Author : Boss Bature Category : Complete Novels
dubanta ga dogayen benayen da tsohuwa Zafreen ta faɗa mata cewa ɗan uwanta na anan A hankali ta ke tafiya tana tunkarar benan Yayin da ta ke cigaba da karanta addu’o’in neman tsari a cikin bakinta, firgita ta yi sakamakon Jin sautin shessheƙar kukan Su Azeeza a cikin kunnanta, ta ko’ina sautin kukansu ne kamar zasu zautar da ita, Tunawa da barazanar da aka yi mata acan lokaci na farko data ta6a shigowa prison yasa ta yardarwa kanta cewa ba kukan su bane Anayi ne don a tsoratar da ita, hakan yasa ta samu ƙwarin gwiwa, Watsawa ta yi da gudu ta Haura saman benan Har ta yi tsakiyarshi Taji ya soma motsawa Matakalarshi ta dinga komar da ita baya kamar dai yadda ya faru a jiya, Gudu ta dinga yi tana haurawa, wata uwar zufa ta wanke fuskarta, daƙyar ta samu ta haye saman Second floor.
Numfashi taja tare da fetsar dashi, sai faman yin haki ta ke yi, Tsawon mintuna takwas kafin taci gaba da tafiya tana bin hanyar, wani abu daya ƙara rikitar da ita, Ginin wurin ya dinga canza mata hanyar da take bi, Sai ta yi nisa taga an dawo da ita Baya, hakan ba ƙaramin gigitar da ita yayi ba. Tarasa ina zata dosa, Tamance ma hanyar da zata bi ta isar da ita hawa na Uku, tana Cikin yin tafiyar kamar zautacciya ita kanta batasan inda ta ke jefa ƙafafuwanta ba, Cikin rashin sa’a ta faɗo cikin wani ɗaki.
Idanuwanta basu sauka a ko’ina ba sai akan wasu tsoffin mata da ke agaban manyan tukwanan girki, An ɗaura su saman murhu Wuta sai Ci ta ke, Hannuwansu ruƙe da ludayi Suna Juya naman da ke a cikin Tukunyar girkinsu, Gabanta ne ya faɗi ganin Naman mutun yatsun hannun da ta gani ne cikin romar miyarsu ya tabbata mata da cewa Naman mutunne su ke yi. farfe sun shi.
Basu lura da ita ba sai da ta daddage ta kwatsa ƙara Mai sautin gaske silar hakan Ya janyo hankulansu ga kallonta, zaro ido waje ta yi ganin sun ganta, a kiɗime ta manne ma bango ɗakin, jikinta sae kerma ya ke yi Tamkar a mafar ki ta ke kallon su.
Halittarsu gwanin ban tsoro Munanan gaske, ga Uban tamoji tamojin akan fatar fuskokin su, kamar jijiyoyin jikin bishiya ƴan rigunan da ke sanye a jikin su launin Ja Kamar yar shara ta maza da su ke sanyawa, Ga uban gashi a hammatocinsu sai ɗoyi suke Yi. a ƙalla sun kai su Shida, uban fason da ke a tafin ƙafafuwan su kamar Kwanannar Fura da ta bushe ta tsastsage.
Kamar mahaukata haka suka fashe da dariya mai sautin gaske Muryoyinsu ne suka Cika mata kannuwanta.
“Laah ga Unaiserh Ta kawo mana ziyara, yau zata sha farfesun Ƴan Ci ki, Zonan Unaisah Yarinyar mu, Zo ki sha roman nama”
La66anta na kerma ta furta”Bazanci ba, Ni ba wurin ku nazo ba, Dan Allah Ku ƙyale ni In tafi....” Tun kan ta ƙarasa maganar ɗa ya daga Cikin tsoffin ta ɗebo farfesun a cikin ludayi hada Yatsun hannun mutun, tunkaro Angel ta yi tare da miƙa mata Ludayi” Kar6i nan ƴata ki sha Roman Farfesun Mutun akwai daɗi” Tashin zuciya ne ya farma mata, a matuƙar firgice ta juya tana ƙoƙarin buɗe ƙofar ɗakin don ta gudu, sai dai kash ƙofar ta ƙi buɗuwa.
Fashewa ta yi da matsanancin ku ka tamkar ranta zai fita, da hannu ta dinga Bugun ƙofar kamar zata 6alle ta ko motsi ƙofar ba ta yi ba har sai da tsoffin nan suka cimmata, Ta ƙarfi Suka zaunar da ita tare da rurruƙe mata hannayenta da ƙafafuwanta ta yadda ba za ta Iya ƙwatar kanta ba. Tsohuwar da ke a ruƙe da Ludayin ce ta zuƙunna agabanta tare da tsoma hannayenta masu zaƙo zaƙon akaifa ta ɗebo Ƴan hanjin Cikin sai tiri suke Yi, runtse ido Angel ta yi sosai ta guntse bakinta zucuyarta na tashi kamar zata yi hauka, Bata ta6a ganin masifa ido da ido ba sai yau da Allah ya haɗa ta da tsoffin nan, Duk yadda tazo ta kufce masu abun ya faskara kamar zata haɗiyi zuciya ta mutu, Ta ƙarfi suka 6are bakinta har saida gefe ya dinga fitar da jini, baiwar Allah taji raɗaɗin azaba, duk ta ciccije la66anta da tsiya su ka dunga tura mata ƴan hanjin abakinta, don dole ta dinga haɗiyarshi da zafinshi harshenta duk ya sale haka la66anta ma sun yi suntum.
Kamar zautacciya haka tsoffin nan su ka maida ta, Sai da su ka gama azabartar da ita kafin suka saketa Anan ƙasa ta shiga kwarara amai suna kallonta suna dariya, kaf saida ta amayar da ƴan hanjin da su ka bata, wani azababben ciwon kai ya farmata, Ga jiri da ta ke gani acikin idanuwanta
“Lami ba ta ƙoshi da farfesun ba, A ƙaro mata wani” maganar su taji a cikin kunnanta, a galabai ce ta miƙe jiki ba ƙwari ta dinga bugun ƙofar ɗakin har sai da ta samu daƙyar ta buɗe ta, gudu ta ke yi jini na wanke rigar Jikinta saboda bakinta da suka sanya ƙarfi wurin 6are shi gefe ya tsage bleeding ya ke kamar jinin jikinta zai ƙare.
Baiwar Allah ga zazza6i mai zafi daya rufar mata, Jikinta sai kakarwa ya ke yi, ta gama fita hayyacinta, Neman hanyar da zata koma cikin ƴan uwanta ta ke yi saboda ta riga da ta sare da kurkukun, mutuwa ka ɗai ta ke gani acikin idanuwanta gashi ba ta son ta mutu ba tare da ta yi bankwana da ƴan uwanta ba.
Tsabar raɗaɗin da bakin ta ke yi mata ne ya jaza mata rauni da rashin kuzari a jikinta Ƙaffuwanta suka harɗe Gaba ɗaya ta kife saman floor, kanta ya daki ƙasa sosai, runtse idanuwanta ta yi yayin da hawaye ke cigaba da wanke fuskarta miryarta babu sauti take ambaton sunan ƴan uwanta tana neman taimakon su akan su zo su taimake ta, kada ta mutu ba tare da sun gana da junan su ba, Babu alamun hankali atattare da ita, sai sambatu ta ke yi ita kaɗai, Addu’o’in da ta ke ƙokarin yi yanzu sun kufce mata......
Sautin tafiya ta soma Ji kamar motsi motsi saman jikinta, a daddafe ta miƙe tana faman yin nishi, Ras taji gabanta Ya faɗi ganin wasu Girgizo kwafta kwafta a kewaye da ita, Tashin hankalin da ta shiga ne yasa ta fasa ƙara tare da yunƙurawa ta miƙe da gudun gaske ta miƙi hanya tana gudu tana waiwayon su gaba ɗaya sumar kanta mai tarin yawa ta rufe mata idanuwanta, Cikin rashin sa’a Ta 6urma cikin wani ɗaki tare da Jan ƙofa ta datse, ba tare da ta ankara da inda ta faɗo ba, Jikinta sai kerma ya ke Yi.
“Barka da zuwa Ɗakin Fiɗa, Ga dukkan Alamu mun samu wata sabuwar ma’aikaciyar” Muryar matashin saurayi taji acikin kunnanta, Tun kafin ta juya ta kalle su Jikinta ya hau tsuma, A furgice ta waiwaya tare da sanya hannu ta nannaɗe sumar kanta da ta rufe mata idanuwanta, Inna lillahi wa’inna ilaihirraji’un bakomai ne yasa ta ambaton hakan ba face Matasan ƴan matan da ta gani kwance saman gadaje kalar na marasa lafiya, zindir babu kaya a jikin su hada masu Ɗauke da juna Biyu, gwanin ban tausayi, Giants ne tsaitsaye akansu Hannayensu ruƙe da kayan theater suna acikin shigarsu ta baƙaƙen Kaya.
“Ƴar uwa dan Allah ki taimake ni, ki fitar dani daga wurin nan kada su kashe ni” waro ido sosai Angel ta yi akan matar da ta yi mata magana, Ita ce mai ɗauke da juna biyu Daga ganin cikinta tsoho ne Ya shiga wata na tara. Sun tu6e mata kaya tsiraicinsu duk abayyane, Wannan wata irin masifa ce? Hasbunallahu wa’ni e mal wakeel Lahaula wala ƙuwata Illa Billah, Allahumma ajirni fil musibati wa aklif ni khairan min ha,’ adabarbarce Angel ta ke ambaton hakan. Matar sai kuka take yi tana rokonta akan ta taimake ta ko dan saboda yaron da ke a cikinta, rushewa Angel ta yi da kuka ba tare da ta Iya furta magana ba.
Ɗaya daga Cikin Giant ɗin dake a ɗakin tiyatar ne Ya tunkarota Hannun shi ruƙe da wuƙa, Tunkan yai magana ta fahimci abinda ya ke nufi, aiko Jiki na 6ari ta juya tana ƙoƙarin buɗe ƙofar ɗakin don ta gudu, sai dai ina kafin ta yi hakan ta ji Ya damƙi hannunta, ruƙo bana wasa ba, ta ƙarfi ya dinga janta har sai da ya kai ta bakin gadon da matar nan me ciki take kwance.
Zura mata wuƙar ya yi a cikin hannunta Ya damƙe shi da nashi hannun, Ta ƙarfi ya soma ƙoƙari sanyata farke cikin matar, Kamar zata zauce saboda tsabar kiɗima har Allah ta dinga roƙo akan ya ɗauki ranta kafin faruwar hakan, Bata ta6a danasanin zuwanta duniya ba sai yau, ta yi fatan ace bata ta6a wanzuwa acikinta ba, ta yi kuka kamar ranta zai fita tayi haukan tayi borin duk abanza, ta ƙarfi giant din nan ya ɗaura hannunta saman cikin matar nan da ke ta kuka tana roƙonta akan ta taimake ta, Saboda rashin imani Ya yi amfani da hannun Angel wurin farke cikinta Kamar an fasa pipe ɗin ruwa Haka jini yadinga tsastsafowa yana wanke fuskar Angel har ta cikin bakinta ya dinga fallasa yana shiga.
Hatta jaririn da ke acikinta bai tsiri ba, Biyu suka raba shi da wuƙar, Allah sarki Angel Gani ta yi kamar ita ta aikata kisan kan, Wata irin kururuwa ta saki da iya ƙarfinta na karshe ta bangaje giant ɗin da ke a ruƙe da ta ita Amakance ta dinga Tafiya tana neman Hanyar fita, muryarta da sautin kuka ta ke faɗin.
“Nashiga Uku na bani na lalace Inalillah wa’inna ilaihirraji’in Na aikata kisan kai! na yi kisa da hannayena Shikanen Na mutu, nasan Allah ba zai ƙyale ni ba, Na kashe mashi baiwarshi da bata ji ba bata gani ba, Wayyo Allah Na......”
Yatsun hannayenta ta ɗaura asaman kanta kamar Aljanna Jinin matar duk ya canza mata kamanninta, duhu ya mamaye idanuwanta da zuciyarta.
Giants ɗin da ke Yin aikin fiɗar sai tiƙar dariya su ke Yi, Hankalinsu kwance su ke Cigaba da gudanar da aikin su, yadda su ke farke cikin mutun kamar dabba babu imani ko misƙala Zarratin.
Da wata irin raunatacciyar murya ta ke faɗin”Allah ba zai ta6a barin ku ba, Mugaye Azzalumai, Tun agidan duniya za ku fara gir6ar abunda ku ka shuka ƴan iska fasiƙai masu zuciya irin ta kafuran farko, In sha Allah Ni ce Ajalin ku, Sai kun ɗanɗani kuɗar ku sai kun gane ba ku da wayau, kamar yarda kuka sa na zubar da hawaye na in sha Allah kuma za ku zubar da naku hawayen Na jini ma, Yadda ku ka cutar dani ku ka sa na aikata kisa kuma sai an yi maku mafiyin shi......” ƙululun baƙin Cikine ya tokare maƙoshinta, silar hakan yasa ta kasa ƙarasa maganar.
Hannayen ta biyu ta sanya saman wuyanta, ta shaƙe shi sosai cikin fitar hayyaci kamar zata kashe kanta, tsabar raɗaɗin da ƙunar da zuciyarta ke yi mata ne yasa ta ke ƙokarin aikata hakan, tana a cikin wannan mawuyacin halin taji An sunkuce ta kamar Ɗiyar roba haka aka ɗauke ta sama, wani gabjejen giant ne yai mata wannan ɗaukar, fucewa yai da ita daga Cikin ɗakin Ɗauke saman kafaɗarshi bai nufi ko’ina da ita ba sai cikin wannan Ƙaton palourn Da taron matsafa su ke gudanar da Bautar su, Wasu dogayen mutane masu sanye da jajayen kaya ko’ina na jikin su arufe ya ke, sun kai su talatin, Agaban dodon tsafin su, Anan Ya sauke ta saman floor, a durƙushe ta kife kasa saboda rashin ƙwarin Jikinta, Hatta numfashinta a hargitse yake fita Jikinta yai zafi rau kamar wadda aka tsomo daga cikin wuta.
A lokacin ta kai maƙura bata iya ta6uka komai, motsin hannun mutun ta ji ajikinta, saboda duhun da idanuwanta su ka yi mata yasa ta makance, bata ganin komai, kayan Jikinta suka cire mata gaba ɗaya iya pant ɗin ta su ka bar mata, duk da bata acikin hayyacinta sai da ta shiga matsanancin tashin hankali tunawa da robar ruwan zamzam ɗin da ke a cikin wandonta, rarrafe ta dinga tana laluban suturarta don ta mayar dasu a jikinta sai dai kash bata samu damar ganin inda aka jefa mata kayanta ba. Kukan zuci ta dinga yi, duk wani motsinta akan idon matsafan, ita damuwarta ba akan tsiraicinta da suke kallo ba, robar ruwan Zam zam ce damuwar ta, Ya za ta yi idan ta rasa ta? Ita kaɗai ce damar da suke da ita.
Kunnuwata ne suka soma Jiyo mata Sautin muryoyinsu Marasa daɗin ji magana su ke yi da yaren su na matsafa gur6ataccen yare mara daɗin ji, kamar zata haukace, Lallai yau Angel ta shaida tana acikin kurkukun ƙaddara.
Ƙwaryoyin ne ruƙe a hannun matsafan masu ɗauke Da zallar Jinin mutane mai ƙarni, Layi suka jera agabanta suka tsaya tare da Kwarara mata Jinin A saman kanta, Wa’iya zubillah Numfashinta ya gauraye da Ƙarnin Jinin Nan ta ke Ta ƙara sa faɗuwa ƙasa tana fitar da numfashi sama sama, basu ƙyale ta ba sai da su ka yi mata wankan tsarki da jinin da ke a hannunsu, wani kalar Jini mai wari da ƙarni daga gani sun tsuma shi sosai, ba ƙaramin zautar da ita su ka yi ba, Kwakwalwarta bazata Iya jure abinda suke yi mata ba, Tana jin motsin hannayensu a jikinta saƙo da lungu su ke cuccuɗata kamar suna yi mata wanka, Sun goga mata najasa a jikinta sun wulaƙanta Martabar jikinta. Allah ne bai nufa Angel zata mutu ba da tuni ta jima da mutuwa lokacinta ne bai yi ba, domin kuwa warin jinin da suka yi mata wanka dashi kaɗai ya isa ya halakar da ɗan adam. Bayan sun kammala yi mata wankan tsarkin nasu na matsafa, Giant ɗin da ya kawota Ya sanya hannu tare da tattareta kamar tsumma Ya ɗauke ta, Ya fito da ita daga Cikin Falon Ya nufi Hawa Na uku da ita, ba tare da sun mayar mata da uniform ɗin ta ba, ko yatsun hannunta bata Iya motsawa, Sautin tafiyar shi ka ɗai ta ke iya ji acikin kunnuwanta, ƙofar Wani ɗaki Ya tura da ƙafarshi Ya shigar da ita, Katafaren bedroom ne na zamani kamar ba’a cikin kurkukun Ya ke ba, Da jinin jikinta da komai Ya jefar da ita saman gadon tare da Juyawa Ya buɗe ƙofar Ya fuce.
Kaɗan daga Cikin Abunda ya faru da Angel kenan A cikin Daren ranar, Shin me kuke Tunani zai biyo Baya? Bayan gaba ɗaya Shirinsu Ya tarwatse Babu alamun zata haɗu da Danish, Ko da ta haɗu dashi daƙyar ma Ta iya gane shi saboda bata a cikin hayyacinta babbar matsalar babu ruwan zamzam ɗin da zata Iya shawo kanshi, saboda kwalbar tana a cikin aljihun uniform ɗinta, Ya salam!! Wannan wace irin mummunar ƙaddarar rayuwace!!! Me zai faru da su Azeeza? Me tsohuwa zafreen zata yi masu🥺
*Boss Bature✍️ Mu haɗu Gobe Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuɗin*
First bank
3196407426,
*Bature Hafsat Muhammad, za’a tura evidence of payment ta phone number ɗina 08103884440, Banda kira whatsapp kawai*
_~*BossLadiesWriters*~_
*KURKUKUN ƘADDARA*
_The Prisoners E3🔥💫_
*Daga alƙalamin Hafsat Bature*
~Middle step~
_A heart-wrenching story of love, romance, and redemption, set against a backdrop of betrayal and cruelty💔._
A yayin da Angel ta ke A Cikin mawuyacin Hali Idan muka koma 6angaren ƴan uwanta da ke ta tsammanin dawowarta, wani mummunan abu Ya faru dasu!! Tun lokacin da suka fuskanci cewa gari ya waye bata dawo ba, Hankulan su su ka tashi matuƙa, Sun kasa fitowa daga Cikin ɗakin tsohuwa Tamira, gudun kada asirin su Ya tonu, tun da ana kallon duk wani motsinsu.
“Yanzu ya zamu Yi? Nifa ina tsoron mu fito daga ɗakin tsohuwa Agan mu dole su zargi wani abu” Deeja ce tai maganar
Haris yace”Zaman mu kuma acikin ɗakin yafi komai haɗari, Idan Giant su ka zo kawo mana abinci zasu ga babu mu aɗaki zasu Iya zargin mu”
Damuwace ƙarara akan fuskokinsu, Kowa yana tofa albarkacin bakin shi, jemimah da ke a ruke da hannun Batul idanuwanta sun kumbura suntum saboda rashin baccin da bata samu damar yi ba adaren Jiya, jikinta hada zazza6i,
“Mun tsaya muna kallon juna, Yakamata Muyi wani abu akai,” eve ce ta yi maganar, fuskokin su duk sun kumbura musamman idanuwanta saboda rashin baccin da ba su yi ba a daren jiya.
Numfasawa Batul ta yi tare da cewa”mu fita kawai” ta ambaci hakan tare da ɗaukar jemimah saman Jikinta, ƙofar fita ta nufa ta sanya hannu ta tura ta, Zura ƙafarta ke da wuya Cikin ɗakinsu Ta yi arba da tsohuwa Zafreen A tsaye hannunta ruke da sandarta fuskar nan ɗauke da murmushi, A gigice Batul ta koma Cikin ɗakin Zuciyarta na bugun uku uku, Ganin yadda ta Faɗo masu yasa su ka haɗa ba ki wurin tambayarta”Lafiya? Me yasa ta dawo”? Muryarta na ruwa ta ambaci sunan tsohuwa Zafreen!
“Wlh ita ce naganta a cikin ɗakin mu, Wayyo Allah mun shiga uku”! Cikin shessheƙar Kuka ta ƙarasa maganar, Kafin wani ya kuma cewa wani abu tsohuwa zafreen ta faɗo cikin ɗakin da su ke a ciki, A firgice Azeeza ta 6oye bayan Gabriel Jikinta nata kerma, Tashin hankali ne tsantsa akan fuskokinsu.
Ɗaya bayan ɗaya ta ke bin su da shu’umin kallon nan nata
“Halan Ƴar uwar ku ku ke Jira ta dawo”? Shiru su ka yi babu wanda Ya tanka mata,” Idanuwan su azazzare jin ta gane me su ke jira, hakan ya tabbatar masu da cewa Sun yi aran gama da Angel, Zuciyoyin su ba ƙaramin karaya su ka yi ba. Dama saida ransu ya basu cewar fitar Angel ba alkhairi bace.
Tuntsirewa ta yi da