Author : Boss Bature Category : Complete Novels
mintuna Biyar, wani kyakkyawan matashin likita Ya nufo motar da saurin shi kamar zai yi tuntu6e.
A gaban motar su ya dakata da yin tafiyar, ya kai hannu yai knocking glass din motar, turo ƙofar da a kayi ne Yasa shi yin saurin gyara natsuwar shi, Sam hankalin shi ba a kwance ya ke ba, tun da sir mubarak ya kira shi awaya ya sanar da shi game da zuwan shi asibitin gaba ɗaya ya rasa natsuwar shi, saboda sanin matsayin shi a ƙasar.
“Dr fawan, shigo ciki mana “ muryar Sir mubarak ce ta fargar da shi, Jiki na rawa ya shiga motar, ya zauna yana faman zazzare idonshi yace”daddy, ina wuni Ya gida ya Iyali” sir mubarak yace”lafiya lou fawan, Ya aiki ya fama da marasa lafiya” tun da ya fara magana bai ɗago Ya daura idonshi akan fuskar fawan ba, Hankalin shi na akan Wayar hannun shi da yake daddanawa.
Still muryarshi na rawa ya furta”Lafiya lou daddy, sai ga kiranka, Na ɗanyi mamaki” sai da ya ambaci hakan sir mubarak Ya ɗago da ido ya kalli fuskar fawan, duk da sanyin A c na motar, abun mamaki zufa ce ke tsastsafo mashi, kallon tuhuma sir mubarak yake jefa mashi, saboda zufar daya gani a saman goshin shi.
“Ya akai naga kana zubar da gumi? Ko baka da lafiya ne”? Yawu fawan Ya haɗiya tare da cewa”babu komai, Lafiya ta ƙalau”
Ta6e baki Sir mubarak Yai”Okey, Inaso ka kaini gidan kajin da kuke kiwo kai da Jazz,” da alamun ruɗu akan fuskar dr Fawan yace”Gidan kaji? Daddy ban fahimci abunda kake nufi ba, waye ya buɗe gidan kaji” yanayin yadda ya furta maganar, babu alamun yasan da zancen.
Fuskar sir mubarak a ɗaure tamau yace”You know who I am. I don’t need to explain this to you, Don haka kada ka 6oye min gaskiya, wani gidan kaji ne kuka buɗe kai da jazz? Da kanshi ya faɗa mini cewa kun zuba jari don kuyi kiwon kaji, kusan kullum ne saina kama shi yana yin waya akan gidan kiwon kajin ku”
Hankalin dr fawan ba ƙaramin tashi yai fa, Muyarshi na rawa ya furta”`wallahi thumma tallahi daddy bansan da zancen gidan kaji ba, sai dai ko ƙarya dr jazz yayi maka, ka ji na rantse maka da Allah...” Lamarin ya ɗaurewa Sir mubarak kai, Sojan dake zaune a driver seat Ya natsu Yana sauraron su, ta cikin ear-view mirror din motar Yake kallonsu.
“Fawan, Ka faɗamin gaskiya, ni nasan Jazz ba zai ta6a yi mini ƙarya ba, na lura gaba ɗaya baka acikin hayyacin ka, idan ma saboda ni ne to ka kwantar da hankalin ka, babu abun da zan yi maka, ni dai buri na shine ka kai ni gidan Kajin ku, inaso in gansu, nayi maka alƙawarin idan ka rakani na gansu zan ƙara maku jari”
cikin ruɗu dr fawan ya girgiza kai yana fadin”bazan yi maka ƙarya ba daddy, ina ganin ka tamkar uba agareni saboda ƙaunar dake a tsakanina da Jazz, wlh Daddy ni bamu ta6a yin maganar buɗe gidan kaji da dr jazz ba”
Da kakkausar murya Sojan dake a gaban motar yace”Sir, this boy isn’t telling us the truth. Why don’t we take him to the headquarter? Maybe if we do, he’ll tell us the truth.”(yalla6ai Yaron nan bazai fada mana gaskiya ba, Me zai hana Mu shiga dashi headquarter Wata’ƙil idan mu ka je can Ya faɗa mana gaskiya)
Zaro ido waje dr fawan yai, jin ance za’aje dashi headquarter, sir mubarak yace”kada ka damu ai basai munje headquarter ba, akwai bindiga a ƙuguna, “yai maganar tare da sanya hannu ya zaro bindigar Ya ɗaurata saman laps dinshi, tsabar tashin hankali ne tsantsa akan fuskar fawan.
Sir mubarak yace”idan na kashe ka na kashe banza, sai dai idan munje lahira ayi mana hisabi, don haka ka faɗa min gasiya, idan ba haka ba zan tarwatsa kanka da bindigar hannuna” bawan Allah dr fawan duk sun tsoratar dashi da barazanar su, ƴan hanjin cikin shi sun kaɗa.
Hawaye tuni sun soma wanke fuskarshi, cikin sanyin murya yace”ko da zaka kashe ni daddy, bazan fasa faɗa maka gaskiyata ba, wlh rantsuwar ɗan musulmi bani da masaniya akan maganar gidan kaji, daddy banyi niyar fada maka ba, amma don in kare kaina zan sanar dakai wani abu da baka sani ba” Hankalinsu gaba ɗaya yana akan fuskarshi.
Numfasawa yayi kafin ya ɗaura da cewa “Daddy, jazz baya zuwa aiki, yau kusan wata ɗaya da sati, bansani ba ko kunsan da hakan, Ni kaina na damu da canzawarshi,”. Zuciyar Sir mubarak a hautsine Ya furta”idan kuwa har hakane Dr fawan baka kyauta mini ba! Meyasa tuntuni baka kira awaya ka sanar dani cewa baya zuwa aiki ba? Kusan kullum sai na ganshi ya shirya zai je asibiti, hakan na nufin ba aiki yake zuwaba wani wurin daban ya ke tafiya? Ya jefa mashi tambayar yana mai jin ɗaci acikin zuciyarshi.
“Ka yi hakuri daddy, Bana son in shiga tsakaninka da shi, sannan ni bansan baku da masaniya akan hakan ba”
“Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un!” Sir mubarak ne ya furta hakan, zuciyarshi tayi matuƙar karaya da jin cewa jazz baya zuwa aiki, Ya fara zargin shi akan ƙarairakin da ya ke yi mashi, bai ta6a tunanin Jazz zai yi mashi haka ba, duk da irin ƙaunar da yake nuna mashi.
Idanuwan shi tuni sun kaɗa jawur, zuciyarshi ta motsa.
“Bana so Jazz ya san cewa nazo asibitin nan! Ko nayi magana dakai! Kaja baki kayi shiru,” dr fawan ya amsa mashi da toh daddy, in sha Allah bazan faɗa mashi ba.
“Ka share hawayen ka,” da sauri dr fawan ya zaro hanky ya soma goge fuskarshi.
“Dr fawan, Na yarda da jazz sai dai a yanzu na fara zargin shi, wallahi If I find out that he’s doing something wrong, sai ya ɗanɗani kuɗar shi,” rai a6ace ya furta maganar, ya ƙara da cewa “dr fawan nagoda da bayanan da ka bani, zaka iya komawa bakin aikin ka” jiki na rawa dr fawan ya fito daga cikin motar, Bayan yayi masu sallama Ya nufi cikin asibitin yana faman sauke ajiyar zuciya.
Shiru su ka yi babu wanda ya ƙara magana acikin motar, Lamarin ya ɗaurewa Sir mubarak Kai, Mamakin shi ƙaryar da jazz yai mashi na cewa Sun buɗe gidan kaji, da kuma zuwa aikin da yake yi ashe duk ƙarya ne.
Driver-operator, Ya fahimci halin da sir mubarak ya shiga na damuwa, cikin kwantar da murya yace”Sir, pls kada hakan ya dame ka, nasan ba daɗi mutumin daka yarda dashi ya sa6aka, sai dai fa har yanzu bamu da tabbacin abun da dr jazz ya ke yi, mu kyautata mashi zato, sannan shawarar da na ke so in baka yalla6ai, me zai hana mu fidda rana ɗaya, Mubi bayan shi ba tare da sanin shi ba, a lokacin da ya shirya zai tafi aiki,”
Ta cikin mirror din motar Yake duban sir mubarak, nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke tare da kallon drivern yace “Ka kawo shawara mai kyau, tabbas inason sanin me jazz yake aikatawa, nagode da shawararka, zamu Iya tafiya”
Cikin girmamawa Ya amsa mashi da toh, sannan ya tada motar Ya fito da ita daga cikin harabar ajiye motocin, atsanake ya ke yin driving har suka haura saman titi, sir mubarak bai dai na cizon yatsanshi ba, saboda Ya damu da jazz, Ƙaunar da ya ke yi ma mahaifiyar shi ce ta shafe shi, ko ƴa’ƴan shi da ya haifa bai jin su kamar yadda yake jin jazz, hankalin shi ba zai ta6a kwanciya ba idan har bai gano abun da ya ke aikatawa ba, ya jima yana danne zuciyarshi akan ƙin amincewa da zargin yaron da ta ke yi, abun da ya jawo shi ga bincikar shi a yanzu ya fahimci aduk lokacin daya kama jazz yanayin waya da zarar Yaganshi yake rasa natsuwarshi, Jikinshi ya hau kerma, shiyasa ya fara suspecting dinsa.
❤ANEELERH❤
Tun kafin ta sallame sallar azahar wayar ta dake ajiye saman drawer take ta buga ringing, da zarar kiran ya katse wani ke shigowa, sai da ta kammala sallar ta ɗaga hannu tayi addu’a ta shafa a fuska, kafin ta miƙe da sauri ta nufi drawer ta ɗauki wayar, murmushi ta saki ganin sunan surukar arziƙi ya bayyana akan screen din wayar, aranta ta ayyana halan baby junaid ne ya matsa a kirani awaya.
Bayan ta ɗaga kiran ta manna wayar a kunnanta, kafin ta furta sallama muryar junaid ta katse mata hanzarin ta.
“Mommy, baby junaid ne, ni ne na kira ki awayar granny,” har sai da ta ji gabanta Ya ɗan faɗi, da mamaki tace”junaid da gaske kai ka kirani? Ina mommy adama? Ko dai itace ta baka wayar don ka yi mini magana”
muryarshi da shagwa6a yace”mommy ai bata nan, suna a falo, Ni kaɗai ne a ɗakin...” tun kan ya ƙarasa maganar tace”Junaid bana hana ka ɗaukarwa mutane waya ba? Faɗamin ya akai ka iya buɗe mata waya”?
“Mommy wasa nake maki, itane ta bani wayar, ta fita falo, ni kaɗai ne a ɗakin”
A faɗa ce tace”ƙarya ka ke yi mini junaid, ba ita bace ta baka wayar, kaine ka ɗauka ka kira ni, maza ka aje mata wayarta tun kan na 6ata maka rai,” ta yi maganar tamkar ranta ya 6aci sai dai azahiri ta yarda bashi wayar akayi, kawai tana son ta hayaƙa shi ne.
Sautin kukan shi ne ya cika mata kunnuwanta.
“Mommy ba ki yi missing dina ba, shiyasa kike yi mini faɗa, Kin barni ni kaɗai agidan su, ni wlh gida zan dawo, ko dai kizo ki ɗauke ni ko kuma in gudu in 6ace kamar Angel” maganarshi tayi matuƙar bata dariya, cikin sigar lallashi tace”am sorry my baby boy, wlh nayi kewarka kamar zan zauce, yanzu dai ka yi haƙuri kadaina kuka, Mommyn ka bata son zubar hawayen ka”
Cikin shessheƙar kuka yace”ni dai kizo ki ɗauke ni mommy, ko in gudu” hankalinta ya dan tashi, zuciya da saƙe saƙe saita dinga tunanin ko dai wani abu akayi mashi ne wanda ya 6ata mashi rai har yake neman dawowa gida.
“Junaid, faɗamin meya faru? Basa baka abinci ne? Ko ba ayi maka wanka ne? Ko wani ya buge ka ne”! A jere ta furta hakan.
“Ni ba su yi min komai, ina cin abinci kuma mommy adama tana min wanka har sau biyu safe da dare, ni kawai ke nakeso kizo ki dauke ni, ko in gudu” ajiyar zuciya ta sauke, hankalinta har ya ɗan kwanta.
“My baby boy, ka kwantar da hankalin ka, zasu dawo mun da kai nan bada jimawa ba,’
Rigima ya sanya mata”Allah in baki zo ba saina gudu” dariya ce ta kubce mata, jin sautin dariyarta ba ƙaramin 6ata mashi rai ba.
“Mommy dariya kike mini ko! Shikenan zan kashe wayar” da sauri tace”sorry nadaina, pls kada ka kashe min waya, Ina jin daɗin yin magana dakai, Yanzu faɗa min a kwance kake ko a tsaye”
“Saman gado” ya bata amsa atakaice, har ta buɗe baki zatayi magana ya katse ta da cewa”Mommy, na tuna sunan mutumin nan da ya kira ki a waya, ran nan, amma ba zan fada maki ba, In kina son ji kizo nan”
“Am sorry my baby boy, yakamata ka fahimce ni, babu yadda za’ai inzo, Zasu yi tsammanin ban yarda ɗazu bane shiyasa na biyo ka, dan Allah ka faɗa min sunan shi, ka ji yaron kirki”
cikin ƙagara da sonji tayi mashi maganar.
“Toh mommy, zan faɗa maki amma bana so kowa yaji har zahra” muryarshi da shagwa6a yake magana.
“Junaid, Ni kaɗaice a ɗakin, Zahra bata nan taje wurin aiki, Mahboob ma baya acikin gida, Abie da Uncle basu dawo gida ba, mami da ummi ne kuma basa a ɗakin, suna a can palour suna fira”
“To zan faɗa maki, amma kada ki faɗa ma zahra da mahboob” ta rasa ya za ta yi da shi, Yaƙi faɗa mata sai jan maganar yake yi kamar baya son fadi.
Kukan ƙarya ta soma yi mashi tana fadin”dan Allah baby junaid dina ka faɗamin, zuciyata zata iya bugawa idan ban ji ba” tuntsirewa yayi da dariya yana fadin”mommy wasa kike ba wani kuka ai na ganoki” gajiya tayi da tsayuwar, ta koma gefen gado ta zauna, tamkar tana agabanshi ta marairaice mashi fuska tana fadin”pls my baby boy, ka faɗa min, komi ka ke so zan yi maka”
“Zoben Angel, da ki ka ce zaki siya mini in bata tun da na maida ba mahboob nashi”
“Kada ka damu, kafin ka dawo gida zan siya maka zoben, Nayi maka alƙawari, Yanzu faɗa min toh”
Sai da ya mula ya ishe iska tukunna Ya furta”wai ma...waima daddyn Unaisah, haka yace min fa” shiru tayi jimm tana tunanin sunan daya furta mata daddyn unaisa? Wanene daddyn unaisa? Ita kanta unaisan wacece ita!, sunan ya shige mata, jin tayi shiru yasa Baby junaid ambaton sunanta”mommy kin yi shiru baki ce komai ba”
“Junaid, na ruɗe ne, na kasa gane wanene daddyn unaysa, amma shi mutumin Iya abun da ya faɗa maka kenan”?
“Eh, bai faɗa min komai ba, Mommy ki kira shi ki ji toh wanene shi, ko daddyn Angel dina ne?”
lokaci ɗaya taji gabanta Ya faɗi Jin Ya ambaci ƙila daddyn Angel ne, nan take ƙwaƙwalwarta ta tunano mata sunan wacece Unaisa, a sukwane ta mike tsaye Tana faman zare idanuwanta, zurfi tunani ta shiga duk duniyar nan mutun ɗaya ta sani mai sunan daddyn unaisa, wato Tajuddeen, ta gaza yarda da abinda zuciyarta ke faɗa mata.
La66anta na kerma ta furta”ka tabbata haka sunan yake? Ko dai abakina ka ta6a jin na ambaci sunan daddyn Unaisa?
“Mommy wlh dagaske nike maki haka yace min wai in faɗa maki daddyn unaisa ne, mommy zan kashe wayar, ga mommy adama nan zata shigo dakin” kafin ta yi mashi magana yai rejecting kiran.
Hakanan tadinga jin bugun zuciyarta na ƙaruwa, jiki asanyaye ta koma gefen gadon ta zauna, tsawon mintuna zuciyarta nayi mata kokwanton maganar da junaid Ya faɗa mata, har dai a ƙarshe ta yanke shawarar cire nombar daga black list, don ta kira ta ji wanene mutumin da junaid ya fada mata cewa daddyn Unaisa ne, fatanta Allah yasa Dagaske ne hasashenta.
Yatsun hannunta har kerma suke Yi wurin daddana wayar, bayan ta cire number daga black list, ta danna call cikin sa’a Kiran Ya shiga, wayar ta fara ringing, tsabar zumuɗi jikinta har kerma yake yi, Har kiran yayi rejecting ba’a ɗaga ba, Miƙewa tayi tsaye ta zame dogon hijabin jikinta ta jefar saman mattress, safa da marwa ta cigaba da yi a tsakar ɗakin, ta ruƙe wayarta a hannunta, a Ƙalla Ta Kira layin kusan sau biyar Yana ringing ba’a ɗaga ba, Hankalinta yaƙi kwanciya burinta taji wanene mutumin nan daya kira kanshi da sunan daddyn Unaisah.
Har ta fidda rai da za’a ɗaga Kiran, Unexpected A kira Na shida data yi mashi sai gashi Anyi picking call din.
Cikin rashin natsuwa ta furta”Assalamu alaikuma” maimakon ta ji muryar Namiji sai taji muryar matashiyar mace tana yi mata magana da wani yare.
“Baiwar Allah, bana jin harshen da kike yi mini magana dashi, Idan kina jin hausa mu yi magana da shi”
Ko da Aneelerh ta ambaci hakan, matashiyar sai ta canza harshenta zuwa Yaren hausa ta ƴan koyo tace”wanene ke magana”? A ƙagare Aneelerh tace”sunana Aneelerh, dalilin dayasa na kira Layin, kwanakin baya ana yawan kirana dashi, Ina tunanin ko wani ne ke nema, pls ina neman me wayar” ta faɗi hakan ne don junaid ya fada mata cewa Namiji ne Ya daga kiran lokacin da aka kira.
Matashiyar budurwar tace”Ni ce me wayar, wato irin kune ku ke bibiyar mazajen mu don ku ƙwace mana su ko”? Sakin baki Aneelerh tayi jin abun da matar tace.
“Kiyi haƙuri, Nima matar aure ce kamar ke, kawai inason nasan ainihin wanene me wayar, ki taimaka min a ƙagare nake da son ji” da alama matashiyar Yarinyar Akwai ƙuruciya atattare da ita, tun daga kan kalamanta zaka shaida hakan.
“Nace maki ni ce me wayar,” atsawace ta furta hakan, Aneelerh tace”ba wayar ki bace, saboda ke da kanki ki ka ce irina ne masu bibiyar mazajan mutane don mu kwace masu miji, hakan na nufin ba wayarki bace wayar mijin ki ce” sautin dariyar matashiyar ne ya cika mata kunnuwanta, lamarin ya ɗaure ma Aneelerh kai, gashi duk ta ƙagara a matse take da son jin wanene.
“Ke dai zan faɗa maki gaskiya, tun da kin gano ni, ba wayata bace, wayar mijina ce, kuma baya nan Ya fita ni ka ɗai ce agidan”
“Okey, pls Ko zan Iya sanin sunan mijin naki”?
“A’a gaskiya, salon ki je ki kai ma boka sunan shi ayi maki asiri ki mallake shi” duk yadda Aneelerh ta kai ga jurewa saida ta fashe da dariya jin abun da Yarinyar tace, daƙyar ta sassauta da yin dariyar tace”wlh ni bana bin boka, Ko hanyar zuwa wurin shi bansani ba, Yar uwata ba duka aka taru aka zama ɗaya ba, ni bana ɗaya daga cikin matan dake zuwa wurin boka, saboda na dogara da Allah shi kadaine zai Iya biyamun buƙatuna”
matashiyar tace”Ni ban yarda dake ba, mata dayawa suna son ƙwace mini mijina saboda kyakkyawa ne kuma yana da ƙarfi”
Aneelerh tace”baiwar Allah na faɗa maki nima matar aurece, da mijina akan me zan nemi mijin ki”!
“Oho nima bansani ba, idan kin gama magana zan kashe wayar” amsar data ba aneelerh kenan” Shiru aneelerh ta ɗanyi tana tunanin hanyar da zata 6ullo mata, ta fahimci Yarinyar bata da cikakken Ilmi da wayau sai a hankali. Dabara ce ta faɗo mata.
Dariya ta fara saki, Matashiyar