KIDA A RUWA BOOK2 BY BILLYN ABDUL

Author :  Billyn Abdull Category :  African Stories & Novels

Chapter   23 / 42

66K to 69K   out of 125.4K words

4:00 PMƘaramin table ta jawo duk da akwai ƴar ƙura haka ta zauna ta saka wayar Mammah a plane mood dan karma a kira, ta zare memory ɗin ciki ta saka wanda tun jiya ke maƙale a jikinta. Tana tabbatar da ya hau ta wuce wajen videos kawai. Videos uku ne kacal a ciki, jikinka har rawa yake ta shiga na farko tai playing...........✍️     
 
KIƊA A RUWA45


.........Babu abinda kallon videos ɗin nan suka zamewa Nimrah face rikicewar tunani da ruɗanin zuciya. Sakamakon abu uku masu tsayawa a zuciya. Na farko kamammin matar dake kama da ita matuƙa. Matar da ƙwaƙwalwarta ke son hasaso mata abubuwa da yawa game da ita da tuna mata sunanta na uwa mahaifiya da take kira da UMMA a wani ƙarni da ba komai take iya tunawa da ƙyau ba sakamakon ƙaracin shekaru. Sai dai wayonta da kaifin basira na hasko mata abubuwa daban-daban, dan wani ɓangare na brain ɗinta na ƙoƙarin hasko mata kamanin Umman tata da rashin ganin ko hotonta bayan rabuwarsu yasa suka fara disashewa kaɗan, amma dai bata manta da ita ba. Abu na biyu dattijon tsoho shima dake kammani da Umman tata dai, duk da furfurar sajen gemunsa ya lulluɓe kaso mafi yawa a zahiri, abin tsoro da ruɗani shima dai tamkar waccan fuskar ta Ummanta an harbesa da bindiga hannunsa da aka juyar a bayansa da handcuffs tamkar wani dabba. Abin sake rikita lissafin mutum ɗaya ne duk yay harbin, mutum ɗaya tak da taga hotonsa a wannan gidan kuma ake kira da suna DADA, Dada dai da kowa ke girmama sunan matsayin uba jigo na wannan gidan. Shi ɗin nan dai ɗaya tak ya ɗaga bindiga fuskarsa da murmurshin rashin tausayi, rashin imani ya harbi mutane biyun nan dai da take jin tabbacin muhimmancinsu a gare ta mai matuƙar girma ne. Girma mara misali balle iyakar hasashe. Abu na huɗu harbe yara ƙanana da sojoji sukayi, yaran da fuskokinsu ke mata kai-kawo na tabbacin ta sansu fa.
        Ba zuciyar Nimrah ba, hatta ƙwaƙwalwata bugawa take tamkar zasu tarwatse a tare da rawar jikinta daya jiƙe sharkaf da zufa kai kace an watsa mata ruwa ne, ruwan ma na zafi dake saurin bayyana gumi.. Shekarunta sunyi ƙanƙanta sosai a wancan lokacin da har ta gagara iya tuna abubuwa da yawa. Sai dai ko bazata iya tuna komai ba wannan fuskar guda ɗaya tak mai kama da tata bazata mantu a cikin zuciya da ƙwaƙwalwarta ba. Fuskar Ummanta, tabbas Ummanta, Ummanta dai Ummanta da sukai wata rayuwa a baya a wani wajen daba wannan da take ba a yanzu da ba komai zata iya tunawa ba. Sai fuska ta biyu, fuskar sojan daya harbi Ummanta, Dadan nan dai da itama ta sanshi amma ba komai zata iya tunawa a kansa ba. Fuska ta biyu da itama dai Soja kuma Dada ya harba da kansa dake ɗaure cikin sarƙar handcuffs, fuskar tsohon dattijo mai kammani da fuskar Ummanta da tata, wanda tunaninta ya fara dawo mata da matsayinsa na kaka da suke zuwa gaidawa ita da Ummanta, sai dai ba komai take iya tunawa game da shi ba shima. Shima dai wannan soja Dada ne ya harbesa ya faɗi ya mutu, mutuwa fa dai da kowa ya sani kuma yake tsoro. Kai wlhy ita kam zata haukace, lallai tana buƙatar fashin baƙi, fashin baƙi a wajen wanda ya aiko mata da wannan rikitaccen video mai sabauta tunani da ƙwaƙwalwa. Kuma da gaggawa take buƙatar hakan, kai in zai yiwu ma a daren nan maybe hakan yasa ta fahimci abinda ake nufi da a yanzu ta gagara fahimta.
      Sai dai a daren nan dai da tasan bazai yiwu mata ba. Karo na farko da taji zafin rashin waya da riƙe number kowa a rayuwarta, dan data san koda number ɗaya ce tak ta Sayyadi Kamal data nemeshi a yanzun batare da ko zaman yin wannan tunanin mai son tarwatsa mata kanta dake sarawa ba. Kamar an bata umarnin shiga videon ƙarshe da bata kalla ba ta ɗauka wayar da sauri ta koma ciki tai playing. Cikin sa'a kuwa sai ga wata fuska ta bayyana. Fuskar wani mutumi da bata taɓa sani ba. Yana zaune ne kawai tamkar suna video call yana ganinta tana ganinsa. Dan kai tsaye idanunsa akan screen ɗin suke. Kalmar farko daya fara ambatawa ta sakata sake nutsuwa a kallonsa.
        “Naja'atu Nimrah! Na tabbatar idan har kin iso kan wannan videon nawa yanzu tom kin kalla bidiyon baya kenan. Bani da isasshen lokacin janki da nisa. Amma zan baki dama da albishir guda ɗaya da zai fiddaki daga ruɗanin da ko tantama banayi dole ne sai kin shiga a lokacin da kika kalla waɗan can bidiyon guda biyu kafin wannan. Da farko dai sunana Dagger, nine na aiko miki da waɗan nan saƙwanin guda biyu ba Sayyidi Kamal Ba kamar yanda kika ji, na saka sunansa ne dan ki amshi saƙon da muhimmanci tunda shi kin sanshi.
Nimrah kina buƙata ta a wannan gaɓar fiye da kowa a rayuwarki, dan kuwa nine kawai zan iya banbance miki tsakanin aya da tsakuwa ta ainahin RAYUWARKI. Ni ne kawai zan miki fashin baƙi akan abinda kika gani a videos ɗin can. Nine kawai zan kaiki inda UMMANKI take. Ba ruɗani zan saka miki a zuciya ba, amma ni ne kawai zan sanar dake gaskiya akan mutanen da kike rayuwa da su a yanzu. Idan kuma baki yarda dani ba na baki ɗan lokaci ki bincika ina wanda kuke kira DADA anan gidan yake? Da gaske yana wata ƙasa ne ko yana prison saboda abinda ya aikata a wannan videos ɗin dana nuna miki. Idan kika samu wannan amsar tayi kama da abinda na kawo miki zaki iya nemana ta wannan number ɗin ni kuma zan sanar miki inda nake na miki dukkan bayanin da kike buƙata. Sai dai da sharaɗi guda biyu tak, wanda in har kina buƙatar duk wannan dole kiyi abu biyun nan. Na farko ki rufe wanan zancen daga UBANGIJI sai ke, idan kikace zaki bari wani ya sani zaki iya rasa Ruƙayya dan akwai masu son kasheta. Abu na biyu na ƙarshe. A duk inda kika ɓuya yanzu dan ganin wannan video ɗin ki tashi ki saita kanki tamkar komai bai faru ba ki koma harkokinki karki sake ki bari wani ya fahimci halin da kike ciki koda Ruƙayya ɗin ce. Idan ba haka ba zan sake maimaita miki wasu zasu kashe ta. Kar kiyi tunanin kirana da wayar da kika kalla video ɗin nan, idan kina son kirana ki samu wayar wani daban ba ɗan gidan ba. Na barki lafiya. Ki kasance cikin aminci ƴar albarka”.
     Ƙitt videon ya ƙare, ya kuma ƙare ne tare da tsayawar duniyar Nimrah a lokaci guda.......

<<<<<。⁠◕⁠‿⁠◕⁠。>>>>>

      Wauta da ƙuruciya suka haɗu sukai tasiri mai ƙarfi ga al'amarin Nimrah da abinda take ta ƙoƙarin hana bayyanarsa a fuskarta da zuciya. Kamar wasa a daren wannan ranar ko sau ɗaya bata rintsa ba, da Ruky ta dameta da tambaya ma sai ta gaya mata baƙar maganar da ta saka sukai faɗa Rukyn tai zuciya itama ta watsar da ita. Ƙarshe ma ta bar mata ɗakin ta koma ɗakin Biebah ta kwanta. Hakan ba sabon abu bane ga Biebah, dan lokaci-lokaci Nimrah da Ruƙayya kanyi faɗa, wanda yafi shaƙa sai ya dawo ɗakinta ya kwanta ko ɗakin Mammah, hakan kuma baya hana gari na wayewa kaga sun shirya, dan sukan jima ma basuyi faɗan ba. Shiyyasa koda Ruky ta dawo ɗakinta a wannan daren batace mata komai ba ba kuma ya hanata kwanciyar ba. Dan ta tabbatar itama Nimrah ɗin da wuya ta kwana a ɗakin nasu zata wuce ɗakin Mammah ne.
      Sai dai hasashen Biebah bai tabbata ba, dan kuwa a yau Nimrah bama ta iya motsawa a gadon da take kwance ba balle fita a ɗakin duk da taji sanda Ruky ta fice ta bar mata ɗakin. Hasali ma sai lokacin ta samu damar fashewa da kuka saboda nauyin da ƙirjinta yay mata. Daga wannan kukan ne zazzaɓi mai azabar zafi ya rufeta, dama gashi tana period. Haka ta kwana tana rawar sanyi tama kasa tashi ta kashe acn ɗakin, kai ko jan bargo ta rufa ta kasa yi ma. A haka sanyin asuba ya sake bayyana ya kuma mata rijif. Lokacin da Ruky ta shigo ɗaukar rigar sallarta da nishinta ta fara cin karo. Tuni ta manta da wani batun faɗan su ta zabura kanta jiki na rawa. Ai tana taɓa jikinta taji matsanancin zafin da yayi sai ta sake rikicewa, tama fita a guje tana ƙwala kiran Small Mom.
     Zambar Biebah data idar da rakata'ainul fijir ta miƙe tayi ƙofa. Hannunta kawai Ruky ta kama suka juya tana maimaita sunan “Ninah! Ninah batare data iya mata cikakken bayani ba. Sai da suka shiga ɗakin itama hankalinta ya tashi da ganin halin da Nimrah ɗin ke ciki.....

Ana idar da sallar asuba doctor ɗinsu da aka kira ya iso gidan. Kasancewar an maidota ɗakin Mammah har nan aka kaisa ya dubata da mata ƴan tambayoyi. Da ƙyar take bashi amsa wasu ma sai Mammah ke bashi. Ya gama ƴan rubuce-rubucen sa yace yana ganin malaria ce ta saka mata zazzaɓi. Sai ƴar damuwa da kukan da tayi.
      Ba ƙaramin mamaki Mammah tayi ba da jin batun damuwa dana kuka. Amma sai batace komai ba tabar doctor yay aikinsa. Allurori yayi cikin drip ya saka mata, kasancewar akwai masu saka barci a take barcin yay galaba a kanta.
Mammah bata sanarma kowa abinda likita ya faɗa mata ba, ta bar komai a hannunta zata saka ido kan Nimrah ɗin harta fahimci damuwar tata..........✍️46


.........Kwana biyu Nimrah na jiyyar zuciya da jiki ko muce sunayi ita da Hassanar tata Ruƙayya, dan itama dai duk ta zama sukuku da ita. Sannan komai Nimrah tace tana so zata tashi tai mata cike da kulawa. Ita Biebah har dariya ma suke bata kamar ba waɗanda suka gama shan faɗa ba a daren ciwon Nimrah ɗin. Uncle's ɗinsu kam da su Aunty Shariffa kowa ƙoƙarin tattalinta yake, bare kuma Mammah da suka dawo ɗakinta ma kwana tare da ita, dan tace har Nimrah ɗin ta samu sauƙi sannan.
     To Alhamdullah sauƙi ya samu, dan yau juma'a ma har cewa tai zata makaranta Mammah ce ta hanata tace dai Monday, amma taso zuwa kodan ta samu hanyar samun wayar da zatai kiran number ɗin can da aka faɗa mata a video ɗin. Dan duk yanda take yaƙin ture abun a ranta da hakan kanta yin abinda suka ce ta kasa. Kamar wadda ake mintsini da azalzalarta haka take ji. Dan ma bata samun sukunin yin tunani saboda Mammah bata barinta koda yaushe tana tare da ita musamman idan du su Ruky sun tafi makaranta. Amma yau da Mammah ta hana tabi su Ruky makarantar ta gama yankema kanta shawarar koma ta yaya sai ta samu tayi magana da mutumin nan a cikin weekend ɗin nan su haɗu a tahfiz. Da wannan tunanin ta kasance har su Ruƙayya suka dawo daga makaranta. Mazan gidan sukai shirin massalaci suka fita..

       ★Ammar ya fito a mota zaije massalacin juma'a shi da su Abees da Mu'azz sai ga Adeel a hanya shima zai je a ƙasa, sai kawai Ammar ya tsaya suka ɗaukeshi. Mu'azz dake gaba ya koma baya Adeel ya shiga. Haka sukaje Central mosque ɗin tare, bayan idar da salla a ƙa'ida sukan wuce gaishe da Baffan su Imran da Hajjo, dan haka tare da Adeel sukaje, acan kuma suka samu su Yaya Ja'afar da Ma'aruff. Ammar ya gabatar da Adeel matsayin abokinsa makwafcinsu. Su mutanene masu daraja ƴan adam, babu wanda ya nuna komai akan Adeel sai mutuntawa, sukaci abinci a gidan akasha hira duk da shi Adeel baya jin Hausa sai turanci, dan haka hirar duk sai ta koma da yaren nasara.
     Sai da a gaɓar da Baffa ke ma su Yaya Ma'aruff nasiha akan batun Uncle ɗinsu Tasi'u daya koma Lagos akan su manta da komai suyi hakuri su karɓesa kamar yanda Mammah ta hakura ne ya koma Hausa. Ya kara musu nasiha sosai duk da kuwa randa su Nimrah suka zo gidan suka samu Uncle Ammar ya fita da shi sun haɗu ne a gidan Uncle Nasiru dama sun musu faɗa akan batun Uncle Tasi'u ɗin. A ranar dai sun ce komai ya wuce, amma basuce sun yafe masa ba. Shine ya koma Lagos ɗin da nufin zai kawo yaransa gidan Mammah ɗin, washe gari ya tafi. Shine yanzu Baffan ya sake musu nasiha shi da hajjo. Daga haka suka koma batun kasuwanci. Dan shima Baffa ɗan kasuwa ne da sukaci zamani a lokacin ƙuruciya....

     ★★★★★

A kusan dai-dai wannan lokacin Nimrah ce ta faki idon su Mammah datai baƙi Ruky kuma na barci ta nufo gate. Ƙanin Baba maigadi kawai ta samu zaune yana latsa ƴar wayarsa rakani kashi harda ƙyauro a jikinta. Sallamar da tai masa ya saka shi ɗagowa yana kallonta, dan tunda yazo gidan magana bata taɓa haɗasu ba daga ita har Ruky. Saboda kallon marasa ji da rashin kunya yake musu ma shiyyasa bai taɓa fatan wani abu ya haɗasu ba.
      Amma mi, a mamakinsa sai ta masa sallama, baima san lips ɗinsa ya fara rawa wajen amsawa ba. Bata damu ba ta ɗora da gaishesa. Nan ma mamaki ya kama shi. Cikin kasa haƙuri ya ce, “Hajiya kina son wani abu ne?”.
        Nimrah ta ɗan sauke numfashi da waigawa ta kalla hanyar cikin gida, har yanzu babu alamar kowa kamar yanda tai fata, sai sabon driver data hango can wajen mota yana fitowa daga ciki alamar wani abun yake yi wanda ta san bai wuce goge motar ba dan ɗazun taga suna wankewa shi da Sanda ɗin. Kauda kanta tai daga kallonsu dan bazai yiwu yaji maganarsu ba daga inda suke, kuma taga hankalinsa gaba ɗaya baya a kansu ma.
        “Waya zaka ara min”.
    Tai furucin idonta akan wayarsa. Shima da mamaki ya kalla wayar sannan ya sake ɗagowa ya kalleta. “Hajiya waya dai? Kalli fa wayar tawa yanda take.”
        “Karka damu ba wani abu zanyi da ita ba.”
    A zuciyarsa ya furta (wannan yarinyar kuwa anya ba zargina take ba, dan na fahimci shegen wayo ne da ita. Ko kuma wani ne dai ya turota gareni a cikin gidan...)
      “Malam Sanda”.
  Nimrah ta katse masa tunani. Firgigit ya dawo hayyacinsa. Ganin yanda ta tsatstsare shi da manyan fararen idannunta baima san ya miƙa mata wayar ba.
     “Na gode”.
  Ta faɗa a hankali tana barin wajen. Da kallo ya bita, kamar yanda Malam Buba driver ke binta da kallon gefen ido, dan tun ɗazun dama hankalinsa a kansu yake duk da baya iya juyo abinda suke faɗa. Ganin ta amshi wayar Sanda ya sashi fahimtar mi take shirin yi, da sauri ya koma cikin motar kamar bai gama abinda yake ba, ya zaro tashi ƙaramar wayar ya shiga neman layin Dagger daya san zai iya samunsa da gaggawa. Aiko babu wani jimawa ya ɗaga shima daga can, dan kwanakin nan gaba ɗaya cikin ƙaguwar jiran kiran Nimrah yake yi, amma shiru kake ji, sai da ma Molen ke sanar masa bata da lafiya ne kwana biyu sannan. Ko gaisuwa basu yi ba Mole ya fara sanar masa, “Oga ka kasance cikin shiri na tabbatar kai zata kira. Dan gata can ta amshi wayar Sanda ta nufi bayan ɗakin janareton su.”
     Sai da Dagger ya sauke wata wawiyar ajiyar zuciya sannan ya ce, “Mole waye Sanda kuma?”.
       Cikin ƙaguwa Mole ya ce, “Wannan ƙanin Almu ɗin fa da nake gaya maka sunzo ranar daya dawo tare”.
      “Oh-oh na tuna, bara na ɗaga inaga gata tana kira.....”
    Bai jira amsar Mole ɗin ba ya katse kiran.....

      A ɓangaren Nimrah data zagaya bayan ɗakin Gen... Ɗin gidan kuwa da sauri ta fara loda number wayar data kwafe a jikin ƙaramar takarda, sai da ta danna kira ta tabbatar ya shiga sannan ta nema waje ta zauna dan ta tabbatar babu mai zuwa nan a cikin ƴan gidan balle yay tunanin tana nan. Sai dai ma'aikatan gidan irin su maigadi, kuma sai da ta leƙa ta tabbatar babu kowa a ɗakin dan dama maigadi ne bata gani ba acan waje, shiko ƙaninsa Sanda da Malam Buba tunda sun ganta tasan baza su zo b......
       Sallamar da akayi ce ta katse mata tunaninta. Duk da yanda muryar mai maganar ke a buɗe ba daɗin ji dai ta daure ta amsa. Daga can Dagger ya sake matse murya shi a dole yau yana waya da masoyiya, dan jikinsa har tsuma-tsuma yake yana dannewa da ƙyar. Saboda yanda muryar Nimrah ɗin ta dakesa ji yay kamar zai shiɗe....
       “Kana magana da Naja'atu Nimrah ne? Dan ALLAH waye kai?”.
     Da ƙyar Dagger ya iya dannewa ya daidaita yanayin sa ya bata amsa da, “Sani na a yanzu ba shi bane mai muhimmanci, ina ya kamata mu haɗu ya dace ki nema kawai. Dan lokacin da kike da shi a gareni bashi da wani yawa, zan iya ɓace miki a kowane lokaci.”
       Ajiyar zuciya ta sauke a hankali, tare da faɗin, “Shi ke nan a ina zamu haɗun? Yau she kuma? Amma ka sani ina son ganin ka da gaggawa”.
     “Baki da matsala indai ni ne. Kamar yanda nai niyyar sanar miki gaskiya ba zan guje miki ba. Na baki damar ki faɗi a indai zai miki sauƙin mu haɗun batare da ko ƴar uwarki ta sani ba, saboda gudun kar a cutar miki da ita”.
      Ba tsoro Nimrah ke ji ba, tsoronta kawai kada a taɓa mata lafiyar kowa a ahalinta ne. Dan haka ta ce, “Ni bani da inda na sani bayan gidan mu, kuma ba'a barina fita ni kaɗai”.
       “Okay na gane, makaranta fa?”.
   “Makarantar

23 / 42