Wani Haske Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Hameedah Category :  Complete Novels

Chapter   6 / 35

15K to 18K   out of 102.7K words

fita ya nufi part din goodness, ta kofar baya ya shiga falon tsit kamar babu mai rai aciki, gabansa yaji ya fadi saboda komai a karkashe yake tun daga light din falonn har socket da fan din falon, falon yabi da kallo yana tunani aranshi mutum ma fa na iya mutuwa ba tareda an sani ba, cikin bedroom din ya nufa ya duba na farko bata ciki hakan yasa ya nufi dayan anan ya hangota kwance saman gado ta kudundune acikin bargo,karo nafarko da taji ya kira sunanta cikin sanyayyiyar voice dinshi

"Goodness" yafada a hankali amma shiru bata amsaba, sake kiran sunanta yayi nanma shiru dan haka ya matsa kan gadon yadan yaye bargon data rufa,ganinta yayi fuskara a kumbure ido yayi hulu hulu saboda kuka gashi da gani bata da lafiya sosai,

"Goodness what's wrong with you?, are you well? Are you fine?" Yafada a hankali,bata iya bashi amsa ba sai hawayen dake kwaranya daga idanuwanta suna sauka akan kumatunta, hucin zafin da ya soma jiyowa daga cikin bargon ne ya tabbatar masa da cewa zazzabi take yi ahankali ya soma yaye bargon data lulluba amma duk da bata da lafiya sosai sai da ta rike bargon saboda bata son yaga jikinta,bai kulata ba ya fusge bargon gaba daya nan ya ganta daga ita sai wata yar doguwar riga iya cinya fara mai siririn hannu wacce ta bayyanar da dukkan surar jikinta a fili gashi ko inner wears babu ajikinta, idonshi ya dauke daga kallonta yace,

"Tashi muje nakaiki asibiti,bakida lafiya shine kuma baki fada min ba why?"

Kankame jikinta tayi tana dan karkarwar sanyi ta tashi zaune da kyar ta mika hannu jikin sif dinta tafara kokarin janyo wani skirt da riga yan kanti, jiri yana dibanta ta tashi tafara kokarin saka skirt din ganin haka yasashi komawa falo ya tsaya ya jirata acan, tana gama saka riga da skirt din ta koma ta sake tukunkunewa, shiru shiru yaji bata fito ba dan haka yasake komawa cikin dakin ganinta yayi tasake kwanciya ta lulluba, fita yayi ya nufi part din ummu ya sameta tana yankewa al'amin farcensa,

"Ummu al'amin dan Allah acikin hijabanki bani guda daya aro zan kai yarinyar can asibiti bata da lafiya"

Tashi ummu tayi tana cewa "Allah ya bata lafiya bari to na dauko maka" tana fita al'amin ya kalleshi "abbu ka siyo mata chocolate itama tana shan chocolate kamar ni"

"To al'amin zan siyo mata" daidai nan ummu ta fito hannunta rikeda dogon hijabi ta mika masa tana cewa "basai an dawo min dashi ba kyauta na bata" karba yayi yafita aranshi yana ganin wannan itace mafita saboda ba zai iya fita da ita babu lullubi ba.

Lokacin da ya koma dakin nata tana nan yarda ya tafi ya barta,

"Tashi muje" ya fada yana kallonta tana lullube,

"Sir bazan iya zuwa ba jiri nakeji, ina ji kamar zan fadi idan natashi" tafada tana shesshekar kuka, tsayawa yayi yana nazari,

"Ki daure ki tashi ahankali"

"Sir bazan iya ba, i can't, since on Thursday nake kwance anan, and now karfina ya gama karewa,my body becomes so weak, i can't"

Bai jira komai ba ya yaye bargon, for the first time yasa lallausan hannunshi ya riko nata wanda duk da tana halin ciwo sai da taji wani irin feelings ya ziyarceta, shima hakan yaji amma ya daure ya tayar da ita zaune tareda mika mata dogon hijabi mai hannu, karba tayi ta saka, hannunta ya sake kamowa a karo na biyu ya mikar da ita tsaye, duhu duhu take ganin gabanta ga uban jiri dake daukarta kamar zai kayarta dole ta runtse idanuwanta saboda bata iya budesu sosai, ganin haka ya sanyashi dole karata ajikinshi yasa dayan hannunshi ya zagaya dashi ya dafe kafadarta dayan hannun nasa kuma yana rikeda hannunta har suka fito daga cikin bedroom din ta,dogon numfashi taja saboda wani irin kamshin dadi da taji yana fita daga jikinshi wanda bata taba jin irinsa ba sai yanzu data rabu da jikinsa, ahankali ta dan bude idonta ta kalli kyakkyawar face dinshi wadda yayi aski ya dan gyara sajensa da dan madaidaicin gemunsa daya tara, yau ma jallabiya ce ajikinsa kalar ruwan kasa da yar mitsitsiyar hularta baka ba karamin kyau yayi ba, "you are good looking my cool" tafada acikin zuciyarta tareda sake lumshe idanuwanta tana jin tattausan hannunsa rikeda nata.






_*Ummi A'isha*_πŸ‘ŒπŸ»
[10/28, 9:28 PM] β€ͺ+234 810 100 9022‬: [8/30, 11:07 AM] Ummi A'ishaπŸ‘ŒπŸ»: *WANI HASKE*



_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_


_37-38_


~~~ _"you are good looking my cool"_ tafada acikin zuciyarta tareda sake lumshe idanuwanta tana jin tattausan hannunsa rikeda nata, yana rikeda ita a barin jikinshi har suka fita daga cikin falonta bayan tasa takalmin ta,sake shigewa cikin jikinsa tayi har su kaje harabar tsakar gidan, ahankali take jan numfashi tana shakar daddadan kamshin turaren dake fita daga jikinsa, malam idi driver ya fara kira da sanyayyiyar muryarsa hakan yasata bude idonta ta daga kanta tabi kyakkyawar fuskarsa da kallo ta dire kallonta akan dan karamin bakinsa wanda yafi komai burgeta a tattare dashi, da gudu driver ya karaso ya je ya dauko mota daga ma'ajiyarta yazo gabansu ya tsaya, bayan motar ya bude mata ta shiga shima ya zagaya daya barin ya shiga ya zauna ya kalli malam idi driver a hankali yace asibitin da nake kai al'amin zaka kaimu, nan da nan driver yaja suka fita, duk abun nan da yafaru ya farune akan idon ummu al'amin wacce ta tsaya ajikin window dan ganin abinda zai faru, tunani ta fara yi acikin zuciyarta to ko har amaryar ta fara laulayi ne? Sakin labulen window din tayi ta koma kan kujera ta zauna, to amma ai shi Abu al'amin bashida yawan bukatar mace asalima koda ya bukaceta to baya wuce minti 20 yayi abinda zaiyi ya gama, sannan wani lokacin ya kan shafe fiye da sati 6 bai bukaci mace ba, tabe baki tayi "koma dai menene su suka sani" tafada a hankali.


Lokacin da su goodness suka nufi asibitin jingina kanta tayi ajikin kujerar motar idanuwanta arufe amma babu abinda take gani sai kyakkyawar fuskar mal jabir ahankali ta bude idonta ta juya ta dan kalleshi idanuwansa tar akan wayar hannunsa yana lallatsawa sake mayar da idonta tayi ta lumshesu har suka isa asibitin, bayan motar ta tsayane ya fito yazo ya bude kofar barin da take ya mika mata hannu ahankali ta mika nata ta kama nasa ta zuro kafafunta ta fito, dan kallonta yayi asace babu laifi hijabin da tasa yayi mata kyau sannan ya fito da round face dinta sosai, kamar dazu haka ya karata agefen jikinsa suka shiga cikin clinic din, a reception ya ajiyeta ya karasa wurin da ake bude folder, bayan ya gama bude mata folder dinne ya koma inda take zaune tana ta kallon masu shige da fice amma kuma jikinta kamar wuta yake dan kuna,

Ba tareda yayi mata magana ba ya dagota tsaye suka nufi wani office inda za adubata suna shiga likita ya fara checking dinta tareda yi mata yan tambayoyi anan yake tambayarta yaushe rabonta da abinci tace kwana 3,cikin sauri mal jabir ya kalleta ransa ya dan sosu domin hakkinsa ne na tabbatar da yanda al'amuranta ke gudana acikin gidansa, fada doctor ya fara yi akan danme zata zauna bata ci abinci ba alhalin kuma tana cikin yanayi na rashin lafiya,jikinta doctor din ya taba yaji yayi laushi dan haka yace gado za abata saboda sai anyi mata karin ruwa, female ward aka kaita aka jona mata karin ruwa, reception mal jabir ya koma ya fara kai kawo lallai abinda yayi bai kyauta ba sannan ai bai ma kamata yaga laifin goodness ba tunda ba itace takai kanta ba takanas mahaifiyarta ta biyota gidan domin yi mata addu'ar, wata faduwar gabace ta sameshi domin tunowa da wani hadisi da yayi wanda annabin rahma, annabi Muhammad (s.a.w) yake cewa _"dukkaninku masu kiwone, kowa za a tambayeshi dangane da kiwon da aka bashi, shugaba mai kiwone akan jama'arsa, mai gida mai kiwone akan iyalansa sannan mace itama mai kiwoce akan al'amuran cikin gidanta"_ tabbas yasan duk da cewa goodness ba musulma bace to tana da wasu hakkoki akansa wanda har yanzu ya kasa saukesu.


Awarsu uku acikin asibitin sai da aka kara mata ruwa leda biyu sannan aka sallamesu bayan an hado mata magunguna kaya guda, hannunsa rike da nata ya sata acikin mota suka nufi hanyar gida, maganar al'amin ce ta fado masa _"abbu ka siya mata chocolate itama tana shan chocolate kamar ni"_ gyaran murya yayi yace da driver ya biya dasu ta super market, wani sabon super market suka je da kansa ya shiga ya kwaso mata chocolates kala kala da sauran tarkacen kayan zaki sannan ya siyo mata take away ya dawo cikin motar inda take jingine idanuwanta arufe.

Mintuna kadan suka karasa gida, kayan da ya siyo mata ya debo tareda riko hannunta suka shiga falonta.

Akan kujera ya zaunar da ita ya ajiye ledojin dake hannunsa ya dan kalleta kasa kasa idanuwanta a lumshe ta jingina kanta ajikin kujerar da take zaune agaskiya kyakkyawa ce ta karshe kawai matsalar dan ba musulma bace shiyasa ya kasa ganin kyawun nata amma dan kyau tana da kyau na asali,

"Kici abincin sai kisha magani kin ji doctor yace ki daina zama da yunwa" yafada cikin cool voice dinshi,

"Ok thank you" tafada har lokacin idanuwanta a lumshe suke,

"Ina zuwa" yafada tareda juyawa ya fita, idonta ta bude tabi bayansa da kallo har ya fice daga cikin falon, zamewa tayi ta kwanta akan doguwar kujerar tareda lumshe idanuwanta.

Yana fita part din ummu al'amin ya shiga, samunta yayi tana shirya al'amin da alama wanka tayi masa, yar karamar jallabiya ta yara fara ta saka masa tareda fesa masa turare,

"Ummu idan kin gama abunda kikeyi kije ki duba yarinyar can ashe bata da lafiya sosai bamu sani ba" ya fada yana shafa kan al'amin,

"Allah sarki, to bari nagama naje, Allah ya bata lafiya" tafada tana gyarawa al'amin wuyar rigarsa, dagudu al'amin ya fita ya nufi part din goodness, yana fita ta kamo hannun sa ta rike cikin nata,

"Meke damunta? Ko laulayi ne?"

Kai ya girgiza mata "bana tunanin haka kawai zazzabi ne ke damunta, bari naje nayi alwala naga lokacin salla ya kusa"

Sakin hannunsa tayi tana murmushi "to adawo lafiya" fita yayi daga sashen ummu ya nufi nasa.

Da gudu al'amin ya shiga falon goodness lokacin tana nan a kwance kamar yadda take dazu, ganinsa yasata tashi zaune ta cire hijabin jikinta tana murmushi,

_"sannu anty, yas'alul lahil azim, rabbul arshil azim an yashfiki"_ yafada tareda zama akusa da ita,

"Al'amin who taught you this?" Tafada tana jansa jikinta,

"Anty abbu nane ya koya min, itace addu'ar da ake yiwa marar lafiya, indai mutum bashida lafiya aka yi masa wannan addu'ar to yana samun lafiya da izinin Allah"

_"thank you soo much my dear son, my God bless your life"_

Zaune ta tashi ta janyo ledojin da mal jabir ya ajiye mata ta ciro take away ta ajiye a tsakiyarsu itada al'amin,

_"oya chop"_ ta mika masa spoon, girgiza kai yayi,

"Alhamdulillah Anty, nakoshi"

"To ungo ledar chocolate maza dauki kayita sha kaji good boy"

Chocolate din ya dauka ya fara sha yana kallonta, hannun hagu tasa tafara cin abincin da spoon, cikin sauri ya rike hannunta,

"Anty bakiyi bismillah ba kuma kin sa hannun hagu"

Mayar da cokalin tayi hannun damanta ta kalleshi "al'amin kenan waye yace maka ba acin abinci da left hand?"

"Abbu nane kullum kullum idan zanci abinci sai yace min sai nayi bisimillah kuma kar naci da hannun hagu saboda akwai wani sahabi da yake cin abinci tareda annabi lokacin sahabin yana dan yaro sai annabi yake cemasa yakai yaro ka ambaci Allah, kaci da damanka sannan kaci gabanka"

Murmushi tayi _"wow al'amin you are such a brilliant boy and talent,komai naka irin na mahaifinka ne like father like son, you take after your father, wow this is wonderful thing oh oh, oya ci gaba da bani labari kana shan chocolate"_

Kafin yayi magana ummu ta bude kofa ta shigo idonta akansu domin ta dade a bakin kofar falon tana sauraren hirar da suke yi.

Cikin murmushi ta karasa ta zauna tana kallonsu,

"Uwa da d'a" ummu tafada tana murmushi,

_"welcome anty"_ goodness ta fada itama tana murmushin domin yaune rana ta farko da fara ganin ummun duk zamanta agidan domin bata samu fuskar shiga wurin kowa ba agidan asalima bata taba shiga wani wuri baya ga part dinta ba acikin gidan,

"Sannu ashe bakida lafiya, ayya sorry" ummu ta fada tana kallonta domin yanzu ta danji sassaucin tsanar da tayi mata acikin ranta saboda ta fuskanci tana son danta al'amin sosai kun san kuma bahaushe yace uwar d'a mahaukaciya ce duk mai kaunar danta to itama tana kaunarsa,

"Thank you anty, nagode nagode"

Mikewa ummu tayi "Allah ya kara sauki,bari nakoma saboda inada aiki"

"Ayya anty come and chop please" goodness tafada tana mika mata abincin gabanta,

"No thank you am ok" ummu tafada tareda juyawa tafita, har bakin kofa goodness ta rakata sannan ta dawo wurin al'amin dake zaune yanata bare chocolate yana sha dan yasha akalla zata kai guda goma, zama tayi kusa dashi tana kallonsa,yaron komai nasa irin na abbunshi ne amma yafi babanshi surutu sosai amma baya ga haka kamarsu daya sannan wani abun burgewar ma ya dauko halayyar abbun nashi,

_"my boy don't full your stomach with this zak'i zak'i"_

Dagowa yayi ya kalleta "anty ai ban koshi ba kuma kece kikace nayita sha har na koshi"

Dariya tafara yi harda rike ciki "oh dama so kake sai ka koshi sannan zaka bar shan chocolate din?"

"Na'am anty" ya bata amsa yana murmushi tareda bude manyan idanuwansa irin na mahaifinshi yana shirin sake wata maganar abbunshi ya bude kofa ya shigo,

Tsumu goodness tayi tareda saurin sunkuyar da kanta kasa, kallonta ya danyi ya kalli al'amin wanda shima shi din yake kallo,

"Al'amin lokacin salla yayi maza tashi kaje kayi alwala kazo muje masallaci"

"To abbu" al'amin ya fada tareda tashi da gudu ya fita, yana fita ya jiyo ya kalleta har lokacin kanta a sunkuye yake tana kallon abincin dake gabanta gashi ta kasa ci gaba da cin abincin, duk jikinta jinsa take ya takure,

"Kinsha maganin?" Ya tambayeta a hankali,

"No, yanzu zansha idan nagama cin abinci" ta bashi amsa

"Ki tabbatar dai kinsha kar kiyi wasa da wannan magungunan, Allah ya kara sauki" yana kaiwa nan ya juya ya fita, lokacin al'amin har ya fito daga part din ummu ya iyo alwala.

Bayan fitarshi ta saki ajiyar zuciya "hmmmm i like u my cool" tafada ahankali tareda tashi tsaye ta kalli window nan ta hangoshi yana rikeda hannun al'amin suna kokarin fita, sai yanzu ta samu damar kallonsa domin dazu da ya shigo kasa kallonsa tayi, ya sake wanka ya sake jallabiyar jikinsa daga kalar ruwan kasa zuwa kalar ruwan madara da yar karamar hula itama ruwan madara, ayanda ta lura bai fiya saka kananan kaya ba daga jallabiya sai manyan kaya amma duk da haka bai hana kyawunsa fitowa ba, komawa tayi ta zauna bayan taga fitarsu, yanzu fes take jinta saboda taga alamun ya huce ya daina fushin da ita dama kuma ciwonta yanada alaka da fushinsa, abincin ta kammala ci tasha magani ta tashi ta shiga bedroom dinta ta kwanta, kamshin turarensa take ta ji ajikinta tamkar itace ta fesa turaren ajikinta, rigarta ta sinsina har yanzu kamshin yana nan kamar yanzu ne ya jinginata a jikinsa.

Wayarta ta dauka ta kira anty Bilkisu suka gaisa sannan ta kira babanta shima ta gaisheshi, gabanta yana faduwa ta kira ma domin itama ta gaisheta, dakyar ma ta daga wayar cikin fada tace

_"goodness kin daina zuwa church ne? Rabonki da church kin jima ko kin canja addini ne?"_

"No ma, banida lafiya ma yanzune na samu sauki amma may be gobe zan zo tunda gobe sunday"

Kwafa ma tayi cikin bacin rai tace,

_"thank you goodness for what your husband have done to me last time, but i want remind u,you promised me that you will not change and fellow his religion, dan haka ina mai gargadinki be very carefull with him, kar ki bari ya yaudareki ya jaki cikin addininsa"_

"Am so sorry ma about what he has done, sannan ma tun jimawa nafada miki son da nake yi masa bazai saka na bi addininsa ba, kiyi hakuri ma it will neva happen again"

"Don't worry my daughter its pass, but you make sure gobe kin zo church kinji"

"Zanzo ma, thank you my sweet mother"

Kashe wayar tayi tana murmushi aranta tana tunanin hali irin na ma, ita dai a duniya bata son addininsu abbun al'amin, da wannan tunanin bacci ya dauketa.

Har yamma tana bacci bata tashi ba, lokacin da mal jabir da al'amin suka dawo daga masallacin ma bacci take, hannun al'amin ya saki ya nufi part din goodness shikuma al'amin ya nufi wurin ummunshi, yana shiga falon yaga bata ciki amma ga su chocolate dinnan da tasha ita da al'amin duk a barbaje, girgiza kai yayi ya danyi murmushi,"ita da al'amin din banbancinsu kadan ne domin itama yarinya ce" yafada acikin zuciyarta, dakinta ya leka tana kwance tana bacci duk ta hada gumi daga gani zazzabin ya saketa, _air condition_ ya kunna mata ya juya ya fita ya nufi sashensa.

Sai wurin karfe shida sannan goodness ta tashi daga baccin da take yi, wanka ta shiga tayi ta fito ta saka wata riga da wando dukkansu jajaye yan kanti _cotton_ masu laushi, falonta taje ta gyara aranta tana jin dadin yanda yanzu abu al'amin ya sauya mata yake bata kulawa, tv ta kunna ta jona DVD ta kunna wakar d banj cikin wakarsa ta _"my woman my everything"_ wani farin ciki yau take ji domin ko wanne lokaci idan ta rufe idonta hangota take yi rungume agefen jikin mal jabir _"my man my everything"_ tafada ta hanyar sauya salon wakar da take ji, nan taci gaba da al'amuranta.

Misalin karfe _8:30_ ya shigo gidan hannunsa rikeda na al'amin yakaishi sashen ummu sannan ya shiga nasa part din tun da yashiga falo yaji sautin kida yana tashi kasa kasa, "sauki ya samu kenan tunda naji haka" yafada tareda ajiye littafin da ya shigo dashi na adabul mufrad sannan ya shige cikin dakinsa, ta window ya hangota acikin kitchen dinta tana aiki wanda bazai iya fahimtar abunda take yi ba amma

6 / 35