Author : Boss Bature Category : Complete Novels
dariya mai sautin gaske kamar zata fasa masu kunnuwan su, har saida suka sanya tafin hannayen su wurin toshe kunnuwan su.
Lokaci ɗaya ta dakata da yin dariyar tare da ɗaure fuskarta tamau babu annuri ko misƙala zarratin.
Wahalallan Yawu su ka haɗiya, Daƙyar Deeja ta samu damar buɗe baki Muryarta na kakarwa ta soma magana”Dan Allah Ki yi haƙuri kada ki cutar mana da ƴar uwar mu, duk abunda ta aikata ba laifinta bane, Laifin mu ne, ta yi ne saboda mu.....” bata ƙarasa maganar ba, Haris yai saurin toshe mata bakinta gudun kada ta tona masu asiri, A hasashen shi Tsohuwa zafreen bata san zancen shirin guduwar su ba, Iya abunda ta sani shine Shigar Angel kurkuku.
Muryar jemimah Cikin shessheƙar kuka da 6acin rai tace”Wlh idan ki ka ta6a mini Genie ɗina saina rama mata, bata ma ku komai ba ku ke cutar min.....” a hanzarce Batul ta toshe mata bakinta da hannu, Hankalin su yai matuƙar tashi ganin irin kallon da tsohuwa Zafreen ta ke bin Jemimah.
“Dan Allah Ki yi haƙuri da kalaman da ta yi maki, yarinya ce bata son komai ba, kuma bata acikin hayyacin ta,” Atare suka haɗa baki suna bata haƙuri, da buɗar bakin ta sai cewa ta yi”Sorry for ur self! Ku ya cancanta in ba haƙuri saboda kune rayuwar ku ta ke acikin matsala, Ni bani da damuwa”
A matuƙar ruɗe suke binta da kallo
Cigaba da yin magana ta yi cikin shaƙiyanci da izgilanci”Na jima inason kasancewa tare da ku ban samu damar Yin hakan ba sai yau, Ganin ku da nayi ahaka yayi matuƙar tayar mini da tsohon tsumina, ya za’ai? Zaku bani haɗin kai ko kuwa zan ƙwaci haƙkina ta karfi”? Ta yi tambayar tana ɗage masu gira.
Kallon kallo su ka soma jefa ma junan su, sam basu fahimci me ta ke nufi ba.
“Au Na manta kufa dabbobine ba ku san komai ba, dole sai ana yi ma ku magana da yaren da zaku iya ganewa,” ta ambaci hakan tare da tunkarar su, bayin Allah sai ja da baya baya suke Ke yi.
“Abunda na ke nufi shine zan kwanta da ku In biya buƙatata, idan ku ka bani haɗin kai salin alin zamu rabu lafiya, har ma In bada umarnin akawo maku lafiyayyan abinci, kuma daga rana irin ta yau za’a daina baku ganye kuna Ci”
Hankalinta akwance ta ke kora masu Bayani, Cikin shessheƙar kuka Deeja tace”Wlh ba zamu ba ki haɗin kai ba” ta ambaci hakan tare da kallon su Hibba
“Kada ku yadda da ita so ta ke ta yi mana irin abunda akayiwa unaiza wanda yaja har ta mutu tabar duniya......” Maganar da Deeja ta yi ne ya fargar dasu, sai yanzu su ka fahimci abunda tsohuwa zafreen ta ke nufi. Ƴan matan cikin su tuni sun fashe da kuka suna roƙonta akan karta ta6a su ta ƙyale su, Baiwar Allah Azeeza ta ƙanƙame Gabriel kamar zasu koma mutun ɗaya. tsananin tausayin kansu ne ya kama su, don basu ga alamun sassauci akan fuskarta ba.
Tsawa ta daka masu tare da nuna mazansu da sanadar hannunta”Maza ku fuce ku bani wuri, ba da ku zanyi ba, Matan na ke kwaɗayin kasancewa dasu” kaitsaye ta basu umarnin fita, kamar sakarkaru haka suka haura ƙafafuwan su su ka nufi ƙofar fita, Azeeza da ke ruƙe da Gabriel tuni ya yi wurgi da ita ƙasa saboda basa acikin hayyacin su, ta yi amfani da sihirine wurin basu umarni su fita, fucewar su ke da wuya ƙofar ɗakin ta datse ta yadda ba zasu Iya tsere mata ba.
Jikin su sai kerma ya ke yi, da gudu Azeeza ta shige ƙarƙashin gadon tsohuwa tamira, ganin ta yi hakan yasa Batul sauke Jemimah tare da turata ƙarƙashin gadon, tace da azeeza ta rungumeta a jikinta, bayan ta ɗago ta jera da sauran ƴan uwanta suka haɗu suna yi mata magiya akan ta ƙyale su kada ta cutar dasu.
Shu’umin murmushi ne ya bayyana akan fuskarta, A hankali ta jefar da sandar hannunta, Dama lafiyar ƙafarta lau, ruƙe sandar da ta ke yi na ado ne. Yatsun hannayenta ta ɗaura kan doguwar rigar da ke a jikinta, Ta zame ta nan take tsiracinta Ya bayyana babu kyan gani jikin ta duk tamoji tamoji kamar jikin faskaran Icce, Undyn da ke a jikinta shara shara ya ke kamar net kana iya ganin komai, uban gashin gabanta gwanin ban ƙyama, Tsayin shi ya kai na ciyawa, wani abun tashin hankalin ma Halittar gabanta sak irin na Namiji ce hakan na nufin tsohuwa zafreen Mata maza ce! Nonuwanta kamar silifas har saman Cikinta. Runtse idanuwansu su ka yi don ba za su Iya jurar kallon tashin hankalin nan ba. Ajikin bango suka ƙanƙame juna kamar zasu tsaga shi su shige ciki saboda tsabar yadda su ka manne mashi.
Bayan ta kammala cire doguwar rigar ta jefar da ita ƙasa.
“Ku kwantar da hankulan ku Ni ba da ku zan fara ba, Na ƙarƙashin gadon su nafi sha’awa” jin wannan maganar yasa suka bubbuɗe idanuwansu azazzare suke kallonta, Kafin su ka kai idonsu kan gadon tsohuwa Tamira da ƙarfi Deeja ta furta sunan Jemimah da Azeeza, Kafin su yi yunƙuri zuwa gare su tsohuwa zafreen ta cimma ƙarƙashin gadon da hannu Ta janyo ƙafar azeeza da ta jamimah da ƙarfi ta fusgosu waje kawunansu ba ƙaramin buguwa su ka Yi ba, A saman gado ta kwantar dasu Sai faman lashe baki take tana ƙokarin cure masu kayan jikin su.
Kukan kura Su Batul su ka yi da gudu gaske suka haye saman gadon, Da iya ƙarfin su na ƙarshe su ke kai mata naushi duk don ta ƙyale masu Ƴan uwansu, sai dai ina ko kaɗan tsohuwa zafreen bata Ji bugun nasu ba, batasan ma su na yi ba don tuni ta tsuduma cikin biyan buƙatarta dasu azeeza, ta raba su da kayan jikin su, sautin kukansu Ya karaɗe Cikin ɗakin wani irin raɗaɗin azaba su ke ji a jikinsu, sai da ta tabbatar ta lala masu rayuwa, tun numfashinsu na fita a wahalce har ta kai ga sun daina motsi, gaban su sharkaf da jini, tukunna ta ƙyalesu ta koma kansu Batul da ke bugun bayanta, wata irin wawura ta kai masu da hannayenta masu faɗi ta dinga Rabasu da kayan jikinsu Zir ta yi masu Mutun biyu ta damƙa acikinsu Sarah da Yasmin Ta kwantar dasu ƙasa ta hau kansu taci gaba da biyan buƙatarta, wa’iya zubullah Tashin hankalin da suka fuskanta Bazai misaltu ba, basu ta6a ganin Masifa ido da ido ba sai yau, Suna ji suna gani ta gama amfani dasu sarah ta koma kan su Rubina ɗaya baya ɗaya ta ke kwantar dasu ƙasa ta hau kansu tana Biyan buƙatarta. sautin koke kokensu da gurnanin tsohuwa zafreen Ya cika kunnuwansu Haris, waɗanda tuni sun jima da haukacewa, Don tun bayan fitar su daga cikin ɗakin ƙofar ta datse, Tunaninsu ya dawo, Sun yi kuka har sun gaji, yayin da su ke jiyo sautin muryoyin su Deeja cikin mawuyacin hali su ke ƙwala masu kira donsu zo su cece rayuwar su sai dai sun gaza yin hakan, basu da wata hanya da zasu iya taimakon su, ji su ke kamar su haɗiyi zuciya su mutu, sun yi fatan ace mafarki ne ba gaske ba.
Mutun ɗaya ce ta rage A tsaye Fuskarta jaga jaga da hawaye ta rasa ya za ta yi don tasan itama zata dawo kanta ne idon ta gama dasu Deeja gani ta ke kamar ƴan uwan su sun mutu saboda wasu daga Cikinsu babu numfashi atattare dasu Musamman jemimah da Azeza zaiyi wuya su rayu. zafreen ta gama kashe masu rayuwarsu ta wulakanta su kamar dabbobi.
A haukace Batul ta nufi table ɗin da ke ɗauke da Tunkunyar shayin nan ta ɗaɗɗago shi da hannu biyu, tana haki ta nufi tsohuwa zafreen da ta duƙufa asaman su Rubina, ta daddage ta buga mata shi, Ko gizau batayi ba, Komawa ta yi tare da ɗauko kujerar table ɗin ta dawo ta kuma buga mata ita saman kanta, still bata ɗago ba.
A fujajan ta koma cikin ɗakin tana neman abunda zata ƙwala mata, Duk ta bi ta haukace sai waige waige ta ke yi fuskarta sharkaf da hawaye, har zata juya ta wutsiyar idonta ta hango Rigar wuƙa da ke a so ke a tsakanin littattafan cikin Book shelves ɗin ɗakin.
Tsohuwar ajiye ce wuƙar da tsohuwa Tamira ta ba Danish Kyautarta a lokacin da ya buƙaci yana son datse sumar kan shi, ashe ya maida mata ita shiyasa ko lokacin da Angel ta yi mashi magiya akan ya bata wuƙar Yaƙi bata saboda bata atare da shi, da gudu Batul ta nufi book shelves din ta zura hannu ta ɗauko rigar wukar ta zaro ta Jikinta har salƙi ya ke yi saboda tsabar kaifinta, wuƙar sihiri ce mai haɗarin gaske, Cikin zafin nama ta watsa aguje bata nufi ko’ina ba sai kan Tsohuwa Zafreen a lokacin ta gama da su Rubina juyowar da za ta yi ke da wuya Batul ta daddage ta Luma mata wuƙar Cikin idonta, kafin ta yi wani yunƙurin yin amfani da sihirinta Batul ta ja wuƙar Tun daga kan idonta har zuwa saman wuyanta ta tsartsarga mata Jikinta, Wani irin ƙarfine yazo mata, Dama jinin ta akan akaifa ya ke, Zuciyar ta bushe, Gaba ɗaya tsohuwa zafreen ta gigice saboda azabar zafin da taji na shigar wuƙar, Ta yi ƙoƙarin Buge Batul sai dai Allah bai bata Ikon Yin hakan ba, ba ƙaramin Illah Batul ta yi mata ba, Sai dai duk da haka wani abun mamaki babu ɗigon Jini da ya fito daga idonta, duk inda Batul ta fasa mata da wuƙar kamar ana ɗinke fatar wurin haka ta dinga haɗewa tamkar ba’a ta6a tsaga ta ba.
So ta ke ta lalubo sandar hannunta saboda ƙarfin sihirinta yana a jikin sandar, Idan har babu ita Sauran sihirin da ke a jikinta ba lallai Ya iya yi mata tasiri ba, Daƙyar ta samu ta yi wurgi da Batul gefe ɗaya gaba ɗaya ta kife ƙasa kanta ya daku, wuƙar hannunta ta kufce mata, yunƙurawa zafreen ta yi tare da miƙewa tsaye Jikinta na kakarwa ta soma tafiya tana tunkararta, so ta ke kawai ta kashe ta har Lahira, Cikin fitar hayyaci Batul ta miƙe zaune daga kwancen da ta ke a ƙasa, Ja da baya ta dinga Yi har sai da ta ƙurewa bango.
Tuni tsohuwa zafreen ta cimmata, tafin ƙafarta ta ɗaura saman Yatsun hannun Batul ta murjesu, tsabar raɗaɗin da Batul ta ji ne yasa ta fashe da matsanancin ku ka na fitar hayyaci, wata irin zufa ta soma tsasstafo mata
“Kafin ki kashe Ni, Ni zan fara kashe ki, Dabba kawai, Kin yi kuskure da ki ka soka mini wuƙa A cikin idona, Angaya maki cewa Ni Mutunce da zan mutu farat ɗaya? Tana huci ta yi tambayar, janye tafin ƙafarta tayi daga kan yatsun hannun Batul ta ɗaura ƙafar saman jikinta da ƙarfi ta danna shi tare da murza ƙafar, Jini ne ya soma gangarowa ta cikin bakin batul Nan ta ke Numfashinta ya soma kokawar ɗaukewa.....
Ba zato ba tsammani tsohuwa Zafreen Taji an buge mata kanta da ƙarfi gaba ɗaya ta kife ƙasa, ta baya aka shammace ta, A hanzar ce ta ɗago don ta ga wanene, a matuƙar ruɗe ta ke kallon fuskarta, Ba kowa bace face TSOHUWA TAMIRA.
“Ban yi mamakin ganin ki ba Dama na jima da zargin cewa ba ki atare damu Tamira!” zafreen ce tayi maganar muryarta akausashe, saboda tsabar 6acin rai facial musles din tsohuwa tamira har kerma su ke yi, Hankalinta yai matuƙar tashi ganin yadda zafreen ta lalata rayuwar Yaran da ta raina gaba ɗaya ta gama da rayuwarsu, ta yi danasanin zuwan da ta yi amakare da duk hakan bata faru ba, idanuwanta sun yi jawur dasu tamkar garwashin wuta, wani irin hu ci ta ke futarwa
Yunƙurawa tsohuwa zafreen ta yi tare da miƙewa tsaye, Ido cikin ido su ke kallon juna babu sassauci akan fuskokin kowannan su.
“Ni dama ba ki ta6a burgeni ba, Muguwa azzaluma baƙar kafura, Ban ta6a ganin dabba Jahila daƙiƙiya irin ki ba, Wai ke baki da hankali ne? Ke fa mutunce waɗannan yaran da kika lalata rayuwar su mutanene fa ba dabbo bi ba, Laifin me su ka yi maki da har su ka cancanci wannan hukuncin daga gare ki”? Rai amutuƙar 6ace ta jefa mata tambayar.
Ɗaure fuska tsohuwa zafreen Ta yi, idanuwanta sun kaɗa jawur dasu, Babu ko alamun imani akan fuskarta
Tana magana tana huci kamar mayun waciyar zakanya” Ni kike gayawa magana? Ka da ki manta ke bakowa bace a gidan kurkukun nan face ƙasƙantacciya mai rainon Yara, dole Ki yi mini biyayya saboda ni ke agaba da ke, Nafi ƙarfin ki Tamira nesa ba kusa ba, Idan har kina son ki tsira da ranki to ki gaggauta barin wajen nan tunkafin In yi maki mummunar Ill......”Bata kai ga ƙarasa maganar ba, tsohuwa Tamira ta daka mata tsawa har saida ta furgita, karo na farko kenan da taga Rashin tsoro acikin idon Tamira.
Nuna ta ta yi da yatsan hannunta”ko da can baya da na ke girmamaki ba dan ina jin tsoron ki bane sai don Ƙudirin da na ke dashi na son Rushe Baƙin tarihin da kuka kafa, Ajali ne ke kiran ki shiyasa har ki ka yi gigin shigowa cikin ɗakina, A yau inaso in nuna maki ƙarfin ikon da na ke shi wanda na samu awurin rainon yaran da nake yi, Zafreen Yau zaki yaba ma aya zaƙinta, Ko da zan rasa raina ne saina fara ganin bayanki wulaƙantacciya kawai”a fusace ta ambaci hakan idonta akan fuskar zafreen ga dukkan alamu mamaki da al’jabi ne ya hana ta mayarwa Tamira martanin maganarta. bata ta6a tsammanin tsohuwa Tamira zata Iya yada mata magana ba tare da jin shakkarta ba.
“Tsautsayi da ƙaddara ne suka jefo waɗannan Watsastsun ƙafafuwan naki cikin ɗaki na, Kin ga babu mai kallon mu bare aji sautin mu, Yau zan huce haushina akan ki....” Tunkan ta ƙarasa maganarta, tsohuwa Zafreen ta 6ace ma ganinta, Hankalin tsohuwa Tamira Ba ƙaramin tashi yai ba, babban abunda ta ke ji ma tsoro kada ace ta bar ɗakin, In kuwa haka ta faru zasu fuskanci azabtarwa domin kuwa za ta je ne ta fallasa su.
Jin motsin mutun abayanta yasa ta yi saurin Juyawa, Har saida gabanta Ya ɗan faɗi ganin tsohuwa Zafreen ta bayyana cikin shigar jajayen kayanta hannunta ruƙe da sandarta, ashe 6acewar da ta yi don ta ɗauko sandar hannunta ne ta kuma mayar da suturarta.
“Na yi tsammanin kin ji tsoro kin gudu ne”; acewar tsohuwa Tamira
Mahaukaciyar dariya zafreen Ta saki tare da cewa”Babu tsoro a cikin zuciyar tsohuwa Zafreen! Tamira kin shiga Uku! Kin tsokanowa kanki Bala’e da masifar da ba za ki Iya jurarsu ba, Zan kashe ki har lahira bayan na gama da ke zan ƙarasa kashe waɗanda basu mutu ba a cikin Yaran can naki, Zan sha Jinin su In ci tsokar naman su”
Tana kai ƙarshen maganar ta, ta yi kukan kura tare da Afkawa tsohuwa Tamira, gaba da gabanta Aljani Ya taka wuta, Domin kuwa Zafreen tafi Tamira ƙarfin sihiri, Faɗane ya kaure a tsakanin su kamar dawakai, ba ka iya jin komai sai sautin buge bugen su da gurnaninsu uwa namun dawa, Ƙura ta karaɗe cikin ɗa ki, Kusan atare su ka canza suffofin su, Tsohuwa Zafreen ta rikiɗa ta koma Damusa, Tamira ta koma kura, Ko a namun dawa Damusa ba abokiyar karawar Kura bace, Faɗan nasu Ya canza salo, kamar a filin daga su ka cigaba da kaima junan su Hari duk suka raunata kawunan su.
*ANGEL*
Tsawon lokaci tana a sume saman Gadon da aka kwantar da ita, fatar jikinta jawur da Jinin da su ka yi mata wanka dashi duk ya daskare mata, zai yi wuya yabar Jikinta, saukar ruwan sanyin da ta ji ajikinta ne ya farkar da ita a firguce ta farka, sai dai ta kasa buɗe idanuwanta saboda nauyin dasu ka yi mata, hatta bakinta Yaƙi buɗuwa la66anta sun kumbura suntum wani irin zogin azaba su ke yi mata.
Ba zato ba tsammani kunnuwanta su ka jiyo mata muryar SALSABEEL.
“Meyasa ki ka yi gaggawa? Kin manta me na faɗa ma ki? Sai da nace ku yi takatsantsan idan ba haka ba za ku ja ma kan ku ne damu kan mu....” Sam ta ƙasa motsa bakinta, Idanuwanta kaɗai ta iya samun damar buɗe su akan jikin shi, Yana atsaye Cikin shigar Giant ko’ina na jikin shi arufe kamar yarda ta ganshi a shekaran Jiya. Ta yi mamaki sosai saboda a tattaunar da su ka yi da ita ya faɗa mata cewa ba zata sa ke ganin shi ba, sai ga shi Ya dawo yau, hakan ya tabbatar mata da cewa suna acikin haɗari gaba ɗayan su, taja masu bala’e.
Rushewa ta yi da matsancin kuka raunin da ke abakinta yaci gaba da fitar da jini
Tsananin tausayin ta ne Ya kama shi, ganin yadda suka raunata Jikinta sun gur6ata mata tsaftatacciyar fatarta, tsabar takaici da danasanin gaggawar da ta yi ne yasa ta yin kukan, tana so ta yi ma shi magana sai dai ta kasa saboda sautin muryar ta yaƙi fita ko da tana yin kukan babu sauti.
“Ban faɗi hakan don na fama maki ciwon da ke acikin zuciyarki ba, Nasan kina yi ne duk don ki cece rayuwan ƴan uwan ki, don kuma ki cika mana alƙawarin da ki ka ɗaukar mana, sai dai kash gaggawar da ki ka yi ta yi silar jefa rayukan mu cikin haɗari, Zai yi wuya mu tsira sai dai bazan bari Ki rasa ran ki ba, Zan yi maku ƙoƙari Ayau ɗin nan ku fuce daga cikin kurkukun nan kafin Hankalin Matsafan ya dawo kanku, Mun ci sa’a shuwagabannin kurkukun basu aciki, Sauran da suka rage Giant ne masu haɗarin gaske, Ni kaina da na ke da sihiri a jikina bazan Iya ja dasu ba, A yanzu haka da nake Yin magana da ke nayi ƙoƙarin Sarrafa ɗakin Da ke ɗauke da madubin tsafin su shiyasa ba zasu Iya ganin mu ba, Nan da Awa ɗaya Zamu Aiwatar da komai Idan har lokacin nan ya cika kuna acikin kurkukun nan mu