Wani Haske Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Hameedah Category :  Complete Novels

Chapter   4 / 35

9K to 12K   out of 102.7K words

ba ashe wurin malam kaje"

Kai ya daga mata "malam ne ya kirani sai nadawo zanyi miki bayanin abunda muka tattauna dashi"

"To adawo lafiya abu al'amin"

Tare suka fito ya shiga falonta yana kiran al'amin domin yazo su tafi masallaci.

Bayan idar da salla zama yayi yafara dorawa mutane karatu kan littafin da suke karantawa ako wacce rana mai suna adabul mufrad, har lokacin sallar isha yayi bayan sun idar da salla ne ya dauko al'amin a kafadar shi ya shiga cikin gida mai gadi ya mayar da kofa ya rufe.

Dakin ummu ya nufa acan ya sameta zaune kan abin salla tana karatun alqur'ani mai girma, gefen gadonta yaje ya kwantar da al'amin ya juya ya fita ya shiga sashensa, abincin ya zauna ya fara ci har ummu ta shigo cikin kyakkyawar shiga ta sanya hijabi babba mai hannu,

"Yau baka samu kaci abinci da wuri ba" tafada tana murmushi,

"Eh wlh dan ban dawo da wuri bane" ya fada cikin muryarshi mai dankaren sanyi,

"Naji kace zaka yi min bayani Allah dai yasa lafiya"

Abincin gabanshi ya ture ya juya ya fuskanceta,

"Lafiya lau, maganar aure ne wanda zanyi"

Kallonsa tayi da sauri amma tasan tunda ya fada dagaske yake saboda baya yi mata irin wannan maganar,

"Aure Abu al'amin? Yaushe? Meya faru?"

Girgiza mata kai yayi 'ban san dai nan da yaushe bane sai abinda malam yace"

Wani bacin rai taji ya fara mamayar zuciyarta, take fuskarta ta sauya ranta ya baci ta mike tsaye,

"Asshhha! Da ace mutane sun san halayenka to da basu zauna sun bata lokacinsu sun saurari wa'azinka ba, kullum kana yiwa mutane wa'azi amma kai kuma Baka yiwa kanka, me nayi maka da kake son sai kayi min kishiya?"

Tsaye shima ya mike "haba Salma akan kawai nace miki zanyi aure shine zaki jefeni da wadannan kalmomin, ubangiji ne fa ya bani damar auren mace fiyeda guda daya acikin suratul nisa'i aya ta uku, yace mun halarta muku ku auri abinda yayi muku dadi daga mataye.......!"

Katseshi tayi da sauri, "ya isa, sarkin wa'azi ni ba aya nace ka jawo min ba, Allah yabaka ikon yin adalci kawai"

Tana kaiwa nan ta juya ta fita tanufi dakinta tana sharar kwalla,shi kam tatafi ta barshi da mamaki karara akan fuskarshi lallai mata akan kishiya basu da dama, ko sun san abu sai su take yanzu duk ilimi irin na Salma akan kishiya tana neman birkicewa.

***

A bangaren goodness kuwa tun ranar da sukaje wurin mahaifin GM ita da nura bata sake komawa office ba saboda yanzu bata son taje ko GM yasan itace itace wacce take son ya aureta,

Dawowarsu kenan daga church itada ma ta tarar da labari mai dadi cewar GM sun zo shida mahaifinsa wurin babanta zuruf ma ta mike

"Papa goodness ban gane abinda kakeso kayi ba, kana son goodness ta auri musulmi hausa man saboda addininku daya?"

"Ma ba laifin baba bane, nice nake sonshi wlh ma yanada kirki"

"Shut up, poor girl, idan ya sakeki ko yayi miki kishiya kar ki kuskura kizo min nan gidan" ma tafada tana zazzaro ido,

Shidai mahaifinta bai ce komai ba domin yana cikeda tsantsar farin ciki domin yasan insha Allahu goodness ta kusa samun rahamar ubangiji,

"Ko kin auri hausa man to ba zaki yi addininsu ba,and papa goodness kasan dai wannan bikin a church za muyishi ko?"

Ba goodness ba hatta mahaifinta sai da maganar ta girgizashi.

Cikin kidima goodness take kallon mamanta kafin mahaifinta ya bada amsa "kiyi bikinki a church nikuma nayi nawa a nan shikenan?"

"Yawwa haka yayi dai dai saboda zan kaita church pastor yayi mata addu'a" tana dasa aya ta tashi ta karasa dakinta, nan baban goodness ya shiga yi mata nasiha da yanda zata zauna da mijinta lafiya sannan ya gargadeta da kiyaye daukar hudubar mamanta domin bikinta nan da sati shida za ayi tunda GM babban mutum ne ba shirme za a tsaya yi ba, wani sanyi ne ya mamaye ruhinta amma bata nuna ba a lokacin har sai da ta tashi ta shiga dakinta ta fada kan katifarta tana murna ta kira nura tana fada masa anan yake sanar da ita ai shine ya jagoranci su GM din har zuwa gidansu kuma yanzu GM yasan itace wacce zai aura saboda har yayi masa maganar cewa ya sake nemo masa wanda zai ci gaba da aikinta a office, tashi zaune tayi tace

"Heyyy nura don't bring female i beg you, ka samo masa namiji"

Dariya nura yayi tareda kashe wayar, wani irin son GM taji yana azazzalarta tana son taji sanyayyiyar muryar nan tashi nan ta tuna da cewar tana da tsohon layi a ajiye na zain, da sauri ta bincikoshi tasa a wayarta ta fara kiran layinshi, sai daf da zata tsinke sannan ya dauka yayi sallama, shiru tayi tana sauraren muryarsa, wata sallamar ya sake yi nanma tayi shiru har sai da yayi sallama sau uku babu amsa hakan yasashi katse wayar, wata ajiyar zuciya ta saki tana mai muradin ganin ranar aurenta da GM.

Acan gidan GM kuwa Ummu al'amin ta dan sauko kadan amma fa ba hakura tayi ba zuciyarta ce kawai ta bata shawarar ta nunawa abu al'amin cewar ta hakura ta yarda yayi aurenshi amma kuma zata rinka yi musu zagon kasa shida amaryar, hakan yasata yin dariyar mugunta ta tashi ta nufi sashensa wanda yake kusa da nata, acan cikin dakinsa ta sameshi yana duba wani littafi na tafsirin suratul hud, da sallama ta shiga ta zauna kusa dashi gamida riko hannunsa, littafin ya rufe ya jiyo yana kallonta "ummu ya akayi"

"Abu al'amin kayi hakuri da abinda nayi maka akan maganar aurenka hakika nasan kai adali ne kawai sharrin shaidan ne yasa na fada maka wannan maganar amma kayi hakuri, Allah ya baka ikon yin adalci a tsakaninmu"

Hancinta yaja yace "ya wuce ummu kidaina bani hakuri, nasan kishiya tana da zafi awurinku mata amma haka zaku daure ku rinka karbarta aduk yanayin da tazo muku"

Jikinshi ta shiga tana murmushin kissa.

***

Tunda biki ya rage saura sati uku mahaifin goodness ya kirawo yayarta anty bilkisu tazo yaje ya ciro yan kudadensa da ya jima yana tarawa saboda auren goodness ya basu yace suje kasuwa su iyo mata siyayyar kayan kitchen domin GM yace kayan daki da sauran tarkace ba sai an kawo mata ba zai zuba komai murna wurin anty bilki harda kuka saboda jin wanda yar uwarta zata aura,tabbas tasan goodness tana daf da samun *WANI HASKE* acikin rayuwarta wadda zai yi sanadiyyar haska danginsu baki daya, nan aka shiga gudanar da shirye shiryen biki mama ta shirya ta tafi okene domin yin tsubbuce tsubbucenta tareda tahowa da dangi, amma har yanzu goodness da GM basu haduba sai lokaci zuwa lokaci goodness tana kiransa da layin zain dinsa tayi shiru tana sauraren muryarsa,

Kudi kimanin naira dubu dari uku GM ya aiko dashi akan ayi komai da komai domin shidai ba bidi'a zaiyi ba wannan kudin da zai aiko dashi za ayi mata duk wata hidima data kamata, tsalle da murna wurin goodness ba a iya musaltawa, anty bilki kuwa sai gyara yar kanwarta take saboda shirin kota kwana sannan sun shiga kasuwa sun jido kaya hadaddu sabbi english wears akwati biyu dogayen riguna ne yan kanti sai riguna da wanduna da skirts da sleeping dress da inner wears domin goodness bata iya saka atamfa ko leshi ba, ma sai da biki ya rage saura sati daya ta dawo ita da mutanensu daga okene tana dawowa gida ya kancame da danginsu ko ina agidan ka juya wani yare suke yi wanda nidai ummi A'isha bana fahimtar sa.

Tunda ma tadawo kullum sai sunje church anyiwa goodness addu'a da haka har ranar bikin tazo ranar a church suka kwana anata addu'o'i, washe gari ranar friday aka daura auren goodness da GM bayan an idar da sallar juma'a a masallacin mahaifin GM, ana gama daura auren ya koma gida yana sanye da farin yadi mai laushi da kyau, da gudu al'amin yazo yana bashi labari

"Abbu wancan gidan wasu sunzo sunje sunata shara aciki abbu, abbu makotan munne?"

Hannunsa ya kama yana murmushi "al'amin surutu, eh makotanmu ne"

"To abbu wasu fa basuda hijabi irin na ummu na"

Ras gabanshi ya fadi shi sai yanzu ma ya tuna da cewar fa ashe ba musulma ya aura ba, "al'amin ya isa haka kayi shiru babu kyau yawan magana"
Yafada tareda jan hannunshi zuwa sashensa.

Biki yayi biki domin ma ta cashe iya cashewa a church yayinda goodness kuma taci ado cikin wedding gown fara gashi anyi mata gyaran gashi tasha attach mai kyau, kafarta da hannayenta duk an gyara mata, musamman ma ta kaita aka yi mata gyaran fuska, su gyaran gira ne duk sai da aka yi mata fuskarta tasha make up tayi kyau har ta gaji, kasancewar a church zasu gudanar da bikin yasa anty bilki ta bisu a dole amma indai bata manta ba rabonta da church tun tana yar mitsitsiya lokacin da ma take zuwa da ita.

Church din an kawatashi da decoration yasha balam balam balloons manya manya kala kala, goodness tana tsugunne gaban pastor ta rufe idonta sauran jama'ar kuma suna zazzaune suna sauraren pastor ciki harda promise tsohon saurayin goodness wanda yaketa dariyar mugunta ganin mijin goodness bai zo church ba,zobuna guda biyu aka mikowa pastor (wedding ring) ya karba,zubunan masu kyau daya na gold daya na silver, na gold din goodness ta saka a dan yatsanta na tsakiya wato marriage, dayan zoben kuma akace na mijinta ne lallai lallai ta bashi yasa, tafi aka hau yi da ihu shikenan aure ya kullu nan aka shiga ihu aka saki kida ma tafito tana rawa kamar zata karye, sai around 3 suka baro church suka dawo gida, nan baban goodness ya kirata dakinsa yayi mata fada akan kar tace zata rinka biyewa ma bayan aurenta domin tana iya kashe mata aure, sannan su shirya anjima da daddare za akaita gidan mijinta, dai dai nan ma tashigo cikin dakin,

"Ah papa goodness whats are you talking about? Akai goodness yau without pastor visit her house and pray? Za akaita gidanta batare da pastor yaje yayi mata addu'a ba?"

Cikin fushi Baban goodness ya mike "ke chioma nafara gajiya da wannan rashin mutuncin naki, akanme pastor zaije gidanta? Ko kin san waye mijinta kuwa? Kina so ya saketa ne tun kafin akaita gidan? Kince wannan na yarda kince wannan nayarda to yanzu kam i won't accept this nonsense, i can't tolerate your nonsense, tun yaushe kuke addu'ar? Duk wacce kukayi bata isheku ba sai kun je gidanta kun kashe mata aure? It can't, impossible" yafada yana huci,wani ihu mama ta kurma ta dora hannu aka tana kuka,

"Oh chineke,papa goodness what do yo mean? You mean you can't allow pastor to visit goodness house to pray? Oh people, people pls come and aid me, oh God, chineke" tashi goodness tayi ta rike ma tana bata hakuri "oh ma, pls stop saying this, am sorry ma, kinji maganar da papa yafada idan kunje zai sakeni, kiyi hakuri ma, pls and pls"

Shiru ma tayi tareda share hawayen fuskarta "that's the reason why i have neva like your marriage with hausa man, i know there is too much crises around it, tun kina yar karama naso ki auri Christian wanda zakiyi rayuwar jin dadi amma see my dream didn't come true,my ambition for you to became a pastor's wife will neva Eva been....!" Tasake rushewa da kuka, nan anty Bilkisu ta shigo tana tambayar meya faru, haduwa sukayi suka cigaba da bawa ma hakuri amma dakyar ta hakura sannan aranta ta dauki aniyar ko bayan bikinne sai sunje da pastor gidan yayi addu'a.

Bayan magrib aka fara shirye shiryen kai amarya GM ya turo musu motoci guda hudu amma ma karfi da yaji ta hana goodness shiga daya daga cikin motocin sai wacce pastor ya kawo wacce tasha decoration tasha balloons ita ma ta saka goodness aciki itama ta shiga suka tafi, tunda akaje gidan kowa yake santi domin gidan ya tsaru yayi kyau sosai kai in banda rabo ma to da goodness ko a mafarki ba zata samu wannan mijin da wannan gidan ba to bahaushe yace rabo sai mai shi, kowa ya yaba wannan gidan, sashenta daban kuma shine na karshe, kayan funitures din da ya zuba mata ba na wasa bane kayane masu shegen kyau da tsada, babban falo guda daya da bedrooms guda biyu, sai kitchen da dining area, abin dai gwanin sha'awa komai green, nan ma ta shiga rawa harda guda, sun dade agidan suna ganin tsarin gidan sannan suka tafi suka bar goodness wanda take kuka biyu, na dadi da farin ciki.


Ko wanne irin zama za ayi tsakanin goodness da Abu al'amin? Mu saurari shafi na gaba.



_*Ummi A'isha*_πŸ‘ŒπŸ»
[10/28, 9:27 PM] β€ͺ+234 810 100 9022‬: [8/24, 10:31 PM] Ummi A'ishaπŸ‘ŒπŸ»: *WANI HASKE*

_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_

_31-32_



~~~ Bayan kowa ya tafi an bar iya goodness acikin dakinne ta mike gamida tattare doguwar gown din dake jikinta wacce ta kasance light blue da adon _flowers_ pink colour ajiki, tashi tayi ta fara zagaya dakunan da suka kasance mallakinta,

Kamar a mafarki take ganin abubuwan da suke faruwa, wai yau itace ta zama matar GM mutumin da yafi karfin ajinta, falo ta fita wanda girmansa kadai abin kallone yasha kayan alatun more rayuwa an zuba komai green, dayan dakin ta shiga shima ciki yana dauke da dan madaidaicin gado shima komai naciki kalarshi green, fitowa tayi ta shiga kitchen, kitchen din ya tsaru kamar a kasar turai ga kayan amfani nan birjik masu amfani da wutar lantarki,

"Thank you God" ta fada tareda runtse idanuwanta nan take hawayen farin ciki suka fara sauka akan kumatunta, wani sanyi taji yana ratsa babban dan yatsan kafarta yana haurawa cikin kwakwalwarta,

Cikin dakinta ta koma ta zauna akan gadonta tana tunanin yadda zata iya hada idanuwa da GM a matsayin mijin aurenta,tana nan zaune har taji bacci ya fara barazanar dauketa domin agajiye take lis gashi kwana biyun nan kullum a church suke kwana dan haka basa samun damar yin bacci, ko gown din jikinta bata cire ba haka ta matsa can tsakiyar gadonta taja pillow ta dora kanta ta kwanta take bacci yace muje zuwa.

A bangaren angon kuwa daidai lokacin da ya jiyo hayaniyar yan kawo amaryar yana zaune a cikin falonshi al'amin yana kwance akan cinyarshi yana koya masa wani littafin hadisi na fawakiha kusan duk hadisan dake ciki saukaka ne kuma gajeru basuda tsayi,jin al'amin yayi shiru ya tabbatar masa da cewar yayi bacci daukeshi yayi ya kwantar dashi akan doguwar kujera ya tafi jikin window ya daga labule ya fara hangen yan kawo amaryar,

Baya iya gano amaryar domin an kakkareta sai dai yana hango sauran matan wadanda duk cikinsu mace daya ce mai lullubi ajikinta, yana nan tsaye har suka shiga part din nata suka fito suka tafi daidai lokacin ummu al'amin ta shigo falon tana cewa,

"Bari na dauki al'amin saboda naga amaryar ta iso tun dazu, Abu al'amin Allah ya baku zaman lafiya"

Danta ta dauka ta saba a kafada ta fice acikin falon ba tareda ta jira amsarshi ba, idan da sabo ta saba da wannan halin nashi na rashin mayar da amsa shi komai wahala yake masa domin bashida zafi ko kadan sanyinsa yayi yawa,

Tana fita ya shiga dakinsa ya shige toilet ya yi wanka ya fito ya hau kan gadonshi ya kwanta yana tunani acikin zuciyarshi,

"Ya dace naje na kwana a dakin yarinyar nan to amma ni bazan iya ba saboda inada kyankyami shiyasa tun farko banyi murna da auren nan ba, tayaya zan auri macen da idan na kusanceta ba zatayi wanka ba, idan tayi period tagama ba zata yi wanka ba, idan tayi fitsari ba lallai ne tayi tsarki ba"

Yafada acikin zuciyarshi duk kuwa da yasan cewa tana da wani babban hakki akansa, kwanciyarshi yayi tareda yin baccinshi, sadaf sadaf ummu al'amin ta leko cikin dakin nasa ta window dinshi ta hangoshi yana bacci a hankali ta sulale ta koma side dinta dama tun lokacin data kwantar da al'amin ta dawo ta labe tana son taga fitarshi amma sai taji shiru wannan ya bata tabbacin cewa bazaije dakin amaryar ba yau.

***

Washe gari da safe misalin karfe 9 goodness ta farka daga naunauyan baccin da tayi ta bi dakinta da kallo da alamun babu wanda ya shigo, taba baki tayi ta mike ta cire gown din jikinta ta daura towel ta shiga bathroom wanda shima ya tsaru kamar ba bayi ba, wanka tayi ta fito tazo ta shirya ta saka jeans da t shirt, jeans din blue rigar kuma pink mai gajeren hannu an zana cartoon guda biyu ajiki an rubuta _don't tell my momy_ turaren rocking girl tayi amfani dashi ta dauki wayarta ta fita falo anan ta fara kokarin hada kayan kallonta ta jojjona komai ta kamo wata channel ta music vox Africa sannan channel din suna saka Nigerian films, wakar p square ta fara saurare cikin wakarsa ta _you are my African queen_ volume ta kara yadda zata rinka jiyowa har a kitchen, tashi tayi ta shiga kitchen ta kunna electric stove ta dora ruwan zafi, kamshin turarensa kawai ta jiyo taji ta rikice tuni zuciyarta ta fara harbawa da karfi numfashinta ya ci gaba da fita da sauri da sauri,

Cikin diriricewa ta nufo kofar kitchen din ta leko yana tsaye ya bawa kofar kitchen din baya yasha farin yadi mai santsi da bakar hula hannunshi rikeda remote yana rage volume din data kure,

Tamkar marar gaskiya ta karaso cikin falon, cikin faduwar gaba tace,

"Good morning sir"

Batare da ya jiyo ya kalleta ba ya amsa gamida ajiye remote din yace "akwai abinda kike da bukata?"

"No sir, but banida brush da maclean" tafada muryarta tana rawa,

"Ok za akawo miki" yana kaiwa nan yayi gaba abinshi ba tareda ya jiyo ba kallo tabi bayanshi dashi tana murmushi har yafice, cikin kitchen ta koma tana murmushi amma har lokacin gabanta bai daina faduwa ba, ruwan zafin data dora ta tarar da ya kusa konewa saura kadan, saukewa tayi ta debo acikin cup komai na bukata gashi nan acikin wani dan karamin store, kayan tea ta debo ta koma falo ta hada tea din ta fara kurba tana yi tana kallon wani Nigerian film mai suna _love avenge_ nutsuwa tayi taci gaba da kallon film din har ta

4 / 35