Kurkukun Kaddara Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Boss Bature Category :  Complete Novels

Chapter   29 / 84

84K to 87K   out of 250.5K words

gaji da haɗuwa, babu tazara a tsakanin ɗakunansu da inda aka kwantar da su Haris duk acikin amenity ward ne.

Abakin ƙofar ɗakin da aka kwantar da Haris suka tsaya, sai da nurse ɗin ta fara tura ƙofar ta shiga tukunna Ɗaya bayan ɗaya su ka soma shiga cikin ɗakin cike da zumuɗin son ganin ɗan uwansu, tun kan su ƙarasa suka hango Haris kwance magashiyan saman medical bed an sanya mashi robar oxygen a hancin sa.

Da sauri suka ƙarasa gaban gadonshi, gida biyu suka raba kansu, gefen dama Gabriel ne da Javed sai Naufal da Parveen ta 6angaren hagu Angel ce da Batul, Jamimah da azeeza sai Hannah, tsananin tausayin Haris ne Ya kamasu, tuni idanuwansu sun cicciko tab da ƙwalla.

Cikin shessheƙar kuka Angel ta ambaci sunansa”Haris!” har cikin dodon kunnanshi Kiran Ya isar mashi, sambatu ya soma yi masu Yana ambaton sunan Deeja yana faɗin”mu koma ku ɗauko ta, Deeja na tana araye suna can suna azabtar min da ita, dan Allah ku taimakamin ku cece rayuwata ku ɗauko min deeja na” tuni Hawaye sun wanke fuskokinsu, Hatta nurse rebecce Dake atsaye jikinta yai sanyi ganin hawayen su, Duk da bata iya jin abunda ɗan uwan nasu ke cewa

“Haris”! Muryar Angel ce ta ƙara ratsa kunnan su, A hankali Ya soma ƙoƙarin buɗe idanuwansa da suka kumbura jawur ya ɗaura su akan fuskarta, Ware su yai sosai, Ganin Yana ƙoƙarin miƙewa yasa Nurse ɗin Yin saurin matsawa bakin gadon ta rankwafa ta zame mashi roban oxygen din daga hancinsa, ta taimaka mashi Ya miƙe zaune Bayan ta sanya mashi pillow a tsakankanin bayan shi da headboard na gadon.

Sun natsu suna kallon shi, azabar ciwo tasa shi canza kamanni, fatarshi ta yi haske Ya rame sosai, hakan ba ƙaramin Kyau ya fiddo mashi ba, sumar kan shi a cukurkuɗe kamar mahaukaci sabon kamu, ɗaya bayan ɗaya ya ke binsu da kallo Yana ambaton sunansu da raunatacciyar muryarsa
“Angel, Batul, Azeeza, Jamimah, Hannah, Javed, Naufal, Gabriel..” Numfashi Yaja Kafin ya furta sunan Deeja”Ya akai banganta ba? Ina aka kaimin deejana? Baku zo da ita ba”? Idanuwanshi acike tab da hawaye yai masu maganar

Cikin sanyin murya Angel tace”Haris pls ka daina sanya damuwa aranka, dubi kaga yadda ka rame, tamkar ba Haris ɗin mu ba, duk kabi ka zauce, Why pls? Bama Jin daɗin canzawar da ka yi, gashi baka da ƙoshin lafiya”

daƙyar sautin muryarshi ke fita”Bazan Iya jurewa bane Angel, inason deejana ina jin tsoron ace narasa ta, donni inaji araina tana araye tun da har su azeeza basu mutu ba, Itama sumane tayi”

“Haris idan har baka kwantar da hankalin ba, Ta ya ya zamu Iya samun ƙwarin gwiwar fallasa asirin masu kurkukun ƙaddarar har muci nasarar ɗauko sauran ƴan uwanmu da suke acan idan basu mutu ba? Dole fa sai ka bamu haɗin kai ka danne damuwar dake aranka tukunna zamu Iya Cin galaba akan su”! Angel ce ke yi mashi magana cikin kwantar da murya

Gabriel ya ɗaura da cewa”Kin faɗi gaskiya Angel, Haris pls ka taimaka ma kanka muma kuma ka taimake mu sannan ka taimaki rayuwar su Deeja Rashin lafiyarka shi zai tarwatsa mana shirin mu, Nurse ta faɗamin abunda ke damun ka, Ciwon zuciyane Haris kuma nasan bakomai ne ya jawo hakan ba face Deeja!! kaga yanzu mun ku6uta daga Daji muna acikin mutanan duniya, Nan inda muke asibiti ne Inda ake duba marasa Lafiya sune suka bincika lafiyarka kuma suka tabbatar mana da cewa damuwace ta silar wani abu daka ƙwallafa rai akan son shi, pls Haris Ka taimaka mana! Idan har ba ka ji sauƙi ba Likitocin nan bazasu ta6a bari mu koma Nigeria ba gidan daddyn Angel” tunda Gabriel Ya fara magana Haris Yake bin ɗakin da suke da kallo, sai lokacin Ya gane ba adaji suke ba, shifa gaba ɗaya baya acikin hayyacinsa baisan ma a ina yake ba, idanuwanshi sun makance.

Azeeza sarkin tausayi tun da ta tsareshi da ido, Hawaye ke bin fuskarta.
Cikin shessheƙar kuka tace”Dan Allah haris ka yi haƙuri, In sha Allah deejan mu bata mutu ba da sauran ƴan uwanmu Zamuje mu ɗauko su”

Batul tace”kwanciyar hankalinka kawai muke buƙata Haris, idan ba haka ba kaga zaka mutune kafin muyi nasarar dawo da su deeja, me kake tsammani idan Ka mutu muka gano deeja araye ya za ta ji? Ka mutu saboda ita? Kaima ka sani yadda take ƙaunarka itama mutuwa zatayi tabi ka”

lumshe idanuwanshi yai, ƴan uwanshi ba ƙaramin sanyaya mashi zuciya suke yi ba, sai kwantar mashi da hankali suke yi duk don su samu ya wartsake

“Ina ɗan uwana”? yai tambayar yana kallom faces dinsu
“Danish bai farka ba Haris Har yanzu, bacci yake yi, “ Angel ce ta bashi amsa, damuwace ƙarara akan fuskarshi
“Angel wani irin bacci ne wannan Har yanzu bai farka ba? Ina jin tsoro wani abu yasame shi” girgiza kai Angel tayi”a’a Hairs ba abunda zai same shi, Ni inaji araina Lafiyar danish qalou, Bacci ne kawai ya ke yi kasan ya ɗauki tsawon lokaci bai runtsa ba shiyasa bai farka ba”

Gyaɗa kai yai”Allah yasa hakane,”
. “Haris ka ci abinci ko kana jin yunwa”? Kallon parveen yai”bana Jin yunwa parveen, Naji daɗin kulawarku agare ni, sannan Ina tayamu murnar barin kurkukun ƙaddara” murmushi kowan nan su Ya saki, shima ya ƙalalo murmushi akan fuskarshi

Muryar Jemimah da shagwa6a tace”Idan ka ji sauƙi, zamu ga deeja ma har kuci abinci atare da ita, kana bata abaki itama tana baka abaki, agidan daddyn genie ɗita” gaba ɗayansu suka sanya dariya, Nurse rebecca dake tsaye tuni ta zauna saman chair tana dubansu sam bata gajiya da kallon Yaran burgeta suke Yi kamar ta sace su take ji.

Haris Ya ji daɗin maganar Jemimah har saida yaɗan murmusa
“Sannan Haris zai dinga wanke ma deeja gashin kanta yana sharce mata shi,” Batul ce tayi maganar, tsabar daɗin maganarta har saida fararen haƙoransa suka bayyana.

“Bayan haka zai dinga goyata a saman bayanshi Suna yawo” acewar Hannah sosai Haris ya fashe da dariya yayin da hawaye ke cigaba da yin sintiri akan fuskarsa, Lamarin ya ɗaurewa rebecca kai, mamakinta yadda yaran suke matuƙar ƙaunar junansu, wani abu da ya ƙara burgeta yadda suke ta sanya shi dariya tabbas su ka ɗai suke Iya sarrafa junansu.

“In sha Allah Haris our dream will come true” lumshe idanuwanshi yai tare da buɗe su akan fuskokinsu sai ya dinga ganin tamkar Deejar sa ce zaune a tsakiyar gadon tana sakar mashi murmushi, hakan yasashi sakin murmushi kamar wani zautacce

“Haris ka kwanta ka huta, kada mu cika ka da surutu, zamuje ɗakin Danish mu duba shi”

“Nima inaso naganshi Angel, muje atare”

Kallon Nurse ɗin tayi”pls sister zamu Iya tafiya da shi ɗakin ɗan uwanmu”?
Smilling gently, nurse rebecca tace”badamuwa, zamu Iya tafiya da shi” ta yi maganar tare da miƙewa Ta nufi gaban gadon, da taimakonta Haris ya sauko daga saman gadon tace mashi ya dafa shoulder ɗinta don ya samu damar yin tafiya, Rurruƙeta yai da hannayenshi a haka suke Yin tafiyar, Su Angel suna abayansu har suka ƙaraso ɗakin da aka kwantar da garkuwa, Jikin Angel har 6ari yake yi saboda tsabar zumuɗi, tun kafin su ƙarasa shiga ɗakin suka hango Danish Baje saman gadon, kamar matacce, lallausar sumar kanshi ta tarwatse saman mattress ɗin gadon, da sauri Angel ta nufi gadon Ta haye daga gefe Idonta akan Kyakkyawar fuskarshi, Har kullum kamar ana ƙara ninka mashi kyawunshi, fatarshi tayi smooth fara sol Ko tabo babu, Sun canza mashi uniform ɗinshi wanda ke a jikin sa Yanzu kalar nasu ne Riga da wando light blue, rigar tayi tighting ɗinsa, gajeran hannu ne da ita Hakan ya bayyana ƙaƙƙarfan Damtsen hannun shi, Likitoci sun sha wahala wurin canza mashi kayan Jikinshi saida suka haɗa ƙarfi tukunna su ka samu damar raba shi da su.

A hankali take bin Shi da kallon so da ƙauna tun daga saman sumar kanshi har i zuwa kan Long eye lashes ɗinsa, dogon hancin nan nashi yayi sam6al babu lanƙwasa, full lips ɗinsa sun ciza launinsu, slowly ta sauke idonta akan Zanan tattoo dake a gefen dogon wuyanshi Yayi bala’in yi mashi kyau
A gefe da gefen gadonshi kowannansu Ya samu wuri ya zauna hada haris da nurse ta zaunar dashi, natsuwa su ka yi a yayin da su ke kallon ɗan uwansu, daɗi kamar zai kashe su
Angel ta shagala da kallonsa ji ta ke kamar ta faɗa saman chest ɗinsa ta ƙanƙame shi ko ta samu sassaucin kewarsa da ta ke yi, Muryar Haris ce ta fargar da ita.

“Angel zuciyarshi tana bugawa”?

A hanzarce ta kwantar da kunnanta saman chest ɗinsa saitin heart ɗinsa nan take taji bugun zuciyarshi na harbawa a tsanake
Ɗagowa tayi fuskarta ɗauke da murmushi tace dasu”zuciyarshi tana bugawa, bacci ne yake yi”

Jin haka yasa Kowan nan su Ya matsa kusa da shi, ɗaya bayan ɗaya suke ɗaura kunnuwansu saitin zuciyarshi, nurse rebecca dake a tsaye murmushine ɗauke akan fuskarta

hankalinsu ba ƙaramin kwanciya yai ba, jin zuciyarshi na bugawa

“Sai yaushe zai farka? Baccin yayi yawa” Javed ne yai maganar, Naufal yace”may be saiya ɗauki adadin kwanakin da yayi bai runtsa ba tukunna zai farka” zaro ido Angel tayi haɗi da girgiza kanta”in sha Allah ba zai kai wannan lokacin ba zai farka.

Ta ƙare maganar tare da ruƙo zira ziran yatsun hannun Danish na dama acikin nata, sosai ta runtse su (nima kuma na runtse alƙalamina)



*Boss Bature✍️ Mu haɗu gobe Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuɗin*



First bank



3196407426,



*Bature Hafsat Muhammad, za’a tura evidence of payment ta phone number ɗina 08169856268 Banda kira whatsapp kawai*



_~*BossLadiesWriters*~_


_*KURKUKUN ƘADDARA*_


~Middle step~


_The Prisoners E17🔥💫_



*Daga alƙalamin Boss Bature*




A ƙalla sun shafe kusan 30 minutes a ɗakin Danish, Ji suke kamar abarsu su kwanta a ɗaki ɗaya saboda haka su ka saba kwana a kurkuku, daga bisani Nurse tace dasu zasu tafi zuwa gobe zasu Iya zuwa su ƙara duba shi’ jiki asanyaye suka miƙe suna tafiya suna waiwayon shi musamman Angel ji ta ke yi kamar ta koma ta rungume shi.

Bayan fitar su daga ɗakin, Nurse Ta raka kowan nan su room da aka kwantar da shi, ba su so aka raba su ba, har yanzu tsoron mutanan su ke ji, ba dan Angel ta lalla6a su ba da ko babu inda zasu je, a ɗakinta zasu kwana, musamman Azeeza da jemimah ɗaƙyar Angel ta lallashesu ta lalla6asu don ta fahimci dokar asibitin ce haka ba’a haɗa mutun fiye da ɗaya a ɗaki, wata’ƙil sai idan ya kama dole, sauƙin ma kowan nan su akwai nurse ɗaya da ke kula da ɗakin shi, duk wani abu da zasu buƙata zasu yi masu, hatta toilet suna raka mutun In ya buƙaci hakan musamman gasu da basu san yadda zasuyi amfani da wasu abubuwan ba.

A daren ranar sun yi kwanan farin ciki basu da wata damuwa.

*Daular Alhaji Musa wadata*

idan nace zan tsaya zayyana maku zunzurutun Kayan alatun da ke a gidan Alhaji musa daga ni har ku zamu koma Yin Mafarkinsa ne, wato Haɗaɗɗiyar Daular arziƙi ce, Katafaren Villa ne Wanda Idan ka zura ƙafarka acikinsa tamkar ka Bar Nigeria ka shiga Dubai ne, Aljannar duniyace ƴar ubansu, A ƙalla security din dake tsaron Kafcecen Gate ɗin shiga gidan sunkai su goma shabiyar, Wasu gabza gabzan Garada Masu Ƙirar sadaukan Yaƙi, Babu wasa akan fuskokin su, Bana tunanin ko aljani zai Iya gifta gate din gidan salin alin ba tare da sun cafke shi ba, Shantalelen titi ne zai sadaka da Cikin gidan kai tsaye daga bakin babban gate ɗin, yadda kasan da zallar goal aka ƙera ginin saboda ɗaukar idon gilassan Ƙofofin da Windows, ko gidan shugaban ƙasa albarka, Babu ce kaɗai ke babu agidan Alhaji musa, komai na gidanshi babu made in Nigeria, an zabga almubazzarancin dollar wurin ƙera ginin, don hatta sample dinsa da ƙwararrun da suka ginasa kaf aikin turawa ne.

Mamaki da al’ajabin dukiyar Uncle din nasa Ya hana shi Kwantar da hankalinsa, Tun Bayan da escords suka ɗauko su daga airport, Motocin suka shigo gidan gabanshi ke ta faɗuwa, saboda sabon gini ne baya a ƙasar Uncle ɗin nasa Ya mallake shi, shiyasa komai yake ɗaure masa kai, Kafin shigarsu gidan Saida shureim Ya dinga jero addu’o’i acikin zuciyarshi Yana neman tsari akan Allah ya kare shi daga shagalar duniya, Idan har zaman shi gidan ba alkhairi bane, Ya roƙi Allah da ya yi mashi silar barin shi cikin sauƙi ba tare daya sha Wahala ba.

Tun da suka shiga gidan Kamar wani baƙauye Haka ya dinga bin ko’ina da kallo, wasu matsiyatan Chandeliers saman ceilling Masu ƙyalƙyali tamkar zasu rubzowa mutun saman kanshi, Ga wasu Haɗaɗɗun twins stairs, masu ɗauke da Glass Elevator a gefensu. Idan ka shiga cikinta Kana iya hangen mutanan dake zarya a palourn Yayin da take Yin sama dakai ko take dawowa dakai ƙasa.


A katafaren Palourn gidan kuwa Wasu Jigunannun Royal Sofas set ne Ƴan ubansu masu numfashi Ga Arm chairs kalar Na sarakuna, A gefe da gefen kujerun Sofa table ne, Tiles din palourn baida banbanci da Mirrored tiles Kana kallon Fuskarka acikinsa Idan kana Tafiya, zallar haɗuwa, An zuba komai na more rayuwa, Idan nace zan tsaya zayyana haɗuwar Komai dake acikin Gidan Tabbas zamu ƙare middle step da last step acikin gidan Alhaji musa (🤣)

Babu wanda Yasan da zuwansu, Hatta Iyalinsa Ba su san da dawowar shi a yau ba, yana ɗaya daga Cikin Halayan Alhaji musa, Idan zai yi tafiya babu wanda ke sani Matar shi ko ƴa’ƴanshi, Haka zalika Idan Zai dawo sai dai su ganshi, saboda zuwan ba zata Ya ke yi masu.

A Kwance take saman Prayer mat, Tasha Dogon Hijabi a jikinta duk ta ƙudundune kanta acikinsa, daga gaban dardumar Qur’anic Stand ne, ga dukkan alamu Bacci ne Yai awon gaba da ita a yayin da take Yin karatun al’ƙur ani mai girma.

“Zeenat! Kiran Sunanta da akayi ne Yasa ta firgita a Hazarce Ta farka daga baccin ta ɗago da kanta tana faman zazzare dara daran Kyawawan idanuwanta farare ƙal launin Ocean Blue, Masha Allah Kyakkyawar matashiyar budurwa Kamanninta sak Alhaji musa tamkar yayi kakinta, sai dai Daga gani Farar fatace Haskenta ya ɗare na mahaifinta, Fara ce sol Jawur da ita, tana da yalwatacciyar sumar kai Launin blonde har saman fore head ɗinta kwantaccen gashi ne, ga doguwar fuska, dogon hanci da ƙaramin baki launin pink, Ba ta da ƙiba ko misƙala zarratin siririya ce, abu ɗayane ke da girma a jikinta, dukiyar fulaninta acike suke kamar an jera balon balon.

“Zeenat! Bacci ki ke Yi”? Muryar Mahaifiyartace ta rasa kunnuwanta, da sauri ta zabura ta miƙe tare da wurga ƙwayar idanuwanta kan Mai shigowa ɗakin, babbar macace mai cikar kamala, Ta ɗauki wankan Shadda ajikinta launin Ja, Tasha uban ado akan fuskarta, baturiyace Siririya bata da ƙiba, daga ganin surarta a wurinta matashiyar budurwar ta gado hasken fata da launin ido, da kuma doguwar sumar kai, Hajiya Sarah Uwar gida kuma amarya awurin Alhaji musa, ta ɗaure kanta da kallabi, hakan bai 6oye doguwar sumar kanta da ta sauko har gadon bayanta, Necklace ɗin wuyanta da earrings ɗinta na zallar diamond ne sai ƙyalƙyali suke Yi da ɗaukar ido.

Muryarta Adisashe ta amsa mata”mommy karatun ƙur’ani nike Yi bacci ya ɗauke ni bansani ba” ta yi maganar tana Yin miƙa haɗi da yin hamma

“Ba ki ji dirar motoci ba ne”? Ras Taji gabanta Ya faɗi, Muryarta na rawa ta furta”dad... daddy is he back “?

Ta6e baki Hajiya Sarah tayi”ya dawo tun ɗazu, yanzu haka yana a ɗakinsa, yace baya son takura, kinsan halinsa”

Hankalin Zeenat Ba ƙaramin tashi yai ba, ta rasa gane farin Ciki za ta yi ko baƙin Ciki, Tana son mahaifinta sosai, sai dai tana mugun jin shakkarshi saboda rashin sakar masu fuska da baya yi, duk da wani lokacin idan yaso yana nuna masu so da ƙauna.

Jin ta yi shiru zugudum tana faman zazzare ido Yasa Hajiya Sarah cewa”ya naga kamar baki farin Ciki da dawowarshi”? A hanzare ta girgiza kai” “I’m so happy he’s back, na yi murna ai shi ɗinne baya son takura”

Murmushi tasakar mata”Albishirinki”!
Da mamaki ta tsayar da eye balls ɗinta kan face din momyn nata
“Goro”!
“Fari ko ja”
“Fari”
Matsawa Mommyn ta yi kusa da ita Cikin raɗa ta furta mata”Ba shi kaɗai ya dawo ba, Hada Yayanki Dr shureim yanzu haka Yana kwance a bedroom ɗin da aka ware masa” Tun kafin Hajiya sarah ta ƙarasa Maganar, Zeenat ta zube saman gwiwowinta tare da ɗaura goshinta saman tiles ta yi Sujjada tsabar farin cikin jin anzo mata da sahibinta

“Ah lallai ashe Har yanzu Kina son Yayan naki, Hada Yin sujjada” ɗagowa Zeenat Tayi, tare da miƙewa tsaye Hijab ɗin jikinta sai Ja da ƙasa Yake yi.

“Mommy bazan Iya jurewa ba, Zanje wurin Yayana inyi mashi barka da zuwa” tsantsar farin cikine akan fuskarta

“No kada ki je Yanzu ki bari masu aiki su kammala Girka mashi abinci, In yaso sai ki je ki kai mashi a ɗakinsa, Daddynki ne Ya bada Umarnin A girka mashi abinci hausawa”

Zeenat da takasa rufe bakinta don Murna duk tabi ta ƙagara don a kwaɗaice take da son ganinsa
“Na faɗa maki zuwanshi ne Don ki kimtsa, Ki gyara kanki, Nasan Halinki da sanya dogon Hijabi salon kije mashi ahaka, Ki samu Ko ɗan gyalene ki yafa a kafaɗa,” turo baki zeenat

29 / 84