KIDA A RUWA BOOK2 BY BILLYN ABDUL

Author :  Billyn Abdull Category :  African Stories & Novels

Chapter   12 / 42

33K to 36K   out of 125.4K words

rufe gate ya nufesu, dole shima driver ya bishi suka iso inda suke. Rissinawa sukai suna gaishesu duk da kusan sa'an Imran yake shi sabon driver, koma ya iya girmarsa kaɗan duk da shi Imran akwai jin daɗin rayuwa da kulawa da lafiyar jiki irin ta soja a tattare da shi. Uncle Nasiru yana tsokanar su. Shi ko Imran sai ya ɗan zuba ma sabon driver idanu. Har sai da Uncle Nasiru ya ce, “Imrana yaya dai? Ko ka san shi ne?”.
Cikin ɗan murmushi Imran ya girgiza kai da faɗin, “A'a Uncle. Kawai na tafi wani tunanin ne daban”. Bai jira amsawar Uncle Nasiru ba ya juya ga drivern ya amsa masa gaisuwarsa. Daga haka suka bar wajen driver na binsu da ido. A zuciyarsa kam dake bugawa ayyanawa yake (lallai akwai matsala. Shegen nan ko bai gane ni ba ya tsargu da ni. Lallai dole na canja takuna kenan. Dan banzo nan dan na tafi batare da na kammala abinda ya kawoni ba) a zahiri kam miƙewa yay ya koma gate ya zauna a kujera. Sai kuma ya zaro wayarsa ƙaramar nokia ya shiga danne-danne kafin ya kai kunnensa.....KIƊA A RUWA 2

25

..........★A falo kam daga Imran har Uncle Nasiru sunji matuƙar daɗin ganin yanda jikin Mammah ya ƙara ƙyau. Da alama ta samu maganin da yafi wanda take samu anan gida. Dan wannan ne karon farko da suka fita Egypt ɗin dama. Kasancewar su Nimrah duk sun wuce islamiyya da ƙyar gidan shiru, dan ca sukai bazasu ba yau suna murnar dawowar Mammah. Sai da Yaya Ma'aruff ya fatattakesu sannan kowa ya wuce baki a sama. Sai Biebah kawai itama bata jima da dawowa daga school ba. Mu'azz yabi Imam gida.
Mammah ta kalla Biebah dake laƙai-laƙai ɗin cin abinci saboda bata jin daɗi yau da ciwon kai ta dawo makaranta ganin Mammah ɗin ne ma ya ɗan watsakkar da ita. Sai dai ganin baƙon dake gidan ya tsaya mata a zuciya kamar sauran ƴan uwanta. Dan yanzu haka ma Aunty Momy da Aunty Ummi da Ammar na ɗakinta suna sake tattaunawa.
“Biebah tashi kira Uncle ɗin ku”.
Idanu Biebah ta ɗago tana kallon Mammah, sai kuma ta amsa da to cikin sanyi tana tashi.
“Kina lafiya kuwa Biebah?”.
Cewar Imran.
Idanunta na cika da ƙwalla ta ce, “Yaya kaina ke ciwo”.
“Ayya Auta stress ne sannu. Jeki dawo kizo kisha magani kije ki ɗan kwanta kafin akkunayen gidan su dawo su hanaki”.
Kai ta jinjina masa. Shima Uncle Nasiru yay mata sannu. Nan ma amsawa tai ta wuce aikar Mammah...

Babu jimawa ta dawo tace yace gashi nan zuwa. Bata zauna cigaba da cin abincin ba ta ɗauka plate ɗin takai kitchen. Koda ta dawo da ruwa a hannunta ƙoƙarin wucewa tai ɗaki. Dai-dai nan Uncle Tasi'u ya shigo falon da sallama. Duk amsawa sukai suna kallonsa. Sai dai zaram Uncle Nasiru ya miƙe yana kallonsa. Shi ko Imran bai san shi ba a zahiri sai labari a sanda wancan abin ya faru, dan haka babu wani alamun mamaki ko damuwa a tare da shi. Sai ma sannu da zuwa da yake jera masa. Sai dai ya gagara amsawa dan hankalinsa shima gaba ɗaya yana kan Uncle Nasiru ɗin ne.
“Tasi'u!”.
Uncle Nasiru ya faɗa cikin matsanancin mamaki da al'ajabi. Karo na farko Tasi'u yay ƙasa da kansa, idanunsa na cika da ƙwalla. Fin sakan biyar kafin ya sake ɗagowa tare da takowa inda Uncle Nasiru yake ƙafafunsa nayi kamar suna rawa. Yana zuwa gaban Uncle Nasirun kawai sai ya zube akan gwiyawunsa. Imran ya zaro idanu waje sosai yana miƙewa, dan zuwa yanzu kam ya fahimci lallai akwai matsala, sannan baƙon yana tare da wani babban al'amari, yo dukda ba yaro bane babba da shi ya durƙusama Uncle Nasiru. Mammah ya kalla, ya ga ta duƙar da ƙai itama kamar mai kuka. Sai shima ya girgiza kansa. Muryarsa a raunane ya ce, “Mammah waye shi dan ALLAH? Naga kuna kama ba ɗan uwa bane ba shin?”.
Ɗagowa Mammah tayi ta kalla Imran tana ƙoƙarin maida hawayen da suka cika mata idanunta. Fuskarta da ɗan murmushi. Babu wani ko ɗar ta amsama Imran tambayarsa. Dan har cikin ranta kallon Imran take dai-dai da su Haysam. Jinsa take tamkar ɗan data ɗauki cikinsa ta haifa.
“Imran Tasi'u ƙanina ne uwa ɗaya uba ɗaya. Baka san shi bane saboda wasu abubuwa da suka faru a baya. Amma sun riga sun wuce na yafe masa. Mun haɗu da shi a asibiti nd kwana huɗu kenan.”
Gaba ɗaya Imran sai yaji kamar ma yayi mutuwar tsaye. Ga kukan Uncle Tasi'u daya cika falon. Dan kuwa ya riƙe ƙafafun Uncle Nasiru ne yana raira kuka da kalmomin ban haƙuri kamar wani yaro. Yayin da shi Uncle Nasirun ya gagara sake iya cewa komai yana tsaye kawai shima idanun nasa sun kaɗe jazur.
Kukan Uncle Tasi'u ne ya sakko da su Aunty Ummi. Ko muce Biebah taje ta kirasu dan komai dake faruwa tana kallo daga inda take laɓe. Ammar daya gama kaiwa wuya cikin fushi ya ce, “Ni wlhy wannan drama ɗin ta isheni haka nan.”
Duk juyawa su Mammah sukai suna kallonsu, dan basu san da sakkowar tasu ba. Sai dai kan wani yay magana Aunty Ummi ta ce, “Ba kai kaɗai drama ɗin nan ta isa ba Ammar harda mu ma. Shiyyasa ma su Yaya Ja'afar suka bar gidan, dama kuma jiran zuwan Uncle Nasiru kawai mukeyi muma. Idan Mammah nada zuciyar kawaici da haƙuri mu bamu san wannan ba, babu yanda za'ai maciji ya saremu a bakin rami mu sake maida ƙafarmu da tunanin bazai sake na biyu ba. Ai ko hausawa sunce sanin hali yafi sanin kama.
Dan haka Uncle! Yaya kodai ku bashi shawarar ya koma inda ya fito, ko kuma ya nema masauki a wajen wannan gidan magana ta gaskiya”.
Tana gama faɗar haka ta juya zata bar falon tana hawaye. Take mata baya su Ammar sukai suma. Mammah zata dakatar da su Uncle Nasiru ya girgiza mata kai alamar ta barsu....
Dole Mammah tai shiru, shi kuma ya miƙe yana sake faɗin, “Tasi'u tashi muje can gidana, mu basu lokaci nan da kwana biyu.”
Daga shi har Mammah ɗin babu wanda yay jayayya, dan Uncle Nasiru yaya suke kallonsa uwa ɗaya uba ɗaya. Bayan wucewarsu shima Imran bai jima ba ya wuce gida abubuwa da yawa na masa kai-kawo a rai da zuciya......

(((★)))(((★)))(((★)))
★PRISON★

Yana komawa ɗakinsa ya zauna a gefen gadon sa yana kallon sojojin dake ƙoƙarin ɗaura tvn da suka kammala haɗawa a jikin bangon ɗakin. Baiyi musu magana ba, dan ko gaisuwar da sukai masa bai amsa ba a sanda ya shigo hannu kawai ya ɗaga musu. Suna kammalawa suka fice daga ɗakin tare da maida ƙofar suka rufe masa. Shima sai ya rufe idanu kamar yana barci amma ƙwaƙwalwarsa ce ta shiga aikin aunawa da lissafin abinda ya faru.
“Facemask Analysis. Camara jikin agogo”. Ya furta a saman lips yana wani ɗan gajeren murmushi har lokacin idanunsa a rufe. A zuciya ya cigaba da ayyana suffar mutumin dalla-dalla da irin ƙwaƙwalwar ma'aikacin daya san aikinsa. (Fuskar bogi, agogo, tsayayyun idanu na masu busashiyyar zuciya da shekarun girma na tantance gwagwarmayar rayuwa na tsawon lokaci. Yanayin motsin ƙwayoyin cikinsu na ƙwararren operatives. Hakan na nufin wani daga cikin manyansu ne. Ba sabon shiga ba. Barazanar da ya faɗa. Sun ce suna sarrafa shugabanni… hakan na nufin akwai infiltration a cikin gwamnati. Wannan na iya zama sashin da ke kai rahoton Board of Inquiry. Ya ambaci makusanta. Hakan na nufin da damar su Imran ya zo wurina shekaru biyar da suka wuce. Yanzu kuma sune suka saka aka dakatar da shi. In dai haka ne to akwai idanu dake zagaye da Imran cikin rundunar soji ko wajenta, lallai Imran zai iya shiga haɗari akoda yaushe dan ko zai mutu bazai bisu fuska da fuska ba.
Ya furzar da iska mai nauyi yana runtse idanu, dan Imran wani sashe ne na jikinsa da taɓashi tamkar ruguza jarumtarsa ne.
Abu na uku tambayar su (Me yasa suka barni da rai har yanzu? Nima wannan tambayar ta jima a raina. Tabbas da nine a matsayinsu, zan kashe wanda nake tsoro musamman in haɗarinsa zai zama babbar barazana ga ƙasata bawai a karan kaina ba. Amma su suna bukata na a raye. Me yasa?) yay shiru na tsawon lokaci, sai kuma ya tashi zaune da ƙyau ya ɗauki pen da takarda ya rubuta wannan tambayar.
_“They need me?. For what? To watch me? To use me? Or to fear me?”_
Pen ɗin ya kai saman lips ɗinsa da suka ɗan bushe dan yau yana azumi. Abu na huɗu (Wasan da suke cewa ya fara… hakan yana nufin wani babban shiri da suke da shi a wannan tsakanin kenan? Wani sabon hari ne?. Ko wata rawar juyin siyasa?. To amma ai basa buƙatar mutum kamar ni wajen gane kosu su waye?, ko ina matsalar?. Wannan kuskurensu ne ko ni ne ban fahimta dai-dai ba?) ya sake yin shiru alamar dogon nazari.
Tsohon lokaci yana kai kawo da tunaninsa, sai kuma ya kai dubansa kan television ɗin da aka saka a ɗakin. Karo na farko ya miƙe yana ajiye littafin hannunsa da pen ɗin, gaban tvn ya isa, sai da ya gama duba ko ina na jikinta ya tabbatar babu camara sannan ya ɗauka remote ya fara searching channels, tashoshin dake cikin decoder ɗin da aka haɗata da ita duk zaɓaɓɓune. Domin guda uku ne kacal ba'a komai a cikinsu kuma sai abinda ya shafi labarai. Labaran ma ba kowane labari ba. Dan a yanzu dai kusan harkokin siyasa ne da campaign da aka fara kusan wata uku kenan. Idanun ya janye a hankali cikin salon yin luuu da su ya maida gefe da sakin murmurshin nan nasa na ƙeta. Sai kuma ya maida remote ɗin ya ajiye inda ya ɗauka ya koma bakin gadon ta sake zama..
Gaɓar da tafi tsaya masa ce ta sake maimaita kanta a brain ɗinsa. (Sun ce suna sarrafa zuciyar manyan. Idan haka ne, bayanan da Imran ya kawo min game da janar mai ritaya… dole sai na sake nazari. Domin kuwa wani daga ciki yana iya zama mai sarrafa Janar a gefe, da wannan damar kuma kaɗai za'a iya cimma Imran. Dan tabbas tunda har suka faɗa ya fahimci cewa ziyara ta farko da ta biyu na Imran sun haifar da damuwa a ɓangaren kungiyar shaiɗanun nan, shiyyasa ma suka hana shi cigaba da zuwa.
Ya ɗan murmusa kaɗan, dan ya fahimci abu mafi mahimmanci har yanzu suna tsoronsa. Shiyyasa suka hana a ziyarcesa, suka hana yay communication da kowa, suka saka aka killaceshi inda baya ganin kowa sai masu tsaronsa dake kawo abinci dama duk abinda yake buƙata. Ya jima da gane a jikin masu tsaronsa akwai camara dake isar da saƙon shigarsu da fitarsu wajensa. Zuwan baƙon nan ma ba saƙon da yazo faɗa bane kawai maƙasudin zuwansa nan, suna son suga ko ya raunata a zuciya zuwa yanzu. Suna son su gane ko ya ragargaje da raunin kaɗaici. Suna son su tabbatar ko har yanzu yana da ƙarfi daga irin ƙarfin da suke tsoro. Gaba ɗaya ma sai yaji ya sake raina wayonsu. Dan da da gaske, suna da ƙarfin ikon da suke faɗa, ba zasu zo su gaya min ba. Babu mai saƙon barazana da ikon cikakke sai wanda yake jin tsoron wanda aka aika wa saƙo.
Yay ƙwafa, saboda wannan tunanin ya ƙara masa ƙarfin gwiwa, da fushi, da nunin ya sake tashi tsaye da shirye-shiryesa. Dole kuma ya aikama Imran saƙo batare da jinkiri ba...........✍️KIƊA A RUWA 2

26

..........KWANA UKU da dawowar Mammah suka karɓi baƙuncin ƴan Bauchi da sukazo sunan Aunty Mommy. Gwaggo Khadijah, Gwaggo Alawiyya, da Gwaggo Nanah. Sai matar Uncle Jamilu da wannan ne karonta na farko da tazo. Dan tun abinda taima su Mammah ɗin a wancan shekarun take jin matsanancin kunyar zuwa inda suke. Sai dai har cikin ranta taji nadama. Musamman da ayanzu su Mammah ɗin ne riƙe da rayuwarsu tunda su Ja'afar ne suka buɗema Uncle Jamilu babban shago kayan sakawa a can Bauchin ƙyauta, da shi suke ci suke sha. Sannan kuma suka ɗauki nauyin karatun yaransu a makaranta mai ƙyau. Gwaggo Nanah kam ta fita zakka a cikin ƴaƴan Inna, tana iya ƙoƙarinta dama tun ma suna cikin wahalar rayuwa kamar yanda Gwaggo Khadijah da Gwaggo Alawiyya keyi. Sai dai tsoron ƴan uwanta su Yaya Babba ke hanata zuwa inda su Mammah suke. Wannan karon kuwa itama sun mata halin nasu, dan mijinta ya gudu ba'a san inda yake ba shekara biyu kenan duk sun ƙi taimaka mata, ga wahala tana ciki ita da yara. Babu mai taimaka mata sai Uncle Jamilu da su Gwaggo Khadijah ɗin. Shiyyasa ta yanke shawarar zuwa sunan nan danta sanar ma Mammah halin da take ciki ko zata samu wani taimako. Kuɗin mota ma Uncle Jamilu ne ya biya mata.
Ba ƙaramin daɗi Mammah taji da ganinsu ba. Musamman Gwaggo Nanah da matar Uncle Jamilu Badiyya da suketa ɗari-ɗari suna jinjina hukuncin UBANGIJI da ganin gidan da Mammah ke ciki a yau da zuri'arta. Lallai duniya budurwar wawa, wanda yace shine kuwa ba shi ɗin bane ba.
Tuni Mammah ta saka su Kulu masu aiki suka gyaro musu ɗakunan baƙi, dan sunyi isowar wuri lokacin sha ɗaya na safe, sunce tafiyar asuba sukayi dan mota suka ɗakko kai tsaye. Mammah dake ta farin ciki ta ce, “Ku fara yin wanka da ruwa mai zafi sai kuzo ku karya. Bara kiga nasa a kakkaɓo min yaran nan duk suna gado jiya sun raba dare ne suna shargallen su”.
Gwaggo Khadijah tai ƴar dariya da faɗin, “Aike da gayyar nan taki Maman Ma'aruff sai ALLAH. Kinga barsu suyi barcinsu, muda ba yau zamu koma ba. Anjima ma wata hidimar ce ta bikin suna a kansu”.
“Kamar ko kin san harda fati suka shirya wai. Biebah ce kawai ta iya bin su Lailah gidan maijegon, yanzu babu jimawa suka fice suma dan jiya sai goma suka dawo”.
Yanzu kam Gwaggo Alawiyya ce ta ce, “Kai waɗan nan yara ALLAH dai ya saka musu da alkairi. Wlhy samun surukai irinsu sai an tona Addah.”
“Ai su Shariffa sun wuce surukai ƴaƴane Alawiyya. Babu abinda zan cigaba da musu sai addu'a da fatan suma ALLAH ya basu masu yi musu”.
Gwaggo Nanah dake jinjina kai ta ce, “Wlhy ki musu ki ƙara muma muyi musu, ga gidan Yaya Babba can su Haire su da surukai ba arziƙi. Jiya matar Haƙilu kamar zatai dambe da Haire akan ɗanta, ke bakiji wannan tujara ba abin kaico”.
Murmurshi Mammah tayi, saboda a saki zancen ta ce, “ALLAH ya ƙyauta to, ai zamanin ne ya zama abin tsoro sai addu'a kawai. Kunga kuyi wankan kuzo ku karya hirar tafi armashi”.
Godiya suka yi ta juya ta fita. Dukan su suna jin ƙaunarta a ransu, Badiyya kam kunyarta take ji sosai shiyyasa tunda suka gaisa tai shiru kanta a ƙasa. Sarai Mammah ta fahimceta, dan haka ta ƙuduri aniyar cire mata abinda ke ranta gaba ɗaya, dan ita babban fatanta ta haɗe kan zuri'ar Abdul-rasheed ba rabuwar kansu ba....

★ Sai sha biyu su Nimrah suka tashi da ƙyar, shima sai da Mammah tazo da kanta ta tashesu. Dan suna yin sallar asuba suka koma gado. Aiko sai shagwaɓa suke mata wai ta barsu sai ƙarfe ɗaya sannan.
“Shike nan kun fasa zuwa gidan sunan kenan? Ai da nasan haka ne sai na tadaku kun wuce Tahafiz. Ga ƴan Bauchi can tun sha ɗaya suka iso ku kuna nan kuna barci”.
Tuni duk suka watsakke, cike da farin cikin jin zuwan ƴan Bauchi. Zasu nufi ƙofa a guje Mammah ta dakatar da su. “Kai kuji min ƙazaman banza. Haka zakuje musu da kayan barci? Ba brush kamar wasu ƙazamai. Maza ku koma ku gyara jikinku, wata taje ɗakin Biebah yanda zakuyi sauri”.
Cike da farin ciki sukace to. Mammah ta fito tana murmurshi. Koda ta dawo falon wajen su Gwaggo Alawiyya ta samu su Ma'aruff sun iso gidan. Dan tun ɗazun ta sanar musu sukace zasu zo yanzu. Sai ko gasu da ledoji niƙi-niƙi na kayan ciye-ciye. Fuskokinsu washe da murmushin ganin gwagwgwannin nasu. Badiyya na sinƙe-sinƙen kai ganin yanda suma basu nuna mata komai ba kamar Mammah sai ta ware aka fara gaisuwa da tambayar yara. Yaya Ja'afar ya ce, “Haba Gwaggo, kwa taho ku kaɗai duk babu yara? Bayan kun san ba ganin juna ake ba tsahon lokaci sai irin haka ta faru”.
“Makaranta tasa haka Ja'afar, amma in sha ALLAHU idan anyi hutu sai su zo. Tunda kudai kun tattaramu kun watsar, yaushe rabonku da Bauchi balle Maiduguri?”.
“Dama idan sunje Bauchin ba ganinsu muke ba Adda

12 / 42