Author : Boss Bature Category : Complete Novels
Yin bacci” Murmushi ya saki yana binsu da kallo, Haris dake zaune gefen gadon Danish ya ruƙe hannunshi a Cikin nashi ji yake kamar za a kwace mashi ɗan uwanshi.
“Meyasa Angel Jiya daya farka baki tada mu daga bacci ba? Bayan kinsan irin ƙagarar da muka Yi na son ganin shi” Hanna ce tayi maganar, Gabriel Yace”Ni dai ba abunda zance sai godiya, saboda ba zamu Iya misalta farin Cikin da muke aciki ba, Yau babbar rana ce agaremu ɗan uwanmu abun alfarinmu Ya farka da ranshi da lafiyarshi” yana daga tsaye yake yin maganar Ya goye hannayenshi saman ƙirjinshi.
“Allah sarki Rayuwa kenan, Har na tuna kokawar da Ku ka yi kaida Danish akan nace zan dire taga” gaba ɗayansu suka sanya dariya.
Batul tace”ai mu bamusan abunda ya haɗa su faɗa ba”
Parveen dake tsaye gefen Naufal hannunta ruƙe da Ayaba sai ci take Yi, Kunnuwanta akansu ta natsu tana sauraransu.
Labari Angel ta basu na abunda ya faru lokacin da zata dire taga, ba ƙaramin nishaɗi su ka yi ba.
Azeeza tace”munyi kuka lokacin sosai, Munyi tsammanin Danish ɗinmu zai rasa idonshi ɗaya, sai gashi Allah ya dawo mana dashi da ranshi da Lafiyarshi, gaskiya munji daɗi” da farin ciki akan fuskarta ta ƙare maganar, idanuwan Danish akan faces dinsu, ita da Jemamah.
Parveen tace”ni banaso muna tuna baya, nafi so inji muna magana akan abunda zai faru agaba”
Jemimah tace”Genie yaushe zamuje gidan daddyn naki? Ni na ƙosa mu koma can, waɗannan mutanan masu jan kumatun, kullum sai sun tsira mana allura a ɗuwawun mu” ta yi maganar tare da nuna ass dinta da indext finger dinta, gaba ɗaya suka tuntsire da dariya, Azeeza tace”Kai jamimah ki ji tsoron Allah, Jiya fa ba ayi mana allura ba, nurse ta faɗamin an gama yi mana ita, sai dai magani da zamu dinga sha na tsawon one month” turo mata baki Jemimah tayi
Javed yace”Kufa baku gajiya da abun magana, Kun Cika ɗan uwanmu da surutu, Ko so kuke yi ya koma baccin” atare suka zaro ido haɗi da ɗan buɗe baki”A’a wlh bamu so Ya koma bacci,”
“Alhamdulillah, Tun da yanzu mun haɗu mu dukanmu, Yakamata Muyi wa Allah godiya” Angel Ce tayi maganar, Tare da Ɗaga tafin hannayenta sama, Da sauri suma suka ɗaga nasu zasu yi addu’a, Mutun ɗaya ne bai ɗaga nashi hannun ba, Hatta Gabriel da ya ke Christian sai da ya ɗaga hannunshi don su yi addu’ar atare, Don shi a yanzu baida za6in addini, yafi ƙarfi ta 6angaren musulunci saboda Angel.
Kallon fuskarshi Angel tayi”danish zamuyi addu’a, ba zaka ɗaga hannu ba”
Girgiza mata kai Yayi alamar a’a, ɗaure mashi fuska tayi sai yayi tamkar baisan tana Yi ba
Cikin sanyin murya Haris yace”Danish meyasa har yanzu baka goyan bayan addinin musulunci”?
Shiru danish bai yi magana ba, Kuma babu alamun zaiyi ta.
Damuwace ƙarar akan fuskokinsu
“Pls danish just for today ka ɗaga hannu Muyi addu’a” Muyar Angel tamkar zata fashe mashi da kuka Tayi maganar.
Marairaice mashi fuska Azeeza da jemimah sukayi”Bro pls, let pray together,”
Runtse idanuwanshi Yai, ba tare daya buɗe su ba Ya furta”I can’t, ku daina yi mini magana akan Inyi, bana so”
Sai lokacin Batul ta sanya baki”tun da ya nuna bayaso mu ƙyaleshi, damu da shi duk abu ɗayane, ko da ace baiyi ba mu zamu yi mashi, hakan ma ya wadatar” Angel bata ji daɗi ƙin Yin addu’a da yai ba, addu’oi’ ta soma karanto masu suna amsa mata da ameen ameen, idanuwanta sun cicciko tab da ƙwalla, bayan sun Kammala kowan nan su Ya shafa saman fuskarshi, banda Angel maimakon ta shafa addu’ar da tayi saman fuskarta, sai ta shafa ma danish saman sumar kanshi, a hankali ya ɗago da idanuwanshi yana duban fuskarta, harara ta watsa mashi tare da murguɗa mashi baki, hakan da tayi ba ƙaramin ƙayatar da shi yai ba, muryarshi ƙasa ƙasa ya furta mata”thank u” ta6e mashi baki tayi”kada ka yi tunanin na damu dakai,” ƙayataccen murmushin gefen fuska yasakar mata, Su Batul sun natsu suna kallonsu.
Muryar Dr. laura ce ta katse masu hanzarinsu”Congratulation! My lovely Children Ina tayaku murnar farkawar ɗan uwan ku daga bacci, banjima da shigowa asibitin ba, dr Harry ke faɗamin cewa ɗan uwanku Danish Ya farka, wannan abun farin Ciki ne” ta ƙarasa maganar, a yayin da take ƙarasowa Gaban gadon Danish. Fararen idanuwanta dake asanye cikin farin glass ta ɗaura su kan face dinshi.
“An sanar dani cewa Baya kula kowa sai ƴan uwanshi, dagaske ne masoyiya Angel? Tayi tambayar tare da kallon Angel
Da fara’a akan fuskar Angel ta amsa mata da cewa “Jiya ne amma yau ya saki jiki, zai Iya magana da kowa”
Dr laura tace”Anya kuwa? Naga ko kallona baisan Yi, danish Ya jikin naka? Ko akwai inda ke yi maka ciwo a jikin ka”? Tayi tambayar cikin ƙagara da son jin muryarshi
Cikin raɗa Angel ta furta mashi”danish pls kayi mata magana, sun taimake mu, kuma suna da mutunci” kamar wanda akayi ma dole daƙyar ya iya motsa lips dinsa ya furta”da sauƙi babu inda keyi mini ciwo,”
Dr Laura taji daɗin maganarshi”ina fata kaci abinci babu yunwa atare dakai”? Ɗaga mata kai yai alamar eh
Ta furta”okey, amma meyasa jiya baka ba likitoci damar duba lafiyarka ba”?
A takure yake yi mata magana”saboda lafiyata ƙalau, bana buƙatar a duba ni,” Jinjina kai ta ɗanyi tayi mamakin Halinshi, basu ta6a samun patient irin shi ba.
Muryar Angel ce ta janyo hankalinta ga dubanta”Aunty, mun gode sosai da kulawarku agaremu, Allah ne kaɗai zai Iya biyanku,” tayi mata maganar ne don ta mantar da ita zancen yi ma Danish maganar duba Lafiyar Jikinshi.
“kada ki damu masoyiya Angel, aikin mun e kula da lafiyarku kuma Alhamdulillah, Naga Jiki yayi kyau Allah ya ƙara Lafiya,” ta ƙare maganar tare da kallon Azeeza da jemimah”My twins, Ya jikin naku” atare suka haɗa baki” da sauƙi” kafin ta ɗaura idonta kan Parveen da sauri ta 6oye Ayabar dake a hannunta, dariya dr laura ta ɗan saki”hmm ai na gani dama kin daina wahalar 6oye mini” duƙar da kai Parveen tayi fuskarta ɗauke da murmushi.
Kallonsu Gabriel Tayi”Ƴan samari, Jiki yayi kyau, badan sister dinku ta matsa akan son komawarku Nigeria ba, da a gidana zan killace ku, In cigaba da rainonku,” murmushi kowan nan su ya saki.
“Zan Koma Office, Ku kula mun da kanku” har ta juya zata fuce Angel tayi saurin cewa”Aunty, har yanzu sojojin basu kira ba naji su shiru basu zo sun duba mu ba”
Dr. Laura na niyar juyowa don ta bata amsa, ba zato ba tsammani, Suka hango Dr. Mark tare da dr. brown sun nufo ƙofar ɗakin, Kusan a tare suka shigo.
Gaisawa suka Yi da dr laura, Cikin girmamawa su Angel suka gaishe da su, Bayan sun amsa masu, suka tayasu murnar farkawar ɗan uwansu
Kafin daga bisani Dr Mark Ya soma Yin magana”Dr. Ke muke nema, Sojojin nan sun Kira Awaya, idan ba damuwa zamu Iya zuwa office muyi magana”
Amsa mashi tayi da toh, ba tare da 6ata lokaci ba suka fuce daga ɗakin.
Hankalin Angel yaƙi kwanciya burinta taji me zasu tattauna, fatanta Allah yasa su amince da maganar maidasu Nigeria.
Bayan fitarsu ɗakin kaitsaye office din dr Laura suka nufa, kowan nan su ya samu wuri saman kujera Ya zauna suna fuskantar Juna da ita
“Ina sauraronku, me sojojin suke ce ne”? A ƙagare ta tambayesu
Dr mark Ne ya soma kora mata jawabi”Commender dinsu ne Ya kirani awaya, Ya sanar dani cewa Chief na Isod Ya Amince zai kar6i case din Yaran....” tunkan Ya ƙarasa maganar, dr laura tasaki murmushin farin ciki
“Bayan haka, sun ƙulla Yarjejeniya tsakanin ita ummin american da su sojojin, zuwa Anjima zasu zo asibitin domin shirya yaran, zasu ɗauke su zuwa gidanta, sai dai zamuyi kewarsu saboda Commender din ya faɗamin next week chief na isod zai bar ƙasar tare da yaran” ya ƙarasa maganar idonshi Akan dr laura, mood din fuskarta ya canza zuwa damuwa, ba ta yi tsammanin zasu bar ƙasar da wuri ba, zaman da su ka yi da su na kwana huɗu ba ƙaramin sabo su ka yi da juna ba, sai dai ta wani 6angaren taji daɗi kodan saboda Angel da ta roƙe ta akan ta taimaka masu su koma ƙasarsu.
“Dr lafiya? Naga kamar yanayin fuskarki Ya canza? Ko baki ji daɗin maganar bane”? dr. Mark ne yayi maganar ganin ta haɗe fuska, Murmushin yaƙe tasakar mashi
“No ba haka bane, Na saba da yaran ne, banaso su yi nesa dani, banyi tsammanin zasu bar ƙasar da wuri ba, inaso zan nemi alfarma abar mana su ko da one month ne su yi anan kafin su tafi”
Dr brown yace”ba zai yiwu ba dr, da ace case dinsu a hannun sojojin yake zamu Iya neman alfarmar abar mana yaran su zauna a wurinmu, sai dai kash sun riga da sun damƙa case din hannun chief na isod, kuma kinsan shi ba ɗan ƙasar nan bane, A ƙasar shi yake zaune Aiki ne mai muhimmanci ya kawoshi america, tun cikin weekend daya wuce yaso barin ƙasar, saboda case din Yaran Ya fasa tafiya, yanzu haka da nakeyi maki magana, yana shirye shiryen barin Washinton zai shigo garin mu saboda ya haɗa kan yaran ya tafi dasu, mutumin babu wasa a aikinsa, Baison 6ata lokaci.
Jikin dr. laura ba ƙaramin sanyi yai ba, tana son su Angel, ganin duk ta damune yasa Dr mark kwantar mata hankali”Tafiyarsu ba yana nufin mun rabu da su ba, Kada Ki manta Sojojin ƙasarmu ne suka tsince su, bayanan su da komai Yana a hannunsu, kuma zasu cigaba da bibiyar rayuwar yaran, wannan dalilinne ma yasa suka haɗasu da Ummin america.
Gyaɗa kai Dr Laura Tayi”Ni damuwata depression din dake damun yaran, da kuma Yaron dake fama da ciwon zuciya, Hankalina bai kwanta da Ummin america ba, Shin zata Iya bamu su kulawar da zata sanya su manta da damuwarsu? nafa santa bata da mutunci macace mai izza kuma ta shahara wurin Iya karuwanci.....” Damuwace ƙarara kan fuskar dr laura, idanuwanta tuni sun ciko tab da kwalla.
“Yaran sunfi buƙatar kulawar mace wadda tasan ciwon haihuwa, bawai karuwa ba! Wadda ta saba ƙwacewa matan aure mazajensu tana fasiƙanci da su! Yakamata Kuyi tunani akan hakan, Ni zanyima Commender din nasu magana, akan su canza masu wadda zata raine su, Yara fa har goma sha ɗaya za’a damka ma karuwa, gaskiya basuyi tunani mai kyau ba, zata Iya 6ata su” ranta amuƙar 6ace take Yin maganar.
Cikin kwantar da murya Dr mark yace”ina baki shawara dr, kada kice zaki shiga maganar nan! Tun ranar da major ya kawo shawarar abata kulawar yaran, Kin nuna kuskuren yin hakan, amma sai basu damu ba, saboda sunsan halinta, kuma sunsan zata Iya ne, kamar yadda yace ta saba yi masu aiki, so bai kamata ki damu ba”
Dr brown ya ɗaura da cewa”sunfi mu sanin wacece Ita, Mu sanin da mukayi mata na karuwa ne, su kuma a matsayin ma’aikaciyarsu suke kallonta, ba zasu ta6a damƙa mata amanar yaran ba tare da sun aminta da ita ba”
Gyaɗa kai Dr Laura Tayi”Shikenan na haƙura, bazan yi masu magana ba, amma inaso zan ba Masoyiya Angel Kyautar waya, saboda inaso mudinga Yin magana da ita akai kai”
“Na fahimci kina son yaran sosai, Ni kaina na kamu da ƙaunarsu, Har na fara jin kewarsu” acewar dr. Mark
Dr brown yace”aini har ƙasarsu zan Iya zuwa ganinsu idan naso, don haka banda damuwa, muna atare da su”
Sun jima suna tattaunawa a tsakaninsu kafin daga bisani, Kowa ya koma bakin aikinsa.
*DAULAR ALHAJI MUSA*
*Dr Shureim❤*
Ƴan kwanakin da yayi a gidan Uncle ɗin nasa Rayuwarshi ta fara canzawa, a yanzu dr. Shureim baida matsalar komai, ta kowani 6angare yana samun kyakkyawar kulawa, kullum yana acikin gida, idan ya gaji da zaman ɗaki yakan fito ya zagaye gidan tare da zeenatu, yana matuƙar jin daɗin kulawar da take bashi, sun shaƙu da juna kamar sunyi shekara atare, hatta abincin atare suke cin shi, sai dai akwai wani abu da ya fara damun zeenatu, hoton da yake yawan kallo awayar shi, abun yabi mashi jiki kamar ibada, Idan ya fara kallon hoton baya so kowa yazo kusa da shi, kuma baya son kowa yasan hoton menene yake kallo, duk idan ta faɗo ɗakin shi yana cikin kallon hoton da sauri yake danna power button na wayar ya kashe ta, ta rasa gane wacece yake yawon kallo? Don ta fahimci ba ƙaramin so yake yi mata ba, gashi ita kuma Allah ya jarabceta da masifaffan kishi, ba ta son ganin yana kallon hoton, Har kuka take yi a 6oye ba tare sanin kowa ba.
A Kishingiɗe yake saman katafaren gadonshi, tun safe bai fita ko’ina ba, ko ƙofar bedroom dinsa bai leƙa ba, farin short ne ajikinsa, babu riga, gaba ɗaya hankalinsa na akan screen din apple laptop dinsa dake ajiye saitin kanshi daya ɗaura saman pillow,
Sam bai ji takun tafiyarta ba, saboda hankalinshi baya atare da shi, wankan swiss lace ne a jikinta, launin ash colour riga da skirt sunbi shape din jikinta, kamar a jikinta aka ɗinka kayan, duk da bata ƙiba kayan sunyi bala’en Yi mata Kyau, Tani da Lami ne sukayi mata Make up, hatta ɗaurin ɗan kwalin kanta sune suka ɗaura mata shi, ziririyar sarƙar wuyanta ta diamond ce, stone din jikinta sai ƙyalli Yake Yi, ta yafa gyale a saman kafadarta, hannunta ruƙe da handbag, fragrance din turaren jikinta mai daɗin shaƙa ahanci.
Hankalinta ba akwance yake ba, tun kafin ta shigo ɗakin tayi mashi sallama bai amsa bata ba, har ta gaji da yin sallamar shiyasa ta yanke shawarar shigowa don ta ga ko bacci yake yi ne
Tun kafin ta ƙaraso gaban gadonshi blue eye balls dinta suka sauka akan screen din Laptop nasa
Ras taji gabanta yai mugun faɗuwa, zuciyarta tamkar zata faso ƙirjinta saboda zafin da take yi mata, zeenatu tana da saukin kai sai dai tana da zuciya idan ta hasala, ranta ya 6aci sosai ganin abunda yake kallo, hoton da ta tsana a duniyar nan duk da batasan hoton menene yake kallo ba, ranta ya bata cewar budurwarsa ce yake kallo.
Idanuwanta sun makance, bakomai suke hango mata ba face dr shureim ɗinta rungume da mace a kirjinsa.
Runtse ido tayi da karfi ta fasa wata irin gigitacciyar ƙara wadda tayi silar firgitar da shi, da sauri Ya miƙe tare da wurga idonshi Kanta, tuni ta saki jakar hannunta ƙasa, Zafafan hawayene suka wanke fuskarta.
Hankalinshi ba ƙaramin tashi yai ba, a hanzarce ya sauko daga saman gadon ya nufeta fuskarshi da alamun ruɗu ya furta”zeenatu! Lafiya? Meya faru?
Girgiza mashi kai tadinga yi tana faɗin”kada ka matso kusa dani yaya shureim, inna lillahi wa’inna ilaihirraji’un” gaba ɗaya ta gama rikitar dashi”zeenatu ki natsu kiyi min bayani meya faru dake? Ko wani abu ne ya tsoratar da ke?
Cikin shessheƙar kuka tace”yaya shureim bazan Iya jurewaba, zuciyata zata Iya bugawa, tun ɗazu mukayi magana dakai akan zamu fita yawo atare, kace min inje in shirya kafin in dawo kaima za ka shiga wanka ka kimtsa, ashe baka yi komai ba, ko wankan ma bakayi ba, ka zauna kana kallon hotonta saboda tafi ni mahimmanci awurinka, ba tun yau ba kullum ne saina ganka kana kallonta, wai wacece wannan ne? Dame tafi ni? Numfashinta na fita da hucin zafi ta ƙarasa maganar, tare da juyawa da gudu ta fuce daga ɗakin nashi.
Hankalin shi ba ƙaramin tashi yai ba, idonshi akan bayanta harta 6ace ma ganin shi.
Dafe kanshi yai da hannu ɗaya, har cikin ranshi baiji daɗin kalamanta ba, baiso yai silar 6ata mata rai ba, duk da bai fahimci inda maganganunta su ka dosa ba, lumshe idanuwanshi ya ɗanyi kafin ya ware su a hankali, yayin da zuciyarshi ke tariyo mashi furucin da tayi mashi, yasan bai kyauta mata ba, ta ƙwalla fa rai akan son su fita tun Jiya shi da kanshi yai mata alƙawarin yau zai ɗauke ta a sabuwar motarshi su fita yawo.
Cikin sanyin murya ya furta”am sorry my zeenat, “ da sauri Ya nufi toilet don yai wanka.
*Boss Bature✍️ Mu haɗu Gobe In sha Allah Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuɗin*
First bank
3196407426,
*Bature Hafsat Muhammad, za’a tura evidence of payment ta phone number ɗina 08169856268 Banda kira whatsapp kawai*
_*💋KURKUKUN ƘADDARA💋*_
~Middle step~
سجن القدر❤🤍❤
_THE PRISONERS E23🔥💫_
*Daga alƙalamin Boss Bature*
Confusion of the heart💫
Sir mubarak ne zaune Cikin Motarshi, da su ka yi parking dinta a harabar ajiye motoci na asibitin Obinna,Tanƙameman asibiti ne Ya haɗu tamkar ba wurin Jinyar marasa lafiya ba, An zuba dukiya wurin gininsa, suna da ƙwararrun ma’aikata na gida Nigeria dana ƙasar waje.
Su biyu ne acikin motar, Shi yana a back seat na motar Ya zauna a hakimce, A yayin da Driver-operator dake driving dinsa Yana zaune saman driver’s seat kowan nan su na sanye ciki kakinsa na sojoji, sun yi shiru, Sanyin A.c din motar na ratsa fatar jikinsu, ga dukkan alamu wani muhimmin abu ne ya kawo su asibitin, akwai wanda suke Jira Ya ƙaraso, tsawon