Kurkukun Kaddara Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Boss Bature Category :  Complete Novels

Chapter   33 / 84

96K to 99K   out of 250.5K words

Ringing ɗin wayarta ne ya janyo hankalinta ga duban hand bag dinta dake ajiye saman pillow.

Ba ta yi niyar ɗaga kiran ba, don ita a ƙa’ida bata picking call idan tana cin abinci saita kammala, hakanan dai tayi ra’ayin duba me kiranta, tissue ta yaga ta goge bakinta, kafin ta yunkura ta ruko handbag din, duba sunan me kiran nata tayi sunan ya fito 6aro 6aro asaman screen ɗin iphone ɗinta

*Princess Mujeedat* murmushi hajiya saratu ta saki da zumuɗi ta ɗaga kiran cikin harshen turanci ta soma yi mata kirari

“Uwargidan shugaban ƙasar Kanada, Gimbiya mai jiran gado ta Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa! Sarauniya ɗaya tilo da ke mulkin zuciyar Yaya Hateem, Wuu hu huu! ina gwanar wata ga tawa, Uwar gida sarautar mata daga ke babu ƙari mun kulle ƙofa” sautin ƙayataccen murmushin gimbiya mujeedat ne ya karaɗe kunnuwan saratu, da alama taji daɗin yabon da saratu ke yi mata.

bayan ta gama yi mata kirarin ta ɗaura da cewa”Habawa auntyna nayi fushi Allah, sai yau aka tuna dani, ai amana batace haka ba fisabilillah, daga ke har Yaya hateem ɗin baku tunawa da mutane sai wanda ya taka yaje inda ku ke” (idan kaga hajiya saratu na magana da mutun fuskarta asake to koma wanene ba ƙaramin mutun bane, babban gorone magogin ƙarfe dai dai da ita koma fiye da ita, zaranne yai dai dai da kalar yadin🤣)

Ni kaina da naji muryar mai magana saida naji shock, kai daga jin voice ɗinta zaka shaida jinin sarauta ce, gaba da baya, Jinin arziƙi waɗanda suka gaji abun, da izza da dattako ta ke yin magana tamkar bata son furtata.

“Ba abun da ki ke tunani bane ƙanwata, ban manta dake ba kina araina shiyasa ma na kira don mu gaisa” itama da turancin ta mayar mata da amsa don ba ta jin hausa.

“Duk da haka ban sauko daga fushin ba, gaskiya idan kinason mu shirya ki biyo yaya hateem kuzo Nigeria taya murnar birthday din baba, nasan halinki bakison taka ƙasarmu” fuskar hajiya saratu awashe take yi mata magana.

“Naji daɗin kirarin da ki ka yi mini, shiyasa a kullum nike ƙara godewa Allah daya bani surukai nagari irinku, wannan abun alfaharine, haƙika ban ta6a danasanin auran hateem da nayi ba, saboda tunda muka kasance a ƙarƙashin inuwa ɗaya har Allah ya azurtamu da samun zuri’a ban ta6a samun matsala da shi ko dangin shi ba, Kuna nuna min ƙauna sosai nima Ina sonku”

Hajiya saratu baki yaƙi rufuwa, sauran burger din dake abakinta tuni ta ƙarasa haɗiye ta, dadi take ji yau gimbiya mujeedat ta kirata awaya.

“Me kike ci ne? Naji bakinki acunkushe da wani abu, wato har yanzu ƙanwata baki daina ciye ciye ba ko”? Tuntsirewa hajiya saratu tayi da dariya annurin fuskarta sai ƙara nunkuwa yake yi. Mamaki takeyi yarda Gimbiya mujeedat keyi mata magana matar da saboda izzarta idan ka kirata awaya bata picking sai ka fara tura mata text message ka nemin iznin yin magana da ita, idan taga dama zata baka reply akan ka kirata a lokaci kaza, amma muddin mutun ya kira layin mujeedat batare da ya fara neman izni ba to bata ɗaga kiran nashi.

*A GIDAN ƊAN IYA*

Idan muka koma 6angaren su Aneeleeh tun ajiya Hajiya adama da Uncle abdallah suka sanar da su game da zancan komawarsu gida, Abie yace bazai yiwuwa ba su ɗan ƙara kwanaki mana, Anan uncle abdallah Yake sanar dasu cewa Ai sun samu gidan da zasu zauna a abuja ya 6oye ne bai sanar dasu, harma ya samu aiki a companyn sharufuddeen, ba ƙaramin farin Ciki su ka yi ba sun tayashi murna sosai, musamman da suka ji cewa bazasu raba Aneelerh da junaid ba ko da yakai shekarun da zasu Iya kar6ar shi ne, Zasu haƙura ne har Allah ya bayyanar masu da su Uzair, dama rashin ɗan nasu ne yaja har suke son kar6ar shi, Aneelerh hada kukan farin Ciki, Ta ƙara jin son surukan nata, ba ita kaɗai ba hatta su mami sun ji dadin ziyarar da suka kawo masu sun kuma jinjina ma ƙoƙarinsu na barma Aneelerh ɗanta, su kansu sun fahimci ba ƙarami so suke yima yaron ba tun da gashi ta dalilinsa sun dawo abuja da zama, ba su kai ga barin gidan ba, abie ne ya dakatar da su yace su ɗan jira akwai malaman da zai sanya su yi masu safkar alƙur’ani a sabon gidan su, hakan ba ƙaramin daɗi yai masu ba, don su basuyi tunanin yin hakan ba.

Hankalin Mahboob yaƙi kwanciya tun da yayi tozali da hoton Angel, a daren ranar daƙyar Ya iya runtsawa, saboda fuskarta da ke yi mashi gizo, ya kwana da mamakin baiwar Kyan da Allah Yayi ma yarinyar, bai ta6a ganinta ido da ido ba sai dai ahoto yasanta tun tana ƴar ƙaramarta, Aneelerh take ɗaukar ta hoto da video tana sanyawa a status dinta to anan yasanta, a ƙarshe daya gaza haƙara bayan sun dawo daga sallar asubahi, ya lalla6a yaje ɗakin aneelerh, tsabar Iya fadanci hada Kiranta da aunty, bai ta6a kiranta hakan ba sai yau da Allah ya jarabe shi da son sanin komai dangane da Angel.

Tambayoyi ya tsare Aneelerh da su akan ta fada mashi dagaske yarinyar mutunce bata haɗa jinsi da aljanu ba? Don shi gaskiya bai yarda da kyanta ba, Ya zarce na jinsin mutane, tun da yake kallon indian film, da korean drama bai ta6a ganin jarumar da ta kama ƙafar Yarinyar a kyau ba.

Aneelerh taci dariyar wautar Mahboob, har tambayar shi ta yi ko dai sonta ka ke yi ne? Naji kanata zuzuta kyawunta, “ da sauri ya dafe ƙirjinshi da hannu Yana faɗin”Sai kace dai bani da hankali aunty Aneelerh? Ae rijiya ba wurin gaɗar makaho bane, Nasan ciwon kaina ban shirya yin jinya a gadon asibiti ba, ni kawai kyanta ne ya ruɗe ni ba wani abu ba, tsakani da Allah yarinyar ba matar yaku bayi bace, ko makaho ya shafa fuskarta zai shaida hakan tafi dacewa da Manyan ƴa’ƴan masu kuɗi waɗanda suka jiƙe da naira, ni yanzu idan nace zanso ta, ko zan aureta, Aunty Aneelerh ina zan samu kuɗin ɗaukar ɗawainiyarta? Kuɗin man shafawarta dana zuwa saloon kaɗai sun isa su takaita jarin mutun balle ni da ba kuɗi gare ni ba”

tsabar dariya Aneelerh hada hawaye, shiko fuskarshi a daure yayi mata maganar bada wasa ba, ya ƙara da cewa”ƙwara na auri ƴar talaka wadda ba ta da tsayin gashi, sai yafi min sauki, in manna mata ƴar naira ɗari biyar taje gidan kitso ayi mata, man shafawa a jiki kuma Ko vaseline na siya mata ya wadatar, Iya kuɗin ka iya shagalin ka, Amma wannan Ifritun yarinyar wlh aunty Aneelerh duk talakan da ya aureta ya cuci rayuwarta, yasin ni har kotu zan Iya kai ƙarar shi, ita kanta idan ta auri talaka batayiwa kanta adalci ba fisabilillahi.

Lamarin mahboob sai addu’a, Haka ya dinga santin kyan Angel, Har faɗi yake shi ya kosa A gano su, in sha Allah zai tayasu da addu’a akan Allah ya bayyanar dasu, burinshi idan Allah yasa ta dawo gidansu da zama zai zama na hannun damanta saboda idan ta auri basarake ko wani mai ji da naira, ya dinga samun ƴan canjin kashewa.

Saboda Angel Ya manta da zancen neman zoben shi, gaba ɗaya ya ɗaura burin duniya akan Angel, harya fara ƙiyasta kuɗin da zai tatsa wurin Mijin da zata aura.

Daƙyar Aneeleerh ta samu mahboob Ya fita daga ɗakinta, ya addabeta da zancan kyawun Angel.

Alhamdulillah, a yau labarin 6acewarsu Angel ya dawo tamkar sabo a shafukan sada zumunta, ta ko’ina buga labaransu Akeyi tare da hotunansu, tun da Ont suka fara yaɗa labarin nan take sauran gidajen jaridu suka bubbuga labaran da gidan radio. Ta ko’ina zancen su akeyi kamar yau abun ya faru, labari ya dawo sabo, Yanzu shine Top story dake trending a social media, mafi yawan mutane Kyawun Angel ke ruɗarsu har su kaiga ɗaukar labarin su karanta sannan suyi share ɗinshi don ataimaka a gano su.

Fuskar Aneelerh tun safe da annuri akanta, Mutane sai kiranta sukeyi awaya sunayi mata jaje haɗi da tambayarta wasu bayanai da suka danganci Angel, a ƙarshe sunayi mata fatan Alkhairi, Numbobinsu ne akan labaran da akayi share nasu shiyasa mutane ke ta kiransu suna yi masu jaje.

Ta natsu saman mirror chair, turkish gown ce a jikinta launin maroon tayi bala’en yi mata kyau, babu mayafi akanta zallar sumar kantace
Hannunta na aruke da wayarta, tun ɗazu take maimaita karanta labarin su Angel da akayi posting ɗinsa a shafin Ont na insta

“Mommy” muryar junaid ce ta janyo hankalinta ga kallonshi, ta cikin mirror, Hajiya adama tayi mashi gayu don yau ma a ɗakinta Ya wuni, ita tayi mashi wanka, tasa Aneelerh ta kawo mata kayan shi ta santa mashi jeans da shirt fara, sumar kanshi tasha gyara.

Ƙarasawa yai gaban kujerar da take a zaune, ya daura kanshi saman laps ɗinta, ƙamshin turaren jikinsa na Hajiya adama ne da ta shafa masa
‘Wow my baby boy, kayi min kyau sosai, lallai granny ɗin nan taka tana matuƙar sonka irin wannan gayu haka da tayi maka”

Ɗaura wayar tayi gaban mirror, ta sanya hannu biyu ta ɗago da junaid ta ɗaura shi saman laps ɗinta, langwa6ar da kanshi yai saman kirjinta

“Mommy namanta ban faɗa maki ba, jiya wani mutun ya kira awaya har yace wai in faɗa maki....” katse shi tayi”yaushe aka kirani? Bana son ƙarya fa”
Muryarshi da shagwa6a ya ce “mai ƙarya fa ɗan wuta mommy, ni dai Allah ba ƙarya nake maki ba” miƙa hannu Aneelerh tayi ta ɗauki wayar, tana shiga call logs tayi arba da New number da aka kira kuma an ɗaga kiran.
“Junaid bana hanaka ɗaga min kira ba”?
Zumbura mata maki yai’to ai nayi tunanin Angel ce ke kira, kuma baki a ɗakin shine na ɗaga, kuma yace in kai maki wayar ku yi magana ni kuma naƙiya nace sai dai ya faɗamin in gaya maki” tun da ya fara magana ta ƙura mashi ido tana kallon shi, komai nashi burgeta yake yi, musamman in yasanya shagwa6a a maganar shi.

“Meyasa baka kawomin wayar ba”?
Ƙura mata ido yai ba tare daya furta kalma ba
Sam hankalinta bai kwanta da baƙuwar number da ake yawan kiranta da ita, tuntuni take ganin missed calls daga Number taƙi yarda ta ɗaga kiran don har yanzu bata daina fargabar mutanan nan da suka ɗauketa da sunan jami’an sirri.

“Junaid, daga yau karka kuskura ka ƙara ɗaga min kira kaji ko”? Ɗaga mata kai Yai alamar eh, tace”yanzu zan sanya number ɗin a black list, hankalina zaifi kwanciya’ ta yi maganar a yayin da take cigaba da daddana wayar hannunta, blocking number din tayi saida ta kammala baby junaid yace
“Mommy namanta ban gaya maki ba yace wai in faɗa maki daddyn um am....” natsuwa ta yi tana kallon shi,
“What”? Shine yace min wai ince maki daddyn ummm...” sam ya kasa tuna sunan duk ta ƙagara da sonjin ƙarashen sunan
“Kai nake sauraro ka fadamin mana”
“Wai ma daddyn.....” girgiza kai ya ɗanyi”mommy kaina ya cunkushe na manta, idan na tuna zan gaya maki”

Murmushine shimfiɗe saman la66anta, Idanuwanta akan face dinsa

“Shikenan My baby boy, yanzu faɗa mun Ina ka 6oye zoben Mahboob? Na duba cikin rigar pillow ban ganshi ba, yakamata mu maida mashi abunsa kada ayi mana kallon 6arayi”

Gatsina mata hanci junaid yai haɗi da murmura idanuwanshi yace”tab ae Allah bani bashi, Na angel ne na 6oye shi wani wuri inda ba wanda ya sani, Allah Angel zan baimawa shi, kuma kada ki fada ma kowa in baki so mu 6ata dake,”

Dariyace ƙumshe abakinta”kai junaid babu kyau fa, da guminsa ya sayi zoben taya zaka ce ba za ka bashi ba? Kana so Angel ɗinka ta sanya abun sata? Kayan haram da ba mallakin ka ba?
Girgiza mata kai yai”a’a mommy, to ai bani da kuɗin da zan siya mata wani”

Shafa sumar kanshi tayi”mommynka tana da kuɗi, zan siya maka wani but pls ka maida ma mahboob zoben shi kaji my boy”

Ɗaga mata kai yai”Toh zan maida mashi badan halinshi ba, kuma Allah idan ya ƙara cinye min chocolate ɗina saina sanya shi kuka” fashewa Aneelerh tayi da dariya, ba ƙaramin nishaɗi yake sanyata ba.

*DAULAR ALHAJI MUSA*

Ya kasa fita ko da ƙofar ɗakinsa ne, tun jiya da ya zo gidan baƙunta yake yi masu, fitowa yai daga Cikin bathroom jikinshi sanye da bathrobe fara ƙyal, ya ɗaure igiyarta a tsakiyar cikinsa daga can ciki akwai short da ya sanya, sumar kansa ta manne ma fatarsa saboda lemar ruwan wankan daya jiƙata, Dr shureim ba dai kyau ba, ta ko’ina sanyin A.c ne ke ratsa fatar jikinsa, ya ji daɗin dawowarshi gidan uncle ɗinsa baida wata damuwa, musamman tarbar da ya samu awurin Hajiya sarah, ta nuna farin cikin ganinshi kamar ɗan cikinta haka take tarairayarsa.

Walking slowly ya nufi dressing mirror Don Ya kimtsa kanshi

Gyaran muryar da aka yi mashi ne yasa shi yin saurin juyo wa baya don ganin wanene

Lokaci ɗaya ya sauke ajiyar zuciya yana kallon uncle ɗin nasa
Yana daga tsaye bakin ƙofa, kayan gym ne a jikinsa, short da riga sun ɗame jikinsa, mutumin akwai ƙira kamar ɗan wrestling.

Da fara’a akan fuskar shureim ya furta”My Uncle” yai maganar yayin da yake tunkarar shi, gabanshi sai faɗuwa yake yi ya rasa gane dalilin dayasa a duk lokacin da ya yi tozali da uncle din nashi sai yaji faduwar gaba.

Kyakkyawar fuskar Alhaji musa, mai ɗauke da ƙayataccen saje, ba murmushi sai dai yaɗan sakar mashi fuska.

“Fushi nakeyi da kai shureim baka iya takowa kazo ɗakina ka gaishe ni, ko dama jira kake inzo room ɗinka”? Cike da izza da nuna isa yake yin maganarsa.

Yawu shureim ya haɗiya”ba haka bane uncle, yanzu nake ƙoƙarin zuwa part ɗin naka”

Yamutsa fuska Yai”okey, nima na fadi ne kawai ba don wani abu ba, ko akwai abun da ka ke buƙata”?

Girgiza kai shureim yai”a’a aini ka gama min komai kawuna, nagode sosai da kulawarka agareni, Allah yabarmun kai” matsawa Alhaji musa yai dab dashi, Ya janyoshi a jikinshi yai hugging nashi tightly, in a whisper ya furta”idan akwai abun da kake buƙata ka sanar dani, idan ma baka Iya fadamin ka tura min ta text message, sannan akwai saƙo da za’a kawo maka zuwa anjima, ya ƙarasa maganar tare da raba jikinsu daga na juna.

Still face din Uncle musa ba fara’a, haka Allah ya halicce shi baida sakin fuska.

“Nagode sosai uncle, tun jiya da nazo gidan nan akayi min kyakkyawar tarba naji daɗin Hakan sosai”

“Shureim ba’ayi min godiya, next time kada ka ƙara” fuskarsa a ɗaure yai maganar
Cikin jin shakkar shi shureim ya furta”in sha Allah” ya ƙara da cewa”burina ka canza rayuwarka shureim, banason ganinka acikin damuwa, kaman ta duk wani abun da ya faru a rayuwarka, shiyasa na dawo dakai gidana saboda nasan zaka fi samun kwanciyar hankali, sannan Inaso naji ra’ayinka, bance ka bani amsa yanzu ba, nafi so sai ka natsu kayi nazari tukunna.

Jinjina kai shureim yai, idanuwanshi na kallon ƙasa, saboda ƙwarjinin alhaji musa bai iya jurar kallon fuskarsa.

“Bazan hana Ka Yin duk wani abu da za ka yi don jin daɗin rayuwarka ba, sai dai ban goyi bayan zamanka a cikin gida ba aiki ba, abu na biyu kuma Aure, kasan shi sunnah ce ta manzon Allah SAW, Aure yana ɗaga darajar mutun yazamto mai cikar kamala da natsuwa, rayuwarka zata canza idan ka yi aure, Na gaji da ganinka a matsayin tazuru” Yai maganar yana ɗaga mashi gira, da zolaya akan fuskarshi, kunyace ta hana shureim furta komai, ji yake kamar ƙasa ta tsage ya shige, Yana jin nauyin uncle din nasa.

“Da ace kayi aure da wuri da yanzu mun samu ƙaruwar babies” da sauri shureim Ya juya mashi ƙeya ya rasa ina zai tsoma ranshi, hakan da yai ba ƙaramin nishaɗi yaba kawun nashi ba
“Zeenatu ta shigo kun gaisa”? Muryarshi ƙasa ƙasa ya amsa mashi da”eh jiya tazo”

“Okey, pls, shureim inaso kana taimaka mata, Kuna fita yawo atare, still ƙanwar taka bata canza ba, sam bata da natsuwa, ni ban ta6a ganin mahaddaciyar ƙur’ani mara natsuwa irinta ba, zaka ga duk min rashin natsuwar mutun indai yana yawan karanta al’ƙur’ani natsuwa na shigarshi amma ita kullum abun nata ƙara gaba yake yi”

A hankali shureim Ya juyo ya kalle sa, mamakine ƙarara akan fuskar Shureim wai yau shine kawu musa keyi ma magana har haka? Mutumin da bai Iya surutu ba.

“In sha Allah uncle, zanyi ƙoƙari wurin ganin na taimaka mata, “ gyaɗa kai yai”haka nakeson Ji, Ni zan shiga Ciki, idan ka yanke shawara game da abunda na faɗa maka, ka same ni a ɗaki ka sanar dani ko kuma ka kirani awaya”

Amsa mashi yai da toh, sallama Uncle musa yai mashi kafin ya fuce daga dakin

Ajiyar zuciya shureim ya sauke, hannun shi ɗaya dafe da ƙirjin sa.

Lokaci ɗaya zuciyarshi ta fara tariyo mashi haukan zeenatu na Jiya, murmushin gefe fuska ya saki, aranshi ya ayyana ko ta na ina yanzu, yasan zai yi wuya ta jure rashin ganinshi.

Ai tun Jiya data bar ɗakinshi Cikin sanɗa ta nufi ɗaki akan hanya suka ci karo da Tani, Abunka game saurin kuka nan take ta ƙware mata baki tana kuka ta faɗa mata abunda ya faru

Lallashinta tani tayi tana fadin to menene aciki, Ki kwantar da hankalinki dr shureim dai ɗan uwanki

33 / 84