Wani Haske Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Hameedah Category :  Complete Novels

Chapter   30 / 35

87K to 90K   out of 102.7K words

taje tafara suya dama ita indai abin soyawa ne to tana daga tsaye take cinye kayanta,

Tana suya tana ci har taji ta koshi, sauran ta diba ta ajiyewa jabir wanda yana can a office yana aiki amma lokaci zuwa lokaci yana kiranta awaya yaji halin da take ciki,

Koda ya dawo gida kuwa rigima ta saka masa ita tuwo take so kuma tuwon ma na dawa miyar kuka,

Ido ya zuba mata yana kallonta, "binti tuwo?"

"Ehh abbu, wallahi yunwa nakeji"

Daukarta yayi suka tafi gidan malam amma acan dinma babu tuwon dawar sai na masara dakyar aka samo mata ma makwafta suka dawo gida.


Da safe kuwa bata barshi yayi baccin safeba tashinsa taje tafara yi,

Kansa ta hau ta zauna tafara jijjigashi,

"Abbu katashi muje ka fafe min gwangwani yau alala zanci"

Bude idonshi yayi ya riketa, "alale zakuci yau binti?"

Kai ta daga "ehh abbu yau alale zanci"

"Za kuci dai keda babynki"

Tashi yayi suka fita tare zuwa corridor dinta inda ta tara masa gwangwaneyen peak kanana,

"Binti meyasa ba zakiyi na leda ba yafi sauki wannan wahalar da kanki zakiyi"

"Abbu nidai bana son na leda, wallahi na gwangwani nake so" ashagwabe tayi maganar gashi ta rakwarkwabe fuska tana shirin yimasa kuka,

"To ya isa kar kiyi kuka zan fafe miki"

Zama yayi yafara fafe mata yana jin tausayinta har acikin ransa domin yanzu ita abar tausayice saboda lalurar da take dauke da ita na juna biyun dake jikinta, shiyasa kullum yake bata abinda take so kuma ako wanne lokaci cikin bata kulawa yake dai dai da rana daya bai taba jin ya gaji da yarintarta ko kuma shirmenta ba domin yasan har yanzu ita yarinyace saboda shekarunta har yau ba zasu wuce 25 ba kuma a ka'ida mata basa yin hankali na hakika har sai sunkai 35 alokacinne suke tantance baki da fari shiyasa ma acikin alqur'ani Allah ya ambaci matan aljanna wato hurul aini da cewar matasane masu hankali malamai sunce anan ana nufin yan shekara 35 ne, koma dai menene dama dole miji sai yana yin hakuri da matarsa saboda hankalinsu da nutsuwarsu ba daya bace,

Yanata yan tunane tunanenshi yana fafe mata gwangwanin ita kuma tana gyara wakenta domin akai mata markade,

"Abbu yanzu fa nan da shekaru 20 kazama tsoho ko" tafada tana dariya,

"Ai maza basa tsufa binti kece dai kika tsufa lokacin, nikuma lokacin zan auro yarinya Yar 18"

Waken ta bari ta koma kusa dashi "abbu dagaske kake yi?"

Kallonta yayi yanda duk ta rirrikeshi ta cukwikuyeshi tana kallonsa tareda hayewa jikinshi,

"Dagaske mana" yabata amsa yana tara mata gwangwanayen wuri guda, babu zato yaji tasaka masa kuka,

"Kai binti ai lokacin kema fa kin girma kilama kinyi auren babbar yarki"

Kukan ta daina ta rufe fuskarta, "kuma dan nayi auren yata shine zaka auro min sa'arta?"

"Ehh mana ai hakan yafi lada" yafada yana janye hannuwanta,

"Tam shikenan Allah ya kaimu lokacin idan ka aurota yayana zan saka suyi mata duka" tana gama fadin haka tatashi daga kusa dashi ta dauki bokitin wakenta takoma cikin kitchen, dariya sosai jabir yayi saboda jin abinda ta fada,

Lafiyayyen alalenta tayi yasha manja da alayyahu _(nasan pherty Xarah uwar kwadayi har yawunki ya tsinke, to kwalelenki, ga Batool Mamman canma na hangota tana lasar lebe to kema kwalelenki)_, yaji ta dauka roba guda ta koma falonta inda jabir yake yana hira da al'amin a waya,

"Ga antyn naka sarkin kwadayi"

Bata wayar yayi ya dauke robar yajin data dauko,

Duk hankalinta ya kasu kashi kashi dan haka agurguje ta yiwa al'amin sallama ta riko hannun jabir "abbu bani yajin, wallahi idan babu yaji bana jin dadin abincin"

"Kullum ke kenan acin yaji, yajifa bashida wani amfani ajikin dan adam"

Magiya tasaka masa, dan kadan ya zuba mata suka fara cin alalen tare, kullum haka yake biye mata yaci abinda ta girka na kwadayi ita kanta tasan jabir namiji ne wanda yasan hakkin mace domin tunda ta samu cikin nan ta daina dafa abinci kullum sai kayan kwadayi daga wainar fulawa sai dan malele, alala, dambu, dan wake da sauransu amma bai taba kin cin abinda ta girka ba, ko kuma yin korafi, sam bai taba yiba.

Yammacine na ranar litinin tana zaune afalon jabir tana shan kafi kaza wanda yasha kifi da albasa tsabar kwadayi ma harda attaruhu tasa asuyar, tasha kwalliya sosai cikin leshi ja da adon baki ajiki,

Jabir ne ya turo kofa ya shigo bakinsa dauke da sallama,

Inda take ya karaso yana kallonta hadida aika mata da wani zazzafan sako ta cikin kwayar idonsa,

"Binti me kikesha ne haka?" Ya tambayeta bayan ya kamo hannunta,

"Abbu kafi tsire ne"

"Binti bakya tsoron yasaki gudawa? Wannan abun ai daga ganinsa zai batawa mutum cikinsa ko ba kuli kuli bane?"

"Abbu shine amma fa da dadi sha kaji"

Hannunta ya saki ya mike yana girgiza kansa "haba binti nikuwa yaushe zansha wannan abun? Kema dan akwai daliline"

Dakinshi ya wuce yana jiyota tana cewa "wallahi abbu akwai dadi saboda har wani zaki zakin maggi yake yi"

Murmushi yayi ya wucewarsa cikin daki, minti kadan ya fara kwalla mata kira cikin sanyayyiyar muryarshi, sanin bazata jiyoshi ba yasashi tashi ya leka falon, har yanzu tana zaune inda ya barta tana shan kafi kazarta,

"Binti zo"

Mikewa tayi ta tashi sai kuma taji wani irin ciwo ya murde mata cikinta da mararta,

Rike cikin tayi tana salati "wash abbu" shine kawai abinda ta iya fada jini yafara bin kafarta.





_Masu karatu kuyi min afuwa naso kammala book dinnan awannan shafin amma hakan bai samu ba, gaisuwa mai tarin yawa gareki khadija magaji bk da dukkan masoyan wani haske_




*_Ummi Shatu_*πŸ‘ŒπŸ»



[10/22, 9:21 PM] Ummi A'ishaπŸ‘ŒπŸ»: *WANI HASKE*


*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*


_121-125_






~~~Durkushewa tayi awurin tana rike da cikinta yayinda jini yake gudu ajikinta yana bin kafarta kamar an bude fanfo,

Da sauri jabir ya karaso inda take yana tambayarta,

"Binti menene? Me ya sameki?" Sai alokacin idonshi yakai kan jinin da yake bin kafafunta,

"Innalillahi" yafada arazane, dasauri ya saketa ya nufi dakinsa domin dauko rigarsa, yana tafiya yana saka rigar ko hula bai tsaya dauka ba, hijabinta daya hango akan kujera ya dauko ko saka mata baiyi ba ya dauketa irin daukar da ake yiwa jarirai,

Yana dauke da ita ya nufi tsakar gida da ita, kamashi tayi ta rikeshi gam numfashinta yana kai kawo yana fita dakyar,

Tunda mai gadi ya hangoshi ya tabbatar babu lafiya dan haka yayi maza ya fara kwalawa mal idi driver kira, shima a sukwane ya zaburo yazo ya shiga motar ya figesu mai gadi ya hangame musu gate suka fita,

_Nasara clinic_ shine asibitin da suka nufa, har lokacin bahijja murkususu take yi ajikin jabir tana sake kankameshi abin gwanin ban tausayi,

Suna zuwa asibitin jabir ya sake daukarta ya nufi ciki da ita yana shiga wata nurse ta garo gadon da ake saka marassa lafiya ya dorata akai aka garata suka doshi wani daki _(antenatal)_ ,jabir binsu kawai yake yi yana yiwa bahijja addu'a acikin zuciyarsa, dole a waje ya tsaya aka shiga da bahijja cikin dakin.

Yana nan tsaye yana kai komo awurin yama rasa abinyi kwata kwata shi kawai ta lafiyar bintinshi yake yi domin bai san acikin wanne hali take ba ahalin yanzu,

Wurin minti talatin yana tsaye a inda yake wani kyakkyawan likita ya fito dan gayu dashi mai mutukar kyau da iyayi (saurayin adda Benazir), hannu ya bashi suka gaisa kafin yajashi zuwa cikin office dinshi yana goge gumin dake fita ajikin goshinsa,

Bayan sun zauna ne dr din ya dubi jabir cikeda damuwa akan fuskarsa yafara jawabi kamar haka,

"Dafarko dai ranka ya dade ina mai baka hakuri sakamakon munyi iya kokarinmu na ganin mun ceto ranta da lafiyar abinda ke cikinta amma unfortunately abin ya gagara...!"

Kallonsa jabir yayi wanda idanuwanshi suka sauya kala daga fari zuwa ja,

"Dr ban fahimci abinda kake nufi ba"

"Abinda nake nufi anan shine madam dinka ta samu miscarriage, tarasa cikin dake jikinta"

Cikin damuwa jabir yadafe kumatunsa da hannunsa guda daya acikin ranshi yana karanta addu'a domin samun sassauci,

"To dr menene musabbabin faruwar hakan, menene ya haifar da hakan?"

Wadannan sune jerin tambayoyin da jabir ya jerowa likitan alokaci guda,

"Ehh to gaskiya shine abinda muka kasa fahimta, har yanzu bamu gano abinda ya haddasa mata wannan miscarriage dinba saboda ahalin yanzu ta lafiyarta muke yi sannan kuma kasancewar ta zubar da jini da yawa to tana bukatar akara mata jini, da ruwa"

"Shikenan dr, thank you"

Tashi jabir yayi yana mika masa hannu domin yin musabaha, fita yayi ya tafi wurin mal idi driver suka koma gida ya dauko kudin da za ayi amfani dashi domin da saboda tsabar rudewa ko kudin ma bai samu ya dauko ba,

Asibitin suka dawo alokacin har ansamo jinin da yayi daidai dana bahijja ana kara mata, wata takarda aka bashi wacce ke dauke da jeren magungunan da ake bukata hakan yasashi nufar pharmacy domin siyo duk magunan da ake bukata,

Yana waje yana jira bai samu ganinta ba har mangaruba tayi, salla yaje yayi ya dawo yana zuwa ya samu dr din yana fitowa daga dakin da bahijja take anan yake sanar dashi cewar zai iya shiga ya ganta,

Jiki asanyaye jabir yasaka kai ya shiga cikin dakin, hangota yayi kwance hannunta daya makale da abin karin ruwa ana kara mata, dayan hannun kuma ta dafe cikinta dashi daga gani kuka take yi,

Gefen gadon ya karasa ya zauna akusa da ita yakai hannunshi kan goshinta yana shafawa,

"Binti na sannu..!"

Bude idonta tayi hawaye yana sauka daga idanuwan nata ta kalleshi,

"Abbu shikenan cikin ya zube ko?"

Duk da yana cikin damuwar shima amma sai da yayi murmushin karfin hali yaci gaba da shafa goshinta zuwa gashin kanta,

"Babu komai binti kar ki damu, wannan wata jarrabawa ce daga wurin Allah, watakila samun babyn ayanzu bashine alkairi agaremu ba shiyasa Allah ya hanamu ya kwace abunshi cikin sauki"

Idonta ta runtse wasu hawayen suna gudu akan kumatunta,

"Abbu yanzu shikenan na rasa wannan cikin? Wannan wacce irin...!"

Sauri yayi ya rufe mata baki da hannunshi,

"Haba binti ita jarrabawa akan mumuni ai tazama wajibi, mutum indai mai imani ne Allah baya taba barinsa kara zube domin Allah cewa yayi _"'Ashe mutane sunyi zaton abarsu suce munyi imani alhalin ba za a jarrabesu ba? Kuma lalle mun jarrabi wadanda ke gabaninsu domin lalle Allah yasan wadanda sukayi gaskiya kuma lallai yasan makaryata"' (suratul ankabut aya ta 3)_ dan haka wannan abun jarrabace daga wurin Allah binti, mutukar kayi imani to dolene sai Allah ya jarrabeka shiyasa acikin suratul bakara sura ta biyu aya ta _155-157_ Allah subhanahu wata'ala yake cewa:

_Kuma lalle ne muna jarrabarku da wani abu guda daga tsoro, da yunwa da nakasa daga dukiya da rayuka da 'yayan itace, kuma kayi bushara ga masu hakuri, wadanda suke idan wata masifa ta samesu sai suce lalle ne mu ga Allah muke kuma lalle ne mu zuwa gareshi masu komawa ne, Allah yace wadannan akwai albarku akansu daga ubangijinsu da wata rahama kuma wadannan sune shiryayyu"'_

Kinga bai kamata ki rinka irin wadannan maganganun ba, addu'a ya kamata kiyi domin shi lamarin mumini akwai abin sha'awa da ban mamaki inji annabi Muhammad acikin wani hadisi haka yafada yace saboda idan wata musifa ta samu mumini sai yayi hakuri ya dogara ga Allah sai Allah ya canja masa da abinda yafi zama alkairi agareshi, idan kuma wani abin farin ciki ya sameshi sai yayi farin ciki ya godewa Allah hakan sai ya sake zama alkairi agareshi, hakika babu mai samun irin wannan garabasar face mumini"

Hannun jabir ta riko da dayan hannunta wanda bashine wanda ake yi mata karin ruwan ba, "abbu nahakura, wallahi nahakura, Allah ya bani ladan jarrabawar da yayi min, Allah yasa hakan shine yafi zama alkairi agareni, agareka da kuma rayuwarmu gaba daya"

Kissing din goshinta yayi yana murmushi "amin binti,haka ya kamata dukkan musulmi ya zama wurin rungumar kaddarar da ubangiji ya aiko masa da ita"

"Abbu marata tana yimin ciwo ga wani irin fitsari da nakeji"

Kanta ya shafa yana yi mata sannu, ya dade azaune awurinta har sai da yaga bacci yayi awon gaba da ita sannan ya tashi ya fita,abincin da zata ci yaje ya samo mata da sauran tarkace irin wanda marar lafiya zai nema.

Kwananta uku a asibitin jabir yana kulawa da ita amma koda wasa bai fadawa kowa abinda ya faru ba, hatta gidansu bai sanar musu ba, haka itama gidansu bai fada ba, Ummu al'amin kuwa kusan kullum sai sunyi waya amma bai taba sanar da ita rashin lafiyar ba,

Yanzu taji sauki sosai ta dawo normal bayan likitoci sunyi mata wankin ciki, ganin ta warware taji sauki yasa aka sallamesu zuwa gida amma har lokacin basu san makasudin zubewar cikin ba shi dama jabir baya son yawan bincike domin yasan koma menene dai to Allah ne ya shiryo faruwar hakan.

Suna komawa gida ta shiga aikace aikace kasancewar jikinta ya warware sosai,

Tana kitchen tana goge goge jabir ya shigo daga shi sai wando baki iya gwiwarsa da farar t shirt mai gajeren hannu,

"Binti sarkin aiki, daga dawowa kuma sai afara da aiki?"

"To abbu idan nabari waye zai yimin?"

Ta bayanta yaje ya shiga jikinta ya rungumeta,

"Kibari anjima zan tayaki kiyi,amma yanzu kizo muje in nuna miki wani abu"

Make kafada tayi tana murmushi

"nidai abbu basai ka nuna min ba,Allah nasan wayo zaka yimin" ta karasa maganar cikeda shagwaba,

"Binti bakya son babyn ne? Naga harda kuka kikayi lokacin da wancan cikin ya zube, ko bakya son kiyiwa al'amin kani?"

"Gaskiya nidai abbu, nidai, nidai....!"

Juyo da ita yayi ya dauketa akafadarshi ya fita da ita yana kwaiwayonta,

"Nidai, nidai, nidai binti" dariya tafara kyakyatawa batare da ta shirya ba.

Rayuwa taci gaba da tafiya musu cikin son juna da yarda da amincewa da junansu da kuma zaman lafiya mai dorewa, har yanzu jabir yana koyar da ita abubuwan da suka shafi addini, gashi kullum tana zuwa makarantar islamiyya inda take kara samun wani karatun,

Kimanin wata uku da yin barinta tasake samun wani juna biyun nan aka koma gidan jiya aka fara laulayi da kwadayi,

Karfe uku na dare ta farka daga baccin da take yi, ido ta bude tafara neman jabir, acan wurin da ya kebe domin sallarshi ta hangoshi yana karatun alqur'ani, juyawa tayi tana fuskantarsa, alqur'anin ya rufe ya taso zuwa inda take kwance,

Agefenta ya zauna ya riko hannunta yana shafa kyawawan kananan kitson dake kanta,

"Abbu gobe ko fate faten tsaki zanyi da wake da alayyahu"

Tafada tana kallonsa, shima kallonta yayi yana murmushi,

"Fate fate? Nikuma me zaki yimin?" Ya tambayeta yana jan hannun rigar baccinta guda daya,

"Abbu kaima shi zaka sha" tace dashi bayan ta rike hannunshi,

"Wallahi abbu ko idan ka tsinka min hannun rigata ba yarda zanyi ba" tafada tana turo masa baki,

"Me zakiyi binti? Ramawa zakiyi?"

Dariya tayi ta riko hannunshi duka cikin nata, "hanaka fate fatena zanyi"

Dariya yayi ya dagota kacokan ya dorata ajikinshi, "to yanzu ba zaki koma baccin ba?"

"Abbu muyi hira ni nagama bacci"

"To ai ni kin san irin hirata indai irin wannan lokacin ne" ya rada mata acikin kunnenta,

Sumar kanshi tafara shafawa "abbu wallahi indai na haifo baby marar gashi to kaine"

"Kedai binti, ni ai duk Sati sati nake yin aski da ace bana aski da tuni yanzu sumata tafi taki yawa"

"Hum um" tafada cikin shagwaba,

Bakinshi yakai saitin nata tagoce tana cewa "um um abbu"

"Ehh binti" yace da ita yana murmushi,

Kwanciya tayi ajikinshi suka ci gaba da nunawa junansu so.

Washe gari da safe kitchen ta shiga ta shirya fate faten tsakinta takoma dakinta ta zauna atsakiyar gadonta tafara sha, dakin nata jabir ya biyota ya sameta tazuboshi a filet tanata sha da cokali,

"Binti tsabar rowa shine zaki gudo nan ki zauna"

"Ba rowa bace abbu"

"To menene?" Ya tambayeta yana kokarin hawa kan gadon,

"Gashi abbu musha"

Hannu yasa yafara diba yana ci,

"Binti bakin nan naki ya iya kwadayi tun jimawa"

"Kaima ai kwadayayyen ne abbu" tafada tana murmushi,

"Naji, nayarda"

Sai da suka koshi dam sannan yashirya domin tafiya office, part din bahijja ya shiga domin yi mata sallama, daure da towel ya ganta ta fito daga wanka tana kokarin karasawa gaban mirror,

"Binti nafito, sai nadawo?"

Juyowa tayi tana kallonsa yasha black din dafaffen boyel da hularshi yayi kyau sosai,

"Abbu kayi kyau, adawo lfy, Allah ya baka sa'a ya saka maka albarka adukkan al'amuranka"

Gareta ya karasa ya rungumeta yayi mata kiss agoshi sannan ya amsa da,

"Amin bintina,Allah yayi miki albarka, me zaki dafa da rana?"

"Fate fatena zansha yana nan dayawa na ajiye"

Hannunta ya kama ya rike yan yatsunta, "to shikenan nima ki rage min kinji"

Kai ta daga, sakinta yayi ya juya yafita yana murmushi, itama da murmushin ya tafi yabarta akan fuskarta tana mai jin wani sabon sonsa yana sake shigarta.

K'arfe 8 nadare yana kwance adakinsa akan gadonshi gabanshi da laptop yana lallatsawa bahijja ta shigo hannunta dauke da hijab jikinta kuma riga da wando ne yan kanti,

"Abbu gari da sugar nake son sha, kazo ka rakani muje mu siyo tare"

Juyawa yayi ya kalleta, "gari?" Ya tambayeta,

"Uhm abbu"

Laptop din ya rufe ya tashi zaune, yana karewa jikinta kallo,

"Muje, amma binti yau kuma ki rasa abinda zakisha sai gari da sugar?"

Hannunshi ta rike bayan tasaka hijabinta suka fara tafiya,

"Amma dai abbu ai ba laifina bane"

Ganin ta rakwarbabe masa fuska yasashi fara rarrashinta, suna tafe suna hira har sukaje wani shago abayan layinsu, tsayar da ita yayi ya karasa da kanshi shagon ya siyo mata garin kwano daya ya dawo suka koma gida,

Suna zuwa ta dauko Kofi ta diba ta zuba ruwa tasa sugar da madara tafara sha jabir yana zaune yana kallonta, bata iya yi masa maganaba har sai da ta kammala shanye garinta tukunna,baki ta turo masa,

"Abbu kuma meye kaketa kallona?"

Jikinshi ya matso da ita "binti wannan cikin naki ya saki kinyi kyau ne, matsalarshi daya ya mayar dake lazy mai dankaren kwadayi"

Kwantar da kanta tayi akan kirjinshi tana dariya, "shi kuma abbu gashi yanzu ya zama wani kala"

Hancinta yaja yana murmushi.

Kullum haka take fama da kayan kwadayi, yau wainar fulawa tayi ita ta wuni tana ci har dare,

Tsakar dare tana tsaka da bacci ciwon ciki ya tadata daga baccin kafin wani lokaci har jini yafara zuba daga jikinta,

Fitowar jabir kenan daga bathroom ya iyo alwala yazo ya risketa acikin wannan halin ba tare da bata lokaci ba yacire mata yar rigar baccin da take jikinta ya saka mata kaya ya dauketa yafita da ita lokacin har ta fita hayyacinta,kasancewar darene mal idi driver baya nan dan haka da kanshi yayi driving ya kaita

30 / 35