Author : Boss Bature Category : Complete Novels
maki” magiya ya dinga yi mata daƙyar ya samu Ana ta zuba mashi abinci kala Biyar ta ɗaura masa saman dinner table na kitchen Yana ci yana santi, Musamman da ya zo kan Farfesun ganda, duk ya bi ya susuce hada siɗar hannu kamar ɗan maroƙi.
Bayan kammala sallar isha’i tun akan hanyar dawowa daga masallaci Uncle abdallah yace da abie Yana so zasu wuce idan sun koma, abie yace ba zai yiwu ba, dama ba kwana zasuyi ba? uncle ɗan Iya da ke atare da su Yace”Yaya ka ƙyale shi, sai mu ga ta ƙofar da zai fita, Dama Hajiyar shi na cikin gidan dole shima Ya shiga, Haba Abdallah yanzu ku kwaso uwargajiya sannan ka ce zaku tafi? A wani masauki zaku sauka ne da yafi namu? Uncle abdallah yace”A hotel ne zamu sauka” ya 6oye masu cewa sunyi gida a abuja, Uncle ɗan Iya na jin haka yace”ai da kuɗin hotel ɗin da zaka bayar ƙwara ka dunƙule su ka bani sai ku kwana a gidanmu dan na fahimci kuɗin ne su ka yi maka yawa” dariya suka saki gaba ɗayansu suna tafiya suna Yin fira gwanin ban sha’awa, Bayan komawarsu gidan uncle adallah da abie suka nufi ɗaki atare.
Hajiya adama na akwance saman gadonta, Har ta canza kayan jikinta daga Lace zuwa Rigar bacci, da har ta yi shirin tafiya tana jiran uncle abdallah ya dawo su tafi, sai ga mami ta shigo ɗakin, ganin tana shirye shiryen tafiya yasa ta ce da ita ina zuwa tace ae zasu sauka a hotel ne, girgiza kai mami ta yi ki ma daina faɗin hakan don ba zai yiwu ba, ga gida kuma sai ku ce zaku kwana a hotel? Hajiya adama tace”bamu son mu ɗaura maku nauyi ne, mami tace”babu wani nauyi wlh, idan ma kina tunanin ko dan saboda gidan ƙaninsa ne, to ki kwantar da hankalin ki, gidansu ne su biyu, kusan ma rabi da kwata na abunda aka kashe a ginin da kuɗin abie ne, Allah ne bai nufa zamu dawo nan ɗin ba, sai daga Baya da ya samu ƙarin matsayi awurin aiki kin ji yadda akai muke zaune agidan, na faɗa maki ne don ki kwantar da hankalin ki, idan da kara ae gidan surukai gidan ƴan uwana ne tun da anzama ɗaya, Ga ɗan jikanmu junaid ya ƙara mana danƙon zumunci”
maganar Mami ce tasa hajiya adama fasa shirin tafiyar, mami bata jima da fita daga ɗakin ba Kiran uncle abdallah Ya shigo wayarta, ko da ta ɗaga kiran sanar da ita yai game da fasa tafiyar su sai zuwa gobe, hankalin ta ya ƙara kwanciya, ba tare da 6ata lokaci ba ta canza kayan jikinta zuwa na bacci, tana shirin kwanciya, muryar Aneelerh daga waje ta katse ta, sallama tayi mata, hajiya adama ta amsa mata da wa’alaikum salam, Suruka ta gari shigo ciki mana’
cikin Jin kunya Aneelerh ta turo ƙofar ɗakin hannunta ɗauke da baby junaid, saukowa yai daga jikinta da gudu ya nufi hajiya adama tana dariya ta ɗauke shi kafin ta zauna gefen gadon tana shafa sumar kanshi, ganin Aneelerh na ƙoƙarin zama daga ƙasa yasa ta katse ta da cewa”ki Zaune gefe na, Muyi fira” komawa gefen gadon aneelerh tayi
“Mommy barka da dare, Ya gajiyar tafiya”?
Hajiya adama tace”ai Gajiya tabi jiki tun da na ga jikana” shiru suka ɗanyi kafin Hajiya adama ta ce”Ya haƙurin rashin da mu ka yi”? Duƙar da kai Aneelerh ta ɗanyi, a duk lokacin da aka yi mata maganar 6acewar su tajudden tamkar an fama mata mikin dake acikin zuciyarta ne, nan take hawaye suka cika idonta, Muryarta na ɗan uwa ta furta”Haƙuri an gode Allah, muna ta binsu da addu’a,”
“Ko akwai wani abu da ku ke shiryawa ne game da 6acewarsu”? Jinjina kai Aneelerh tayi”Eh mommy, dama na jira ne sai kun huta mu yi magana.....” gaba ɗaya Aneelerh ta kwashe komai dangane da tada zancen 6acewar su Uzair ta labarta mata, annurin da ta gani akan fuskar Hajiya adama ne Ya tabbatar mata da zata samu goyon bayanta,
“Kunyi tunani mai kyau surukata, Naji daɗin shawarar da zahra ta baki, Yarinyar tana da hankali, duk cikinmu babu wanda yai tunanin tada zancen, idan har akaci nasara silar shawarar da ta bada, Na yi mata alƙawarin kyauta ta musamman” Ba ƙaramin daɗi Aneelerh ta ji ba, Mommy adama ta ɗaura da cewa”In sha Allah zamuyi magana dashi abdallahn dangane da tada zancen, sannan zamu bada tamu gudummuwar, fatana Allah ya dafa mana, Ya dube mu da idon Rahma, Ya bayyanar mana da su idan suna a raye, ko da basa a raye da buƙatar muji meya faru da su”! Cikin girmamawa aneeleeh tace”In sha Allah zamuyi nasara mommy, saboda bana son in rasa surukai na gari irin ku” Sam batasan Ta furta hakan ba, Dariya Hajiya adama ta yi”Nima ai bana so na rasa suruka ta gari irin ki Aneelerh, domin kuwa zai yi wuya asamu tamkar ki,” cikin jin kunya aneelerh ta miƙe tana faɗin”Bari na kawo maki abun sha” bata jira amsarta ba, ta yi saurin Juyawa ta fuce daga ɗakin, Bayan fitarta Hajiya adama ta dubi Baby junaid dake kwance saman ƙirjinta, Ya tsareta da ido, tun da suka fara magana bai tanka masu ba, ya kasa kunne yana sauraronsu, sai yanzu ya samu damar yi mata magana
“Granny kinsan Angel” jinjina mashi kai tayi”nasanta mana, Inason Angel sosai” marairaice mata fuska yai tamkar zaiyi kuka”baiwar Allah Angela ɗina, Mommy ta faɗa min da ita da daddynta da daddyna sun 6ace, ni tsorona ma kada ace 6era ne ya cinye su ba....” Zaro ido Hajiya adama tayi can kuma sai ta tuntsire da dariya
“Granny, mommyna kusan kullum sai ta yi kuka saboda su angel, ƴar baiwar Allah, mami ta hanata Yin kuka amma bata Jin maganarta, sai da nayi mata faɗa, na nuna mata raina ya 6aci tukunna ta daina” sosai hajiya adama ke yin dariya, Sambatu iri iri junaid ke yi mata ba ƙaramin nishaɗi ya ke sanyata ba,
“Gobe akwai school junaid, mu kwanta mu yi bacci” maƙe mata kafaɗa yai”Ina tsaraba na”?
“Nayi maka amma sai gobe zan baka, nafi so ka huta yanzu muyi bacci” amsa mata yai da toh mu jira mommy ta kawo mana abun sha ko? in mun sha sai mu kwanta,
Turo ƙofar ɗakin Aneelerh tayi hannunta ɗauke da cup of coffee asaman table ta ajiye mata shi, Godiya hajiya adama tayi mata, daga nan su ka yi sallama da junansu Aneelerh ta fuce,
Atare da junaid suka sha coffee ɗin Bayan sun kammala, Hajiya adama Ta kwantar dashi ta tottofe shi da addu’a, sauka tai daga saman gadon ta nufi switch ta kashe hasken ɗakin, kafin ta dawo ta hau gadon ta rungume jikallanta aƙirji, ahaka bacci ya ɗauke su
****JOS CITY MUN WAYI GARI LAFIYA AGIDAN ALHAJI UBAID*******
zazzaune suke a saman dining suna Yin breakfast A tsanake shiru baka jin sautin komai saina cokulansu, kwas kwakwas kamar zasu fasa plates ɗin, sun natsu suna tura abinci a cukunnansu, Alhaji ubaid na sanye da Jallabiya Hajiya Laila dake agefensa arab gown ce a jikinta launin royal blue ansha uban make up, Alhaji musa ya ɗauki wankan tsadaddun suit sun zauna mashi, mutumin fa akwai kyau kamar shi ya tsara kanshi ya iya ɗaukar wanka ga aji, daga gefen shi Dr shureim ne cikin shigarshi ta gado wato Kayan larabawa, daddaɗan ƙamshin turarensu mai daɗin shaƙa, musamman turaren Alhaji musa fragrance ɗinsa na dabanne. A hankali ya ɗan ɗago yana duban shureim ya lura ba abincin ya ke ci ba, tun da suka zauna yake ta faman jujjuya spoon ɗin hannun shi acikin plate ɗin gabanshi, gyaran muryar da Alhaji musa yai mashi ce tasa shi ɗagowa ya kalle shi
Cikin kulawa ya ke yi mashi magana”meyasa bakasan cin abinci shureim? Na lura tun shekaran Jiya da nazo gidan nan baka ci wani abun kirki ba” Hajiya Laila ta ɗan dakata da cin abincin fuskarta a yamutse take kallon alhaji musa aranta tace”ji wani ikon Allah ko’ina ruwanshi da cin shi da shan shi? Ni narasa gane shisshigin nan da yake yiwa shureim, mutumin da bai damu da shi ba, sai yanzu ne yasan da zaman shi’
Cikin sanyin murya shureim ya kalli uncle ɗin nashi”ina ci mana, kawai ni nafi sha’awar abincin hausawa ne wannan baya min daɗi abaki” Alhajin ubaid yace”Meyasa tuntuni baka yiwa zainab magana ta girka maka ba? Kamar ba ka da bakin magana, komai naka ya zama na shiririta shureim so ka ke ka koma yaro”? shiru shureim yai shi kanshi haushin rashin ƙwarin gwiwarshi yake ji, ya koma kamar wani sakarai komai sai yadda akayi da shi.
“Kada ka damu Yayana, da zarar mun koma abuja zai dawo asalin Dr shureim ɗin da ka sani ne, Kasan matata ta iya bada tarbiya zata gyara maka ɗanka ya zama namijin gaske”
Wannan maganar ta Alhaji musa tayi matuƙar ƙona ran Hajiya layla, har dai tagaza jurewa
“Me kake nufi? Ni ban iya bada tarbiya ba kome”? Ko kallo bata ishe shi ba saima Ya ɗauki glass ɗin lemu mai sanyi yakai baki Yana kur6a.
“Haba layla, meyasa bakya iya 6oye fushin ki ne? Laifine don ya yabi matarshi? Harara ta wurgawa Alhaji ubaid tamkar ƙwayar idon zata faɗo kasa
“bansan meyasa kake goya mashi baya ba, idonka ya rufe kwata kwata baka ganin laifin shi, wannan ba adalci bane” rai a6ace ta ƙarasa maganar tare da buga table din, A fusace ta miƙe tabar dining ɗin
Miƙewa shureim yai da niyar yabi bayanta da sauri Alhaji ubaid ya dakatar dashi”dawo ka zauna” komawa yai ya zauna
“daddy bana jin daɗin hakan, kasan halina tunfil azal bana so inga ran wani daga cikin ku ya 6aci” Shureim ne yai maganar
“ka kwantar da hankalinka, In sha Allah zan sasanta tsakaninsu, Yanzu zan shiga wurinta in lallasheta” Yai maganar tare da miƙewa yabar dining din bayan tafiyar Ubaid Alhaji musa ya ɗago ya kalli shureim
“You should start preparing, Ƙarfe shabiyu zamu bar jos, already nayi magana da pilot ɗina, bana buƙatar ka tafi da komai naka, Duk wani abu da za ka buƙata za’ayi maka acan” murmushin yaƙe dr shureim ya ɗan saki
“in sha Allah Uncle yanzu zan shiga ciki In ƙara shiryawa” amsa mashi Yai da toh, Kafin miƙewar Dr shurem P.a Ɗin Alhaji musa yai sallama daga wajen palourn, Hakan yasa shi saurin miƙewa cikin takun izza ya nufi ƙofar fita daga palourn
Ajiyar zuciya dr shureim ya sauke, shi kanshi shakkar Alhaji musa yake ji, mutumin babu wasa a harkarshi.
*Boss Bature✍️ Mu haɗu gobe Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuɗin*
First bank
3196407426,
*Bature Hafsat Muhammad, za’a tura evidence of payment ta phone number ɗina 08169856268 Banda kira whatsapp kawai*
_~*BossLadiesWriters*~_
_*KURKUKUN ƘADDARA*_
_The Prisoners E13🔥💫_
*Daga alƙalamin Boss Bature*
~Middle step~
_A heart-wrenching story of love, romance, and redemption, set against a backdrop of betrayal and cruelty💔._
Juyawa yai da sauri ya nufi kitchen maimakon ɗakin shi, Yana shiga ya ci karo da zainab tana goge tiles da floor wiper sam bata lura dashi ba, har saida yai mata sallama tukunna ta ɗago suka haɗa ido
Fara’a ta sakar mashi”shuraim tun jiya na ke son yin magana da kai, fargaban Iyayenka ta hanani tunkarar ka” ƙarasa shiga kitchem ɗin yai
“Aunty zainab Ya zamuyi? Uncle musa ya matsa min akan saina bishi abuja, ƙarfe sha biyu zamu bar jos, “ dafe kai ta yi da hannu ɗaya
“Naji takaicin jin haka shureim, Duk plan ɗin da muka shirya ya tashi abanza kenan”
Girgiza mata kai yai”in sha Allah komai zai tafi dai dai aunty zainab, ko da ace bana nan that will not change anything”
Damuwa ce cunkushe akan fuskarta
“How ka ke tunanin komai zai tafi dai dai bayan bamu a wuri ɗaya”?
murmushin gefen fuska ya sakar mata har dimples ɗinsa suka lotsa.
“Kin manta da waya? Ina da ita kina da ita, zamu dinga yin communicating da junanmu, hakan ma zai fi ba tare da wani ya zarge mu ba” ƙayataccen murmushi zainab ta saki
“Allah ya yi maka albarka shureim ni sam na manta da waya, amma fa zan yi missing ɗinka sosai mutumina
Murmushin fuskarshi bai washe ba yace”Ni kaina zanyi missing ɗin auntyna mai share min hawayena, amma in sha Allah zamu dinga yin waya akai akai, Inaso komai da ke faruwa a gidan nan kidinga sanya min ido, da zarar an samu update ki kirani awaya ki sanar dani, amma fa sai kinyi takatsantsan kinsan Iyayen nawa ba ƙananun mutane bane”
jinjina kai Zainab ta yi don ta gamsu da bayanin shi
“In sha Allah zan kiyaye shureim, kaima ka kula min da kanka, “ idanuwansu duk sun ciko da ƙwalla, don ba ƙaramin ƙaunar juna su ke yi ba, tana jinshi tamkar Ɗanta, shima Yana jinta tamkar mahaifiyarsa, sun jima a kitchen ɗin sunayin magana kafin daga bisani yai mata sallah.
Ba tare da 6ata lokaci ba, Dr shureim Ya fara shirye shiryen tafiya abuja, bai canza komai na suturar jikinsa ba, Iya turarurrukansa kaɗai ya feshe jikinsa, sannan ya warware Ɗaurin larabawan dake akanshi, Ya sharce lallausar sumar kanshi Ya gyarata tsaf yabi da mayukansa ya shafe ta, Kafin barinsa ɗakin saida yai Nafila Ya roƙi Allah da ya tsare shi ya kare shi daga sharrin mutun sharrin zuciya da duk wani abun cutarwa, ya kuma roƙi Allah da ya sa silar komawarshi gidan uncle din shi abuja rayuwar shi ta canza ya dawo kamar yadda yake ada, addu’o’i sosai shureim yayiwa kanshi, Bayan ya kammala ya zaro memory ɗinshi da ya 6oye a cikin rigar pillow ya zaura shi awayarsa, Hankalin sa Ya ɗan kwanta zai samu natsuwar cigaba da kallon hotunan Abar ƙaunarsa awayarsa.
A gefen gadon shi ya zauna yana daddana wayar shi, Lokaci ya ke jira ya cika.
**DAULAR OBIE ESTATE**
A Hankali Jigunannun Motocinsu su ke kunno kai saman shantalelen titin obie estete, gaba da baya Sojoji ne ke tafiya akan ƙafafuwansu, Hannayensu ruƙe da bindigu, Motar farko mallakin Sir mubarak ce, motar dake a biye da ita zungureriya ƙirar Navigator limousine wadda cikinta tamkar bedroom ya ke saboda tsabar haɗuwarta, Dattijon arziƙi ne hakimce acikin motar tare da Jikokinsu tagawaye zain da zaid sai Dr Jazz shalelensa, Motar da ke abiye da tasu Danƙareriyar gaske mai numfashi mallakin Senate president Lateef Obinna ce, Yayin da motar ƙarshe Ta pravin Obinna ce, gayu mutanan Allah su kansu motocin da dattaku ake yin driving ɗinsu a tsanake cikin ƙwarewa, sautin karatun kur’ani mai girma ne ya karaɗe ko’ina, Ƙirar Ahmad suleiman mai matuƙar ratsa sassan jiki, daga motar dattijon arziƙi ƙirar ke fitowa, ƙa’ida ne a lokacin da suka fito zasu tafi masallaci sai yasa an kunna masa ƙirar Ahmed suleima haka zalika idan zasu dawo daga masallaci sai an kunna masu karatun wani sa’in Idan ƙirar takai mashi karo har bi yake yi yana lumshe ido, A yanzu haka dawowarsu kenan daga masallacin Juma’a.
Sannu A hankali su ke tunkarar Moto park ɗinsu, kusan atare motocin suka Yi parking at same time, Da azama sojoji su ke bubbuɗe masu mota, A hankali Obie Ya sauko ƙafarshi dake sanye cikin takalma kalar na sarakuna, Jikinsa Jallabiya ce daga sama Ya ɗaura alkebba haɗaɗɗar gaske sai ƙyalli ta ke Yi, ɗaya bayan ɗaya su ke fito daga Cikin motocin, gaba ɗayansu haɗaɗɗun Jallabiyoyi ne a jikin su daga Iyayen Har ƴa’ƴan.
“Mu shiga ciki ko”? Obie ne Yai masu maganar, Zaid da zayn Sai faman sunnar dakai ƙasa suke yi kamar marasa gaskiya, mamakin hakan yasa Mahaifinsu pravin tanka masu
“Lafiya”? Kafin su yi yunƙurin bashi amsa Sir Mubarak ya tari numfashin su
“Zaku ci ƙaniyarku ne, ƙananun Ƴan iska masu kwana da wando, har ni zaku dinga kakkaucema wa? Kun raina ni ko”? Fuskar shi a ɗaure ya ke yi masu magana, sir mubarak mutunne mai fusatacciyar zuciya abu kaɗan ke hasala shi sai da ta wani 6angaren yana da sauƙin kai.
Dr jazz Yana ruƙe da hannun Obie dariya ce ƙumshe abakinsa, ya ƙi bari ta kubce masa gudun kada Ya ji saukar mari daga Sir mubarak, Twins kuwa Duk sun sha jinin jikinsu sai faman noƙe kai suke yi haɗi da sosa ƙeyarsu.
A fusace Ya daka masu tsawa har saida suka ɗan razana atare su ka ɗago da fararen idanuwansu akan fuskarshi” Ina magana kuna kallona? Saboda tsabar fitsara”? Da sauri suka sunnar da kawunansu ƙasa, Alkunyace ta hana Pravin sanya baki, Gyaran murya senate Lateef Ya yi ma ɗan uwan nashi, Ya juya yana duban shi, cikin muryan Manyantaka Ya soma magana
“Aymasu afwa, Yarane su har yanzu, basu mallaki hankalin su ba, Sai ana haƙuri da su”
girgiza kai Sir mubarak yai”Pls ka daina wannan maganar, Yara sun balaga kana faɗin basu mallaki hankalinsu ba”? Juyawa yai tare da kallon su twins muryarshi a kausashe yace”Dagaske baku mallaki hankulan ku ba”? Har suna haɗa baki wurin furta”wlh mun mallaki hankalinmu, pls Ka yi haƙuri Uncle mun gane kuskurenmu zamu gyara in sha Allah, Dan Allah daddy ka bashi haƙuri wlh ba zamu ƙara ba” A marairaice suke kallon Mahaifin nasu pravin, Shi dai Obie bai tanka masu ba, murmushi ne ɗauke akan fuskarshi.
“Za ku Yi bayanine, muddin Owais ya dawo ƙasar nan zan sanya shi Ya ba ku horon isod, Ni dama can ban Goyi bayan aikin Company da ku ke zuwa yi ba, saboda ba ku iya komai ba” Zaro ido waje su ka yi jin abunda yace Hankalinsu ya tashi matuƙa, saboda suna mugun tsoron training ɗin Isod har ƙwara abasu horon aikin Soja,