Author : Boss Bature Category : Complete Novels
ubaid yayi rejecting call din, yana mai mamakin Halin Alhaji musa.
“Me ku ka tattauna ne”? Layla ce ta jefa mashi tambaya
Muryarshi a raunace ya furta”yace bazai samu damar zuwa nan ba, shine ma ya hana shureim zuwa saboda yafi son muje can gidan shi”
Ta6e baki hajiya layla tayi”shine kai kuma sai ka ce mashi zamu samu lokaci muje can din ko?
Jinjina mata kai yai alamar eh, masifa ta soma zazzaga mashi”kasan Allah babu inda zamuje sai dai kai daya gama asirce ka kama hanya ka tafi,Ni ban ta6a ganin mutun mara kunya irin shi ba, yarinyar ta 6ace tsawon shakaru sai jiya tsakar dare ƙarfe shabiyu tadawo bata ahayyacinta shine zaice mu kwasa mu tafi gidansa saboda muke son yaganta? Kwata kwata bashi da tunani kuma baida hankali, kaida kakeyi mashi biyayya gayanan shi bai damu da ƴarka ba,
...” tun da tafara faɗa, jikin benazir yai sanyi duk sai taji ba daɗi, Cikin sanyin murya tace”mommy dan Allah ki yi haƙuri, kada hakan ya dame ki, Ni banga laifin shi ba saboda ai ni na gudu da kaina ba korata akayi ba, wata’kil Yana jin haushin abunda na aikata shiyasa yace muje can....”
Katseta hajiya layla tayi”benazir ba abunda kike tunani bane, mutumin nan baya ƙaunarki, saboda bai damu dake ba, tun lokacin da kika 6ace bai ta6a magana akanki ba, Mune kaɗai muka damu dake munyi nemanki har mungaji mun fidda rai da kina araye, amma musa bai ta6a sanya baki akan maganar 6atanki balle har ya taimaka wurin bada gudummuwar mu nemo ki.....” Muryar Alhaji ubaid ce ta katse mata maganarta”kidaina faɗa mata wannan maganar, bai dace ba, taya zakice kawunta ƙanin mahaifinta bai sonta? Akan wani dalili? Shiya furta maki da bakin shi”
Harara layla ta watsa mashi”alama nagani shiyasa nace haka”
Idanuwan benazir ne suka cicciko tab da ƙwalla, cikin sanyin murya tace”Ni ban damu ba, koda ace baya sona, tun da Iyayena suna sona Alhamdulillah, soyayyarku kaɗai ta ishe ni sai kuma ta mijina da ƴata, da kuma Yayana, sannan Ni na amince zanje abujan bawai don saboda shi ba, saboda inason ganin Aneelerh”
Girgiza kai layla tayi”bafa zan ta6a bari ki je gidan mutumin nan ba, Saboda Ni ban yarda da shi ba, Idan kuma kika takura akan kinason zuwan bazan hanaki ba sai dai ki sani bazan biku ba” babu alamun wasa akan fuskarta tayi maganar.
Magiya benazir ta dinga yi mata akan ta amince suje da ita, don ita batason suyi nesa da juna, daƙyar layla ta amince zata bisu abujan, da wata manufa a ƙasan zuciyarta don taci alwashin idan sukaje gidan Alhaji musa saita fada mashi baƙaƙen maganganun da zasu hana shi sukuni, yanzu dai sun tsaida magana zuwa jibi zasu yi tafiyar.
Aranar shureim ya samu damar kiran Alhaji ubaid ya fada mashi uzirin daya hana shi ɗaga kiran shi, bayan sun gama magana, har benazir yace abata waya su gaisa, sun jima suna waya da ita kusan awanni suka kwashe, kafin daga bisani yayi masu sallama.
Idan muka koma 6angaren zahra tun bayan da ta koma gida, babu mutunci a tsakaninta da Aneelerh ko gaisuwar arziki bata haɗa su, ta canza mata bata sakar mata fuska ba kamar yarda suke ada ba, aranar mahboob yai mata maganar motar ta da wayarta yace dama jingina yabada su, idan tana so zata bada kuɗin adawo mata dasu, farin ciki kamar zata zuba ruwa ƙasa tasha dama bada Son ranta ta bada su ba, ta haɗa mashi kudin ta bashi, a daren ranar ya dawo mata da su, tuni ta fara amfani da wayarta bayan ta mayar da sim dinta.
A washe garin ranar laraba suka fara shirye shiryen fara aiki a Obie estate tare da sauran Interior designers dake aiki a ƙarƙashin company dinsu, tuni kaya sun iso daga dubai, Hankalin zahra ya kwanta bata da sauran damuwa yanzu, ta ƙagara gobe tayi don suje su fara gudanar da aikinsu saboda gagarumin taro ne zasuyi idan obie zai yi birthday kamar shagalin biki saboda dukiyar da suke kashewa wurin ƙawata gidan, shiyasa zasu fara yi masu aiki tun alhamis kafin Juma’a da za’a gudanar da shagalin
❤🤍❤🤍❤🤍❤🤍❤🤍❤🤍❤
❤ANEELERH❤
A zaune take saman mirror chair, bata jima da fitowa daga wanka ba, ta zauna ne domin gyara jikinta, ƴar rigar wanka ce a jikinta, ta kasa ta6uka komai hannunta na a ruƙe da wayarta layin hajiya adama take dannawa kira, phone din na fara ringing taji sanyi ya ratsa zuciyarta, bayan hajiya adama tai picking call din Aneelerh ta yi mata sallama, on the other hand muryar Hajiya adama ta bayyana da alamun kasalar bacci”wa’alaikum salam daugher in-low, ya ki ke ya gidan yasu mami da ummi”
Da fara akan fuskar Aneelerh tace”Lafiya lou mommy, yasu daddy fatan duk kuna lafiya”
“Alhamdulillah Aneelerh, halan kin ji ni shiru yau ban neme ki ba shiyasa kika kira”
Cikin jin kunyar maganarta Aneelerh tace”haka ne dama nakira ne don mu gaisa” da zolaya Hajiya adama tace”kodai kin kira ne don ki faɗa min jibi zaki zo ɗaukar baby junaid tun da time ya cika”
Ƙumshe dariya Aneelerh tayi kamar tana agabanta sai faman noƙe kai take yi, jin tayi shiru yasa Hajiya adama cewa”dama nasan ba zaki faɗamin ba, to ki kwantar da hankalinki, in sha Allah friday zanzo dashi gidan naku”
Abeelerh taji dadin maganarta”nagode mommy, Allah yakaimu lafiya.
“Nima ngde ki kulamin da kanki, ki kuma gaishe min da su mami, junaid din bacci yake yi zuwa anjima idan ya farka zan kira ki video call ku gaisa, dama yanata sambatu yana ambon shi wurin mommy zaije”
Murmushi Aneelerh tadan saki kamar tana agabanta”zasuji nima agaishe da daddy, “ daga nan suka yi sallama da juna.
❤A washe garin ranar Alhamis❤
Wuraren sallar Asuba Unaisah tana zaune saman darduma ta zumbula hijabi, Batul tana akwance agefenta saman dardumar, tun jiya da suka fara sallah da zarar sun gama sai ta kwanta wahala take ji idan tana yin sallah hada ƙarin rashin sabo har ƙwara ita akan su azeeza masu yin kalle kalle in suna yin sallah, mazan cikinsu sunfi natsuwa shi kanshi Boss man yayi mamakin yadda suka Iya sallah da karatunta ya ƙara jinjinama Unaisah akan ƙoƙarinta, yanzu karatun addinine zasu ƙara koya masu dana boko kafin asanyasu makaranta bayan kammala bincike akansu.
Tafin hannayenta biyu ta ɗaga sama tanayin addu’a muryarta abuɗe take fadin
“Ya Allah ka jiƙan ƴan uwanmu da suka rigamu gidan gaskiya, Ya Allah kakai rahama ƙabarinsu, Ya Allah kabamu ikon cinye jarabawarka, Ya Allah ka bamu haƙuri da juriyar rungumar duk wata ƙaddara da zata riske mu mai kyau ko mara kyau, Ya Allah ka tsare min sauran ƴan uwana da nake atare dasu da sauran al’ummar musulmai, ya Allah ka bamu nasara akan burinmu da muke son cimmawa na ganin mun kawo ƙarshen azzaluman mutanan da suka ƙasƙantar da rayuwarmu suka cutar damu Allah kada ka basu nasarar cigaba da aiwatar da zalunci..........” cikin shessheƙar kuka ta ƙare maganar, hawaye tuni sun wanke fuskarta tunawa da rayuwar sauran ƴan uwansu ƙananun yara da ake cutarwa a cikin kurkukun ƙaddara, tasan ba zasu fasa cin zarafinsu ba suna lalata rayuwarsu kamar yadda su ka yi silar mutuwar ƴar uwar su Unaiza ƴar gidan daddy da Majnoon yaran da ba suji ba basu gani ba.
Sautin kukan Unaisah ya karaɗe cikin ɗakin, batul ko motsi batayi ba, tunda ta kifa kanta saman darduma bacci mai dadine yai awon gaba da ita ko addu’a bata samu damar yi ba.
“Bazan ta6a mantawa da wasiƙar da kika bani ba, kuma bazan manta sunan mugun mahaifinki ba, In sha Allah zan ɗaukar maki fansa koda kuwa zan jefa rayuwata ne cikin haɗarin da zaiyi silar mutuwata ne.....” cikin karyayyar murya take furta kalaman masu ta6a zuciya, idanuwanta sun kaɗa sunyi jawur, hawaye sun kwanta saman fatar fuskarta har zuwa gaban hijabin dake a jikinta.
“Ya Allah ka bayyana min daddyna idan yana araye, Inason nasake ganinshi shi kaɗaine nake da burin haɗuwa dashi a duniyar nan”
Tunda ta fara karanta addu’o’i, yana la6e bakin ƙofar dakinsu Yana sauraronta, basu jima da dawowa daga sallar asuba ba, ya rakosu Sajeed ne tuni sun nufi bedroom dinsu.
Zuciyarshi ta karaya da jin kalamanta, abubuwa dayawa sun so su rikitar dashi, kamar yarda take zubar hawaye haka shima yake zubar da su saman fuskarshi, farar jallabiyace a jikin shi ya sanya mask akan fuskarshi, Ji yake kamar ya faɗa ɗakin Ya rungumota a jikinshi, duk a tunaninshi Unaisah ta manta dashi ashe ba haka bane yana aranta har addu’a tana yi mashi, haƙiƙa yayi farin ciki mara misaltuwa, cikin sanɗa Ya juya zaibar ƙofar ɗakinsu kwatsam muryar Jemimah ta tona mashi asiri da ƙarfi ta furta”BOSS MAN!!!” cak Ya dakata da tafiya, hatta Unaisah dake a ɗaki saida taji sautin sunanshi da jemaimah ta ambata, aiko da sauri ta miƙe ta nufi kofar fitowa daga ɗakin.
A hankali Ya waiwaya baya yana duban jemimah, tasha dogon hijabi ajikinta kamar zatayi tuntube da gudu ta nufo shi, Azeeza ma ta fito tabiyo bayanta itama hijabin ne a jikinta.
Kallon da yake binsu dashi tamkar kallon da uba yake yiwa ƴa’ƴanshi ne, saboda yana matuƙar ƙaunar yaran ya dauke su kamar jininsa, musamman yadda suka fara nuna mashi yarda, Jiya izuwa yau sun saki jiki dashi, duk in zai gifta sai sun ambaci sunanshi kamar su suka raɗa mashi.
Jemimah na ƙarasowa ya sanya hannu biyu ya ɗagata sama, ta kama tiƙar dariya tana fadin”dan Allah kada ka sauke ni ƙasa”
Fuskarshi dauke da murmushi yace”raini ya fara shiga tsakanina dake ko? Tun jiya badama kiga na gifta sai kin ƙwala min kira kamar wani tsaran wasanki, bakisan ni baba ba ne”?
Tace”to aini daɗin sunan nake ji, Boss man shiyasa nake kira,” tana magana yana kallon jajayen kumatunta bakomai yake tunawa ba face Angel ɗinsa, lokacin ƙuruciyarta yaci wuyarta yakuma ji dadin shiriritarta.
“Jemimah Ina fata yau kinyi sallah ta hankali, don jiya Azeeza ta faɗa min abun kunyar da kika yi” ya faɗa yana sauketa ƙasa, duban Azeeza yai har ya miƙa hannu zai ɗauke ta ganin ta tsare shi da ido yayi tunani ko itama so takeyi ya daga ta sama, da sauri ta maƙe mashi kafaɗa tana fadin”ai ni ba ƙarama bace, Na girmeta da shekaru” dariyace ta kubce ma Boss man.
“Oh saboda kin girmeta shine bakyaso in ɗauke ki? To aini a wurina jinjira nake kallonki” ya faɗa tare da ɗaukarta ya ruƙeta a hannunshi, Kunyar duniya ta cika Azeeza sai faman noƙe mashi kai take Yi.
“Kasan Allah Boss man itama Azeeza bata Iya sallaba, ko karatun sallah ma bata iyaba, idan nayi ƙarya kace ta maimaita maka Rabbighfir li” tuntsirewa yai da dariya.
Ran Azeeza ya 6aci tace”wallahi ƙarya take yi min, ai acikin zuciya nake yin karatun sallah tayaya har tasan abunda nake faɗi acikin zuciyata” gwalo jemimah tayi mata”oho dai, ni dai duk rashin Iya sallana nasan yadda ake karatun sallah”
Idanuwan Azeeza tuni sun cicciko da ƙwalla, boss man yace”badai kuka zakiyi min ba”? Cikin shessheƙar kuka tace”wallahi ƙarya take yi min na iya karatun sallah, kaji na rantse maka, idan ma kanaso sai in faɗa maka kaji, itace fa bata Iya komai ba, jiya muna sallar isha’i tana buga min dundu abayana, kuma ban rama ba”
Kwantar da kanta yai saman kafaɗar shi haɗi da daura hannun shi saman kanta Yana lallashinta.
Idanuwanshi akan jemimah dake ta dariya, dama tun jiya da yayi tozali da fuskarta ranshi ya bashi daƙyar in bata iya rashin ji ba, kamar dai Angel dinsa da tana ƙarama .
Lallashinta yai”yi hakuri my daughter, kuruciya ke damunta dama kince min kin girmeta don haka inaso ki ruƙe girmanki kada ki biye mata, idan tayi ba dai dai ba kiyi mata nasiha a matsayinki na babba mai hankali da tunani, in sha Allah wata rana zata daina ne” tunda ya fara magana Azeeza take amsa mashi da toh, jemimah kuwa sai faman ta6e mashi baki take yi hada ruƙe qugu, tana fadin”tab ita ɗin zata min nasiha, Allah ya kiyaye, ai ni bana jin maganar kowa idan bata Unaisa ba”
Mamaki jemimah take bashi gata ƴar ƙarama idan tana magana sai kayi tsammanin ta ɗare shekarunta.
Sauke Azeeza yai saman floor, yace da ita”ki ruke hannun ƴar uwarki ku tafi ɗaki, da anjima idan nashigo zamuyi magana” ta amsa mashi da toh nagode, kafin ta ruƙo hannun jemimah tuni ta watsa da gudu ta nufi hanyar komawa ɗakinsu duk don kada azeeza ta ruƙe hannunta.
Murmushi ya saki yayin da yake bin bayansu da kallo, Har ya ɗaga ƙafa zai nufi hanyar fita ɗakin, Muryar Unaisah ta dakatar dashi”Boss” A hankali ya juya baya yana dubanta tun ɗazu tana tsaye tana kallon su, sai da ta bari su Azeeza sun tafi tukunna ta yanke shawarar yi mashi magana.
Ta wanke hawayen fuskarta, tana tafiya hijabinta na ja da ƙasa, har gabanshi ta ƙarasa ta tsaya, tsananin tausayinta ne Ya kamashi, ji yake kamar ya rungumeta koya rage radadin da yake ji acikin zuciyarshi, sai dai ba halin yin hakan yasan yadda take da masifa idan Ya kuskura yai hugging dinta tsaf zata mare shi tunda batasan wanene shi ba.
Ido cikin ido suke kallon juna, tsawon mintuna kafin ta numfasa tace”ina kwana? Ka tashi lafiya? ya fama da mu”
Cikin sanyin murya yace”lafiyalou Unaisah, ya akai naga idanuwanki sun canza launi, ko baki da lafiya ne”?
Girgiza mashi kai tai, cikin disasshiyar murya ta furta”lafiyata qalou, kasalar bacci ce,”
Jinjina kanshi ya ɗanyi, ji take kamar tace mashi ya cire face mask dinshi sai dai bata son ta takura mashi don ta fuskanci bayason su san wanene shi.
“Kin tsare ni da ido kina kallona ko akwai wani abu da kike son fada min ne”?
Murmushin gefen fuska ta saki, Har dimples dinta suka lotsa,
“Dan Allah taimako nakeso kayi min sai dai bani da ko sisi a hannuna”
“Kada kiji komai ki faɗi koma menene zanyi maki shi in sha Allah”
Tana faman noƙe kai tace”um dama waya ce da Aunty laura ta bani kyauta ɗaya daga cikin likitocin da suka kula da lafiyarmu a america, to wayar babu sim aciki gashi inason in fara amfani da ita”
ta faɗa tana duban fuskarshi, ya natsu yana sauraronta idan tana magana kuruciyarta yake tunawa, yarinyar data sanya shi ciwon kai da zazza6i, cikin ikon Allah yanzu ta ƙara girma ta zama kamilar mace ta mallakin hankalinta.
“Sim kaɗai kike buƙata”? Girgiza mashi kai tayi”a’a, da Allah kada kace na takura maka, “ aranshi ya ayyana takura kuma ta nawa My Angel, nida nayi jinya gadon asibiti saboda ke”
“Cikin Kayan da aka tsunto mu da su a daji, akwai backpack ɗina inason jakar, gadonmu ce bansani ba ko sojoji sun haɗo mana da su” ta tambaya tana dubanshi.
“Duk wani abu naku yana atare damu, saboda muna buƙatar abubuwan da zasu taimaka mana wurin yin bincike tamkar shaidune agare mu, amma kada ki damu zan ɗauko maki backpack din, da anjima zan shigo maki da ita tare da sim din da zaki sama wayar” wani irin farin cikine Ya lullu6e Unaisah, godiya tadinga yi mashi, yace mata yaji daɗin ganin farin cikinta, juyawa tayi da niyar ta koma ɗaki, hijab din jikinta dake jan ƙasa ta harɗe ƙasan takalmin ƙafarta, gaba ɗaya ta tafi zata kife kasa da zafin nama Boss man Ya ruƙo damtse hannunta Ya janyota ta faɗa saman kirjinsa, har saida taji gabanta ya fadi, ƙanƙameta yayi da hannayensa biyu daya zagayo dasu ta bayanta, Jikinta yai wani irin sanyi kamar wadda aka zare ma laka, bawan Allah tunda ya rungumeta yai tighting dinta kamar karya saketa, ita kanta takasa raba jikinta daga nashi, saima hannayenta data zagayo dasu saman bayanshi, ta ƙankameshi, Jini ɗaya ba wasa ba, sai faman sauke ajiyar zuciya suke yi at same time, batasan ya akai ba ta tsinci kanta da jin hawaye sun cicciko idonta, shi kuwa tuni sun wanke face mask dinshi.A hankali yake ɗan bubbuga bayanta kamar yana lallashinta, tsawon shekaru rabon daya ji ɗumin jikinta anashi, bazai ta6a manta ƙaddarar data afka masu ba, wadda tayi silar rabuwarsu, bazai ta6a manta sautin shesshekar kukanta da muryarta a lokacin da yake gudu dasu cikin mota tana daddy hancina jini, haka zalika bazai ta6a manta lokacin da ya jefar da ita cikin ruwa ba duk don ya ceci rayuwarta Sai gashi cikin ikon Allah ta rayu Allah ya tsare mashi ita, Allah kaɗai yasan irin wahalhalun rayuwan data fuskanta da ƙananun shekarunta.....
Kamar yadda yake tariyo rayuwarsu haka itama take tunano daddynta, ji take kamar shine ya rungumeta, shiyasa ta ƙara narke mashi tayi lamo saman wide chest dinshi......
Gaba ɗayansu sun shiga yanayi mara misaltuwa, ba zato ba tsammani Boss Man yaji dirar wani abu saman bayanshi, da sauri ya ɗago da kanshi idanuwan shi sun canza launi sun kada jawur kamar mai fama da ciwon ido, yayi mamakin ganin pillow da aka jefo mashi ya fadi ƙasa, da sauri ya ɗaga ido sama don ganin wanene ya wurgo mashi pillow saman bayanshi, karaf idanuwan shi suka sauka akan Danish dake tsaye can second floor, hannun shi ruƙe da wani pillown Yana niyar ƙara jeho mashi, fitowar shi kenan daga ɗaki idanuwanshi suka hango mashi Angel ɗinsa rungume da wani ƙato, shine fa yaje ɗaki ya ɗauko fululluka har biyu Ya jeho mashi ɗaya.
Ya haɗe fuska babu annuri, kayan bacci ne ajikinshi riga da wando launin pink sunyi bala’en yi mashi kyau.
Harara ya watsa ma boss man, ganin Angel taki barin ƙirjin mutumin yasa shi ƙara daddagewa ya wurgo mata pillow, da sauri boss man Ya tarbe pillown a hannun shi, Lamarin ya ɗaure mashi kai, sai yanzu ya gane dalilin dayasa yaron yaƙi sakar mashi fuska tun jiya yake daure mashi fuska, ashe kishi ne