Author : Boss Bature Category : Complete Novels
magana.
“Lafiya? Baku ji ina magana ba”?
Saida suka taushi zuciyoyinsu tukunna suka Iya yi mashi magana,
Zaid yace”Sannu da dawowa daddy, Ya office din? Naga yau ka yi marece ko duk Aikin ne ya ruƙe ka”?
Basarwa Yai tare da cewa”Eh, “ daga haka bai ƙara tanka masu ba, Sai bi da yai ta gefen su Ya wuce, kamar sakarkaru haka suka Bi bayanshi da kallo, Sam baisan cewa sun san abunda yake aikatawa ba.
Kusan atare suka girgiza kawunan su.
“Zayn tunda Ya dawo mu koma ɗaki, dama Ni agajiye nake wlh, inaso na ɗan kwanta In huta”
Juyawa sukayi Atare suka nufi part dinsu.
Hajiya saratu na zaune gefe gadonta, baiwar Allah damuwar duniya ta isheta Hannu biyu ta zabga uban tagumi, gabanta sai faɗuwa yake yi gani take yi kamar wani abunne Ya faru da mijinta, Kasa samun natsuwa tayi zumbur ta miƙe kamar an zungureta da sanda, safa da marwa taci gaba da yi acikin ɗakin tana ƙarewa agogon bango kallo.
Ba zato ba tsammani muryar Pravin ta ratsa kunnuwanta”Assalamu alaikum” tunkafin Ta juyo ta kalleshi ta soma sauke nauyayyar ajiyar zuciya, tsabar farin ciki da sauri ta nufeshi, hannu biyu ya rungumeta a ƙirjinsa.
Sai faman sauke ajiyar zuciya take Yi, yayin da take ƙara shaƙar ƙamashin turaren jikinsa.
“Am sorry My wife, nasan ban kyauta maki ba....”tunkan Ya ƙarasa maganar, Hajiya saratu ta dago da fuskarta, babu annuri ko misƙala zarratin tuni yasha jinin jikinshi.
Da kakkausar Murya ta furta”PRAVIN DAGA INA KAKE”!? Rass Yaji gabanshi Ya faɗi
“Na kira p.A dinka Awaya ya sanar dani cewa tun ƙarfe 12 kabar office, Inason Jin ya akai kabar office ina kuma kaje”? Rai a6ace take Yi mashi magana, Hannunta ruƙe da qugunta.
Ya tsareta da Ido batare daya furta kalma ba, hakan ba ƙaramin Ƙona mata rai ba, Tsawa ta daka mashi kamar mahaukaciya Ta cakumi Gaban rigarshi.
“Nace ka faɗamin Ina kaje pravin? Saboda ka maidani shashasha ban da amfani awurinka shine zaka kama Hanya kabar office tun ƙarfe sha Biyu baka kirani awaya ka sanar dani ba, Kasa duk nabi na tashin hankalina akanka, ni na ɗaukama wani abunne ya same ka sai gashi ka dawomun lafiyarka qalou”
Ƴan hanjin cikinsa tuni sun soma kaɗawa, Abunka ga shu’umin namijin wanda yasan takan mace, runtse idonshi yai tare da kai hannu ya dafe gefen cikinsa.
Nan take Hankalinta yai matuƙar tashi la66anta na rawa take faɗin”pr...pravin? Lafiya? Meke damunka”
Da wata irin kasalalliyar murya ya furta”My stomach, bana jin daɗi ai tun Jiya na faɗa maki,” ya ƙarasa maganar yana faman cizon la66ansa, lokaci ɗaya fushin fuskarta ya sassauto, tsananin tausayin shine Ya kamata, ganin yana tangal tangal kamar zai faɗi yasa tayi saurin talla6e waist ɗinsa, da taimakon ta suka ƙarasa gaban Gado Ya hau Ya kanta Yana fuskantar ceilling, daga gefen gadon ta zauna daga gefenshi tana kallon shi
“Pravin am sorry nayi maka faɗa bansan baka da lafiya ba, kaine kaƙi Yi min magana, why pravin kasan baka da lafiya meyasa baka kira awaya ka sanar dani ba? Cikin kulawa take yi mashi magana, har ta manta da zancen tambayarshi Ina yaje.
Wahalallan Yawu ya haɗiya, Cikin mawuyacin Hali Ya furta”wayar bata a hannuna ne a mota nabarta, Ina Cikin Yin draving zan dawo gida, Ciwon ciki Ya takura min, draving dinma na gagara Yi, shine na wuce gidan abokina dake anan kusa, to acan bacci ya kwashe ni,
“Pravin why baka je asibitin Gida ba? ai da komai yazo maka da sauki, yanzu ka tashi ka shirya In kaika asibiti da kaina inyaso sai in dubaka acan”
Tana Ƙoƙarin miƙewa yai saurin fusgo hannunta, gaba ɗaya ta faɗa saman jikinsa, Ƙanƙame ta yai da hannayenshi biyu
Yana faman cizon le6e ya furta”rashin lafiyata bata asibiti bace, My wife kece kike damuna saboda rashin bani haƙƙina da bakya yi akai akai, shiyasa nake fama da ciwon cikin nan, ko da yaushe Aikinki ne agabanki, idan dare yai nayi maki magana kina danna laptop sai kice min In jira ki kammala daga nan har bacci ya ɗauke ni baki gama ba......”
Pravin Ya kashe mata Jiki da kalamansa, ta yarda da abunda ya faɗa mata saboda tasan bata kyauta mashi ta 6angaren nan mafi yawan time idan Ya matsa mata tana Yin aiki bata kula shi saita kammala.
“Am sorry dear, indai nice zan gyara, kayi haƙuri nayi kuskure but bazan ƙara Ba, tun da abun Yana affecting dinka”. Lumshe ido Yai, har cikin zuciyarshi ba ƙaramin daɗi Yaji ba, ganin yai nasara akanta.
“Yanzu ka faɗamin me kakeso? Za ka yi wanka in taimaka? Ko zaka fara Cin abinci ne”
Yana faman sakin nishi Ya furta”nafi buƙatar wankan, amma idan kin amince muyi atare”
Murmushi tasakar mashi”is Okey, shine kaɗai abunda kakeso”? Ɗaga mata Gira yai alamar eh, A hankali ta ɗaura yatsun hannayenta saman coat din jikinsa Ta cire mashi ita, kafin ta zame mashi belt din wandonsa, yunƙura yai tare da miƙewa ya sauko daga saman gadon Ya ƙarasa zame wandon ya rage daga shi sai short da singlet dinsa, Yaja hannunta suka nufi toilet, da gudu nabi bayansu sai dai kafin in ƙarasa Pravin Ya kulle ƙofa.
*EX-PRISONERS❤*
Idan muka koma 6angaren Prisoners, sai dai muce Alhamdulillah, tun bayan da Dr laura davis ta tattauna da Sojoji bata ƙara Ji daga gare su ba, An dai samu damar Kammala Yi masu injections ɗinsu kuma kullum sai sunsha magani na safe daban na rana daban na dare daban, injection ɗin duk mutun ɗaya uku suke Yi mashi arana, Likitoci sun ci kwakwa Wurin ma Matan allura, Musamman Azeeza da Jamimah, mugun tsoron Allura su ke ji, idan za’ayi masu sai an kira Angel ta ruƙesu, tukunna ake samun sauƙin yi masu allurar, Mazan dai da sauki basu tsoron Allura tamkar basu son ana tsira masu ita a jikinsu ba, cikin kwanaki huɗu da su ka Yi a Texas Rayuwarsu ta fara canzawa, saboda kyakkyawar kulawar da suke samu tarairayarsu ake Yi kamar new born babies, abinci sau uku ake basu, Breakfast, lunch and dinner, Lafiyayyan abinci mai gina jiki, sau ɗaya ake sanyasu yin wanka, su canza Kayan Jikin su, Su Angel an dage da yin sallah da addu’a, har tsakar dare tana tashi yin night prayers, yawanci addu’o’inta akan Danish ne, ta roƙi Allah da ya kare mata shi, idan farkawarshi Alkhairi ce Allah Yasa ya tashi cikin amince, idan kuma farkawarshi ba Alkhairi bace Allah yasa yaita sharar baccina har zuwa su koma Nigeria zaifi masu sauƙin su Yi control dinshi, duk da yanzu ta fara fargaban kada su zo Nigeria A nemi Ruwan zam zam arasa tabbas ba ƙaramar matsala za’a samu ba, damuwarta yanzu akan Sojojin ce shiru basu dawo ba, Kuma bata Ji daga bakin dr laura Ya ake ciki ba, Shin za’a maidasu ƙasarsu ne ko kuwa a’a, Ta dai zubawa sarautar Allah Ido 👀
Sam ta kasa runtsawa, tun wuraren ƙarfe tara na dare ta farka, saboda mugun bugun da ƙirjinta ke yi mata, tabbas tana ji aranta wani abun ne ke shirin faruwa.
Miƙewa Tayi zaune saman gadonta, ta jingina Bayanta Jikin pillow, idanuwanta suna a lumshe, sanyin A.c sai ratsa fatar jikinta Yake yi wata irin kasala take Ji da matsanancin faɗuwae gaba.
“Masoyiya Angel, Lafiya kika farka daga bacci? Na lura kamar wani abu ke damunki”
Muryar Nurse Jessica ce ta fargar da ita, har saida ta ɗan zabura don bata yi tsammanin jin Muryar mutun a kusa da ita ba.
Slowly ta wurga eye balls ɗinta akan fuskar nurse ɗin, tana daga zaune saman chair ta kusa da gadonta, hannunta ruƙe da wayarta, fara ce sol, uniform ɗin jikinta light blue ne kalar nasu, ta ɗaure jar sumar kanta da ribbom.
Nauyayyar ajiyar zuciya Angel ta sauke tare da cewa”sister, nagode da kulawarki agareni, nakasa runtsawane saboda inason ganin yan uwana ko zaki Iya taimaka min”?
Smiling gently nurse jessica tace”Na lura kina son ƴan uwan nan naki, cos tun ranar dana fara kula da ke, sau uku kike zuwa room ɗinsu Kina duba su, faɗamin ko dai akwai damuwane? Ko tsoro kike ji kada mu sace maki su”? Da zolaya nurce jessica tayi mata maganar
Cikin jin kunya Angel takama ƴan kame kame tana faɗin”am.... Ba haka bane just inason su sosai, mun shaƙu da juna, shiyasa bana samun natsuwa idan ban gansu akai akai ba”
Nurse jessice tace”Kuna burgeni sosai, inaso Inga ƴan uwan masu son junansu, masu haɗin kai, ta hakanne ake cin ribar zaman duniya, idan har kana da ɗan uwa mai share maka hawayenka, mai nuna maka ƙauna wanda baya gajiya dakai tabbas ka gode ma Allah, zai yi wuya ka rasa madafa a duniyar nan, babu wanda zai yi gigin cutar dakai muddin kuna da haɗin kai a tsakaninku, amma idan Ya kasance kuna ƴan uwa baku da haɗin kai, danasani zai biyo baya cos dayawa rashin kulawa keja har damuwa tayi ma ɗan uwanka Illa, ya akaita abunda zakuyi danasani gaba dayanku”
Angel ta natsu Tana sauraron Kalaman Nurse Jessica, Haƙika kalamanta sun ta6a mata zuciya, sai taji ta ƙara ƙaunar ƴan uwanta, ta ɗanyi mamakin yarda nurse ɗin take sakar mata fuska suke Yin fira, saboda ta ta6a Jin ana faɗin turawa sun tsani baƙar fata suna nuna masu wariyar launin fata, sai dai tayi tunanin ba duka aka taru aka zama ɗaya ba, sannan kuma su basu da banbanci dasu, hasken fata, launin ido da kuma sumar kai, shiyasa suka zama ɗaya.
“Ki tashi muje in raka Ki ɗakunan ƴan uwan naki, Nima Inason ganin su, musamman twins ɗin nan” murmushine Ya bayyana akan fuskar Angel jin abunda nurse ɗin tace, tuntuni ta faɗa mata, ba twins bane Jamimah da azeeza ɗaya ta girma ɗaya amma taƙi yarda, ba ita kaɗai ba hatta sauran nurses ɗin da likitocin kallon twins suke Yi masu acewarsu Basu da banbanci, Komai nasu kala ɗaya.
da zumuɗi Angel ta sauko daga saman gadon, light blue uniform ɗinta ne a jikinta, sai da ta fara zuwa gaban closet ɗin ɗakin ta buɗe ta ɗauko Hijabin da aka bata Nayin sallah ta zura a jikinta.
Hannunsu ruƙe cikin na juna ita da nurse ɗin suka fito daga ɗakin, hasken electric bulbs Ya haskaka Asibitin tamar da rana, a tsanake suke Yin tafiya suna tattaunawa a tsakaninsu, ɗakin Gabriel suka Fara shiga, tayi mamakin ganinshi idon shi biyu Shida nurse rebecca, ta kunna masu kallo sun natsu abunsu.
Jin motsin shigowar Mutun yasa suka kai eyes dinsu ga ƙofar, murmushi ne ya bayyana akan faces dinsu
Mayar masu da martanin murmushin nasu Angel tayi”ɗan uwana, Baka Yi bacci ba? Fadamin meya hana ka Yin bacci”!
Kafin Ya bata amsa nurse rebecca tace”Ni na hana shi, Ko bakisan mun fara soyayya bane, Gabriel baka faɗa mata ba”? Gaba daya suka sanya dariya, jessica tace”har kinyi kamu kenan” ɗaga mata gira tayi”yap, taya zan bari damar nan ta wuce ni”? Firarsu ba ƙaramin nishaɗi take sanyasu ba, Angel tuni ta haye saman gadon gabriel, Ruƙo hannunshi tayi acikin nata,
“My sister, meya hana Ki yin bacci”? Ƙasa ƙasa da murya ta furta”Danish, Hankalina Yaƙi kwanciya da rashin farkawarshi, Yaufa kusan One week kenan a lissafina, Gabriel bansan ya zanyi ba, Ni nafi so Mu koma nigeria....”katse mata maganar yai da cewa”ai kin faɗamin dr laura tace zata taimaka mana mu koma can ko?
Ɗaga mashi kai Tayi”eh, amma har yau shiru, banji daga gareta ba, Kuma kaga sojojin basu ƙara dawowa ba”
Ganin kamar duk ta damu yasa shi kwantar mata da hankali”Wani jinkirin alkhairi ne Angel, wata’ƙil ki ga gobe anzo mana da kyakkyawan labari, don haka Mu ƙara haƙuri kada mu damu kanmu komai zai tafi dai dai My lovely sister” Yai magabar Tare da jan kumatunta da hannunshi, Hakan ba ƙaramin dariya Ya bata ba.
“Masoyiya Angel, zamu Iya tafiya “? Muryar nurse Jessica ce ta katse masu tattaunawar tasu.
Peck tayi mashi saman cheek dinsa”ka kwanta ka huta,” ta ambaci hakan tare da saukowa daga saman gadonshi ta nufi nurse jessice taja hannunta suke fuce bayan sunyi masu sallama.
Room ɗin Batul suka shiga, A kwance suka same ta saman gado, ta ƙudundune da bargo, da alama tayi zurfi abaccinta, Basu shiga ɗakin ba suka wuce ɗakin Jemimah, Itama baccin take Yi, ta wawware ƙafafuwanta ta saki baki da hanci, nurse din dake kula da ita, Tana acikin ɗakin har gaisawa sukayi da ita kafin suka nufi ɗakin Azeeza, Kamar yarda suka samu jemimah haka suka sameta a kwance bacci yai daɗi, murmushi Angel tasaki kafin suka ƙara gaba zuwa ɗakin Parveen, Hallau dai mai hali Baya ta6a canzawa, bata Yi mamakin ganinta a zaune gefen gado ta tasa abinci saici take Yi, An kunna mata tv tana kallon mbc channel Suna Yin cartoon tom and jerry, Sai tiƙar dariya take Yi kamar zata kifa kanta saman table din gaban gadon, babu alamun bacci a idonta, sam bata ji motsin shigowarsu ba, plate ɗaya ne agabanta shaƙe da chicken wings, gefen plate ɗin kuma Apple juice ne, Duniya Ta yi mata daɗi, Gyaran muryar da Angel Tayi mata ne yai silar Jawo Hankalinta ga dubansu, bakinta cunkushe da nama ta furta “Angel”
Nurse ɗin da suka zo atare da ita sai murmushi take saki, Da alama parveen ta burgeta, ba tun Yau ba, duk in tazo dubata sai ta sameta tana Cin abinci, da wuya ka same ta bakinta babu abun taunawa.
Farin Cikine Ya bayyana akan fuskarta, Da sauri ta ƙarasa suka rungume juna ita da Angel.
Shafa sumar kanta Tayi”Parveen kowa Yai bacci banda ke, kina nan kinata cin abinci Ko gajiya bakya yi, so kike ki karya masu jari ko”? Da zolaya tayi maganar, bayan ta raba jikinta daga na Angel, Just 4days Har kumatu ta ƙara.
“Ai nurse ɗinne Yace min duk in ina buƙatar wani abu Inyi mashi magana...” zaro ido Angel Tayi hada ruƙe ha6a tace”Eyehh! Wato saboda yace maki haka shine kuma ko da wani lokaci sai kince mashi zaki ci abinci, Angaya maki nan Restaurant ne? You’re a patient bai kamata aga kina cunkushe cunkushen abinci, kamar me fama da cutar Yunwa” sam Sun manta da nurse din da ke abayansu, Da turancin Angel Keyin maganar, hakan Yasa ta fahimtaci abunda suke tattaunawa, sai faman sakin murmushi take Yi tana binsu da kallo.
“Angel ai su ba ruwansu, komai mutun yake so suna yi mashi, baki ga yarda nurse din Ya ke ji dani ba, Shine ma Ya kunna mun abun nan ba ƙaramin Daɗi naji ba” ta yi magana tana nuna mata plasma tv
Watsa Hannu Angel Tayi”Okey, Koma Ki cigaba da cin abincinki, pls Ki samu ki kwanta ki huta, ki kula mun da kanki” murmushi parveen ta sakar mata
“Thank u sis, Allah yabar mana Angel ɗinmu” Nurse jessica ta tsaresu da ido, gwanin ban sha’awa take kallon su
Sallama sukayi Ma parveen bayan sun fito daga ɗakin suka nufi ɗakin Hannah, Yarinya ƴar madara, hankalinta kwance take sharar baccinta, Rabin jikinta duvet ne.
Bayan sun ƙara gaba ɗakin Naufal su ka shiga da ɗakin Javed, Kowan nan su bacci Yake Yi, daga ɗakin Javed suka nufi ɗakin Haris, Bawan Allah ba laifi Jiki Yai kyau, yana samun kulawa fiye da sauran ƴan uwanshi saboda lalurar shi.
Sunyi tunanin bacci yake yi ganin shi kwance ya rufe idanuwanshi, Har sun Juya zasu fuce muryar shi ta katse masu hanzarinsu
“Angel!” Atare suka Juyo suna kallonshi, Ya buɗe idanuwanshi da suke a lumshe, farin Cikine Ya lullu6e Angel, da sauri ta nufi gadon shi daga gefe ta haye, taimaka mashi tayi ya mike zaune, ta rungume shi a chest ɗinta, hannunta asaman bayanshi tana shafashi
“Haris ɗina Ya jiki naka da sauƙi ko”? Muryar shi, ƙasa ƙasa Ya masa mata”da sauƙi Angel, bana jin ciwo a jikina sai dai har yanzu ina yin mafarki akan Deejana, ina ganinta a prison suna azabtarmin da ita, tana kuka tana roƙona akan in taimaki rayuwarta’ cikin rauni na murya yai maganar
“Ka kwantar da hankalinka haris, Mafarki ba gaskiya bane, sau dayawa mafarki Shaidanne yake assasa shi, wani daga Allah ne wani mafarkin kuma ya danganta daga Yarda ka ƙwallafa abu aranka, shiyasa nace ka dage da yin addu’a, in sha Allah haris in dai Deeja tana araye zaku haɗu ne,”
Nurse ɗin ta zuba masu ido tana kallon su, bata san me suke tattaunawa ba a tsakaninsu, saboda sunyi amfani da harshen hausa.
Still Haris bai ɗago kanshi daga saman chest ɗinta ba ji yake kamar deejanshi ce
“Wlh Angel inason deejana, Kuma inayi mata addu’a, Ko yanzu da kika sameni na rufe idanuwana, addu’a nakeyi mata, Ni bazan ta6a gajiya dayima deeja addu’a ba, Har nunfashina na ƙarshe”
Tuni idanuwan Angel sun cicciko tab da ƙwalla, (Ƙaunar dake a tsakanin haris da Deeja, daga Allah ne, irin son da ake kira true love, Inason ka kana so na badan wani abu ba❤ Allah Ya bamu masu sonmu tsakani da Allah🙏)
Shafa sumar kanshi Angel Ta yi da hannunta, Jin shessheƙar kukan shi Ba ƙaramin Karya mata zuciya yai ba
“Haris pls don’t cry, kasan bana son jin kukan ka, ko ba danni ba, nurse da ke kula dakai bazata Ji daɗi ba, Suna iyakar bakin ƙoƙarinsu wurin ganin sun sanyaka farin ciki duk don ka rabu da ciwon zuciyar dake damunka” a hankali ya ɗago da kanshi Idanuwanshi sun ɗan kumbura.
“Angel, nadaina bazan ƙara ba” tafin hannunta ta ɗaura saman fuskarshi tana share mashi hawayenshi
“Zan tafi Yanzu nurse tana Jirana, Amma kafin nan kayi min murmushi mana” daƙyar ya ƙaƙaro