Author : Billyn Abdull Category : African Stories & Novels
hannun nasa Dada yayi sukai musabaha irin ta amintattun sojoji masu kishin ƙasa da tsayayyar zuciya, musabaha ta tarihi, ta alƙawari da cikakkaiyar JARUMTA.
Janar dake murmurshi ya furta, “Ina ji a jikina Haysam, da izinin UBANGIJI a ranar da ka dawo ƙasar nan zata fara canjawa da canji irin na masu son a shinfiɗa gaskiya. Da taku irin na masu girgiza zukatan ɓoyayyun munafukai. Daren gobe in sha ALLAHU zaku wuce”.
“ALLAH ya kaimu”.
Dada ya faɗa......
=================
Ranar Lahadi su Nimrah suka dawo gida da yamma. A kuma ranar Daddy Imran da tunda suka je gidan bai kwana ba dan Ammie ta faɗa musu yana wajen aiki yazo gidan da safe, sun nuna farin cikin ganinsa shima kuma yaji daɗin ganinsu. Dan haka suka zagayeshi da uban surutunsu yana biye musu. A ƙasan ransa kam ji yake badan yau ne tafiyar nan tasu ba daya shiryata da Nimrah a ciki. Amma lokaci ya riga ya ƙure, dan yau ne jirginsu zai tashi ƙarfe goma na dare shi da Haysam. Tunanin ya ture gefe ya cigaba da biye musu, dan sunata masa shagwaɓa wai zasuyi missing ɗinsa saboda ya sanar musu zai yi tafiya, kuma zai jima dan wata ɗaya zai yi ko sama da haka. Da yammar ma da kyar suka yarda suka bi Yaya Khalifa da zai maidasu gida. Shi Daddy Imran yace sai anyi isha'i zai shigo yayi ma Mammah sallama...
Da yamma Mu'azz yazo ɗaukar su shima, sai kawai Khalifa yay zamansa dan dama yana da uzirin aikin makaranta. Ammie ta haɗa musu kayan kwalliya da kayan ƙamshi na musamman na turarrukan SHUWA INCENSE AND MORE +234 704 229 3387. Suna da turare wuta da khumra kaloli har uku: black humra, white humra, brown humra. Akwai oil perfume da kullacham da genine da Turare kabasa kaloli uku shima. white, black, and brown. Akwai man kitso, da kayan gyaran jiki masu gyara fata da sanyata laushi da santsi kiyita glowing abinki hajjaju. Duk da kuwa Aunty Biebah ta saya musu kwanaki. Yanzu ɗin ma harda na Biebah Ammie ta bada, sannan taima Mammah gasashen nama mai ɗan karen daɗi itama a kai mata. Suka wuce Asma'u na musu tsiyar yau zatai barci mai daɗi. Lolo kuwa yana islamiyya ma suka wuce da ansha rigima duk da shima fa ya zama ɗan saurayi tunda 2years kawai Rukyn ta bashi. Gasu yanzu suna shekara sha biyar da watanni. Sai da suka fara sauke Fedoo a gidansu, sannan Bintu. Dan gobe in sha ALLAHU Monday ba batun tafiya gidan Mammah a cigaba da shargalle. Su kuma su biyu Mu'azz ya wuce da su gida cike da jin kewar ƴan uwansu da aka rabu.
Duk abinda suke Ammie na jinsu, itama kuma hirar tasu ta fara kai hankalinta akan al'amarin Asma'u ɗin da Bilal, dan kwan biyun nan ta fahimci ko yaushe Asma'u na maƙale da waya, idan ta tambayeta sai tace wai assignment take yi. Ashe ita ta maida assignment ɗin. Kai yaran yanzu sai a barsu dai kawai. Tai murmushi mai yalwa, dan har cikin ranta wannan haɗin ya mata. Wlhy idan duk ƴaƴan data haifa zasu kasance matane ace yaran gidan Mammah suka auresu zatafi kowa farin ciki, dan jinin Mammah jinin alkairi ne. Abotar Imran da Haysam babban rahama ce kuma alkairi ga zuri'arsu guda biyu. Addu'ar fatan alkaici tayi ta cigaba da sabgarta.........✍️
43
........Shima Imran lumshe idanu kawai yayi a wajen yana jingina da kujera. Ya san wannan ganawa ba ta siyasa ba ce, ganawa ce ta gaskiya, ta amana, ta zumunci, ta yarda da bashi na tarihi. Ciki ya koma ya sanar ma Faro, dan haka suka nufi ɗakin da Dada yake duk da su a zatonsu har yanzu barci yake.....
★2:42am★
Shugaban ƙasa Yusuf Shu'aibu Tafida suka iso cikin base ɗin. Fita ce ta sirri dan a cikin ɓadda kama ma yake. Dan haka daga shi sai dogarinsa ne a motar. Su Imran dake faman zaman jiran tsammani na zaune a falo dan tunda suka leƙa ɗakin Dada suka samu yana barci har lokacin basu zauna ba suka sake dawowa falon. Sai dai abinda basu sani ba likimo Dadan yay musu yana jin motsin shigiwarsu a lokacin, baya son su san yasan abinda suke ɓoyewar, dan haka yay likimo ɗin.
Shigiwar Shugaban ƙasa Yusuf Shu’aibu Tafida ba tare da hayaniya ba ya sakasu miƙewa tsaye a tare. Basuyi mamakin ganinsa a shigar ɓadda kamar ba, kuma ba tare da yan rakiya ba sai dogarinsa kaɗai. Sai da ya zauna, dogarin nasa ya juya ya fita a falon sannan yay musu nunin su zauna suma.
Kawuna suka jinjina cikin girmamawa, sannan suka zauna suna gaishe shi. Da kai kawai ya iya amsa musu. Daga haka shiru ya biyo baya na tsawon sakanni kaɗan, babu wanda ya yi magana kowa da abinda ke a ransa.. Janar ne ya katse shirun nasu da faɗin, “Yana ina?”.
Ƙofar ɗakin da Dada yake Faro ya nuna masa. “Ranka ya daɗe yana ciki yana barci”.
“Muje in gansa”.
Ya faɗa yana miƙewa. Suma duk miƙewar sukai. Imran a gaba Janar a tsakkiya sai faro ƙarshe. A mamakinsu suna shiga da sallama suka samu Dada a zaune ya jingina da gadon idanunsa a lumshe. Da ɗan sassarfa Imran da Faro suka ƙarasa garesa har suna haɗa baki wajen tambayar, “Ka tashi?”. Idanun sa dake lumshe ya buɗe a hankali ya sauke a kansu. Sai kuma ya jinjina kansa yana maida dubansa kan Janar. Yanda Janar ɗin ke kallonsa ko ƙyaftawa babu ya saka Dada sakin ƙaramin murmushi a karo na farko, sai kuma ya fara ƙoƙarin yaye blanket ɗin da yake ciki cikin nutsuwar sa. Karo na farko shugaban ƙasa ya matso gaban gafon, tsayawa yay a gabansa sosai yana mai dafe hannunsa da girgiza kai alamar kar ya sauka. Nan ma murmurshi ƙarami Dada yayi. Sai kawai Imran ya gyarama janar kujera a gaban gadon suka fice shi da Faro a ɗakin tare da rufe musu ƙofa...
Janar yakai zaune, har lokacin hannunsa na riƙe dana Dada tamkar mai gudun ya ɓace masa, murya ƙasa amma da nauyin fitar sauti ya furta, “Na yi maka laifi. Haysam”.
Dada ya ɗan murmusa, murmurshi irin na dattako da kamewar nutsuwa, sai kwarjininsa ya sake bayyana da cikar kamala. Kaɗan ya motsa lips ɗinsa ya furta, “Ranka ya daɗe, bazaka taɓa zama mai laifi ba a wajena. Duk abinda ka gani a rayuwar bawa ƙaddararsa ce, sai dai idan tazo a mummunar ƙaddarar saɓama UBANGIJI wannan kam daga mu ne da jagorancin shaiɗan. Ina fatan kana cikin ƙoshin lafiya, ina kuma tayaka murnar tare da addu'ar baka ikon sauke nauyi da haƙƙokin al'umma. ALLAH yasa baka cikin shugabannin da zasuyi dana sanin samuwar mulki a garesu a ranar rarrabe ayyuka”.
“Amin ya rabbi Haysam na gode sosai. Sai dai ka sani shi gudanar da wannan mulkin namu ne a tare, dan kana da muhimmanci a cikinsa wajen sauke nauyin haƙƙin al'ummar ƙasar nan. Shiyyasa nake jin kaicon kaina na kasa kare ka da nayi a shekarun baya.”
Dada ya sauke numfashi, kafin cikin nutsuwa irin tasa ya furta, “ALLAH ya fi kowa iko. Shi ne Alƙali mafi adalci. Wannan rubutacciyar ƙaddara ce tun daga alkalamin farko. Sir ka daina damun kanka”
Kai Janar ya jinjina yana sauke numfashi mai nauyi, tabbas ya yarda ilimin addini duniya ne, wanda ya samu wannan ilimin yay kuma aiki da shi ya more, dan kasancewar Haysam a yau ya tabbatar masa da hakan. Sake duban Dada yayi cikin katsewar tunani ya cigaba da faɗin, “Na zo ne ba a matsayin shugaban ƙasa kawai ba. Na zo a matsayin soja… a matsayin mutumin kuma da ke bin ka bashi.”. Ya ɗan dakata, yana kallon idanuwan Dada kai tsaye. “Akwai guba a jikinka Haysam.”
Maigadi ya buɗe musu gate, Mu'azz ya shige da motar yana samun waje yay parking. Sun fito suna gulmar ƙanin maigadi Sanda dan gayene, akwai son yin gayu sai dai irin namu na ƙauye.
Har zasu wuce ciki sabon driver ya iso wajen yana kiran sunan Nimrah. Kusan lokaci guda Nimrah, Ruky, Mu'azz suka juyo da mamaki. Nimrah da ƙirjinta yay mummunar bugawa da ƙyar ta iya daurewa ta amsa masa. Sai dai ta kasa motsawa taje inda yake sai shine ya ƙaraso. Ledar hannunsa ya miƙa mata yana faɗin, “Yaron nan daya kawo mage ranar ne yace a baki. Yace a gaishe ku ke da yar uwarki”.
Ji Nimrah take kamar jikinta na rawa. Ta dai daure ta amsa tana gyaɗa masa kai dan ta kasa magana. Shi kuma bai damu ba ya juya ya bar wajen. Sai ma Ruky ce dake ƴar dariya cikin tsokana ta ce,.........✍️
Jininta na tsinkewa ta ciroshi, haka ta shiga buɗeshi zuciyarta na rawa. Kamar Ranar kuwa sai ga takarda ƙarama a ciki, ɗauka tai ta buɗe.
_Da alama baki duba saƙon ranar ba ko? To ki sani, cigaba da sakacinki na nufin yin dana sani. Duk da kuwa a cikin dana sanin kike shekaru da dama. Idan kuma bakiyi gaggawar dubawa ba zaki dawwama a dana sanin har karshen rayuwarki musamman idan kika fara cin karo da gawar wani a cikin gidank....._
Batama iya ta ƙarasa ba saboda wani yuuuu data risketa na hajijiya. Ta miƙe zambar tana nufar inda suke ajiye handbags ɗinsu. Laluben ta wadda tai amfani da ita a ranar ta shiga yi dan ko books ɗin batama cireba a ciki. Haka ta zazzageta litattafan suka zubo ƙasa. Tsabar ta rikice tama manta littafin da ka rubuta saƙon yake a ciki a ranar, dan haka dukansu ta shiga buɗewa ɗaya bayan ɗaya sai ana ƙarshe taga takardar, ɗauka tai ta sake karantawa, jin book mai jan bango yasa ta ɗaukesa ta fara buɗo shafukan ƙarshe tana duba lamba harta samu wanda akace. Data buɗe shafin bataga komai ba, sai da ta maida zata rufe ta farga da memory card da aka tura ciki sosai kaɗan ake ganinsa. Tana jawo shi ta wani sauke ajiyar zuciya mai nauyi, sai da ta zuba masa ido ranta fal tambayoyin da basu da amsa. Dai-dai nan aka fara buga ƙofa dan haka ta miƙe tana tattare books ɗin da sauri ta maida a bag ɗin, memoryn ta saka a cikin bra dan dole ta nema waya yanzun nan.
Koda taje ta buɗe ƙofar sai taga Afrah ce. Da ƙyar ta daure ta ce, “My Afry ya akayi?”.
“Aunty yunwa nake ji, kuma ke nake so kimin noodles”.
Kai ta iya jinjina mata kawai ta kama hannunta suka fita......
<%><<%>><%>
A yau Adeel ya sake dawowa ƙasar bayan tafiyar kwanaki da yayi amsa kiran mahaifiyarsa. Sai dai masaukinsa na hotel ɗin can ya fara sauka, dan kwana biyu kawai yake ganin zai yi ya sake komawa sai ya kammala uzirin daya taso masa sai ya dawo sannan yayi shirin da yake so. A bazata Hajiya Hasiba da suka samu labarin yaje gida batare da gaya musu ba a bakin First Lady taga kiran nasa a yau. Sai da gabanta ya faɗi, ta daure da ƙyar dai ta ɗaga dan voice call ne na WhatsApp yay mata. Tashi tai a falon dan duk suna zaune ne idan ka cire Mamawo da bata ƙasar ma. Nabeeha na charting da ƙawayenta ne. Su Amima na kallon Film, sai dai hankalin Nabeeha ya rabu ne gida biyu da tunanin hukuncin data gama yanke ma kanta na komawa gidan Abbansu itama kamar Ismat. Dan haka koda taji Momyn tana gaisuwa da yanayin girmamawa taji a ranta Adeel ne, dan duk da tana tare da manyan mutane girman da take bama Adeel da banne dana kowa. Kuma zata iya girme masa, sai dai bazata haifeshi ba a kwatance duk da tayi karatu kafin aure, ita ba'ai mata auren ƙarancin shekaru ba kamar yanda take basu labari........
((%))★((%))★((%))
Har washe gari duk yanda Nimrah taso samun waya ta saka memoryn nan hakan ya gagara, ba kuma samun wayar ne mai wuya ba, keɓewa gefe ne ta gagara samu. Dan kowa yau na gida su Mammah ce ma ta ɗan fita tare da Uncle Bilal kuma zuwa sha biyu suka dawo. Gashi tana fashin salla. Ruky ce kawai ke shiga yi balle ta fake da wannan. Da dare kuma suna tare da Ruky, bata son fito mata da abinda ke faruwa saboda ance wani zai mutu. Koda Rukyn ta tambayeta ma littafan da Sayyid ya kawo kawai ta nuna mata cewar ta kaisu cikin littatafan su dake shirye a ƴar kanta, wajen yana a ƙasan hannun bene ne matsayin study table ɗinsu.. Ita kuma tana bata labarin yanda sukayi da su Uncle's jiya.
Nimrah bata samu yanda take so ba sai da kowa ya tafi sallar magriba , ta tabbatar sai isha'i kuma. tana ganin Ruky ma ta kabbara salla ta zare jikinta tabar bedroom ɗin zuwa sama da wayar Mammah a hannu, dan tasan itace zata jima bata fargaba fiye da sauran. A sama a kwai ɗakin kusan ƙarshe da ƙofarsa ta ɗan juya ma nasu Yaya Ammar, shi ta shige. Babu kowa a ɗakin babu ma wanda ya taɓa zama cikinsa. Amma akwai kaya da aka ajiye sai dai komai na a leda a jingine kawai.44
..........“Da alama fa Sayyadi Kamal ya buɗe wuta Sisi, kwanaki a gidan Aunty Mimi books, kwana biyu da suka wuce ma haka, yau kuma mi muka samu?”.
Har Nimrah ta sakar mata ledar sai kuma ta amshe da sauri saboda tuna takardar cikin wancan saƙon. Dai-dai Mu'azz na ƙarasowa yana tambayar, “Sayyadi Kamal ɗin dai again yau ma?”.
“Ai kuwa dai Yaya Mu'azz, halan bakuyi masa maganar da kuka ce ba?”.
Ruky ta bashi amsa cike da shaƙiyanci. Sai dai kafin yay magana Nimrah tabar gurin da sauri, ga kuma su Yaya Ma'aruff sun shigo suma gidan da alama daga wani waje suke dan a ƙafa suke, sai ya zam hankalinsu Ruky ya rabu har su Yaya Ammar ɗin suka tambayesu lafiya ganin yanda Nimrah ta wuce ciki kamar da sassarfa. Cikin takaici Mu'azz ke sanar musu wai saƙo sayyadinsu na islamiyya ya aikoma Nimrah.
“Saƙon mi?”.
Yaya Ma'aruff ya tambaya.
Kallon Ruky Mu'azz yayi da faɗin, “Wlhy Uncle ban sani ba nima. Ruky ce tasan komai duk da dai ranar muna gidan Daddy ya aiko mata books nan ma”.
Hankalinsu duk suka maida akan Rukyn, sai duk taji tsoro ya kamata. Da sauri ta ce, “ALLAH ba komai fa Uncle, kawai dai ina ga litattafai ne.”
Yanda tayi yasa duk suka fahimci akwai abinda ya dace su sani bayan hakan. Dan haka Yaya Ammar ya ce, “Kinga zo nan”.
“Uncle nace fa ba komai ALLAH”.
“Nima ai bance da komai ba Ruky, canai kawai kizo naji.”
Ita tsoronta kar suji son Nimrah yake a musu faɗa, amma babu yanda ta iya ta ƙarasa inda suke. Wani lokacin Yaya Bilal ya fisu sauƙi su ukun nan har Dadan ma. Amma yau sai ga Yaya Ja'afar cikin lallashi yana tambayarta ta faɗa musu bazasu musu faɗa ba. Minene tsakanin Nimrah da Sayyadin nasu?.
“Idan kuma bazaki faɗa ba zan sanar da Yaya.”
Tasan Daddynsu ake nufi, dan haka ta shiga girgiza kai, “A'a Uncle dan ALLAH karka faɗa masa. Dama kawai shi Sayyadin yana son Ninah ne. Amma wlhy bata kulashi, kuma ka tambaya ma kaji”.
“In bata kulashi miyasa yasan gidan ku?”.
Yaya Ma'aruff ne yay magana yanzu. Da sauri Rukyn ta ce, “Randa ya kawo mage ne, sai kuma ranar sunan Baby Nawal ya kai saƙo gidan Mah-mah na books, kuma can gidan ma muka mantasu. Shekaran jiya ma a gidan Daddy haka”
Ammar zai yi magana Yaya Ja'afar ya hanashi ta hanyar riƙe masa hannu, ƙofa ya nunama Rukyn da faɗin, “Shike nan shige ciki”.
Aiko da gudu ta wuce. Koda ta shiga falo ba taga Nimrah ba sai su Aunty Biebah, sai kawai ta rungume Biebah ɗin, kafin ta saketa ta koma kan su Aunty Lailah tana tambayar ina Mammah?. Bedroom suka nuna mata inda Nimrah dama tana ciki, dan itama tana shigowa ta gansu sai ta shanye tashin hankalinta tayi kamar yanda Ruƙayya tayi sannan ta shige bedroom ɗin Mammah. Tana rungume da ita itama Rukyn ta shigo, sai kawai itama ta rungume Mammah ɗin dan kewarta suke ji mai girman gaske......
==============
Da daddare kamar yanda Daddy Imran ya faɗa yazo yay ma Mammah sallama akan zaije wani aiki. Amma zai jima dan zai iya ɗaukar wata ɗaya ma. Mammah ta jimanta sosai, amma tai masa addu'a ranta duk babu daɗi. Ganin Imran na rage mata kewa Dada sosai a zuciyarta. Shiyyasa bata cika son taga shima zaiyi nesa da su ba. Sai dai babu yanda suka iya tunda aikinsu ne.
Su kansu su Yaya Ma'aruff sunji babu daɗi, dan kamar dai Mammah ɗince Imran na ɗauke musu kewar Dada. Amma da yake su maza ne sai suka danne suka bishi da addu'a suma. Daga nan suka taɓa hira Ruky da Nimrah na jera masa tsarabar da suke so idan zai dawo harda wayoyi. Duk da dai Nimrah dauriya kawai take yi tun ɗazun hankalinta nakan saƙon Sayyidi Kamal da bata samu ta duba ba. Ƙarfe tara dai-dai Imran yabar gidan, daga nan kuma airport zai wuce dan a can zasu haɗu da Dada kawai...
Bayan wucewarsa Nimrah ta faki idonsu ta wuce ɗaki ganin hankalin Ruky ya koma wajen yima su Abees homework ita da Mu'azz. Gabanta sai faɗuwa yake, tana shiga ta maida ƙofar ta rufe harda mirza key dan jikinta ma rawa yake. A haka ta buɗe ledar ta leƙa, a mamakinta yau ma books ne kamar koyau she. Sai dai yau guda ɗaya ne kawai, hisnul muslim ne kuma ƙarami.
Received at