Wani Haske Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Hameedah Category :  Complete Novels

Chapter   24 / 35

69K to 72K   out of 102.7K words

kuka idan ba haka ba zaki haifi yaro ruwa ruwa"

Dariya ce ta subuce mata bata shirya ba "abbu nida ko cikin banyi ba har zaka fara yimin maganar yaro" tafada tana yi masa murmushi,

"Saurin me kikeyi binti? Zakiyi ai soon"

Murmushi tayi har lokacin tana rikeda hannunsa "abbu ka taho min da chocolate"

"Muga bakin kwadayin shan chocolate?"

Bakin ta bude tana turo masa dan yagani, kiss ya manna mata akan lips dinta duka yana murmushi,

Sakinsa tayi ta juya tana murmushin itama, fita yayi yana mai jin babu dadi acikin ranshi dalilin nisantar ta da zaiyi,

Tana labe tana lekenshi har yabar gidan, kan kujera ta fada ta kwanta tana tunanin hali irin na jabir.

Tunda ya tafi yabarta taketa kirkirar ayyuka domin bata son zama kurum saboda idan ta zauna tasan kadaicine zai dameta gashi kuma tunda jabir yafita take tunaninshi acikin zuciyarta,

Babu irin aikin da bata yi ba domin ganin ta ragewa kanta lokaci, kananan kayan jabir duk ta tattare da jallabiyoyinshi da kayan baccinshi duk ta wanke, bayan ta gama taje ta dora girki, tuwon shinkafa miyar agushi tayi tahada lemonta na kwakwa da madara kamar yadda ta saba,

Wayar jabir tafara kira lokacin misalin karfe 1:30 narana, yana tsaka da aiki a office sai rubuce rubuce yake gashi files tuli guda akan teburinsa kasancewar ya dade baya office din shiyasa ayyuka suka tarar masa,

Agajiye ya daga wayar yana murmushi aranshi kuma yana tunanin ko yanzu da wacce rigimar ta bullo kuma,

"Binti ya akayi?"

Fuska ta shagwabe kamar yana kallonta, "abbu sai yaushe zaka dawo?"

"Binti aiki yayi min yawa, sai 5 zan tashi may be ma yau sai nayi over time saboda inada ayyuka dayawa"

"Abbu kar kayi over time dan Allah, kadawo 5 din"

"Kina son ganina ne binti?"

"Ehh abbu"

"Me zaki bani?"

"Abbu sai kadawo dai, yanzu dai ka turo min mal idi driver"

"Ina zaki aikeshi?"

"Wurinka abbu, dan Allah karka manta"

"Bazan manta ba"

"Yawwa abbu nagode, ayi aiki lafiya"

Wayar ta tsinke tana jin wani irin dadi acikin ranta,

Shima jabir wayar ya ajiye yana murmushi ko me zata aiko masa kuma oho,

Lokacin da mal idi driver yazo dama tuni ta gama harhada masa kayan acikin kwando babba, komai da zai bukata ta zuba kama tun daga filet da cokula da cups da tissue domin goge hannu, dan haka yana zuwa bashi kawai tayi takoma sashenta,

Lokacin da sakon ya riski jabir ba karamin mamaki yayi ba, domin abincine wanda akalla mutane biyar zasu ci ya ishesu gashi harda hadadden lemon kwakwa,dadine yake ratsashi tako ina dama meeting zasuyi shida directors dinsa Wanda duk lokacin da sukayi meeting din abincin sayarwa ake siyo musu amma shi baya ci saboda gaskiya yanada tsananin kyankyami,

Wannan abincin da bahijja ta aika musu shi sukaci sukayi kat Suna santi kowa sai yabawa yake yi, shikuwa jin bahijja yake har acikin zuciyarsa saboda yasan ta damu dashi sannan tana kiyaye duk wani abu wanda zai sakashi cikin damuwa, ranar har 6yakai a office sai 6:30 ya nufi gida, duk ya gama kosawa burinsa kawai yaje gida yayi ido hudu da ita.


Tana falonta tana kallon wani American film ya shiga yana gyara babbar rigarsa,

Tashi tayi tana murnar ganinsa yayinda shikuma yayi mutuwar tsaye yana kallon kyakkyawar shigar da tayi domin wata rigace orange colour mai wasu fararen duwatsu ajiki, iya cinya rigar take sannan bata da babban hannu, hannunta dan karamine, ga wani wando baki fela tasaka, kanta ta daura bakin dan kwali,

Gabansa taje ta tsaya tana kallonsa,

"Abbu sannu da zuwa"

Hannu ya mika ya kamo nata hannun yajata ya hadata da barin jikinshi ya nufi sashensa da ita,

"Yawwa binti ya gida? Natafi nabarki ke daya ko?"

Daga kai tayi "abbu ai gobe sai nabika"

Murmushi yayi yana mai tuno al'amin dinshi domin shima kusan kullum haka yake cewa sai ya bishi office lokuta da dama sai yayi masa dabara sannan zai samu ya zare jikinsa ya fita,

Har cikin falonshi ta rakashi tana shakar kamshin jikinsa, cikin bedroom dinsa ya shiga yayi wanka ya fito yayi shirin masallaci, gaba daya kamshine ke tashi daga jikinsa,

Har inda take yaje ya kamo hannunta ya yatasheta daga zaunen da take ya rike yan yatsunta yana kallon kwayar idonta, sunkuyar da kanta tayi ta kasa kallonsa,dago habarta yayi yakai bakinsa kan goshinta yayi mata kiss,yana murmushi,

"Binti zanje masallaci kinji? Sai nadawo"

Kai ta daga masa sannan ahankali tace "adawo lafiya abbu".

Fita salla yayi ita kuma ta koma sashenta tayi tata sallar, anan ta zauna tafara yin azkar irin wanda jabir ya koya mata, dab da sallar isha ta tashi takoma sashensa tana sanye da zumbulelen hijabi mai hannu wanda ya saukar mata har kafafunta domin yanzu jabir ya kawo mata hijabai manya kala daban daban.

Asashensa tayi sallar isha, tana idarwa tafara karanta hadisin da ya koyar da ita adaren jiya wanda aka karbo daga baban hurairata Allah ya kara masa yarda wanda annabi Muhammad sallallahu alaihi wassalam yake cewa "yaku mutane ku yada sallama, kubayar da sadaka, kuyi sallar dare alokacin da mutane suke bacci, idan kukayi haka hakika zaku shiga aljanna da aminci"

Shigowar jabir ce ta katse mata tilawar karatun da takeyi, kafadunta ya kama ya mikar da ita tsaye,

"Tashi muyi salla binti"

"Abbu ni nayi sallata yanzun nan na idar"

Dan malalacin murmushi yayi mata "binti wannan ai daban, wannan ta nafila ce zamuyi, sannan ina son ki dage ki rinka yin sallar shafa'i da wutr domin tanada tsananin falala mai tarin yawa"

"Abbu zan rinka yi kaga shikenan basai nayi ta tsakar dareba irin wacce kake yi"

"Waya fada miki? Koda ace kinyi shafa'i da wutr to zaki iya tashi da daddare kisake yin sallolin nafilarki kuma zakiyi shafa'i,wutr ne kawai bazaki yiba domin sau daya ake yinsa idan mutum ya sake to yazama shafa'i, nasan mutane da dama suna son tashi yin sallar dare to amma idan har sukayi shafa'i da wutr sai su zaci Cewar shikenan babu damar yin wata sallar tunda sun rufe da wutr to ba haka bane mutum zai iya yin wasu sallolin acikin dare koda kuwa yayi shafa'i da wutr kawai dai ba ason ya sake yin wutr ne domin wanda yayi afarko ya wadatar"

Kai ta kada masa tafara gyara masa abin sallar yanda zai ishesu,

Limanci yayi yajasu sallar suka gudanar da sallolin nafila wanda hadda shafa'i da wutr, addu'o'i sosai jabir yayi musu wadanda ba zasu faduba,

Bayan ya shafane ya jiyo yana kallonta, "binti idan kin idar akwai kaya acikin babban falo kije ki dauko, ina fata dai bakiyi wani girkin ba? Saboda yau naga kinsha aiki da yawa"

Addu'ar ta shafa tana kokarin cire hijabin jikinta "hmm abbu banyi ba dama yanzu nake tunanin dafa mana indomie"

"To na hutar dake basai kin dafa ba"

Hijab din ta ajiye ta fita taje ta shigo da kayan da yazo musu dashi,

Kaza dukekiya ta gani guda biyu gasassu ga chocolates dinta kala kala sannan ga kayan marmari suma daban daban,

Baje kayan tayi tana kallon jabir "abbu yau ka hutar dani nagode da yanzu sai nasake shiga kitchen"

Yan yatsunta ya kamo "babu komai binti, ai naga sakonki ya sameni har office, me yasa kika bini dashi har can?"

"Bana son ka zauna da yunwane shiyasa kuma nasan kai ba cin abinci zakayi ba haka zaka wuni da yunwa nikuma bana son haka"

"Nagode binti, ga abinci nan kici nakine ke daya"

Idanuwanta ta ware "abbu wannan sunyi min yawa, bazan iya cinyesu ba"

Kankana ya dauka yakai bakinsa "ni kinga iya abinda nake sha'awa kawai, ita kadai zansha"

"Abbu kazar fa?"

"Takice yarinya, kici kayanki kinji"

Kai ta girgiza tafara yagar kazar tana ci har taci rabi nan taji tafara koshi,

"Abbu yau zaka doramin karatu ko sai gobe?"

"Duk yanda kikeso binti, amma karatunmu na yau daban yake dana ko wacce rana, karatun yau na musamman ne"

Cigaba tayi da shan chocolate dinta domin bata fahimci inda maganar tasa ta dosa ba, har ta kammala yana zaune yana kallonta, kanta ta dora asaman cinyarsa,

"Washh abbu cikina nakoshi da yawa"

Kanta ya fara shafawa yana yi mata lalube acikin gashinta

"Kinyi irin koshin da ba aso mutum yayi, annabi yace idan dayanku zaici abinci to ya raba cikinsa gida uku, kashi daya abinci kashi daya ruwa, kashi dayan kuma iska saboda gudun kada ya cutar da jikinsa"

Zaune ta tashi "hmm abbu komai dai a musulunci ana bashi hakkinsa, Allah abbu musulmai sunji dadin rayuwarsu"

"Tashi muje nasaki aiki a kitchen"

Tashi yayi yaja hannunta suka fita zuwa kitchen, shayin na'a na'a ta dafa masa da kayan kamshi sannan suka dawo sashensa, tana kwance akan cinyarsa akan doguwar kujera shikuma yana shan shayinsa ga tv kuma yana kallo,

Wayarshi ce tafara kara, yana dubawa yaga ummu ce,

"Ummu al'amin kin dawone daga siyayyar?"

Tana jin ya ambaci sunan ummu tafara kokarin mikewa, cup din shayin ya ajiye ya riketa ya mayar da ita jikinsa yaci gaba da wayarshi daga karshe sukayi sallama yana tambayarta al'amin tace yayi bacci tun jimawa,

Wayar ya kashe yana kallon bahijja bayan sunyi sallamar da ummu,

"Abbu bacci, zanje nayi wanka" tafada tana mutsusstuka idonta,

"Bari nagama nakaiki kiyi" bata sake magana ba ta zauna tana jiransa, kasancewar komai nashi cikin sanyi yake yinsa shiyasa ya dade bai gamaba,

Yana gamawa ya kama hannunta zuwa cikin bedroom dinsa,

"Ki shiga kiyi wankan" ya nuna mata bathroom dinsa,

"Abbu brush dina da kayan baccina fa"

"Duk zan baki binti, ai na tanadar miki komai saboda zuwan wannan ranar"

Sabon brush ya dauko ya mika mata hadeda babban towel sabo fil,

Karba tayi ta shiga bathroom din amma duk tana cikeda mamaki da al'ajabi,

"Binti yau bazaki bar kofar bathroom din abude ba? Ko yau babu tsoro?" Yafada cikin tsokana,

Batayi magana ba tasaka key ta kulle kofar, mayukan wanka ta gani masu kamshi dayawa kala kala, duk sai da tayi amfani dasu ta wanke jikinta tas sannan tayi brush ta tsaftace bakinta bayan ta shaftace jikinta da shaving stick, hatta bayan kunnuwanta sai da ta tsaftacesu kasancewar wurine dake rike kazanta dan haka dole sai ana kulawa dashi,

Sai da ta dauki tsawon lokaci tana gyara jikinta sannan ta fito duk a tsure take da jabir sai muzurai take yi.


Acikin dakin tasameshi kishingide agefen gado yana kallonta, irin kallon da yake binta yasata jin kunya,

"Abbu nafito" tafada adirirce,

"Ga rigar baccinki nan kishirya sai kisa"

Towel din jikinta ta gyara,

"Abbu to ka fita daga dakin"

"Tofa, wata sabuwa" tashi yayi yana kallonta yafita ya koma falo, gaban mirror ta karasa ta fara shafe jikinta da man shafawarsa na touch me mai dadin kamshi, turarurrukansa ta fara dubawa har ta samo wani guda daya mai suna taibah, shi ta dauka ta feshe jikinta dashi sannan ta feshe rigar baccinta,

Bathroom ta koma ta tsaya tafara duba rigar, tabbas rigar ta hadu sai dai kuma zatasha kunya yau domin rigar za a iya kiranta da shararatu, banbancinta da gidan sauro kawai ita rigace amma net shine yanayinta,

Rigar bata bukatar bra domin akwai ajiki sannan tanada dan karamin pant,kalarta pink colour,

Daurewa tayi tasaka rigar, tana gama sakawa ta juya tafara kallon jikinta ajikin mirror din cikin bayin, tayi kyau iya kyau abunka da yar duma duma sai kace oh oh, jin alamun za a bude kofar yasata saurin janyo towel ta lullube jikinta, jabir ne ya leko ya jawota waje,

"Haba binti me kika sake komawa yi acikin bathroom kuma?"

Towel din yafara ja yayinda ita kuma ta rike kam, dakyar ya janye towel din hakan ya sata saurin rufe fuskarta da tafukan hannayenta,

"Masha Allah, binti irin wannan kyau haka?"

Sake damke idonta tayi tana doddoka kafafunta akasa,

"To jeki ki kwanta kinji"

Hannunta ya kama ya rakata har inda ta saba kwanciya ya saketa ya juya, cikin bathroom din shima ya shiga yayi wanka bayan ya tsaftace kowanne lungu na jikinsa,

Fitowa yayi yanata faman kamshi, gaban mirror yaje ya fara shafe jikinsa da mayuka masu kamshi,
Kayan baccinshi ya dauko yasaka ya karasa gefenta ya kwanta gamida janta jikinsa,

"Binti ko har kinyi baccine bayan ba muyi hira ba yau?" Yarada mata ahankali yana wasa da zip din rigarta, tana jinsa tayi shiru tayi luf,

"Nasan idonki biyu, jiyo kiji"

Yafada ahankali, jin shiru yasashi jiyo da ita tana fuskantarsa, cakulkuli yafara yi mata cikin sauri ta rike hannunsa bayan tafara dariya,

"Abbu kabari dan Allah"

"Au dama kina jina shine kikayi min shiru?"

"Bazan karaba yi hakuri abbu"

"Yawuce binti, shikenan saura karatunmu da muka fara rannan ko?"

Bata iya yin magana ba hakan ya sashi kashe wutar dakin bayan ya lalubi bakinta cikin nashi.


***

K'arfe 8 daidai ta bude idonta, dakin shiru babu motsin komai aciki,sama ta daga kanta take kallo take abubuwan da abbu yayi mata suka fara dawo mata, hawayen farin ciki tafara yi fuskarta dauke da murmushi domin wannan rana ta jiya da yau ranakune masu mutukar muhimmanci acikin rayuwarta,

Dakyar ta juya jikinta daga barin da take kwance nan taga tsakiyar gadon tamkar an yanka kaza,

"Hmmmmm abbu kenan" shine abinda kawai tafada ahankali tafara kokarin tashi, lallabawa tayi ta shiga toilet tana dingisawa, ruwan zafi ta tara mai mutukar zafi amma bata saka dettol aciki ba kasancewar ta taba jin wani likita yana bayani kan illolin dettol ajikin mace shiyasa ba ason ayi sit bath dashi amma babu laifi ayi wanka dashi ko kuma awanke kaya domin yana da karfi yana kashe bacteria kowacce iri ciki harda mai amfani da marar amfani, gishiri kawai ta zuba acikin ruwan zafin ta shiga ta zauna domin shi gishiri har maganin kaikayin dake damun mutum yake yi haka kuma yana riga kafin ciwon cutar sanyi,

Ta dade acikin ruwan har sai da ya huce sannan tafita tayi wanka tayi brush amma duk agaggauce take yin wadannan abubuwan saboda bata son jabir ya shigo ya isketa bata shirya ba kuma haka ya kamata ga kowacce mace domin lokacin da aka tashi daga bacci agaskiya lokacine dake bayyanar da munin mutum kasancewar daga bacci aka tashi zaka samu wata ma launin fuskarta ya sauya idonta yayi ja wata harda kwantsa, sannan ita kanta yanayin fuskar wani iri yake zama har sai anyi wanka,

Fitowa tayi daga cikin bayin tayi maza tafara bincikar kayan sawarsa, wata farar t shirt ta zaro mai layi layi ajiki mai dogon hannu da maballaye ajiki, cikin sauri ta saka rigar sannan ta zaro jeans blue shima tasaka sai dai kayan tsayinsu yayi mata yawa kasancewar jabir dogone ajin farko,

Hijabinta ta dauka tayi salla tana idarwa tayi musu addu'o'i musamman ma kan samun zuri'a tagari duk da cewar jiya taji jabir ya dade yana yi musu wannan addu'ar lokacin da abubuwa zasu faru,

Cire hijabin tayi ta tashi bayan ta kammala addu'ar,gashin kanta taje gaban mirror ta fara tajewa amma kuma sai kamshin man datayi amfani dashi wurin wankewa yake, domin ita ba zata iya kwarawa kanta ruwa kawai tabarshi ahaka ba har sai tasaka man wanke gashi ta wankeshi domin idan aka zubawa gashi ruwa kawai aka kyaleshi to zakaji yana wani irin tashi marar dadi har maigida yaji babu dadi,

Cure gashin tayi ta daureshi ta nufi hanyar fita, akofa sukayi kicibus da jabir yana kokarin shigowa yasha wando iya gwiwa da yar shirt dinshi bashida banbanci da samari irin yan makarantar nan,

Da sauri ta juya masa baya tayi niyyar komawa cikin dakin, a tsakiyar dakin ta tsaya tana karewa royal bed dinsa kallo wanda yake a hargutse,

Jinsa tayi ta bayanta ya rungumeta ya zagayeta da hannayenshi gamida ziro kansa ta kan kafadarta,

"Binti kin tashi?" Yafada acikin rada,

"Abbu good morning"

"Morning bintin abbu, how was your night?"

Shiru tayi tana yamutsa fuskarta,acikin ranta ta tace "too harsh"

"Binti ba zaki amsa ba?"

Jiyo da ita yayi sai ta rufe idonta sai ga hawaye sharrr sun fara zuba akan idonta,

Baki bude ya kalleta dama a banza ma tana yin kuka inaga yanzu da dalili ya samu,

"Kiyi hakuri binti kinji, nine ko? Yi hakuri"

Hadata yayi da jikinsa yafara rarrashinta har ya samu ta daina hawayen, hanmunta ya kama ya zaunar da ita akan wani dan karamin stool yaje yafara gyara mata gadon, kallonshi kawai take yanda yake da sanyin nan to komai ma nashi a sanyaye yake gudanarwa dan haka ya zame mata dole ta nemo mafita duk da tasan ba ita kadai bace mai irin wannan matsalar ba mata da dama suna fuskantarta,

Hannun nata ya sake kamawa ya rakata kan gadon ta kwanta, agefenta ya zauna ya fara jan yan yatsun kafarta, da haka ya ware ya fara yi mata tausa ajikinta, kamar wacce take jira sai bacci, zama yayi yana kallonta acikin ranshi yana tunanin irin banbancin dake tsakaninta da ummu domin yagane akwai banbance banbance masu tarin yawa bawai kasancewarta budurwa kawai ba ko a ta fannin ni'ima ni'imarta tasha banban data ummu, kodan ita bahijjan tana shan kayan marmari ne da sauran abubuwan datake hadawa da kanta,

Haka yayita yan tunane tunanensa yana zaune yana kallonta, drewar din gefen gadonshi ya bude yafara bincike har ya binciko abinda yake nema, wani dan kyakkyawan zobe ne na gold mai kyau, dan yatsanta na hagu ya kamata ya saka mata zoben, ya kwanta agefenta yana makale da hannunta,

Sun jima suna baccin kafin jabir ya tashi yana kallon bahijja wacce keta faman baccinta tana fitar da numfashi ahankali, ahankali yafara kokarin zare hannunsa daga cikin nata, yana gama zarewa ta tashi firgigit,sai kuma tafara kallonsu shida ita, sunkuyar da kanta tayi tana kallon kayan jikinta,

"Abbu kagani kayanka sunyi min yawa ko"

Murmushi jabir yayi ya matsa kusa da ita "amma ai sunyi miki kyau binti"

Kallonshi tayi tana tuna wani abu acikin ranta wanda ita kadai tasan ko me take tunawa,

"Abbu yunwa nakeji" tafada tana turo baki,

"Zakici abinci yanzun nan binti, ai nasan bakya wasa da abinci shiyasa kike da karfi sosai kusan ma kinfini karfin"

"Haba abbu wanne karfi nafika? Tayaya kasan haka alhalin nida ba dambe muka yi dakai ba"

Sakin hannunta yayi yana murmushi tare da kokarin sauka daga kan gadon yana cewa "dambe na nawa kuma binti"

Falo ya fita ya shigo mata da kayan Karin kumallon da ya shirya mata shida kansa, akasa ya ajiye mata ya kamota ya sauko da ita,

Kazar jiya taga ya dumama mata sannan ya soya mata kwai ya dan soya mata dankali da plantain, sai ruwan tea, "yau zanci girkin maza kenan" tafada aranta,

Dankalin taci da plantain din tasha tea ta tashi tana mik'a, "abbu natafi dakina sai ka taho"

Kafin ya dago yayi mata magana har takai bakin kofa hakan ya sashi yin shiru, fita tayi ta koma dakinta tana zuwa tafada gado

24 / 35