Author : Hameedah Category : Complete Novels
asibiti suna zuwa aka karbeta likitoci suka fara kiciniyar hana cikin dake jikinta fita sai dai kaddara ta riga fata domin kafin wani lokaci har cikin ya karasa zubewa,
Bahijja tasha wuya sosai azubewar wannan cikin amma jabir sai kwantar mata da hankali yake yi yana bata hakuri sannan yana nuna mata cewar ta rungumi wannan jarrabawar da Allah ya aiko mata da ita domin doctors din sunce bawata matsala ce da itaba kawai dai kaddara ce,
A wannan karon ma jabir bai sanarwa da kowa ba har aka sallamesu a asibitin suka koma gida, komawarsu kuma keda wuya bahijja tafara yi masa kuka mai cin rai,
Hakurin dai yaci gaba da bata har ta hakura itama ta dangana kamar yadda taga shima yayi ita kam har mamaki jabir yake bata domin bata taba ganin mutum mai tawakkali irinshi ba, duk abinda Allah ya aiko masa karbarsa yake yi da hannu bibbiyu, bai taba nunawa Allah gajiyawarshi akan wannan jarrabawar ba, ganin haka ya sanyata itama daukar kaddarar suka ci gaba da zamansu cikin aminci da kaunar juna.
Bayan faruwar haka babu dadewa ta sake samun wani cikin amma kuma wannan tun yana wata daya da yan satittika shima ya zube tunda sukaje asibiti aka bata gado dr din ya kira jabir office dinshi yafara yi masa jawabi kamar haka:
"Agaskiya ayanda muke zargi matarka tana shan magungunan zubar da cikine in banda haka yaza ayi ace tayita samun miscarriage har sau uku, gaskiya kasaka ido sosai akanta sannan ka dauki matakin da ya dace"
Jabir jin jikinsa yayi ya mutu yayi sanyi amma kuma acan kasan zuciyarshi wani irin tafarfasa yaji tanayi ga wani uban bacin rai da ya ziyarceshi lokaci guda.
Shiru kawai yayi yaci gaba da sauraron bayanin da dr din yake yi masa,
"Yanzu gobe idan Allah ya kaimu zamu iya sallamarku ku koma gida amma gaskiya kasaka ido sosai akan matarka domin duk yadda akayi itace ke zubar da cikin da take samu"
Tashi jabir yayi batare da yace komai ba ya mikawa dr din hannu ya fita ya nufi resumption domin bazai iya shiga dakin da bahijja take ba lokacin saboda bacin ran da yake tare dashi,
Tunani kawai yake yi aranshi me yake yiwa yarinyar nan da har ya sata kin hada jini dashi, shin me yake tare dashi da har take kyamar jininshi, sanin bashida amsar wadannan tambayoyin ya sanyashi mikewa yafara zagaya farfajiyar wurin,
Har gari ya waye bai samu nutsuwa ba yana nan dauke da takaicin abinda likitan nan ya sanar dashi,
Sai da ya danne zuciyarsa sannan ya shiga dakin da bahijja take kwance duk ta dan rame daga daren jiya zuwa yau kadai, bai iya yi mata magana ba asalima ya kasa koda kallon fuskarta,
"Abbu zan sha tea" shine abinda ya jiyota tana fada cikin kasalalliyar murya,
Bai bata amsa ba ya juya ya fita, minti kadan sai gashi ya dawo hannunsa dauke da kayan shayi da tea flask domin ya tura akawo musu dama,
Zama yayi ya hada mata tea din ya mika mata, dakyar ta iya tashi ta kafa kai tafara sha,
Har tagama jabir baiyi mata magana ba,
"Abbu kace su sallameni mu tafi gida, bana son wannan wankin cikin wallahi da wahala"
Tafada tana ajiye cup din dake hannunta,
"Dama wannan time din sunce ba zasu yi miki ba amma ai bai kamata ki tsorata ba tunda kece kika jawowa kanki" yace da ita tareda mikewa ya fice, Gida yayi tafiyarshi batare da ya sanar mata ba,
Mamakine ya kamata sosai saboda jin abinda ya fada, sam takasa fahimtar inda zancen nashi ya dosa, tana nan zaune har dr ya shigo ya sake dubata ya bata sallama, shiru shiru babu jabir sai da rana tayi sannan mal idi driver yazo ya dauketa yakaita gida, ba karamin mamaki tajiba lokacin da taje gidan ta tarar jabir baya nan yayi tafiyarshi office,
Duk da jikinta babu kwari haka ta daure ta gyara gidan tayi girki amma koda jabir ya dawo bata samu fuska awurinshi ba, abincin ta kai masa amma yanda ta ajiye masa haka ya tashi ya barshi yayi wanka ya ficewarsa,
Duk tabi ta damu da sauyin da tafara gani daga gareshi,tana zaune tana nazarin abinda ya fara faruwa agareta tsakaninta da jabir har ya dawo misalin karfe 9:30,bai kulata ba ya wucewarsa cikin daki yayi wanka yayi shirin bacci ya kwanta, jin shiru bai fitoba ya sanyata binshi cikin dakin,
"Abbu bakada lafiyane?" Ta tambayeshi tana kokarin zuwa kusa da ita,
"Kar ki zauna min adaki, kikoma dakinki bana son damuwa" yafada ahankali yana kokarin juya mata baya,
Kuka tafara "abbu dan Allah idan wani abun nayi maka kayi hakuri, abbu dan Allah kafada min laifin da nayi maka, wallahi bazan iya kwana ni daya adakina ba"
Jin kukan da take yi masa yake yi har acikin ranshi, shi kansa yana tunanin ta yanda zai iya ganin wannan daren ba tare da bintinshi ba amma kuma radadin ciwon abinda tayi masa shine bazai barshi ya iya kwana da ita adaki daya ba ayau,
"Ki tashi ki fice min" yafada cikin tsawar da bata taba sanin ya iyata ba, cikin rawar jiki ta mike ta fita tana tafe tana kuka wanda har yana iya jiyota,
Dakinta ta koma ta kwanta taci gaba da kukanta ga wani azababben sabon son jabir da taji yana shigarta, shima abangaren jabir din kukanta kawai yake jiyowa acikin kunnensa tana rokonshi kan ya sanar da ita laifin da tayi masa wani irin tausayinta yaji har acikin ranshi, dukkaninsu ranar babu wanda ya iya yin bacci acikinsu, bahijja kuwa kwana tayi tana kuka har gari ya waye, mamakin canjawar jabir kawai take yi,
Tana dakinta da misalin karfe 10:30 ta jiyo alamun fitarsa zuwa office ba tare da ya koda kalli sashenta ba, lokacin da ya dawo ma haka wasa wasa sai da suka yi kwana biyar ahaka akwana na shidane ta kuduri niyyar sai anyita ta kare ranar domin itama yanzu ta shirya rayuwarta ita daya ba tare dashi ba domin gani take kamar ko dan yaga tana sonshi ne shiyasa yayi mata haka,
Tana falonta zaune tana jiran dawowarsa har taji shigowarsa batayi kasa a gwiwa ba ta nufi sashensa, acikin dakinshi ta sameshi yana kokarin cire kayan jikinshi,
"Zuwa nayi yau ka fada min abinda yake ranka, idan zama danine baka ra'ayi yanzu ka sanar min ko ka sawwake min"
Bai jiyo ya kalleta ba yace "ke kar ki saka min ciwon kai pls, ki fitar min daga dakin nan kingane?"
"Akan me zan fita bayan baka sanar min da abinda kake nufi dani ba"
"Duk abinda kike tunani shi nake nufi"
"To meye nufinka, nabar maka gidanka kenan?"
"Yanda kika zaba" yafada tareda shigewa cikin bathroom,
Bin bayanshi tayi da kallo ta hadiye kukan da yazo mata,
"To sai me dan nabar maka gidanka? Zan barshi yanzun nan saboda basai lalle dashi zanyi rayuwa ba, idan dan saboda kaga ina sonka ne yasa kayi min haka to kasani nima yanzu nadaina sonka, zanyi rayuwa ba tare da kai ba"
Tana kaiwa nan ta juya tafita tanufi dakinta tana hawaye tana zuwa tafara harhada kayanta acikin katuwar akwatinta, hijabi ta zira taja jakarta domin ji take yi itama yanzu tana iya fitar dashi daga ranta saboda dama tun asali bashi ya ganta yana soba itace taganshi taji tana sonsa su kuma maza dama haka halinsu yake indai kaine ka nuna kana sonsu to babu irin wulakancin da bazaka gani ba,shiyasa duk tsawon lokacin da suka dauka atare bai taba furta mata kalmar so ko kauna ba, akwatinta taja tafita daga gidan me gadi yana tambayarta ko lafiya amma bata bi takansa ba tayi gaba,
Jabir yana tsaye agaban window yana kallonta har tafice, duk da yana jin haushin abinda tayi masa amma yaji rashin dadin tafiyarta domin ganinta kawai wani abune awurinshi wanda yake jinsa har cikin ransa,labulen ya saki ya koma cikin dakinsa ya zauna ya dafe kansa yana tuna irin daddadar rayuwar da suka gudanar tare da ita,hakika yanzu ya yarda bahijja wani tsagi ce na rayuwarsa kuma bazai taba jin dadin rayuwarshi ba sai tana kusa dashi.
Tsayar da kukan da take yi tayi lokacin da zata shiga gidansu,
Iya papa tasamu domin ma tatafi church,tunda babanta yaganta yasan babu lafiya dan haka ya tsayarta yafara tambayarta, bata iya sanar dashi ba kawai dai tace jabir dinne yace tadawo gida,
Shiru mahaifinta yayi yana tunanin anya kuwa jabir zai iya yin haka, akwatinta ta dauka ta nufi dakinta nada tasaka aciki, kokari tayi ta danne duk wani tunanin jabir wanda yake kokarin hanata sukuni,
Tana falo azaune tana lazimi ga Nigerian film ta kunna tana kallo ma ta shigo hannunta rikeda bible,
"Welcome ma" tafada tana kallon maman nata,
"Ah goodness me kika zo yi? Ba nahanaki zuwa gidan nan ba indai wurina ne ba?" Ma tafada cikin fada,
"Ma mijinane yace nadawo gida" tafada idonta cikeda kwalla,
"Ah goodness wannan shine abinda nayita fada miki but you refuse my advice that time, tun farko sai da nafada miki karki Auri hausa man but kika ki ji, yanzu gashi kinje ya koroki gida"
Zama ma tayi ta ajiye bible dinta ta kalli bahijja "my daughter yanzu wannan abunda ya faru to abun farin cikine agareki sannan kuma damace agunki wacce zaki bar wancan addinin ki tuba kidawo addininmu nagaskiya"
Girgiza kai bahijja tayi "ma ai ni narigada nabar wannan addinin har abada, addinin musulunci addini ne nagaskiya,sannan kuma shi addinin *Wani haske* ne ga kowa da kowa, amma kuma wannan ba shine yake nufin suma masu addinin basa aikata kuskure ba, yanzu 'ma' akwai mutanen da kika taba gani masu tsarin komai na rayuwa samada musulmai? Yanzu 'ma' bakya mamakin yanda Allah ya tsaya ya shirya sama ya shirya kasa? Allah shi kadaine ya halicci sammai da kassai acikin kwanaki shida ba tare da taimakon kowa ba,
Shine wanda ya daidaita akan al'arshinsa yana kallon kowa kuma yana jiransa a madakata, wallahi ma addinin musulunci shine addini na gaskiya kuma shine addinin da yake dauke da abin al'ajabi iri iri domin Allah shine ya tsara addinin ba mutum ne ya tsarashi ba, addinin musulunci shine addinin da Allah ya halicce mutune domin su kasance acikinsa ta hanyar bauta masa shi kadai ba tareda kowa ba, ma shigata addinin musulunci naga abubuwa daban daban naban mamaki wanda addinin kiristanci bai bayar da koda rabinsa ba, asali Allah ya halicci mutum da aljan ne domin su bauta masa, annabi Isah ba kowa bane face bawan Allah, halittar Allah kamar kowa sai dai Allah ya aikoshi zuwa ga mutane domin ya kirasu zuwa ga bautar Allah shiyasa Allah ya azurtashi da mu'ujuza ta warkar da marassa lafiya musamman ma kutare da makafi wannan ne yasa mabiya addinin kiristanci suka gajeshi suna bude asibitoci suna bawa mutane magani na rashin lafiyarsu"
Shiru ma tayi tana kallon yar tata amma fa duk jikinta yagama yin sanyi sai dai bata jin zata iya barin addinin datake kai,
Mikewa tayi ta shiga dakinta batare da tayi magana ba hakan yasa bahijja daga hannu tana addu'ar Allah yasa itama ma ta amshi Kalmar shahada.
Daren ranar kasa bacci tayi tunanin abbunta kawai take yi gashi dan jaraba takasa mantawa da kyakkyawan yanayin da kullum suke kasancewa aciki kamar yadda shima jabir din yana can yana tunaninta acikin ranshi gashi gidan gaba daya yanzu jinsa yake ya zame masa wani shiru kamar makabarta,
Alwala ta dauro tazo tafara sallar dare domin takasa yin baccin, ta dade acikin sujjadarta tana rokon Allah kan ya daidaita tsakaninta da mijinta ya kawo zaman lafiya mai dorewa atsakaninsu.
Babu laifi yanzu ta samu sakin fuska awurin ma domin har suna zama suyi hira hakan da ta samu yasata cigaba da yiwa ma nasiha akan addinin musulunci saboda ta fuskanci yanzu tafara yin sanyi,
Kullum ita kenan acikin ibada,sallolin nafila irinsu walaha ga azumin litinin da alhamis da take yi, satinta biyu da dawowa gida ta tashi da wani azababben ciwon ciki wanda take jin kamar mutuwa zatayi tabar duniyar,
Mota babanta ya samo suka kinkimeta shida 'ma' suka sakata aciki suka nufi asibiti da ita, 'ma' sai kuka take yi tana rirriketa,
_Dr Tafida females & children's care hospital_ suka kaita, ana shigar da ita dakin da za a dubata 'ma' tafashe da wani sabon kuka tana leka dakin,
Mintuna kadan da shigar da ita wata likita mace tafito tana kiran mahaifan bahijja, binta suka yi zuwa wani office,
"Am ina mijinta? Muna son zai yi mana signing saboda theatre zamu yi mata"
"Baya nan sai dai ni, ni mahaifinta ne?" Papa ya ce da likitar wacce take kyakkyawa mai mutukar fara'a,
"No mijinta muke so yayi signing din" tafada tana Ciro wani file agabanta,
"Bari anemoshi, bari akirashi"
Fita papa yayi ya fara neman jabir awaya amma dakyar ya sameshi, yana dauka ya sanar da shi abinda yake faruwa,
Arikice jabir yabar aikin da yake yi ya taho asibitin dama sam baya cikin nutsuwarshi aikinma kawai yinsa yake amma bawai dan dadi ba sanin idan ya zauna agida kewa da kadaicin bintinshi ne zai dameshi shiyasa yake zuwa office din,
Yana zuwa ya samu papa yana tsaye yana jiransa, jagora yayi masa zuwa office din dr hanfa, tare da mijinta dr tafida suka sameta suna tattauna matsalar bahijja,
"Kaine mijinta?" Dr hanfa ta tambayeshi,
"Ehh nine" jabir yabata amsa,
"Ok zo muje to" dr tafida yafada tare da fita, bin bayanshi jabir yayi zuwa office dinsa,
"Wato ita wannan matar taka nayi scanning nagano tana dauke da wani k'ari acikin mahaifarta wanda indai wannan k'arin yana nan to bazai taba barinta ta haihu ba, duk lokacin data samu ciki to zubewa zai rinka yi, gashi har k'arin ya fara girma"
Wani yanayine ya zuyarci jabir naban mamaki,
"Dr ban gane abinda kake son fada ba"
"Ina nufin yanzu dole sai mun yiwa matarka theatre mun cire mata k'arin dake mahaifarta domin shine yake sanya mata ciwon ciki dana mara wanda wannan ciwon zafinsa zai rinka sanya mata yin miscarriage, shiyasa muke cewa mata da zarar sun fara fama da rikicewar al'ada to su zo asibiti domin hakan yana haifar musu da matsala"
Turo masa wani file yayi anan jabir yayi signing yatashi ya fita lokacin tuni har anwuce da bahijja zuwa dakin da za ayi mata aikin,
"Allah sarki bintina na hukuntaki akan laifin da ba nakiba, Allah yasa ayi miki aikin nan acikin nasara afito dake nikuma nayi alqawarin baki kulawar da tafi wacce nabaki ada" yafadi hakan acikin zuciyarshi,
Suna tsaye awurin 'ma' sai kuka take tana zagaye wurin takasa zama, shi kansa jabir ya kasa zaman domin rabonshi da bintinshi tun sati biyu da suka wuce, hakika yasan ya hukuntata da hukunci mafi tsauri agaresu shida ita,wani irin zazzafan tausayinta yaji yana ratsashi da wata irin sabuwar soyayyarta wacce bazata fasaltu ba.
Karfe 3 daidai dr tafida yafito daga theatre din da yashiga yiwa bahijja yana rikeda hannun matarsa dr hanfa wacce suke tafe tana goge masa zufar dake tsattsafowa agaban goshinsa domin jin cikakken labarin wadannan ma'auratan likitocin duba littafin ummi Aisha _(Alheri dankone)_,
Cikin hanzari ma da papa da jabir suka doshesu domin jin halinda bahijja ke ciki.
_Ina cigiyar safiyya ummu Abdoul, idan sak'ona ya riskeki my regards to you!_
_*Ummi Shatu*_ππ»
[10/26, 8:43 PM] Ummi A'ishaππ»: *WANI HASKE*
_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_
_126-130_
_(second to the last page)_
~~~Kowannensu fuskarsa dauke da alamun tambaya suke kallon dr tafida,
"Dr ya akayi? Wanne hali binti take ciki yanzu? Anyi nasarar cire karin daga mahaifarta?"
Wadannan sune jerin gwanon tambayoyin da jabir ya zayyanowa dr tafida alokaci guda,
"Dr kafada mana halin da my daughter take ciki" ma tafada cikin tashin hankali,
"Duk ku kwantar da hankalinku patient dina tana nan lafiya, anyi aiki cikin nasara amma sai nanda 4 sannan zata farfado"
Sai alokacin dukkaninsu suka samu nutsuwa, wata sanyayyiyar ajiyar zuciya jabir yayi domin hankalinsa da ba karamin tashi yayi ba gani yake kamar ya rabu da bintinshi kenan har abada,
Masallaci yatafi yaje yayi salla ya fito daga nan kasuwa suka wuce bayan ya biya ta bank ya ciri kudi,
Kayan dubiya irin wadanda wanda aka yiwa tiyata zai iya ci ya sissiyo mata da sauran kayayyaki marassa nauyi,
Sai da yakoma asibitin ya kaiwa su 'ma' kayan ya biya kudin aikin da aka yiwa bahijjan da kudin magungunan da za abata sannan yatafi gida domin yin wanka,
Agaggauce yayi wanka ya shirya ya fito tsaf cikin farin yadi mai laushi shara shara wanda ya bayyanar da farar vest din da yasaka, kamar yadda ya saba komai nasa fari yasaka tun daga kan agogonshi har zuwa takalmin kafarsa hularshi ce kawai light blue mai ratsin fari ajiki, turaren _Special oud_ da _muqalatul shaikha_ yayi amfani dasu ya feshe jikinsa dasu,
Lokacin da ya koma asibitin misalin karfe 5:30 na yamma yasan yanzu dai bintinshi ta farfado, da Anty Bilkisu yayi clash ahanya hannunta dauke da flask din abinci,
Ganin 'ma' da papa suna dakin da bahijjan ke ciki ya sakashi kin shiga domin shi mutumne mai alkunya da kara,yafi minti 10 atsaye awaje yana jiran fitowarsu,yana nan tsaye har papa ya fito ya sameshi,
"A'a malam jabiru ya kake tsaye anan? Ka karasa ciki mana ai ta farfado"
Papa yace dashi yana murmushi fuskarsa cikeda annashuwa,
"Allah ya kara bata lafiya" jabir yafada yana kokarin shiga cikin dakin,
"Amin, amin" papa ya amsa yakara gaba,
Kofar dakin ya bude ya shiga idonshi fes akan gadon da bahijja ke kwance mamanta tana gaban gadon tana tattare mata rigar da tasaka mata sannan tana kokarin gyara mata zanin jikinta gudun kar ya rinka gogar wurin da aka yi mata aikin,
Anty Bilkisu ce ta tura masa kujera ya zauna yana gaisar dasu, bahijja najinshi yana magana cikin wannan sanyin muryar tashi kamar marar laka ajiki,
Dauke kanta tayi tayadda ma ba zasu iya hada ido ba, ganin yadda take cikinta awaje, kasan cikinta awaje yasa jabir jin wani irin kishi yana taso mishi, yanzu shikenan wani ya kalle masa cikin bintinshi da mararta,
Fita anty bilkisu tayi 'ma' itama ta mara mata baya, suna ficewa ya tashi daga kan kujerar da yake ya nufi gadon da bahijja take kwance,
"Sannu bintina, ya jikin naki?" Yafada ahankali cikin sanyin muryarshi bayan ya rankwafar da kanshi kusa da fuskarta,
Idan gadon da take kai yayi magana to itama tayi magana, shiru tayi masa ta rabu dashi amma kuma yanda ya kusanto jikinshi da nata yasata cikin wani irin wahalallen yanayi ga wani kamshi mai dadi wanda yake fita daga