Author : Boss Bature Category : Complete Novels
hannunshi ɗaya ruƙe da Cup na coffee
Mamaki ne ƙarara akan fuskarshi Jin dr jazz na Zancan kajin turawa awaya
“Okey toh, Zuwa anjima idan nashiga gidan Gonar zan Kiraka Awaya” Daga haka sukayi sallama, Juyawar da zaiyi karaf suka haɗa ido da sir mubarak, tuni yasha jinin jikinsa, Duƙar da kai ƙasa yai ido ya raina fata
“Jazz! Dawa kake magana a waya? Kajin menene naji ana magana akai? Ni dai A iya sanina likitan mutane ne kai bana dabbobi ba” sosa ƙeya jazz yai, mirya dabarbarce yake faɗin”am...umm..dama “ Ya rasa ta ina zai taro zancen,
Kallon tuhuma Sir mubarak ke jafa mashi hakan yasashi yin saurin fauzewa
“daddy, Ni da abokina ne dr fawan muka buɗe gidan gona, kajin turawa ne muke kiwo, wasu ne babu lafiya shine ya kira muna tattaunawa game da yadda zamu shawo kan matsalar”
Ajiyar zuciya Sir Mubarak Ya sauke”Okey, mu shiga gidan” yai maganar tare da miƙa mashi Cup din hannunsa, da sauri jazz Ya kar6a Yana sha atare suka nufi gidan sai faman sauke ajiyar zuciya yake yi.
*GIDAN ƊAN IYA*
Mahboob ne ke ta faman zuba sauri Yana tunkarar harabar ajiye motocin su, ya ɗauki wankan shadda, tunkan Ya ƙarasa idonshi ya sauka akan motar Uncle abdallah, ƙura ido yai yana kallon bayan motar sunanta Ya karanta, Aranshi Ya ayyana lallai mutanan nan ba ƙananun shaggu bane wannan mota haka mai tsada! saboda almubazzaranci da rashin sanin ciwon kuɗi, Ina laifin ko ƴar ƙaramar honda mutun ya saya ya wadatar, mutane sun ɗaurewa ƙaryar arziƙi wurin zama, Allah dai ya shirya mu, ae ni wlh ko nayi arziƙi ban Iya fidda kuɗina in sayi mota, na ƙwammace duk inda zanje in taka da ƙafata, idan ma da nisa ne ƙwara in biya kuɗi In hau motar Haya, Ita ma wannan motar da nake amfani da ita ba don babansu abokina ne ya bani kyautarta ba kuma ina ganin mutuncin shi saboda ya ji tausayina ya siyamin ganin ina hawa motar haya yasin da tuni na jima da siyar da ita’ Shi kaɗai ya ke yin sambatunsa, Har ya ƙarasa gaban motarshi Ya buɗe front seat Ya shiga Ciki Yana ƴan dube dube, da alama wani abu yake nema, saƙo da lungu na motar yake ta bincikawa, har ƙarkashin seat, tuni ya haɗa uban gumi.
“Ina na ajiye zoben nan Jiya? Ko dai ban shigo da shi mota bane? fuskarshi a hautsine Ya jefawa kanshi tambayar, zurfin tunani ya shiga yi still bai tunano inda ya ajiye shi ba, A ƙarshe Ya soma tunanin kodai Ya shigar da shi ɗaki ne,
Fitowa yai daga cikin motar Ya datse murfin, Jiki na 6ari ya nufi cikin gidan.
Abie da Uncle ɗan Iya ne zaune a saman sofas na palourn tare da Uncle abdallah, Sun nutsa suna tattaunawa dangane da 6acewarsu tajuddeen, Mahboob Ya faɗo falon Ko kallo basu ishe shi ba hankalin shi na akan zoben shi da bai gani ba.
“Wancan ba mahboob bane? Kamar naso na wayi fuskarshi” Uncle abdalla ne yai maganar,
Girgiza kai uncle ɗan Iya yayi Yayin da yake bin bayan mahboob dake ƙoƙarin karya kwana zai nufi sashen ɗakinsa
“Shine, halan bai gaishe ka ba”?
Murmushi ɗauke akan fuskar Uncle Abdalla yace”Tun da muka zo ban yi tozali da shi ba, sai dai naji labarin shi awurin junaid”
Cikin nuna 6acin rai Ɗan Iya yace”baida wayau ne ai ni bansan baizo ya gaishe ka ba, bari ya fito daga ɗakin ɗan rainin wayau, Zahra tafi shi hankali”
Abie yace”Ƙuruciyace ke damunshi, Zahra kuma ae tafi shi shekaru baza a haɗata da shi ba”
Ɗan Iya yace”babu wata ƙuruciya atare da shi, Sarai yasan me yake yi sai girman jiki ba wayau” da alama Ranshi ya 6aci da rashin gaishe da uncle abdallah da baiyi ba.
Kafin wani daga cikinsu ya ƙara yin magana Hajiya adama ta fito daga ɗaki hannunta ɗauke da baby junaid, tun da ya dawo daga school a wurinta ya wuni ya hanata sakat duk inda za ta je ƙafarta kafarshi toilet ne kaɗai yake bari ta shiga, Ta canza Kayan jikinta zuwa atampa riga da skirt, Ta yafa mayafi akanta, kafin ta ƙarasa shiga palourn Mamie ta fito daga ɗakin Ummi su biyu ganinta yasa suka nufi wurinta fuskokin kowannansu da fara’a suka soma gaisawa da junansu
Atare suka ƙarasa shiga palourn, Kowa ya samu wuri ya zauna, Kafin suka fara gaishe da Mazajensu, miƙa ma junaid hannu uncle abdallah yai”zonan kyakkyawan Jikana mu gaisa,” da sauri Junaid ya sauko daga saman laps din Hajiya adama ya nufi sofa ɗin da uncle abdalla yake azaune Ya haye saman jikinshi yana faman sakar mashi murmushi, shafa fuskarshi yai da tafin hannunshi”Masha Allah mutumina, Ka tashi lafiya? Fadamin meyasa baka je school ba yau? Sannan baka bi mu zuwa masallacin Juma’a ba” Zaro ido Junaid yai haɗi da ɗan girgiza kanshi muryarshi da shagwa6e yace”nafa je, ae yau da wuri ake tada mu duk ranar juma’a, kuma ni ai ban isa zuwa masallaci ba inji mommy” maganarshi ba ƙaramin ƙayatar da su take yi ba, musamman In ya haɗa da shagwa6a,
“Junaid kaji tsoron Allah, Aneelerh ce ta faɗa maka haka? Faɗamin gaskiya ka dai san me ƙarya ɗan wuta ne” jin haka yasa shi saurin sanya tafukan hannayenshi biyu ya toshe fuskarshi Yana tiƙar dariya” muryarshi ƙasa ƙasa ya furta”ba ita bane, ae malaminmu ne yace mu ƙananu ne bamu isa ɗaukar zunubi ba” gaba ɗaya suka saki dariya, bayan sun tsagaita da yin dariyar ne, Uncle ɗan Iya yai masu gyaran murya hakan yasa suka dawo da dubansu gare shi.
“Dama yanzu nake shirin aikawa a kira mun ku, don mu haɗu duka muyi magana, Kafin mu shiga cikin zancen Ina ƙara yiwa baƙinmu barka da zuwa fatan kun wayi gari lafiya” da fara’a Hajiya adama ta amsa mashi a mutunce
Mami tace”tun ɗazu da safe take son yin magana mun fara sai nace ta bari idan kuka dawo daga masallacin juma’a zaifi mu haɗu mu duka mu tattauna tunda abune daya shafi kowannanmu da buƙatar aji shawara daga bakin kowa”
Jinjina kai Abie yai”hakane, Yanzu Ina aneelerhn take”?
“Tana a ɗakin zahra, Bari na shiga na kirata” kafin ta mike muryar junaid ta katse mata hanzarinta.
“Ni zan Kirata” Bai jira amsarta ba, Ya sauko da gudu Ya nufi Ɗakinsu, uncle abdallah ne ya ɗan ɗaga murya yana yi mashi faɗan ya daina gudu kada ya faɗi yaji ciwo, Jin haka yasa shi dakatawa da yin gudun ya soma yin tafiya a tsanake
A lokacin Aneelerh da Zahra suna zaune saman gado kowa ya dafi waya suna fira suna chatting, sun ɗauki wankan dogayen riguna
“Ba zaki leƙa wurin surukar taki ba? Kin barta a ɗaki ita kaɗai” acewar zahra
“Ɗazu da safe na shiga na gaishe ta, har ma na tarar da mami zaune suna tattaunawa shiyasa ban tsaya ba,”
“Gaskiya aneelerh ki godewa Allah, surukarki tana da mutunci ta iya magana ga faran faran da jama’a, Ni wlh ba ƙaramin burgeni take yi ba, Inasonta sosai, da ace tana da wani ɗan Bayan Yaya uzair Allah dana aure shi” har cikin zuciyarta take yin maganar,
Aneelerh na murmushi tace”Chief Owais din fa? Ko kin fasa”! farfari Zahra Tayi mata da ido
“shi wannan na dabanne, idan ana maganar ƙarauƙarau ba a maganar Zinari, My dream man inaji araina ma ya kusa dawowa ƙasar jiya har mafarkinsa nayi”
Murmushin gefen fuska Aneelerh ta saki
“Allah Ya cika maki burinki zahra, Ni na ƙosa inga fuskar Owais ɗin nan, har tambayarki nayi hotonsa kinƙi ki nuna min, bansani ba ko rowa kike yi min” dariya Zahra tayi”Ina jin fargabar zuciyarki ta buga silar ganin kyakkyawar fuskarshi, kuma kinga ke matar aure ce bana son ki kalli haramun” Sakin baki aneelerh tayi yayin da take kallonta, tama rasa bakin magana
“Fuskarshi tsadane da ita, idan har zaki Iya biyan farashi sai muyi ciniki in nuna maki” fashewa da dariya aneeleeh tayi jin wani zancen abakin zahra.
Faɗowa Ɗakin Junaid yai tun abakin ƙofa yake faman ƙwala mata kira”Mommy!mommy!” a hanzarce ta kai idonta ga ƙofar
“Babyn mommy lafiya kake ta ƙwalamun kira” tai maganar tare da sakowa daga saman gadon ta nufe shi, hannu biyi tasa ta ɗauke shi tana kallon fuskarshi
“Mommy ana kiranki, ki zo inji su abie”
“Sune sukace ka kira ni”? Ɗaga mta kai yai alamar eh ya ƙara da cewa”ke kaɗai banda Zahra”
Harara zahra Ta wurga mashi”aiko sai naje ɗan baƙin ciki, so kake kayi mun buƙulu wata’ƙil ƙudi ne za’a raba mana,
Saukowa tai daga saman gadon ta ɗauko masu mayafi a closet ita da Aneelerh ta yafa mata akanta, atare suka fuce daga ɗakin zuwa palour
Hankalin Mahboob Ba ƙaramin tashi yai ba, ganin babu zoben a ɗaki, duk yabi ya birkice ɗakin, ya tarwatsa komai, Hatta zanin gadon shi da fululluka duka yayi wurgar dasu saman tiles, ya zazzago da jerin ninkakkun kayansa na cikin wardrobe kaf dinsu Ya bazasu saman gadonshi, zufa ta ko’ina, Bawan Allah shine har ƙarkashin gado neman zobe, Cikin drawer chest, da laundry basket, kanshi harya fara yi mashi ciwo, ya tsani asara a rayuwarshi, a haukace ya tura ƙofar toilet dinsa ya shiga ciki Yana neman zoben, gaba ɗaya ya fara zaucewa, ganin babu zoben a toilet ɗin ya dawo ɗakin, yana haki zufa sai tsastsafo mashi take Yi, Idanuwanshi sunyi jawur dasu luhu luhu yakai maƙura tamkar zai rushe da kuka, jiri ne ya fara ɗibarshi a hanzarce ya koma gefen gadon shi ya zauna tare da sanya hannayenshi biyu ya tarbe kanshi Takaicin duniya ya ishe shi, bakomai yake tunawa ba face kuɗin da Aka sayi zoben, har zazza6i yai daya miƙa su dubu goma sha biyar. Ahakama kuɗin bada guminsa ya same su ba, Abokin shi ne ya siya mashi zoben saboda ya nuna yana so kuma baida kuɗi.
*Boss Bature✍️ Mu haɗu monday Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuɗin*
First bank
3196407426,
*Bature Hafsat Muhammad, za’a tura evidence of payment ta phone number ɗina 08169856268 Banda kira whatsapp kawai*
_~*BossLadiesWriters*~_
_*KURKUKUN ƘADDARA*_
~Middle step~
_The Prisoners E16🔥💫_
*Daga alƙalamin Boss Bature*
Kusan a tare Aneelerh da zahra su ka shigo palourn, a saman carpet kowan nan su yai zaman cin tuwo Junaid na azaune gefenta, tun da su ka zauna idanuwan su Mami da Abie na akan su, at same time suka haɗa baki wurin gaishe dasu cikin girmamawa, fuskokinsu Uncle abdallah da fara’a suka amsa masu.
Bayan kowan nan su Ya natsu, Hajiya adama ta soma magana cikin nutsastsiyar murya
“Dama jiyane Aneelerh ta ke faɗamin dangane da tada zancen 6acewarsu tajuddeen da za’ayi, a gaskiya naji daɗin jin hakan sosai, Kuma na yabama zahra da ta kawo wannan shawarar ta yi tunani mai kyau” Tun da ta fara magana sun natsu suna sauraronta, Zahra sai faman washe baki take yi jin anyabi shawararta, tana matuƙar son taga An yabeta.
Bayan Hajiya adama ta ƙare magana Uncle abdallah Ya ɗaura da cewa”yanzu haka abun da mu ke tattaunawa akai kenan, Ni kaina Naji daɗin tunanin nan da akayi abune mai kyau da buƙatar atada zancen 6acewar su ya dawo sabo, wata’ƙil ta silar hakan Allah ya agaza mana Muji ɗuriyarsu duk da bamu da tabbacin ko suna araye don ni har yau bana ji araina cewa babu su a doron duniyar nan!”
Numfasawa Abie Yai Kafin ya ɗaura da nashi jawabin”In sha Allahu muna sa ran wannan Karan zamuci nasara, dama dalilin taruwar mu anan don kowa Ya bada tashi shawarar” Bayan Kammala Maganar abie, Uncle ɗan Iya Ya soma magana
“Na riga nayi magana da Ziyad babban ɗan jarida ne, Tun ranar da muka Yi magana da Aneelerh, ta turo min hotunansu already na tura mashi su, da duk wasu bayanai da za’a buƙata, Ya ce min in sha Allah cikin weekend da zamu shiga komai za’a fara yaɗa labarinsu” Murmushine Ya bayyana akan fuskokinsu da alama sun ji daɗin Jin hakan
Uncle abdalla yace”Wai kana Nufin Ziyad ɗan Gidan senate Lateef”?
Jinjina kai Uncle ɗan Iya yayi”ƙwarai kuwa, Ziyad yanzu ae shi ke jan Ragamar Companynsu Na jarida mai suna Obinna News Network (ONT) Yaron Akwai hazaƙa Kullum ne saina bibiyi Labaransu a shafinsu, ƙwararrune a 6angaren Aikin Jarida, duk wani labari da zaiyi trending a social media Sune na farko da zasu fara buga shi a shafinsu”
Uncle abdalla Yace”Allah sarki, Uzair Da tajuddeen Sunci burin yin Aiki a companynsu, suna son Yin aiki tare da Ziyad Allah bai nufa ba” cikin karyayyiyar Murya Uncle abdallah ya ƙarasa maganar, jikin kowan nan su Yai sanyi
“Nima a bakin uzair na ta6a jin labarin Ziyad ɗin nan shahararran ɗan Jarida, “ Acewar Hajiya adama
Uncle ɗan Iya na murmushi yace”Allah sarki, ae muna mutunci da Iyayensu, lokacin da ace nasan suna da burin yin aiki da shi ai dana haɗasu, Yadda Taj da uzair suke da hazaƙa a 6angaren Jarida tabbas da suna atare ba ƙaramin Cigaba za’a samu a ƙasar nan ba, don shima Ziyad ɗin Akwai ƙwalwa Bashi da tsoro gaskiya tsirararta yake faɗin ta” murmushi kowannan su Ya saki.
“Yakamata ka gayyato mana shi agidan nan, tunda kowa nasan ganin shi, Ko da ya ke nasan zaiyi wuya ya iya samun lokacin zuwa sai dai mu muje inda Yake” Abie ne yai maganar
“In dai ziyad ne baku da matsala, mutunne mai sauƙin kai, zan Gayyace zuwa gidan nan”
Tun da suka fara magana sai Yanzu ummi tasa baki”kaga daga nan Idan Yazo sai mu bashi auran zahra....” tunkan ta ƙarasa magana zahra dake chatting da wayarta A sukwane ta ɗago Girarta a haɗe tana kallon fuskar mami.
Hakan da ta yi ba ƙaramin dariya ya basu ba, Uncle ɗan Iya yace”kin kawo shawara mai kyau, Ni kaina nayi tunanin hakan don yaron akwai farin Jinin ƴan mata ita kanta zahra nasan zata ƙyasa” Kifa kai zahra tayi saman cinyoyinta, takaicin Duniya ya isheta, ita da ta ke da burin mallakar Uban gayyar family ɗin su kuma suna yi mata zancen Ziyad.
“Akwai Kyauta ta musamman da zan ba Aneelerh, nasan Itama zata taimaka mana sosai” Hajiya adama ce ta yi maganar idonta Akan uncle abdallah.
“Na baro ta a mota, jiya na manta ban shigo da ita gidan ba, Bari naje na ɗauko” yai maganar yana yunƙurin miƙewa Sai ga Mahboob Kamar an wurgoshi Rai a6ace yake Tafiya Fuskar shi a haɗe babu mutunci.
“Ka koma ka zauna Ga mahboob nan, ka bashi key ɗin motar ya ɗauko maka” Karaf acikin kunnanshi Maganar ta sauka, Har ƙara sauri yake yi don yabar falon
Ɗaga murya Uncle ɗan Iya yai”Kai Mahboob zonan” Cak Ya tsaya da yin tafiyar fuskarshi A murtuke ya Juyo Ya nufi inda suke zazzaune saman sofa.
Zuƙunnawa Yai ƙasa Ya ɗago da fuska Yana kallon Abie ɗin nasu
Rai a6ace yace dashi”Mahboob ba ka ga munyi baƙi bane a gidan namu”?
Hannu yasa ya ɗan sosa ƙeyarshi Muryarshi ƙasa ƙasa Ya furta
“Bana Jin ɗaɗi jiya shiyasa ban samu damar zuwa ganin su ba,”
Wani kallo Da Ummi ke wurga mashi daga inda take zaune saman Sofa kamar zata kifa masa mari, Hakan yasa shi yin sauri kallon Uncle Abdallah Ya furta”sannunku da zuwa, ya gajiyar tafiya, ya kuma aka baro mutanan can”
fuskar uncle abdalla asake ya amsa mashi”lafiyalou Mahboob, ya school ko an kammala” fuskar shi ba yabo ba fallasa ya ce”diploma ce na kammala”
Ganin yanayin fuskarshi babu walwala Uncle abdalla yace “Ko dai har yanzu ba lafiyane? Naga kamar baka acikin natsuwarka”
Sai lokacin Ya ɗan sakin murmushin yaƙe “Bakomai, ai naji sauƙi” Iya abunda ya furta kenan, Baby Junaid ya tsareshi da ido, Dariya ce ƙumshe a cikin bakinshi don ya fahimci damuwar rashin zoban shi ce ta sanya shi shiga wannan halin, Cikin kunne yai ma Aneelerh raɗa”Mommy zoben yake nema, kalli idonshi ki gani sunyi jawur, Allah bani bashi mommy sai ya zubar da hawayensa”
Ƙiris ya rage Aneelerh ta saki dariya yayin da take sauraron muryar junaid, ita kanta ta lura da 6acin ran da ke akan fuskar Mahboob.
“zai baka Key ɗin mota, saƙo zaka ɗauko mashi” Fuska a ɗaure uncle ɗan Iya yai mashi maganar, tare da kallon uncle Abdalla
“Bashi key ɗin motar,” acewar ɗan Iya, ciro key ɗin uncle abdallah yayi kafin ya miƙa ma Mahboob, Ya sanya hannu biyu ya kar6a.
Yunƙurawa yai ya miƙe ya fuce daga ɗakin yana ƙunƙuni.
Kafin dawowar Mahboob Junaid Ya miƙe da sauri Ya nufi ɗakin Mommyn shi don Ya duba zoben da su ka 6oye.
Yana shiga ɗakin Ringing wayar Aneelerh Ya daki dodon kunnan shi, Da sauri ya nufi wayar dake Ajiye saman pillow Ya haye gadon ya janyo ta.
Jikinshi har kerma yake yi wurin yin Picking call ɗin ya kara wayar a kunnanshi.
Da ƙarfi Ya furta”Wanene”? Shiru ba”a tanka masa ba.
Hakan baisa ya fasa yin maganar shi ba
“Mommy bata nan tana a palour suna magana da su Abie, I’m the only one in the room.” still ba’a tanka mashi ba, Surutu Yaci gaba da Yi
“Angel ce ke kira”? Shiru ba amsa”Sister Angel, say something! It’s your brother, Baby Junaid. I miss you so much”
Da shagwa6a ya yi maganar, Sai lokacin Muryar mutumin da ya kira a wayar ta bayyana da sauti mai matuƙar Ratsa zuciya.
“Where is the owner of the phone?” ta6e baki Junaid yai”ai na faɗa maka tana