Kurkukun Kaddara Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Boss Bature Category :  Complete Novels

Chapter   48 / 84

141K to 144K   out of 250.5K words

saurayin? A jin farko afagen kyau da ƙasaita, Namijin duniya, A halitta madai-dai ci ne, mai wani irin faffaɗan ƙirji a buɗe yake, ga wannan six pack din nasa baro baro, Vest din jikinsa tayi tighting dinsa, kana iya ganin zanen ƙirjinsa, Ko ɗan wrestling bazai nuna mashi ƙirar ƙarfi ba, in ka kalli damtsen hannunsa sai ka tsorata, mutun ne mai ji da ƙarfi, Allah yabasa kyawawan idanuwa farare tass ga su so sexy, masu ɗauke da launin ƙwayar ido reddish brown, har shining suke yi, ga wani kwantaccen saje mai shegen kyau, eye brows ɗinsa kuwa tamkar an zana ta, tayi wani irin shape ga gashi cike da ita, kiris ya rage jagirarsa su haɗe da juna saboda Yana da yalwatacciyar suma, lallausar sumar kanshi tasha gyara anyi mashi Military haircut yayi bala’en yi mashi kyau, abun da yafi komai jan hankali a jikin shi tsadaddiyar launin fatar shi, chocolate colour, har wani glowing take yi, hutu ya zauna mashi, jikinshi ya wanku da dollar, duk inda namiji yakai to ya zarce nan, komai nashi na kece raini ne ba wasa a tattare dashi, kuma burin kowace ƴa mace ne shi, a 6angaren wadatar arziki kuwa basai an faɗa maka ba, su kan su kuɗin raina kansu suke yi agabanshi, duk da tarin dukiyarsa baida girman girka, mutum ne shi da bai ɗauki duniya da zafi ba, Allah ya bashi kaifin basira, Yana da ilmin addini dana zamani, ta ko’ina Allah ya hore mashi, yana matuƙar jin ƙan talaka, Yana da tausayi ga son taimako, shi sam abun hannunshi bai rufe mashi ido ba, kyawawan halayansa da ɗabi’unsa abun burgewa ne, shiyasa ya fita daban ko acikin jikokin family ɗinsu, ya shahara aduniya sosai, babu inda ba’a sanshi ba, mutane basa gajiya da yabon shi, burin kowane ya yi tozali da shi, babban abunda ya tsana a duniyar nan shi ne yaga mugun mutun mara imani acikin mutane Yana zalunci, In kuwa ya damƙi irin su, mai ƙwatar su sai Allah, shiyasa mutane masu irin halin suke mugun jin shakkar shi, dai dai da sunan shi aka fada sai gabansu ya fadi, don baya yi masu da kyau, ni nasan bazan Iya misalta ƙasaitaccen Namijin nan ba, Kaɗan ne na Iya faɗa maku sauran ku biyo ni acikin labarin, Yanzu ne wasan Ya fara.

Tun da ya ɗaura lumsassun idanuwanshi akan tsadaddar laptop din gabanshi ƙirar Apple macbook pro bai ƙyafta idon shi ba, Hannun shi na dama na sanye da wrist watch ƙirar Rolex submariner haɗaɗɗar gaske, ya tattara dukkan natsuwar shi akan abun da yake kallo, duk wani motsin prisoners dake acikin jirgin yana kallon su ta cikin laptop dinsa, Ƙayataccen table din dake agaban gadon shi ɗauke ya ke da Mug na cofee ga fresh fruit da aka ajiye mashi, daga gefen shi saman mattress, suit jacket dinsa ce daya cire launin Navy blue, trouser din ta ne a jikin shi, hankali a kwance bai da wata damuwa.

Awanni da suka ɗauka acikin jirgin ba ƙaramin daɗi suka ji ba, saboda an gatanta su, sunci abinci har sau biyu, sun yi bacci sun tashi, komai suke so yi masu ake yi, Danish ne kaɗai baici komai ba, tun da bacci ya ɗauke shi bai farka ba.


*💋ABBAN SOJOJI💋*
*💋KURKUKUN ƘADDARA💋*


*Assalamu alaikum, fatan mun wuni lpy, ga masu son abban sojoji complete 400 da kuma kurkukun ƙaddara wanda nake cikin rubutawa, ga number da zasuyi mini magana da ita, new number ce wadda nake da ita me 08103884440 whatsapp din ya samu matsala, ga wadda za’a same ni da ita (08134387050) ayi mini magana ta whatsapp, message from Boss Bature*

*✍️ Mu haɗu Gobe In sha Allah Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya, Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuɗin*



First bank



3196407426,



*Bature Hafsat Muhammad, za’a tura evidence of payment ta phone number ɗina 08169856268 Banda kira whatsapp kawai*

_~*BossLadiesWriters*~_


_*💋KURKUKUN ƘADDARA💋*_


~Middle step~

سجن القدر❤🤍❤


_THE PRISONERS E26🔥💫_



*Daga alƙalamin Boss Bature*



Confusion of the heart💫



Tun da Aneelerh ta turawa numbar saƙo har yau ba’a tuntu6eta ba, abun ya dame ta, ta rasa ina zata tsoma ranta taji daɗi, kullum ne sai ta ƙara jaraba kiran layin ko za’aci sa’a mamallakin wayar ya ɗaga amma wani iko na Allah a kashe take samun layin duk ta damu da son jin wanene.


Fitowa ta yi daga cikin ɗakinta hannunta ruƙe da wayarta, ɗakin zahra ta nufa da niyar ta faɗa mata halin da take ciki wata’kil ta bata shawara akan abun da ke damunta.

A bakin ƙofar ɗakin ta fara yin sallama, shiru ba’a amsa mata ba, kusan sau uku tana kwaɗa sallama zahra bata amsa ba, tunani ta soma yi ko dai ta koma wurin aiki ne? Ko kuwa baccin lalacin da ta saba yi ne, wata’ƙil kuma wanka ta shiga.

Haura ƙafa ta yi ta shiga ɗakin zahra, tun abakin ƙofar room din ta fara cin karo da takalmanta da jakarta da mayafin ta gaba ɗaya ta watso su saman floor, nan take hankalin Aneelerh ya tashi da sauri ta ɗago da ido tana kallon gadonta, duvet dinta da pillow dinta duk ta watso su ƙasa, Komai na ɗakin ta tarwatsa shi.

Aneelerh ta fahimci babu lafiya wani abu ya faru da ita, Zahra da ta sani Mai tsafta dagangan dai bazata ta6a barin ɗakinta a hargitse ba.

Cikin tashin hankali ta soma ƙwala mata kira”Zahra! zahra!!” shiru babu amsa, ranta ne Ya bata cewar ko dai bata agidan ne ko kuma ta shiga ɗakin ummi, da sauri Aneelerh ta fuce daga ɗakin, Har zata gifta ta falo ta wutsiyar ido ta hango Mami da ummi zaune suna fira, juyawa tayi da sauri ta nufe su, babu wanda Ya lura da ita acikinsu har saida ta furta”ummi mami Ina zahra” kusan atare suka ɗago suna kallonta, gaba daya sun fahimci babu kwanciyar hankali atattare da ita.

Ummi tace”kin duba ɗakinta baki ganta ba”?
Kafin ta bata amsa mami tace”Aneelerh wai lafiya? Ya akai naga kamar bakya acikin natsuwarki”
Muryarta na ɗan rawa ta furta”bakomai, na duba ɗakin zahra ne ban ganta ba”

Mami tace”shine duk kika ɗaga hankalin ki? Sai kace yau ta fara fita daga gidan, kema kinsan zahra idan har ba wurin aiki taje ba toh tana acikin gida”

Ummi tace”tun ɗazu fa ta dawo, ki kwantar da hankalin ki, bata wuce cikin ɗakinta, Ki koma ki sake dubawa”

Juyawa tayi da sauri ta nufi ɗakin donta ƙara dubawa.

Bayan tafiyarta ummi ta dubi mami”ƙawancen Aneelerh da zahra ba ƙaramin burgeni ya ke yi ba, har mamaki nake yi idan naga yadda Aneelerh take jan zahra a jiki, duk da ta girme ta”

Mami na murmushi tace”ai shi ƙawance ba a shekaru yake ba, indai mutum Ya mallaki hankalin shi ko da ya girme ka zaka Iya ƙawance da shi, Ni kaina ba ƙaramin burgeni suke Yi ba, Allah dai Ya bar zumunci”

Ummi tace Ameen ameen.
Daga haka su ka ci gaba da tattaunawa a tsakaninsu.

Afujajen Aneelerh ta faɗo ɗakin zahra tana faman Yin haki, ta kware murya tana ambaton sunanta”Zahra! zahra! Nasan kina jina, Dan Allah kiyi mini magana”

Still babu alamar za’a tanka mata, ranta ne ya bata cewar wata’ƙil ta fita ne ba tare da sanin kowa ba, Har ta juya zata fuce daga ɗakin ba zato ba tsammani ta soma jin shessheƙar kukan zahra, da sauri Aneelerh taci burki, a sukwane Ta juya tana bin ko’ina na ɗakin da kallo, a ƙoƙarinta nata gano inda zahra ta 6uya, hankalinta yafi karkata akan toilet din ɗakin, da sauri ta ƙarasa bakin kofar ta kara kunnanta, sosai take jin kukan zahra mai matuƙar tsuma zuciya.
Muryarta na rawa ta furta”Zahra meya faru dake? Wanene ya ta6a min ke? Dan Allah ki faɗamin zahra, ashe kina jina shine kika ƙi tanka mun ko?” cikin shessheƙar kuka zahra tace”...Aunty Aneelerh babu abun da ke damuna, kawai bana son kowa ne a kusa dani”

“Ki fito daga cikin toilet din muyi magana zahra, ni bana so inganki acikin damuwa, kema kin sani har farin cikina zan Iya sadaukarwa saboda ke, don haka ki fito muyi magana” cikin kwantar da murya Aneelerh take yi mata magana.

“Zahra ke nake jira ki fito muyi magana, wlh idan kika bari na haura ƙafa ta daga cikin ɗakin nan to kada ki yi tsammanin zan waiwaye ki, haba dan Allah, ina amfanin irin hakan? Ashe dama baki ɗauke ni kamar yadda na ɗauke ki ba? Har zaki Iya ke6e kanki cikin damuwa ba tare da kin neme ni ba”?

A faɗace Aneelerh ta ambaci hakan, duk don ta samu zahra ta buɗe ƙofar toilet din.

Bugun ƙofar tayi da hannunta”kada Allah yasa ki buɗe ƴar rainin wayau” ta faɗa tare da juyawa ta nufi ƙofar fucewa daga dakin, Buɗe ƙofar toilet din zahra tayi, Fuskarta sharkaf da hawaye idanuwanta har sun kumbura, kumatunta sunyi jawur dasu, Short ne a jikinta tare da farar vest, Sumar kanta kamar ta mahaukaci sabon kamu.


Da gudun gaske ta nufi Aneelerh dake ƙoƙarin fita daga ɗakin, Gaba ɗaya ta faɗa saman bayanta ta rungume tana cigaba da yin shessheƙar kuka.

Ajiyar zuciya Aneelerh ta sauke, tare da kai hannu ta ruƙo damtsen zahra ta zagayo da ita, har saida gabanta ya faɗi ganin yadda hawaye suka wanke mata fuskarta tamkar ba zahra ba, damuwace ƙarara akan fuskarta, kwantar da kanta Aneelerh tayi saman kirjinta, a hankali take shafa sumar kan zahra da yatsun hannayenta.

“Ya isa zahra, ki daina kuka bana son ganin hawayenki,’ cikin murya kuka tace”Aunty Aneelerh ba zaki gane ba, Ni kaɗai nasan halin da nake aciki, Allah ji nake kamar in haɗiyi zuciya in mutu kowa ya huta”

Kalaman zahra sun ƙara ɗaga mata hankali, tabbas akwai gagarumar matsala, Yarinyar da koda yaushe fuskarta dauke da murmushi komai zaka yiwa zahra a duniyar nan baka isa ka 6ata mata ranta ba, sai gashi a yau itace take Yin kuka har tana faɗin kamar ta haɗiyi zuciya ta mutu.

“Kiyi haƙuri zahra, bai kamata kina yin wannan furucin ba, Idan ma wani abune ke damunki meyasa ba zaki kai kukan ki ga Allah ba? sai kawai ki kulle kanki a toilet kina kuka? Hakan ya dace? Kina tunanin shine mafita a gare ki? Ga ummi ga mami, ga mahboob, ga abie da uncle uwa uba ga kuma ni meyasa ba zaki tuntu6i ɗaya daga cikin mu ki faɗa masa damuwarki ba? Kin tsaya kina yin zurfi ciki a ƙarshe ki yi wa kanki illa amma faɗamana da zakiyi shi zaisa ki samu maslaha na abunda ke damunki, ko da ace bamu da abun da zamu taimaka maki wurin yaye damuwarki zahra zamu Iya baki shawara ko mutayaki da addu’a akan Allah ya yaye maki”

Faɗa Aneelerh tayi mata, sai faman sauke ajiyar zuciya take Yi, ruƙo hannunta Aneeleeh tayi”wuce ki shiga toilet ki wanke fuskarki Ina jiranki” ta faɗa tare da sakin hannun zahra, baiwarAllah jikinta duk ba ƙwari tana tafiya tana waiwayon Aneelerh, yayin da hawaye ke cigaba da fita a idonta.

Kafin fitowarta Aneelerh ta bar ɗakin ta nufi falo, fridge ta buɗe ta dauko mata ruwa me sanyi.

Cikin tafiyar sauri ta nufi ɗakin.

“Aneelerh kinga zahran ne”? Muryar mami ce ta katse mata hanzarinta, ba tare da ta juya ta kallesu ba ta bata amsa da cewa”Eh mami, ashe toilet ta shiga”
Bayan ta shiga ɗakin, ta daura ruwan a gaban mirror, ta koma bakin door din ɗakin ta soma tattara kayan da zahra ta watsar ta maida su a ma’ajiyarsu.

Ba ta jima da zama a gefen gadon ba, Zahra ta fito daga toilet, ta wanke fuskarta kamar mara gaskiya ko haɗa ido da Aneelerh bata son yi, saman mirror chair ta zauna tana fuskanta Aneelerh, sai dai ta taƙi ɗagowa su haɗa ido da ita.

“Ga ruwan nan ki sha” ta faɗa tana nuna mata robar ruwan, data ajiye mata, Yatsun hannunta na kerma ta ɗauki bottle water din ta cire murfin ta soma ɗaɗɗakar ruwan kamar zata haɗa da robar duka ta shanye, bayan ta gama sha ta maida murfin robar ta daurata gaban mirror.

“Zahra ina sauraronki, Ki natsu ki fadamin meya faru dake? Da har yaja kika kulle kanki a toilet, bana so ki furta mun kalmar babu komai! Ranki zai Iya 6aci” fuskarta a ɗaure tamau tayi mata maganar.

Zahra na faman sunnar dakai, idanuwanta akan yatsun hannunta muryarta adabarbarce ta soma magana.

“Aunty aneelerh zan faɗa maki amma kada ki faɗa ma kowa dan Allah,” jinjina kai Aneelerh tayi”in sha Allah”

Cigaba da yin magana tayi”dama akan decorating company dinmu ne, ban ta6a faɗa maki cewa banawa bane, mallakin mamansu ƙawata ne, Ni a lokacin dana kammala karatu ina neman aiki bansamu ba, Nayi ma daddy magana akan ya taimaka mini in buɗe Beauty saloon nawa nakaina, amma sai yace min shi baida halin da zai Iya taimaka mani, bayan ni nasan yana da arziƙin shi kawai baison bani ne kusan halin shi ɗaya da mahboob in dai wurin maƙone ko mami fama take yi dashi, dawowar ku gidan nan ne ma ya fara sakin hannunshi gudun kada ku gane halin shi,’ Aneelerh ta natsu tana sauraranta.

Numfasawa zahra tayi kafin taci gaba da cewa”akwai wata rana da naje gidansu ƙawartawa, muna zaune a falo muna fira akan yadda zamu buɗe beauty saloon da zamu gudanar da kasuwancin su, har take ce min mommynta tana da kuɗi sai dai itama maƙone da ita ba ta Iya fidda kuɗi ta bata hakanan idan ba abun da ya shafi karatunta bane, amma da zata amince mana ko da bashine ta bamu idan muka samu kuɗi tun da kusuwancin ana samu sosai indai mutun ya samu kar6uwa awurin mutane, sai na zaro ido nace mata a’a ni bana so muci bashi muzo mu kasa biya, na faɗi hakanne saboda sanin halin mahaifiyarta masifaffiyace bata da mutunci in dai akan kuɗin ta ne, Aunty Aneeleh fatima ta matsa mini akan muje muyiwa mommynta magana tasan idan na sanya baki zata bamu tallafin da zamu buɗe, saboda muna mutunci da ita, duk cikin ƙawayen fatima tafi sakewa dani har idan nayi kwana biyu banzo gidan su ba takan tambayi fatima ina ƙawarnan taki mai dimple da yake haka take kira na, sai tace mata zata kira ni idan tana son ganina, Aunty aneelerh tsautsayi ne ya kai ni ga amincewa da maganar fatima, muka kwasa muka je wurin mommynta, muka fada mata dangane da beauty salon din da muke so za mu buɗe gashi bamu da kuɗi, matar nan tayi dariya tace mana ai ba wani abu, ta ji daɗi da mu ka yi tunani mai kyau, ita tana son mutun me burin ya nemi na kansa, don haka zata buɗe mana company da zamu dinga gudanar da kasuwancin mu harma mu zuba ma’aikata acikin sa da zasu dinga taya mu aiki, idan yaso zamu dinga raba riba da ita, a lokacin munyi mamakin jin zata buɗe mana company mu da muke maganar buɗe ƙaramin beauty saloon, ni bansan da wata manufa a ƙasa ba, Ni da fatima munyi murna muka dinga yi mata godiya da addu’o’i, tun da ta buɗe mana companyn bata ta6a kar6ar ribar da muke rabawa ba, duk in muka kai mata kasonta sai tace mana mu ruƙe a hannun mu zata nema yanzu bata buƙatar kuɗi, Aunty Aneelerh tun muna tara mata kuɗin har dai fatima tace min mu kashe kudin ai mommynta bata buƙatarsu shiyasa bata kar6a ba, in yaso daga baya in muka tara wasu kuɗin sai mu biyata, zuciya ta ɗebeni muka haɗu ni da fatima mu ka kashe kuɗin, acikin su na cika da nawa kuɗin na sayi mota, Na canza wayata na sayi iphone 15, wayar da kika ga ina ruƙewa a hannuna, Na ciri dubu ɗari uku naba ummin mu nace gashi nan tasa mun albarka kasuwanci yayi kyau, ummi taji daɗin kuɗin nan, dama tana buƙatarsu daddy baya bata kuɗin da zatayi hidindimu dasu, duk nice fa nake taimaka masu idan na samu kudi, shi kawai ta 6angaren abinci ne yake yi mana ƙoƙari, sai kuma kayan sallah idan tazo amma inba sallaba babu abunda daddy yake yi mana, kudin shi sai dai muga wasu suna ci, acikin kuɗin naba mahboob dubu hamsin shima yai ta yi mini godiya hada ƴar ƙwallar shi saboda daɗin da yaji....’ dakatawa ta ɗanyi da yin maganar hawaye nabin fuskarta, tun kafin ta ƙarasa jikin Aneelerh yai sanyi don tasan ƙarshen zancen bamai daɗi bane.

Jinjina kai zahra ta ɗanyi kafin ta daura da cewa”Aunty aneelerh saida na tabbatar kuɗin sun ƙare tukunna hankalina Ya kwanta, sai kwanan nan da Hajiya saratu ta kira awaya suna buƙatar ayi masu decoration da kitso da ƙunshi, lokacin dana duba asusun mu, ba mu da isassun kuɗin da zamuyi order na kayan da za’ayi masu amfani, dama dai ita hajiya falmata itace take yi mana hanyar da ake shigo mana kayan adon daga dubai, muka zauna nida fatima mukayi shawara sai tace min zatayi ma mom dinta magana, bayan sunyi magana da ita, sai ga fatima tazo wurin aikin mu idanuwanta jawur dasu, hankalina atashe na tambayeta lafiya meya faru da ita, cikin shessheƙar kuka tace min mominta tace idan har muna so tayi mana order din kaya mu fara tura mata ribar da muka tara mata a hannun mu, tana buƙatar kuɗin da gaggawa, tun anan fatima tace mata ai babu kudin nan mun kashe su, tsabar 6acin rai ta zazzaga mata masifa tamkar ba ƴar ta ba, hada mari ta kwasa mata a fuska, ko

48 / 84