Author : Boss Bature Category : Complete Novels
mutu, Tun shigowar Danish ɗakin kusan suman tsaye yayi, saboda tsabar Kiɗima da ganin halin da ƴan uwan shi su ke aciki, Ya rasa bakin magana, Ya yi matuƙar girgiza da ganin yadda aka wulaƙanta rayuwar Ƴan uwan shi, Hankalin shi yai mugun tashi, Zuciyar shi tamkar zata faso ƙirjin shi ta 6allo saboda tsabar ƙunar da ta ke Yi mashi, Ya fusata Iya fusatuwa, ganin yadda yake huci ƙirjin shi na motsi ga wata narkakkiyar zufa dake wanke mashi fuskarshi, yasa Salsabeel yin saurin dakatar dashi ta hanyar yi mashi magana”Danish ka sassauta fushinka idan ba haka ba giant’s heart ɗin ka zata iya motsawa, pls ka ceci rayuwar su ku gudu daga kurkukun nan, duk wani abu da ya toshe maka kai, Unaisah zata yi maka bayani idan kun fita” daƙyar ya samu Danish ya iya sarrafa fushin sa.
Muryar Angel adisashe tace dashi”Ni bazan Iya tafiya in bar gawar su Azeeza acikin wannan ƙazamin ginin ba, inaso na cika masu burin su duk da basa araye zan fitar da gawarsu waje in yaso sai mu binne su a akan hanya, dan Allah ku taimaka min” Tana magana hawaye Na wanke fuskarta.
“Unaisah bamu da isasshen lokaci pls ku tafi kawai ku barni dasu zan san inda zan 6oye gawarsu” fashe mashi ta yi da kuka kamar zata haɗiyi zuciyarta, Hankalin Danish gaba ɗaya ya dawo kanta, tsananin tausayinsu duk ya kama shi.
“Bazai yiwu ku iya tafi da su ba! Kubar su a wurina zan tsaga ƙasa In binne su” acewar Salsabeel
Ataƙaice zan yi bayanin yadda su ka gudu daga KURKUKUN ƘADDARA, Angel ce ta goya Jemimah abayanta tare da sanya Mayafin kayan su da ta ɗauko acikin akwatin su, Gabriel ya goya gawar Azeeza abayanshi ya ɗaureta da mayafi, Naufal ya goya Parveen asaman bayanshi, Haris yaso ya goya Deeja abayanshi sai dai Salsabeel Ya hana shi gudun kada su ja ma kansu wata wahalar, Iya waɗannan kaɗai su ka ɗauka sauran Sun bar su awurin shi bayin Allah badan sun so ba, kusan mutun shida daga Ciki hada Deeja, Sarah, Eve, Yasmin, Rubina da Hibba, Danish ya yi ƙoƙarin yin amfani da sihirin shi wurin farfaɗo dasu, mutun ɗaya kaɗai ta samu damar tashi Hannah, a ƙarshe ya tabbatar masu da cewa Heart attack ne Yai silar mutuwar su, zuciyar su ce ta buga.
Ƙululun baƙin Ciki kamar su Zauce, Kafin tafiyar su Mubeen ma ya yanke jiki ya faɗi, Don dole suka haƙura da shi, Lamarin ya yi matuƙar gigitar da su.
Salsabeel ya yi masu alƙawarin Zai yi nesa da gawarwakin Ƴan uwan su, tare da ta mahaifiyarshi ba zai bari a wulaƙanta su ba, sun yi kukan rabuwa dashi, har magiya Angel ta dinga yi mashi akan ya zo su tafi atare da shi, amma yace masu ba zai iya bin su ba, su yi haƙuri su tafi idan Allah yasa yana da tsawaicin kwana zasu sake haɗuwa ne duk da yasan abune mai wuya ya rayuwa ko dan saboda 6arnar da suka aikata dole matsafan su azabtar da shi.
Rabuwar su ta yi matuƙar ta6a zuciyar kowannan su, a gurguje su ka nufi sashen makewayin su, Tsabar tashin hankali yasa Gabriel mantawa da zancen Ƴar uwar shi Gabriella da ke a cikin kurkuku, tun da ya ga mutuwar ƴan uwan shi prisoners, yasa wa ranshi dangana.
Suna shiga Cikin Toilet ɗin, Danish Ya datse ƙofar da sihirin shi, ya Janye tukunyar fulawar daga kan ƙofar, nan ta ke ta bayyana duk irin wahalar da suka sha ta ƙi buɗewa shi Bugu ɗaya yayi mata gaba ɗaya ta 6alle murfin ƙarfen ya dare biyu, Sun yi mamaki da al’ajabi yace da su”Ba zai bi su ba, zai tafi da Akwatin kayan su tare da back pack ɗin su, za su tarar dashi a bakin ƙofar da zasu 6ula idan sun ƙarasa” hankalin su bai kwanta da maganar shi ba, gani su ke yi kamar wani mummunan abun zai faru da su idan baya atare da su, ganin sun toge sunƙi tafiya yasa shi Kwantar masu da hankali, daƙyar ya samu su ka Zuƙunna ƙasa tare da kutsa kai ɗaya bayan ɗaya su ke shiga cikin ƙofar da rarrafe, Bayin Allah ga yunwa ga ƙishin ruwa, ga raɗaɗin da zuciyarsu ke yi masu, Ita kanta hanyar da suka biyo Wata uwar ƙura ga yanar girgizo da ƙwari sai hawan masu jiki su ke yi, Amma saboda rashin kwanciyar hankali yasa basu damu da su ba. Babu mai magana acikinsu saboda ƙunar da ran su ke yi masu, Angel ce tai ƙoƙarin tunasar dasu akan suci gaba da ambaton addu’o’in data koya masu ko sun samu sassaucin a wurin Allah, sun ɗau ki shawararta ahaka suka Dinga tafiya da rarrafe babu ƙaƙƙautawa, idan suka gaji su kan ɗan zauna su huta kafin su dasa da wata tafiyar, A ƙalla sun shafe tsawon awanni Takwas suna rarrafawa ba tare da sun kawo ƙarshen Ƙofar ba, a takure su ke Bayin Allah sun ga rayuwa gwiwowin ƙaffuwan su duk sun gurje sun sage, maƙoshinsu ya bushe ƙamas, tun suna ambaton ƙishir ruwa suke ji har sun gaji sun yi shiru.........”😭
💔Prisoners💔
Sun ci baƙar wahala saboda tsohuwar hanyace da ta yi shekaru aru aru a datse ba tare da an yi amfani da ita ba, Muggan ƙwarin da ke a ciki sai ɗallinsu su ke Yi, amma saboda azabar raɗaɗin da zuciyar su ke yi masu yaci uban raɗaɗin harbin da ƙwarin ke yi masu yasa ba su ji, A makance suke tafiya basu ji basa gani, ga wani azababben zafi daya addabe su, kowan nan su ya haɗa uban gumi burin su kawai su cimma ƙarshen ƙofar, wani ƙarin tashin hankalin fitilun da ke a hannun su Batul hasken su ya fara ƙoƙarin ɗaukewa abunda basu ta6a yi masu ba, sun fuskanci matsanancin tashin hankali har sai da suka fidda rai da fita saboda ganin tsawon awannin da suka shafe ba tare da sun kawo ƙarshen ta ba, tun da suna rarrafawa Hannah ke kuka tana faɗin ƙaiƙayi ta ke ji a jikin ta, duk da halin da su ke aciki hakan bai hana su rarrashin ta ba akan ta yi haƙuri, a lokacin da ba su yi tsammani ba kwatsam! hasken fitilun hannun su Ya ɗauke ɗuff Innalillahi wani irin duhu baƙiƙƙirin ya mamaye idanuwan su, ko fuskokin su basa Iya gani, duk sunbi sun firgice saboda hanyar ta 6ace masu, Sunan Danish su ke ta kira a bakunan su, sun manta cewa baya atare da su.
“Danish ka taimaka mana, duhu bamu iya ganin komai, bamu san ya za mu yi ba,” abu biyu ya haɗe masu ga fargabar kar a rutsa su ga kuma Rashin haske gani su ke kamar Aljalinsu ne zai risƙe su awurin, Sautin koke koken su ne ya cika hanyar, sun kasa jurewa tsananin tsoro suke ji, Danish ka yi mana magana pls Ya zamuyi? Kada a rutsa damu, idan ba mafita ne ka faɗa mana.....” Cikin shessheƙar kuka Angel ta yi mashi maganar, kamar zasu yi hauka, sun rasa gane me ke shirin faruwa dasu ne?
“Innalillahi wa’inna ilaihirra’un! ya Allah kawo mana ɗauki! Wai ina Danish ɗin ya ke bai jin mu ne ko baya atare damu”! Naufal ne yai maganar, tsabar matsewar da su ka yi yasa wani bai iya motsawa daga inda yake balle har su iya gano inda Danish ɗin ya ke, Yadda kasan kifin gwangwani haka suka cunkushe, Bawan Allah Haris gaba ɗaya baya acikin hayyacin shi, Damuwar shi Deejarshi da ya rasa, Yaji ƙuncin da har abada bazai ta6a goge mashi ba, zuciyarshi ta yi mashi nauyi ga dukkan alamu wani mummunan ciwon ne ke shirin kama shi.
“Nifa ina jin tsoro ace Danish Ya canza ra’ayin shi na taimakon mu, zai iya komawa giant”! Gabriel ne yai maganar cikin rauni na murya
“Ni da ma na fidda rai da rayuwa, bansawa raina zan bar kurkukun nan araye ba.” Javed ne yai maganar cikin rauni na murya.
Suna Cikin Jimamin rashin Jin motsin Danish da fargabar me zai Biyo Baya.
Ba zato ba tsammani suka soma hango haske Yana kurɗaɗowa ta Cikin wata ƙofa Yana gauraye inda su ke zazzaune, Tsabar ruɗani Ya sanya su ka Waro idanuwan su waje Kamar ƙwayar Zasu faɗo ƙasa Sun kasa gane hasken menene ke isowa gare su.
Ba kowa ba ne abakin Ƙofar fa ce Garkuwar kurkuku shine ya buɗe ƙofar Kogon Bishiyar, Ashe ta inda zasu 6ullo Cikin kogon bishiya ne Mai girman gaske Wurin Ya wawake........
Saboda rashin wadataccen haske basu Iya ganin shi da kyau, Cikin sanyayyiyar murya ya furta masu “You ave reached the door. Today, you will finally leave the prison of destiny, am happy for the first time that you will live a happy life. am ready to be your shield, and I will not let you get hurt by the lows and difficulties of life.”
Abun farin Ciki sai dai ba halin nuna shi saboda ba haka suka tsammaci zasu bar kurkukun ba, Ƴan uwan su duk sun mutu, duk irin burin da suka ɗaukarwa kansu na son Yin rayuwar Ƴanci gaba ɗaya ya tashi abanza, Cikin su goma sha takwas mutun goma suka tsira, ahakan ma basu da tabbacin zasu ƙarasa da ran su da lafiyar su ba tare da wani abun ya kuma faruwa da su ba, Kusan atare suka rushe da matsanancin kuka tamkar ana zare rayukansu, Kukan baƙin Ciki da ƙunci da raɗaɗi, Kuka mai matuƙar tsuma zuciya, Tsananin tsauyin su ne ya kama Danish A hankali ya ke ƙare masu kallo, Cikin sanyin murya yace da su Idan nace Ku yi haƙuri Na cuce ku, I can’t stop you from shedding your tears, except to encourage you to cry. It’s the only thing that can ease the pain in your heart.”
Fuskar shi ɗauke da matsananciyar damuwa yai maganar, kamar ya ƙara tun zura su aiko suka ƙara sautin kukan nasu, Idanuwansu duk sun kumbura Fuskokinsu sun yi jawur. ganin basu da alamun motsawa yasa shi matsawa tare da ruƙo hannun Angel dake goye da gawar jemimah abayanta, ya turo ta waje a hankali, Tana fitowa ta runtse idanuwanta da ke tsastsafo da ƙwalla.
ƙurmin Daji ne mai nau’ikan tsirrai da dabbobi iri-iri. Manya manyan bishiyoyi masu tsayi da faɗi suna da Dogayen rassa, Faɗaɗan Ganyayyakinsu Sun toshe hasken Farin watan da ke a sararin samaniya kaɗan ne ke samun damar haskowa ta tsakankanin Ganyayyakin, yau shekara Uku da watanni rabon da ta tsinci kanta A waje, Ina ga sauran ƴan uwanta Prisoners waɗanda tun da uwar su Ta haife su basu ta6a tozali da haske rana ba, Ɗaya bayan ɗaya Danish ya dinga janyo su kamar basu son fitowa, Kaf ɗin su Ya fiddo da su, kafin Ya maida ƙofar kogon tamkar ba’a ta6a ratsa cikinta ba.
Sai faman zazzare idanuwansu suke yi suna bin Dajin da kallo duhu Ya hana su ga komai da kyau, Tsananin tsoro ne ya kamasu, Ga wani irin bala’intaccen san yi kamar Jaura ta gifta, Haƙoran su sai kakarwa su ke yi, muryoyinsu Na rawa suka soma ambaton sunan Danish Suna faɗin sanyi su ke Ji.
Da sauri Ya buɗe akwatin kayan su dama shi ne ya ɗauko shi Tare da back pack ɗin Unaiza, Ya zaro masu bargunan su, A saman bayan su Ya lullu6a ma kowannansu bargo, Tunani ya shiga yi ya zaiyi dasu? Ga dukkan alamu sun gaji basu Iya motsawa gashi yana fargabar kada akawo masu hari yasan dole abiyo bayansu. Babu mai ƙoshin lafiya acikinsu kowa takan shi ya ke yi shiyasa ko farin cikin fitowar ba su yi ba duk da irin ɗaukin da suka dinga yi, su fa har yanzu basu yarda cewa sun fito daga kurkukun ƙaddara ba, gani su ke yi kamar har yanzu suna aciki, saboda duhun daya mamaye idanuwansu basu Iya gani dakyau hada ƙarin nauyin da idonsu yai masu sakamakon kukan da suka sha, wasu ma daga cikin su ciwon ido suke fama dashi, Danish ne kaɗai yake Iya ganin su da kyau.
Yanke shawarar ya yi da zuciyarshi nan take ya haifar masu da jin matsanancin bacci, Asaman dogayen ciyayin da ke shimfiɗe masu cukowa, Kowan nan su Ya kwanta hada masu goyan cikin su, Ajiyar zuciya ya sauke tare da miƙewa, Ya ɗauki bargo ɗaya daga Cikin wanda Ya lullu6a masu Kamar walƙiya ya 6ace Bai dura a ko’ina ba Sai acikin kogon dutse mai girman gaske, da sihirin shi ya kawar da duk wani abun cutarwa Ya gyara wurin tsaf babu ko ƙura balle aje ga batun halittun da ke rayuwa a cikinshi, Bayan ya tabbatar da babu abun cutarwa Ya shimfiɗa bargon dake a hannun shi, Kafin Ya juya tare da 6acewa ya dawo wurin da yabarsu kakkwance suna bacci, Cikin mintuna Biyar Yai aikin da acikin awa biyu mutun zai iya yin shi, Bai da banbanci da Jinni, kamar walƙiya ya dinga ɗaukarsu ɗaya bayan ɗaya yana kaisu saman shimfidar da yayi masu a cikin kogon dutse bai bar kowa ba, Bayan ya kammala kwashe su ya ɗauke masu akwatin kayansu da jakar ya shigo dasu Cikin kogon ya ajiye shi. Komawa yai cikin dajin Ya haɗo itace dayawa ya shiga dasu ruƙe a hannun shi Cikin kogon dutsen, Ya jera su a ƙasa nesa da inda su Angel su ke akwance, Ya tsinto duwatsu guda Biyu ya gurzasu jikin juna nan take wuta takama Ya cinna ta a jikin itace sosai Wutar ta ruru, a ƙalla ya sauke ajiyar zuciya yafi sau a ƙirga, ya hada uban gumi shi kaɗai, jiki bai saba da wahala ba, fuskarshi sai naso ta ke yi kamar an watsa mashi ruwa, Ya jima zuƙunne abakin wutar Yayin da idanuwanshi ke akan ƴan uwanshi dake lullu6e cikin bargo suna bacci, wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyarshi kamar an kora ruwan san yi, haƙika yayi danasanin duk wani abu da ya faru dasu, Ya ji ƙunci sosai A cikin ran shi, miƙewa ya yi a hankali ya ke tafiya yana tunkararsu a gaban shimfiɗar su Ya zuƙunna tare da miƙa yatsun hannayenshi Ya ruƙo bakin bargon dake lullu6e dasu Ya yaye shi, Hasken wutar da ke cini ne Ya haskaka mashi fuskokinsu, Idanuwanshi na akan Marasa ran cikin su, idan ka kalle su a yadda suke kwance baka ta6a cewa gawawwaki ne, Tuni idanuwanshi sun kaɗa jawur, Zuciyarshi ta ƙara karaya tsananin tausayin rayuwar ƴan uwanshi ne ya kama shi, Ya rasa ya akai duk waɗannan abubun su ka faru ba tare da sanin shi ba? Shin me ya faru da su bayan An ɗauke shi daga Cikin su? tambayoyi ya shiga jefa ma kanshi. Ataƙaice Daren Ranar Danish bai runtsa ba, Kwana yai a zaune yana gadin su.
*MIDDLE STEP THE PRISONERS BOOK TWO🔥💫*
*BIRNIN ABUJA🏙*
*Boss Bature✍️ Mu haɗu Gobe Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuɗin*
First bank
3196407426,
*Bature Hafsat Muhammad, za’a tura evidence of payment ta phone number ɗina 08103884440, Banda kira whatsapp kawai*
_~*BossLadiesWriters*~_
_*KURKUKUN ƘADDARA*_
_The Prisoners E5🔥💫_
*Daga alƙalamin Hafsat Bature*
~Middle step~
_A heart-wrenching story of love, romance, and redemption, set against a backdrop of betrayal and cruelty💔._
*ANEELERH*
Kwance ta ke asaman katafaren gadon ta da ke acikin haɗaɗɗen bedroom ɗinta da ke a sabon gidan su na Abuja mallakin Uncle ɗan Iya ɗaya daga Cikin ƙannan Abie ɗinta mazaunin garin Abuja, Attajirin mai kuɗi ne mai yiwa ƴan siyasa hidima, Tun bayan da Abie ya samu ƙarin matsayi a wurin aikin shi aka yi mashi transfer zuwa ministry of finance da ke anan Abuja, a ƙalla yau watan su bakwai da barin jihar jos, ba ƙaramin canjin rayuwa su ka samu ba a gidan ɗan Iya, mutunne mai son jama’a ga iya mu’amala da kyautatawa mutane, kusan halin shi ɗaya da matar shi Aishatu wadda ake da Aunty Ummi.
“Aunty Aneelerh! Auntyna! Where are u? i’m back” can cikin bacci ta dinga jin ana ƙwala mata kira, Sautin muryar matashiyar budurwa.
Nauyin bacci ya hana ta buɗe idanuwanta sai ma ƙara ƙudundune kanta da ta ke yi acikin lallausar bargonta, faɗowa cikin ɗakin ta yi Tabarakallahu Zankaɗeɗiyar budurwa jawur da ita, Jikinta na sanye da egyptian gown launin shuɗi, Ta yi rolling veil akanta, Light make up ne akan fuskarta daga ganinta ba ƙaramar wayayyi bace a jin farko, Takalman ƙafarta high hills ne launi ɗaya da Mayafinta white colour, hannunta na dama na asanya da Tsadadden agogo silver colour. Ƙamshin turaren Jikin ta mai matuƙar sanyaya zuciya, wayar da ke a ruƙe a hannunta ƙirar i phone 15 pro ce.
Agogon bangon da ke a ɗakin ta kalla ƙarfe 9 Na safe, Da sauri ta wurga ƙwayar idanuwanta kan Aneelerh dake kwance saman gado, girgiza kai ta ɗanyi fuskarta ɗauke da ƙayataccen murmushi tace”Auntyna kenan bakya gajiya da bacci, sam kin canza mini ba kamar yarda na sanki ba, Gaskiya zanyi magana da Daddy ya hanzarta sama maki aiki ki fara Ni bana son inga mutun yana zaman kashe buje” da zolaya ta yi maganar a yayin da take ƙarasa shigewa Cikin bedroom ɗin, Cikin sanɗa take tafiya tana tunkarar A.c remote da ke ajiye saman bedside drawer, ɗaukar shi ta yi saboda mugunta ta ƙure mata sanyin A.c, Jikin Aneelerh tuni ya fara kakarwa Sosai ta ke ƙara nannaɗe kanta Cikin bargo, Dariya sosai *FATIMA ZAHRA* ta sa ki a yayin da ta ke kallonta, Kasa jurewa Aneelerh saboda sanyin ya addabe ta, A gigice ta sanya hannu ta yaye bargon ta jefar dashi kafin ta yi yunƙurin buɗe ido da sauri Zahra ta rage sanyin a.c ta ajiye remove ɗin saman drawer, ta ruƙe qugu tana binta da kallo.
Sleeping dress ne a jikinta Riga da wando Milk colour, Gashin kanta a hargitse, Tunkan ta buɗe ido ta soma surfa masifa tana faɗin”junaid bana hana ka ƙara