Author : Hameedah Category : Complete Novels
kamar girki take yi dan hancinshi ya fara jiyowa kamshin wainar kwai, ajiyar zuciya ya saki domin tunowa da yayi bai taba shan koda ruwa ba acikin part dinta ba,saboda shi kyankyami gareshi, jallabiyar jikinsa ya cire ya shiga wanka ya fito lokacin tabar cikin kitchen din, turaren _right man_ ya fesa yasa karamar jallabiya riga da wando ya koma falo nan ya tarar da al'amin hannunsa rikeda hadisi yana bitar karatun da ya dora masa,
"Al'amin yau ba za muyi karatu ba dare yayi kaje ka kwanta maza, sannan kar ka manta kayi addu'a kaji, yama addu'ar kwanciya bacci?"
"Abbu bismikallahumma amutu wa ahyana"
"Yawwa yarona maza tafi kayi bacci" littafinsa ya dauka ya fice yatafi wurin ummunsa yayinda shi kuma mal jabir ya zauna yafara cin abincin da ummu ta ajiye masa, bayan ya kammala ya kunna tashar huda tv ya fara kallo har _10_ tayi alokacinne ya mike ya nufi sashen goodness.
_*Ummi Aisha*_ππ»
[10/28, 9:28 PM] βͺ+234 810 100 9022β¬: *WANI HASKE*
_NA_
*_UMMI A'ISHA_*
_39_
~~~Sashen _goodness_ ya nufa, tun akan hanyarsa yake jiyo alamun karar tv wadda daga ji babu tambaya kallo take yi,
Ahankali ya kama handle din kofar falon ya bude ya shiga, ganinta yayi ta yiwa tv kuri da ido ko kiftawa ba tayi tana kallon wani Nigerian film _its my life_,agogon falon ya kalla karfe goma da yan mintuna,
"Goodness you have to go to sleep now" ya fada cikin sanyayyiyar muryarshi, arazane ta jiyo ta ganshi dan bata san ya shigo ba domin hankalinta gaba daya ya tattara ga kallon da take yi,
"Yes sir, ina son ne nagama kallon wannan film din yanzu zai kare" tafada tareda sakin ajiyar zuciya,
"Alright, sai da safe" ya fada gamida juyawa zai fita daga falon,
"Sir ina son gobe nafara zuwa church pls"
Dam ya danyi ba tareda ya jiyo ya bata amsa ba amma kuma bai fita ba, to shi yanzu zai hanata zuwa church dinne ko kuma zai kyaleta taje? "Dole babu yadda zakayi tunda itama addininta zata je tayi" zuciyarsa ta bashi amsa,
"Shikenan kije" ya fada a takaice tareda ficewa daga cikin falon ya nufi hanyar komawa nasa sashen, fuskarta ta maida kan tv taci gaba da kallon da take yi.
***
Washe gari da safe tun misalin karfe 7 na safe goodness ta dau wanka tasha wasu English wears riga pink colour da yar top dinta baka, tasha bakin jeans mai beza daga kasa, ta kawo hill ta dora bayan ta fente fuskarta da kwalliya, part dinta ta kulle ta fita mai gadi ya bude mata gate ta tari abin hawa ta tafi church a lokacin su mal jabir ko tashi daga bacci ba suyi ba,
Sai around 9 sannan ya tashi kasancewar weekend ne, tunda yaji shiru babu alamun tashin sautin kida yasan goodness bata gidan tayi sammakon zuwa church, wanka ya shiga yayi ya fito ya shirya ya fita falo lokacin ummu al'amin har ta tanadar masa abin karyawa, yana zama al'amin yana shigowa dan haka da gudu ya fada kansa yana dariya,
"Abbuna yau anty bata nan"
"Taje unguwa ne al'amin"
"Abbu muma za muje unguwar nida kai?"
"Eh za muje bari mu gama cin abinci"
Wani tsalle ya sake yi ya fada kan abbun nashi yana murna yayinda shi kuma mal jabir yake tunani acikin ranshi oh yanzu shi kuma haka Allah ya doro masa ana zuwa church a gidansa.
Wuni su goodness suka yi acikin church, kuma gashi ta samu fuska sosai awurin ma dan tayi murna da ganinta ba kadan ba gashi duk da ba wata kulawa take samu daga wurin mijin nata ba duk da haka tayi kyau kumatunta sun dan kara cika, basu bar church din ba sai wurin karge uku na yamma, ma tabi zuwa gidanta.
Suna tafe suna yan hirarrakinsu ma tana ta shan cikinta kan zamantakewar ta da mijin nata, wani ta fada wani kuma tayi shiru da haka har suka karasa cikin gidan,
Suna shiga tayi ido hudu da mahaifinta acikin falo yana karanta jarida, "Allah sarki my papa" tafada acikin zuciyarta,
"Ah papa goodness you dey here?" Ma ta fada tana ajiyewa Bible dinta,
Da sauri goodness taje ta durkusa ta gaida babanta wanda rabonta dashi tun bikinta,
"I dey here mama goodness" ya bawa ma amsa wacce ta shiga kitchen ta fara kokarin hado musu abinci, teba miyar kubewa ta zubo ta kawowa goodness bayan itama ta zubo nata,
"Ehem goodness ina son za muje okene, za muje nida ke zaki gaisa da family wanda baki sansu ba suma basu sanki ba"
Cikin sauri mahaifin goodness ya kalleta,
"Mama goodness why are you always .....?"
Da sauri ta katse shi "papa goodness always what...? Kana nufin bazan kaita wurin dangina ba saboda kai ka fita acikin addininmu tun jimawa?"
"Mama its ok,kiyi hakuri papa baice komai ba ai"
Mikewa baban nata yayi ya fita shi har yanzu ya kasa gane kan Maman goodness tun lokacin da ya musulunta ta saka masa karan tsana adole take zaune dashi,
Yana fita ma ta kalli goodness "you made a big mistake my daughter, kinyi kuskure da kika yarda kika auri hausa man saboda su komai sai suce babu kyau, sannan sai ki samu 1 man yana auren 4 wives, gashi sun iya divorce kamar me"
Jijjiga kai goodness tayi tana ci gaba da cin tebar da take yi "hakane ma amma shi wannan man din da nake aure bashida wani problem"
"To naji amma kin san dai yanzu kullum zaki rinka zuwa church ko?"
"Eh ma shiyasa nake sauri na koma gida da wuri saboda gobe ma ina son zuwa da yamma"
"Yawwa my daughter duk yadda zaiyi dake kar ki yarda kibar addininki"
Nan ma taci gaba da yi mata hudubar tsiya har ta gama ta yimata sallama ta tafi gidanta, lokacin da ta shiga gidan Ummu al'amin tayi bakuwa ta rakota compound din gidan suna sallama sai gata ta shigo,
Daga nesa suka gaisa da ummu ta wuce part dinta, nan bakuwar ta kalli ummu "wannan kuma wacece?"
"Itace amaryar abu al'amin din ai"
Rike haba tayi "oh lallai yanzu duk yanmatan garin nan hausa fulani masu addini ace malam ya tsallakesu yaje ya debo ahlul kitabi? Allah ya kyauta to"
"Amin dai" Ummu al'amin tafada tareda yi mata sallama ta koma sashenta.
Goodness kam tana shiga daki ta sauya kayan jikinta zuwa wata yar karamar riga mai karamin hannu da wando tied red colour iya gwiwarta, aikin gyara sashen nata tafara domin yau kasancewar bata zauna agidan ba babu abinda tayi ta fita, tana ta ffaman aikin tana yan wake wakenta al'amin ya shigo wanda dawowarsu kenan shida abbunsa daga unguwa,
"My boy ina abbunka?"
"Anty yana falonsa"
"Oya maza kaje kace masa nace i love you"
Dagudu al'amin ya fita yana nanata kalmar a bakinsa gudun kada ya manta yana shiga falon abbun nashi ya same shi zaune shida ummun sa da karfi yace "abbu anty ta aiko ni wai i love you".
_*Ummi Shatu*_ππ»
[10/28, 9:29 PM] βͺ+234 810 100 9022β¬: [9/1, 7:05 PM] Ummi A'ishaππ»:
*WANI HASKE*
_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_
_40-41_
~~~Shi kam ma abun dariya ya bashi, dan murmushi yayi gamida shafa dan kyakkyawan gemunsa, ba tareda yace komai ba, kallonsa ummu tayi ta na murmushi,
"Ya an aiko maka da sako amma ba kace komai ba?"
Kallonta yayi da sexy eyes dinshi ya sakar mata lallausan murmushi,
"To ai naji ba shikenan ba"
Murmushi tayi ta mayar da idonta kan al'amin Wanda yake tsaye yana kallon tv, shi kuma mal jabir acikin ransa yana mamakin wannan yarinyar goodness shifa daidai da rana daya bai taba jin yana sonta ba kai asalima bazai iya cewa ga yanayin halittarta ba amma dole yaci gaba da zama da ita babu yadda ya iya.
Ita kam goodness aikinta take yi hankalinta a kwance har ta gama gyara ko ina na bangaren ta, kitchen ta shiga duk da ba wani yunwa take jiba sosai amma tana da bukatar tasha ruwan lipton, lokacin da ta shiga kitchen shikuma ya fito daga bathroom din dakinsa cumb ya dauka ya je gaban mirror ya fara gyara sumar kansa da gemunsa, daga kan da zaiyi ya hangota acikin kitchen tana kaiwa da komowa, kasa ci gaba da abinda yake yi yayi yaci gaba da kallonta har ta fice daga cikin kitchen din shi dai bazai iya fassara yanayin da yake jinta acikin ransa ba na so ko k'i, turaren right man ya fesa ya saka yar hula ya fito domin tafiya masallaci, part din ummu ya shiga ya kama hannun al'amin suka fita.
Karfe 9 da yan mintuna ya dawo gidan shida al'amin, part din ummu ya kaishi sannan ya fito ya shiga part din goodness wacce a lokacin take bararraje akan center carpet tana shan iska tana kallon wani Nigerian film, ahankali ya bude kofar ya shiga cikin falon, motsin da taji ya sata saurin juyowa, tsayawa yayi daga bayanta yayinda ta tashi zaune amma ta kasa juyawa ta kalleshi saboda nauyinsa da taji tana ji yanzu,
"Naji sakon ki awurin al'amin" ya fada da sanyayyiyar muryarsa, shiru tayi babu amsa,
"Ko ba kiji abinda nafada ba? Nace naji sakonki awurin al'amin"
Nanma shirun ta sakeyi sannan bata iya juyawa ta kalleshi ba,
"Sai da safe to" ya fada tareda juyawa ya fita, bayansa tabi da kallo tana murmushi ashe dai al'amin ya fada masa sakon, "hmm kana burgeni sosai, i like your style" tafada tana murmushi wanda ji take yi tamkar tabishi ta rungumeshi dan so.
Washe gari bata tashi da wuri ba saboda dare ta raba tana kallo sai wurin 2 ta kwanta, shiyasa ta makara, tana tsaka da bacci kamar a mafarki ta jiyo cool voice dinshi yana kiranta zumbur ta tashi tana mutsuttsuke idanuwanta da bayan hannunta tsabar gigita ta manta ma da kayan baccine ajikinta, karo suka yi a daidai kofar shigowa dakin nata shi ya sako kai da nufin shigowa ita kuma tasa kai da niyyar fita falo tana daga labule da niyyar fita taji ta ci karo dashi take ta jita acikin kirjinsa, wayar hannunshi ce ta silmiye ta fadi hakan yasata saurin durkusa dan dauko masa cikin rashin sa'a shima hakan yayi niyya take suka sake yin wani karon,
Mikewa yayi yayinda itama ta dago hannunta rike da wayar tashi, idonta a kasa ta mika masa wayar tana cewa
_"am sorry sir"_
Jikinta yabi da kallo wanda ke saye cikin wata hadaddiyar rigar barci armless, kalarta yellow marar nauyi tsawonta bazai wuce iya gwiwa ba da dan karamin wandonta iya cinya, kallonsa ya maida kan fuskarta har yanzu idonta kasa yake kallo takasa kallonsa, jin shiru bai amshi wayar ba yasata dagowa caraf suka hada ido dashi, manyan idanuwan nan nashi cikin nata, ahankali ta sauke idonta tabi kafarsa da kallo, takalminsa farine half cover, kamar kullum farin lallausan yadine ajikinsa da jar hula, kamshin turarensa na _explore_ da _right man_ sun taru sun bada wani daddadan kamshi na musamman, fuskar nan tashi tamkar ya shafa farar _powder_,
Hannunsa ya mika ya karbi wayar,"morning sir" tafada a hankali
"Morning, how was your night?" Ya fada ahankali, shiru tayi bata amsa ba, ganin haka ya sashi juyawa zai fita,
"Excuse me sir" cak ya tsaya ba tareda ya juyo ba,
"Am hearing you" yafada yana kallon agogon azurfar dake daure a hannunsa,
"Sir zanje saloon ne anjima sannan ina son zuwa church in the evening"
"You can go" yafada tareda ciro 1000 ya miko mata ba tareda ya jiyo ba, da sauri ta karasa ta mika nata hannun da niyyar karbar kudin nan ta hado da yan yatsunsa biyu ba tareda ta saniba, wani shock taji cikin sauri ta matsa baya, bai sake cewa uffan ba ya fice ya barta tsaye tana kallonsa, gaskiya ita dai yana mutukar burgeta gashi yauma ya tafi ya bar mata sanyayayyen kamshinsa a cikin hancinta, juyawa tayi ta fada kan gado taci gaba da tunaninsa acikin ranta.
Wurin misalin karfe 12 tabar gida ta tafi shagon wata yar church dinsu mai suna blessing dama tun asali awurinta take yin kitso da saloon, gyaran gashi aka yi mata sannan aka jona mata attach nan ya zubo har gadon bayanta, ba atsaya a iya nan ba sai da aka yi mata gyaran farce gamida fenteshi sosai, sai wurin 3 suka gama ta dauki jakarta ta nufi church.
Karfe shida daidai ta taso daga church din ta nufo gidanta, lokacin da ta karaso an kusa shiga masallaci, sauka tayi daga kan machine din da ta hawo ta bude yar karamar jakarta ta mikawa dan acabar kudinsa ta juya ta nufi hanyar shiga gida, a kofar masallaci taga mutane wasu zazzaune wasu kuma na yin alwala, haka ta wucesu zata shiga cikin gidan, tana zuwa bakin gate taga wasu mutane su biyu da mal jabir yana tsaye yana yi musu bayanin da bazata iya gane ko na menene ba, kallo mutanen suka bita dashi har shi kansa jabir din sai da ya rakata da ido, tasha riga da wando ga gashi har gadon bayanta ko dan kwali babu akanta hannunta daya rike da Bible dayan kuma rikeda yar jakarta, tana wucewa daya daga cikin wadanda ke tsaye kusa dashi yace
"Malam wannan fa? Me zataje tayi agidanka kodai tayi batan kai ne?"
Shiru yayi tsabar takaice bai iya bada amsaba saboda yasan ko bai fada ba idan sun bar wurinshi dole ne suyi zancen amma yau yayi damarar takawa goodness burki akan wannan sakarcin nata, shi bazai yarda da wannan banzar dabi'ar ba.
Bayan ta shiga gidan part dinta ta bude ta shiga, ko zama ba tayi ba ta shiga wanka ta fito, three quarter da yar body hug tasa ta shiga kitchen ta dafa indomie ta debota ta kawo falo ta kunna tv taci ta koshi, kwanon ta ture ta mayar da hankalinta kan film din da take kallo a tashar _African magic_ mai suna _the present time_ hankalinta duk ya tattara akan wannan film din domin ganin tirka tirkar dake ciki, bude kofar da akayi ya sata bin kofar da kallo dan ganin waye zai shigo,
Shine ya shigo amma daga gani yana cikin fushi "goodness as from to day kar ki kuskura na sake ganinki da riga da wando a waje, are you crazy? Who told you wadannan kayan da kike sakawa na mutumcine? Kina son ki bata min sunane a garinnan ko me? Daga yau sai yau kar ki bari naganki da irin kayan dazu awaje, sannan its compulsory ki rinka daura head tied, wannan ai zancen banza ne kullum ki ringa fita gashinki awaje jikinki awaje, i can't tolerate this"
Tunda ya fara fadan bakinsa kawai take kallo wanda yayi tsananin bata sha'awa, "am sorry sir" tafada cikin kalar tausayi,
"Hold your sorry, sorry for yourself"
Juyawa yayi ya fita bai sake cewa komai ba, ajiyar zuciya ta saki tare da rike kanta "hmmm to plan for you how to love me is my headache now, problems neva finish in this house oh oh" tafada tana kallon agogon falon wanda ya nuna karfe 10 saura minti 5,tv din ta kashe ta tashi ta shiga dakinta ta kwanta yau duk yanda taso ta ga karshen film dinnan amma yanzu taji ya fita daga ranta gaba daya, juyi tayi tareda jan dan karamin tsaki,juyi tayi ta mika hannunta kan bedside drawer dinta ta dauki Bible dinta tafara dubawa, ganin bata gane komai yasata ajiyeshi ta tashi tafita taje ta rurrufe ko ina na part dinta saboda bata son gobe jabir ya shigo dan tasan haduwar ba zai yi mata dadi ba, dawowa tayi ta kwanta amma kuma ta kasa baccin akalla sai da takai karfe 1 kafin bacci yayi nasarar daukarta. Bata iya tashi ba sai karfe 11 nasafe lokacin kam tasan abu al'amin ya dade a office, sabgoginta ta shiga yi amma yau bata da niyyar zuwa church, tana falonta tana gugar kayan sawarta al'amin ya shigo hannunsa rikeda chocolate,
"My dear son i miss you so much, where did you hide?"
"Anty ummu na tace nazo na gaisheki" yafada yana kokarin bare chocolate din hannunsa,
"Oh al'amin clever boy, abbuna, ummuna, every one na your own ba?"
TV din da take kallo ya kalla, "anty zan kalla carton"
"Oya carry that remote and change the channel, al'amin ina abbunka?"
"Ya tafi office baije dani ba"
"Ayya sorry my dear, na kawo maka wani chocolate din ta kara akan naka?"
Girgiza kai yayi "abbuna ya siyo min jiya da yawa da yawa yace in tasha nawane ni daya"
Murmushi tayi tana son hirar al'amin domin yaron akwai kwakwalwar daukar abu gashi komansa irin na abbun shi ne shiyasa yaron ya shiga ranta, biye masa tayi yayita yi mata labari har tsawon wani lokaci kafin ya fice ya koma wurin ummunshi.
Zama tayi shiru bayan fitar al'amin taci gaba da gugar ta har yamma saida ta goge kayanta tsaf kafin ta tashi ta dora girki taci tayi wanka ta fito bayan ta shirya cikin wasu riga da skirt blue masu adon stones ajiki.
Falo ta dawo ta rufe kofar falon sannan ta nutse cikin kujera ta fara kallon channel din _music plus_ tashar zallar wakoki kawai ake nunawa, tana nan kwance har ta jiyo dirin motar jabir alamun ya dawo daga office, bata tashi ba taci gaba da kallonta har duhu yayi, tunani ta fara yi acikin ranta lallai ya kamata taje ta sake bashi hakuri tunda itace tayi masa laifi kuma gaskiya ya fada mata wadannan kayan da take sawa na iya janyo zubewar mutumcinsa a idon jama'a, da wannan shawarar ta zuciyarta ta aminta cewar anjima taje ta bashi hakuri.
Misalin karfe 9:30 ta nufi part dinsa wannan shine karo na farko da zataje sashensa domin bata taba shiga kowanne sashe agidan ba baya ga nata, kofar falon ta murda ta shiga babban falo ne wanda yasha kayan alatu amma gaba dashi ma wani falon ne dan madaidaici, ahankali ta tasamma falon sai dai tana saka kai ta hangoshi rungume da matarsa ummu al'amin suna soyewa nanfa gabanta ya fara dukan uku uku zuciyarta ta shiga harbawa da karfi da karfi, dan karamin bakinsa dake sakata cikin wani yanayi ta hango yana cusawa cikin na matarshi sai juyi yake da ita tamkar wata yar baby kasancewar a tsaye suke, wasu zafafan hawaye ne suka shiga sintiri akan kumatunta wanda ita kanta bata san ko na menene ba, kamar wanda akacewa bude idonka yana