Author : Boss Bature Category : Complete Novels
murmushi kan fuskarshi, Hakanan taji gabanta Ya faɗi ƙura ido tayi akan face dinshi kamar tana son gano wani abu sai dai ta kasa gane menene shi.
Ganin yadda take kallonshi yasa yace mata Lafiya Angel’? Girgiza mashi kai Tayi bakomai, ka kula mun dakanka, Sai Allah Yakaimu” daga haka ta sauko daga sama gadon, suka fice daga ɗakin shi ita da nurse jessica.
Last room da suka Nufa ɗakin Garkuwa, tunkafin su ƙarasa take Jin faɗuwar gabanta na ƙaruwa, ji take yi kamar idan ta shiga ɗakin wani abu zai faru, Da bismillah abakinta ta kutsa kai dakin nurse jessica tabi Bayanta, kamar matacce haka suka same shi kamar kullum Sai sharar baccin shi Ya ke yi, Lamarin Danish ba ƙaramin ɗaurewa likitoci kai Yai ba, tsawon kwanaki mutun Yana yin bacci yaƙi tashi? Tun abun na damunsu har sun haƙura sun zubawa sarautar Allah ido.
Saman chair nurse ta zauna idonta akan face din Danish
A hankali Angel ta zauna gefenshi Tana ƙare mashi kallo, Ji take yi tamkar ta fasa ihu acikin kunnuwanshi wata’ƙil idan Yaji zai farka, sai da tasan ko Tayi abanza, Allah shine shaidarta, ta matsu a ƙagare take da son farkawarshi kamar ta yi hauka
Sam ta manta da nurse dake a ɗakin, ta natsu tana kallon shi kamar zata Haɗiye shi, A hankali Ta ɗaura small pink lips ɗinta farar fatar cheek dinsa ta manna ma kiss.
Murmushin gefen fuska nurse jessy ta dan saki, abun ba ƙaramin ƙayatar da ita yai ba, kamar ta samu tv haka take kallonsu.
A hankali Angel ta kwantar da kanta saman faffaɗan chest dinshi ta kasa kunne tana sauraran heart beat dinsa
Muryarta cikin raɗa take Yin magana”My man pls wake up, nayi kewarka kamar zan zauce, dan Allah ka taimaki rayuwana ka farka danish, a matse nake duk na takura da rashinka, pls idan kana Jina Ka amsa min” hauka ta soma yi mashi asaman jikinsa tabi duk ta hayeshi, shessheƙar kuka tadinga yi mashi duk don ya farka sam babu hawaye akan face dinta, ɗagowa tayi da kanta, gray eyes dinta akan fine face nasa, eyes lashes dinsa ta ƙurawa ido masu kyau da tsari.
Bakomai take tunawa ba face Farkon haɗuwarsu a prison, a karo na farko da Ta yi tozali dashi saida gabanta Ya faɗi saboda zazzafan Kyanshi, Murmushi tasaki tunawa da maganar farko data fara haɗasu lokacin da tana zazzaga masu masifa akan afaɗa mata ubanwa ya kawota prison
Muryarshi ta ratsa kunnanta, tamkar ana busa sarewa
“Bansan wacece ke ba, amma na lura kamar kina son wuce gona da iri, yakamata ki kiyaye harshen ki, wannan tsohuwar da ki ke gani tamkar uwa take agare mu, tun da mu ke da ita bata ta6a cutar damu ba, muna samun kyakkyawar kulawa daga gare ta, don haka bazamu bari zuwan ki ya zama silar tarwatsewar farin cikin mu ba hope u understand me!” a lokacin takai maƙura A zafafe Ta juyo ta kalle shi tsabar mamaki tamkar ba daga bakinshi maganar ta fito ba, duk da bugun da zuciyarta tayi mata na ganin kyanshi hakan bai hanata zazzaga mashi masifa ba.
“Sannu isasshen me walkin sa! Kai kuma a suwa ɗan wake a hotel? am talking you are talking? duk wanda ke son zaman lafiya acikin ku, kada ya kuskura ya shiga gona ta, domin ni ba irin ku bace! Wlh uban mutun zanci kuma a zauna lafiya!”
Batasan lokacin da dariya ta kubce mata ba, Rayuwa kenan, Idan mutun ya kasance ƙaddararka baka isa ka canza shi ba, bata ta6a tunanin zasu sasanta tsakaninsu ba, saboda rashin jituwarsu sai gashi a yanzu sun shaƙu da junansu ita da sauran ƴan uwanta prisoners.
Nurse Jessica Har tafara Gajiya da zama bacci na shirin kwasarta a saman kujera, sam batason ta katse Angel donta fahimci ba ƙaramin so take Yiwa ɗan uwan nata ba, duba da yadda ta haye saman jikinshi tana sambatu hada murmushi da dariya.
Soft lips ɗinsa ta ƙurawa ido tamkar anyi mixing din launinsu da pink
“Masoyiya Angel Yakamata mu koma ɗaki ko”? Muryar Nurse jessica ce ta fargar da ita, Amsa mata Tayi da toh Kafin ta miƙe ta ɗan dukar da kanta saitin fuskarshi sumar kanta ta yi mashi rumfa, A hankali ta ɗaura small mouth ɗinta saman Forehead dinsa Da Niyar ta manna mashi peck ba zato ba tsammani taji ya damƙi waist dinsa ruƙo bana wasa ba, Agigice Take kallon face dinsa wani abun mamaki bai farka daga baccin ba, tashin hankalin da ba’a sama shi data, Nan take Jikinta Ya hau Yin kakarwa ido Ya raina fata, wata irin zuface ta soma tsastsafo mata ta cikin hudar gashin jikinta.......
*Boss Bature✍️ Mu haɗu Monday Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuɗin*
First bank
3196407426,
*Bature Hafsat Muhammad, za’a tura evidence of payment ta phone number ɗina 08169856268 Banda kira whatsapp kawai*
_~*BossLadiesWriters*~_
_*💋KURKUKUN ƘADDARA💋*_
~Middle step~
_The Prisoners E20🔥💫_
*Daga alƙalamin Boss Bature*
Hankalinta a matuƙar tashe take kallon fuskarshi, Numfashinta na hauhawa zuciyarta na bugawa da sauti mai ƙarfin gaske tamkar zata tsaga ƙirjinta, tsabar tsoratar da ta yi, Nurse Jessica da ke a zaune ta rasa gane meke faruwa ne? taga dai tun da Angel ta yi mashi rumfa taƙi motsawa, kamar an daskarar da ita, idanuwanta ba su hango mata hannun Danish da ya damƙi Qugun Angel da shi, sakamakon Sumar Kanta da Hijabin jikinta sun lullu6e shi.
“masoyiya Angel, Ke nake Jira, kusan ƙarfe goma na dare, Yakamata Muje ki kwanta ki kwanta ki huta” Cikin Kulawa ta yi mata maganar Tana leƙen fuskarta sai dai bata samu damar ganinta ba, saboda wuyan Hijabinta Ya zame tuntuni sumar kanta ta zazzago gefe da gefen fuskarta, ta rufe su.
Yunƙurin kubcewa tayi daga ruƙon nashi sai dai ko gizau wannan bai yi ba, kuma bai motsa ba, Ya matseta A jikinshi, tamkar an ɗaureta da igiyoyi, duk da sanyin A.c na room din hakan bai hana ta zubda gumi ba, zufar dake wanko fuskarta kaitsaye take sauka saman fatar face nasa, idanuwanta azazzare, yayin da acan cikin zuciyarta ta ke ta ambaton”INNA LILLAHI WA’INNA ILAIHIRRAJI’UN”! Ba ƙaƙƙautawa.
Muyar Nurse Jessica ce ta ƙara fargar da ita”Lafiya kuwa Angel? Ya akai naji Kinyi shiru? Ko kinyi bacci ne a jikin shi” ta ƙare maganar tare da yunƙurawa ta miƙe daga saman chair ɗin ta nufi gaban gadon ta tsaya tana ci gaba da yi mata magana, tsabar yadda la66anta ke yin kerma ta kasa buɗe baki ta faɗa mata Halin da take a ciki.
Miƙa Hannu nurse jessica ta yi da niyar ta ɗago da Angel, saboda ta yi tsammanin bacci ne Yai awon gaba da ita, Sai dai Kafin ta ruƙo ta, Angel Ta yi ƙoƙarin Yin magana Muryarta A hargitsa ba natsuwa ta furta”ɗan Uwana Ya farka! Shine Ya ruƙe Ni”
Mamaki Ne Yasa Nurse jessica Zaro Ido haɗi da buɗe Baki, Ta Furta” Are u serious Ya farka?
“Ya farka, but he didn’t open his eyes. He held me so tightly that I couldn’t separate myself from him” cikin shessheƙar Kuka Angel ta furta maganar.
Jin haka Yasa Nurse jessica faɗin”Bari Na taimaka maki ki miƙe”
Hannu Biyu ta sanya ta ruƙe Angel ta soma kiciniyar 6an6arota daga Jikin Danish da Iya ƙarfin ta na ƙarshe sai dai takasa ta6uka komai, Mugun ruƙo Yai mata, Hatta dogayen nails ɗinsa sun yi mata shatu saman bayanta, Lamarin ya ɗaurewa Nurse Jessica kai, ganin ta sanya Iya ƙarfinta na ƙarshe Amma abanza, hakan ba ƙaramin ruɗar da ita yai ba, Muryarta na rawa ta furta”Bari naje na kira doctor”
Da sauri ta fuce daga Cikin ɗakin hada ɗan gudunta
A lokacin da bata Yi tsammani ba, Sexy voice ɗinsa ta ratsa kunnuwanta muryar da ta daɗe tana mararin Jinta
“My Angel” Iya abunda ya furta mata kenan.
nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke, jin ya ambaci sunanta, hakan na nufin Yana acikin Hayyacinsa, ƙura ma fuskarshi ido tayi ganin yana mutsu mutsun buɗe idanuwanshi, sannu A hankali yake ƙoƙarin ware su, sunyi mashi nauyi saboda baccin da yai na tsawon kwanaki, Ta yi matuƙar ƙagara da son Yin tozali da kyawawan Reddish-brown eyes ɗinsa, kaɗan Ya buɗe su bai ƙarasa ware su ba, sun ciza launinsu, hakan ba ƙaramin kyau suka ƙara ma shi ba, Tsabar farin ciki batasan sa’adda ta fashe mashi da kuka mai tsuma zuciya, tana haɗawa da dariyar farin Ciki, ya natsu yana kallonta da wata irin kasala a jikinshi, sam bai san a ina suke ba Iya fuskarta Yake Iya gani.
Cikin shessheƙar kuka haɗi da shagwa6a take faɗin”Nayi missing ɗinka My man, sai yau zaka farka? Kabarmu da kewarka da fargabar a wani hali zaka tashi, sannan kuma ka tsoratar dani sosai....” lumshe idanuwanshi ya ɗanyi tare da ware su saman fuskarta, Hawayenta sai jiƙa masa face dinshi suke Yi, har cikin bakinsa, hakan bai dame shi ba, tamkar ya samu ruwan sha, haka ya ke yin swallowing dinsu.
Kallon da ya ke yi mata kallo ne dake nuni da tsantsar ƙaunarta da kewarta da yayi, hucin numfashinsu sai gaurayewa yake yi dana juna, hakan bai sha masu kai ba.
Idanuwanta sharkaf da hawaye sun rune jawur taci gaba da cewa”dan Allah ka faɗamin ba abunda ke damunka? Naga kanata kallona kaƙi kula ni” ta ƙare maganar still da shagwa6a, yamutsa fuskarshi yaɗanyi haɗi da motsa tausasan la66ansa calmly ya furta
“ke ce damuwata, kinsan bana son zubar hawayenki, ki daina yi min ku ka or else I’ll go back to sleep
yai maganar yana ƙoƙarin lumshe idanuwanshi da zolaya yai mata hakan aiko da sauri ta shanye kukanta, tana faɗin”na daina My man, kaine ka ƙi kwantar min da hankali na” ba zato ba tsammani taji ya manna mata peck saman fore head dinta, farin ciki duk ya cikata.
Muyarta har shaƙewa ta ke yi saboda kukan da tasha”ka sake ni, Ka matse ni” tayi maganar tana ƙoƙarin kubcewa daga ruƙon da yai mata, so ta ke yi ta nuna mashi sabon wurin da suke acikin shi, ƙanƙameta Ya ƙara yi yana faɗin
“Ki jira, zan sake ki, ina samun natsuwa atare da ke”
ƙayataccen murmushi ta saki, ta ɗan dakata suna kallon cikin idon junansu, lokaci ɗaya taga Ya haɗe face dinsa.
“Lafiya”? Tai tambayar tana cigaba da kallon shi
“Namanta, ban sama maku abincin da zaku ci ba, Na bar ku da Yunwa”
Murmushin gefen fuska ta sakar mashi”Ka kwantar da hankalin ka, Muna cin Lafiyayyan abinci har sai mun ture, shiyasa nace ka sake ni inason nuna maka wani abu” slowly ya zame hannunsa daga ruƙon Da yai Mata, Light bulb ɗin ɗakin Ya haske mashi ido, saukowa tayi daga saman gadon ta fuskanci gabas Ta duƙa tayi sujjada tana godewa Allah daya farkar mata dashi cikin ƙoshin Lafiya ba tare da wani abu ya same shi ba.
Alhamdulillahi Ala kulli Halin.
Ya yi matuƙar Yin mamakin ganin room ɗin da ya ke aciki, a kasalance ya yunƙura Ya miƙe zaune yana ƙarewa ko’ina Kallo, tunani ya shiga yi Ina ne nan? Waye ya kawo su? Fuskarshi da alamun ruɗani ya Tura yatsun hannunshi cikin yalwatacciyar sumar kanshi yaci gaba da cakuɗata tamkar yana sosata, saukowa ya yi da ga saman gadon.
Jikinshi yayi mashi nauyi daƙyar yake taka ƙafarshi, yayin da yake ƙarewa ɗakin Kallo, Angel tana a duƙe tun da tayi sujjada bata ɗago ba, addu’o’i take tayi masu.
Yana ƙoƙarin buɗe baki da niyar ya yi mata magana, Sai ga doctors da nurses sun shigo ɗakin da saurin su, Kusan atare su ka ci uban burki suna kallon kallon a tsakanin su da shi, Mutumin da suka daɗe suna mararin ganin Ya farka, sai yau Allah ya nufa zai tashi, Sun yi matuƙar girgiza da ganin Shi a tsaye kan ƙafafun shi, kyan fasalin shi Ya yi masu ƙwarjini.
Da hannu Yai masu Alamar su wanene su? Sai Ƴan kame kame suke Yi An rasa me Iya buɗe Baki Yayi mashi magana.
Juyawa yai da sauri Yaje gaban Angel da ta yi sujjada, Da hannu ɗaya ya ruƙo damtsen ta, Ya ɗago da ita tsaye kamar wata ƴar baby, nuna mata likitocin Ya yi da hannun shi
“Who are they, and where are we?”
daƙyar ta samu natsuwar Fayyace mashi komai tun daga kan Yadda aka tsunto su a daji aka zo da su asibitin kamar yadda Gabriel Ya sanar da ita.
Bayan ta gama kora mashi jawabi ta kalli fuskokin likitocin tace “ku ta ya ni murna ɗan uwan mu Danish Ya farka”
murmushi kowan nan su Ya saki Nurses din dake a cikinsu kamar sun samu tv haka suke Binshi da mayataccen kallo, ba mazan ba ba matan ba.
“Muna ta ya ki Murna masoyiya Angel, munga brother ɗinki Ya farka cikin koshin Lafiya” nurse jessica ce Tayi maganar
Daƙyar wani dr ya iya buɗe baki yace”Danish Fatan Ka tashi Lafiya, tsawon lokaci muna jiran ranar da zaka buɗe idanuwanka, Sai yau muka samu damar ganin ka, Mun ji daɗi sosai” yai maganar tare da miƙa mashi hannu don su gaisa, Man ɗin fa bai yarda da su ba, dama yana da wuyar sha’ani ga ƙiwuya kamar ƙaramin Yaro.
“Danish Ka miƙa mashi hannu ku gaisa” Angel ce tayi mashi magana, goya hannayenshi yai saman broad chest dinsa, Alamar ba zai miƙa mashi hannun ba”
murmusi yaƙe ta ɗan saki”ku yi haƙuri, Danish baisan ku ba, Har yanzu baccin bai sake shi ba, nasan kafin zuwa gobe zai Warware’
Nurse rebecca tace “badamuwa, Dama mu fatan mu Ya farka da ranshi da lafiyarshi, Hakan ma ya wadatar”
Dr. Anthony Yace”Calm down, Danish. No one will bother you. We are doctors, and we have the right to check your health until you feel better.” still bai tanka masu ba.
Dr harry yace”ni dama tun kafin Ya farfaɗo raina Ya bani zai yi wuyar sha’ani, sai gashi maganata ta tabbata, mutane masu irin Kyanshi bakowa suke kulawa ba” da zolaya yai maganar, Ya ƙara da cewa “mu dai yakamata asaki jiki damu tunda malaman lafiya ne, muna so ka bamu dama mu ƙara bincika Lafiyarka” tun da suka fara Magana bai tanka masu ba sai kallo da yake binsu dashi kamar yaga wasu halittu daba na mutane ba.
“Ko akwai Inda ke yi maka ciwo yanzu”? Dr anthony ne yai mashi maganar, Angel sai ƙoƙarin ingiza hannunshi take Yi don yayi masu magana amma Yaƙiya, Nurse jessica tace”ga dukkam alamu rowar muryarsa yake yi mana, Ni inaga Mu ƙyale shi zuwa gobe nasan zai warware kuma zai saki jiki da mu”
Kamar za su yi hauka wurin yi mashi magiya don yayi masu magana yayi shiru abunshi, har so sukayi su bincika lafiyarshi amma Ya hana, duk wanda yai gigin matsowa kusa dashi, zazzare masu ido yake yi alamar zaiyi fighting dinsu, lamarin ya ɗaure masu kai, ganin sun sanya naci akan sai sun duba shi, Angel ta roƙe su akan su ƙyale shi zuwa gobe, fargabanta kada su hayaƙa shi azo asamu matsala, tunda harya fara zare masu ido yana ɗaure masu fuska. Ba don sun so ba, su ka yi masu sallama da niyar gobe zasu dawo, kusan atare suka fuce waje, aransu suna Ayyana irin kyawun fuskarshi da surarshi, sai santin shi suke Yi musamman nurses din cikin su.
Su Uku Suka rage a ɗakin, Nurse Jessica ta dubi Angel”na lura brother ɗin nan naki, ke kaɗai yake jin maganarki, Inaso ki tambayar min shi ko akwai abunda yake buƙatar ci”? Kallon shi Angel Tayi, idonshi na akan plasma tv ta ɗakin, sai ƴan kalle kalle yake yi.
“My man kana jin Yunwa”? Da budar bakinsa sai cewa yai”Ina haris da su Batul? Inason ganinsu”
Kallon Nurse din Tayi”yace yana son ganin ƴan uwanmu” gyaɗa kai tayi”badamuwa Zamu Iya zuwa”
Ruƙo Hannunshi tayi acikin nata”muje in nuna maka su” nurse jessica tana agaba suna abayanta, tun da suka fito daga ɗakin Yake ƙarewa ko’ina kallo, agogo kaɗai mutun zai kalla ya gane cewa dare ne amma donta hasken light bulbs na asibitin ba za ka ta6a gane dare bane.
Nurses ɗin dake yin zarya da doctors sai satar kallon shi suke yi, hada masu yin tuntu6e.
Ɗakin Haris suka Shiga, tun bayan fitar Angel bacci ya ɗauke shi.
Rabin jikinshi lullu6e da bargo, da sauri Danish ya ƙarasa daga gefen gadonshi Ya zauna Yana kallon shi, nurse da Angel suna a tsaye suna dubanshi.
“Bacci ya ke yi Danish, ko zamu bari sai gobe idan Ya farka mu dawo” ɗaga mata kai Yai alamar eh, dama burinshi ya gansu hankalinshi sai yafi kwanciya, ɗaura hannunshi yai saman sumar kan Haris ya shafata a hankali, tsantsar farin Cikine akan face dinsa’ mintuna Biyar kafin Ya miƙe, suka nufi ɗakin Batul, ko da suka shiga, basu sameta a saman gadonta ba, nan fa hankalin Angel Ya tashi, “ina batul taje” nurse jessica harta buɗe baki zata bata amsa, suka ji motsin fitowarta daga toilet, Kamar a mafarki take kallonsu kafin ta tsayar da idonta kan Danish, da ƙarfi ta ambaci sunanshi, da gudun gaske fa ƙarasa ta faɗa saman faffaɗan ƙirjinshi, ɗaura Hannayenshi yai saman bayanta sosai ya yi tighting ɗinta, daɗi kamar zai kasheta, annurin fuskarshi sai ƙara nunkuwa yake yi, da alama yaji daɗin canjin rayuwar da suka samu.
Ɗagowa tayi da