Author : Hameedah Category : Complete Novels
amma bata ganshi ba, dauka yayi ya dora mata akan hannunta, karb'a tayi ta soma gogashi akan fuskarta,
"Washhh this pepe want to blinded my eyes"
Juyawa yayi ya fita daga bathroom din har yaje tsakiyar dakinta ya jiyota tana fitowa,
"Sir bai fita ba wlh it dey inside my eyes especially this one" ta nuna idonta na dama,
"Sir pls hure min, yana ciki"
Yana nan tsaye cak har ta karaso gabansa, kanta ya d'ago ya bude idonta daya yasa bakinsa ya fara hure mata, tabbas dagaske take ga kwayar cikin attaruhu nan guda daya acikin idonta yana gani, nan yaci gaba da huhhure mata amma fur kwayar attaruhun nan taki fita ita kuma goodness ji take kamar za tayi hauka dan zafin da take mata acikin idonta,
Hannunta yaja ya zaunar da ita abakin gado yaci gaba da hure mata idon, gaba daya idonta yayi ja bau kamar me yin afolo,
Dakyar kwayar nan ta fice ta can gefen idonta, dan yatsansa yasa ya cirota murza idon taci gaba dayi domin wani radadi yake mata,
"Kin ganta" ya mika mata yatsansa dan ta gani,
"Abbu na ashe kaima kana son anty na ko?"
Suka jiyo maganar al'amin daga bakin kofa, da gudu ya karaso ciki, "sannu anty, abbu me kayi mata take kuka?"
"Al'amin babu abinda nayi mata yajine ya shiga idonta shine na cire mata"
"Ya salam, sannu anty, taso muje falo ki kalli cartoon" hannunta yaja ta tashi tabishi, murmushi mal jabir yayi yabi bayansu, kyalesu yayi ya tafi office saboda yaga hankalinsu ya tafi kan wasan yaran da suke kallo a tashar mbc 3,sai da taji saukin idon nata sannan taje ta karasa girkin amma har alokacin tana jin zafin yajin ga wani irin ja da idon yayi tasan dama dole ne zai zame mata eye ache.
Misalin karfe 5:30 mal jabir ya dawo gida, sashenta ya fara zuwa amma basa ciki, nan yayi tunanin to ko suna cikin falonsa, can dinma da yaje basa ciki, mamaki ya yi to ko ina yaran nan suka tafi?
Agurguje ya shiga yayi wanka ya fito sai alokacin yajiyo hayaniyar su abayan part dinsa,ta window ya lekasu, goodness sanye cikin green din t shirt da blue din jeans idonta daure da bakin k'yalle tana neman al'amin, wanda ke tsaye a bayanta sai faman ja mata riga yake suna dariya amma ta kasa kamashi,
Murmushi yayi na jin dadi domin al'amin ya sake sosai da goodness saboda yadda ta sakar masa fuska takoma yarinya karama kamar age mate dinshi yasan ba dan goodness ba da tuni al'amin ya addabeshi ya kaishi wurin ummunshi amma yanzu ko zancenta baya yi iyakaci su gaisa a waya,
Kaya ta taka ta saki yar kara "oh God"
"Anty ba oh God ake cewa ba, annabi ya kasance idan wani abun da yake k'i ya faru agareshi sai yace Alhamdulillahi ala kulli halin, idan kuma na farin ciki ya zo masa sai yace Alhamdulillahil lazi bi ni'imatihi tatimmus salihatu, anty kema kiyi koyi da annabi sai ki samu lada"
"Thank you al'amin zanyi nima"
Sakin labulen window din yayi yakoma cikin falo yaje ya zauna akan dining ya zuba cous cous din data dafa ya dan ci, bayan ya gamane ya tashi ya zagaya baya inda su goodness ke wasa ita da al'amin,
Lokacin da ya karasa wurin yanzu al'amin dinne fuskarshi adaure da kyallen ita kuma goodness sai dariya take yi masa itama tana rama abinda yayi mata dazu,
"Welcome sir" tafada tana jan rigar al'amin,
"Abbu na kadawo? Har kai zan kama yanzu ba iya anty kadai zan kama ba"
"Thank you, al'amin nikuma daga zuwana za ace harda ni?"
Dagudu al'amin ya taho,cikin sauri goodness ta matsa tabar wurin,
"Abbu in dai na kamaka to kai za adaurawa"
Da sauri ya matsa ya koma jikin karfen tanki ya tsaya, ita kuwa goodness tana bayan wata kujerar karfe dake ajiye awurin, bayan karfen tankin ya nufa ganin haka yasa goodness fara yiwa malam jabir dariya ta hanyar toshe bakinta da hannunta,
Fitowa yayi da niyyar sauya waje, caraf al'amin ya rikeshi yana cewa "yes na kama wani tsakanin anty ko abbu"
Cire kyallen yayi yana ganin abbunsa ya fara dariya,
"Abbu yanzu kai za adaurawa"
"Ya na iya al'amin tunda na kawo kaina, nidai kawai tsautsayine ya fito dani har nazo wurinku"
Karbar kyallen yayi ya daure fuskarsa ya fara lalubensu, da gudu al'amin ya arce yayi bayan dakin abbunshi ya tsaya, ita kuma goodness ta labe agefen karfen tanki,
Lalube yake tayi amma baiji ko daya daga cikinsu ba kamar basa wurin, al'amin ne ya sadado yazo yaja rigarshi ta baya ya kwalkwale da gudu, da aka sake jimawa kadan ya sake dawowa ahankali yace
"Abbu ga anty can agefen karfen tanki kaje ka kamata saboda ni ba iya kamani zaka yiba duk nifiku gudu"
Yana gama fadin haka yaja gefen rigarshi ya zura da gudu,
Shawarar al'amin yabi dan yasan bazai iya kamashi ba kam, gefen tankin yabi yana tafiya ahankali ganin haka yasa al'amin daukewa goodness hankali daga can inda yake yafara yi mata rada wacce bazata iya jiyo abinda yake fada ba.
Hankalinta ta mayar kansa tana tambayarshi da hannu wai me nene? Dariyar mugunta al'amin yayi mata saboda dama yayi hakane dan abbunshi ya kamata,
Juyowar da zatayi taji jabir ya taka kafarta daya, daurewa tayi batare da tayi motsi ba har zai juyawa ya wuce sai yaji alamun fitar numfashinta, kansa ya dan matsar nan ya tabbatar da cewa itace, cikin sauri ya fisgota da karfi, nan ta fada jikinsa wanda saura k'iris su zube su kai k'asa.
_*Ummi Aisha*_ππ»
[10/28, 9:30 PM] βͺ+234 810 100 9022β¬: [9/13, 5:16 PM] Ummi A'ishaππ»: *WANI HASKE*
_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_
_Assalamu Alaikum masoya masu karanta wannan littafin na wani haske, ina mai baku hakuri na dan jina shiru da kuka yi kwani biyu da suka wuce hakan ya farune sakamakon abubuwa da suka sha kaina amma insha Allahu yanzu komai ya daidaita zaku rinka jina akoda yaushe har labarin ya kare, ina yi muku barka da sallah da fatan Allah ya maimaita mana amin._
_54-56_
~~~Cikin sauri ya fisgota da karfi, nan ta fada jikinsa wanda saura k'iris su zube su kai kasa,
Fuskarshi na daure da bakin kyallen ya fara yi mata magana a hankali cikin rad'a rad'a,
"Pls remove this thing from my face"
Daga kanta tayi ta kalleshi ya matseta sosai Wanda har tana iya jiyo bugun da zuciyarshi keyi ahankali,
Ahankali take jin saukar numfashinsa akan goshinta, dan motsi tayi ta fara kokarin kwace hannuwanta dake rike a hannunsa,
"To ka sakar min hannuna mana"
"Idan nasake ki guduwa zaki yi i know"
Sake take kafarta yayi, "ohhh..!"
Tafad'a ahankali, "ki kunce min daurin fuskata sai na sakeki"
"Sir you have match your leg on the top of mine"
Tafada tana sake k'ankameshi,
"Oh sorry" sausauta rik'on da yayi mata yayi ya dan sake hannunta kadan amma har lokacin yana rikeda su, ahaka ta kunce masa bakin kyallen dake fuskarsa,
Sakinta yayi, dagudu al'amin ya garzayo yazo ya dale abbunshi,
"Abbu nayiwa anty wayo nasa an kamata"
"I already know you are the one who plan this al'amin,but i will take revenge next time" ta fada yayinda take daura dan kwalinta,
"Sorry anty i know what i will do so that you can't take avenge"
Tsaye yayi yana kallonsu, sauke idanuwansa yayi akan al'amin yace
"Al'amin muje kayi alwala lokacin salla ya kusa"
Hannun goodness al'amin ya kama yana dariya "anty let's go"
Binsu a baya jabir yayi suna tafiya al'amin yana lilo ajikin goodness har suka je sashenta ya shiga ya dauro alwala ya fito wurin abbunshi suka tafi masallaci.
Yau ta Kama ranar juma'a, karfe 1 mal jabir ya taso daga office, lokacin da yazo gidan goodness ta yiwa al'amin wankan juma'a tana shiryashi,
"Anty fararen kayana zaki samun saboda ummu na duk ranar juma'a fararen kaya take samun kuma kinga ai abbuna ma duk kayansa farare ne saboda annabi yace mu yawaita dinka kaya farare"
"Tom bari nasaka maka wannan farar shaddar"
"Yawwa anty dama irinta abbuna ce, shima yana da irinta"
Yana tsaye a bakin kofa yana kallonsu har ta sakawa al'amin kayan,ajikinta taji alamun ana kallonta hakan ya sata saurin juyawa hada ido tayi dashi yasha farar shadda sabuwa kar, ya gyara sajensa da gemunsa fes sai zuba kamshin turare mai sanyi yake,
"Hmmm you are always cool, even your perform is like the way your are" tafada ahankali,
"Anty me kike fada? Da abbuna kike?" Al'amin ya fada yana mika mata hularshi dan ta saka masa,
"No bada abbunka nake ba da kaina nake, have you get me?"
"Na'am anty" hularsa ta saka masa ta dauki turare gaban mirror dinta ta feffesa masa,
"Anty baki bamu carpet ba"
"Zo nan da akwai abun salla acikin mota" ya fada yana gyara zaman agogon hannunshi, hannunsa yaja suka fita nan ta rakasu da ido, al'amin ba karamin kyau yayi ba shida abbunshi tamkar ta sacesu ta gudu dan kyau.
Da yamma tana corridor dinta tana wanke inner wears dinta al'amin yazo yana tsalle "anty nima zanyi wankin"
"No bari kar ka bata kayanka"
"Nidai anty zanyi" ganin zai dameta yasata tura masa bocket daya ya fara jagwalgawalawa,
Mal jabir ne ya shigo jin hayaniyarsu acikin corridor yasa shi binsu can amma falon k'ure yake da wakar akon cikin wakarsa ta _black girl_,
Yana zuwa corridor din ya kallesu "me kuke yine? Naji banji motsinku ba gashi kuma ina son fita"
"Abbu kayan anty muke wankewa kaga irinsu" bra daya da pant daya ya kwaso da gudu da niyyar kai masa dan ya gani, da sauri goodness ta rikoshi,
"Hy give me my kaya" karbewa tayi ta mayar cikin bokitin, wata uwar kunya taji ta rufeta yau kuma da wanne ido zata kalli abbunshi yaga bra da pant dinta alhalin ita kuma tanada kunyar wadannan abubuwan shiyasa ko a toilet bata shanyasu gudun kar yagani ko shi ko al'amin din,
"Bari naje wurin malam" yafada yana kallonta ta baya,
"Abbuna zan bika ko? Muje wurin malam"
"Adawo lafiya, agaida shi" tafada ba tareda ta juya ba, tana ji al'amin ya kwashi takalmansa ya bishi suka tafi, girgiza kai tayi yaro dai yaro ne.
Ranar Saturday da safe bayan ta shirya breakfast ta yiwa al'amin wanka, kitchen ta shiga ta dan gyaggyara shi saboda ta dan kwana biyu bata yi masa gyara na tsanaki ba, digirgire tayi ta bude drewar din sama tana zuba dinner set, cikin tsautsayi tana dora wani kofi ashe bai zauna ba, dawowa kofin yayi ya fadi akan babban dan yatsanta na kafa taratsatsa kaje ji ya fashe akan yatsan nata, take ya yankata kamar ansaka wuka an yanka gun kun san dinner set da uban nauyi,
Wata kara tasaka da karfi, da gudu al'amin yazo daga falo inda yake zaune yana kallon cartoon a mbc 3,
"Anty" ya fada tareda zaro ido, ganin jini yana malala a k'afarta ya sashi fashewa da kuka tareda juyawa da gudu yayi hanyar sashen abbunshi, yana zaune yana karanta jaridar _weekly trust_ al'amin ya shigo da gudu yana kuka yazo ya fara girgizashi ya rike hannunshi,
"Abbu jini da yawa a kafar anty... Abbu zo muje ka gani"
Ajiye jaridar yayi ya saka silifas dinshi yabi bayan al'amin wanda keta faman kuka, tsoro da mamakine suka kamashi a lokaci guda, to ko menene ya faru? Tambayar da yaketa nanatawa kenan acikin zuciyarshi,
Suna shiga ya ganta ta jawo kafar tana zaune akan kujera amma jini duk ya b'abbata wurin gashi tun daga kitchen din jinin yake zuba,
"What's happening? Goodness what's happen?" Ya tambayeta gamida bin jinin da kallo, kitchen ya leka anan ya hango kofin da ya fashe ga uban jini awurin,
Dawowa yayi inda take, yana kallon fuskarta yasan dauriya kawai take amma tana jin jiki saboda gaba daya naman wurin gashi nan awaje yana gani kai kadan ma ya rage dan yatsan ya rabe biyu,
"Am coming" ya fada ya juya ya fita, sashensa yaje ya dauko hydrogen acikin kwalba da farar audiga, har ya dawo al'amin yana kuka,
Hydrogen din ya dan tsiyayo acikin murfin kwalbar ya dauki audiga ya zuba akan dan yatsan nata, wani uban tsalle goodness ta daka ta sauko kasa ta kankame shi sosai kamar zata koma cikin cikinsa,
"Sir pls stop it, pls sir wlh da zafi" hawaye ta fara yi tana rirrike hannunsa tana kokarin janye kafarta,
Kallonta yayi nan yaji tausayinta tana sanye da rigar bacci _maroon colour_ mai siririn hannu da dan buje din wandon rigar iya cinyarta, kanta sanye da hula baka,
"Sorry kadan zan saka miki saboda jinin ya tsaya kinga har yanzu jinine yake zuba ko kina son jinin jikinki ya kare gaba daya?"
"No sir but pls don't put it again"
Hannunsa ta sake kankamewa, tana kuka, ga al'amin shima agefe yana nasa kukan, rikeshi tayi gam taki sakinsa har shi kansa sai da yayi mamakin karfinta ita kuma ganin haka ya sata mamakinsa har aranta tana cewa "ashe ma bashida karfi nafishi, he's not strong see him like a woman"
Bata karasa zancen zucin da take yi ba taji ya zame rikon da tayi masa yasa hannunsa daya ya rike hannayenta duka, auduga ya dauka ya sake zuba hydrogen ajiki zai saka mata,
Wani kuka ta saka "ohhh...! Sir i beg u pls don't put it, pls sir, pls, pls"
Kankameshi tayi ta cukwikwiyeshi tana kuka hawaye nabin kumatunta, "abbu ka kyaleta kar ka sake saka mata dan Allah" ya jiyo muryar al'amin yana rokonshi,
Biris yayi dasu duk da yasan akwai zafi amma haka ya danneta ya sake saka mata,
Shure shure ta fara har tana yaye rigar barcin dake jikinta ba tare da ta sani ba, birgima taci gaba da yi tana kuka, kallonta yayi duk ta kwaye rigarta takaita kirjinta, gaba daya cikinta yana waje dan har yana iya hango ash colour din bra din dake jikinta,
"Tashi muje chemist ayi miki dressing din wurin"
Jijjiga kai tayi tana kuka "no sir abarshi haka zai warke"
"Ba komai zasu yi miki ba kawai dressing ne tunda na rigada na wanke miki wurin"
Tashi tayi ta dingisa ta shiga dakinta yanzu jinin ya tsaya ya daina zuba, shi kam al'amin yana zaune gefe ya hada kai da gwiwa yanata kuka, gabanshi yaje ya kamo hannunsa,
"Al'amin daina kuka kaji, kaga antyn ma ai ta daina alamun ta warke"
"Abbu yau babu wanda za muyi wasa tare tunda anty bata da lafiya"
"Waye ya fada maka? Za kuyi wasa mana, ai ta warke"
Tashi yayi yana share hawayen fuskarshi, dai dai lokacin ta fito sanye da doguwar rigar da ya kawo mata tsaraba lokacin da ya dawo daga madina.
Rigar ba karamin kyau tayi mata ba gashi tayi rolling wanda indai ba saninta kayi ba babu abinda zai hana ka dauka bahaushiya ce ita,
Dagudu al'amin yaje ya kama hannunta "sannu anty kin warke? Ya daina yi miki ciwo? Yanzu babu jini ko?"
"Wannan antyn naka al'amin ai Raguwa ce tunda tana yiwa hydrogen kuka" ya fada da niyyar zolayarta,
Kallonsa tayi yanda yayi maganar yaso bata dariya amma sai ta dake bata yi ba,
"Muje ko, ko har yanzu baki daina jin tsoron hydrogen din bane?"
Murmushi tayi ita gaba daya yau abbun al'amin mamaki yake bata yanda ya sake yake janta da wasa, ashe dama haka yake? Ya iya jan magana ga iya soyayya kamar wanda ya zauna a class aka koya masa,sai dai ita tanada masaniyar baya sonta kawai yana karanta matane saboda danshi al'amin sannan yana zaune da ita ne a bisa k'addara wacce masu iya magana kance ta riga fata,
Hannun al'amin ta kama suka fita yana biye dasu a baya har tsakar gida, mal idi ya kira ya karbi key din mota yace zaije chemist din baya ya dawo,
Da kanshi yayi driving, goodness na zaune agaba al'amin na kan cinyarta, sautin kira'ar karatun al'qur'ani tana tashi sama sama cikin muryar sheikh Ahmad Sulaiman kano inda yake karanta suratul taubah,
Bayan layinsu ya zagaya sai gasu a wani chemist (Al haq medicine & cosmetics store),dan satar kallon fuskarshi tayi yayi bala'in yi mata kyau.
_*Ummi Shatu*_ππ»
[10/28, 9:30 PM] βͺ+234 810 100 9022β¬: [9/9, 9:17 PM] Ummi A'ishaππ»:
*WANI HASKE*
_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_
_Sak'on gaisuwa da godiya ga"yan k'ungiyar fik'ira writers group 1and 2,bisa jinjinar da kuka yimin akan wannan littafi da nake rubutawa na wani haske, hak'ika nayi mutuk'ar farin ciki ganin akwai littattafai bila adadin amma acikinsu kuka zab'i nawa k'waya daya kuka yabeshi tare da yimin jinjina, ummu abdul naga sak'onki kuma nayi murna da ganinsa Allah yabar zumunci, ummi A'isha tana sonku._
_57-58_
~~~Zuba masa ido tayi bata ko k'iftawa tana kallonsa yana kokarin zare key din motar, "muje ko" ya fada ahankali, dan mitsil din bakinsa ta kalla yanda yake motsawa da k'yar idan yana yin magana,
Al'amin ta sauke ta fito tabi bayanshi har zuwa cikin chemist din,
Suna shiga suka samu wani nurse yana dan rubuce rubuce nan jabir yayi masa bayanin ciwon da goodness taji, tashi nurse din yayi yazo inda take zaune ya kalli d'an yatsan nata wanda har ya kumbure yayi suntum,
Kayan dressing ya d'ebo yazo inda take zaune ai tana had'a ido da hydrogen ta mik'e tsaye,
"Any problem?", jabir ya tambayeta,
"Sir hydrogen, pls kar asa min shi" ta fada kamar wacce zata yi kuka,
Nurse din ya fad'awa cewar ya saka mata hydrogen agida yanzu dressing kawai za ayi,
Take aka d'an goggoge mata d'an yatsan nata aka yi mata dressing suka fito, cikin motar suka koma ta dora al'amin akan cinyarta, shigowa ciki yayi yana kallonsu ita da al'amin din,
"Abbu kaima kana tsoron hydrogen ko kamar anty?"
D'an k'ayataccen murmushi yayi wanda ya k'awata fuskarshi sannan ya kalli goodness ta gefen ido,
"Ga mai yiwa hydrogen kuka nan antyn ka"
Ya bawa al'amin amsa, kallonshi tayi gaba d'aya ya mayar da hankalinsa akan driving din da yake yi, bata yi magana ba sai shida al'amin ne keta hirarsu har suka koma gida,suna shiga tafito hannunta rike da na al'amin suka shiga part dinta, doguwar rigar jikinta kawai ta cire ta dawo falo ta gyara inda jinin da ya zuba dazu ya babbata, tana gama gyaran wurin ta koma kitchen ta dora abincin rana,tuwon alabo miyar ganye ta yi tana kammalawa ta shiga wanka kamar kullum k'ofar bathroom din a bude ta barta, tana wankan jabir ya shiga dakin domin dawowarsu kenan daga masallaci sallar azahar shida al'amin,
"Wai ba zaki daina wanka toilet a bud'e ba" ya fada