Author : Boss Bature Category : Complete Novels
Gabriel, hankalinta kwance sai sharar bacci ta ke Yi, Jemimah kuwa Idonta biyu Sai faman baza ido ta ke yi Hannunta na a ruƙe dana Angel.
"Me yakamata Mu yi yanzu don ganin An dawo mana da ɗan uwan mu Danish"! Haris ne yai maganar
"I'll go and get him back tonight!" da ƙwarin gwiwa Angel ta yi maganar.
"Ta yaya hakan zai yiwu? Angel muna jin tsoron wani abu ya same ki, Me zai hana mu tafi gaba ɗayan mu"! batul ce ta yi mata maganar fuskarta da alamun damuwa
"Zan bi ki Angel Mu tafi atare"! Gabriel ne Ya yi maganar" girgiza kai ta yi"Bana so wani abu ya samu ɗaya daga Cikin ku, Bazan bari ka bini ba Gabriel ni kaɗa nake so na jefa kaina cikin hatsari Zan roƙi Allah ya tsare ni....." muryarta na ɗan rawa ta ambaci hakan kamar akwai rauni atattare dani, tabbas tana matuƙar fargabar abu biyu, Na farko tafiyar da zata Yi tabar su da jimamin Awani hali take a ciki, Na biyu Haɗuwarta da garkuwar kurkuku, Wani irin azababben tsoron shi ta ke ji tun kafin ta yi tozali da shi.
"Genie Pls don't leave me Ki tafi dani..." cikin shessheƙar kuka Jemimah ta yi maganar tana ƙara damƙe hannun Angel dake ruƙe da nata.
"Wlh Angel hankalin mu ba'a kwance ya ke ba, Gani mu ke kamar wani abu zai faru da ke idan kika tafi kika barmu" Deeja ce ta yi maganar, ta fahimci kowannan su atsorace ya ke da tafiyarta.
"Angel bazamu ta6a yafewa kan mu ba idan har wani abu ya faru dake ta silar taimakon mu da ki ke ƙoƙarin Yi,"
Javed ne yai maganar, Tuni zafafan hawaye sun wanke fuskokin kowannan su, La66anta sai kerma su ke yi sam ta kasa buɗe baki ta yi masu magana sai binsu ta ke yi da ido, Zuciyarta ba ƙaramin karaya ta yi ba, Ita kanta tana ji a jikinta cewa wannan karan zaiyi wuya ta dawo cikin su ba tare da wani mummunan abu ya faru da ita ba.
"Idan har muka ji kin daɗe baki dawo ba, Zamu biyo ki ne"! Hibba ce tai maganar hawaye kwance saman kuncinta
Daƙyar Angel Ta iya tattara natsuwarta tare da cewa"Ku daina sanyawa ranku cewa wani abu zai faru dani, idan ma ya faru dani to ku sani ƙaddarata ce wadda ban isa in sauyata ba, Ni da Allah na dogara wani mutun ko Aljan ɗaya daga cikinsu bai isa ya cutar dani ba face da izninsa, ƴan uwana addu'arku kawai nake buƙata akan Allah ya bani Sa'a akan abunda zan je nema......." Sautin shessheƙar kukansu ne ya gauraye Ɗakin tsohuwa.
Muryarta adisashe tace"Tunkafin ma na tafi kun fara kuka? Meyasa? Dan Allah ku daina kamar fa kuna discouraging ɗina ne, Nafi so inga kuna ƙarfafa mini gwiwa, ganin hawayenku da nake yi ba ƙaramin raunata mini zuciya ya ke yi ba.
"Ba zamu iya jurewa rashinki atare damu ba Angel, wlh muna ƙaunarki fiye da yarda muke son kanmu, bamu son wani abu ya same ki, saboda mu kike ƙoƙarin jefa kan ki ga halaka taya ba zamu yi kuka ba? Angel ke uwace agare mu, Kin fiye mana iyayenmu da su ka yi watsi damu, Dan Allah Angel karki bari mu rasa ki" Sosai suka sanya mata kuka
Itama ta fashe masu da matsanancin kuka mai cin rai tamkar ana zare ranta Cikin muryar kuka take magana
"Shiga prison Ya zamar mun dole, Idan har ban je ba rayuwar mu tana a cikin haɗari, sannan Alƙawari ne na ɗauka Dole na cika shi ku daina raunata mun zuciyata kada kusa Na gaza......" Kasa ƙarasa maganar ta yi saboda raɗaɗin da ta ke ji a cikin zuciyarta.
Tsawon lokaci suna kallon kallo a tsakanin su kafin ta tsagaita da yin kukan tace da batul"Ga amanar jemimah, Ki rungume mun ita a ƙirjin ki har sai ta yi bacci, da zarar na dawo zan kar6i abuna" cikin sanyin murya batul ta amsa mata da cewa In sha Allah zan bata kyakkyawar kulawa har ki dawo Angel, murmushin yaƙe ta ƙaƙaro kan fuskarta tare da kallon su Parveen da ke atsaitsaye tace"Zan tafi ba za ku rungume ni a jikin ku ba"? Jin haka yasa da sauri suka matso kusa da ita, Ɗaya bayan ɗaya suka dinga rungumeta a ƙirjin su, kamar karsu sake ta, a ƙarshe Ta Soma tafiya tana ja da baya tana kallon su idanuwansu akanta, Jiki amace ta juya tare da buɗe ƙofar ɗakin tsohuwa tamira, Da gudun gaske Cikin duhu ta nufi sashen toilet ɗinsu tana faɗowa Hasken sauran fitilun dake a cikin toilets Ya haskaka idanuwanta, buɗe ƙofar toilet ɗin ta yi tare da shigewa Ciki. Yatsun hannunta na kerma ta sanya jamlock ta datse ƙofa don kar su yi gigin cewa zasu bi bayanta, A jikin ƙofar ta jingina bayanta sosai ta fashe da kuka gudun kada su ji sautin kukanta yasa ta toshe bakinta da tafin hannunta, tsawon mintuna goma shabiyar tana sharar ƙwalla kamar ruwan hawayenta zasu ƙare sai da tayi mai isarta kafin ta soma tafiya tana tunkarar Tagar da zata dura, har zata gifta tukunyar fulawar nan ta ɗan dakata da yin tafiya kafin a hankali ta kalli inda ta ke a jingine jikin bango, duk da halin da take aciki na fargaba sai da tayi mamakin ganin an maida tukunyar a mazauninta na asali, shiyasa ɗazu tsohuwa Zafreen bata samu damar ganin ƙofar ba saboda an toshe ta, ajiyar zuciya ta sauke tare da lumshe idunuwanta daga bisani ware su sosai akan furen Danish da ganyayyakin shi su ka bubbuɗe gwanin ban sha'awa, Kyakkyawar fuskarshi ta ke imagining acikin idanuwanta, aranta kuwa tana ayyana koya Zata Ganshi a yanzu daya koma Giant? Da wannan tunanin Angel Ta ƙarasa gaban glass window ɗin Ta janyo bokitin Ta haye sama A hankali ta 6a66ako glass ɗin tare da curo shi ta dire shi ƙasa kafin ta daddage ta haura Saman tagar bakinta ɗauke da Bismillah.
Zuƙunna tayi a jikin bangon da ta faɗo, wani irin Sanyi ne ya mamaye sassan Jikinta, Ga tsoro daya mamaye zuciyarta, Biji biji take ƙarewa doguwar hanyar kallo, duhu sosai babu haske sai dai da alamun haske a ƙarshen hanyar Inda Babban filin nan ya ke.
miƙewa Tayi tsare tare da Sanya hannayenta Biyu ta ruƙo duguwar sumar kanta tare da nannaɗeta ta jefar da ita saman gadon Bayanta, tunawa da addu'oin da ta karanta a jiya da tayi fitar nan yasa a yanzu ma ta soma ambaton su acikin zuciyarta, A yayin da take tafiya tana nufar cikin kurkukun........
*Boss Bature✍️ Mu haɗu Monday Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya Game neman ƙarin Bayani Ya tuntu6i Layina na whatsapp 08103884440 banda Kira just message😊*
_~*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*~_
*KURKUKUN ƘADDARA*
_The Prisoners 2🔥💫_
*Daga alƙalamin Hafsat Bature*
~Middle step~
_A heart-wrenching story of love, romance, and redemption, set against a backdrop of betrayal and cruelty💔._
Bayin Allah su Batul zullumi da fargabar Halin da Angel zata shiga Ya hana su runtsa a daren ranar, A ɗakin tsohuwa Tamira su ka zazzauna saman floor, zuciyarsu na harbawa da faɗuwar gaba, Sun yi shiru kowa da a bun da ya ke saƙawa acikin ranshi. Deeja ce tai ƙoƙarin tunasar dasu akan su yi mata addu’a. Su ka amsa mata da toh, nan fa kowan nan su ya soma karanto addu’o’in da Angel ta koya ma su.
Dare ya nutsa sosai Azeeza tuni ta koma bacci, a saman ƙirjin Gabriel ta kwantar da kanta, Hannun shi na dafe da bayanta kamar zai mai da ta cikin sa.
Jemimah tana a kwance saman cinyoyin Batul ta ƙi yin bacci, ba yadda ba su yi da ita ba akan ta runtse idon ta ta yi bacci amma ta kafe akan sai Genie ɗinta ta dawo, a ƙarshe ma da su ka matsa mata sai ta sanya masu kuka, Tsananin tausayinta ne ya kama su, Haris yace ku bita a hankalin ni banga laifin ta ba, saboda ita yarinya ce ta saba kwana rungume da Angel dole taji ba daɗi, Rarrashin ta ya kama ta mu yi, Amsa mashi su ka yi da toh, atare su ka haɗu suna rarrashin jemimah daƙyar su ka shawo kanta.
Parveen sai hammah ta ke yi Ga yunwa ga Bacci, Naufal da ke zaune a gefenta Yace da ita Ki kwanta ki yi bacci mana, Kin ishe ni da hammah” harara ta ɗan jefa mashi tare da cewa”in yi bacci fa ka ce? Sai kace bansan ciwon kaina ba, Ta ya zan iya runtsawa bayan yan uwar mu tana acikin kurkuku....” ta6e la66ansa Yai”Naji daɗi da ki ka yi Hankali” bata tanka mashi ba sai ma ɗaura kanta da ta yi asaman laps ɗinshi.
“Batul mu tashi mu bi Genie mu ɗauko ta” Muryar Jemimah ce ta yi maganar Fuskar ta ta yi sumtum saboda kukan da tasha, Lallashinta Batul ta yi” Ki yi haƙuri kin ji, In sha Allah zata dawo Cikin Mu, Badajimawa ba,” Zumbura ba ki ta ɗanyi “Toh idan ta dawo zamu gudu ko”? gaba ɗaya hankalinsu Haris ya dawo kanta
Murmushi Batul ta sakar mata”Eh mana da zarar ta dawo zamu gudu mubar kurkuku....” tunkan ta kai ƙarshen maganar Jemimah ta katse ta da cewa”Zamu koma gidan daddyn Genie Ko? In da zamu sakata mu wala mu yi rayuwar mu babu takura Allah yasa genie ɗin mu ta dawo da wuri na ƙosa muje inga gidan daddyn ta”
farin cikin da su ka gani akan fuskar jemimah a yayin da ta ke yin maganar yai matuƙar karya masu Zuciya, Har sai da suka ji hawaye sun cika idanuwansu, cikin rauni na murya Deeja tace da ita
“Jemimah Pray for Her! Tana buƙatar addu’ar mu, mu dage da yi mata addu’a har sai ta dawo Cikin mu” jinjina kai jemimah ta yi tare da cewa”tom zan mata addu’a” ta ambaci hakan tare da lumshe idanuwanta, acikin zuciyarta tana ambaton Ya Allah ka dawo min da Genie ɗita in dai kana son farin ciki na....”
“Gabriel Ka tada azeeza ta tashi Mu haɗu mu duka wurin yi mata addu’a ba yadda za’ae muna acikin tashin hankalin nan ita tana bacci, ko dai jemimah da ta ke ƙarama a cikin mu ta kasa runtsawa balle ita” Rubina ce ta yi maganar, Girgiza mata kai Gabriel yai alamar Bazai tayar da ita ba
“I’m sorry to say I can’t wake her I don’t want to worry her, Just Let her sleep.” ɗaure fuska Rubina ta yi jin a bun da yace, ita haushinta yadda suka tashi hankalin su akan Angel amma ita Azeeza ta lafe jikin shi Hankalin ta kwance ta ke sharar bacci.
“Akwai matsala fa! Dare Yana ƙara nutsawa babu alamun Angel zata dawo” Sarah ce ta yi maganar tana daga zaune Ta jingina bayanta jikin bango, Ta saki dogayen ƙafafuwanta ƙasa.
“Duka yaushe ta tafi da har za ki fara tunanin akwai matsala! Pls mu yi mata fatan Alkhairi, Ni gajan haƙuri ke bana so” acewar Haris.
To jama’a abu fa kamar wasa A ƙalla Angel ta ɗauki tsawon awanni babu ita babu alamarta, Idanuwansu sun kaɗa sunyi jawur dasu ga bacci ga yunwa ga zullumin rashin ta atare da su, sun dage sai addu’a Su ke Yi mata, Ba zato ba tsammani Hasken Ɗakin su ya gauraye ko’ina, ta jikin ƙofar ɗakin tsohuwa da bata ƙarasa datsewa ba su ka hango hasken da ke kurɗaɗowa, Hankalinsu Ba ƙarami tashi yai ba, A kiɗime su ka mimmiƙe tsaye hatta Azeeza da ke bacci sai da ta farka tana faman murza idanuwanta da yatsun hannayenta.
kallon kallo suka shiga jefawa junansu fuskokinsu ɗauke da matsananciya damuwa
“Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un;’ shine kalmar da ta fara fitowa abakunansu Deeja, Yayin da su ke a tsaitsaye cirko cirko, Bakomai ne ya tayar masu da hankali ba face ganin Safiya ta yi ba tare da Angel ta dawo ba. Nan ta ke ransu ya basu cewar wani abu ya faru da ƴar uwarsu.................
Shine meke Faruwane ata 6angaren Angel!?
Ai tun lokacin data watsa da gudu ta nufi Cikin kurkuku, Sautin kururuwa
Mai ƙaraji da gurnani ya cika kunnuwanta, ga wani azababben San yi da ya addabe ta, kamar jaura ta gifta Cikin duhu ta ke gudu
Adai dai lokacin da ta ɗaura ƙafarta saman ground floor ɗin nan Inda ke kewaye da dogayen benaye Ba zato Ba tsammani idanuwanta su ka sauka akan ƙafafuwan Tsohuwa Zafreen Lamarin yai matuƙar gigitar da ita, sam Ba ta yi tsammanin Zata ci karo da wani abu ba ita kawai ta sanyawa ranta cewa Danish ne kaɗai mutumin da zata haɗu da shi.
Mummunar faɗuwa gabanta yai, ƙirjinta ya hau bugu da ƙarfi da ƙarfi A firgice ta ɗago da idonta akan tsohuwa zafreen da ke a ruƙe da sanda, Kasancewar Filin Yana da Fitilu masu haske can saman silin ya gauraye ko’ina, daga ƙasa har sama shigar Jajayen kaya ne a jikinta kamar kullum Fuskarta na asanye da takuntumi.
“Ya Allah saida nayi addu’a kafin in fito but why na fara Cin karo da mummunar tsohuwar nan Ina lillahi.....” acikin zuciyarta ta ambaci hakan, Kafin ta yi wani yunƙuri tsohuwa Zafreen ta soma tunkarota sautin takalmanta ƙwas ƙwas har cikin dodon kunnan Angel, Duk ta ku ɗaya idan ta yi sai gaban Angel Ya faɗi, tauraruwa mai wutsiya ganin ki ba alkhairi ba.
Ko da ta ƙaraso gabanta, Bata tanka mata ba, Sai bin ta da tayi da wani matsiyacin kallo irin na marasa imani, Shuɗayen idanuwanta sun Ciza launinsu.
“Ban yi mamakin Ganin ki ba Unaisah! Ina ji arai na ba yau ba ne rana ta farko da kika fara ƙetare Iyakar Ki, Taurin kan ki da kafiyar ki da kuma rashin tsoron ki su ne suka ƙarfafa maki gwiwar shigowa Cikin prison! Ko a tarihi ba a ta6a samun prisoner ɗin da ya ta6a ƙetare Iyakar shi ba sai Akan Ki”!
Magana ta ke yi muryarta na fita da sauti mai amo.
yawu Angel ta haɗiya, tuni tasha Jinin jikinta, Ido ya raina fata sam ta kasa magana, Zufa sai tsastsafo mata ta ke yi kan fuskarta har ɗiɗɗiga ta ke a ƙasa.
“Ko za ki Iya faɗa min menene Ya fito da ke? Kuma Ta yaya akai Kika tsaga bangon ɗakin ku kika fito”? Muryar Angel na rawa ta soma magana”Tsautsayi ne da ƙaddara, dan Allah kada ki cutar dani, Zan koma inda na fito, Kawai Inason ganin ɗan uwana Danish ne shiyasa na fito neman shi.....” kasa ƙarasa maganar ta yi sakamakon sautin Dariyar tsohuwa zafreen da ya tari numfashinta.
Tsagaitawa ta yi da yin dariyar, ta soma matsawa tana ƙara kusanta kanta da Angel, A tsananin tsoroce Angel ta ke Ja da baya tana girgiza mata kai
“Tun jiya dana shigo ɗakin ku Raina ya bani cewar Wani abun ku ke shiryawa kuma ke ce jagora a cikin tafiyar, Saboda prisoners basu da wayan da zasu Iya ta6uka wani abu, Unaisah ke ce ƙwarin gwiwar su, Babban kuskuran da ki ka aikata shi ne ƙetare Iyakarki! Hakan Ya sa6awa dokar Kurkuku! Na yi imanin babu mai Iya ƙwatarki daga hannu na! Saina rushe duk wani sashe na Jikin Ki da ke da ƙarfi zuwa mai rauni......” Zazzare ido Angel ta yi tamkar ƙwayar zata faɗo ƙasa Jikinta sai kerma ya ke yi.
“Kin jama kan ki bala’i da masifa! Not only u! Hatta Ƴan uwan ki da Ki ka baro ɗaki, suna cikin masifa, Zanje gare su Bayan na gama da ke, duk saina tarwatsa farin Cikin da ku ke da shi” Muryarta a kausashe ta ke furta maganar.
Hawayen da su ka taru a cikin idonta ne suka soma gangarowa saman kuncinta da wani irin rauni na murya ta furta”duk horon da za ki yi mani kada ki haɗa da ƴan uwana, Ni ce mai laifi don haka Ni za ki hukunta”
Fuskar Tsohuwa Zafreen a murtuke ta jinjina kai tare da cewa “Umarni ki ke Bani? In yi abunda kike so”? A ruɗe Angel ta girgiza kai ba tare da ta iya furta mata komai ba.
“Zan jaraba Ki inga idan zaki Iya ceton Kanki, Nasan baki ta6a shaƙar ƙamshin mutuwa ba amma yau zansa ki shaƙeta sosai, waɗannan Idanuwan naki launin ruwan toka yau zansa su koma launin Ja, Hawayen da ke fito wa ta cikinsu zansa su janza launi zuwa na Jini, La66an ki da su ka saba gaya wa Mutane magana Ayau ɗin nan zan canza masu kamannin.....” Hankalin Angel idan yai dubu to ya tashi tarasa gane inda kalaman tsohuwa Zafreen suka dosa.
Ja da baya tsohuwa zafreen ta soma Yi yayin da ta ke sakin Shu’umin Murmushin nan nata na tantiran Ƴan duniya waɗanda su ka ga jiya su ka ga yau
Juyawa Baya ta yi tare da nuna ma Angel Third floor da sandar hannunta
“Ɗan Uwan ki da ki ke nema Yana a hawa Na Uku, Za ki Iya zuwa gare shi, Fatan Nasara” Kalmar ƙarshe da ta furta mata kafin Ta buga sandar hannunta ƙasa, Nan ta ke hayaki Mai kamar an watsa tiya gas Ya cika idanuwan Angel, bata Iya ganin komai amma taji aranta cewa tsohuwa Zafreen ta 6ace daga wurin da ta ke a tsaye, a hanzarce ta kamo sunan Allah taci gaba da ambaton duk wata addu’a da tazo bakinta, Cikin ƙankanin lokaci ƙurar ta washe Idanuwan ta suka dawo dai dai. A lokacin ta riga ta yanke shawarar komawa ɗakin su gurin ƴan uwanta saboda gudun kada tsohuwa zafreen ta cutar mata dasu kamar yarda ta furta mata cewa zata je gare su, A hautsine Ta juya da niyar tabi hanyar da ta 6ullo don ta koma ɗakin su, Rass gaban yai mugun faɗuwa ganin babu corridor ɗin kwata kwata kamar ba’a ta6a yinta ba, Yawu ta haɗiya zuciyarta na harbawa da sauri da sauri tamkar zata faso ƙirjin ta.
A fujajen ta mayar da