Author : Hameedah Category : Complete Novels
kallo a karon farko ya fara kissima yanda halittar ta take, doguwa ce ba can ba amma tanada kiba dan har tsayin nata ya buya ata sanadiyyar kibar tata, tanada dantse masu kauri gata da cikar kirji sosai, hips dinta da mazaunai kuwa abin ba acewa komai, fatarta baka ce dan har ya dan fita haske ma duk da cewar shima bakin ne, tanada round face ma'ana fuskarta a kewaye take mai dauke da fararen idanuwa madaidaita zagayayyu masu zubin k'wai, tana da yalwar gashin ido dana gira, sannan tanada zankadeden dogon hanci tamkar ummi A'isha ta sammata, bakinta shima zagayayye ne ba mai girma ba sannan ba dan tsul ba sai yar hab'arta wacce ta sake kawata fuskar tata domin harda dan beautiful point a tsakiyarta,
Idanuwansa ya sauke daga kallonta ya mayar dasu kan carpet, tana kammala jera masa abincin ta koma inda yake ta tsaya tare da zuba masa ido, zara zaran yatsun hannunshi ta kalla na tsakiyar da na kusa dashi duk sanye suke cikin zoben azurfa, yan yatsun nashi yake lank'wasawa suna k'as k'as, yayi kyau sosai yau dinnan,
Tana tsaye har ya gama wayar ya tashi zaune yana kallonta, "welcome sir"
"Yawwa thank you, ya hanyar okene kun dawo lfy?"
"Yes Sir lfy lau, ina al'amin?"
"Al'amin yana gaisheki shida ummunshi"
"Ina amsawa sir"
Mikewa yayi ba tare da yace komai ba ya shiga cikin bedroom dinshi, kujera ta samu ta zauna, mintuna goma sha biyar sai gashi ya sake fitowa cikin wata farar doguwar jallabiya bisa dukkan alamu wanka yayi,
Kan dining table ya wuce ya zauna ya zuba abincin data jere masa yaci, sai da ya k'oshi sannan ya dawo falon ya zauna ya dauki remote ya kunna tv ya kamo huda tv, hankalinta itama ta mayar kan tv din wurin kallon program din da suke gabatarwa a lokacin _(financial crisis and Islamic analysis by sheikh Muhammad Akbar India)_,shima jabir hankalinsa duk ya tattara ga program din, suna nan zaune basu sake magana ba har lokacin sallar magrib yayi domin shi jabir mutum ne shi marar surutu, kallonta yayi yace,
"Bari naje salla nadawo"
"Adawo lafiya Sir" tace dashi, mikewa yayi ya fita ya tafi masallaci ita kuma taci gaba da zama awurin.
Sai misalin karfe 8:30 jabir ya dawo gidan har lokacin goodness na zaune a inda ya barta tana kallo amma ta canza channel daga huda tv zuwa mbc 3 abin ma dariya yaso bawa jabir lokacin da ya shigo ya ganta tana kallon cartoon,
"Kin zama al'amin ne?" Ya fada yana tsareta da manyan idanuwansa,
"No sir" ta bashi amsa,
"Koda yake naga kema banbancinku da al'amin din kadan ne" ya fada tareda zama akan kujera,
"No,nidai nafi al'amin sosai kadaina cewa mate dina ne shi" tafada cikeda shagwaba tareda tsuke dan madaidaicin bakinta, kallo ya bita dashi shidai shagwabar da take yi mishi ba karamin burgeshi take yi ba,
"To in banda yaro ki fada min wanda yake bada sautun chocolate" ya fada ahankali da niyyar sake zolayarta,
"Dan na bada sautun chocolate shine zaka cemin nima small girl ce? Am not small girl" tafada cikin wata shagwabar, murmushi yayi ya cire hular kanshi ya fara shafa sumarshi.
_*Ummi A'isha*_ππ»
[10/11, 2:52 PM] βͺ+234 701 117 6189β¬: [9/12, 9:59 PM] Ummi A'ishaππ»: *WANI HASKE........!*
_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_
_64-66_
~~~
"Ai kuwa tsakanina da al'amin akwai banbanci da yawa" ta fada tana mai saka dan yatsanta a baki tana tsotsa kamar wata karamar yarinya,
Murmushi yayi ya kalleta "to ina tsarabata ta okene? Ko baki kawo min komai ba?"
"Sir na kawo maka let me go and bring it here" mikewa tayi ta tafi sashenta taje ta kinkimo akwatin data ciko masa da kaya ta jawota ta kawo part dinsa, agabansa ta ajiye akwatin ta tsura masa ido ba tare data bude ba domin tana son taga yanda zai karbi kayan ko zai yi murna dasu ko kuma sabanin haka, jan akwatin yayi ya bud'e ya fara cicciro kayan ciki, kayan bacci ya gani irin nasu na maza riga da wando sai short trousers kala kala sannan ga jeans da t shirt nan suma kala kala, mamakine ya kamashi ya dan kalleta yana duba kayan shifa kusan ma idan ba mantawa yayi ba rabonshi da kananan kaya tun yana saurayi lokacin yana dan makaranta kuma yana kammala karatunshi ya tattara kayan ya bayar lokacin da zai dawo gida Nigeria,
"To in banda abinki goodness wadannan kayan ai na samari ne ni kuma kinga ni na nafara tsufa" yace da ita yana dan murmushi mai tsada,
"Sir kaima ai saurayinne tunda baka tsufa ba" ta bashi amsa tana kallon kayan,
"Na tsufa mana gashi nan har al'amin ya fara zama saurayi"
"Sir baka tsufa ba i swear, wlh idan ka saka zasu yi maka kyau"
"To nagode sosai, zan saka" ya bata amsa,
Mikewa tayi "sir sai da safe"
"Ok" ya fada a takaice, sashenta ta koma tayi shirin bacci tayi kwanciyarta, shi kuma jabir kallon kayan kawai yake yana mamaki acikin ranshi ta yadda goodness har tayi tunanin siya masa kaya, hakika hakan ya sashi farin ciki domin kyauta tana kara dankon soyayya ga ma'aurata,sannan ma ai abun burgewa ne tsakanin mata da miji yawan bawa juna kyaututtuka lokaci zuwa lokaci, cikin akwatin ya mayar da kayan aransa yana ganin dolensa ya sanya kayan tunda siyo masa aka yi.
Washe gari da safe goodness ta tashi ta hada abin karyawa soyayyiyar doya da kwai da miya sai ruwan zafi, bata jima da kammalawa ba ta fita falo tana mopping tana sauraren wakar d banj, daga ita sai rigar bacci irin wacce Ummu al'amin ta aiko mata da ita a tsaraba waccen zuwan da jabir ya rakata,
Tana cikin aikin ne jabir ya shigo,kallonta yayi, "ki kawo min breakfast ina son zan fitane"
"Ok sir"
Da sauri ta shiga kitchen ta debo kayan ta nufi sashensa tana shiga bayan ta ajiye flasks akan dining ta jiyo tana kallonsa,
"Sir the food is ready"
"Ok am coming" ya fada ahankali, juyawa tayi ta fita takoma sashenta tayi wanka a gaggauce ta fito ta shirya cikin riga da wando blue, tana daure gashin attach dinta da ribom jabir ya shigo cikin farar shadda yana ta zuba kamshi,
"Bari naje gidan Malam" yace da ita,
"Sir zan bika pls" tace dashi a shagwabance,
"Kiyi zamanki agida naje na dawo tsarabarsu zan kai musu kema idan nadawo zan baki taki"
Juyawa tayi ta fara doddoka kafa a kasa irin na yara idan suna rikici,
"Nidai,nidai, nidai sai na bika" haka taketa fada cikin muryar shagwaba,
"Zo mu tafi" yace mata yana mai juyawa dan tafiya, cikin sauri ta dauko doguwar bakar rigarta ta dora akan kayan jikinta ta nada dan kwalin rigar tabi bayansa, lokacin da taje inda yake yana tsaye yana jiranta, gidan baya suka shiga dukkansu driver yaja motar suka fita daga gidan, kasa kasa take kallonshi tana murmushi hakika tasan ta fara cin gari awurin jabir koda baya sonta tasan ya bata wani matsayi na daban,
Shiru motar har sukaje gidan malam, fitowa sukayi suka shiga gidan a tare, a soro suka sameshi yana karatun littafi mai tsarki, ba karamin dadin ganinsu yaji ba musamman ma ganin goodness tayi shiga irinta musulmai, cikin gidan ta shiga bayan sun gaisa ta barsu domin su tattauna.
Sun dade agidan malam tun safe har wurin 3 gashi taji dadin zama da mutanen gidan babu tsana babu tsangwama babu komai saima tarairayarta da suka yi koda zasu tafi kuwa tsintsiyar laushi da muficai suka babbata hakan ba karamin dadi yayi mata ba.
Suna komawa gida ta wuce part dinta,yau tunda bata wuni agidan ba ya sanyata niyyar yin tuwon amala miyar yauki, kitchen ta shiga ta soma aikace aikacenta daga falo ta kunna music tana jiyowa daga cikin kitchen din, jabir yana hangota ta window din dakinsa lokacin da ya shiga dakin.
Lokacin sallar magrib kafin ya fita ya shiga part dinta ya bata tsarabarta ta farin almiski amma kayan baccin da ya siyo mata ya boye mata su acikin dakinsa, karbar turaren tayi ta bude ta fara sinsina shi kamshinsa yayi mata dadi wannan dalilin ne ma ya sata zuba shi acikin ruwan da zata yi wanka, nan jikinta ya gauraye da kamshi bayan ta fito daga wankan, rigar bacci tasaka riga da wando masu laushi green ta dauki abincin jabir ta kai masa lokacin karfe 9 na dare,
A falonshi ta iskeshi yana kallo kamar koda yaushe jallabiya ce jikinshi, a gabanshi ta dire abincin,"ajiye min wannan cikin waccan drewar din" ya mika mata wani kwali, tashi tayi taje ta bude drewar din ta saka kwalin ta tura murfin drewar din dan ta rufe cikin tsautsayi ta matse da dan yatsanta daya,
"Ohhhhh" tafada da karfi tana jan dan yatsan amma yaki fitowa,
"Sir my pinger, i done close it with my pinger inside" ta fada tana mai ci gaba da janyo yatsanta,
Tashi yayi yaje inda take, da sauri yakai hannunshi mai mutukar taushi ya kamo nata yana ja, duk da tana halin jin ciwo sai da taji yarrrrrr! Ajikinta kamar yadda shima yaji,
Drewar din yayita kokarin budewa amma bata budu ba haka ya dage yanata kokarin zare yatsan nata amma abin yaci tura, dakyar da sudin goshi ya zaro yatsan nata wanda duk ya yanyanke da glass din jikin drewar din,
Yau za ayita kenan ya fada aranta domin yasan zasusha kokawa da ita kafin ta yarda ya saka mata hydrogen, ai kuwa hakance ta faru lokacin da taga ya nufi kan wata drewar domin dauko kwalbar hydrogen din da sauri ta tashi zata fita ta gudu, cikin azama ya kamo hannunta ya fisgota ta fado kanshi, tun kafin ya fara kokarin bude kwalbar ta fara kuka,
"Pls sir don't open it, pls i beg you" hannunta takai ta rike kwalbar, har lokacin tana rike acikin jikinshi, janta yayi zuwa kan kujera,
"Ki bari kadan zan saka miki"
"No sir ba sai ka saka ba"
Kwalbar ta rike sosai, dakyar ya murde hannunta ya kwace nan kuma sabon dambe ya tashi domin shigewa cikin jikinsa tayi ta kankameshi yanda har suna iya jiyo bugun zuciyoyin junansu,
"Sakeni nasaka miki"
"No sir" ta bashi amsa bayan ta sake makalkale shi tare da rirrike hannunshi duka biyu, hannun nata ya kamo ya dage ya bankare dan yatsan da taji ciwon ya zuba mata hydrogen agun,
Kuka ta kwalla ta fara yarfe hannunta tana kuka, tashi tayi ta fita tana kuka ta koma sashenta tana zuwa ta shiga bedroom dinta ta kunna air condition tabi lafiyar gado amma har lokacin yatsanta zugin zafi yake yi mata, mintuna kadan bacci ya dauketa.
Bata jima da yin bacci ba jabir ya shiga sashen nata tunda yaji tsit bata kunna kallo ba aranshi yace "yau hydrogen yayi aiki kenan tunda gashi har ya hanaki raba dare kina kallo"
A cikin bedroom dinta ya sameta tana bacci hannunta da taji ciwon ta ajiyeshi akan _pillow_ yana shan iska gashi ta rungume wata katuwar teddy wadda ta siyo daga lagos sannan da kadan tafi teddy din girma, murmushi yayi ya karasa gaban gadon yasa hannunshi ya dago hannunta da lausassan hannunshi mai laushin gaske wani zimmmmm!,yarrrr! Yaji ajikinsa,dan yatsan nata ya kalla sannan ya mayar mata da hannun ya ajiye shi akan pillow din kamar yadda tayi,
Juyawa yayi ya fita bayan ya kashe mata wutar dakin.
Washe gari da safe tana cikin kitchen tana aiki gefenta kuma wayarta ce ta ajiye ta kunna waka tana ji, tana aiki tana bin wakar _every body move your body now, tomorrow is a good day,good day, every body move your body now forget about the blue day, blue day imagine that_,
Daga ita sai wata yar karamar _vest_ yellow mai yar tattara agaban kirjinta, sai dan wandon vest din iya rabin cinyarta ta dage sai aiki take tana juyi tana bin wakar da take ji,
Ya jima akofar kitchen din a tsaye yana kallon ta acikin ranshi yana fadin "wannan yarinya kina adon tsokoki agidan nan" ,cikin kitchen din ya shiga ya mika mata wayarshi yana karewa kitika kitikan cinyoyinta kallo,
"Take this phone al'amin want to talk with you,ban san me yake son fada miki ba da sanyin safiyar nan"
Yace da ita cikin cool voice dinshi yana mai mika mata wayar tare da bin jikinta da kallo bayan ta makala wayar ajikin kunnenta ta matseta da kafadarta da kanta,
"Hello my boy what's happen?" Tafada bayan ta juyawa jabir baya,
"Anty albishirinki?"
"Goro my son"
"I have a dream about you yesterday" yafada da karfi,
"Oya fada min abinda ya faru my boy, am hearing you,tell me the story"
"Anty nayi mafarki kema kinzo wurinmu nida ummuna, munata wasa dake" ya kyalkyale da dariya bayan ya gama maganar,
"Woohhh al'amin and then what happened next?"
"Lala anty nidai nayi murna ko ummuna da abbuna ban bawa wannan labarin ba sai ke"
Thank my boy, ya sch dinka?"
"Anty sch dinmu alhamdillah har nayi sabon aboki mai sunana kuma shima yanada surutu Irina"
Jin hirar tasu taki karewa yasa jabir juyawa ya fice ya bar mata wayar taci gaba da surutunta ita da al'amin wanda sun shafe tsawon lokaci suna yinshi.
Misalin karfe _11_ na safe ta shiga wanka sai da ta gama sabe jikinta da kumfa ta ji motsi akan window da sauri ta wanke idonta ta duba nan ta ga kadangare lab'e ai cikin sauri ta finciki towel dinta ta daura jikinta duk kunfa ta fita ta kofar baya ta tafi sashen jabir, tana shiga ta sameshi zaune kan kujera a falo yana karanta wani littafi mai suna _tarbiyatul aulad_ kansa ya dago ya kalleta,
"Meya faru?"
"Sir is lizard inside my toilet"
Littafin ya ajiye ya tashi yafita, bayanshi tabi tana saka gefen towel dinta tana goge cikin kunnenta, koda suka shiga toilet din saura kadan jabir yayi dariya domin kadangaren ba wani babba bane jaririne saboda dan karami ne sosai ta wata yar karamar kofa ya samu ya shigo,
Daga kanshi yayi ya kalli pant da bra dinta dake shanye akan karfen jikin cikin toilet din, nan mamaki ya rufeshi domin bra din wata katuwa ce ba ta wasa ba haka ma pant din,
"Lallai yarinyar nan katuwa ce, yanzu wadannan kayan take sawa" ya fada acikin zuciyarshi domin ko Ummu lokacin da take shayar da al'amin bata saka bra rabin girman wannan,
Jelar kadangaren ya dauko ya jiyo zai fitar dashi, k'ara goodness ta saka ta fita da gudu, a falo ya ganta tsaye tana rikeda towel din jikinta wanda iya mazaunan ta kawai ya rufe amma cinyoyinta duk a bayyane suke,
"Look at what you called lizard,even you, you can catch this small thing but you are afraid " ya fada tare da fita da kadangaren, dawowa yayi bayan ya fitar dashi yaje ya toshe yar kofar da kadaganren ya shigo ya fito ya wuceta ya koma sashensa, a tsorace ta je ta karasa wankan ta fito ta shirya tayi kwalliyarta cikin riga da skirt jajaye masu adon stones ajiki.
Sashen jabir taje bayan ta shirya, baya falon yana cikin bedroom dinshi, a falo ta zauna tana yin game din _angry run_ a wayarta, ta dade a zaune kafin ya fito, kamshin turarensa kawai taji, tana zaune ahankali ta dan daga idonta ta kalleshi "wow" tafada ahankali, yayi kyau sosai acikin daya daga cikin kayan da ta kawo masa, jeans black sai t shirt coffee colour mai gajeren hannu, bashida maraba da saurayi dan _27_,
Sir this dress suits you" ta fada tana Mai cigaba da kallonsa,
"Thank you goodness" ya bata amsa bayan yaje ya zauna, ci gaba da satar kallonshi tayi domin ba karamin kyau yayi ba, tun daga ranar indai yana gida kullum kananan kayan yake sawa sai dai idan zai tafi masallaci ne yake saka jallabiya,duk lokacin da ya saka kananan kayan fito mata yake a saurayi sak domin kayan suna tsananin yi masa kyau.
Misalin karfe _3_ na yamma tana cikin kitchen tana aiki kasancewar yau ranar juma'a ne, wainar fulawa take soyawa wani katon bera ta gani ya taho da gudu ya shige cikin drewar dinta ta kasa, tsalle ta daka ta kashe rishon ta fice da gudu ta tafi wurin jabir,
Bai dade da dawowa gidan ba yana kan dining yagama cin abincin daga shi sai dogon wandon farar shaddar da ya saka da farar singileti ta maza, arude goodness ta shigo cikin falon nashi,
"Excuse me sir, sir rat ne acikin kitchen"
Kallonta yayi abin nata ma abin dariya ita komai tsoronshi take ji kenan "beran ma tsoronshi kike ji?"
Yace da ita "sir, sir katone fa i swear"
"Its ashamed, ke komai tsoro yake baki" tashi yayi ya fita ahaka ba tare da ya saka riga ba, bin bayanshi tayi tana lallabewa har suka je kitchen din, yana bude drewar din beran yayi tsalle ya fito ya wuce ta window ya fice, juyowa yayi ya kalleta,
"Nasha fada miki ki daina barin windows dinki a bude saboda ta nan duk abubuwan da kike tsoron zasu rinka shigowa"
"Yes sir i will maintain it sir" ta bashi amsa, wainar fulawar da take soyawa ya kalla tasha kayan hadi gashi tasha curry tabada kala mai kyau,
"Wannan bakin ya iya kwadayi" ya fada ahankali yanda ba zata ji ba, bata jin ba kuwa kawai dai ta ga dan mitsitsin bakinshi ya motsa kadan amma bata san abinda yace ba, juyawa yayi ya fita ita kuma ta koma taci gaba da suyar wainar fulawarta.
Wurin karfe _5_ tana zaune a falo tana cin wainar fulawar da tayi sai gashi ya shigo yanata zuba kamshi.
"Bari naje aski na dawo" yace da ita yana mai gyara zaman hularshi,
"Sir zan rakaka" ta fada cikin shagwaba,
"Aski fa zanje, barbing"
"I know sir, zan rakaka pls"
Girgiza kai yayi wato yarinyar nan fitinanniya ce itama nan gaba daina gaya mata zaiyi idan zai fita saboda yaga tana ji da rigima,
"Yi sauri kizo mu tafi"
Zumbur ta mike ta tattare kwanukan wainarta takai kitchen ta shiga bedroom ta shafa powder ta sako doguwar bakar riga ta fito suka tafi. Lokacin da suka je shagon askin a mota ya barta ya shiga ciki aka yi masa bai wani jima ba ya fito yazo ya sameta suka tafi wata unguwa inda zai gudanar da wata tattaunawa da wani mutum acanne ya dade sosai kafin ya dawo suka koma gida.
Ranar Sunday wuni tayi tana wankin kayanta sai yamma ta gama bayan ta gaji likis, dakyar ta iya yin abincin dare taliya