Wani Haske Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Hameedah Category :  Complete Novels

Chapter   3 / 35

6K to 9K   out of 102.7K words

kaga chocolate dina"

GM baice komai ba sai kallonshi da yayi yakuma maida kallonshi jikin window nan ya hango goodness tana dagawa al'amin hannu.


Tun daga wannan rana bai dawo office ba saima tafiya da yayi zuwa jihar katsina nan goodness ta shiga cikin damuwa amma kullum cikin yi masa waya take tana fadar karya da gaskiya dan kawai taji muryarsa shi kuwa baima san tana yi ba, ganin irin mutanen da suke zuwa wurinshi yasata tambayar massinger dinshi kodai GM yanada traditional tittle ne? Murmushi yayi yace da ita kawai dai malamin addini ne shiyasa mutane suke zuwa sosai hakan ba karamin dadi yayi mata kuma dama taga alamun hakan sai dai ita ahalin yanzu tana cikin matsala domin ma tafara tasowa da maganar bikinsu da promise wanda ita kuma yanzu bashi take so ba.




_*Ummi Shatu*_πŸ‘ŒπŸ»
[8/22, 9:02 AM] Ummi A'ishaπŸ‘ŒπŸ»: *WANI HASKE*

_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_

_21-25_


~~~Bayan ta tashi daga aiki tana komawa gida ta samu ma zaune tsakar gida tana tace gasarar koko yau da alama ba taje church ba ko kuma taje da wuri ta dawo,

Agajiye ta zauna tana kallon ma "ma sannu da aiki"

"Yawwa my daughter, daga gani kin gaji"

"Ma nagaji sosai wlhi, ina baba?"

"Bai jima da fita ba, sannan gobe ne birthday din promise dan haka gobe ba zakije office ba church za muje, gobe zaki sawa promise zoben alqawari (promise ring) shima zai sa miki, daga nan kuma sai maganar biki"

Wata uwar faduwar gaba goodness taji saboda jin maganar da ma tafada nan ta bata rai ta kalli ma,

"Ma nifa yanzu bana son promise, akwai wanda nake so, shi promise kwata kwata bai dace dani ba ni bana son mai shan giya"

Ido cikin ido ma take kallonta "waye wanda kike so?"

Cikin faduwar gaba tace "ma oganmu ne a office"

"Musulmi ko? Bahaushe? Kina so ya aureki ya sakeki ko? Hausawa saki suke yi gashi suna yin kishiya saboda su basa yin auren zobe"

Daga kai tayi "ma nayarda indai zai aureni"

Matacin gasarar ma ta saki yafadi a kasa tana tafa hannu "oh chineke, goodness you want to marry hausa man? You want to marry a person that your religion and his religion are not the same, the man that your tribe and his tribe are not the same even your culture are not the same with his own culture, hmmm any where, tunda haka kin zaba, Allah yabaki sa'a amma idan kika auri hausa man duk abinda yayi miki babu ruwana, kar ki zo wurina and lastly koda kin auri hausa ba zakibi addininsu ba, idan kikace zaki bi addininsu sai na kasheki goodness"

Ajiyar zuciya goodness ta saki "ma kin san dai nima ina son wannan addinin namu bazan iya rabuwa dashi ba dan haka ki daina doubting akaina"

"Goodness in kin bar addininmu kin karbi nasu sai na tsine miki albarka, sai nasa Allahnmu yayi fushi dake"

"Ma bazan karbi addininsu ba kidaina fadin haka"

Tashi ma tayi ta kinkimu bokitin gasarar ta tayi kitchen dashi tabar goodness da tagumi tana tunanin yanzu ta ina ya dace tafara tunkarar auren GM? Tambayar da tayita nanatawa zuciyarta kenan.

Daren ranar ba tayi bacci ba, asussubar fari ta dauki bible ta tafi church lokacin ma ta dade acan tana zuwa ta shiga sahun masu bauta ta zuba gwiwoyinta a kasa ta rufe ido ta fara addu'ar samun nasara awurin Malam jabir, sai da rana ta fito sannan ta dauko jakarta ta dawo gida tana kiran _"fire, fire"_ domin su a church dinsu wuta suke bautawa (Allah yayi mana tsari da ita)

Tana zuwa gida wanka tayi ta shirya cikin riga da wando matsattsu ko tea bata sha ba ta nufi office, karfe _9:00_ ta isa lokacin har GM ya dade a office dan haka jakarta kawai ta ajiye ta nufi cikin office dinshi domin ta kagu taga kyakkyawar fuskarshi gashi zuciyarta sai harbawa take yi fat fat,

Kwankwasawa ta danyi kafin ta bude kofar ta shiga, can ta hangoshi zaune kan kujerarsa hannunsa rikeda wani littafi wanda ba zata iya tantancewa ba yana dubawa sannan ya kunna karatun alqur'ani kasa kasa yana saurare, yana sanye cikin farar shadda mai kyau sai kyalli take, kusan duk kayansa farare ne a yanda ta fuskanta domin bata taba ganinshi da wasu kalar ba daga fari sai milk colour,

"Good morning sir" tafada tare da dan durkusawa,

"Morning" yafada a hankali, sanin bazai kara magana ba ya sata juyawa zata fita,

"Am kinga" yafada ahankali, hakan yasa ta dawo tace "na'am sir"

"Kidaina irin wannan shigar idan zaki fito office, ki rinka sako normal kaya saboda nan kinga cikin mazane kuma mu a addininmu hakan bai dace ba, kamar yadda kuma a addininku hakan laifi ne, dan Allah akiyaye"

Kur tayiwa dan karamin bakinsa da idonta lokacin da yake mata magana, dagowa yayi ya kalleta yaga itama shi ta kurawa ido,

"Kinji abinda na fada"

Sai alokacin ta dawo hayyacinta "yes sir, nagode sir"

"Ok kina iya tafiya" yafada tareda mayar da idonsa kan littafin da yake karantawa,

Office dinta ta koma ta zauna tana murmushi amma kuma zuciyarta har yanzu bata daina bugawa ba, tunani tafara yi itafa duk kayanta totally babu atamfa domin bata dinkasu kuma ko ta dinka ba dinkine na cin mutunci domin sai anyiwa atamfar kaca kaca kafin a dinkata, sai anyi mata gutsi gutsi, dan haka kayanta daga riga da skirt sai riga da wando amma duk da haka zata daure ta zabo masu dan dama dan ganin tabi maganar da ya fada mata kuma hakan da yayi ba karamin sake burgeta yayi ba.

Da yamma ta tashi daga aiki ta koma gida, a kofar gida ta hadu da nura cikin murna ta jashi cikin gidan domin dama tana son ganinshi,

"Yanzu kin zama worker kinyi wuyar gani ko?" Nura ya fada ya dariya,

"Sorry nura dama inata son nayi maka waya, nura dan Allah ka taimakeni ka sanar dani wani abu dangane da GM dinmu domin zuciyata ta kasa kyaleni in huta"

Kallonta nura yayi "ban fahimceki ba, wai malam jabir kike nufi? Me ya faru?"

"Nura nothing, i beg ka fada min pls nura, am in bad condition, ina bukatar jin wani abu game dashi domin ina son na aure shi"

Zaro ido nura yayi "aure? Aure fa kikace goodness, taya kike tunanin wannan auren naku zai yiyu kina Christian kina ikirararin Allah ukune, kina mai yarda da cewa Annabi Isah Allah ne, kina cewa Maryam Allah ce, kina cewa Isah dan Allah ne, shikuma mal jabir yaki yake da wannan kalmar, kiran mutane yake akan su daina furta wadannan kalmomin, kira yake abi Allah shi kadai,tayaya wannan hadin naku zai yiyu? Da ace shi ba malami bane mai wa'azi tabbas may be zai iya aurenki, to amma shi mai wa'azi ne malamine wanda yayi suna ba a iya kasar nan ba har da sauran wasu kasashe na musulmai ai kinga abun kunyane agareshi aji yana auren wacce ba musulma ba"

Ajiyar zuciya goodness ta sauke mai nauyi "gaskiya ka fada nura amma kuma ni rashin aurenshi agareni wlhi tamkar rasa rayuwata ne dan Allah nura ka taimakeni" ta fadi hakan lokacin da kwalla tafara bin kumatunta,

"Shikenan goodness babu komai zan taimaka miki domin nasan haduwarki da malam jabir _*Wani Haske*_ ne acikin rayuwarki, zan taimaka miki har kikai ga samun wannan hasken, yanzu kin san ya za ayi? Zanje gidansa anjima da daddare zan halarci majalissinsa inda yake karantarwa bayan sallar magrib anan zan nemi fatawa cewar wata wacce ba musulma ba ta ganni tana sona shin zan iya aurenta? Kinga anan zan gane ko zai yarda ya aureki ba tare da kin musulunta ba"

"Good nura nagode sosai, ina jiranka idan ka dawo"

Tashi nura yayi ya fita a lokacin ma ta shigo tana rikeda bible dinta "hey goodness, meya hanaki zuwa church? Am asking you meyasa ba kije church ba? Kin fara wasa da addinmu ko goodness? Idan kinci gaba da haka pastor will punishe you nikuma ba ruwana ehem"

"Sorry ma dawowana kenan daga office, gashi nagaji shine nabari sai da daddare zanje church din night service"

Fara,a ma tayi cikeda murna tace "i like you my daughter, God bless you, ina babanki fa?"

"Ma babu kowa agidan lokacin da na dawo ina jin ya fita"

Kada kai ma tayi ta wuce cikin daki tabar goodness zaune anan zuciyarta tanata harbawa domin rashin sanin abinda nura zaizo mata dashi.

Kamar yadda nura yace haka yayi bayan an tashi daga karatu ya dubi malam jabir yace "malam ina da tambaya, wata yarinya ce ta yaba da nagarta ta kuma ta yaba da rikon addinina da halayyata tace tana son na aureta to amma fa ita ba musulma bace, mahaifiyarta ma ba musulma bace mahaifinta kuma musulmi ne, to malam ya halarta na aure ta?"

Kallonsa malam jabir yayi yana murmushi "ya halarta ka aureta,addini ya baka dama amma sai ta kasance wacce ba mazinaciya ba, sai ta kasance ya ba baiwa ba wannan shine sharadin, addinin Allah mai saukine, babu haramci a auren ma'abota littafi kwata kwata sai dai idan mutum bashida ra'ayi ne domin ba kowanne mutum ne zai auri wacce ba musulma ba, kaga kamar ni idan ka bani wacce ba musulma ba bazan aureta ba saboda wasu dalilai amma nasan aurenta ba haram bane".

Daga kai nura yayi dama tun farko abinda ya zarga kenan, "to malam amma misali idan kaga yarinyar zata fada cikin wani hali marar kyau ai zaka aureta ko?"

Murmushi malam yayi har sai da hakoransa suka fito "kune yara ku ya kamata kuyi irin wadannan taimakon"

Yana kaiwa nan ya tashi ya shiga gida, tahowa nura yayi jikinsa a sanyaye, a farkon layinsu ya hango goodness tsaye tana jiran dawowarshi.

Tana hangoshi zuciyarta taci gaba da dukan uku uku har ya karaso suka samu wuri suka zauna,

"Goodness gandoki kin kasa zama agida kin biyoni nan"

Murmushin karfin hali tayi "ya akayi"

"Komai mai yiyuwane da yardar Allah amma shi dai a ra'ayinshi bashida sha'awar auren wacce ba musulma ba sai dai wannan ba shine yake nuna cewar bazai aureki ba, kinga na farko shi mutumne wanda ya karanci addini tsantsa saboda asalima baifi shekara 5 da dawowa _Nigeria_ ba daga _madina_ acan yayi karatunsa na addini wanda ya shafe fiyeda shekaru _20_ acan, bayan dawowarshi ne yayi aure yanzu yana da yaro guda daya, amma goodness mezai hana ki yarda ki karbi musulunci idan kikayi sa'a ta sanadiyyar karbar musuluncin ya aureki"

Da sauri ta girgiza kanta hawaye na bin kumatunta "no, nura ba zan iya musulunta ba nidai ya aureni a haka nayi addini na yayi nashi, idan nace zan musulunta ma bazata yarda ba"

"To shikenan yanzu kin san ya za ayi? Mahaifinsa za muje mu samu kiyi masa bayani, shi mal jabir mutum ne mai tsananin biyayya wa mahaifinsa, baya ketare umarninsa, nasan indai mahaifinsa ya yarda shima zai yarda"

Dan murmushi tayi "Allah yasa ya yarda, nura nagode, yaushe zamuje?"

"Gobe za muje da safe sai ayi masa bayani"

Cikeda murna sukayi sallama ta tafi church, acan ta kwana sai da asuba ta dawo, yanzu promise ya gama gane cewar ta daina sonshi dan haka shima ya fita a harkarta.

Karfe 10 nasafe suka hadu da nura suka tafi unguwar masanawa inda acan mahaifin mal jabir yake, gidane babba kato da masallaci a kofar gidan, acikin masallacin suka sameshi yana lazimi, tsoho ne dan kimanin shekaru 70 aduniya fuskarshi duk farin gashi amma jikinsa ras yake,

Ita goodness bata shiga ciki ba awaje ta tsaya tasa doguwar riga yar kanti ta daura bakin dan kwali, nurane ya shiga ciki suka gaisa da tsohon yayi masa bayanin komai wanda yasani babu abinda ya boye tun daga farko har karshe sannan ya kara da cewa "mahaifinta da mahaifiyarta dukkaninsu yan okene ne amma suna zaune anan jalingo, sannan mahaifinta ya dade da musulunta tun shekaru masu yawa da suka wuce ta sanadiyyar wani makocinsa da suka zauna tare agarin jos, amma ita mahaifiyar har yanzu tana nan akan addinin yahudu da nasara"

Dan murmushi tsohon yayi yace "yaro wannan mutumin da kace ya musulunta nine nabashi kalmar musulunci lokacin ina zaune agarin jos ina koyarwa a jami'ar addinin musulunci dake garin, shekarune masu yawa bana mantawa aka kawo min shi akace zai musulunta, nine nan nabashi kalmar shahada, babu komai insha Allahu jabir zai aureta kamar yadda take son ya auretan, amma ka sanar da ita idan tasan zata aureshi ne da niyyar ta cutar dashi to gara ta fasa idan kuma tsakani da Allah take sonsa to falillahil hamdu insha Allahu sai jabir ya zama _*WANI HASKE*_ acikin rayuwarta"

"Mun gode malam, Allah ya kara girma da nisan kwana" nura ya fada tareda tashi ya fito inda goodness ke tsaye tana sauraronsu, duk wadannan maganganun da akayi acikin kunnenta akayi su shiyasa farin ciki ya mamaye zuciyarta marar misaltuwa, machine din nura suka hau suka bar wurin ya tafi kaita office duk da cewa yau tasan ta makara sosai amma haka zata daure taje dan ta ganshi,

Murna fal acikin zuciyarta nura yana ta kara yi mata karin bayani har suka je office din ta sauka tana yiwa nura godiya ta shiga ciki, Massinger dinsu ta samu zaune shi kadai ganinta ya fara yi mata sannu da zuwa, anan yake sanar da ita oga yana conference room yana meeting da directors dinshi, wannan rana ta yau goodness na cikeda farin ciki.

Sai da lokacin salla yayi sannan masu meeting din suka firfito domin zuwa salla, office dinsa ya nufa domin yin alwala, yana shigowa sukayi ido hudu da goodness, dauke idonsa daga kanta yayi yashiga office dinsa bayan massinger ya bude masa kofa, binsa ciki tayi lokacin ya cire hular kansa yana saka silifas zai shiga toilet,

"Sannu sir" tafada cikin farin ciki

"Yawwa" yafada yana balle clips din hannun rigarshi,

"Sir yau naje unguwane shiyasa ban zo da wuri ba"

"Babu damuwa amma ki kiyaye next time"

"Yes sir" bai sake magana ba ya nufi toilet.

***

Bayan ya tashi daga office around _5_ ya nufi gidan mahaifinshi, a babban falon shi ya tarar dashi zaune ya bude katon alqur'aninshi yana karantawa, jin sallamar malam jabir yasashi rufe alqur'anin ya juyo ya dubeshi da fara'a a fuskarshi,

Zama yayi kusa dashi ya russuna ya gaisheshi,bayan ya amsa ne yace

"Jabir dalilin kiran da nayi maka ayau shine kaga dai nafarko kana daya daga cikin mutanen da ake girmama su acikin garin nan ake koyi dasu, kuma kallum aikin samun lada kake yi, wannan dalilin ne yasa yau na sake kawo maka kokon barar wani aikin samun ladan, nasan Allah ya hore maka arziki, da kuma zuciyar da zaka iya rike mata biyu, wannan dalilin ne yasa na umarceka da kayi hakuri ka daure ka auri wata yarinya ma'abociyar littafi wanda nake kyautata zaton cewa idan Allah ya yarda _*wani haske*_ ce agareka kamar yadda kaima zaka kasance _*wani haske*_ agareta, ba musulma bace amma ta kamu da tsananin sonka saboda nagartarka da kyawawan dabi'unka gamida kyawawan halayenka da ta duba,ni kuma nasha mata alwashin insha Allahu zaka aure ta zaka zame mata _*wani haske*_acikin rayuwarta"

Tun farko tun asali ko acikin mafarki bai taba tsammanin zai iya aurar wacce ba musulma ba saboda basa burgeshi amma yanzu bazai iya yiwa mahaifinshi gardama ko musu ba dan haka ya aminta "shikenan malam insha Allahu zan aureta kuma zan zauna da ita"

"Allah yayi maka albarka jabir, amma kayi min alqawari zaka riketa bisa amana"

"Malam insha Allahu zaka sameni mai rikon amana akanta tareda yin adalci"

Albarka mahaifin nasa ya shiga saka masa tareda yi masa fatan alkairi acikin rayuwarsa, sallama yayi masa ya tashi ya tafi yana jimamin wannan al'amari acikin ranshi, wai a matsayinsa na mai wa'azi shine zai auri wacce ba musulma ba.




_*Ummi Shatu*_πŸ‘ŒπŸ»
[10/28, 9:26 PM] β€ͺ+234 810 100 9022‬: [8/23, 10:08 PM] Ummi A'ishaπŸ‘ŒπŸ»: *WANI HASKE*

_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_

_26-30_

~~~Tun yana hanya ya fara laluben number uwar gidansa wato ummu al'amin kamar yadda yake kiranta, ringing biyu ta daga cikin sallama,

"Abu al'amin yau baka dawo da wuri ba, duk aikin office dinne ya rike ka haka?"

"Gani nan nataho yanzu, na dan biya ta gidane naga malam"

"To Allah ya kawoka lafiya, ga al'amin"

Karbar wayar al'amin yayi cikin murna yace "hello abbu na kaga ummu ta dakeni"

"Ohhhhh al'amin rikici, laifi kayi mata ko?"

"Abbu ni banyi mata laifi ba"

"Haka kawai ta doke ka? To idan na dawo zan rama maka"

"Yawwa abbuna sakallahu kairan wa ilal liqa"

Kashe wayar yayi yana murmushi a rayuwarshi yana son yaron nan nashi shiyasa yake son yaga ya tsaya tsayin daka don ganin rayuwarshi ta inganta to amma yanzu gashi wani al'amari mai girma ya na kokarin kunno kai cikin rayuwarshi data iyalinshi, sam bashida ra'ayin auren ma'abota littafi wato (ahlul kitab) to amma yanzu hakan ya zame masa tilas ko dan samun ladan yin jahadi amma yana jinjina ta yanda zai iya rayuwa da macen da bata tsarki.

Lokaci kankani suka isa gidansa dake unguwar farin gidaje, gidane na alfarma tamkar gidan wani sarkin nidai ummi A'isha nace ashe malamai suma yan jin dadine, farfajiyar gidan driver yaje yayi packing yafito ya budewa GM kofa shima ya fito ya nufi cikin gidan, part ukune part din farko shine na ummu al'amin, nakusa da nata nashi na karshen kuma empty yake babu kowa aciki, yana shiga falonta ya jiyo surutun al'amin wanda yaketa wasansa yana kallon tashar spaceton Arabiya, da sallama ya shiga, da gudu al'amin ya taso ya rungumeshi, hannunshi ya rike yabi ta kofar falon yafita wani dan korido ya shiga sashensa yana shiga daki al'amin yafito ya tafi falo yana kokarin kunna tv, wanka ya shiga yayi ya fito ya shirya cikin jallabiya fara da yar hularta itama fara ya fito falonshi nan ya tarar da al'amin yana kallon tv, zama yayi kusa dashi daidai lokacin wata kyakkyawar mace yar madaidaiciya ta shigo tana sanye da doguwar riga da dan karamin hijabi shekatunta ba zasu fi 28 ba fara doguwa,

Hannunta dauke da food flasks guda biyu, "barka da isowa Malam" tafada tana dan murmushi,

"Yawwa yagida" yafada yana duban al'amin wanda yaketa faman dariya saboda cartoon din da yake kallo na larabci,

"Tashi kaje kayi alwala mu tafi salla ko walad"
"Abbu ni yanzu ba walad bane na girma"

"Yaushe ka girman?"

"Abbu nagirma nazama rajulin" yana gama fadin haka ya tashi da gudu ya fita,

Murmushi ya rakashi dashi yayinda ita kuma matar ta matso kusa dashi "yau baka dawo da wuri

3 / 35