Author : Hameedah Category : Complete Novels
ayi da auren mai mata yanzun ma tasan yana can tare da matarsa ita kuma gashi tun zuwanta gidan babu abinda ya taba hadasu"
Tafada acikin ranta, haka ta zauna ta bata lokaci da yawa tana cikin yanayi na bacin rai,
Lokacin da taje bacci ma ta dade bata yi baccin ba juyi kawai take tana tunanin jabir, pillow taja ta rungume tana tuno mijinta abin sonta.
*
Tunda satin da jabir zai dawo ya kama tafara shirin tarbarsa, kullum sai ta shirya masa kayan dadi amma shiru sai taji babu alamunsa, yauma sai da tayi masa girki tayi kwalliya sosai amma har 9 shiru,
Wayarshi ta kira yana dauka ta fara kukan shagwaba,
"Abbu bazan sake yi maka girki ba har sai ka dawo, kullum sai nayi sai kaki dawowa"
Sai da tsikar jikin jabir ta tashi saboda yanda take masa wannan kukan shagwabar,
"Binti dama ai cemiki nayi acikin satin nan ban fada miki date dinba, kidaina wahalar da kanki, ki bari kawai duk ranar da nadawo sai kiyi min girkin ina gidan, kinji?"
"Nidai abbu ban yarda ba ka fada min" ta sake fada cikin shagwaba,
"To ai kinga saura 3 days week din ya kare, dan haka may be gobe zan dawo ko jibi ko...."
"No abbu nidai ban yarda ba ka fadamin Allah"
Lumshe idanunshi yayi acikin ranshi yana cewa "yarinyar nan tana son tayar min da hankali fa" amma afili sai yace,
"Kwana uku ne fa kawai binti ai kinga nabaki satar amsa"
"Ok to nadauki jibin, gobe bazan yi maka girkin ba, sai jibi, idan ranar ma baka dawowa shikenan ko ranar da zaka dawo bazan yi maka ba"
Duk wadannan maganganun cikin kukan shagwaba tayi su,
"Haka kika tsara?"
"Ehh abbu" tasake fada cikin sigar farko, ita kanta wani iri takeji ajikinta bare kuma jabir wanda ko kwakkwaran motsi ya kasa,
"Ohhhhh abbu my cooking, girkina ya fara konewa, bye bye" wayar ta katse ta ruga kitchen da gudu inda take dafa indomie guda daya tal dan shegen kwadayi,
Bin wayar jabir yayi da kallo yana murmushi tareda tuno shiririta irin ta goodness.
Aranar da zai dawo wani boutique ya shiga ya kwaso mata english wears hadaddu _(sexy dress)_ masu kyau da aji domin yasan bata saka atamfa ko shadda kullum cikin kananan kaya take,
Wasu kyawawan braziers yagani amma yana tantamar ko zasu yi mata daidai kuwa saboda yaga ita din bata wasa bace, braziers din sunyi masa kyau sosai domin masu daukar hankaline, diba kawai yayi aranshi yana tunanin idan sunyi mata kadan tasan yadda zata yi dasu,
Akwati guda ya ciko mata da kananan kaya bayan shima ya lodi nashi, gida ya koma inda ummu ke jiranshi ita da al'amin duk tabi ta damu saboda tafiyar da zaiyi ya barta,
Hannunta ya kama ya kwantar da kanta agefen kafadarshi al'amin kuma yana kan cinyarshi,
"Haba Ummu menene abin damuwa ne?"
"Abu al'amin dan Allah kadawo hajji, zamu yi kewarka nida al'amin"
Murmushi jabir yayi "ummu ba lallai ne nazo aikin hajji ba saboda wasu dalilai masu yawa, kiyi hakuri idan sabuwar shekara ta kama zan turo muku kudi sai kuzo gida"
"Yawwa abu al'amin Allah ya saka da alkairi, Allah ya kaika lfy"
Ya dade tare dasu yana rarrashinsu kafin yayi wanka Ya shirya suka rakashi har airport, wani kwalin chocolate al'amin ya bashi wai ya kaiwa goodness, murmushi jabir yayi,
"Ohh Al'amin ka rasa abinda zaka bawa antyn naka sai chocolate?"
"Abbu anty mayyar chocolate ce wani lokacin ko abinci bata ci sai dai tai ta shan chocolate"
"To shikenan al'amin zan kai mata"
Sallama yayi musu ya shige cikin jirgi, Ummu harda yar kwallar ta yayinda al'amin keta daga masa hannu, suna nan tsaye har jirginsu ya tashi,sai da suka ga tafiyarsa sannan suka koma Gida.
K'arfe uku na yamma jirginsu ya sauka yayiwa driver waya yaje ya daukoshi,
Tana falonshi ta baje akasan carpet tana bacci daga ita sai yar body hug dinta baka da short trouser milk colour, dama tana hutun salla,
Yana saka kansa cikin falon ya hangota, idonsa ya sauke akan lukuta lukutan cinyoyinta wadanda suke afili domin wandon data saka iya rabin cinyoyinta ya iya rufewa,
"Masha Allah"shine kawai abinda ya iya fada bayan ya lashi lips dinsa,
Ciki ya karasa ya tsaya akanta yana karewa halittarta kallo kamar yau ya soma ganinta,
Babu zato tayi wani juyi tare da wata mika nan rigar jikinta tayi sama cikinta ya bayyana,
"La ilaha ilallah, muhammadur rasulillah"
Shine abinda yaji ta fada, ahankali ta soma bude idonta, shidai jabir mutuwar tsaye yayi saboda jin abinda ta fada,
"Lahh abbu yaushe ka dawo?" Tafada tana kokarin tashi zaune,
Kan kujera ya karasa ya zauna yana kallonta,
"Yanzu shigowata kenan yar lukuta"
Bakinshi ta kalla ta hadiyi yawu ita dai aduniya tana son bakin nan na jabir, duk ranar data kamashi babu sauki ta ayyana hakan acikin ranta,
"Sannu da zuwa, bari naje nayi maka girki abbu" tashi tayi tana sake yin wata mikar ta fita, kitchen ta shiga duk tana cike da murnar ganinsa jinta take kamar anyi mata albishir da gidan aljanna,
Kasancewar tanada kayan amfaninta wanda zata bukata yasata dora jalop din shinkafa da kayan lambu, sai murna take har ta yanke hannunta wurin yanka cabbage,
Tana kokarin yanda zata yiwa yatsan nata jabir ya shigo cikin kitchen din,
"Yankewa kika yi?"
Boye hannun tayi ta bayanta ta jiyo tana kallonshi, bata son ya gani saboda kar yace sai ya saka mata hydrogen,
"No abbu" tafada tana raurau da idanuwanta,
"Ya salam" yafada acikin ranshi,
"Bani to ingani, bazan saka miki hydrogen ba Allah"
Fito da hannun tayi ta mika masa, rike hannun yayi ya fito da ita zuwa falonta, dan kyalle ya samu ya daure mata wurin ita dai tana daga tsaye tana kallonshi yana sanye da jallabiya ruwan kasa kansa babu hula amma ba karamin kyau yayi mata ba ahakan,
Kitchen ta koma ta ci gaba da girkin da take yi shikuma jabir ya fita zuwa masallaci domin lokacin sallar la'asar yayi,
Bayan ta sauke girkin sai da ta hada lemon kwakwarta kamar yadda ta saba amma na yau harda jabir tayi shi,
Wanka ta shiga tayi ta fito daure da towel sai ga jabir ya shigo sashen nata,
Dan doddoka kafafunta akasa tafara yi tana rike towel din jikinta,
"Abbu bana salla kabani pad"
Dama can ai ba sallar kike yi ba ya fadi hakan aranshi amma afili cewa yayi,
"Ke wai kullum acikin jini kike ne? Koda yaushe jini,koda yaushe jini sai kace wata marar lafiya"
Farr tayi da idanuwanta tana matse cinyoyinta gudun kar tayi staining,
"Abbu lafiyata k'alau, ni sau biyu nake yi awata"
Tab nashiga uku kenan, yafada aranshi danma shi ba mai yawan bukata bane, sai yayi wata bai bukaci mace ba wani lokacin ma zai iya yin fiyeda haka,
Kallonta yayi sai ya hango jinin yana bin cinyoyinta,
"Ina zuwa bari na kawo miki" juyawa yayi ya fita, yana fita ta fashe da dariya dama tana sane tayi masa haka saboda tun lokacin da yayi mata maganar wannan ta ukun da yace zai aura ta daura aniyar haukatashi da salonta kala kala wadanda anty Bilkisu ta koyar da ita,
Tana nan a inda yabarta har ya dawo yana rike da pad din guda biyu,
"Gashi,amma haka wannan abin yake yi miki rushing?"
"Ehhh abbu amma zuwa kwana ukune, yana yin kwana uku zai daina"
Juyawa yayi ya fita baice da ita komai ba, nan tasake komawa toilet tayi wani wankan ta fito, shiryawa tayi cikin riga da wando na jeans baki rigar kuma light green mai gajeren hannu,
Abincin da ta shirya ta dauka ta nufi sashen jabir, yana zaune yana waya dasu al'amin da ummu, abincin ta ajiye ta tasashi agaba kamar zata shige cikin cikinsa, abin har dariya yaso bashi gashi ta wani kafeshi da ido duk motsin da bakinsa yake yi akan idonta ne,
Wayar ya mika mata yaja abincin ya zuba ya fara ci yana sauraren hirarta itada al'amin wanda gaba daya yarintace aciki,
Har yagama cin abincin bata gama wayar da al'amin din ba, lemon kwakwar da tayi yasha madara dan haka ba karamin dadi yayiwa jabir ba, sai da ya shanye rabin jug amma abincin kadan yaci,
Kan doguwar kujera ya koma ya zauna ya kamo huda tv yafara kallon wani program da suke yi alokacin mai taken _Da'awah workshop_,
Yana jin lokacin da goodness tagama wayar ta ajiye,guntun abincin da ya rage acikin filet tasa hannunta zata ci sam ta manta da yankewar da tayi dazu a yatsanta, tana saka hannunta taji yaji ya ratsa wurin, babu shiri ta zubar abincin ta zabura tayi inda jabir ke zaune,
Tana zuwa tasaka kuka tare da zama akan cinyarsa,
"Abbu yaji..."
Hannun ta mika masa tana kuka,
Rike hannun nata yayi baiyi wata wata ba yasa dan yatsan abakinsa ya fara tsotse mata shi,
Kanta ta kwantar acikin kirjinshi tana jin wani sanyi har cikin ranta,
Tsotsar dan yatsan nata yaci gaba dayi yanayi yana hura mata iskar bakinshi a wurin, acikin zuciyarsa kuma yana tuna rak'i irin na mata su mata babu wuya sun yiwa abu kuka komai kankantarsa.
In banda haka menene abin kuka dan yaji yashiga wurin da ta yanke,
Cusa kanta cikin jikinshi take tayi tana shakar kamshin turarensa na _beautiful touch_ wanda ya cakudu da kamshin _special oud_ ita dai arayuwarta tana tsananin son jabir domin jin sonshi take har acikin jinin jikinta yana yawo,
Mak'aleshi tai tayi shikuma sai tsotsar yatsan nata yake yana hura mata iska awurin, gaba daya ta gama shagala sai kamshinsa take shaka mai mutukar dadi, hakika babu abinda yafi kamshi dadi ajikin mutum musamman ma Ma'aurata amma wasu mazan sam tsafta bata damesu ba harma wasu matan suma duk samma kal, ya kamata arinka kulawa da tsafta domin tana daga cikin imani inji fiyayyen halitta, sannan turare abune da yake kara soyayya, duk lokacin da mutum ya kasance mai mu'amula da turare to kowa zakaga yana burin zama kusa dashi amma idan sabanin hakane to mutane basa kaunar hada wurin zama dashi,
Tana ta yan tunane tunanenta idonta a lumshe bata san lokacin da bacci ya dauketa ba shi kansa jabir bai san tayi baccin ba kawai dai yaji shiru ta daina kakkamashi sabanin dazu data rinka kankameshi tamkar zata koma cikin cikinsa,tana faman cuccusa kanta acikin kirjinsa,
Yana rikeda hannun nata acikin tattausan hannunsa wanda yafi na baby pherty Xarah laushi, dan yatsan abakinshi ya dago manyan idanuwanshi ya kai dubansa gareta nan yaganta tana bacci abinta,
"Wuh binti case, komai kuka kike masa, hydrogen kuka, pepe kuka,ruwan zafi kuka, zan so naga ranar da zaki je maternity" ya fada ahankali kamar da wani yake maganar, koda yake matanfa kenan,ya ayyana hakan aranshi,
Zare dan yatsan nata yayi daga bakinshi ya zameta daga jikinshi ya kwantar da ita akan doguwar kujerar ya tsaya yana kallonta yana tunanin anya kuwa idan tayi kwakkwaran juyi ba zata fado ba,
"Kai ai yarinyar ce ta fiya lukutanci yanzu idan nace zan kaita daki wuya zansha, kila ma ta tashi tai tayi min rikici" ya fadi hakan acikin zuciyarshi,
Rabuwa yayi da ita ya shiga cikin _bedroom_ dinshi yayi wanka yasha manyan kaya, dafaffen boyel light blue riga da wando harda babbar riga, hularshi samfarin dinkin zannabukar itama light blue,agogon da ya daura na azurfa ne kirar kamfanin _Gucci_ ,kamar koda yaushe turare masu dadin kamshi da sanyi ya fesa, yasaka takalmi half cover light blue ahankali ya fito daga cikin dakin nasa idonsa akan goodness wacce take mike tana faman bacci,
Sadaf sadaf ya fice daga falon domin yasan idan har ta tashi cewa zata yi sai tabishi,
Fita yayi shida mal idi driver, shagon aski ya fara zuwa bayan ya fito kuma ya nufi gidan mahaifinsa,
Acikin babban falonshi ya sameshi zaune yana hutawa amma hannunsa kuma rike yake da carbi yana ja,
Bayan yan gaishe gaishe ne Malam yake ce masa,
"Kaga abinda nake fada maka ko jabiru? Yanzu gashi ta sanadiyyarka musulunci ya samu karuwa, dama shiyasa tun farko nace kayi hakuri wannan yarinyar *wani haske* ce agareka kamar yadda kaima kake *wani haske* acikin rayuwarta, sanin kankane duk mutumin da yayi sanadiyyar da wani ya shiga musulunci yanada rabo mai girma, rannan kawai ina zaune sai ga yarinyar nan tazo min da magana mai dadi cewar zata karbi musulunci, agaskiya nayi farin ciki kuma dan Allah jabiru ka zauna da yarinyar nan zama na amana, tunda yanzu kasan dole zata fuskanci matsalar rayuwa dalilin shiga musuluncin da tayi, sannan kuma yanzu ta amshi sunan mahaifiyarka, wato BAHIJJA, nasan ta sanar dakai komai"
Tunda Malam yafara wadannan bayanan jabir sakin dan mitsitsin bakinshi yayi yana kallon malam domin bashida masaniyar duk wadannan abubuwan, haba lallai biri yayi kama da mutum tunda dazu lokacin da ya tarar da ita tana bacci tana farkawa da salatin annabi ta fara,bayan haka kuma lokacin da zata karbi pad awurinshi ce masa tayi yau bata salla,sannan lokacin da yana madina tafada masa cewar yanzu ta koma bahijja sai dai shi sam bai yarda ba ashe dagaske take, wani farin cikine marar misaltuwa ya soma shigarsa ga wani yanayi da ya samu kanshi aciki, kyakkyawar fuskarta ya shiga hangowa acikin zuciyarsa,
"Jabiru lafiya?" Malam ya tambayeshi jin yayi shiru bai bashi amsa ba,
Sai alokacin ya dawo cikin hayyacinshi,
"Lafiya lau malam, Allah ya kara girma, Allah yasa ta shiga musuluncin kenan har abada kuma Allah yasa ta mutu akansa"
"Amin jabiru",nan Malam yayita saka masa albarka yana yi musu kyakkyawar addu'a shida iyalansa, awurin malam yayi zamansa bai koma gida ba har wurin 9 nadare.
***
Tunda jabir ya fita ya barta take bacci sai daf da magrib ta iya tashi, bude idonta tayi taganta akan kujera,
Tunowa tayi da abinda ya haddasa mata barcin, wani murmushi tayi tana mai kallon dan yatsan nata wanda jabir dazu yayita tsotsa kamar ya samu sweet, "tabbas maganar Anty Bilkisu ta zama gaskiya" tafada cikin zuciyarta domin itace ta bata wannan sirrin cewar awurin mijinta ta zamto yar karamar yarinya tamkar yar 14,sannan ta dimamci shagwaba kamar yar yaye hakan zai sa miji ya mace akan kaunarta,
Yanzu gashi tun ba aje ko inaba har tafara ganin amfanin shagwaba,murmushi ta sake yi akaro na biyu ta tashi taje wurin abincin da tabari dazu bata ci ba, dauka tayi taci ta koshi sannan ta kwashe kwanukan ta nufi sashenta aranta tana tunanin yadda akayi jabir yabar gidan batare da taji motsin fitarsa ba,
Sabon wanka tayi ta hade cikin wata doguwar riga ja mai siririn hannu, tattauran gashinta ta kama ta tufke tanayi tana tsaki domin duk ya yi under grow, dolenta tasaka masa relaxer indai tana son taji sawaba gashi gashin mai cika ne cukus,
Turarruka masu kamshi ta dan feffesa amma sai taji kamshinsu baiyi mata dadi irin na jabir ba, sashensa taje ta shiga _bedroom_ dinshi taje gaban mirror ta dauki nasa ta feffesa nan dakin ya gauraye da kamshinsa,
Fitowa tayi yanzu jinta take kamar suna tare dashi saboda ga irin kamshinsa nan tana shaka,
Part dinta ta koma ta kunna kallo yanzu bata yin kallon ma da yawa sama sama take yinsa, ganin har 9 tayi yasata fara tunanin to ina jabir ya tafi kodai wurin ta ukun ya tafi ne, itafa ta ukun nan ta shiga ranta tun lokacin da jabir ya fada taji ta kasa mantawa da maganar.
Tana nan zaune ita kadai tana kallo har 9:30 tayi,
Idonta kyar akan tv ko kiftawa bata yi ya turo kofar ya shigo tun kafin yayi sallama kamshin turarenshi ya ziyarci hancinta,
Dagowa tayi ta kalleshi lokacin da yake rufe kofar bakinshi dauke da sallama,
Sallamar ta amsa tana mai cigaba da kallonsa yau dinnan ba karamin kyau yayi ba cikin blue din boyel din da yasa,
"Wowww....!" Tafada ahankali tana kallonsa,
Zama yayi akan kujera "wato bakya jin magana ko? Har yanzu kina nan da wannan mayen kallon Daren da kikeyi ko? Dama baki daina ba?"
Kallonsa ta sake yi kamar yaune tafara ganinsa "abbu wlh ba nayi, anadade inkai 11"
Tafada cikin shagwaba,
"Ahaf" kawai yace ya mike zai fita,
Mikewa tayi da sauri, "abbu tsayani mu tafi tare"
Kayan kallon ta kashe ta bishi suka fita tare, a falonshi ta zauna ta fara duba kayan ciye ciyen da ya shigo dasu, kaza ce gasasshiya da fruits su kankana, apple, banana, oranges da sauransu, sai kuma chocolate wanda tasan ko ba afada mata ba ita ya siyowa,
Filet da fork ta dauko da wuka ta zauna ta yanyanka masa fruits din tabar sauran da zummar gobe zata yi musu lemon kankana dasu,
Tana tsaka da shan chocolate dinta ya fito sanye da kayan bacci, _maroon_ colour masu santsi riga da wando, tana kasa akan carpet azaune shi kuma yana kan kujera zaune, akan stool din gabanshi ta ajiye masa fruits din takoma ta zauna taci gaba da shan chocolate dinta sai da tasha da yawa sannan ta fara cin gasasshiyar kazar, yana zaune yana kallonta ta gefen ido yanda bama zata san yana kallonta dinba,
Sai da taci rabin kazar sannan ta tashi ta dauki tsinken sakace hakori tafara sakatar hakorinta tana son cire naman da ya makale mata ahakori, kasa cirewa tayi dan haka ta matsa kusa da jabir,
Kneel down tayi agabansa ta mika masa tsinken,
"Abbu pls ka cire min, nakasa cirewa"
Kallonta yayi ya karbi tsinken "oya bude bakin" budewa tayi ta daga kanta ya fara cire mata, ido ta runtse ta dafe hannunsa wanda ya dafe kanta dashi,
"Ko sakacen hakorin ma kuka zaki yi masa?" Ya tambayeta yana mai sake tura tsinken matsematsin hakorinta,
Janyewa tayi ta matsa gefe "abbu barshi haka, idan nayi brush zai fita"
Tashi tayi ta kwashe sauran kayan ta fita taje bedroom dinta tayi brush ta sake shafa turare ta dauko wata arniyar rigar barci _coffee_ colour mai santsi wacce sai ta baya ma ake daureta da madaurinta, bata da wani girma dan iya gwiwa take sannan siririn hannu gareta,
Yar karamar hula ta dauka ta saka akanta takoma sashen jabir, acikin dakinsa ta sameshi zaune agefen gado gabanshi laptop ce a ajiye yana dubawa,
"Abbu daure min rigata ta baya nakasa daurewa"
Dagowa yayi yana kallonta, wani irin kyau yaga rigar tayi mata gashi tayi mata cif cif komai yaji,
Shagala yayi lokacin da yake d'aure mata rigar, saboda gaba daya gadon bayanta a bayyane yake gashi wasu zarirrika ne wanda suke a tagaban rigar suka taho har ta baya,kwata kwata ma ya kasa d'aurewar, idan ya d'aure sai ya kunce sai ya sake d'aurewa haka yayita yi har wurin sau goma, ita dai goodness tana zaune ta juya mushi baya tana jiran ya gama,
Dakyar ya iya hakura ya d'aure mata ya janye hannunshi