai da gaske akan al'amarin yarannan idan ka cire Jiddah da ALLAH yay saurin fargarwa...”
Cikin ɗacin murya da sauyawar idanun da ɓacewar murmushin kan fuskarsa ya ce, “Ya kike so nayi Juwairiyya? Shin basu ne suka zaɓi irin rayuwar ba shiyyasa suke ciki? Ai su duka ba yara bane har Ismat ɗin da ake ganin batai aure ba, amma suke biyewa gafalar uwarsu da son duniya ta rufema idanu ko”.
“Hakane, amma abinda zamu duba har yanzu su yara ne akanmu. Sannan mata ne. Mufa mata a kowace sigar rayuwa a karkacen nan muke tamkar haƙarƙari. Shekaru basa saka mu canja ko ilimi. Sai wanda UBANGIJI yaso ya gane kawai daga cikinmu. Mu godema ALLAH da yarannan basu tasirantu da huɗubarta ba ma har suka fahimta illar al'amarin. Dan wlhy UBANGIJI ne kawai ke riƙe da igiyoyin auren Nabeeha saboda Haysam mutumin kirki ne, in sha ALLAHU ALLAH bazai haɗa masa zafi biyu a lokaci guda ba. Dan ALLAH kayi wani abu kodan Haysam, saboda koba komai da saka hannunka ya auri Nabeeha, sannan yana sonta”.
“Hummm Juwairiyya....”
“Dan ALLAH karka ce A'a Abban Jiddah”. Tai maganar cikin katse masa hanzari. Ajiyar zuciya ya ɗan sauke kawai. Tare da faɗin, “Shike nan zan duba. Amma ki sani Adeel yaro ne mai dauɗar duniya a hannu, sannan ya fito daga babbar zuri'ar da yake da ƙarfin aji ako ina a duniya musamman ma ƙasashenmu na Afirika. Barowarsu ƙasar nan zai zama babban al'amari. Amma zan gwada wata hanya idan za'a dace.”
“ALLAH yasa a dace, dan duk ƙarfinsa bai kai na UBANGIJI ba ai. Darajar auren dake kan Nabeeha ALLAH zai hanashi dukkan nasara. Itama ALLAH ya shiryar da ita ta gane halakar da take neman jefa yarannan da kanta.”
“HUmmm”.
Kawai Uncle Nasiru yace, itama sai ta saki zancen ta ɗakko na batun zuwa sake duba Aunty Mimi mai haihuwa duk da kuwa randa ta haihu taje. Amma a matsayinta na kamar uwa koda Mammah na nan dama ita ya kamata ta yi abinda uwa zatayin, saboda ita da Mammah suna jin kansu kamar ya da ƙanwa uwa ɗaya uba ɗaya. Kamar yanda Uncle Nasiru ke ɗaukar Mammah ƙanwarsa uwa ɗaya uba ɗayan. Bai hanata ba, shima ya miƙe yana faɗin zai shirya dan yau yana da ganawa da sanata Yusuf Shu'aibu Tafida tsohon janar.
ƘIDA A RUWA 2
23
.........A wannan rana ƙarfe sha biyu na rana jirgin su Mammah ya sauka, tare take da Ammar ɗinta sai ƙaninta Tasi'u da Ammar ke kira Uncle. A tsakkiya suka sakata har inda motoci suke. Aiko cikin sa'a sukai arba da tagwaye biyu Yaya Ma'aruff da Ja'afar da suka zo ɗaukarsu da kansu. Sai dai me suna yunƙurowa a tare suka koma suka ƙame kamar gunkinaye idanunsu akan Uncle Tasi'un. Dan duk da suma suna yara sosai ya aikata abinda ya aikata hakan bai sa sun mance wannan fuskar tasa ba. Dan bayan mahaifin Biebah shine mutum na biyu daya bar musu tabo a zuciya na zahiri. Abinda dangin mahaifinsu suka aikata duk a labari suka sanshi, a labarin ma ba komai ba daga bakin Mammah ko Dadansu. Gwaggo Alawiyya ce ta gaya musu komai.
Ganin yanda sukai ɗin ya saka Mammah cikin dakewa furta, “Oh bakwa farin ciki da ni na koma kenan ko?”.
Jikinsu ne yay sanyi, cikin dauriya da danne zukata suka nufota, batare da ko kallon Uncle ɗin nasu sun sake yi ba suka rungumeta ita da Ammar suka manta da shi. Ammar daya tsargu da abinda ya farun da ƙyar ya iya dannewa yana murmurshi. Haka suka kama Mammah a tsakkiya har mota. Sai da ta shiga suma suka shiga Ammar ya shiga, ganin Uncle Tasi'un bai shigo ba Mammah tace su masa magana ya shigo. Kallonta sukai kamar zasu fasa kuka. Amma kallon da itama tai musu na gargaɗi ya sasu risinar da kawuna Ja'afar ya fita yay masa magana. Sum-sum kamar munafuki ya shiga kusa da ita suka sakata a tsakiya shi da Ammar......
Sun iso gida da yake shiru kasancewar basawan cikinsu duk ana makaranta. Masu aiki ne kawai sai Aunty Shariffa da Aunty Lailah da yay basu je gidan haihuwa ba saboda dawowar Mammah. Hasalima da kansu suka shiga kicin yi mata abincin da suka san tafi so da ƙauna. Masu aiki da suma ke farin ciki da dawowarta na tayasu da ƙananun ayyuka. Daga Aunty Shariffa har Aunty Lailah kowace fama take da ƙaramin ciki, dan cikin ikon ALLAH kamar yanda sukai haihuwar su Abees a tare da tasu Afrah da Ayyan haka wannan cikin ma basu da nisa a samu. Sai dai Aunty Lailah ce ta fara samu kafin Shariffa. Dan haka nata yafi fitowa sosai har ana iya gani.
Mu'azz ya fita akan batun karatunsa dan Imam ne yazo har gida suka fita a mashin ɗinsa. Wannan ya ƙara haifar ma da gidan shiru. Motar su Mammah na gama tsayawa Lailah da Shariffa suka fito cike da ɗoki da farin ciki dan Mammah uwa ce a garesu ba uwar miji ba. Itama fuskata ƙawace da murmushi ta fito da taimakon Ammar. A tare ta kamosu jikinta ta rungume tana mai jin farin cikin ganinsu da sanya musu albarka. Yayinda suma suka zame suka zube cike da girmamawa suna mata barka da dawowa. Ta amsa musu da kulawa tana kamasu ta miƙar.
Cike da tsokana Ammar ya ce, “Wato kunga Mamanku ni in ma na ɓata a can babu ruwanku ko Auntys?”.
Yanda yay maganar yana cika baki da iska har su Ma'aruff dake faman haɗe fuska saboda Uncle Tasi'u Sai da suka