Author : Boss Bature Category : Complete Novels
Aneelerh tace dashi ya jirata anan, ya amsa mata da toh, da sallama abakinta ta shiga palourn gidan, adai dai lokacin mai aikin gidan ta fito daga kitchen ta yi arba da aneelerh, fuskarta da fara’a suka gaisa tace mata wurin hajiya falmata tazo, Allah yasa tana nan, Mai aikin tace bata jima da dawowa daga office ba, ki zauna bari naje in sanar da ita, da sauri mai aikin taje ta fado mata, jim kadan ta dawo ta sanar da aneelerh sakon hajiya tace ta jirata gata nan zuwa, aneelerh ta amsa mata da toh, kusan mintuna biyar Aneelerh tana a tsaye ta ruƙe qugu tana jiran fitowarta, cikin jin fargabar ganin matar, sai faman bin palourn take yi da kallo.
Sautin takun tafiyarta ne Yaja hankalin Aneeleerh ga kallonta, A hankali take saukowa down stair, ta ɗauki wankan tsadaddan leshi, kanta yasha ɗaurin ɗan kwali, ta manna farin glass a idonta, Babbar macace tana da jiki, tana tafiya tsokokin jikinta na motsawa, Fatar jikinta tasha hutu har ta gaji, daga ganin fuskarta masifaffiyace, idanuwanta mitsi mitsi da su kamar na mutanan Yankin china, hancinta kuwa abaje yake, ga big mouth dinta yasha man baki.
Ta6e baki Aneeleerh tayi aranta ta furta jibarta dan Allah, ƙatuwar banza da ita kamar buhun masara, a haka take lalata rayuwar matasan ƴan mata, Allah dai ya shirya, wasu mutanan sunyi asarar rayuwarsu.
Lokacin da hajiya falmata ta ƙarasa saukowa daga saman benan, idanuwanta suka Yi mata tozali da kyakkyawar fuskar Aneelerh nan take taji ta burgeta, tayi mamakin ganin baƙuwar fuska agidanta, bakomai yafi tafiya da imaninta ba face Kyawun surar Aneelerh.
Ganin Yadda Ta tsareta da idone Yasa Aneelerh tayi saurin gyara mayafinta ta rurrufe jikinta, Aranta ta furta A’uzubillahi minasshaidanirrajin, Aniyarki ta biki baƙar mayya”
Saman sofa din dake fuskantar Aneelerh Hajiya ta zauna, tana dubanta da wani irin mayataccen kallo.
Yamutsa fuska Aneelerh tayi fuskarta ba wasa tace”barka da Yamma”
Hajiya falmata ta amsa mata da”barka dai, bismillah ki zauna mana”
Ɗaure fuska Aneela tayi”bana zama agidan da ake aikata sa6on Allah, saboda ni tsarkakakkiya ce, bai kamata in goga ma jikina najasa ba”!! Mamakine Ya kama hajiya falmata, a hankali ta sauke glass din dake saman fuskarta don ta samu damar ƙarewa Aneelerh kallo.
“Bansan wacece ke ba, sai dai na fahimci haukan talauci ne ke damunki shiyasa kika kwaso ƙafa kika zo gidana don in taimaka maki”
Dariyar rainin wayau Aneelarh Tayi kafin tace”ki kalleni daga ƙasa har sama, kema kinsan nafi ƙarfin ki kira ni da talauci, Ni banzo don nayi cece kuce dake ba saboda bani da lokacinki, Maganar kudin zahra da kike bin ta bashi ne”
Shu’umin murmushi ne Ya bayyana akan fuskar Hajiya falmata da shaƙiyanci ta furta”oh, kinzo ne ki fanshe ta, shiyasa kika kawo min kanki? Donni banga alamun zaki Iya biyan kuɗin ba”
Girgiza kai Aneelerh tayi ranta a6ace tace”wato shi dai jaki duk yadda akai dashi sai yaci kara, idan kina tunanin na kawo maki kaina ne don in fanshi zarah to ki daina, domin kuwa nafi ƙarfin ƙasƙantacciyar mace ballagaza jahila kuma daƙiƙiya irinki, Mace mara tsoron Allah, me yin amfani da dukiyarta don lalata rayuwar matasan ƴan mata masu neman nakansu, Wlh kinji haushin rayuwar......” gigitacciyar tsawa Hajiya falmata ta daka ma Aneelerh, tamkar damusa ta yunƙura ta miƙe tsaye tana duban Aneelerh da mummunar fuskarta babu annuri ko misƙala zarratin ta nuna mata Hanyar fita da yatsan hannunta”Ke Fuce kibar min gidana, tunkafin ranki Ya 6aci, matsiyaciyar banza masu ƙashin tsiya”
Aneelerh da ƙarfin Hali tace”idan kinga na fita gidan nan to nagama faɗin ta cikina ne, Kuma wallahi koda gigin wasa kika ce zaki ta6a lafiyar jikina saina naƙasa ki bakisan wacece Ni ba” ta faɗa tana jefa mata harara, lamarin Ya ɗaurewa Hajiya falmata kai, ganin karfin hali na Yarinyar nan data zo gidanta tana Yi mata rashin Kunya.
Goya hannayenta tayi saman ƙirjinta”ina sauraronki, Me ya kawo ki gidana!”
Gyaɗa Kai Aneelerh Tayi”zuwa nayi don Inyi maki nasiha, don na fahimci Wadda iyayenki suka yi maki tuni shaiɗan Ya hure maki kunne, dan Allah Jibarki cikin shiga ta mutunci kamar wata mutuniyar arziƙi, al’halin nan kuwa fuska biyuce ke, A fili musa a zuciya fir’auna, Haba baiwar Allah, Da hankalinki da tunaninki da shekarunki kika za6i ki sa6awa Allah don kawai ki ji daɗin duniya? Kin manta da Allah yana ganinki kuma zaki mutu ki koma gareshi, a ko’wani yanayi mutuwa tana iya riskarki, idan taƙamarki kuɗine ki tuna Allah ne Ya baki Arziƙin bake kikayi ma kanki ba, Idan yaso zai Iya ƙwace wa, kuɗi da kike gani wallahi masifane Idan baka tafiyar dasu ta hanyar da ta dace ba, Ita kuma rayuwar duniya jin daɗinta ƙalilan nan bata da tabbas, bakisan yaushe zaki mutu ba, kin sanya mugunta aranki saboda Allah Ya azurtaki, Kina cutar matasan Ƴan mata, waɗanda Iyayen su suka sha wahalar basu tarbiya ke kuma kina gur6ata masu rayuwarsu, Allah kaɗai yasan adadin Ƴan matan da kika 6ata, kin goga masu jarabar da bazasu Iya gogeta ba, Kin cutar da rayuwarsu mutane suna kuka da su saboda sun addabi rayuwar al’umma kuma ire-iren ku ne ku ka yi silar lalacewarsu, wallahi kiji tsoron Allah kamar yarda ba zaki so ayi da ƴar ki ba to kema kada Kiyi da ɗan wani, duk da naji irinku Harda ƴa’ƴan naku kuke Yi, saboda shafewar basira da neman duniya kun makance bakwaji bakwa gani ku ala dole saikun siyama kanku tikitin shiga wuta”? Tun da Aneelerh ta soma Yi mata magana da faɗa haɗi da tsiwa take ta faman zare ido tana binta da kallo, tun da take arayuwarta wani ɗan adam bai ta6a gigin tunkararta Ya faɗa mata magana game da abunda Take aikatawa ba sai Yau da Allah Ya haɗa ta da Auntyn Zahra mai dimple, Ayoyin kur’ani aneelerh ta soma karanto mata tana fassara mata, kamar an rufe mata baki takasa dakatar da ita duk irin masifar da take da ita yau an kashe mata bakinta
“Allah Yana son bayinshi waɗanda suka aikata 6arna suka tu6a saboda tsoronshi suka koma gareshi, dan Haka ina baki shawarar tunkafin lokaci Ya qure maki Hajiya falmata ki Gyara Halayanki, Ni bance zan sanyaki ki shiryu ba don nasan irinku taurin kaine daku kamar kwakwa, ko malamai sunyi maku nasiha bakwaji bakwa gani sai ranar da Allah Ya damƙe ku tukunna zaku gane kurenku, Ni in banda ma shafewar basira, wai ku bakwa tuna mutuwa da kwanciyar ƙabari ne? Baku tuna duk abunda kuka mallaka zai ƙare, daga kai sai halinka za’a binne ka a ƙabarin ka fa? Ke yanzu kin za6i ki mutu kina aikata mummunan zunubi na bin Ƴan uwanki mata? Ga hakkin Iyayen da kika sanyasu zubar da hawayensu ta silar lalata masu rayuwar ƴa’ƴa da ki ka yi ga kuma Matasan ƴan matan da kika gur6ata ma rayuwa, wannan fa zunubine mai cigaba da yaɗuwa ko bayan kin mutu zaki cigaba da samun kamasho acikin shi, saboda kinbar tarin ƴan matan da kika gur6ata agari suna aikata fasadi, wallahi kiji tsoron Allah tunkafin lokaci Ya qure maki, Ina ƙara jan hankalinki ki tuba ki koma ga Allah tunkan mutuwa ta risƙe ki don ita bata kwankwasama mutun ƙofa balle Yace zai shirya mata”
Wata irin zuface ta soma wanke goshin Hajiya falmata, Haƙiƙa kalaman Aneelerh sun fara karya mata zuciya, sai faman zare ido take Yi, batasan ya akai ta tsinci kanta da jin maganar Aneeleerh ba, Yarinyar tayi matuƙar burgeta kuma ta bata mamaki da har ta iya yi mata nasiha batare da jin shakkarta ba, saboda mutane dayawa basa Iya yin magana agabanta, amma Ita wannan ido cikin ido take furta mata magana .
“hajiya falmata, duk runtsi duk wuya kada ki Karya zuciyar wanda Ya aminta dake! Ina magana akan zahra da ta dauke ki tamkar mahaifiyarta saboda ƙaunar dake a tsakaninta da ƴarki fatima, Kin karya mata zuciya, naji daci lokacin da na sameta ta kulle kanta acikin toilet tana Yin kuka babu ci babu sha ita kaɗai batare da kowa ya sani ba, Kin hanata runtsawa saboda taƙi baki haɗin kai ku aikata sa6on Allah, haba baiwar Allah, idan kece akayima yarki haka zakiji daɗi! Don kawai mutun Na buƙatar agazawarka sai kayi anfani da dukiyarka donka cutar dashi? Babu wanda yafi ƙarfin ya nemi taimako a duniyar nan, koda ba a wurin mutun ɗan uwansa ba, zai nema awurin Allah Idan har baka agazama bawansa ba tayaya kake tunanin zai agaza maka?
Jinjina kai Aneelerh tayi, Tuni zafafan hawaye sun wanke fuskarta cikin muryar kuka taci gaba da cewa”Kin ƙona mata rai, zahra ta yarda dake fiye da tsammaninki, tana kuka tana fadamin yadda ta aminta dake amma kika karya mata zuciya, Zahra da kike gani tafi ki Hankali, Yarinyar tana da tawakkali, tana jin tsoron Allah, Na jarabata don inga ko tana da wayon jure ƙaddara idan ta sameta, Ni dakaina nabata shawarar ta baki haɗin kai, da buɗar bakinta sai ce mun tayi ita ko duniya za’a mallaka mata bazata ta6a amincewa ta sa6ama Allah ba, saboda tana jin tsoron shi kuma tana jin tsoron ranar da zata koma gare shi, Hajiya falmata kin ta6a tunanin hakan? A matsayinki na babbar mace wadda ta haura shekara arba’in da ɗuriya a duniya? Shekaru sunja amma baki tsoron mahaliccin ki? Kina amfani da dukiyarki wurin Gur6ata duniyarki da lahirarki, maimakon kiyi amfani da su wurin taimakon bayin Allah marasa ƙarfi wadanda zasuyi alfahari dake ko bayan ba ranki kuma ki samu lada awurin Allah, Yanzu ina amfanin irin wannan rayuwar da kika daukarwa kanki”!?
Ƙafafuwanta ne suka gaza ruƙeta, Jiri Ta soma gani a cikin idanuwanta, adaddafe ta nufi sofa ta zauna tana faman fitar da numfashi.
Hankaɗe Kafaɗa Aneeleerh Tayi”Alhamdulillah nagama faɗar ta cikina, duk wanda yayi da kyau don kanshi, akwai mutuwa akwai hisabi, maganar kuɗi Kuma nazo maki da su miliyan Uku Cuf, Idan ma kina son ƙari zan ƙara maki, saboda inaso kisan muba jinin faƙirai bane idan arziƙine muma mun gaje shi gaba da Baya”
Ɗaga murya Aneelerh Tayi da ƙarfi ta furta sunan Mahboob, shigowa ɗakin Yayi hannun shi ruƙe da jaka baƙa, tunkan ya ƙarasa yake bin ko’ina da kallo, ganin haɗuwar falon gidan aranshi Ya ayyana Lallai hajiyar nan ta tara shiyasa take tsula tsiyarta son ranta saboda tana da arziƙi.
“Zoka ajiye mata tsiyarta,” Aneelerh ta faɗa tana nuna mashi gaban Hajiya falmata, Ta zabga uban tagumi da hannu biyu, da alamun nadama atattare da ita.
Koda mahboob Yayi arba da fuskarta saida yasha jinin jikin shi ganin yadda ta haɗe rai, ga gumi na fita a goshinta.
Kamar mai jin tsoronta Haka Ya ajiye mata jakar agabanta.
Aneelerh ta ruƙo hannun shi acikin nata, har sun ɗaga ƙafa zasu bar falon muryar Hajiya falmata ta dakatar da su
“Dan Allah Ku tsaya”!! Kusan atare zuciyarsu ta buga, a sukwane suka waiwayo suna dubanta, Gabansu ba ƙaramin faɗuwa yayi ba ganin ta fashe da kuka, miƙewa tayi daga saman sofa din ta nufe su tana fadin”wallahi nayi nadama, dan Allah kuyi haƙuri da abun kunyar dana aikata, Nima ba halina bane ƙawayene suka tunzurani har na faɗa harkar” zubewa tayi saman gwiwowinta agaban aneelerh tana kuka tace”Tun da nake a rayuwata wani ɗan adam bai ta6a yi mini nasihar data ratsa zuciyata ba sai akanki, bansan wacece ke ba, amma nayi sha’awar In yi koyi da kyawawan halayanki, duk naji na tsani kaina, na zubda mutuncina da girmana a idon zahra, wallahi naji kunyar da ban ta6a jin taba, Naji ƙuncin Halin dana jefa zahra, saboda ni tagaza runtsawa Na hana baiwar Allah yin bacci na hanata cin abinci, na jefa rayuwarta cikin ƙunci batare da nayi tunanin raɗaɗin da zataji acikin Zuciyarta ba, wallahi nayi nadama koda ace bazaku yarda dani ba, Na tuba kuma in sha Allah bazan ƙara aikata zunubin nan ba, angama bi’iznilillahi, saboda inaso Inyi kyakkyawan ƙarshe kuma inaso in tsira ranar gobe ƙiyama, In sha Allah daga yanzu nagama yin amfani da dukiyata don in sa6awa Allah, da kuma gur6ata tarbiyar ya’yan mutane.....”daƙyar ta ƙare maganar tana faman jan magina.
Ba Aneelerh ba hatta Mahboob Yayi mamakin wannan Ikon Allahn, sun yi sototo suna kallonta kamar sakarkaru duk ta zama abun tausayi tsoron Allah ya shigeta, wata’ƙil dama itace silar shiriyarta shiyasa Allah Ya haɗasu da ita.
Muryar Hajiya falmata na rawa tace”Ku taimaka mun dan Allah, inason in wanke kaina awurin zahra, saboda inason taci gaba da kallona kamar yarda tasanni ada, Nayi alƙawarin zan taimakamata, kuɗin da ku ka zo dasu na yafe mata ku ɗauka ku maida mata su, Sannan inaso taci gaba da yin aiki a company dina, Kayan da suke son ayi masu order A dubai gobe in sha Allah zasu iso Nigeria”
Kallon juna mahboob da Aneelerh suka ƙara Yi, Atare suka furta Alhamdulillah, Aneelerh tace”nagode ma Allah daya bani baiwar Iya tsara kalamin da har suka ja hankalinki, Naji daɗi dana zama silar shiriyarki, Ina fata zaki canza rayuwarki daga Yau ki koma ta gari, wadda kowa zaiyi alfahari da ita”
Jinjina kai Hajiya falmata tayi Cikin sanyin murya tace”in sha Allah,” ruƙo hannayenta aneelerh tayi acikin nata, miƙewa tayi tsaye suna fuskantar juna
“Ki godema Allah, saboda Yana son ki da shiriya shiyasa Ya baki damar gyara rayuwarki tun da sauran numfashinki,”
Jinina Kai Hajiya falmata tayi.
Aneeleerh ta ƙara da cewa”sai dai kiyi haƙuri, ba zamu maida kuɗinba, nariga dana kawo maki dasu, Ki ruƙe su a hannunki, zahra kuma bazata ƙara Yin aiki a companynku ba, zan nema mata aiki awani wurin”!!
Magiya hajiya falmata tadinga yi mata akan tayi haƙuri su koma da kuɗin, ta yafe masu, amma Aneelerh taƙi yarda, mahboob ne yace ta jira zasu yanke shawara a tsakaninsu, ruƙo hannun Aneelerh yai acikin nashi yajata zuwa gefe ɗaya akwai tazara tsakaninsu da hajiya falmata, tayi kasake tana kallonsu
“Aunty aneelerh tunda tace ta yafe kuɗin mu koma dasu kawai, ai ba roƙonta mukayi ba”
Girgiza kai aneelerh tayi”nidai hankalina bai kwanta da matar ba, wallahi irinsu shaiɗanune Mahboob, inajin tsoron ace wani tuggun zata kitsa mana shiyasa tace ta yafe kuɗin, ƙwara mu maida mata aniyarta”
Yamutsa fuska mahboob yai”aunty aneelerh just ki gane, ni dai na yarda da ita, sau dayawa zaki ga mutun yana aikata ba daidai ba idan Allah yaso shi da rahama saiki ga ya shiryu cikin sauƙi batare da ansha wahala ba, Yanzu ki duba matar can, hada fa kukanta kuma har zuƙunnawa tayi saman gwiwowinta tana roƙonmu, why bazamu yafe mata ba? Komai ya wuce, ita kanta zahran ba ƙaramin daɗi zataji ba saboda tana son fatima ƴarta aminnan junane tun tuni, sannan taci burin zuwa obie estate, bayan haka aikin nan da take Yi a companyn su ba ƙaramin ƙaruwa take Yi ba, ita kanta tana faɗi da bakinta irin alheran da take samu ta silar aikin da suke Yima mutane, idan ma da wata manufa tace hakan to mu barta da Allah, In sha Allah babu abunda zata Iya yi mata,” gyaɗa kai Aneelerh tayi”shikenan na amince da buƙatarta, mu koma mu faɗa mata” komawa sukayi cikin falon, bayan sun sanar da ita shawarar da suka Yanke ta dinga yi masu godiya farin ciki duk Ya cikata, kafin tafiyarsu saida ta roƙe su alfarma akan su taimaka mata, tana so zahra taci gaba da ganinta a matsayin mahafiyarta, tasan ayanzu bata da sauran mutunci a idonta.
Aneelerh ce tabata shawarar yadda zata tsara ma zahra, duk don ta amince da cewa ba halinta bane, sun jima agidan kafin daga bisani sukayi mata sallama, sunyi rabuwar mutunci da hajiya falmata, har musayar number sukayi da Aneelerh saboda acigaba da zumunci.
( kunji abun da Ya faru, kafin washe garin ranar da zahra taje kaima Hajiya falmata kuɗinta)
Wuraren ƙarfe takwas na dare, motar drivern da yaje dauko su Alhaji ubaid daga airport ta kunno kai gate din gidan, tunkafin ƙarasowarsu, Dr Shureim da zeenatu suna atsaye bakin Entry hall din falo, hannunsu ruke cikin na juna, daga ita har shi jallabiyace ajikinsu, ta yafa mayafi akanta, tsantsar farin cikine akan fuskokinsu, sunyi matuƙar ƙagara da son ganinsu.
Zeenatu sai faman washe baki take Yi, tunda tayi tozali da motar dake shigowa tana tunkaro bakin entry hall din
Da zamudi tace”ya shureim kana ganin aunty benazir zata Iya gane ni kuwa? Saboda mommy ta fadamin tun ina jaririya ta 6ace ba’a ganta ba”
Fuskarshi dauke da murmushi yace”idan ma bata gane ki ba, da zarar anyi mata bayani zata shaidaki, zan faɗa mata cewa zeenatu ce ɗiyar uncle musa, and my wife to be” tuntsirewa tayi da dariya taji daɗin maganarshi, muryarta da shagwa6a tace”amma ya shureim ai ni banaso ka faɗa mata, wallahi kunya nake ji, ko mommy layla ma kada ka fada mata please da daddyn ku” ta faɗa tana duban face dinshi.
“Ai ni nafiso suji My zeenatu, saboda a fara shirye shiryen shafa fatihar auranmu” zaro mashi blue eyes dinta tai kafin tai saurin sanya tafukan hannayenta biyu ta rufe fuskarta cikin jin kunyar maganarshi ta furta”dan Allah yaya shureim dina kada ka fada masu yanzu, nidai kunya nake ji”
“Kunya kamar bafullatana, kin manta mommynki baturiya ce, daddy musa kuma Hausa fulanine, kakarmu bafullatana ce kakan mu namiji kuma bahaushe ne, Ni bansan inda kika gado Kunyar nan taki ba, a haka zamuyi aure kina jin kunyata”?
Kafin ta bashi amsa, motarsu Alhaji ubaid ta ƙaraso gab dasu, bayan drivern yai parking, da sauri Dr shureim Yaja hannun zeenatu suka ƙarasa bakin motar, yakai hannu ya buɗe masu murfin back seat, a hankali ta zuro da ƙafarta dake sanye cikin takalma, ƙarasa fitowa tayi tun daga ƙasa dr shureim yake binta da kallo, wankan atamfa ne a jikinta riga da skirt, ta kashe daurin dankwalinta, yalwatacciyar sumar kanta ta sauka gadon bayanta, gyalen asaman kafaɗa ta yafa shi, idan kaganta ahaka bazaka ta6a ce