Kurkukun Kaddara Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Boss Bature Category :  Complete Novels

Chapter   71 / 84

210K to 213K   out of 250.5K words

ɗazu”

Tuntsirewa yayi da dariyar mugunta, ran hajiya saratu ya 6aci matuƙar masifa ta soma zazzaga mashi sai da tayi mai isarta tukunna ya katse ta da cewa”saratu kenan, kefa da kanki kikace nine ɗan kwali ke ce hula, hakan na nufin kece namiji ko? To meyasa kike neman mace donta baki kariya? A tunanina ni yakamata inji tsoro bake ba, shi namiji da jarumta aka san shi bada ragwantaka ba”!

Takaicin duniya ya ishi hajiya saratu, cikin lalama tace”pravin dan Allah ka dawo ɗaki, idan saboda abun da na fada maka ne ya 6ata maka rai, zan baka haƙuri”

“Bana buƙatar haƙurin ki saratu, lokacin daya dace ki lallasheni ki tarairayeni ki bani hakuri bakiyi ba till now da buƙatar kan ki ce ko? An gaya maki ni shashashane bansan ciwon kaina ba”?

Shiru bata tanka mashi ba, kuma tana sauraronshi.

“Ko gobe kada kiyi tunanin zan dawo gida, ni yanzu haka ma gani akwance tare da wadda tafi ki iya tarairayar miji.....”tsawar da ta daka mashi ce ta sanya shi yin shiru, tamkar zata fasa mashi screen din wayarshi”ya isa haka! Ya isa! Kada ka ƙara maimaita min maganar da kayi idan ba so kake ranka ya 6aci ba......” bata ƙare maganar ba, yai rejecting kiran, Ya jefar da wayar saman mattress, Ya janyo hajjaty a jikinshi, ya daura hannunshi saman sumar kanta, har cikin ranshi yana ƙara jin ƙaunarta, bai da tamkarta a duniyar nan, saboda kyautata mashin da take Yi, yana matuƙar ƙaunarta, kiss ya manna mata saman forehead nata, kafin ya cusa kanshi gefen wuyanta, ƙamshin turarenta ya daki hancinsa ahaka bacci yai awon gaba da shi.

Jefar da wayar hannunta tayi saman gado, ranta ya 6aci matuƙa pravin ya ƙona mata rai, kishine da ita, gani take kamar dagaske ne abun da ya faɗa mata yana can shida wata suna sheƙe ayarsu, kokwanton maganarshi take Yi, ta riga ta yarda da pravin tasan bazai Iya cin amanarta ba, wata’kil ya faɗa mata hakanne don ya huce raɗaɗin abunda tayi mashi.

Damuwace ƙarara akan fuskar hajiya saratu, adaddafe ta nufi gado ta haye ta kwanta idanuwanta suna fuskantar ceilling, babu alamun zata runtsa adaren Yau.


*Hajiya Turai💔*


Safa da marwa take Yi acikin ɗakinta, Hannunta ruƙe da wayarta, night gown ce a jikinta.

Fuskarta tayi jawur tamkar wadda tasha kuka, musamman kumatuntu, green eyes dinta kuwa sun ciza launinsu, tarasa ina zata tsoma ranta taji daɗi, since wuraren ƙarfe goma take kiran layin dr.jazz babu alamun zai ɗaga, gashi har dare ya nutsa bai dawo gida ba, ta kira layin Sir mubarak kusan sau talatin shima Bai daga ba tamkar ta fasa ihu haka take ji.

“Mom” kamar daga sama taji an ambaci sunanta, tsabar ruɗi sai taji kamar muryar jazz ne.

A firgice ta juyo don ganin wanene, Yana daga tsaye bakin ƙofar ɗaki, cikin shiga ta kayan bacci ya zura hannayenshi cikin aljihun wandonshi, matashin saurayi ne kamanninshi sak dana Sir mubarak.

“Ibad kai ma baka yi bacci ba”? Muryarshi da kalasa ya furta” How can I sleep, Mom? Jazz hasn’t come home yet. na jaraba kiran layukan wayarsu duk akashe, bansani ba shi jazz ko aikin kwana yake yi a asibiti, nazo ne naji ko sun faɗa maki meya hana su dawowa gida”?

Ta lura da yanayin shi tsantsar damuwace akan face dinsa, batayi mamaki ba saboda ƙaunar da suke yi ma Jazz, sun dauke shi tamkar shaƙiƙinsu

“Ibad, I don’t know why they haven’t come home yet, I’ve been trying their phones since 10 o’clock, and nobody is picking up. I’m really worried, inajin fargabar ace wani abun ne ya faru da su” tuni idanuwanta sun ciko tab da ƙwalla.

Ruƙo hannunta Ibad yai”haba mommy, kada ki zubda hawayenki please, ki kwantar da hankalin ki, Everything is going to be okay. They’ll come home safely.”

girgiza mashi kai tai”basu ta6a yi min haka ba ibad, daga jazz din har daddyn naku, kullum ne idan zasu kai dare awaje, sai sun kira awaya sun faɗa min, amma yau shiru babu wanda ya tuntu6eni” muryarta na rawa ta furta maganar, tausayinta duk ya kama ibad, jinta yake yi tamkar mahaifiyarsu data rasu.

Gyaran muryar da akayi masu ne Ya janyo hankulansu ga duban shi, tafiya yake yi yana tunkarosu tamkar baisan da su ba, Hannun shi ruƙe da apple laptop dinshi, daga shi sai short a jikinshi, Ƙirar jikinshi da komai kalar na daddynsu ne, sai dai shi yafi ibad da daddynsu hasken fata nashi chocolate colour ne mai kyan gaske, sumar kanshi tasha gyara luf ta kwanta saman bayanshi, Yana da kirar karfi kamar ɗan wrestling, wani irin daddaɗan kamshin turarene ke fita sako da lungu na jikinshi, komai nashi da aji yake yin shi, mutunne shi maiji da kanshi, baida wasa a aikinshi, yana ruƙe da muƙamin CEO na babban Companynsu dake a ƙasar canada.

Kafafuwanshi suna asanye da slippers, magana ya somayi tamkar baisan furtata

“Mom, yanzu major ya kira ni awaya, ya fadamin suna atare da jazz wani aiki ne mai muhimmanci ya tsayar da su, so they couldn’t come home tonight. But they’ll be back early tomorrow”

Ajiyar zuciya ta sauke, har cikin ranta taji dadin jin hakan, Murmushi Ibad ya saki yana fadin”mun samu nutsuwa yanzu, Mom ki koma daki ki kwanta, ƙarfe 3 fa ta buga, gobe nasan zakiyi ramuwar bacci, murmushi tasakar mashi”bari na koma ciki, mu kwana lafiya My Sons,” ta faɗa tare da juyawa ta nufi ɗakinta, saman gado ta haye idanuwanta suna fuskantar ceilling, bakomai take jimawa ba face kwanan da za ta yi ba tare da mijinta ba, sun saba faranta ma junansu kafin su runtsa yau kuma babu shi atare da ita, ga kuma ɗanta da take jin kewarshi,
Pillow ta janyo ta rungume a ƙirjinta.


“Babban yaya nan fa ba kasar canada bace, taya zaka dinga yi mana yawo da short a tsakar falo? Kai ala dole ga bature ko? Ko kunyar mommy baka ji,” Ibad ne ya fada da zolaya.


Ko kallo bai ishe shi ba, saman Sofa mai mazaunin mutun uku ya kishingiɗa kanshi saman sofa hand, Ya daura laptop dinsa saman flat stomach dinsa.

In a husky voice ya furta”ibad! Ina buƙatar abun sha”

Ruƙe qugu Ibad yai sam baya gajiya da zolayar yayan nashi duk da tazarar shekarun dake atsakaninsu, domin kuwa Zaki ba ƙaramin mutun bane

“nan fa ba canada bace, Nigeria ce daddy Ya hana ana aikena idan dare yayi” yamutsa fuska Zaki Yai Ibad ya fara hayaƙa shi.

Calmly ya furta”Don’t make me repeat myself” kama kunne ibad yai”sorry big bro, na tuna kada ka hanani silallan kashewa” ya fada tare da nufar frigde Ya bude ya dauko mashi coke mai sanyi, ya dawo Ya daura mashi saman sofa table din gabanshi.


“Babban yaya gashi na kawo, Ni zan cire maka murfin?” banza yai mashi tamkar baiji me yace ba.

Bottle opener yaje ya dauko ya zuƙunna agaban table din Ya soma kiciniyar bude murfin, sai nishi yake yi, sam bai saba da wahala ba, ibad mugun sangartacce ne yayanshi ya 6ata shi da hutu, dogon tsoki zaki Yaja, ya yunkura ya miƙe Ya ajiye laptop din gefe ɗaya, ya kai hannu ya kar6e coke din da bottle opener din, sau ɗaya ya murɗa murfin ya cire.

Washe baki Ibad Yai”babban yaya ba za ka yi bacci ba? kana buƙatar hutu fa, kai kullum aiki baka gajiya”!

Banza yai dashi baice komai ba, a tsanake yake kur6ar coke din me sanyi, Ibad ya ƙura mashi ido yana kallon bakinsa har haɗiyar yawu yake yi.

Janye coke din yai daga bakinshi, Ya galla mashi harara”meyasa kake kallona kana haɗiyar yawu kamar wani maye? Idan so kake kasha bakasan inda zaka dauko bane”

Kwa6e mashi fuska ibad yai”Ai ni nafi so kasha ka rage min”

Sakin baki yai galala yana dubanshi”oh dole sai na baka ragowa na zaka sha” ɗaga mashi gira yai alamar eh.

Babu musu Ya miƙa mashi, don ya san rigimar ibad idan har ba bashi ragowar yai ba to kuwa zasu kwana azaune”

Yana sha yana kallon fuskar Zaki, aiku sarkin ɗumi.

“Big bro, where’s my sister pretty ? You told me she came back to Nigeria. When can we see her? Should we go to their house, or will she come to ours? (Babban yaya Ina sister pretty dina? Ba ka ce min ta dawo Nigeria ba, to yaushe zamu haɗu da ita? mu zamuje gidansu ko ita zata zo gidanmu?)

Dafe kanshi yai da hannu ɗaya”Ibad, I don’t like making noise, Please go to your room, lie down on your bed, and sleep.”

“Shikenan zanje na kwanta amma kafin nan inaso ka fadamin gaskiya, dagaske babu soyayya atsakaninku”?

Ji yake tamkar ya dauki laptop din gefenshi Ya kwalama ibad saman kanshi, Ya takura mashi.

“Ka yi shiru bakace min komai ba”!

Miƙewa zaki yai ya dauki laptop dinsa Ya nufi sashen bedroom dinsu, da sauri Ibad Yabi bayanshi, har yakusa shiga dakin ya ɗan dakata da yin tafiyar, in a cool voice ya soma magana

“Ibad, she is married and even has a daughter, And she loves her husband. But there is no love between me and her. taimakon da nayi mata dan Allah nayi shi”

Da mamaki Ibad yace”babban yaya kana nufin duk tsawon shekarun data dauka a canada a gidanka, da auranta? To ya akai ta gudu tabar mijinta da ƴarta? kuma take rayuwa agidanmu harma kuke rungume juna ai ina ganinku idan kuna shan soyayya....” kafin ya ƙare maganar, afusace zaki ya waiwayo da niyar ya kwaɗa mashi laptop din hannunshi da gudu Ibad Yabar wajen yana dariya.

Guntun tsoki Zaki Yaja, Ya faɗa katafaren room dinsa, saman gadonshi ya kwanta, haɗi da daura laptop dinshi on his broad chest, hoton fuskarta dake akan wallpaper din laptop nasa ya ƙurawa ido yana kallonta, bazai Iya misalta ƙaunarta da yake ji ba, yana sonta baya jin zai iya son wata ƴa mace aduniyarnan kamar yadda yaso baiwar Allahn nan, sun rayu na tsawon shekaru tamkar ma’aurata rana ɗaya Allah ya ƙaddara rabuwarsu, yana fatan sake haɗuwa da ita, da tunaninta bacci yai awon gaba da shi.


*ANEELERH❤*



Kiran sallar asubar farko, ringing din wayarta ya daki kunnanta, firgigit ta farka daga bacci tana faman sauke ajiyar zuciya, yayin da la66anta ke ambaton sunan baby junaid, mafarkin da tayi da shi ya ɗaga mata hankali, a ruɗe ta mike zaune, rigar baccin jikinta duk ta yamutse, haka zalika sumar kanta a hautsine take.

Daukar wayar tayi dake ajiye gefenta, ta duba me kiranta, missed calls ta gani sun kai biyar na hajiya adama, aranta ta ayyana Allah yasa ba mafarkin da tayi bane ya zama gaske.

Bin kiran tayi nan take kiran ya shiga, bugu uku kafin hajiya adama ta ɗaga.

“Assalamu alaikum, daughter in-law, fatan dai ban katse maki baccin ki ba” da buɗar bakin Aneelerh sai cewa tayi”mommy ina junaid”
Sautin dariyar hajiya adama ne ya fargar da ita, da sauri ta dafe baki tamkar tana agabanta tace”au...namanta ban gaishe ki ba, ina kwana mommy”

“Lafiya lou Aneelerh, lallai yau na shaida kin ƙosa kiga ɗanki, tun da gashi har kin fara ambaton sunan shi tunkafin ki gaishe ni”

Cikin jin kunyar maganarta Aneelerh tace”ba haka bane mommy, daga bacci na tashi bansan Na ambaci sunanshi ba”

Hajiya adama tace”oh am sorry na tada ki daga bacci tun da asubahi, agafarce ni, jikana ne ya takura min akan in kira mashi ke awaya, yaban mamaki da sunanki Ya farka yanata kuka yana fadin wurin mommy zaije shine nace bari na kiraki kuyi magana wata’ƙil hankalinshi zai kwanta, kafin mu shigo gidan zuwa anjima in sha Allah”

Hankalin Aneelerh yaɗan tashi jin abun da mommy adama tace, aranta ta ayyana kodai shima yayi kalar mafarkin da tayi da shi ne?

“Aneelerh kinyi shiru, ga shi ku gaisawa” muryarta adabarbace tace”toh mommy”

Sautin kukan baby junaid ne ya cika mata kunnanta, murmushi tasaki tana fadin”My baby boy, ba hello ba hi sai kuka? So kake hankalina Ya tashi ko”?

Cikin shessheƙar kuka yace”mom..my wallahi kizo ki ɗoke ni, idan ba haka ba bazaki sake gani na ba, mutuwa ma zanyi” rass taji gabanta ya fadi,

“Junaid kadaina ambaton mun mutuwa, banaso, idan wani abu ke damunka ka faɗamin mana!” aɗan tsawace ta furta mashi maganar, tunawa da hajiya adama yasa ta sassauta muryarta,
“My baby boy, ka kwantar da hankalin ka, Yau in sha Allah mommy adama zata dawo min da kai”

Tsagaitawa yai da yin kukan, Muryarshi da shagwa6a yace”Ai ni tsoro nake ji, bana son zama agidansu....” bai ƙare maganar ba tayi sauri furta”shiru! Agaban mommy adaman kake fadin haka”?

“A’a mommy, ba agabanta bane, ai ta fita daga dakin”

Ajiyar zuciya ta sauke”yanzu fada min me ke baka tsoro? Ko wanine yake bugunka”?

“A’a mommy, idan ina bacci, sai ina ganin wani mutun sanye da baƙaƙen kaya hannun shi ruƙe da ɗan kwano, kalar wannan abun na ɗakin mami, wanda ake zuba fura a cikin shi, hannun shi zaƙo zaƙo da akaifu kalar na Ana mai girka mana abinci, wai yake ce min inzo mu tafi” zaro ido waje aneelerh tayi”Junaid ka natsu kayi min bayani, a mafarki kake ganin shi ko kuwa a zarihi? Kai kaɗai ka ke kwana aɗaki idan dare yayi”

“Ni ba mafarki nake yi ba, dagaske nake ganin shi, kuma a ɗakinsu nake kwana” aneelerh duk tabi ta ruɗe.

“Junaid kaji tsoron Allah, ka faɗamin gaskiya, nasanka da ƙarya, Idan baka fada ba, to bazan baka zoben Angel ba”

“Kin siyane”? Ƙumshe dariya tayi don tundaga kan yadda ya tambayeta ranta ya bata cewar ƙarya ya shirga mata.

“Na siya mana, ai jiya naba mahboob kuɗi Ya siya maka zoben mai kyan gaske”

Tuntsirewa yayi da dariya yana fadin”to mommy wasa nake yi maki, wallahi dama awani cartoon ne da muke kallo a tv, anan naga mutumin” fashewa tayi da dariya sosai har fararen haƙoranta suka bayyana”yanzu naji magana ɗan rainin wayau, duk kabi ka tasar min da hankalina, Yau har mafarkin ka nayi saboda nayi kewarka babyn mommy, ina sonka Yarona”

Yace”nima inasonki mommyn baby” dariya tasaki, idan yana yi mata magana kamar wani babban mutun daya mallaki hankalin shi, sai idan yayi wata kwa6ar ne zaka gane ƙaramin yaro ne.

“Mommy ina mamina? da abie, da uncle mai ƙaton hanci, da mahboob mai son kuɗi, da zahrah mai dogon wuya”

Tsabar yadda take yin dariya hada dafe ciki,
“Junaid baka da mutunci, Uncle dinne mai ƙaton hanci”!
Kaitsaye yace mata”eh mana, baida kyau Allah, mummuna ne uncle dan Iya, ni naji dadi ma bashine daddynki ba, da wallahi bazanyi kyau ba”

Mamaki ne ya kama Aneeleerh, jin yadda yake kushe mata kawunta.

“Junaid dan Allah ka yi shiru kada wani yaji ka, Ni zan ajiye wayar, ka koma bacci zuwa anjima Mommy adama zatayi maka wanka ta shiryaka sannan zata dawo mun dakai gida, fadamin me kake so in tanadar maka”?

Da shagwa6a yace”fura nakesho, asanya kwakwa da yoghurt aciki” bakomai ya tuna mata ba face Angel, tana son furar da aka sanya kwakwa da youghurt, kusan kullun idan tazo gidansu sai ta sanya Aneelerh ta haɗa mata ita, musamman saboda Angel take ajiye damarmar fura cikin robabi ta sanya mata su a frigde don su yi sanyi.

Tuni idanuwanta suka cicciko tab da ƙwalla, Muryarta na rawa ta furta”zan ajiye maka my baby boy, ka kwanta ka huta zuwa anjima zamuga juna” daƙyar ta samu baby junaid Ya ƙyaleta, badan ta gaji dashi ba, ta ajiye wayar on pillow, ta sauko daga saman gadon, A hankali take bin bedroom dinta da kallo, har idonta ya sauka akan hotonsu da ta liƙa shi a bango, wanda sukayi tare da aminnanta, su uku abunsu, kowacce ta ca6a uban adon lace, fuskokinsu ɗauke da murmushi.

Ta natsu tana kallon hotunansu, sam ba ta ji takun tafiyar mutun ba, har ta ƙaraso gefenta ta tsaya, Ƙamshin turaren zahra ne yaja hankalinta ga dubanta, tayi mamakin ganinta a ɗakinta, tun ranar da abunnan ya faru na hajiya falmata ko magana bata ƙara haɗa su ba, amma yau sai gashi ta tako ta shigo room dinta, dogon hijabi ne a jikinta daga ƙasa har sama launin maroon hannayenta biyu ta fiddo dasu ta cikin hannun abayar, hada cazbaha ta ruƙe tana ja kamar wata matan limam.

“Aunty Aneelerh Ina kwana, kin tashi lafiya”?

Daƙyar ta iya amsa mata da lafiyalou, ina fata kema haka”
Daga mata kai tayi alamar eh, idanuwanta sam basa akan Aneelerh suna akan hoton da take kallo, wani irin kunyarta take ji, tunawa da rashin mutuncin da tayi mata akan ta bata shawarar ta ba Hajiya falmata haɗin kai, tayi danasani tun jiya da Mahboob Ya fayyace mata komai.

“Nayi mamakin ganinki a ɗakina zahra, ai nayi tunanin mun rabu kenan har abada”

Girgiza kai zahra tayi”Idan kinga mun rabu to mutuwace ta raba”

Aneelerh sam batasan Mahboob ya fada ma zahra ba, bayan ta gargade shi akan karya gaya mata, shi kuma bayason suna gaba atsakaninsu, don ya fahimci zahra ta fusata sosai, Idan har bai fada mata gaskiya ba to kuwa zata cigaba da zabga ma Aneeleeh rashin mutunci abisa rashin sani shiyasa ya yanke shawarar ƙwara ya faɗa mata, don ta yi takatsantsan kada ta wuce gona da iri azo aji kunya.

“Kiyi haƙuri da abunda Ya faru atsakanin mu, nasan na 6ata maki rai, tuntuni nake taso in nemi yafiyarki, sai dai baki bani damar yin hakan ba” Aneelerh ce tayi maganar tana duban zahra.

Cikin sanyin murya zahra tace”ni yakamata nabaki hakuri auntyna bake ba, saboda ni ce mai laifi, ban kyauta maki ba, duk irin shaƙuwarmu da kyautatamin

71 / 84