Author : Boss Bature Category : Complete Novels
and other hair removal services.
Bayan ta kammala rubuta sakon a ƙalla saida ta maimaita shi yayi sau ashirin gudun kada ace tayi kuskure kafin ta tura mata, fuskarta ɗauke da murmushi ta ajiye wayar saman pillow, ta miƙe ta nufi falo domin Yin breakfast, fatanta Allah yasa Hajiya saratu ta mayar mata da martanin saƙon da wuri, taci buri sosai akan zuwa estate dinsu, ko dan ta haɗu da Owais idan Allah yasa lokacin ya dawo ƙasar.
*KURKUKUN ƘADDARA*
*AN YANKA TA TASHI☠️👹*
Babban ɗakin tarone mai girman gaske, wanda akeyiwa laƙabi da fadar matsafa, Mallakin shuwagabannin kurkukun ƙaddara, ta ko’ina manya manyan matsafane maƙil acikin fadar, zazzaune saman kujeru dake a jere tsakiyar fadar, kowannansu yana sanye cikin shiga ta baƙaƙen dogayen riguna masu huluna, sunyi 6adda kama ta yadda mutun bazai ta6a Iya ganin koda ziririn gashin kansu bane, Hannayensu da ƙafafuwansu baƙaƙen safunane, Yayin da fuskokinsu sun sanya masu mask me suffar ƙwarangwal gwanin ban tsoro, saƙo da lungu ta fadar, Wasu Gabza gabzan giants ne daga masu ƙaramin miƙami har izuwa manyansu masu star uku a gaban kakinsu, wata irin ƙira garesu mai matuƙar ruɗarwa, rikitarwa da razanarwa da kuma tsoratarwa, kallonsu kaɗai zai Iyasa zuciyar mutun ta buga, Ga tsawo da Allah yayi masu tun daga kan tsayuwarsu zaka tabbatar babu ɗigon imani akansu.
Daga can saman karagar fadar, wasu jigunannun arm chairs ne guda shidda ƴan ubansu, mutane shiddan dake zaune saman kujerun dogayen rigunane launin jajaye na maza a jikinsu masu huluna, baka ta6a Iya tantance suffarsu saboda sun 6oye ko’ina na jikinsu, hannyensu na ruƙe da Sanda wadda aka ƙerata da zallar zinari, daga gabansu zungureran teburi ne, samanshi maƙil Yake da kayan ciye ciye dana shaye shaye daga ciki hada Jinin mutun da farfesun naman mutun ga zungura zunguran kwalaban giya, da Kayan marmari nau’i kala kala, da gasasshen nama na dabbobi daban daban.
Komai na fadar matsafan tun daga kan ƙofofi da tagogi da fentinta da jan carpet din dake shimfiɗe ƙasanta, gaba ɗaya Launin baƙi da Ja ne, saman rufin fadar wasu haɗaɗɗun fitilune masu haskaka cikinta.
Zanunnukan dake a jikin bangon fadar, na kan ƙwarangwal ne, da yatsun hannun shaiɗanu masu akaifu zaƙo zaƙo da sauran zanunnuka masu ban tsoro.
Daga gefe ɗaya tacan 6angaren da Arm chairs din nan suke Tanƙameman madubine wanda suke Kira da Allon tsafi, gaba ɗaya Hankalin matsafan yana akan Allon tsafin nasu, fadar tayi tsit tamkar mutuwa ta gifta, ga dukkan alamu wani abu suke kallo wanda yai silar ɗauke masu hankulansu..........
(Nima kuma na ɗauke alƙalamina)
*Boss Bature✍️ Mu haɗu Monday Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuɗin*
First bank
3196407426,
*Bature Hafsat Muhammad, za’a tura evidence of payment ta phone number ɗina 08169856268 Banda kira whatsapp kawai*
_~*BossLadiesWriters*~_
_*💋KURKUKUN ƘADDARA💋*_
~Middle step~
_The Prisoners E21🔥💫_
*Daga alƙalamin Boss Bature*
A ƙalla sun shafe mintuna suna kallon Allon tsafin, ga dukkan alamu sun girgiza da ganin abun da idanuwan su ke gane masu, Hankulan su sun yi matuƙar tashi, abun ya yi mugun ɗaure masu kai, bakomai bane suke kallo acikin Allon tsafin face Garkuwar kurkuku tare da Angel, duk wani motsinsu akan idonsu tamkar video haka suke ganinsu, lokaci ɗaya Allon tsafin yayi duhu hoton fuskokin su ya 6ace.
Kowan nan su ya sauke Ajiyar zuciya, sun natsu suna jiran jin bayani daga bakunan shuwagaban nin su.
Ɗaya daga cikinsu ne yai gyaran murya, da wata irin kakkausar murya mai sautin gaske tamkar bata mutun ba, ya soma Yin magana Cikin harshen su na shahararrun matsafa ni kuma ina fassara maku.
“Wannan ne Karo na farko da muka yi babban kuskure arayuwar mu, wanda idan bamu miƙe tsaye mun nema ma kanmu mafita ba, to tabbas za’ayi nasara akan mu, Ko a tarihi ba’a ta6a samun prisoners ɗin da suka tsira daga kurkukun ƙaddara ba, su ne na farko kuma sune na ƙarshe, da farko sunyi nasarar ƙetare kurkuku da taimakon Garkuwarmu, Na biyu sun ku6uta daga dajin evil forest da taimakon shi, Babu wani mahaluƙin da ya isa ya iya ƙetare kurkuku da dajin evil forest salin alin ba tare da ya Rasa ranshi ba, amma saboda suna atare da garkuwar prison mun rasa cin galaba akansu saboda mu kanmu bamu isa mu Iya ja da shi ba, babu wata muguwar halittar data Isa ta tunkaresu muddin Yana atare da su, rashin baccin da baiyi ba shine Yaja har muka gaza tunkarar su, lokacin da baccin Ya ɗauke shi munyi nasarar yi mashi abunda ya dawo gare mu sai dai wani abun al’ajabi ya ku6uta daga hannunmu Ya koma ma gangar jikin shi, kamar yadda kuka gani a allon tsafin mu, shin me ya jawo hakan”? Yai tambayar yayin da yake gyaran zaman shi.
Mutumin dake a gefenshi, Ya ɗaura da cewa”Yarinyar da ke atare da shi itace silar komai, kamar yadda yazo mana a allon tsafin mu, Cewa itace za ta yi silar tarwatsa tarihin kurkukun ƙaddara, gangancin da mu ka yi shine Haɗa su wuri ɗaya da garkuwar mu, sakamakon shaƙuwar da sukayi a tsakanin su, taja shi ga faɗawa tarkon sonta, mu kan mu bamu ta6a tsammanin Garkuwar prison zai Iya kamuwa da matsanancin so irin haka ba” dakatawa yai da yin maganar yana motsa yatsun hannunsa, kafin ya cigaba da cewa
“Sai dai har yanzu bamu rasa power ɗinmu ba, Garkuwa namu ne har abada, mu ke ruƙe da masarrafin da zamu Iya sarrafa linzamin shi, mu kaɗai ne mu ke da iko da shi, ba zamu ta6a yin danasanin Ɗaura shi amatsayin magajin kurkukun ƙaddara ba, kuskure ɗaya da muka tabka shine sakacin da mu ka yi da har ya samu nasarar guduwa daga kurkuku, Ni ban damu da sauran Yaran da suka ku6uta ba, saboda basu da amfani a wurinmu, mun ci moriyar su, mutun ukun ne sune rauninmu, Na farko Garkuwarmu dole sai da shi za’a Iya Cin galaba akanmu, Na biyu ƙaddarar kurkuku, yarinyar ta fi sauran hatsari tun da har ta Iya Jan hankalin garkuwarmu, wanda nayi imanin da ace babu ƙauna a tsakanin shi da yarinyar ba zai ta6a taimakon sauran ƴan uwan shi don su gudu daga tarkon mu,” Ya faɗa yana mai jan dogon numfashi Ya fetsar da shi, ya cigaba da faɗin “Itace silar komai, kuma itace kaɗai zata Iya sarrafa shi bayan mu, idan kuwa hakan Ya faru zai Iya fallasa mana sirrin mu ya kuma taimaka wurin ruguza kurkukun ƙaddara”! Da ƙarfi Ya ambaci hakan Yana mai nuna fusatar shi.
“Yarinya ta ƙarshe itace bugun zuciyar kurkukun ƙaddara, kamar yadda ya zo mana a allon tsafin mu, idan har muka samu nasarar Cire Zuciyarta daga ƙirjinta zamu samu ƙarfin Iko fiye da wanda muke da shi a yanzu, Ita kuma ƙaddarar kurkuku dole mu dawo da ita cikin mu idan har muna son ta zamar mana ƙaddara mai kyau, barin ta awaje shi zaisa ta zamto mummunar ƙaddara agare mu” Tamkar mayunwacin zaki haka yake kora masu jawabi yana fitar da huci.
Bayan ya rufe baki Na gefen shi ya soma magana da wata irin murya ta dattawa waɗanda suka Shahara a fagen zalunci.
“Tun fil azal, Banso Muka damƙa amanar mu ga tsohuwa tamira ba, dama tun lokacin Sai da na musa akan hakan, Ni dama nasani Jinin Habibullah ba zasu ta6a zama amintattun mu ba, sai gashi sun yaudaremu sunci amanar kurkuku, sun kashe mana Zafreen ɗaya daga cikin shuwagabannin mu, babu wanda ya ta6a tsammanin zasu Ci amanar mu ita da ɗanta Salsabeel, sai da suka bari mun basu yarda mu su kuma suka butulce mana, haƙiƙa Nayi takaicin rasa gangar jikin tamira, da ba abun da zai hana mu azabtar da ita, mu sa6ule naman jikinta sannan muyi farfesun shi muba ma Karnuka su shanye roman, amma duk da haka bamu makaro ba, Zamu huce haushin mu akan ɗanta Salsabeel” mutumin da yayi maganar babu ɗigon imani akansa.
Bayan ya dasa aya a maganar shi, wani daga cikin shuwagabannin Ya numfasa tare da cewa”Garkuwa ya yi mana mummunar 6arnar da ba zamu Iya gyarata ba, bamu ta6a tsammanin zai Iya yi mana haka ba, sai dai ba zamu Iya hukunta shi ba, saboda shi jinin mu ne, abu ɗaya da zamu Iya yi mashi shine mu hana shi jin daɗin rayuwarshi da Yarinyar, mu shiga tsakaninsu, horon da zamu bashi kenan, sannan zamu ci gaba da sarrafa shi wurin azabtar da mutane, kafin muyi nasarar dawo da su Cikin mu, hikmar yin hakan mutane zasu fara tsoranshi suna nuna mashi ƙyamata, zai ji duk duniya kamar ba’a sonshi ne, kunga anan zai yi tunanin mu kaɗaine gatanshi, kurkukune kaɗai inda zai zauna yayi rayuwarshi ba tare da ƙuntata ba, daga lokacin daya fara wannan tunanin mu kuma zamu samu damar kwashesu su ukun mu dawo da su cikin mu”! Ya kai ƙarshen maganar tare da buga hannun arm chair ɗin da yake a zaune, gaba ɗaya matsafan suka fashe da dariya mai sautin gaske tamkar ana bubbuga ganga, jikinsu har jijjiga ya ke yi saboda tsabar yadda suke yin dariyar kamar dokuna.
“Mun Fi ƙarfin mutun, Ko mutuwa tsoron tunkararmu take Yi, shiyasa muka daɗe muna sheƙe ayarmu, shan jinin mutune da cin tsokar naman su yanzu muka fara, Rainon Yara ba zamu fasa ba, zamu cigaba da tarasu a cikin kurkukun ƙaddara muna biyan buƙatarmu dasu domin samun ƙarfin ikonmu” Ihu suka dinga Yi sunayin shewa sautin muryoyinsu tamkar zasu fasa bangon Fadar, kusan atare matsafan suke miƙe tsaye suna taka rawarsu ta matsafa, kowan nan su, ya ɗauki abunda yake ra’ayin ci asaman table wasu giya, wasu farfesun naman mutun wasu jini wasu kuma naman dabbobi suke ci, Yayin da wasun su a tsaye suke saduwa da junansu kamar dabbobi wa’iya zubillah.
*DAULAR OBIE ESTATE*
*Dr. jazz❤*
Ƙudundune yake acikin bargo, saman katafaren gadonshi na gidan Sir mubarak, cikin muryar raɗa yake yin magana a wayar shi.
“I’m not working today, I’m at home. yanzu haka da ni ke yi maka magana Ina akwance saman gadona” shiru ya ɗanyi yana sauraron mutumin da suke yin wayarshi, can yaci gaba da cewa”Boss Man kasan bana wasa da aikin ka, idan ka bani umarni jiki na rawa nike yin shi, ko jiya na shiga gidan gonar na duba lafiyar kajin, sai dai muce Alhamdulillah, Jikin su yayi kyau baka ga yadda suke tafiya ba tsokar jikinsu har girgiza take yi saboda ƙoshin lafiyar dake gare su” ya ƙare maganar muryarshi da sautin dariya
“My Boss Man, Amma dani da kai zamu ɗubi na azumi ko? Ko zamu bari sai sallah Ayi layya da su”? Tuntsirewa yayi da dariya jin amsar da mutumin ya bashi muryarshi cikin harshen turanci yake yi mashi magana.
“Amma ai kasan nayi ƙoƙari, tun da na fara kiwon kajin nan wlh ko ɗaya ban ta6a gigin kamawa don in yanka ba, kuma miyau na ya biya fa” da shagwa6a ya ƙare maganar.
Abun da bai sani ba, tun da ya fara yin wayar, Sir mubarak Ya shigo ɗakin jikinshi sanye da kakin sojoji, Hannunsa biyu ruƙe da faffaɗan plate, daga saman shi an jera Chocolate raspberry cupcakes.
Ya shigo ɗakin ne da niyar ya faranta mashi, tun lokacin da turai ta faɗa mashi game da gorin da Hajiya saratu ke yi mashi akan cewa shi ba mahaifin shi bane sai yaji ya ƙara ƙaunar yaron yana matuƙar sonshi.
Lamarin Ya ɗaure mashi kai, ba tun yau ba, Ya jima yana mamakin wayar da dr jazz ke yi akan Kajin gidan gona, cikin tafiyar sanɗa Sir mubarak Ya ƙarasa shiga ɗakin ya zauna gefen gadon shi hannun shi ruƙe da plate din, Ya kasa kunne Yana sauraron tattaunawar jazz da Boss man din shi.
Jin shiru Jazz bai ƙara yin magana ba yai tunanin ko ya kammala yin wayar ne, Gyaran murya ya yi mashi.
Jazz da ke ƙudundune cikin bargo yai lamo jikinshi ya kama yin kerma jin muryar Sir mubarak Hankalin shi ba ƙaramin tashi yai ba.
“Jazz nasan idonka Biyu Ka tashi inason magana dakai” A hankali Ya zame bargon, Ƴar singlet ce ajikinshi tare da Gajeran wando, sumar kanshi duk ta hargitse.
Yana faman mutsustsuke ido da hannu ya saci kallon Sir mubarak
Muryarshi da kasala Ya furta
“Daddy ina kwana, ka tashi lafiya, ya mommy’ adabarbarce ya ambaci hakan sam bai lura da plate din hannunsa ba.
Babu alamun zai amsa mashi gaisuwar tashi, wani irin kallon tuhuma Yake jefa mashi, Ƴan kame kame jazz ya kama Yi, don Ya fahimci dadyn nasa yaji komai da ya ke faɗi a wayarshi.
“Jazz, da wa ka ke yin magana a waya? muryar shi a kausashe Ya jefa mashi tambayar.
Cikin rawar murya Jazz yace”daddy abokina ne dr fawan ai na faɗa maka tare da shi muka buɗe gidan kaji muna yin kiwon su’ yaƙi yarda su haɗa ido da uncle mubarak.
Gyaɗa kai yai”Jazz zan ƙara jan kunnanka akan Ka kiyaye mutanan da za ka yi mu’amala dasu! Bana son kayi abunda zaka Yi danasani, Ni bana zargin ka da wani abu, Ina yi maka kyakkyawan zato My son, Nasihar da zanyi maka shine Kaji tsoron Allah komi za ka yi a duniyar nan kada ka manta Allah Yana ganin ka, kuma zaka koma gare shi ne, jin daɗin duniyar nan ƙalilan nan komai da muka samu anan zamu barshi, a kowani yanayi na rayuwa mutawa zata Iya riskar mutun, me yakamata muyi? Mu kasance muna aikata aikin Alkhairi akoda yaushe, sannan duk runtsi duk wuya kada ka ta6a karya zuciyar wanda ya aminta dakai.....” cikin kwantar da murya Sir mubarak Yake yi mashi nasiha, jikinshi duk yai sanyi, idanuwanshi sun cicciko tab da ƙwalla Ya ɗago Yana kallon fuskar Sir mubarak, Har Ila yau yana mamakin Halin Sir mubarak da Obinna suna da mutunci da daraja ɗan adam, duk da kasancewar shi ɗan mai aikin gidansu sun maida shi tamkar jinin su, tun kafin Ya mallaki hankalinshi suke yin ɗawainiya dashi, cin shi shan shi suturarshi da karatun shi sune suka ɗauki nauyin komai na rayuwarshi.
Yayi zurfi acikin tunanin shi muryar sir mubarak ta katse shi”Ina magana ka tsareni da ido” da sauri Ya sunnar da kanshi ƙasa, Ƙwallar da suka taru cikin idonshi tuni sun soma gangarowa saman kuncinsa.
“Jazz Why are you crying”? Ya faɗa yana duban face dinsa.
cikin shessheƙar kuka ya soma magana”nagode sosai daddyna, ina matuƙar alfahari dakai, saboda ƙaunar da kuke nuna mun kai da baba, ban ta6a danasanin kasancewata acikin family dinku ba, Ina jin daɗin nasihar da ka ke yi min daddy, ka maidani tamkar ɗanka komai na rayuwa kana Yi min...” murmushin gefe fuska sir mubarak yaɗan saki.
“My son ya isa Haka, share hawayenka, Ni dai fatana Ka ruƙe mutuncinka Jazz, Kada ka bani Kunya, inaso ka zama abunda duniya zata yi alfahari dakai”
Jinjina kai yai tare da ɗago da kai Ya ɗaura rinannun idanuwanshi akan fuskar Sir Mubarak “In sha Allah, Nayi maka alƙawarin hakan, Zan kama mutuncina kuma bazan ta6a baka kunya ba”
Miƙa mashi plate din hannun shi yayi
“Your mother made this for you. I know how much you love cupcakes.” fuskarshi ɗauke da ƙayataccen murmushi Yake dubanshi, Hannun Dr Jazz Har kerma Yake yi wurin kar6ar Plate din
“Kayi brush kuwa? Naga kamar yanzu ka farka daga bacci,”
Girgiza kai yai”ban kaiga Yi ba, Yanzu zan shiga toilet din’
“Okey, Ka ajiye plate din idan ka fito sai kaci” ƙaƙaro murmushi yai akan face dinsa”Okay, Dad, I appreciate your care.”
Miƙewa sir mubarak Yai”Ni zan wuce Office, ka kula mun da kanka”
“Daddy Allah Ya dawo min dakai Lafiya, Allah ya tsare mun ya kare mun kai daddyna”
Yaji daɗin maganar Jazz, har saida ya dan juyo ya kalle shi kafin Ya fuce daga ɗakin”
Nauyayyar Ajiyar zuciya Jazz ya sauke, kalaman Sir mubarak sun tsaya mashi aranshi, Cikin sanyin murya ya furta”Am sorry My daddy, Na riga dana jefa kaina Cikin Tarkon da bazan Iya fidda kaina ba, addu’arka kawai nake buƙata Allah Ya bani ikon cinye jarabawar nan”!! Ya ƙare maganar tare da saukowa daga saman gadon ya ɗaura plate din hannun shi saman Table Ya nufi toilet Ya shige.
*Hajjaty the head maids💋*
A tsanake Take Yin tafiya tana nufar haɗaɗɗen garden din gidan, ta ɗauki wankan Sari Launin Ja, Hannunta biyu ruƙe da Tray na Kayan Marmari tare da mugs biyu na black tea, ta ko’ina ƙamshin turare ne ke fita a jikinta, tasha uban ado na sarƙar wuya da awarwaro, make up din fuskarta Ya ƙara mata Kyau.
Tun kafin ta ƙarasa shiga garden din idanuwanta suka hango mata, Obinna tare da babban amininsa daya kawo mashi ziyara, kallo ɗaya zaka yi mashi ka gane Inyamuri ne, fari ne fat sumar kanshi da jagirarshi dukkansu hurhurace, hatta dogon Gemunshi fari ne fat kalar na Obinna, sunyi shigar Manyan Kaya na hausawa, zaman hular kanshi zai ƙara tabbatar maka da ƙabilar shi, suna a zaune saman shimdiɗar da Hajjaty tayi masu ta alfarma, kowan nan su ya tada kanshi saman tuntun kalar na sarakuna.
Tun kafin ta ƙaraso gabansu, ƙamshin turarenta Ya daki hancinan su, abokin obinna Ya furta”masha Allah” Ya kafe ta da ido yana faman Jan gemunshi.
Zuƙunnawa tayi agabansu Ta sauke tray din, cikin girmamawa ta gaishe da abokin”sannu da zuwa, ina wuni Ya iyali” lumshe idonshi yai tare da ware su kan fuskarta, Obinna dake kallonshi ya fahimci kamar baya a hayyacinsa, hajjaty ta tafi da