KIDA A RUWA BOOK2 BY BILLYN ABDUL

Author :  Billyn Abdull Category :  African Stories & Novels

Chapter   7 / 42

18K to 21K   out of 125.4K words

tare suka ƙame tare da yin salute ɗinsa, kafin na gefen damarsa ya furta, “Sir kana da vistor ne”.
      Cak ya ɗan tsaya na sakan, sai kuma ya cigaba da abinda yake batare da yace da su komai ba. Fin mintuna uku, dan har sai da ya cika adadin da yake buƙata kafin ya tashi da ƙyau tamkar ba shi ya gama push-up ɗin ba yaja ƙaramin towel dake jikin ƙarfen gadon kusa da sallaya ya fara goge hannunsa zuwa wuyansa. Sanye yake cikin uniform ɗin prison ɗin, amma hakan bai hana su kasancewa fes ba alamar baya barinsu da datti, sai dai sun koɗe sosai alamar tsufa da gajiya.
A karo na farko ya furta, “Tsawon shekaru biyar kenan a tsarin jadawalin da doka ta sharɗanta a kaina No visitors, no communication. Miya canja hakan a yau daga dokar?”.
     Sake duƙar da kawuna sukai, kafin ɗayan yay magana cike da girmamawa. “Sir muma bamu sani ba. Umarni kawai aka bamu na zuwa da shi inda kake”.
      Idanu ya zuba musu sosai su duka biyun. Wani ɗan murmurshin gefen baki da shi kaɗai yasan yayi kayansa yayi. Ya ajiye towel ɗin a kan ƙarfen gadon ya taka a nutsensa cike kuma da tafiyar nan tasa ta nutsuwa, dattako zuwa gabansu bayan ya saka slippers a ƙafarsa.
       “Ku aikata aikin soja, Captains. Na fahimta.”
     A tare suka sara masa, zukatansu na sake jin rauni, ƙaunarsa da girmamawa.
    “Sir… I’m sorry.”
Suka sake faɗa a tare. Bai ce da su komai ba face miƙa musu hannayesa duk biyu. Dan doka ce fita da shi sai da handcuffs. Jikin sojan har ɗan rawa-rawa yake a ƙoƙarin ɗaura masa handcuffs ɗin, haka dai ya gama suka koma gefe suka bashi hanya. Shine ya fara fita sannan suka bi bayansa har ɗakin ganawar. Vistor ɗin nasa ya juya baya, dan haka bai fahimci ko wanene ba sai da ya zauna a kujerar da aka tanada domin shi.....
 
<<<>>><<<>>>
   ★EGYPT★

       “Mammah dan ALLAH ki daina kukan nan ya isa haka”.
    Ammar ya faɗa cikin tashin hankali muryarsa na rawa idanunsa shima cike da hawaye. Sai kuma ya dubi mutumin da shima ke sharar hawaye ya ce, “Bawan ALLAH ka min bayani dan ALLAH. Minene alaƙarka da Mammah ta? Ku taimaka ku sanar min kada zuciyata ta fashe, dan kukan Mammah ba ƙaramin azabtarwa bace mai ƙuna a zuciyata”.
        Hawaye mutumin ya sake sharewa da handkachiff harda ɗan fyatar majina. Kafin ya kalla Ammar cikin rawar muryar alamun tahowar wani sabon kukan ya ce, “Ɗana ka kwantar da hankalinka, duk da ban san wanne a cikin ƴaƴan nawa ba ina ji a raina ko Bilalu ko Abdul-rasheed (Ammar) ne kai. Dan kune dai ƙananu da zan iya gani a wannan shekarun ba Haysam ko su Ja'afar da Ma'aruff ba”.
    Kafin Ammar yay magana cikin zafi Mammah ta ce, “Har kana iya cigaba da riƙe zuri'ata a cikin ƙwaƙwalwarka amma ka gagara waiwayen inda nake Tasi'u....?”
        “Wlhy Adda A'isha kunya ce ta hanani, tsananin kunyarki nake ji da tsoro da nadamar son zuciyata. Ina ganin bazaki sake kallo na ba a rayuwarki, bazaki sake son ji koda daga wani ne kina da ɗan uwa irina ba. Adda A'isha ni azzalumi ne butulu da ban cancanci gafara daga gareki ba balle marigayi Yaya Abdul-rasheed, dan kuwa mun kasance butulu da ga ni har Bashir da danginsa......”
        “Bashir bai kasance butulu a gareni ba, dan kuwa na tabbatar idan shine a raye komai girman laifin da yake ganin ya min bazai ɓoyema ganina a tsaho waɗan nan shekarun ba. Haba Tasi'u, kun maida ni mara kowa a duniya, mara gata, mara dangi gaba ɗaya. Badan Yaya Nasiru ba da nace ban san daɗin zuri'a ba a duniya. Da ƴaƴan Kawu kamar sun waiwayemu munata zumunci har bikin su Haysam duk dasu a kayi suma yanzu sun sake ɗauke min wuta gaba ɗaya saboda ƙaddarar rayuwa da muka sake shiga. Shike nan kowa ya juya bayansa a garemu dangina dana Abdul-rasheed idan ka cire Jamilu da su Khadijah saboda kawai sune ciki ɗaya da Abdul-rasheed. Wlhy idan kowa zai barni banyi tunanin harda kai ba da muke ciki ɗaya Tasi'u, kada ka manta nice na fita a cikin Inna ka kwanta, sannan nice na gama sha daga jikinta ka amsa. Miyasa zaka gujeni tsawon shekaru ashirin da shida, a talatin kaɗan ne babu rabona da kai fa Tasi'u. Miyasa? Miyasa haka?”.
        “Wlhy kunya ce kamar yanda na sanar miki Adda, dan ALLAH ki yafeni ki gafarce ni na tuba”.
    Yay maganar yana sauka ƙasa ya durƙusa a gabanta tare da riƙe ƙafafunta duk da kuwa shekarun dattijantaka sun bayyana a gare shi shima. Bata hanashi ba, sai kuka da take itama. Ga Ammar dake rungume da ita shima tuni kukan yake, dan a duniya basa ƙaumar ganin hawaye Dada da Mammah na ɗiga. Tsohon lokaci suna a haka kafin Mammah ta fara tsagaita nata kukan ta kama dattijon tana miƙarwa da faɗin, “Shike nan ya isa. Na yafe maka  ka share hawayenka. ALLAH ya yafe mana gaba ɗaya. Ya jiƙan Inna da Baba da Abdul-rasheed da Bashir.
Amma dan ALLAH karka sake yin nesa da ni kaji”.
       Tashi yay ya koma kan kujerar yana share hawayen nasa da faɗin, “In sha ALLAHU har abada bazan sake nesa dake ba Adda, na baya ma kunya ce da nadama ta sakani dole. Amma wlhy a kullum cikin begen son ganinki nake keda zuri'arki”.
       “ALLAH ya rufa mana asiri”.
  Mammah ta faɗa tana shafa kan Ammar alamar lallashi. Ɗakin ya sake ɗaukar shiru na wasu mintuna kafin ta kallesa ta ce, “Mi kake yi a Egypt? Ko nan kake aiki?”.
        “A'a nazo ganin likita ne kawai. Yanzu ina Paris. Sai dai kusan shekara ma biyar kenan na koma ƙasarmu, kawai dai ina zaune a kudanci ne sakamakon tsoro da fargabar tunkarar ki.
     Murmurshi Mammah tayi mai ƙayatarwa da faɗin, “Ja'iri ashe kana shakkata?”.
         “Adda wlhy ina yi dan kece madadin Inna a wajena. Ya bayan rabuwa ya iyalai?”.
      “To sai godiyar ALLAH, Iyalai kuma duk gasu nan sun girma sun zama magidanta. Duk da dai Bilal da Ammar da Biebah basu kai da yin aure ba. Amma Alhamdullah duk komai ya dai-daita babu abinda zamuce da UBANGIJI sai godiya”.
        “Alhamdullahi naji daɗi sosai wlhy Adda. Kice yanzu gida ya cika da ƴan jikoki na”.
      “A ya cika kam. Dan a ƙalla yanzu kana da jika goma sha bakwai zuwa sha tara nan gaba kaɗan, dan yanzu haka yau ɗin nan Mimi ma ta sake haihuwa ta huɗu. Matan Ma'aruff da Ja'afar ma duk suna da ciki a yanzu haka na uku-uku duk da ƙarami ne.”
       “Kai Masha ALLAH lallai zuri'a ta haɗu. Ina yaron kirki Haysam?”.
    Shiru Mammah tayi na sakanni, sai kuma tai murmurshi gajere da faɗin..........✍️

16


..........“Yana lafiya shima Alhamdullah. Kai fa ina fatan dai ƙanwata ta koma ko ka sake sabon aure?”.
    Kansa ya ɗan shafa yana murmurshi, sai kuma ya ce, “Ta koma bayan taga na koma da kuɗin gidan nan, dan har mun sake haihuwar yara biyu ma. Amma ta rasu shekara kusan bakwai data wuce. Sai yaran yanzu kawai.” ya ƙare maganar idanunsa na tara ƙwalla. A take tausayinsa ya sake kamata. Ta shiga jajantawa da masa ta'aziyya. Shima Ammar yay masa ta'azziya. Dan har yanzu bai san ainahin wanene shi ba, tunda sanda wacan abun ya faru suna yara sosai musamman shi da Mimi ma da basu wuce shida zuwa bakwai ba maybe, sai dai ya fahimci ɗan uwan Mammah ne na jini koda kamanni da yanayin tattaunawar tasu.
     Cikin share sabbin hawaye Tasi'u yake amsa musu. Mammah dai ta babbashi haƙuri daga haka ta koma jansa da hira harya saki jiki shima yana jan Ammar a jikinsa......

%><%><%><%><%>

         Kwance take a madaidaicin gadon ɗakin daya kasance guda biyu iri ɗaya hannunta da waya tanata faman zabga murmushi, kai da gani kasan wani abu dake ƙayatar da ita take kallo. Dai-dai nan Ruky ta buɗe ƙofar bayinsu ta fito, ɗaure take da towel alamar wanka tayo, ganin yanda Nimrah ke zabga uban murmurshi bakinta har kunne yasa ta matsawa kusa da ita ta yarfa mata raɓar ruwankan dake ta bin farar fatarta.
       Ɗagowa Nimrahn tai da sauri irin na firgita, dan haka Ruky ta ƙyalƙyale da dariya. Cikin harara ta kai hannu ya goge ruwan data yarfo mata ɗin ta ce, “Ƴar wulaƙanci miye na yarfa min ruwa?”.
     Ruky na ƴar dariyarta har yanzu ta ce, “Gani nai kinata faman washe baki kamar ƴar tallar makilin, wai har yanzu hoton jaririyar kike faman kallo?”.
        “Humm bazaki gane ba Ruky ALLAH jarirai nada ƙyan kallo, ina son jariri sosai, shiyyasa kike ganin duk sanda su Ammie suka haihu nake tarewa a sashensu. Ke nifa ko aure nayi duk shekara zan dinga hauhuwa”.
      “Kambu, Ninah amma baki da hankali, duk shekara fa?”.
    “Eh wlhy, ke ni ƴan bibbiyu ma”.
  Zama kusa da ita Ruky tai da mai a hannu ta ce, “To ALLAH ya baki. Ni sai da kikai maganar haihuwa ma kika tuna min da sayyadi Kamal. Hummm bawan ALLAHn nan fa da gaske kamar yanda ƴan ajinmu ke gulma ya mutu a kanki Ninah, idan yana karatu hankalinsa duk a kanki. Ga kuma Teacher Khalil, yanda ya wani dage yana karemu randa muka suburbuɗi Hibba Abubakar na sake tabbatar da zancen Maimoon Qasim fa”.
     Baki Nimrah ta taɓe tana gyara zama. “Ruky rabani da wannan shashancin kinji, ni wlhy duk basu min ba.”
       “Kai Ninah kiji tsoron ALLAH, wlhy duk ɗinsu sun haɗu, dama dai kawai kice ba yanzu ba ne sai na yarda, dan mukace mun kawo samari yanzu ai ƙaniyarmu Uncle's zasu ci, musamman Uncle Bilal da akoda yaushe yake mana gargaɗin nan. Amma ALLAH nidai ina son soyayya, kinga idan naga Seniors ɗin mu na lobewar nan da boyfriends ɗinsu, ko mazan da ƴan mate ɗin mu sai naji kamar na bama Anwar ko Uncle Haneef ɗin gidan Mamy dama”.
         “Lallai Ruky baki da hankali, yo ALLAH na tuba ko soyayya zanyi mi zan wani yi da ƴan tamatsitsin yaran school ɗin mu. Yo yaushe suma aka gama aikarsu kiran yayunsu gida. To ALLAH bari kiji, ko dariya naga kimma wannan Anwar ɗin sai na ci masa mutunci. Karki maida mu marasa aji mana, ƴan yara da su inama laifin kamar Yaya Ammar haka. Amma kosu Teacher Khalil nawa suke”.
       “Hhhh shegiya Ninah, wato marasa aji? To yaushe ma muka gama tafasar balle mu ƙone har kike batun wani aji. Shekara sha biyar fa muke. Ga aunty Biebah nan harta kammala master ɗinta bata ma zancen aure, ta dage sai Dada ya dawo gida zatai aure. Hakama Aunty Ma'u dake ƙoƙarin kammala Secondary ita da Aunty Halimatu, balle azo kammu haihuwar jiya inji Yaya Mu'azz. Da kike kiran su Teacher Khalil yara kuma, ai bana jin Yaya Ammar zai girmesa. In baki so kamarsu ba tsoho kike so kamar su Daddy ko mi?”.
       “Ƴar wulaƙanci, kamar su Daddy kuma? Kamar shekarun Uncle Ammar dai, amma kamar su Daddy ai da kunya ƴar soyayyar nan bazaka samu ka bajeta ba, kin san kuma nifa ina son harkar nan ta love ba wasa” tai maganar tana kashema Ruky ido ɗaya, bata jira cewar ta ba ta cigaba da faɗin, “Ya Mu'azz kam bar ɗan rainin hankali, shima sai kace ba haihuwar jiyan ba. Ya gama mana rashin m ɗinsa dai sai mun riga shi aure. Dan mu yanzu idan Daddy yace rana ɗaya za'a haɗa auren da Small Mom da su Aunty Ma'u mune next. Shifa, sai ya jira Uncle Bilal, Uncle Ammar da Yaya Khalifa ma ƙila, to ko Yaya Imam ya girmesa.
      “A'a wlhy kar ki masa baki, duka shekara nawa Yaya Khalifa ɗin ya bashi, sai dai ayi musu tare, gara Yaya Imam to, kuma shima tare suke tafi a school ai”.
    Cike da dariyar mugunta Nimrah ta ce, “Oho dai, ko haka ɗin mun more masa. Ke muyi gulma mana. Dan ALLAH baki ga wai kamar Uncle Bilal da Aunty Ma'u akwai wata a ƙasa bane?”.
      “Humm wlhy na gani, ranar graduation ɗin su Small Mom sai wani kallon ƙasan ido yake mata.” dariya suka kwashe da ita harda tafawa.
Nimrah ta ce, “Wlhy soyayya tayi Besty, idan ban samu ɗan soyayya ba na rako mata duniya”.
Cikin dariya Ruky tace, “Muna son soyayya zaki ce, ai duk wanda yazo sai mun tantance shi walle karki damu, love ai duniya ce”.
“A wlhy love duniya ce, shiyyasa nake son maƙalewa a sashen su Mamy, dan in ana bajakoli su da su Uncle's nasha kallona”.
“Muguwa, wlhy Ninah kiji tsoron ALLAH, tun baki tafasa ba zaki ƙone. ALLAH yasa su ganoki suci ƙaniyarki, kinga sai ai miki auren ai”.
“Shegiya ni da ke ai duk sammakal ne, zatace ta tadda muje mu”.
Dariya suka sake fashewa da ita suna tafawa.....
    Buɗe ƙofar ɗakin nasu ya saka su yin shiru, sai kuma duk suka rufe bakunan nasu da hannu. Biebah ta hararesu.
       “Anya kuna duba agogo kuwa? Kuke mana irin wannan ihun dariyar haka kamar sabbin kammu”.
      “Kai Mom ALLAH hira ce kawai tai daɗi”.
     “Kuma da ihu haka? Na sake jin wannan dariyar kamar ba mata ba sai na ɓata muku rai. Dalla ku bani wayata kuyi shirin barci ku kwanta” tana gama faɗa ta amshi wayar tata da Nimrah ke kallon hoton baby, Dan su basu da waya Uncles nasu sunce ba yanzu ba. Juyawa tai ta fita tana mai rufe musu ƙofar. Gwalo sukai ma bayanta a tare, kafin Nimrah ta miƙe zuwa bayin itama dan yin wanka. Bata wani jima ba ta fito, lokacin har Ruky ta gama nata shirin barcin ta haye gadonta, dan kowa da nashi. Ƙasa-ƙasa suka cigaba da hirar a haka kuma duk ta sanari har Nimrah ta shirya itama ta haye nata gadon.

       WASHE GARI da wuri suka ta shi, babban burinsu tafiya gidan Aunty Mimi ganin baby musamman ma Nimrah da jiya ba'aje da ita ba. Dan tana barci su Aunty Shariffa suka wuce da Ruky, sai yau Biebah tace zasu je tare tunda itama bataje ba taje Tahafiz, amma tace mata yau ma sai sunje sun dawo daga Tahafiz suma sannan. Rashin sabon barcin safe saboda makaranta yasa suna kammala salla sukai bitar karatun Alkur'ani dan sun san yau sayyadinsu zai amshi hadda sukai azkar kowa ya miƙe. Ruky ta fara gyara ɗakinsu ita kuma Ninah ta wuce gyaran ɗakin Biebah. Koda ta shiga ɗakin Biebah harta sauka ƙasa taya masu aiki haɗa breakfast ita kuma. Sun kammala gyara ɗakuna har bedroom ɗin Mammah duk da bata nan basa gajiya da gyarawa sannan suka shiga wanka. Dama bedrooms suke gyarawa da sama ɗakin su Yaya Ammar, sauran wajaje kuma masu aiki. Shirin sukai cikin uniform ɗin islamiyya su ash color na wando da hijjab har ƙasa tsahon hijjab ɗin yasa da yawansu basa yin rigar suke saka t-shirt a ciki. Fitowarsu dai-dai da fitowar Biebah daga nata ɗakin tana wani kalar sassanyan ƙamshin turare. Su duka kasa haƙuri sukai sai da suka tanka.
      “Woow Small Mom kin sayi sabon turare ne? Wlhy wani ƙamshin bala'i mai kassara jiki”.
      Murmushi tayi tana ɗan girgiza kanta. “Yan biyun Mammah kenan iyayen iyayi ƴammatan gobe. To wannan ƙamshin da kuke ji ba turaren kanti bane, haɗaɗen turaren gida ne dan khumra ce ma kawai na ɗan shafa sai kabasa da nayi a kaya na, nima a sashen Aunty Lailah na samoshi.

.......Gaba Biebah tayi tana musu dariya, dan in dai halayen Twins ɗin gidan nasu ne tafi kowa sabawa. Suna sakkowa dining suka nufa, Mu'azz ne kawai zaune yana kari shima sanye da uniform ɗin islamiyyar. Cike da neman magana Ruky ta ce, “Su Yaya yau kuma da yunwa aka tashi?”.
     Harara ya wulla mata, batare daya tanka ba ya cigaba da danna doyarsa a baki. Nimrah tai dariya tana zama a kujerar kusa da shi. “Kaga rabu da ita Yayana. Kasan ita Ruky wani lokacin uwar gulma ce. Ina kwana”.
      “Ai ke da ita duk sammakal. Wannan saurin gaisuwar bana ALLAH bane faɗa min nawa kike so?”.
     Dariya Biebah da Ruky suka sanya. Cikin ɓata fuska da tura baki Nimrah ta ce, “Kai Yaya sai kace wata mayyar kuɗi, kai shike nan bazamuyi shirin arziƙi ba sai ina son kuɗi”.
          “A to nasan halinki ne ai Ninah”.
    Tashi tai a kusa da shi ta canja kujera, ya ce, “Oho dai”.
Bata kula shi ba, dan dai-dai nan ma su Abees suka shigo da gudu suma sanye da irin uniform ɗinsu. Tuni Nimrah ta miƙe tana faɗin, “Oyoyo my Afry”.
     Ai ko da gudu Afrah tai kanta, ta ɗagata sama tana juyi da ita suna dariya dan ƴar gidanta ce. Su Aheel kuwa wajen Ruky da Biebah da Mu'azz sukayi suma. Nan fa surutun falon ya ƙaru, dan bayan yaran sun gaishesu suma duk zama sukai Ruky ta saka ma kowa abinci a gabansa. Sai da Biebah ta tsawatar ma surutun basu sannan sukai shiru kowa ya maida hankali ga abincinsa. Shaf-shaf suka kammala suka fito karsu makara.
      Yau sabon driver ɗin su ne zai kaisu. Wanda suna haɗa ido da shi yau ma gaban Nimrah ya faɗi, dan haka ta kauda kanta gefe tana gaishe shi kamar yanda su Biebah ke gaishe shi. Dan ba yaro bane. Gaba Mu'azz ya shiga shi da Abees da Aheel. Su kuma ita da

7 / 42