Author : Billyn Abdull Category : African Stories & Novels
da nake son sanin sirrin ta ba da taimakon ka. Ni mai rauni ce a yanzu, sannan makauniya dake buƙatar koda sandar jagora ce. Na maka alƙawarin bazan sake wasa da damar da zaka bani ba”.
“Shike nan naji, zanyi haka ne kuma kawai dan Ummanki data bani amanar faɗa miki gaskiya a duk lokacin da kika kai minzalin girman ki. Sannan ta bani wasu sirrika na baki. Ban baki da farko bane, sabo da ina son auna hankalinki da yardarki gareni. Yanzu sai ki faɗi ina zamu haɗu”.
“Na gode sosai. Sai dai kamar yanda na faɗa maka a baya ba'a barina fita ni kaɗai, sannan a yanzu gidanmu zagaye yake da jami'an tsaro saboda dawowar mutumin dake cikin video ɗin nan. Idan suka ganka zasu zarge ka ko kazo cutar da shi ne, dan saboda shi aka ajiye su......”
Wani mugun girgiza zuciyar Dagger tayi, kaɗan ya rage yawun bakinsa ya biyo masa ta hanci tsabar yanda kalmar Nimrah ta dake sa. Da rawar lips ya maimaita, “D...awo wa...?”.
Ɗan jimmm Nimrah tayi, sai kuma tace, “Eh mana, ba shugaban ƙasa ya masa afuwa ba? An fiddo shi ko ka manta ne?”.
“Haka ne! Haka ne! Na manta ne sam, kin san abubuwan yawa suke”.
Duk da yanda yayi ɗin ya ɗan sake taɓa zuciyar Nimrah da bata mamaki sai ta share kawai. Ta ce, “Ka bani nan da mintuna goma, akwai mamanmu zata haihu suna asibiti, idan an yarda muzo zan kiraka da wannan layin, dan zan riƙe wayar a wajena sai mu haɗu a cikin asibitin”.
“Shike nan ba damuwa, sai na jiki”.
Ya faɗa daga can wasu jerarrun zufa na yanko masa ta ƙofofin gashin jikinsa gaba ɗaya. Ita ko da bata san yanayi ba wayar ta yanke tana barin wajen. Koda ta fito maimakon zuwa gate ta bama Sanda wayarsa sai ta wuce ciki kawai....
+++++++++++++
“Tabbas gaskiya mutumin nan ya faɗa Oga, Zak-Shadow na cikin ƙasar nan, a cikin gidansu. Kuma a ƙalla sati guda kenan yake cikawa. Kaga kenan kwanaki huɗu kacal tsakani da sanar da afuwar shugaban kasa. Wato mutumin nan lallai ya masifar raina hankalinmu. Dan a majiya mai ƙarfi na samu tabbacin Zak-Shadow yafi wata biyu da barin prison, a ƙalla satin da ya fara shiga office ya fitar da shi.”
Gaba ɗaya Oga Jush yama gagara iya cewa komai saboda yanda zancen yay masa dukan tasar ruwa a kai. Shin Yusuf Tafida ne ya raina musu hankali? Ko yaran da suka zagaye ko'ina a ma'aikatun ƙasar ne suka maidasu wawaye jahilai?. To lallai lokaci yayi da sabon wasa zai tashi, badai sai sun bari ayi mulkin lafiya ba. Daga shi Tafidan har Zak-Shadow ɗin zasu ɗanɗana kuɗarsu ne. Batare daya tofa komai ba akan batun ya bama Iron Fang umarnin sanar da meeting, ko ina kake kuma dole ka dawo ayi wannan zaman dakai, ba'a buƙatar kowa ya kiran waya ko video call. A zo kawai..
Iron Fang yasan oga ya ɗau zafi, sai kuma abinda ALLAH yayi, dan dole itama ƙasa ta ɗauki zafi a wannan gaɓar, zafin daya tabbatar muninsa sai yafi na baya girgiza kowa. Bai musa ko ja da nisa ba ya rubuta text message ya turama kowane member na ƙungiya. Shima ya kaɗa kansa ya tafi tashi sabgar sa........✍️
72
.........Gaba ɗaya gidan Mammah ya hargitse da farin cikin saukar Shariffa lafiya. Bakin Uncle J kam har kunne. Suka rungume juna shida Twinyn sa. Bilal da Ammar ma suka haɗasu suka rungume. Dole suyi farin ciki zuri'arsu nata ƙara yawa da faɗi. A take sukai kiran Mammah suka sanar mata, dan tana gida bata bisu asibiti ba, sai ma su Nimrah ne dake ta damunta suje-suje?.
Da farko ta hana su ne, dan bata son su tafi su barta ita kaɗai a gidan, dan Dada da Imran sun fita. Su Kulu kuma yau juma'a sun tafi gida su gaisa da mutane kamar yanda sukeyi duk bayan sati biyu. Su Dayyan kam sai a hankali, dan zatace ma tun bayan dawowa massalaci ta sake ganinsu ba. Garama Hanoon uwar son kallo da tana maƙale da tv kafin ta tashi itama ta shige.
Hankalin Nimrah a rabe yake, ga farin cikin samun ƙaruwa da sukai ga lamarin son haɗuwa da Dagger. Ta tabbatar idan su Ammyn suka dawo gida ba lallai ta samu wata dama ba kuma balle suna hutun tahfiz ma gobe babu, dan cikin satin sama za'ai bikin saukar ƴan ajin sauka su su maye gurbinsu. Duk da suma dai saura ƙiris ne fa. Kawai dan makarantar nada ƙa'idar bin komai daki daki ne.
Ganin yanda suka dage Mammah tace su duba idan driver na nan, idan baya nan sai dai su haƙura kam, tunda yanzu suma zasu dawo kasancewar an haihu lafiya asibiti bazasu riƙesu ba.
Nimrah tafi kowa zumuɗi, kasancewar tata fitar da manufa biyu ne. Koda Ruky taje ta duba sai gata ta dawo baki a sama. Wai Malam Buba ya fita. Kaɗan ya hana Nimrah ta saki kuka, ta dai daure dan kar Mammah ta fahimci halin da take ciki. Suna cikin hakan ma sai ga ƴan asibitin sun dawo da kyakkyawan Jariri mai kama da Uncle Ja'afar Masha ALLAH.
Sam ba haka Nimrah taso ba, dan ba ƙaramin ƙwallafa rai tayi da son haɗuwa da mutumin nan tai ba a yau. Sai dai ta san wannan damar kuma ta suɓuce mata. Dole ta saki jiki aka cigaba da murnar jariri, dan tabi ta katantane ta hana kowa ɗauka saboda Nimrah akwai son yara matuƙa. Kusan ma ganin jinjirin ne ya kwashe kaso mafi yawa na damuwar tata ta ɓuya daga fuskar ta, duk da sai da Mammah ta tambayeta ganin idonta ya canja tace abu ne ya faɗa mata.....
================
Hajiya Hasiba ta baro gidan Uncle Nasiru rai mace kiran Fomer First Lady ya sake harziƙa mata zuciya. Dan ko gaisuwa bata bari sunyi ba cikin bada umarni tace tazo tana nemanta duk inda take. Daga haka kuma ta yanke kiran batare data bari tayi magana ba. Tsabar takaici kamar zuciyarta zatai bindiga haka taji, kuma dole taje kasancewar da bazar First Lady ɗin take rawa. Akalar motar ta canja tana jan tagwayen tsaki. Mintuna kaɗan ya kawota gidan saboda gudu tai sosai.
Securitys ɗin gidan sun riga sun san wacece ita a wajen masu gidan, tunma suna gidan gwamnati bata da shamaki. Dan haka kai tsaye suka buɗe mata gate ta shige. Tun a compound ta fara gamo da abin takaici, wasu matan ƴan siyasa dake zaman jiran son ganawa da First Lady ɗin sukai mata caaa. Sama-sama ta amsa su da cewar su jirata shiga tukunna, daga haka ta shige. Yanda bata tsaya falo na farko ba balle na biyu zai baka tabbacin lallai ita ɗin ƴar gida ce. Dan kaitsaye upstairs ta haura abinta. Ga masu aiki nata miƙa mata gaisuwa cike da girmamawa.
A falon saman ta samu First Lady harda tsohon shugaban ƙasa, sai Zahir dake kwance a kujera zuru-zuru alamar baida isashen lafiya. Idonta akan Zahir ɗin ta gaida shugaban ƙasa da take kira Daddy, sannan ta gaida First Lady. Cikin ƙasa haƙuri ta furta, “Zahir lafiya kuwa?”.
Kai tsaye First Lady ta amsa mata da, “Inafa lafiya Hasiba, wasu shegun yara ne a makaranta suka nema illatashi. Shiyyasa ma Excellency yace na kiraki, dan binciken mu ya nuna yaran nada alaƙa dake”.
“Alaƙa dani kuma ranki ya daɗe? Nida yarana sun kammala har University su duka balle secondary. Sannan banda yaro namiji da har zai iya faɗa da Zahir”.
“Ba alaƙar jini ake nufi ba. Sannan ba maza bane yaran mata ne”.
“Mata fa! Suka masa wannan abun?. Amma ina fatan ba'a barsu ba ko Daddy?”.
Daga First Lady har Fomer President cikin takaici sukai ƙwafa a tare. First Lady ta ce, “Yanzu ne dai zamu ɗau mataki, dan mun saka ƴan sanda sun kama su amma sun sake su wai basu cika shekara 18 ba. Sai dai sukai maganar kotu.”
“Ai gwara aje kotun, kaji ƴan iskan yara kamar wasu ƴan daba. To wai ƴaƴan ma uban waye a ƙasar nan?”.
“Wannan shine dalilin da yasa muka kira ki. Dan muna son musan ƴaƴan waye ɗin. Dan a bincike na naga abokin mijin Nabeeha ne yaje ya cire yaran daga station, ya kuma kai lawyer. Sannan sunje da wani gadararren mutum daya ɓoye fuskarsa shine ma yace aje kotun Saboda yaran sun faɗi wata magana. Yanzu haka sun shigar da makarantar ƙara gaba ɗaya. Shi kansa alƙalin Excellency ya kirashi kan ya kora ƙarar yace case ɗin yafi ƙarfinsa”.
“Abokin Haysam! Imran kenan? Indai kuma haka ne zata kasance ƴaƴansa ne shi Imran ɗin. To amma waye suka je taren?”.
“Wannan shine amsar da muke nema muma. Yaran kuma ɗaya tabbas ƴarsa ce, dan da sunan sa take amfani, suna ma kama. Ɗaya kuma Muhammad”.
“Miye sunanta?”.
“Naja'atu Muhammad”.
“Mom anfi kiranta da Nimrah, a register kawai ake kiranta da Naja'atu ”. Zahir yay magana da ƙyar a karo na farko.
“Nimrah, eh lallai wannan yarinya sheɗaniyar yarinya ce. To ai itace nake gaya miki shi Haysam ɗin ya tsinto a ƙauye shekarun baya wai an kashe iyayenta. Nabeeha tace bata yarda ƴarsa bace shine ya aureta. Mafari kenna na samu Nabeeha ta baro gidan”. Salati First Lady ta fara, shiko tsohon shugaban ƙasa da bai fahimci zancen ba ya nema ƙarin bayani. Nan fa sukai masa. A kuma lokacin ne tunanin Hajiya Hasiba ya dawo baya. Ta ce, “To kodai zancen Ismat gaskiya ne. Kusan sati guda kenan muna Chaina ni dake ba Amima ta kirani ba take min bayanin.....”
“Tabbas anyi haka”.
Cewar First Lady.
Hajiya Hasiba ta ce, “To shine fa ni kuma na kullesu a ɗaki har yanzu na hana su fita, yanzu haka ma daga yima Uban nasu gargaɗi nake dan na zata shine ya shiryo makircin dan itama Nabeeha ya janye hankalinta. To lallai bana raba ɗayan biyu Haysam ne. Dan babu mai wannan ɗabi'ar gadarar irin tasa. To amma yaya haka? Duka yaushe shugaban ƙasa yace ya masa afuwa? Kodai makirci ne abun dama ba'a prison ɗin yake ba?”.
Gaba ɗaya tsohon shugaban ƙasa ya ma kasa magana, sai first lady ce ta furta, “A lallai biri yayi kama da mutum. Kuma yanzu na yarda gargaɗi mai razani akama alƙalin nan. To ai inaga Hajiya Hasiba kawai ki bar Nabeeha ta koma gidan, ta haka ne zamu san gaskiya. Dan tabbas bazamu bar wannan abin ya tafi a banza ba, dole ne yaran nan sai sun ɗanɗan kuɗarsu. Bazasu illata min yaro a banza ba, dan yanzu haka likitoci sunce sai an fiddashi waje, in ba haka ba nan gaba ya samu matsala a privete part ɗin”.
“Kai jama'a wann shaggun yara. Banƙi ta taki ba ranki ya daɗe, kanku komai kuma zan iya yi. Amma baƙya tsoron sharrin Adeel. Jiya jiyan nan nake ganin saƙonshi wai na shirya zai sake sauka a ƙasar nan, kuma wannan karon komai yake so ayi a gama”.
“Karki wani damu, ki barmu dashi. Yanzu kawai kije ama Nabeeha gyara kona kwana uku ne ta koma a cikin satin nan. Zan tura miki kuɗi, zan kuma kira ƴar Kamaru ta sameku gida”.
“An gama raki ya daɗe. ALLAH ya ƙara girma”.....
×==×===×==×===×==×
Sai dare Dada ya dawo gidan, lokacin kusan tara. An kawo masa jinjiri domin ya gani. Nimrah dake maƙale da shi ce kuma ta kawo. Dan har faɗa sukai da Ruky babu jimawa da taƙi bata shi shine tai zuciya taje tai kwanciyarta. Itako ko alamar barci bata ji, ga yunwa na cinta taƙi cin abinci, Mammah da Ammie dake gidan sunyi faɗa har sun gaji.
Tunda ta shigo falon ya zuba mata ido. Dan yanda ta rungume jaririn famm abinta sai tai masa ƙyau. Kai tsaye ta nufo inda yake tunda shi akace ta kawo mawa. Cikin tsokana Ammar yace, “To ALLAH yasa dai shi Dada a bashi kona minti biyar ne, dan mu minti bibbiyu aka bamu”.
Dariya Mammah tayi, “Ai ku kun samu minti biyun ma, Mu'azz sai a hannunta ya gani. Ruƙayya kam yanzu ba jimawa ta shige tayi fushi”.
Dariya Bilal da su Ma'aruff suka sanya, Mu'azz ya dalla mata harara da faɗin, “Ai wlhy sai na rama”.
“Sai dai kuwa ka rame”.
Cewar Nimrah tana murguɗa baki. Kasancewar Dada a falon kuma ya sa ta tsaya iya hakan. Takawa tai ta ƙarasa inda Dadan yake, dan shima Mu'azz ya mata shiru saboda Dadan na nan. Maimakon ta bashi sai ta durƙusa a gabansa tana faɗin, “Dada gashi ka gani a haka. Idan aka tattaɓashi da yawa zai yi ciwon jiki”...........✍️
🤣🤣ASHE Dadan ma bazai tsiraba Ninah😂🏃🏼♀️🏃🏼♀️🏃🏼♀️.
73
.......... “Bala'i”.
Cewar Ammar suna fashewa da dariya shi da Bilal. Ja'afar ya ce, “Haba Ninah harda Dadan kuma?”.
Baki ta tura cike da shagwaɓa ta ce, “To Uncle dan ALLAH kace masa minti uku kawai ya bani. Ko kuma na saka masa a ƙafafu daga hannuna ya gani.”
Dariya Ja'afar da Ma'aruff suka gimtse suma, karo na farko Mammah ta ce, “Adai yi haƙuri a bashi Auta. Kinga kafin ya gama gani sai kije ki dafa Noodle kizo kici dan abinci ma ya huce yanzu, ni kuma bazan bari ki kwanta da yunwa ba”.
Mammahn ta kalla kamar zatai kuka. “Mammah ALLAH bana jin yunwa nifa”.
Kafin Mammah ta bata amsa kawai taji za'a ɗauke mata jaririnta. Ai firgigita ta juyo. Suka kuwa haɗa ido da mai shirin ɗaukar. Ba kowa bane kuma face Dada. Dan shi kam ya gaji da jan ran da ake masa. Kannewa kawai yake. Amma ya ƙagara shima jaririn yazo hannunsa. Rabonsa da ɗaukar jariri kamar haka har ya manta. Idanunta da suka tara ƙwalla ta risinar, dan bazata iya jurar kallon nasa ba. Sai dai fa tsabar ƙarfin hali taƙi sakin yaron, ƙarshe ma tashi tai akan gwiyawunta tai kneeling a haka ta saka masa jinjirin saman cinya, hannayenta nakan cinyar tasa itama, dan ita sam a wannan yanayin bafa ta gane ma dawa take tare balle abinda tayi.
Babu wanda bai gimtse dariya ba a falon nan. Dan hatta Mammah kauda kai kawai tayi tana murmurshi.
“Tashi min anan?”.
Dada ya faɗa cikin law voice ta yanda ita kaɗai taji shi. Maimakon tashin sai ta saki hawaye sharr. A matuƙar shagwaɓe tace, “Dada dan ALLAH ka bani to, ai ka gani”.
Shi kam yau yaga lukutar jaraba. Yarinyar nan bata san a ina suke ba ne.
“Kina son duka?”.
Ya sake faɗa ciki-ciki. Kafaɗa ta maƙe masa tana tura baki. Bai sake ce mata komai ba, yasa hannu ya zare hannayenta duk biyu. Zatai magana ya wulla mata kallon daya sakata duƙar dakai ƙasa. Babu alamar wasa ya sake furta, “Tashi ki wuce ki dafa Noodle ki dawo sai ki amsa”.
“Dada kayi alƙawari?”.
Yanda ya zuba mata ido ya kasa magana ma yasa kowa ɓoye fuska yana danne dariya. Dan duk sunji mita faɗa ɗin. Shi ko ganin yanda ta tsatstsare shi da idanu babu alamar tsoro balle shakka yasa shi jinjina mata kai kawai. Tashi tai da sauri ta nufi kitchen ɗin, sai dai tana tafiyar tana waigen babyn. Kaɗan ya rage taci karo da kujera. Mu'azz ya fashe da dariya. Sai dai hararar da Dada ya watso masa ta sashi saurin danne bakin. Nimrah data hararesa itama tai ƙwafa tana shigewa kicin ɗin.
Bilal ya ce, “Kai jama'a, anya duk randa Ninah ta haihu zata bari a ɗauka ɗan kuwa?”.
“Gaskiya kam da kamar wuya”.
Ja'afar ya bashi amsa. Mammah dake murmurshi ta ce, “Hummm ina wannan tunanin nima kam, dan kwanaki fa da suka rakani barka tunda ta amshe yarinyar mutane ta hana, duk wanda yazo sai dai ya gani a hannunta. Babyn ta fara kuka akace ta bada ita maman ta shayar da ita taƙi, wai sai-dai maman ta saka nn a fida ita zata bata.”
Dariya suka sanya sosai. Shi kansa Dada da hankalinsa ke kan Baby yana masa addu'a duk da yayi kamar baya jinsu sai da yay ɗan murmurshi. Mammah ta cigaba da basu labarin kicimillin da akasha ranar. Ta ce, “In dai fa akai haihuwa a gidan nan Nimrah da Ruƙayya basa ƙara shiri, kullum cikin faɗa suke saboda ƙarfa-ƙarfar Nimrah akan Baby. Shiyyasa yaran nan duk suka shaƙu da ita, dan rainon datai musu ko iyayen iyaka kenan”.
Motsawar Babyn ya saka Dada cema Mu'azz yazo ya kaishi dare yayi a kwantar da shi haka nan kada sanyi ya kamashi. Tasowa Mu'azz ɗin yay ya amshesa. Ya fita kenan shima Dada ya miƙe zai haura sama dan hutawa ihun Nimrah ya ratsa kunnuwansu.
“Wayyoooo yaji wayyo idona?”.
Gaba ɗaya suka kalla hanyar kitchen ɗin, Dada ya tsaya cak. Kafin wani ya miƙe Nimrah ta fito tana laluben hanya da faɗin, “Wayyo Mammah ki cire min zan haukace idona. Zafi-zafi na shiga uku Mammah zan mutu....”
Mammah da duk ta rikice itama har zata miƙe dan kamo Nimrah ɗin, duk da ga Dada a kusa da inda take amma taga bashi da niyyar hakan sai kuma Nimrah ɗin data iso gab da Dada tana lalube ta taɓa shi. Ai tana jin mutum bama ta tsaya son sanin waye ba kawai ta damƙeshi tana cusa fuskarta a jikinsa, dan wani irin tashin hankali take ji da raɗaɗi har tsakiyar ƙwaƙwalwa, sakamakon yajin ya shiga mata sasai cikin idon. Gata dama