Author : Boss Bature Category : Complete Novels
daga kurkukun ƙaddara da Evil forest.......” a tsanake Gabriel Ya kwashe komai Ya sanar da ita, Cikin harshen hausa, hakan yasa Doctors din basuji me yake faɗa mata ba.
Maimakon tayi dariya Sai gani suka yi ta rushe da matsanancin kuka, abunda da ya ɗaure masu kai, tana kuka tana dariya a lokaci ɗaya, slowly ta zube saman gwiwowinta, tare da ɗaura goshinta saman tiles, Sujjada tayi domin nuna godiyarta ga Allah daya nuna mata wannan ranar da suka daɗe suna Jiranta!
*Boss Bature✍️ Mu haɗu gobe Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuɗin*
First bank
3196407426,
*Bature Hafsat Muhammad, za’a tura evidence of payment ta phone number ɗina 08169856268 Banda kira whatsapp kawai*
_~*BossLadiesWriters*~_
_*KURKUKUN ƘADDARA*_
_The Prisoners E15🔥💫_
*Daga alƙalamin Boss Bature*
~Middle step~
Lokacin da ta ɗago daga sujjadar fuskarta jaga jaga da hawayen, Tafin Hannayenta ta ɗaga sama ta soma ambaton sunan Allah tana Yi mashi kirari, Hakan Ba ƙaramin ruɗar da likitocin yai ba, shi dai Gabriel sai murmushi yake saki yana dubanta, Bayin Allah su kaɗai suka san Wahalar rayuwar da suka fuskanta Dole suji daɗin wannan Ranar, Ta jima tana addu’a,
Sam takasa miƙewa daga zaunan da take, Hawayen fuskarta tamkar zasu ƙare Sai sintiri suke yi saman kuncinta
“Angel pls stop shedding ur tears” Gabriel ne Yai mata maganar, Cikin shessheƙar kuka ta ɗago ta Kalle shi da rinannun idanuwanta waɗanda suka kada jawur da su
“Gabriel dole in yi kukan farin Ciki, kai ka sani irin wahalar da muka sha, munyi rayuwar kulle tamkar dabbobi har ƙwara ni akan sauran ƴan uwana tun suna jarirai, wannan ne karo na farko da zasu ɗanɗani rayuwar ƴanci acikin ƴan uwansu mutane, Iya cuta an cuci rayuwarsu mun tsira amma raunin dake acikin zukatanmu na har abada ne, saboda akwai abubuwan da muka rasa wanda nayi imanin baza su ta6a gogewa a tarihin rayuwarmu ba”
Hankalin likitocin ba ƙaramin tashi yai ba ganin yadda take kuka tana surutu gashi ba su fahimtar abunda take cewa, sai dai sun gane akwai abunda ke damun su wanda yai silar haifar masu da ciwon damuwa da baƙin ciki
Gabriel da ke a tsaye tuni shima ya fara zubar da hawaye.
Gabanta ne Ya ɗan faɗi Jin kukan Jemimah, Nan take shessheƙar kukan da ta ke yi ya dakata, Dr. Laura ce ta shigo Ɗakin hannunta ɗauke da Jemimah Tsabar jaraba ta runtse idanuwanta sun yi suntum saboda kuka, Sunan Genie kaɗai Take furtawa, jikin Angel na rawa Ta yunkura ta miƙe da sauri ta nufi dr. laura Hannu biyu tasa ta kar6eta sosai ta rungumeta a ƙirjinta, hannunta hada cannula da aka sanya mata.
“Angel” Muryar Batul ce ta ratsa kunnuwanta, da sauri ta ɗago tana kallonsu, A jere su ke shigo ɗakin kowan nan su Yasha kuka Idanuwa sunyi luhu luhu, doguwar suman kawu nan su A hargitse kamar waɗanda aka koro daga gidan mahaukata.
Kowan nan su Na sanye da light blue uniform da aka sanya masu, hannayensu sanye da cannula na drip da aka sanya masu.
Batul ce ta farko, Bayanta Parveen ce da hannah, Sai mazan Javed da Naufal, da gudum gaske suka ƙarasa shiga ɗakin gaba ɗaya suka ƙanƙame Angel kamar zasu kada ita ƙasa.
Al’ajabi Ya hana Likitocin cewa komai, Sun saki baki galala suna kallon Ikon Allah, Aransu suna Mamakin ƙaunar da suke yi ma ƙaramar Yarinyar da su ke kira da Suna Angel.
Farin Ciki kamar zai kasheta, Daɗi take ji tarasa ina zata tsoma ranta, Sun lullu6eta suna yi mata kuka, ko numfashi daƙyar take Iya fitarwa
“Angel ina ne nan? Wanene Ya kawo mu? Wlh tsoro muke ji, munga wasu mutane da bamu saba gani ba, kada su cutar damu Angel, sai kallon mu suke yi kamar zasu lashe mu” Su parveen ne ke kora mata jawabi
“Ko dai mafarki muke Yi ne? Mu dake acikin Daji Ya akai muka tsinci kanmu a wannan wurin tare da wasu mutane masu fararen Kaya, Angel ko dai Aljannace da kike bamu labari? Idan mun mutu zamu shiga” Maganar Batul tayi matuƙar bata dariya, Daƙyar ta samu suka saketa, Ga jemimah ta ƙanƙameta Jikinta sai kerma Yake yi.
Azeeza tana maƙale da Gabriel Sarkin tsoro, Ta kasa ɗauke idanuwanta daga kan faces ɗin Likitocin dake a tsaitsaye cirko cirko suna kallonsu.
“Angel mun shiga ku, Sai kallon mu suke yi,” Hanna ce ta yi maganar
Muryar dr. Laura ce ta katse masu Hanzarinsu cikin harshen turanci ta ke yin maganar
“Ku kwantar da hankalinku, babu wanda zai cutar daku, Anan inda kuke Asibiti ne, mu kuma da kuke gani likitoci ne da nurses haƙƙinmu ne kula da Lafiyarku, Za mu taimaka maku don ganin kun warware daga lalurar dake damunku, Muna so ku ɗauke mu tamkar Ƴan uwanku, idan ku ka yi hakan munyi maku alƙawarin zamu share maku hawayenku, Zamu gatanta ku mu baku kyakkyawan kulawa har izuwa lokacin da zamu miƙa ku ga Iyayen ku.
Tun da tafara Yi masu magana kowannansu Ya natsu yana sauraronta, da alama sun fara fahimtarta
Matsowa Kusa Dr Brown Yai daga gefenta Ya tsaya”duk wani abu da kuke buƙata zamu yi maku shi, ku ɗauka tamkar kuna a gidan Iyayenku ne, burin mu shine ku bamu haɗin kai, Ku daina Jin tsoron mu”
Muryar Dr Jack Ce Ta janyo hankulansu ga dubanshi
“Mun haɗa ku wuri ɗaya ne saboda mun fahimci ba za ku ta6a sakewa damu ba, idan har ba Kuna atare da Ƴar uwarku Angel ba, Muna fata Yanzu hankalinku zai kwanta, ga ku ga Mamanku Angel” Da zolaya yayi masu maganar, murmushi Angel ta saki tana kallonsu, daga gani suna da mutunci.
“Masoyiya Angel faɗa min me ki ke yi wa Yaran nan naki ne? Don na lura ba ƙaramin ƙaunar ki su ke Yi ba” Dr Brown ne yai magana haɗi da ɗaga mata gira ɗaya, Sunnar da kanta ƙasa Tayi dariya takeso tayi sai da takasa.
“Yaushe kika haife su ne? Sannan Ina Mijin naki”? Kunyace ta rufe Angel da sauri ta ɗaura Kanta saman sumar kan Jemimah dake ruƙe a hannunta.
Dariya Dr. laura ta saki”Wow Kunya take ji, To ko dai Matashin saurayin nan mai bacci ne mijinki? Wannan kyakkyawan don naji kamar kina ambaton sunanshi” gaba ɗaya sun sanyata jin Kunya ji take kamar ta nutse ga farin Ciki da ya lullu6eta.
Da biyu likitocin suke zolayarta, Yana daga cikin aikinsu kwantar da hankalin Mara lafiya musamman su da suke son su saki jiki da su, Ta hakanne zasu samu bayanan da suke so daga gareta.
“Mun fahimci Masoyiya Angel bakinta ya mutu, saboda An sosa mata inda ke yi mata ƙaiƙayi, Yanzu faɗa min me kikeson Ci ke da Ƴan uwan naki mu kawo maku” Cikin kulawa Dr. laura ke yi mata magana.
Kallon sauran Ƴan uwan nata tayi
“Ko ba ku jin yunwa ne”? Shiru suka yi ba wanda Ya bata amsa, idonsu akan Angel, Dariya doctors ɗin suka saki
“Oh Baku Iya magana sai da izninta, to ke masoyiya Angel Faɗa mana me kikeso akawo maki keda Ƴa’ƴan naki don bama son barinku da Yunwa”
Cikin Jin kunyarsu Angel ta furta”komai muka samu zamu ci” Jinjina kai Dr Laura Tayi kafin ta juya ta kalli Sister rebecca”A shirya masu lafiyayyan abinci da Kayan sha” amsa mata Tayi da toh da sauri ta juya ta fuce.
Dawo da dubanta tayi akan fuskokinsu
“Yanzu zamu tafi mu baku wuri Pls Idan an kawo maku abincin Ku tabbatar Kun cinye min shi duka kaf, zanji daɗin hakan,’ dr Laura davis Na rufe Maki Dr Mark Yace”Zamu dawo Da Anjima, Kyawawan ƴan mata, dole in za6i ɗaya daga cikin ku, irin wannan Kyau haka”
Dr Bown Yace”ai ba kai kaɗai ba mutumina, Ni ruwan ido ma ya hanani zabar ɗaya, ta ko’ina Kyau nake gani musamman Masoyiya Angel ta tafi da ni” Dariya ce ta kubcewa Angel da Gabriel
Harara Dr Laura davis Ta watsa mashi”bazaiyiwu ba, Duk na riga ku, Nima nayiwa ƴa’ƴana kamun matan aure a Cikin su’ Nishaɗi sosai suka sanya su.
“Zamu tafi Masoyiya Angel, Amma kafin nan Ki kula mana da ƴa’ƴanki, Ki lallashesu su daina mana kuka dake kanki bama so kuna zubda tsadaddun hawayenku” Cikin sanyin murya Angel ta amsa mata da toh, Sallama suka Yi masu atare suka fuce daga ɗakin suna masu santin Kyawun Yaran acikin ransu.
Fitarsu keda Wuya Ange Ta fada saman Gadon rungume da jamimah tana tiƙar dariyar Farin Ciki tana faɗin”ALHAMDULILLAHI ALA KULLI HALIN”
“Kuyi Farin Ciki mana, Ina Tayamu murna Mun ku6uta daga Kurkukun ƙaddara, Mun zama masu ƴanci” Su Batul sunƙi sakin jiki har yanzu basu fahimci Ta ya ya akai suka tsinci kansu a wannan wurin ba.
Gabriel ne yai ƙoƙarin fahimtar da su abunda Ya faru zuwan Sojoji Dajin.
Wayyo Allah daɗi Wani irin annurin farin cikine Ya bayyana akan fuskokinsu, Bakunansu sun kasa rufuwa Fararen haƙoransu tamkar Gonar auduga
“Gabriel kana nufin Yanzu mun bar kurkuku da daji? Muna acikin Mutanan duniya” Fuskar Gabriel da murmushi Ya amsa masu”ƙwarai kuwa, Babu ku babu zubar da hawaye baƙin ciki da kunci sun ƙare” Tsabar Farin Ciki Suna kuka suna dariya, gaba ɗaya suka Haye saman Gadon Angel, suka kwanta a jere da ita sai daɗi suke ji saman ceilling ɗin ɗakin suka ƙurawa ido kowa Yana tariyo abubuwan da suka faru a rayuwarshi jin shessheƙar kukansu ta cika ɗakinne Yasa ta soma yi masu magana cikin lallashi
“Dan Allah ku daina, Yanzu lokacin farin ciki ne, Godiya yakamata Muyiwa Allah, a koda yaushe shi mahaƙurci mawadaci ne, yau gashi dai mun shaida hakan Allah ya kar6i kokenmu yaji ƙanmu ya raba mu da ƙangin rayuwar da muke aciki, A yau mu masu ƴan ci ne zamu shaƙi Iskar duniya son ranmu batare da wani yayi mana Iyaka da ita ba” Murmushine Ya bayyana akan fuskokinsu
Cikin shessheƙar Kuka Azeeza ta soma magana tana fadin”Ni ƴan uwanmu nake tunanawo waɗanda muka rasa acikinmu, tare da Salsabeel da ya taimaki rayuwar mu, nasan dole su kashe shi idan suka kama shi Yana acan kurkuku Suna azabtar dashi”
Naufal ya ɗaura da cewa”babu Deeja! Babu Mubeen Akan idonmu ya yanke jiki Ya faɗi, a lokacin muna aga6ar barin kurkuku.....” Kasa ƙarasa maganar Yayi saboda kukan da ya ciyo shi.
Javed ya dasa daga Inda ya tsaya”Mun rasa tsohuwa tamira! Mun rasa Eve da Yasmin sannan mun rasa Hibba da Rubina, da Sarah! “ tunkan Ya rufe Baki Angel ta ɗaura da cewa”Allah Sarki Unaiza Ƴar gidan daddy, da Majnoon Bayin Allah ban ta6a tunanin zamu tsira ba tare dasu, Muna ƙaunar ƴan uwanmu sosai, Sai dai mutuwa tayi mana Yankan ƙauna, Ta raba mu da su, In sha Allah zamu haɗu da su agidan Aljanna inda babu kurkukun ƙaddara babu duk wani mugu, Allah sarki tsohuwa tamira da Salsabeel waɗannan bayin Allahn Har duniya ta naɗe bazamu ta6a mantawa dasu ba, saboda Sun kafa tarihi acikin zukatanmu In sha Allah a koda yaushe zamu dinga binsu da addu’a, sannan zamu Cika masu burin su na ruguza tarihin KURUKUKUN ƘADDARA.
Abubuwa da dama suke tariyowa na rayuwarsu na baƙin Ciki da farin Ciki
“Angel Danish fa har yanzu bai farfaɗo ba, Haris kuma Bashi da ƙoshin lafiya nurse ta faɗa min abunda ke damun shi ni nasan silar deeja ne, Amma tace Ciwon nashi bazai jima ba, Zaiji sauki”
Jin wannan maganar yasa gabanta faɗuwa, A hanzarce ta miƙe zaune saman mattress ɗin, su Batul ma suka mimmiƙe suna kallonta, sun sha kuka fuskokinsu sunyi jawur dasu abunka ga farare, Ita dai Jemimah tunda ta lafe ma angel hankalinta kwance bata da sauran damuwa.
Ƙasa ƙasa da murya ta ambaci kalmar Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un! Gabriel Akwai matsala! Wai ni wace ƙasa ce wannan”? A matuƙar ruɗe ta jefa mashi Tambayar, duk budurin da akeyi bata lura da fararen fata bane sai da yayi mata zancen Danish.
“Ni kaina Angel bansani ba” Dafe kai tayi da hannu ɗaya, Yayin da take bin ko’ina na room ɗin da kallo, karaf idonta ya sauka akan wani hoto dake manne jikin bango, a jikin shi an rubuta
SAN ANTONIO TEXAS United states of America
zazzare idanuwanta waje tayi wuƙi wuƙi Muryarta Na kakarwa ta soma maimaita Sunan America, tun da take arayuwarta bata ta6a taka kafadarta a ƙasar waje ba, Iya Nigeria ne, Yau ƙaddara Ta jefo su America a maimakon Nigeria! Hankalinta idan yai dubu toh ya tashi, ta ya ya zasu Koma Nigeria har su samu damar ɗauko ruwan zamzam da zasu ba Danish? Don tana Ji aranta Baccin da yake yi bana lafiya bane zaiyi wuya ya farka batare da giant’s heart ɗinsa ta motsa ba, Muryoyinsu Aruɗe su ke ambaci sunanta”Angel menene? Bamu tsira ba ko? Wani abu zai faru damu”? Girgiza masu kai tayi muryarta tamkar zata fashe da kuka tace”Wlh ba Nigeria bace wannan ba ƙasa ta bace, America ce ƙasar turawa, taya akai haka ta faru!? Nauyayyar ajiyar zuciya suka sauke, don su basu san abunda take gujemawa ba, Lamarin ya girgizata har tafara tunanin dama kurkukun ƙaddarar ba A nigeria ya ke ba? Akwai gagarumar matsala dole su nemi mafita.
“Angel ae zamu Iya zuwa can ko”? Da sauri Gabriel ya amsa masu da cewa”Eh mana ba wani abu, kada ku damu kanku, Sojoji sunce idan muka basu haɗin kai zasu damƙa mu wurin Iyayenmu, Idan suka tambayemu sai mu faɗa masu cewa Mu ƴan nigeria ne”
Kafin wani Ya ƙara magana acikinsu, Nurse rebecca Ta turo ƙofar ɗakin Hannunta ruƙe da faffaɗan tray na kayan abinci da aka jera masu, A saman table ta ɗaura masu, kafin ta ɗago tana dubansu fuskarta ɗauke da murmushi tace”Idan kuna buƙatar wani abu zaku Iya kira awaya ku sanar dani” Ta yi maganar tana nuna masu wayar dake ajiye saman table, al’ajabi ne ya kama su wai yau sune ake tarairaya? har tambayarsu ake yi in suna buƙatar wani abu? Wannan wani irin abun farin ciki ne!
Har ta juya zata fuce, Muryar Angel ta dakatar da ita “Sister, which country are we in?” ? ta tambaye ta ne don ta ƙara tabbatarwa
Juyowa Nurse rebecce tayi fuskarta da fara’a ta furta”San antonio texas” idanuwan angel luhu luhu ta ce”Thank u”
Hankalin Angel Yaƙi kwanciya, sam bata lura Sun fara Cin abincin ba, gaba ɗayansu sun dawo bakin gadon, Su parveen banza ta samu, soyayyar kaza mai maiƙo ta damƙa tana turawa abaki atsiyace take cizgar Naman kazar, Jemimah ta sungumi tsiran nama ita da azeeza, Batul kuwa Soyayyan ƙwai ta ɗauka tana Ci har wani nannaɗe shi take yi kafin ta tura abaki, Hannah ko warmer ta ɗauka shaƙe da Chips tana ci, Ba baka sai kunne, Su naufal an dahi Chicken shawarma, Javed ko Kayan marmari ya damƙa yana sha, kamar kwancen Yunwa Sun zaƙe suna ci suna Korawa da lemu me sanyi kala kala aka kawo masu, basu san akwai cctv ba a ɗakin, Duk wani motsinsu ana kallonsu😂
Ita kanta Angel data dubesu saida gabanta ya faɗi, Ganin yadda suke cunkusa abinci abakunansu Kamar kuraye, Muryarta na rawa take faɗin’pls ku bi a hankali kada ku shaƙe” tamkar kurame babu wanda ya dubeta bama su san akan me take magana ba, a dole ta ƙyalesu ta zura hannu ta ɗauki burger tana ci...........
*BARI MU LEƘA GIDA NIGERIA*
*A DAULAR OBIE ESTATE*
A Zaune take dirshan acikin Katafaren Bedroom ɗin Obinna, wa’iya zubilla kai kace ɗakin matashin saurayine saboda tsabar haɗuwarshi, An kashe dukiya a furniture ɗin ɗakin komai na cikinsa launin Red and golden ne, Ko sarki Albarka, Tanƙamemen gadonsa Royal state bed irin gadon da ko mutun baijin bacci ya hau sai Ya runtsa, Ga wasu matassan kai launin red da golden jere a gaban headboard ɗin, Dogayen labulaye ne a kewaye da ɗakin, ga wasu bedside drawers masu ɗauke da lamp, daga saman ceilling ɗin ɗakin Haɗaɗɗen Chandeliar ne dake bada hasken ɗakin ga wata zungureriyar Sofa Bayan ita akwai arm chairs masu ɗan banzan kyau, Ga wani ƙayataccen table dake ɗauke da Kayan Ado na ɗaki. Daga jikin bangon ɗakin haɗaɗɗiyar wallpaper ce mai zanan flowers masu matuƙar ƙayatarwa da jan hakalin me kallonsu, floor ɗin ɗakin tamkar mirrored tiles ne Kana Iya ganin fuskarka a cikinsa tamkar madubi, ga wani Jigunannan Dressing mirror Tafkekan gaske Jerin tsadaddun turarurrukane ne asaman shi da sauran kayan gyaran jiki, idan nace zan cigaba da zayyana haɗuwar Ɗakin dattijon arziki tabbas zamu ƙare takun tsakiya wurin fasalta Kyawunshi.
Yana daga kishingiɗe saman lallausar mattress ɗin gadon, Apple laptop ce agaban shi, Da alama Video call Ya ke yi da wani, ɗabi’arsa ce yana magana yana shafa gemun shi wani sa’in har Jan shi ya ke yi.
Hajiya saratu tayi zaman cin tuwo saman lallausan carpet ɗin gaban gadon shi, tana jiran Ya kammala Yin wayar, ta tsare shi da ido babu annuri akan fuskarta, Hankalin shi gaba ɗaya yana akan fuskarta, Nazarin yanayinta ya ke yi, kamar daga sama ta tsinkayi muryar shi akanta
“Saratu kin wuni lafiya”? Ƙara tamke fuskarta tayi”lafiyalou baba, fatan na same ku lafiya” murmushin gefen fuska ya sakar mata”Alhamdulillah, in ce ko lafiya? Naga yanayin fuskarki da 6acin rai, Waye ya ta6amin autata ne yanzu in ɗaura ɗamarar yin yaƙi da shi” murmushin Yaƙe ta ƙaƙalo, har ta buɗe baki zatayi magana yai saurin tarar numfashinta”nasan kinzo gaishe da baban nakine kamar yadda kika saba, Naji daɗi sosai mamana, Bari na kira hajjaty