Author : Hameedah Category : Complete Novels
daga jikinta,
"Abbu ina al'amin, shine ko yace yana gaisheni ko?"
Tafada tareda hawa kan gadon ta kwanta agefenshi daf dashi, domin har jikinta yana gogar nashi,
"Yace agaisheki mana, har da sako ya bani in kawo miki, sai gobe zan baki idan na bude kayan"
"Yawwa nagode, Allah sarki my boy i missed him so much"
Idanuwansa ya mayar kanta ya kalleta,
"Dazu da naje gidan malam yayi min maganarki, ina tayaki murna, barka da shigowa addinin musulunci, addinin gaskiya,ina yimiki addu'ar kasancewa acikinsa har karshen rayuwarki"
Hannunsa ta kama ta rike acikin nata ta lumshe idanuwanta,
""Abbu nagode, bayan tafiyarka nayi mafarkinka"
Hannun nata ya sake makalewa cikin nasa "meya faru a mafarkin? Me nayi miki? Fada min"
Murmushi tayi tafara shafar gashin da yake kwance a hannunshi, wani irin yammmmm! Yafara ji amma sai ya dake,
"Abbu ganina nayi acikin wani bakin daji mai tsananin duhu sai kawai nafara hango *wani haske* yana tahowa daga nesa har ya karaso kusa dani yana karasowa sai naga ashe kaine,kana zuwa sai ka kama hannuna muka yita tafiya har muka fita daga cikin wannan bakin dajin muka shiga wani wanda yake mai tsananin haske ga wani kamshi mai dadi yana tashi ga ciyawa koraye awurin sannan ga tsuntsaye sunata rera kuka mai dadi, ka bude baki kenan da niyyar fara yimin bayani sai nafarka, naji haushi ba kadan ba saboda naso ace naji abinda kayi niyyar fada min"
Hannunsa daya yasa ya rike dayan hannunta wanda take shafar gashin hannunsa dashi,
"Shigowarki addinin musulunci shine fassarar mafarkinki binti, hakika kafurci duhune yayinda musulunci kuma ya zama *wani haske* wanda ya haskaka dukkan komai"
"Hakane abbu, yanzu na tabbatar da duk abubuwan da ka fada min abaya"
"Dazu kikace min sau biyu kike yin jini awata?"
Idanuwanta ta rufe duk ya sakata taji kunya saboda yadda yake fadin maganar afili inama laifin ya dan sakaya yace period,
"Uhmmm?" Ya sake tambayarta, daga masa kai tayi batare da tayi magana ba,
"Yaushe da yaushe?"
Dakyar ta iya bude bakinta "farkon month da karshensa" ta fada cikin shagwaba ga wata uwar kunya data lullubeta,
Kin taba ganin dr akan hakan" ya tambayeta gamida murza yan yatsunta,
Kai ta sake dagawa batayi magana ba,
"Me yace miki?"
"Yace ba problem bane" ta bashi amsa har lokacin idonta arufe yake amma tana jinshi yana matsa yatsunta duka,
"Allah ya albarkaci rayuwarki binti"
"Amin abbu, kayi min addu'a inyi bacci"
Kansa ya rankwafar zuwa kusa da ita ya fara yi mata adu'o'in Wanda har lokacin tana rike da hannuwansa duka biyun, sai da ya kammala tofeta da addu'a sannan ya kalli idanuwanta wadanda suke a lumshe,
"To ki sakeni mana binti"
Murmushi tayi tasaki hannun nashi duka biyu acikin sloww motion ba dan taso ba,
Murmushi yayi ya koma yadda yake yaci gaba da aikinshi, sake matsawa daf dashi tayi bada jimawa ba bacci ya dauketa,
Ya jima zaune yana amsa fatawar mutane daban daban kafin ya rufe laptop din ya jiyo yana kallon goodness wacce take kankane ajikinsa domin lokacin da tayi baccin batare data saniba acikin barci ta sake shiga jikinsa dan harda zira hannunta acikinsa da haka har ya gama aikinshi tana zagaye dashi da hannuwanta,
Hannunta ya zare ahankali ya dubi lukuta lukutan cinyoyinta wadanda ta yayesu ba tare da ta sani ba, rigar yaja ya gyara mata yaje ya dauro alwala ya fito yazo gefenta ya kwanta yana mai karanto addu'o'in neman tsari daga dukkan abin k'i.
_*Ummi A'isha*_ππ»
[10/2, 3:45 PM] Ummi A'ishaππ»: *WANI HASKE*
_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_
_91-95_
~~~Bargo yaja ya rufa mata sannan shima ya dan rufe rabin jikinsa,shiru yayi yana tunani aranshi wanda kusan rabin tunanin akan goodness ne, hakika Allah shine mai yadda yaso aduk halin da yaso kuma alokacin da yaso,
Tun farkon haduwarshi da goodness lokacin data fara aiki a office dinshi har yau dinnan da suke tare a matsayin Ma'aurata duk sai da ya tino su acikin wannan dare,
Jinta yayi ta matso jikinshi tana mai kankameshi,ahankali yasa tattausan hannunshi ya dagota ya kwantar da ita ajikinshi gamida shafar kanta har bacci ya saceshi.
Tun kiran sallar farko ya tashi ya gyara mata kwanciyarta ya lullubeta yaje yayi alwala yafita masallaci,
Har k'arfe 6:30 bai dawo gidan ba alokacin goodness ta farka tunda taga dakin wayam tasan bai dawo daga masallaci ba, sashenta taje tayi wanka da ruwan dumi ta shirya cikin dan karamin wando tied iya gwiwarta da yar riga fara mai hannun shimi,
Sashen jabir tayi maza ta koma ta gyara masa cikin bedroom dinshi ta gyara falo har lokacin bai dawo ba domin wani lokacin har sai rana tafito yayi sallar walaha sannan yake dawowa,
Part dinta ta koma bayan ta kammala gyara sashen jabir, kitchen ta shiga ta dora abin karin kumallo,
Dankali da kwai ta soya sannan tayi farfesun hatta ta dafa tea da kayan kamshi,
Sai da ta gama shirya komai sannan ta nufi sashen jabir tasan lokacin kila ya dawo,
Akan doguwar kujerar falonshi ta ganoshi yana kwance da doguwar jallabiya fara ajikinshi, yanda yayi kwanciyar ba karamin kyau taga yayi mata ba domin ya harde duka hannuwanshi guda biyu akirjinshi idanuwanshi alumshe amma fuskarshi dauke da murmushi kamar wanda yake ido biyu,
Ahankali ta sadada ta je inda yake kwancen, hannuwanshi ta warware ahankali ta budesu tashiga cikin jikinsa ta kwanta duk da tanada masaniyar kujerar tayi musu kadan, matsuwa tayi sosai ajikinshi tana mai kallon kyakkyawar fuskarshi,
Kanta ta kwantar akirjinshi tana mai shafa kyakkyawan sajensa,
Hancinshi taja sannan ta dora dan yatsanta akan lebenshi na kasa, "ohh abbu badai kyau ba, Kanada kyau sosai, shiyasa al'amin shima ya zama mai kyau"
Kanta ta cusa acikin kirjinshi tana shakar kamshinsa mai dadi,bakinta tasa ta ringa jan botir din gaban rigarsa har sai da ta bubbudesu duka da hakorinta nan ta tura kanta cikin rigarshi tana sinsinar kirjinshi, ta dade ahaka har jabir ya farka, ganinta yayi tana makale dashi gashi duk ta bubbude masa botiran jikin rigarsa da bakinta,kallonta yayi yanda suke kwancen nan kamar wasu hanta da jini,fuskarta yafara karewa kallo yana kokarin gyara mata kwanciyarta acikin jikinshi,
Da saninta tayi wani juyi zata fada kasa,cikin sauri ya tarota ya rungumeta,
Bude idonta tayi dama ba bacci take ba tana jinsa,
"Dama ai rigimace tasaki zuwa ki kwanta anan tunda kin san wurin yayi mana kadan, ke kadai ma wurin kadan zaiyi miki balle mu biyu" ya fada yana kallon idanuwanta,
"Yanzu wannan wurinne yayi mana kadan abbu?" Ta tambayeshi tana kallonshi itama,
"Ehh tunda saura kadan yanzu kisha k'asa, ba dan natashi ba da sai dai kijiki akasa"
"Abbu duk lokacin daka tashi magana sai kace ni katuwa ce bayan banga ta inda nafika kiba ba"
"Haba yarinya, kinfini mana"
"Ta ina?"
Hannunshi yadora akan cinyarta,
"Wannan cinyar taki guda daya tayi ahada nawa duka biyu"
Hannunshi ta rike saboda sai taji kamar tafiyar tsutsa yake yi mata acinyar tata,
"Sannan kuma waye yace miki ki bude min botiran rigata?"
"Yi hakuri abbu bari in rufe maka dama can ba laifina bane, hakorina ne ya bude"
Hannuwanta ya rike, "yanda kika bude da baki to yanzunma da bakin zaki rufe"
"Yi hakuri abbu bazan iyaba"
Bakinta tasa tafara kokarin wai sai ta balle botiran amma ta kasa,
"Abbu bari naje na kawo maka abinci, tun dazu nagama"
Sauka tayi daga kan kujerar ta fita da gudu, binta da kallo jabir yayi yana girgiza kai, wato yarinyar nan yarinyace danya sharaf bata da maraba da yar 14 komai nata na yara take yi,
Tashi yayi yaje yayi brush ya fito lokacin har goodness ta kawo abincin tana zuba masa,
Akasa ya zauna yafara ci yana kurbar tea din,
"Abbu insa hannu nima muci tare?" Dagowa yayi ya kalleta tana tsotsar dan yatsanta wanda ta yanke jiya,
"Uhm" yafada atakaice saboda wani lokacin shi baya son surutu,
Cokali tasa tafara ci tanayi tana satar kallon bakinshi wanda yake motsi mul mul lokacin da yake taunar dankalin,
Ya rigata kammalawa dan haka tashi yayi ya shiga cikin dakinsa ya janyo jakar kayan da yazo mata dashi, anesa da ita ya zauna ya fara kokarin bude jakar,
Da sauri ta ajiye spoon din hannunta tadawo kusa dashi ta zauna tana murmushi,
"Ungo sakonki inji danki al'amin" mika mata chocolate yayi acikin wani babban kawali,
Cikeda doki da murna ta karba, "nagode, Allah Sarki al'amin dina"
Yana kallonta ta bude chocolate din tafara sha ya yi tunanin abin na wasane sai yaga sha kawai take babu kakkautawa kafin ya farga har tasha guda biyar tana kokarin bude ta shida,
Hannunta yakama yarike wadda take da niyyar budewar,
"Ke bakya gajiya da shan zakine? Wannan kayan zakin da kikesha sune suke sakaki rushing dinnan idan kina period, kar nasake ganin kinsha wannan chocolate din, mayarta cikin kwalin ki bani nan"
Langabar da kanta tayi cikin sigar shagwaba tace "ayya abbu kabarni nasha wannan din, daga ita bazan sake shan wata ba"
"Bazafa kisha ba, bani nan" fusgewa yayi ya mayar cikin kwalin ya rufe ya ajiye akusa dashi,
Wasu kananan kaya masu kyau ya shiga futo mata dasu yana mika mata,
"Woww..!" Shine kawai abinda take furtawa,
Bra din da ya siyo mata ya ciro, "ungo wannan idan kuma sunyi miki kadan shikenan"
Karba tayi duk kaloline masu kyau kuma manya irin size dinta,
"Haba abbu wannan ai sunyi min yawa, wanne irin kadan?"
"Wadannan abubuwanne suka yi miki yawa?" Ya tambayeta yana satar kallon kirjinta, dago kanta tayi daga sunkuyen da yake tana kallon kayan, caraf suka hada ido, dauke kansa yayi duk sai yaji yar kunya ta rufeshi saboda yadda goodness ta kamashi yana kallon kirjinta,
Lips dinta ta cije ta zuba masa ido kamar zata cinyeshi,shikuma sai basarwa yake yaki sake kallonta,
Sunfi minti biyar ahaka tana kallonsa shikuma yana kallon wani wuri, juyowa yayi suka sake hada ido har lokacin tana cije da lips dinta fuskarta dauke da murmushi,
"Lafiya? Ki duba sauran kayan mana, wannan kuma idan sunyi miki kadan ki bayar kawai"
Murmushi tayi aranta tace "dama fa sai da ka gama karewa kirjina kallo kasan size dina sannan ka siyo min wannan braziers din idan ba haka ba ya akayi kasan size dina"
Kallonta ya sake yi jin bata yi magana ba,
"Abbu wlh wannan ba zasu yi min kadan ba"
Mikewa tayi da bra daya a hannunta tashiga bedroom dinshi bata jima ba sai gata ta fito,
"Abbu kaga tayi min daidai"
Juyawa yayi yaganta daga ita sai bra din, kuma tayi mata cif cif, dama shi bai kawo cewar zata yi mata yawa ba yafi zaton kada zata yi mata,
Kansa ya dauke daga kallonta,
"Nagani,tunda tayi dai dai shikenan"
Dakinsa ta koma ta sako rigarta, ta dawo wurinshi inda yake zaune yana nazarin cikar halitta irin tata.
Agabanshi ta zauna ta cigaba da dudduba sauran kayan dake cikin akwatin,wasu hadaddun turarruruka tagani wadanda daga gani masu tsadane nagaske,
"Bani wannan turaren nawane ba naki ba" yafada tareda mika mata hannu,
"Abbu bani ka siyowa ba?",ta tambayeshi a shagwabance,
"Ehh, nawane saboda me karfine, kinga ai bai kamata kisaka turaren maza ba saboda duk inda kikaje sai anji kamshinki kuma hakan haramunne"
Mika masa tayi, tafara kokarin mayar da kayan cikin jakar,
"Abbu dan Allah ka barni naje gidan anty bilkisu anjima, kaina ya cika da yawa saloon yake so" tafada tana shagwabe fuskarta,
"Saloon dinne har sai kinje gidan anty bilkisu?"
Kai ta daga masa batare da tayi magana ba,
"Indai wannan ne dalilin kadai to basai kinje ba"
"Abbu kagani fa" hular kanta ta cire, nan yaga gashin kan nata cukus kamar me amma baza asata asahun marassa gashi ba,
"Koni ai zan iya yimiki saloon din tunda ina yiwa ummu ma, badai saka relexer bane kawai?"
"Abbu relexer Kadai?"
"Akwai hand drayer ta ummu sai in dauko miki"
Jakar kayan ta dauka tafita ta nufi sashenta tana dariyar yadda za ayi jabir yayi mata shamfo,
Abincin rana ta dora ta dafa shinkafa da miya sannan tayi lemon kankana wanda ta hada da ayaba da apple tasaka madarar ruwa ta dan zuba sugar kadan,
Lokacin data gama komai tatafi wurin jabir domin ya saka mata relexer din, a dakinshi ta iskeshi yana kwance akan gado da wani littafin addini a hannunshi yana karantawa,
Ajikinshi ta kwanta, "abbu nagama aiki kazo ka shafa min relexer din"
Littafin hannunshi ya ajiye yana kallonta, "da wanne relexer kike amfani?"
"Abbu soft and beautiful ne"
Wayarshi ya dauka ya kira driver yace ya taho masa da relexer,
Tana nan kwance ajikinsa har driver din ya dawo, da kanshi ya fita yaje ya karbo ya dawo,
Tun awurin tajewa aka fara samun matsala domin rike hannunshi tayi "washh abbu wlh da zafi bani na taje da kaina"
Sakar mata cumb din yayi tagama tajeshi da kanta sannan ya fara raba mata shi gida uku,
"Abbu kasaka leda a hannunka karka ji ciwo"
"No basai nasaka ba"
Tana zaune akasa shikuma yana kan kujera yana shafa mata har yagama amma duk ya yayyabe mata goshinta da keyarta sosai da relexer din,
Tashi tayi taje gaban mirror ta gyara fuskarta ta dan goge na goshin nata, shi kuma jabir ya shiga bathroom ya wanke hannunsa, fitowa yayi ya koma falo ya kunna tv,
Tun relexer din baifi minti goma ba ta fito tazo wurinshi, "abbu zo muje ka wanke min, yafara yimin zafi"
Dago idonshi yayi ya kalleta "daga sakawa sai wankewa? Ki bari yayi 30 minutes kamar yadda suka rubuta ajiki"
Zama tayi kusa dashi tana jijjiga hannuwanshi, "abbu zai kona min kai, wlh da zafi"
"To bari idan ya kara 25 minutes sai in wanke miki"
Tashi tayi tana yarfe hannunta ta shiga bedroom dinshi, kallo yayita binta dashi har ta shige,
Dakyar ta bari yayi 20 minutes tazo tasaka shi agaba sukaje bathroom yafara wanke mata, wata uwar kara ta cillara,
"Wohhhhh abbu goshina, wayyo goshina,abbu wlh na kone"
Da kokawa da komai yake wanke mata kan daga karshe ta rirrike hannunshi,
"Nidai ka bari zan karasa wankewa da kaina"
Fita yayi ya barta ta dan lallaba kan ta wankeshi sama sama, duk kayan jikinta ya jijjike dama jabir ba iya saka relexer din da yayi asalima ita ummu al'amin bata shanfo iyakacinta kawai ta wanke gashinta,
Agefen gado ta sameshi zaune yana jiran fitowarta,
Rigarta ta kwaye ta fara goge goshinta da cikin kunnenta hakan ya bashi damar ganin jikinta hatta jar bra din dake jikinta sai da yagani,
"Abbu wlhi duk na kone agoshina da ta keya na",tafada idonta rau rau da kwalla,
"Ayya sorry binti, zo nagani"
Gabanshi taje ta tsugunna yafara ganin goshin nata hakika gashi nan kam duk ta kokkone wurin yayi alama,
"Sorry binti, zanje masallaci in dawo"
"Abbu har lokacin sallar yayi?"
"Ehh ke ai bayi kike ba shiyasa zaki ga lokaci yayi saurin yi"
Bathroom ya shiga yayinda ita kuma ta jawo towel dinshi ta daura ta fara kiciniyar cire kayan jikinta, tana tsaye daure da towel din yafito ya wuceta ya tafi masallaci.
Bangarenta ta koma ta shiga wanka ta sake wanke gashinta wanda keta yi mata radadi,
Kwalliya tayi ta shirya tsaf cikin riga da skirt yan kanti masu kwalliyar beza ajiki,
Kanta abude ta dauki abincin jabir tatafi part dinsa lokacin ya dawo daga sallar,
"Abbu wlh har yanzu wurinnan radadi yake yimin, nidai basai nayi amfani da hand drayer din ba, nafasa"
Abincin tafara zuba masa tana kallonshi,
"Zai daina zuwa anjima, gashinki yanada karfine, ni matar da zan aura gashinta mai laushine sosai kuma bata saka relexer"
Dagowa tayi ta kalleshi tareda kicincine fuskarta amma batace komai ba, ta gefen idonshi ya kalleta yana dan murmushi, salon yanda take kishinta yana burgeshi,
Abincin ta ajiye masa ba tareda tayi magana ba, mikewa tayi zata tafi saida taje har bakin kofa ya kirata,
"Binti zo nan"
Dawowa tayi tazo ta tsugunna agabanshi amma har lokacin taki kallon fuskarshi,
Kallonta yayi sosai yana mamakinta domin kishinta yawane dashi duk tabi ta damu daga fadar haka,
"Dubo kan drewar adakina akwai wasu littattafai da nake koyawa al'amin karatu ki debosu duka"
Mikewa tayi taje ta kwaso littattafan ta kawo masa,
Guda daya daga ciki ya dauka ya mika mata "wannan littafin akdari ne, shi zan rinka koya miki, bari na gama sai muyi"
Har lokacin taki kallon fuskarshi sannan taki magana, littattafan tafara dubawa acikin ranta tana tunanin kenan duk littattafan al'amin ya kwaso mata wanda yake koya masa,
Wani mai hoto ajiki ta bude tana gani, babu zato taga hoton zaki ajiki yana bin wani mutum da gudu, dariya tayi bata shirya ba,
"Abbu kagani" ta juya masa littafin, murmushi yayi yana cin abincinshi, kallon hoton tai tayi tana dariya har ya gama, hadadden lemon kankanar da ta hada musu ya zage ya shanye sai dan kadan ya rage wanda baifi rabin cup ba,
"Abbu shine ka shanye lemon ni baka rage min ba" tafada tana zumbura bakinta,
Wal yayi da manyan idanuwanshi wanda suka fi na cwt Kausar girma "au dama baki sha ba? Yi hakuri ai ban saniba"
Jikinshi ta matsa tana tuttura baki, nan yafara koya mata karatun har suka dauki tsawon lokaci,sai yamma sannan yayi wanka ya fita, tunda ya fice kuma bai dawo gidan ba sai da daddare,
Tana dakinta tana ninke kayanta ya shigo,
"Binti zanje unguwa in dawo"
Kallonsa tayi yasha shadda mai mutakar kyalli sai maiko take yi kalarta dark brown, yasha hula sai faman kamshi yake yi,
Rau rau tayi da idanuwanta tana tabe fuska kamar zatayi kuka "abbu zan bika dan Allah" amma duk atunaninta wurin budurwar da yake ta fada mata zaije,
"Yanzu idan naje dake fada zaki hadani da budurwata dan haka kiyi zamanki naje nadawo"
Tashi tayi taje ta rirrikeshi, "abbu wlh bazan zauna ba sai nabika" kuka tafara mai hawaye da dan sauti kadan,
Sakin baki yayi yana kallonta cikeda mamaki, ya fahimci sam bata da wahalar kuka abu kadanne yake sakata kuka,
"To yi shiru amma kiyi min alkawai idan munje amota zaki zauna ba zakice sai kin bini cikin gidan ba"
"Abbu nayi alqawari"
"To sake kayanki mu tafi"
Har lokacin tana rirrike dashi, dakyar ta cikashi ta fara binkito after dress dinta, agurguje tasaka tabishi suka fita,
Ko acikin mota ma shiru tayi tana mai jin haushin kanta biyoshin da tayi bayan kuma wurin budurwarsa yace zaije, idonta ta rufe taci magani ta bata rai har sukaje inda zasu bata bude idonta ba,
"Binti ina zuwa" yafada lokacin da yake kokarin fita daga cikin motar, bata bashi amsa ba kuma bata bude idonta ba har ya fice din,
Tadade zuciyarta tana kuna tana jin haushin koma wacece mijinta yake so,
Ahankali ta bude idonta ta kalli wurin kamar amafarki sai tagansu akofar gidansu ashe gidansu zaije shiyasa ya hanata shiga, wani farin ciki taji aranta take bakin cikinta ya yaye,
Tana nan tana jiransa har yafito shida papa,akofar gidan suka yi sallama yazo ya shiga motar yayinda mal idi driver ya bude boot yafara jidar kayan dake ciki yana shigar dasu cikin gidan,
Jikin jabir ta matsa ta kama hannunshi ta