Wani Haske Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Hameedah Category :  Complete Novels

Chapter   28 / 35

81K to 84K   out of 102.7K words

kallo domin bakar doguwar riga irinta larabawa tasaka da dan karamin hijab, hannunta rikeda na al'amin, ko ba a fadawa Ummu ba tasan bahijja ta musulunta domin ta tabbatar da ace bata musulunta ba to da babu abinda zai saka jabir yazo da ita,

Ahankali suke tafiya har suka karasa inda su ummu ke tsaye, da gudu al'amin ya fusge yaje ya rungume bahijja yana murna, ita dinma rungumeshi tayi ta dagashi ta saba akafadarta duk kuwa da cewar yanzu ya dan kara girma,

Dukkaninsu daga ummun har jabir tsayawa suka yi suna kallon al'amin da bahijja saboda yadda suka manta dasu sai dariya suke yi suna kara rungume juna,

"Anty ashe dama kema zaki zo? Anty kema kina salla yanzu ko?"

Al'amin ya tambayeta yana rungumeta,

"Ehh al'amin, me kakeci hakane naga ka sake zama kato?"

"Anty shinkafa kaza kema idan kina so ummu na zata dafa miki ta iya sosai"

Dariya tayi ta saukeshi kasa,"ohh al'amin ashe har yanzu dai kana nan da labarin nan ko?"

"Kuzo mu karasa gidan tukunna" muryar ummu ta katsesu kafin al'amin yabada amsa, tare suka jera suka nufi wurin da zasu samu taxi suhau,

Ganin yanda ummu ta shige jikin jabir tana yi masa rada suna dariya yasanya bahijja jin wani kololon bakin ciki yataho ya tokareta akirji, ita kam badai zafin kishiba musamman ma akan jabir,

Suna tsaye abakin titi tana rike da al'amin da yar trolley dinta tana kallon yanda jabir yasakala hannunshi tabayan ummu ya karata jikinshi sai rade rade suke yi suna dariya, duk ji tayi tsayuwar ta isheta alla alla take su samu taxi su isa gida dan ta daina ganin wannan abun haushin,

Sun dade atsaye kafin suka samu taxi, jabir ne ya shiga gaba sukuma suna baya azaune har lokacin al'amin yana manne da ita,

Tafiyar da batafi ta mintuna 20 bace takaisu kofar gidan da ummu take, nan suka firfito ita dai bahijja kallon garin kawai take tabbas wannan gari mai ni'ima ne domin iskar dake kadawa ma aciki daban take da sauran iskar dake kadawa aduniya, jabir ne ya biya mai taxi din sannan suka dunguma zuwa cikin gidan,

A falo suka yada zango inda ummu ta shisshirya musu kayan tarba kala kala, abincin larabawa tayi musu iri iri wani kuma ta siyo musu a restaurant,

Bin dan madaidaicin gidan bahijja take yi da kallo aranta tana tunanin gaskiya indai mutum yana zaune awannan wurin babu abinda zai dameshi shiyasa ummu da al'amin sukayi fes dasu gashi al'amin larabci abakinsa kamar sudais,

Abincin ummu ta fara zuzzuba musu, tana cewa,

"Antyn al'amin anzo lafiya? Ya mutanen gida?"

"Lafiya lau maman al'amin, kowa lafiya" bahijja tabata amsa tana gyarawa al'amin zama ajikinta,

Acikin babban faranti ummu ta zuba musu abincin dukkaninsu suka hadu suka fara ci ita dai bahijja duk jinta take atakure saboda yadda taga ummu sai rawar jiki take da ganin jabir, hakan yasata niyyar suna gama cin abincin nan zata nemi da anuna mata wurin zamanta domin ta tafi tabasu wuri,

Kallonsu take yi kasa kasa yanda ummu take manne dashi ta dora hannunta akan nashi tana wasa dashi gashi ko acikin kwanon abincin ma sai tsokanarshi take yi tana daukar spoon dinshi wai adole sai dai suci da spoon daya ita dashi,

Duk jin zaman tayi ya gundureta dan haka ta mike ta koma saman kujera ta zauna akujerar da tasan bazata cigaba da hangosu ba, al'amin ne ya biyota ya dale jikinta suka ci gaba da labarinsu.


Murmushi tayi takama hannuwan al'amin ta rirrike "al'amin kaga yanda ka zama kato kuwa? Sai kace irin kajin agric dinnan"

Dariya yayi yana jan mayafinta "hakama ummu na take cewa kullum"

Su jabir sun dade agaban kwanon abincin shida ummu suna dan taba soyayya,tashi jabir yayi yana kallon wurinda bahijja suke,

"Binti muje nakaiki masaukinki saboda ki samu kiyi wanka ki huta"

Yafada yana shafa sumar kanshi, kallonsa ta juyo tayi dama ta gaji da wannan zaman takurar dan haka batare da tace dashi komai ba ta tashi tana rike da hannun al'amin,

"Abu al'amin bari nazo muje mu kaita"

"To amma ki dan daukowa al'amin kayanshi koda guda 3 ne sai su zauna tare ya tayata hira" yafada yana kamo dayan hannun al'amin din,

"Al'amin ni bazaka kulani bane sai iya antynka zaka kula?"

Rungumeshi al'amin yayi yana cewa "abbu zan kulaka mana,ai tare zamuje da anty ko?"

Kafin jabir ya bashi amsa Ummu har tafito hannunta rikeda wata yar karamar jaka mai kyalkyali wacce ta zubowa al'amin kayansa aciki,

Dukkaninsu suka dunguma zuwa hotel din da za a kamawa bahijja daki domin gidan da ummu take ciki daki dayane sai falo da toilet da kitchen dama gidane na yan makaranta,

Wani hotel sukaje jabir ya biya kudin dakin ya karbi key suka dunguma zuwa dakin, sai da suka shigar dasu har ciki suka dudduba yanda tsarin dakin yake sannan suka yi musu sallama zasu tafi, ko jiyowa bahijja bata yi ba ayanda take ta juya musu baya tana ninke zanin gadon da suka samu acikin dakin domin shinfida nata,bata ko jiyoba tace su gaida gida domin bata ma son ta juya ta gansu saboda taga tun ahanya acikin mota suke wani shisshigewa junansu kamar wasu sabbin shiga,

"Abbu mu anan zamu kwana nida anty ko?"

"Ehh al'amin, bye bye ko"

Al'amin bai ko damuba saima daga musu hannu da yafara yana yi musu bye bye,

"Binti babu wani abu ko?"

"Babu" tafada atakaice, jan hannunshi ummu tayi suka fice daga cikin dakin suka tafi,zama bahijja tayi agefen gadon ta dafe goshinta kafin wani lokaci har hawaye sun fara sintiri akan kuncinta, al'amin ne yaje kusa da ita yana leka fuskarta,

"Anty bakida lafiya?"

Kai ta daga masa tayi sauri tafara share hawayen fuskarta, "idona ne yake ciwo al'amin"

"Sannu anty, ki fadawa abbuna ya kawo miki magani"

Kai ta sake daga masa amma bata kara magana ba domin ita kadai tasan yanda takeji acikin zuciyarta.

Dakyar ta iya tashi ta karasa gyara kan gadon ta tube ta shiga toilet tayi wanka amma acikin toilet dinma ta dan jima tana sharar hawaye sannan ta yi alwala tafito tadawo cikin dakin amma al'amin baya ciki, falo ta leka anan ta hangoshi ya kunna tv ya kwanta yana kallo,

Simple make up tayi tazira riga kalar ruwan madara marar nauyi doguwa tayi salla ta kwanta domin kanta ciwo taji yana yi mata saboda kukan da tayi,

Baccine yayi nasarar daukarta har lokacin sallar magrib yayi, sai alokacin ta iya tashi tana jin jikinta yana yi mata wani ciwo marar dadi ga kanta shima kamar zai fashe dan azaba.




_Masu karatu mu hadu ashafi nagaba domin jin karshen labarin wani haske, nagode sosai da kulawarku_





*_Ummi A'isha_*πŸ‘ŒπŸ»
[10/26, 1:51 PM] πŸ¬πŸ›πŸ’SalmaπŸ¬πŸ›πŸ’: [10/19, 4:35 PM] Ummi A'ishaπŸ‘ŒπŸ»: *WANI HASKE*



*_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*


_116-120_





~~~Ahankali cikin sanyin jiki ta sauko daga kan gadon tafara tafiya ahankali ta shiga bathroom, alwala tayi ta fito tana tafiya tana hada hanya saboda duhun da take gani agabanta sakamakon rufe mata idanuwanta da ciwon kan dake damunta yayi,

Azaune tayi sallar tana idarwa ta kwanta awurin tana rike da kanta saboda jinsa take kamar zai fice daga jikinta,

Al'amin ne ya shigo cikin dakin yana faman kwala mata kira,

"Anty zo muje muyi kallon tom and jerry...!"

Ganinta kwance tana hawaye yasashi yin shiru ya karasa kusa da ita,

"Anty har yanzu bakida lafiya?"

Kai ta daga masa sannan ta bude bakinta dakyar tace "al'amin anyi salla fa, ka bar kallon nan kaje kayi salla"

Hannunta ya kamo yana kallon "nayi sallar ai anty yanzun nan nadawo daga masallaci"

Zama yayi ra'as agabanta yana kallonta, "anty ki yiwa abbu na waya ya kawo miki magani"

Kasancewar bata son surutu yau yasata daga masa kai, wayar ta yaje ya dauko mata ya kawo mata sai alokacin ma tagane ashe kiran bazai yiyu ba,

"Al'amin bazan samu abbu awaya ba sai dai mubari har sai lokacin da ya gama abinda yake yi yazo"

Tana fadar maganar ne cikeda damuwa domin hawayene ke bin kumatunta,rike hannunta al'amin yayi yana girgizashi,

"Anty inyi miki addu'ar kamun kai?"

Kai ta daga masa, hannunsa yasa ya rike kan nata ya fara yi mata addu'a tana jinsa yayi bisimillah kafa uku sannan yafara karanto mata "As'alul lahil azim rabbil arshil azim an yashfiki" itama sau uku yana yi yana tofa mata a goshinta,

Babu laifi ta dan ji sausauci kam amma kuma ciwon da zuciyarta take yi mata ahalin yanzu ji take kamar tacireta ta yar,

Tana nan kawance al'amin akusa da ita suka fara jin bugun kofa, murna al'amin ya shiga yi "anty watakila abbuna ne yadawo"

Dagudu yaje ya bude kofa, ma'aikatan hotel din yagani masu bi daki daki suna raba abinci, nasu suka mika masa suka juya sukayi gaba,

Jikinsa asanyaye ya nufi wurin bahijja wacce duk tana jiyosu shida masu rabon abincin,

"Anty ba abbu bane, masu raba abincine"

"Al'amin ajiye abincin a falo bana son ganinshi,dama nasan ba abbu bane domin abbu bazai taba iya tunawa damu a wannan lokacin ba"

Tana maganar tana goge hawayen fuskarta, tashi tayi ta gabatar da sallar isha sannan tasake kwanciya a inda tayi sallar, kwanciyarta keda wuya wani naunauyan bacci yace muje zuwa,shi kansa al'amin shima baici abincin ba yana dawowa daga salla yayi kwanciyarsa a falo akan doguwar kujera.

Misalin karfe 2 nadare ta tashi daga naunauyan baccin da ya dauketa, bude idonta tayi tafara tuno jabir acikin kwakwalwarta, yanzu tasan yana can tare da ummu al'amin suna shan soyayyarsu,

Zaune ta tashi tayi tagumi tana karewa dakin da take ciki kallo, hakika kishi abune mai nauyin gaske wanda indai mutum baiyi takatsantsan ba zai iya halaka shi ta raya hakan acikin zuciyarta domin ita yanzu ji take ko kadan bata kaunar ganin fuskar jabir, haushinsa take ji sosai babu laifin tsaye babu na zaune,

Tana nan zaune tana karanta wasikar jaki zuciyarta ta shawarceta da taje tayi alwala tazo tayi salla ko dan koyi da jabir domin haka taga yana yi akowanne dare kai kusan ma baccinsa kullum ragagge ne bashida yawa, tsayuwar darensa tafi baccinsa yawa domin ko sunyi bacci tare to tsakiyar dare sai ya tashi yayi sallar nafilar da ta zame masa jiki,

Tashi tayi tafara bin jikin bango har ta shiga toilet din tayi alwala ta fito tazo kan abun salla, zata tada kabbara kenan taji motsi a falo, ahankali taje ta leka abun mamaki al'amin tagani shima yana tsaye yana sallar,

"Kyan da ya gaji ubansa" tafada ahankali gamida komawa cikin dakin tana tunanin babu ta inda al'amin yabar abbunshi a fannin dabi'u da halayya,

Salla tayi rak'a hudu domin kasala take ji ajikinta sosai, zama tayi tafara yiwa kanta da mijinta addu'a sannan tafara addu'ar Allah ya ganar da mahaifiyarta gaskiya itama tabi addinin da farin jakada masoyinmu na hakika annabi Muhammad yazo dashi.

Kan gado ta koma ta kwanta ta rungume pillow aranta tana tuna da agida ne da jabir zata rungume ba pillow ba amma yanzu gashi jabir dinma yayi mata wahalar gani balle har ta rabu jikinshi, shiru tayi tafara kiran sunayen Allah acikin zuciyarta amma yau tana ganin daren yayi mata tsawo da yawa ko dan bata tare da abin sonta ne, kasa komawa bacci tayi har asuba tayi ta tashi tai salla ta sake komawa ta kwanta. Har gari yayi haske idonta biyu, tana ganin al'amin yazo ya shiga toilet yayi wanka ya fito ya fara shafa mai ajikinsa,

"Inye ashe boy din nawa ya girma tunda yanzu ya iya wanka da kanshi" tafada tana kallonsa tana murmushi,

Juyowa yayi yana shafa mai akansa da fuskarsa "sabahul khair anty"

"Yau babu sch ne my boy?"

"Anty bama yin karatu ranar alhamis da juma'a, mu shine weekend dinmu"

Murmushi tayi tana kallonsa "hakan yayi kyau my boy, nima so nake natashi nayi wanka amma jikina duk a mace yake wallahi"

"Ki daure anty"

"To al'amin bari natashi" tafada tare da tashi ahankali ta shiga bathroom, bata wani jima ba tafito tana daure da towel, muryar al'amin ta jiyo daga falo yana cewa,

"Anty idan kin gama ga abinci an kawo"

"To al'amin" tafada tareda fara goge jikinta, mai ta dauko ta zauna agefen gado tafara shafawa,

Kamar a mafarki ta fara jiyo kamshin turaren gogan nata yana ziyartar hancinta ahankali ta daga kanta ta kalli kofar dakin,abbunta ta hango tsaye ya sha farar shadda riga da wando dinkin boda kansa ko hula babu ya zira hannayensa cikin aljihunsa,

Kicin kicin tayi da fuska ta bata rai, idonta ta dauke daga kallonshi ta mayar kan man shafawarta taci gaba da shafe jikinta dashi, ahankali ya tako ya karaso inda take yana murmushi,

Zama yayi agefenta daf da ita domin har tana jiyo jikinsa yana gogar nata, mai ta lukuto zata shafa yayi saurin rike hannunta,

"Haba binti yau ba zaki gaishe da abbun naki ba alhalin ba tare muka kwana ba, kawo na shafa miki man"

Batare da ta jiyo ta kalleshi ba ta bashi amsa "mantawa nayi, ashe fa ba tare muka kwana ba, ina kwana, mai kuma ka barmin kayana zan shafa"

Tunda tafara wannan bayanin ya zubawa fuskarta ido anan yagano kishi tsababa dankare akan fuskar tata hakan ya sashi yin murmushi,

"Binti me nayi mikine? Fushin nan naki na menene?"

"Ni me aka yimin da zanyi fushi? Ni babu wani fushi da nake yi"

Jikinta ya karasa shiga ya rungumeta, "idan ma wani laifin nayi miki to kiyi hakuri"

Man ya dauka ya fara shafa mata abayanta, bata yi magana ba har ya gama, yana jiyo da ita yaga kuka take, duk iya kokarinta na taga ta danne kishin dake azalzalar zuciyarta amma takasa dole sai da ya fahimta,

"Kiyi hakuri binti, jiya bakiyi bacci ba ko? Nima banyi baccin ba amma kiyi hakuri kinji, 3 weeks za muyi sai mu koma muci gaba da kwana tare, amma anan dinma gobe tare zamu kwana"

Da sauri ta kalleshi yana rike da hannunta yana kallon fuskarta, girgiza kai tayi

"Nidai indai nice na yafe ka zauna awurin ummun al'amin" azuciyarta kuwa tunani indai haka ta faru amma da ta cika marar hakuri da kawaici,

"A'a binti karfa ki cuci kanki ki fadi gaskiyarki"

"Kaji abbun nan, da karya nafada?",ta fada tana zumburo masa baki, kiss yakai mata akan bakin nata ta zille tana dariya,

"Binti ba zaki bari in baki good morning massage ba?" Yafada yana dan miskilin murmushi kamarsa,

"Abbu naki wayon" ta fada tana make kafada,janta yayi zuwa jikinshi,

"Binti fada min gaskiya jiya kinyi barci?"

Kai ta daga "nayi mana, me zai hanani bacci abbu?"

Fuskarta ya dago yana kallon idanuwanta, "binti karfa ki koyi karya domin karya babban laifi ce indai mutum yana karya to bazai gushe ba har sai mala'iku sun rubuta sunansa acikin littafi na makaryata, haka kuma idan mutum shima yana kwatanta gaskiya to bazai gushe ba har sai mala'iku sun rubuta sunansa acikin masu gaskiya, daga ganin idon nan naki bakiyi bacci ba, kar ki boye min binti fada min gaskiya, kinyi bacci jiya?"

Kanta ta kwace ta sunkuyar dashi kasa ta girgiza kai "abbu kasawa nayi, ban san dalili ba"

Kumatunta ya dafa da hannuwanshi masu laushi,"ni nasan abinda ya hanaki binti, kishine, amma akwai mafita, ki rinka yawaita fadin la ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin, ba ke kadai ba duk wata mace da take jin zuciyarta acushe muddin ta riki wannan tasbihin da yardar Allah zata samu saukin damuwarta"

"Nagode abbu" tafada idonta fal da kwalla,

"To kukan ya isa haka kinji, maza kiyi shiru, yau ba zaki sha chocolate din taki ba?"

Ya tambayeta yana jan hancinta, dago idonta tayi ta kalleshi cikeda kunya,

"Abbu kaga" ta nuna masa wani wuri, juyar da idonsa yayi, kafin ya juyo gareta har tayi digirgire ta taka kafafunsa takai bakinta kan nasa,

Ta jima tana tsotsar chocolate dinta kafin ta hakura tana kallonshi,

"Abbu wallahi kaima dogone sosai, kalli fa duk tsayin nan nawa a kafadar ka natsaya"

Kugunta ya rike yana murmushi, "ke dama ai ba doguwa bace, gajeriya ce"

Murmushin itama tayi ta rike hannuwanshi, "ahakan? Wallahi nima inada tsayi"

Sakinta yayi ya nufi jakar kayanta domin ciro mata wanda zata sa, tana daga tsaye tana gyara fuskarta sai aikin murmushi takeyi ita Kadai domin idan akwai abinda ta tsana to bai wuce rashin jabir akusa da ita ba, ita kanta takasa gane wanne irin so take yi masa,

Wata blue din doguwar riga arabian gown ya ciro mata sannan ya fara zabo mata inner wears, duk suma blue colour ya cicciro mata saboda yaga haka take yi idan ta tashi saka kaya,

Niyyar tsokanarta yayi yace "gaskiya binti kema fa katuwace sosai, jibi wadannan abubuwan da kike sawa"

Daga inda take ta turo baki "haka dai ka gani kake so"

Murmushinsa mai sanyi yayi ya taso da kayan ahunnunsa ya nufota, "ni dama bafa wani abu nace ba, ungo juyo nafara saka miki kinga mafi sauri"

Sunkuyawa yayi yana ware mata pant din, "abbu tsaya, na b'ule sai na nemo pad"

Dagowa yayi daga duk'en da yake yafara kallonta, "wai binti anya kuwa lafiyarki kalau? Nifa wannan abin naki yafara bani tsoro, ace ba zakiyi kwana 15 ba sai kinyi wannan abun"

"Nidai, nidai abbu lafiyata kalau" tafada cikeda shagwaba tana tutturo baki, wurin jakar tata ya koma ya ciro mata pad din ya kawo mata,

"Gashi nan sai ki saka danni ba sanin yadda ake yi nayi ba"

Kafa tafara bugawa akasa "abbu kaine zaka saka Allah"

"Oh binti yanmatan rigima, ya na iya, bani"

Taimaka mata yayi ta shirya sai dariya take tana murna, shi kansa jabir wani farin ciki yaji yana shigarshi domin kullum bashida burin da ya wuce na yaga bintinshi cikin walwala, hannunta ya kama suka fita falo inda al'amin yake zaune yana kallo bayan yagama cin abinci,

"Al'amin ummunka fa ta shirya muku breakfast mai dadi gashi kuma ka zauna anan ka cika cikinka da na yan hotel" jabir ya fada yana mika masa hannu,

"Abbu anty na bata da lafiya jiya ko bacci bata yiba idonta ne yake ciwo gashi yayi ja kuma yanata kuka"

Juyawa jabir yayi ya kalleta yana kashe mata idonshi daya,

"Ai nabata magani al'amin, kaga ai yanzu idon ya daina kukan ko?"

Kai al'amin ya daga, hannunshi jabir ya kama suka fice daga cikin dakin bahijja tana biye dasu abaya, taxi suka tare suka shiga suka tasamma gidan ummu,

Lokacin da suka shiga ummun tana cikin daki tana shiryawa domin fitowarta kenan daga wanka kasancewar tunda ta tashi tafada kitchen domin hada hadar shirya musu abin karyawa tunda jabir yace mata har su bahijjan ma anan zasu zo su karya,

Labule ummun ta dan bude ta leko tana yi musu sannu da zuwa kafin ta koma cikin dakin,zama suka yi shikuma jabir ya nufi cikin dakin,

Su bahijja na nan afalo

28 / 35