Kurkukun Kaddara Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Boss Bature Category :  Complete Novels

Chapter   65 / 84

192K to 195K   out of 250.5K words

ba kuwa? Kodai tsufane Ya fara kamani”?



THE GIANT SNAKE😳🔥




Tamkar Chief Owais bai ji me big guy yace ba, Hankalinshi baya akanshi, har saida Ya furta”Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un! yalla6ai maciji nake gani, gashi can Yana tafiya”a matuƙar ruɗe big guy yai maganar, sai lokacin Chief owais Ya ɗaura idanuwanshi kan narkeken macijin dake ta faman jan jiki yana bin floor, Lamarin yai matuƙar ɗaga mashi hankali, tsantsar mamaki da al’jabi ne suka kama shi, Fitowa sukayi daga cikin elevator din tamkar a mafarki suke kallonshi sun gaza motsawa, tsabar ruɗi Yasa Unaisah ta rasa inda zata tsoma kanta, Hannayenta bibbiyu ta ɗaura saman kanta ta ƙware murya da ƙarfi ta furta”wayyo Allah na, nashiga ukuna! danish dina ya koma maciji, dan Allah ku taimaka min” sautin muryarta ya karaɗe ko’ina, hatta su Ummi dake a dining saida suka Jiyota, aiko Da gudun gaske suka soma fitowa daga dining room din, Hankalinsu a matuƙar tashe suka ɗaura idanuwansu akan fuskarta kafin wani yai yunkurin tambayarta lafiya meya faru, Giant snake din Ya daka uban Tsalle Ya haura ta ƙarafunan jikin bene Ya kurɗaɗa hawa Na uku Yabi jikin bango yaci gaba da tafiya ga dukkan alamu hanya yake nema.


Tsabar firgici da tsorone Ya kama su Batul, Azeeza tuni tajima da silalewa ƙasa ta sume, Ummin america jikinta sai kerma yake Yi, tamkar wadda sanyi ya kama, batul kuwa zufa ce ta soma tsastsafo mata, Parveen tuni ta saki fitsari a cikin wando, Jikin jemimah na kakarwa ta ƙanƙame naufal ta fashe da kuka tana fadin”mun shiga uku, wannan katon abun menene, Hankalin kowa ya tashi, da rarrafe Hannah ta lalla6a ta 6oye ƙarkashin dining table.



Unaisah dake atsaye Jiki ba ƙwari sai kuka take Yi tamkar ranta zai fita, Cikin zafin rai take Fadin”Danish ne ya zama maciji dan Allah ku taimaka min banaso wani abu ya same shi, za’a iya cutar dashi nasan bakowa bane zai yarda cewa mutum ne Ya rikiɗa”

Girgiza kai Gabriel Yai, Iduwanshi akan macijin La66ansa na kerma ya furta”taya haka zai yiwu? Danish ya zama maciji? Ko a tarihi ban ta6a ji ba”!
Fashe masu tayi da matsanancin kuka”wallahi shine akan idona Ya canza halittarshi, ina maku magana kunƙi ku fahimceni, yakamata muyi wani abu akai danish zai Iya komawa prison” tana magana Hawaye nabin fuskarta, shatun Jijiyoyin wuyanta sun fito ruɗu ruɗu saman fatarta,gana saman goshinta.


Chief Owais yayi tsaye a yayin da yake bin macijin da kallo, babu alamun tsorata ko firgita atare dashi, sai dai tsantsar mamaki da al’ajabi da ruɗanin da suka kamashi, big guy Har ya yunƙura zai zaro bindigar daya soke a waist dinshi Chief Yai saurin dakatar dashi ta hanyar ɗaga mashi hannu, A hankali Ya furta”Don’t shoot him! Can’t you hear what she’s saying?

Zufa nabin fuskarshi yace”yalla6ai zai iya cutar damu, Maciji ne fa kodai baka ganshi bane”?
Batare daya dube shi ba yace”naganshi”

Gaban sune yai mugun faɗuwar ganin yadda macijin Ya haura saman taga ya faffasata Gaba ɗaya glass din Jikinta Ya zazzago ƙasa, Jami’in dake kula da cctv footage din gidan ne suka watso da gudun gaske Cikin shiga ta kakinsu, hannunsu ruƙe da manyan bindigu, kafin owais yai yunƙuri dakatar dasu tuni sun Haura upstairs, sai dai kafin suyi yunƙurin kai mashi hari, Ya daka uban tsalle Ya fado saman floor na down stairs Yabarsu atsaye can saman third floor kamar sakarkaru, Hankalin Unaisa Idan yai dubu toh Ya tashi, Agigice ta fasa ƙara tana fadin”kada ku harbeshi! Ba maciji bane mutunne! Ɗan uwanmu ne danish, dan Allah na roƙe ku kada ku kashe mana ɗan uwanmu, wayyo Allah na Ya Allah ka kawo mana dauki”

Chief Ya kasa buɗe baki Ya dakatar dasu daga yunƙurin harbin shi da suke Niyar yi, Tuni sun saita shi, Kusa atare suka fara Sakar mashi alburishi, tamkar baisan sunayi ba, saima nannaɗe kanshi da yai a tsakiyar falon, Jikin ummi na rawa ta dinga ingaza su batul cikin dining room, da gudu sajeed dasu naufal dukansu suka koma dining din, har zata rufe ƙofa Sajeed Yai saurin furta Azeeza tana awaje, fitowa yai jiki na 6ari ya cuccu6i azeeza ya shigar da ita dining room din, Ummi taja kofa ta datse, duk da haka hankalinta bai kwanta ba, zufa duk ta wanke fuskokinsu, parveen kusan sau uku tana sakin fitsari awando, ta jiƙe sharkaf, bakinta cike da donut data tura takasa ƙarasa haɗiyeshi, kowa fa yasha jinin jikinshi.

Da kakkausar murya ɗaya daga cikin jami’an isod dake acan third floor Ya daka ma Unaisah tsawa haɗi da furta”ki matsa daga nan, Ki koma cikin ƴan uwanki” Fashewa unaisa tayi da kuka tana fadin”wallahi babu inda zanje, saidai ku haɗa dani ku kashe, Nace maku ɗan uwan mu ne ya rikiɗa ba yin kan shi ba ne”

Muryarta adisashe ta ƙarasa maganar, sam bata lura da chief Owais ba saboda bata acikin hayyacinta, tayi tsaye tana faman yin shessheƙar kuka,
Umarni Chief Yaba big guy”ka kawar da ita daga gabanshi” cikin jin faɗuwar gaba Big guy ya nufi wurin Unaisah, kafin ya ƙarasa macijin Ya warware jikinshi daga nannaɗewar da yai, da wani irin sauri yake jan jiki Yana nufar ƙarshen falon inda glass door din nan take, fasa ƙara unaisa tayi har ta yunƙura zata bishi big guy yai saurin cafkota, aiko ta daddage ta gartsa mashi cizo a hannunshi azabar zafin da yaji ce tasa shi sakinta, a lokacin jami’an isod Sun watso da gudu sun sauko down Sai faman harba mashi bullets suke Yi, tsabar mamakine Yasa suka koma kokwanton macijin, da zarar harsashin ya daki fatarshi Yake faɗuwa ƙasa batare daya huɗa fatarshi ba, hakan ba ƙaramin tayar masu da hankali yai ba.

Wani irin bahagon tsalle ya daka saman glass din Ƙofar, Ya faffasa shi Yabi ta ƙatuwar huɗar daya 6ula Ya dira tacan Bayan gini, da gudun gaske unaisah tabi bayanshi, tamkar zata tashi sama, sam bata acikin hayyacinta, ba ta ji bata gani ta makance, gani take kamar hanyar komawa kurkukun ƙaddara yake nema.

Gaba ɗaya jami’an sunbi bayanshi aguje, Sai dai sun kasa cimmashi, unaisa tana gudu haɗi dayin tuntu6e har tafi jami’an sauri, duk inda ya nufa tana abiye dashi, sai faman ƙwala mashi kira take Yi tamkar ranta zaifita.........

Moving quickly Chief Owais Ya fito daga part din, Big guy yana abiye dashi, hankulan kowannansu Ya tashi, kaitsaye suka nufi Harabar ajiye motoci na gidan, wata dankareriyar mota suka nufa, Big guy ya buɗe mashi kofar ya shiga ya zauna shima Ya zauna, yai ma motar key, sai da yakusan ƙure speed din motar tamkar zasu tashi sama tsabar yadda take yin gudu direction din da macijin yabi suka nufa.............

*OBIE ESTATE🏙*

*HAJIYA SARATU❤*

A tsaye take gaban Dressing mirror, bata kaiga cire Swiss cord lace din Jikinta ba, babu mayafi akanta, hakan ya bayyana kitson zanan da akayi mata, fitowa pravin yai daga toilet jikinshi sanye da bathrobe fara ƙyal, da alama wanka Yai, sam bata lura dashi ba ta dai ji motsin mutun abayanta, amma dayake hankalinta ba akanshi yake ba shiyasa bata samu damar waigowa ta kalle shi ba, A hankali Yake ƙarema bayanta kallo, Kayan sun ɗanyi tighting dinta sun bayyana dirin jikinta, musamman faska faskan hips dinta.

Ba zato ba tsammani taji ya kwanto da kanshi saman wuyanta, ta baya ya rungumota, ya zagayo da hannayenshi saman flat stomach dinta.
muryarta tamkar tame jin bacci ta murya”pravin meye haka”?
Manna mata kiss Yai saman wuyanta,
“Ba tambayata yakamata kiyi ba, ɗazu ina kallonki cikin taro, Kin saki jiki sai tiƙar rawa kikeyi Alhazawan nan masu dogon gemu sun tsareki da mazuran idanuwansu sunata kallon jikinki”

Ɗaure fuskarta tayi tamau, tare da sanya hannayenta biyu ta damƙi hannunshi dayake ƙoƙarin ɗaurawa saman ƙirjinta.

“Kaga Bana son surutu, Yanzu na dawo cikin gidan nagaji ina buƙatar in huta,” yaƙi bari ta ƙwace kanta daga ruƙon da yai mata.

“Bansan meyasa kike Yi min haka ba! Sam baki darajani a matsayina na mijinki, bakya jin shakkar fadamin kin fita ba tare da iznina ba” a faɗace ta fusge kanta daga jikinshi ta juya tana dubanshi.

“Oh gidan Yaya hateem din ne saina nemi izinin ka zan shiga? Sai kace na tafi wata uwa duniya, ko kamanta ne? Acikin estate din nan gidanshi yake, na shiga wurin matarshi ne don mu ƙara gaisawa, shi kenan komai zanyi dole saina faɗa maka”? Ta faɗa tana jifarshi da harara, bawan Allah Ya tsare ta da ido yana kallonta, Idan tana yi mashi magana tamkar zata rufe shi da bugu

Guntun tsoki taja”ka daina kallona, ka wani tsareni da ido kamar zaka lasheni, ni bansan meyasa kake son zama ɗaki ba kamar wani munafuki, gasu baba can a falo ka shiga wurinsu ka zauna ayi fira dakai”

Shiru yai bai tanka mata ba, babu alamun zai daina kallon nata.
Ta6e baki tayi”Idan baka da abunyi ni inada shi, don haka bani wuri In wuce”

ta faɗa tana ƙoƙarin bi ta gefenshi da niyar ta tafi, ba zato ba tsammani taji ya damƙi damtsen hannunta, ruƙo bana wasa ba, har saida ta ɗago idanuwanta azare take dubanshi.

“Kidaina yi min faɗa, bafa tsoronki nake ji ba, Ina raga miki ne saboda ƙaunar da ke atsakanina dake” har saida taɗanji gabanta ya faɗi rass, ganin yadda ya haɗe fuskarshi, kwata kwata babu annuri tamkar bai ta6a dariya ba.

“Ke komai baki Iya ba dangane da zamantakewar aure? Sai kace ba mace ba? Baki Iya soyayya ba sannan baki da lokacina sai idan kinga dama zaki bani hakki na? Abu kaɗan saiki rufeni da faɗa kamar ɗan cikinki? Ko kin manta matsayina awajenki? Idan kin manta bari na tuna maki, Ni mijinki ne a ƙarƙashin ikona kike, Nafi kowa Iko dake hatta mahaifinki, Aljannarki tana a ƙarƙashin ƙafata idan har bakiyi min biyayya ba tayaya kike tunanin zaki sameta”? cikin jin ƙunar rai Ya furta hakan, maimaikon yaga nadama akan fuskarta sai gani yai ta tuntsire da dariya har fararen hakoranta suka bayyana, fisge hannunta tayi daga ruƙon da yai mata.

Ta ruƙe qugu ta matsa dab dashi kafin ta soma magana”Naji abunda kace babyn baby, sai dai akwai gyara a kalamanka, bani ce nake a ƙarƙashin ikonka ba, Kaine kake a ƙarƙashin ikona, ko kamantane, agidanmu kake zaune, cin ka shan ka suturarka dama komai nice nake kula dasu, baka da wata power pravin, babu yadda za’ai nayi maka biyayya sai dai kai kayi min saboda nina cancanci hakan, Nice hula kaine ɗan kwalin, aljanna kuma ta mai rabo ce” da wulaƙanci take furta maganar, lamarin ya ɗaure mashi kai, a iya saninshi saratu tana da ilimin addini amma idan tayi wasu kalaman ba ƙaramin mamaki take bashi ba, Ƙululun bakin ciki Ya hana ya furta mata magana, idanuwanshi sun kaɗa jawur dasu, Ranshi Ya 6aci sosai a fusace Ya juya ya fuce daga ɗakin, ta6e baki tayi aranta ta ayyana”matsalarka ce koda yake laifina ne dana auri dangin kirishna, masu bautawa soyayya” ta faɗa tana dariya.


❤🤍❤


A Zazzaune suke saman tattausan carpet, ɗan ubansu zubin kafi mage Laushi dake A cikin katafaren falon gidan baba obie, daga tsakiyar Royal sofa set din falon carpet din Yake a shimfiɗe hadadden gaske, tamkar shimfiɗar sarakuna, an kewaye bakin carpet din da tuntun, asaman su dattijon arziƙi Ya ɗaura kanshi, Prime minister Hateem Yana a kishingiɗe shima ya ɗaura kan nashi saman tuntun, Basu kaɗai bane saman carpet din akwai senate lateef tare da his excellency deen da kuma His excellency abdul Razak duk sun kishingiɗa kansu saman tuntun, kowan nan su jabbiyace a jikinshi, ta obie data hateem launi ɗayane ruwan toka, hateem ya manna farin glass a idanuwanshi hannunshi na dama hadaddiyar Agogon azurface mai kyan gaske, zobenta ne a yatsun hannun shi.
Jallabiyar sharafuddeen data his excellency deen launin brown ce, yayin data Senate lateef ta kasance milk colour, hankalinsu kwance suke shan firarsu, sun baro iyalansu a makwancinsu, yayin da su kuma suka haɗa majalissarsu afalo.

Babban tray ne aka ajiye masu kan carpet din, Saman shi Tea pot ce mai ɗauke da green tea, ga jerin kofuna, suna fira suna shan abunsu
“Baba mun cika ka da surutu ko”? Senate lateef ne Yai maganar yana duban fuskarshi.

Ɗaura hannu yai saman gemunshi tamkar yana kitsa shi Yace”Ni ai banƙi kuyita surutu ba daga yau har gobe, wallahi bana gajiya da sauraronku, Ina jin daɗin ganin ku atare dani, nayi kewarku sosai”

Murmushi kowan nan su Ya saki, In ka cire hateem daya lumshe idanuwanshi ga dukkan alamu bacci yake ji.
“Kamar yadda baka gajiya da sauraronmu muma haka bama gajiya da faranta maka,” acewar his excellency deen
lumshe idanuwanshi yadanyi hadi da jinjina kanshi
His excellency abdul razak Yace”baba, akwai wata magana mai mahimmanci da nakeson Yi dakai, tunda yanzu duk mun haɗu agaban ka, Inaga Yakamata muyi anan idan ka bani dama”!

Mayar da hankali obie Yai akan abdul razak”ina sauraronka”

“Dangane da matasan family dinmu, bai kamata mu zuba masu ido muna kallonsu ba, yakamata kowan nan su ya fidda matar da zai aura”

His excellency Deen Yace”Ni kaina abun yana damuna, wani abin ɗaure kanma Yaran tamkar basu da ra’ayin ajiye Iyali, kaga Justice namu da dr nawaz sam basu son Inyi masu zancen aure”

Murmushi obie Yasaki yana binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya.

Senate yace”har ƙwara Ziyad, idan nayi mashi maganar aure sai kaji yace inada wannan burin baba in sha Allah nan bada jimawa ba zan fidda matar da zan aura ka tayani da addu’a Allah ya bani mace ta gari”

Mai girma sharafuddeen dake sauraron yayyan nashi, hannun shi ruƙe da mug na tea da yake kur6a, da alama yana jin dadin tattaunawarsu.

Deen yace”su kuwa waɗannan ba’a maganar ƴa’ƴansu, dama ance magaji mafiyi, akansu na fara shaidar hakan” yai maganar Yana nuna Sharafuddeen da Hateem.
Gyaran murya sharafudden yai kafin ya soma magana atsanake”lamarin Owais namu sai addu’a, Ni bana gane kanshi, mace bata agabanshi, na ta6a yi mashi zancen aure sau ɗaya sai ce min yai baya son ya ɗaurawa kanshi nauyin da bazai Iya sauke shi ba”

Murmushi kowan nan su ya saki, Obie yace”kada ku takura kanku akansu, lokacin yin auran nasu ne baiyi ba, da zarar time yayi babu wanda zan saurara acikinsu sai dai kawai suji sanarwar ɗaurin auransu a masallaci”

Jinjina kai sanate Yai”baba ka kawo shawara mai kyau, mu haɗa kowan nan su da abokiyar rayuwarshi, tunda muna da ƴan mata a family namu”
His Excellency abdul razak Yace”wai Ina ɗan uwa mubarak Yaje ne”?
Senate lateef Ya bashi amsa da cewa”ɗazu dai muna zaune naji wayar shi na ruri har nace mashi ya dubata ana kiranshi, tun da ya fita har yanzu shiru bai dawo ba, wataƙil ya wuce gidanshi”
“Mu ma yakamata muje mu kwanta, mu huta” acewar deen.
Daura ido obie yai akan fuskar Hateem babu alamun Yana sauraronsu.
Gyaran murya yai mashi haɗi da zungurin kafaɗarshi da hannu, firgigit Ya ware idanuwanshi Yana faman yamutsa fuska”Idan bacci kake Ji yakamata kaje ka kwanta” girgiza kai yai”a’a ba bacci nake ji ba, Ina sauraronku”

da zolaya senate lateef yace”Oh, mu ka maida shashashu mun saki baki munata surutu ka kasa kunne kana sauraronmu, Wato kafi ƙarfin ka tanka mana”

Mai girma sharafudeen Yace”bacci yake ji fa, ba sauraronmu yake yi ba, tun ɗazu na lura dashi, baba ne Ya farkar da shi,” ya faɗa yana duban hateem”malam ka tashi kaje wurin Iyalinka ka kwanta ka huta”
Yamutsa fuska Hateem yai”Na faɗa maka ba bacci nake ji ba, idona biyu” ya faɗa yana zare mashi manyan idanuwanshi, dariya suka saki gaba ɗayansu.

Kafin wani Ya kuma furta kalma, kwatsam ba zato ba tsammani, kunnuwansu suka Jiyo masu sautin fashewar glass, Baba obie Yace”kuna jin abunda nake ji kuwa? Ko dai kunnuwana ne suka jiyo mun badai dai ba”

Senate yace”kamar fashewar glass, bari in duba” ya faɗa yana mikewa tsaye, karaf idanuwanshi suka sauka akan Giant snake din dake ƙoƙarin faɗowa ta ƙofar glass din wani ɗaki dake acan upstair hawa na Uku, ras yaji gabanshi Yai mugun faɗuwa, Muryarshi na rawa ya furta”inna lillahi wa’inna ilaihirraji’in!” Jin ya zabga salati yasa Sauran ƴan uwan nashi sukayi saurin miƙewa, tare da daura idanuwansu saitin inda senate Yake kallo, tashin hankalin da ba’a sanya mashi date, sunyi matuƙar firgita da ganin danƙareran macijin dake bin jikin bene Yana ƙoƙarin saukowa down, jikin baba obie Ya hau yin kerma abunka ga tsoho, Ido Ya raina fata, lamarin ya ɗaure masu kai, Deen yace”maciji kuma? Tayaya akai ya shigo gidan nan? ina jami’an dake tsaronshi? Wannan wani irin ganganci ne”?

Kafin wani ya bashi amsa, kwatsam suka jiyo takun tafiyar jami’an isod, da gudun gaske suke shigowa cikin falon, hannayensu ruƙe da bindigu, atare suka hada baki wurin furta”yalla6ai ku kwantar da hankalinku, zamu kawar maku dashi,” A matuƙar ruɗe baba obie yace”baku da hankali, taya akai kuka bari maciji Ya shigo gidana? A haka kuke fadin mu kwantar da hankalinmu? Kun makance ne baku ganin girman shi? tayaya zaku Iya kamashi”! Da sauri Senate ya tari nunfashinshi”baba kayi haƙuri, zasu fitar dashi, mubarsu suyi aikinsu”

Daya daga cikin jami’an yace”kayi hakuri yalla6ai ba laifinmu bane, mu kanmu bamusan tayaya akai Ya faɗo cikin estate din nan ba, babu wanda yasan daga ina Yake”

da hannu deen Ya nuna masu hanya”ku shiga kuyi aikinku” da sauri suka nufi benan.

Adaidai lokacin Unaisah dake ta faman gudu ta shigo cikin falon tana haki, duk ta fita hayyacinta, kusan atare suka ɗaura idanuwansu akanta, da mamaki akan fuskokinsu suke dubanta, kafin wani yai yunkurin yi mata magana, Chief owais Ya faɗo falon tare da big guy, sunyi mamakin ganinshi babu wanda yasan yana a ƙasar, tsabar firgici da tsoro Ya hana Obie furta sunanshi sai faman binshi Yake Yi da kallo.

Umarni yaba big guy akan ya dauki Unaisah ya maidata gida, jin

65 / 84