Author : Hameedah Category : Complete Novels
tare da juyawa zai fita daga cikin d'akin,
"Sorry sir i have finish, yanzu zan fito"
Ba tareda ya jiyo ba ya fice ya nufi sashensa, yana zuwa ya zaunar da al'amin a kusa dashi ya fara koya masa wani hadisi.
Tana fitowa daga wanka ta shirya cikin riga da skirt ta dauki abincin jabir ta nufi part dinsa, tana shiga tun daga babban falo ta jiyo muryar al'amin yana karatu,
"An abi hurairata, an karb'o daga abi huraira radiyallahu anhu, Allah ya k'ara masa yarda,k'ala yace, k'ala rasulullahi sallallahu alaihi wassalama, manzon Allah yabo da amincin Allah su tabbata agareshi yace, man la yashkurun nasa, duk wanda baya godewa mutane, la yashkurullaha, baya godewa Allah"
Saka kai tayi ta shiga cikin falon nasa tana murmushi domin tsarin irin yadda jabir ke bawa al'amin tarbiya abin yana burgeta she like his fathering,
Hannunta dauke da food flasks ta karasa kan dining table ta ajiye tareda dawowa wurinsu,
Zama tayi ta zubawa jabir ido yana zaune hannunsa rike da littafin _sahihul bukhari_ yana dubawa, ido ta ware taci gaba da kallonsa har tsawon wani lokaci,babu zato ya dago kansa caraf suka hada ido dashi,
"Akwai damuwa ne?" Ya fada yana kallonta,
"Me ya faru?" Ta tambayeshi, mayar da kansa yayi kan karatun da yake yi ba tareda ya kara yin magana ba hakan ya sake bata damar ci gaba da kallonsa,
"Abbu anty tanata kallonka tun d'azu" al'amin ya fada yana girgiza abbunshi,
D'agowa yayi ya sauke idonsa akan goodness wacce ta mayar da kallonta ga tv,
Murmushi yayi ya tashi ya shiga _bedroom_ dinshi domin yin wanka, yana tashi ta jawo al'amin,
"Al'amin me yasa baka jin magana? Uhum? Am asking you? Yaushe ka ganni ina kallon dad dinka?"
"Anty naganki mana sai kallonshi kike yi, ko ya zama tv ne?"
Murmushi tayi tajashi jikinta tana dariya, "ohh al'amin you are talkative"
"Anty ina jin yunwa"
"Oya tashi muje muci abinci to"
Mikewa suka yi suka koma sashenta anan ta kunna wak'ar _if do me i do you..._,zaunar da al'amin tayi ta kawo musu abincin ta ajiye suka fara ci,
"Anty me yasa kike yawan jin kid'a?" Al'amin ya tambayeta,
"Al'amin yana sakani cikin nishad'i ne that's why"
Ta bashi amsa tana jinjina basira irin ta al'amin domin komai mutum yake yi yana haddane dashi,
"Anty yawan sauraron kid'a yana sanya munafurci acikin zuciya, amma sauraron karatun alqur'ani yana sakawa zuciya nutsuwa da farin ciki"
Spoon din hannunta ta ajiye ta tsurawa al'amin ido tare da kama hannunshi, "al'amin a ina kake koyan wadannan abubuwan masu ban mamaki?"
Dariya yayi irin tasu ta yara, "anty abbuna da ummuna ne ke koya min, kema idan kina so abbuna zai koya miki"
Murmushi ta saki tana wani tunani acikin zuciyarta, "al'amin ina son abbunka sosai, abbunka ya zame min wani bangare na rayuwata, i can't do without him, he's parts and parcels of my life, i like him soo much"
Lokacin da take yin wadannan maganganun jabir yana tsaye a kofar falon yana saurarensu, kuma duk maganganun da tayi yajisu acikin kunnensa but shi matsalarsa guda daya ce bazai iya nuna mata soyayya acikin wannan yanayin da take ciki ba domin bata da tsarki shi kuma mutum ne shi mai tsananin kyankyamin kazanta komai kankantarta,
"Anty abbuna ma yana sonki soo much" al'amin ya fada yana dariya,
Bude kofar yayi ya shiga cikin falon suna zaune suna cin abinci ga _music_ nan yana tashi k'asa k'asa,
Gefenta ya wuce ya zauna yana kallonsu, "abbu yanzu anty take zancenka"
"To al'amin ka manta idan ana cin abinci ba a magana har sai an kammala?"
"Abbu na manta ne" ya fada yana rufe bakinshi da hannunshi,
Wani sanyayyen murmushi jabir yayi tareda kallon goodness wacce take ta sussunkuyar da kai k'asa domin bata son had'a ido dashi saboda akwai wani sirri a k'unshe cikin idanuwansa wanda ita bata iya jurewa,
"Goodness zan fita ina son zanje wata unguwa da aka gayyaceni domin bud'e wani sabon masallaci"
"Abbu zan bika nima"
"A'a al'amin ka zauna awurin antynka kaji, bazan jima ba zan dawo"
"Adawo lafiya sir" goodness ta fada tana kallonshi lokacin da yake mikewa domin fita,
"Abbu ka siyo min chocolate" al'amin yayi tsagal ya fada,
"Zan siyo maka,antynka fa me zan siyo mata?" Yana tsaye a bakin k'ofa ba tare da ya jiyo ba,
"Sir alewar tsinke" goodness ta bashi amsa, murmushi yayi acikin ranshi kuma yana mamakin k'uruciya irin tata shiyasa lokuta da dama yake danganta yarintarta da irin ta al'amin, bud'e kofa yayi ya fita ba tare da yayi magana ba,
Yana fita goodness ta kalli al'amin "al'amin meye ambition dinka a rayuwa?"
"Anty ina son idan na girma na zama kamar abbuna nima ina tara mutane ina koya musu karatun alqur'ani saboda annabi yace '''mafi alkairin cikinku sune wadanda suka san alqur'ani kuma suka koyar dashi"' kinga abbuna ma yana koyawa mutane"
"Good boy, ina sonka my boy" mikewa tayi ta shiga cikin bedroom dinta tabar al'amin yana k'arasa cin abincin.
Tunda jabir ya fita bai dawoba sai misalin k'arfe 8:30 bayan sallar isha ko al'amin ma ranar sai agida yayi salla baije masallaci ba saboda baya nan,yana idar da sallar taji ya fara karatunsa kamar kullum annabi yace "'sallu kama ra'aitumuni usalli, kuyi salla kamar yadda kuka ga ina salla"'.
Lokacin da ya shiga gidan basa part din goodness hakan ya sashi tunanin k'ila suna sashensa ai kuwa hakan take domin yana shiga ya hangosu suna wasa goodness tana yi musu after money amma da yake wayon al'amin yawane dashi sai runto yake yi mata,
Sallama yayi ahankali ya shiga, da sauri suka d'ago suka kalleshi yayinda al'amin ya tashi da gudu yaje ya rungume shi,
Ciki suka karasa yana rikeda hannun al'amin, "welcome sir" goodness ta fada tana kallonsu,
"Yawwa anty" ya fada ba tareda ya kalleta ba,murmushi tayi ta kalli dan mitsitin bakinsa wanda ya iya fadar magana sannan yayi fuska,in banda haka taya zai kirata da anty,
Ledar hannunshi ya bawa al'amin "maza kaiwa anty ta baka naka"
Ledar ta karba sautin sune ita da al'amin, alewar tsinke da chocolate manya manya, jan hannun al'amin tayi suka koma part dinta suka zauna suka fara shan kayan zakin da ya kawo musu, mintina kadan al'amin yayi bacci dan haka ta kwantar dashi kan cinyarta taci gaba da tsotsar alewar tsinkenta, tana kallon tv,
Ahankali ya bude kofa ya shiga hangota yayi zaune tanata tand'ar baki da loly pop a hannunta kan cinyarta kuma al'amin ne kwance yana bacci ta dage ta zubawa tv ido, ahankali yaje kusa da ita ya mika hannu zai dauki al'amin nan tayi wata zabura har tana tuttuje bandejin dake kan yatsanta wanda aka nad'e mata ciwon kafarta,
"Oh Sir ka tsorata ni banji shigowarka ba" tafada tana mai sauke ajiyar zuciya,
"Kawo na rage miki aiki na kaishi daki" mika hannu yayi ya daukeshi nan jikinshi da nata ya hadu wanda yayi sanadiyyar haifar musu da wani yanayi na musamman, daukarshi yayi ya nufi dakinta dashi yaje ya kwantar dashi tare da yi masa addu'o'in kwanciya bacci, bargo yaja ya rufa masa ya fito daga cikin dakin, agogo ya kalla 11 daidai,
"Ba zakije ki kwanta ba sai dare ya sake yi?"
"Sir sai anjima ina son na karasa kallo ne"
Jijjiga kai yayi, ya juya ya fita acan kasan ransa yana tunanin anya kuwa yarinyar nan bata da aljanu? Saboda kullum bata da aiki sai sauraron kida da kallon TV, Komawa sashensa yayi yaje ya kwanta.
Washe gari da safe bayan ta kammala yiwa al'amin wanka ta shiryashi cikin wata jar riga wacce ajiki aka rubuta Good boy da bakin wando,
"Oya take this, ka kaiwa watchman kace yaje ya siyo min ya baka ka kawo min kaji? Yawwa my boy" kudi ta bashi da yar karamar takarda wacce tayi rubutu ajiki,
Da gudu ya fice ita kuma ta shiga wanka, bakin gate yaje amma mai gadin baya nan sannan kofar gidan akulle take, da gudu ya juya ya shiga part din abbunshi,acikin dakinsa ya sameshi yana kwance akan gado,
"Sabahul khair abbuna, gashi inji anty na tace asiyo mata"
Karb'ar takardar jabir yayi ya bude ya tashi zaune, always ta rubuta ajikin takardar,
Drawer din gadonshi ya jawo anan yaga akwai saura guda biyu kasancewar yana siyowa ummu al'amin kuma anan yake ajiye mata sannan itama goodness din yakan siyo mata duk lokacin da yayi mata provision na kayan amfanin gida wannan watanne kawai ya manta,
Dauka yayi da kansa ya tafi kai mata shikuma al'amin ya haye gadonshi yana wasa, lokacin da ya shiga ta fito daga wanka tana daure da towel ta kwanta rub da ciki akan gado tana jiran al'amin ya kawo mata Aiken da tayi masa,
"Gashi" ya fada lokacin da yake mika mata ledar, zumbur ta tashi tana kallonsa,
"Thank you Sir"
"Kar ki sake aiken watchman siyo miki wannan abin, ai ina siyo miki wannan month dinma mantawa nayi"
"Sorry sir, bazan sake ba"
Kudinta ya mika mata da yar takardar ya juya ya fita
Cikin sauri ta shiga shiryawa tana wani dan kasaitaccen murmushi ita kadai, tana kammalawa ta shiga kitchen ta fara harhada abincin karyawa da abincin rana domin church zata tafi kuma ba zata dawo ba sai yamma,
Sai da ta gama kammala komai sannan ta debi kwanukan abincin ta nufi sashen jabir, lokacin da ta shiga yana tsaye a tsakiyar falonsa yana latsa wayarshi, kan dining ta wuce taje ta shirya komai ta nufi wurinshi da niyyar sanar dashi cewar zata tafi church, tana tsayawa al'amin na shigowa aguje, da gudu yazo ya banketa ta tafi ta fada jikin jabir, ko tsayawa al'amin baiyi ba yayi cikin dakin abbunshi da gudu,
Tana rungume ajikinsa ta dago kanta tana kallonshi shi dinma ita din yake kallo zuciyarsa dauke da tambayoyi kala kala na dalilin da yasa duk lokacin da ya tabata sai yaji wani sabon yanayi yana ziyartar shi koda kuwa dan yatsanta ya tab'a.
_*Ummi Shatu*_ππ»
[9/11, 10:50 AM] Ummi A'ishaππ»: *WANI HASKE*
_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_
_59-60_
~~~Kasa sakinta daga jikinsa yayi yana rike da ita yabi jikinta da kallo kanta ta daura bakin dan kwali wanda yana iya hango tarin tulin gashin kitson attach din dake kanta wanda ya sauko har kan kafadunta, blue din body hug ce ajikinta tareda bakar skirt ta jeans wacce tayi mata dadas ajikinta,
"Anty, abbuna kuyi hakuri fitsari ne ya matse ni shiyasa na shigo da gudu"
Suka jiyo muryar al'amin yana fada daidai lokacin da yake fitowa daga cikin bedroom din jabir,
Cikin sanyinshi ya saketa ta matsa daga jikinsa kanta yana kasa,
"Sir zanje church" ta fada ahankali,
"Ok sai kin dawo" yafada tareda juyawa zuwa kan kujera ya zauna,
Kan al'amin ta shafa "my boy sai na dawo ko?"
"Sai kin dawo anty kinga nima gurin abbuna zanje muyi wasa tunda ke tafiya zakiyi ungunwa ki barni"
"Yawwa al'amin maza kayi wasan kafin na dawo kaji good boy"
Kumatunsa ta shafa ta juya ta fita ta koma sashenta agurguje tayi breakfast ta dauki katon Bible dinta da yar karamar jakarta ta fita daga gidan.
Lokacin da goodness ta fita daga falon jabir, ido ya zubawa al'amin yana tunanin irin shakuwar dake tsakanin al'amin din da goodness gashi Ummu ta fara yi masa maganar cewar ta samowa al'amin din sch akusa da inda take dan haka nan da d'an wani lokaci kankani zai kai mata shi,
"Abbu kaga anty idan zata yi addu'a sai ta rufe idonta kuma ko abinci zata ci wani lokacin sai ta rufe idonta sannan bata yin bisimilla"
Muryar al'amin ce ta dawo dashi hayyacinsa, hannun al'amin din ya kama yana fuskantarsa,
"Al'amin addininmu da addinin antynka ba iri daya bane, dan haka duk abinda kaga tayi irin na addininsu to kar kayi koyi da ita"
"Abbu to itama ka koya mata karatu ka sanar da ita ilimin addininmu saboda ka samu lada da yawa tunda annabi yace idan mutum ya mutu dukkan ayyukansa suna yankewa in banda abubuwa guda uku, sadaka mai gudana, ko ilimin da ake anfanuwa dashi ko kuma d'a na kwarai wanda zai rinka yi masa addu'a"
"Nasani al'amin, insha Allahu zan fahintar da antynka addininmu"
"Yawwa abbu jazakallahu khairan"
Hannunsa yaja suka koma dining table domin karyawa,Amma acikin zuciyarshi ya dauki niyyar koyar da goodness dukkanin kyawawan dabi'u wanda addinin musulunci yazo dasu kuma zai fahimtar da ita menene musulunci cikin salo da dabaru irin na d'a namiji.
Goodness bata samu damar dawowa gida ba sai wurin 6,tana shiga dakinta ta ajiye kayanta ta nufi sashen jabir a falo ta samesu sun baje al'amin yanata rubutu acikin exercise book shi kuma jabir yana rikeda littafin _fiqhul aulawiyyat_ yana nazarinsa,
Ahankali ta shiga idonta kan jabir tana kallonsa,
"Sannu sir" tace dashi tareda zama akusa da al'amin,
"Yawwa" yace da ita a takaice,
"Anty kin dawo? Nima kinga abbuna ne yasani rubutu"
"Dakyau my boy"
Dunkufar da kansa yayi yaci gaba da rubutun yayinda ita kuma ta fara kallon jabir kasa kasa tana nazarinsa acikin ranta, dan mitsitsin bakinsa dake burgeta akoda yaushe ta kalla ta lashi lebenta.
Suna nan zaune kowa yana abinda ke gabansa har lokacin salla ya gabato, hankalinta ta mayar kan tv din dake kunne tana faman aiki,
"Al'amin tashi maza kaje kayi alwala kazo muje masallaci". Ta jiyo muryar jabir yana yiwa al'amin magana cikin muryarsa sai dan karen sanyi,
"Na'am abbu" al'amin ya bashi amsa tareda rufe exercise book din da yake rubutu aciki,
Tana zaune tana kallo suka fita masallaci ganin zaman baya yi mata dadi ya sanyata mikewa ta koma sashenta ta shiga wanka ta fito ta shirya ta saka wani wando tied da rigarsa mai gajeren hannu purple colour, tana tsaka da fesa turare al'amin ya fado dakin,
"Anty kizo inji abbuna"
"Yana ina?"
"Yana falonshi yana kallo"
Tare suka fito ta kunna masa cartoon ita kuma ta wuce sashen jabir.
A falo ta tarar dashi yana jan cazbaha ga tv kuma ya kunna yana kallon din huda tv ya mayar da hankalinsa sosai wurin sauraron program din dasuke gabatarwa a lokacin mai taken _missing ingredient_ wanda sheikh Muhammad salah yake gabatarwa,
"Excuse me sir" ta fada ahankali, manyan idanuwansa ya dago ya kalleta kanta babu ko dan kwali ko yar hular ma da take sawa yau bata saka ba,
"Dauki wannan grass din ki dafa min da Lipton"
"Ok Sir"
Na'a na'ar ta dauka wacce ke ajiye akan center table ta juya ta fita, bin bayanta yayi da kallo tabbas dan sura tana da cikakkiyar surar da duk wani da namiji yake bukata a wurin mace,domin yar duma duma ce ita sam bata da rama, singalalinta kuwa cikarsa za tayi cinyar wata siririyar, idanuwansa ya dauke daga kallon kofa ya mayar dasu kan tv yana sauraron dawowarta.
Part dinta ta koma ta iske al'amin ya nutsu yana kallon cartoon dinsa, wuceshi tayi ta shiga cikin kitchen ta dafawa jabir na'a na'a ta juyo acikin dan karamin tea flask ta fito,
"Anty nima zan sha shayin" al'amin ya fada yana tashi zaune,
"Oya zo muje abbunka ya san maka"
Tashi yayi yabi bayanta, a yanda ta tafi ta barshi dazu yanzun ma haka ta dawo ta sameshi, hannun al'amin ta kama suka koma sashenta bayan jabir ya tsiyaya masa shayin a kofi,
"Wash anty na kona bakina"
"Ka ringa fifitawa da bakinka kafin kasha"
"Lah anty annabi ya hana hura abinsha da baki"
Kallonsa tayi ta jinjima kai "al'amin kenan kai kam komai kasani, ko wanne abu yana ajiye acikin brain dinka, maza kasha kazo muje muyi bacci yau bazan yi kallo ba".
***
Watan Ummu al'amin uku da tafiya ta kira jabir ta sanar dashi ya kai mata al'amin tun lokacin yaji babu dadi domin zai rabu da al'amin gashi uwa uba yasan goodness zata shiga wani hali na rashin abokin wasanta amma dole ne shi yanzu ya zame mata abokin wasan domin karta shiga halin zaman kunci acikin gidansa.
Sashenta ya shiga dawowarsa kenan daga office misalin karfe _5:30_ na yamma, part din nata tsit da alama babu kowa aciki hakan ya sashi komawa nasa, a falo ya jiyo hayaniyarsu sunata kokawa ita da al'amin yana kokarin sai ya saka mata kadangaren roba ajikinta ita kuma tsoronshi take, tana ganin jabir ta nufi wurinshi da gudu,
"Yawwa Sir kaga al'amin wai sai ya saka min lizard" ta fada tana haki,
"Abbu wlh na wasane fa bana gaske bane, anty tsoron kadangare take yau ko throughout bata zauna a falonta ba saboda da safe kadangare yabi ta corridor ya shiga falonta"
"Ai yanzu ya dade da fita bazai yi ta zama acikin falon ba"
"No sir, yana ciki bai fita ba idan munje zaka gani"
"Muje Nagani" yace da ita yayinda yayi gaba ta juya tabishi a baya, ta bayansa ta tsaya take tafiya ahankali har suka shiga cikin falon, al'amin yana bayanta ya sadada ya jefa mata kadangaren robar yace "anty gashi nan ajikinki"
Wata kara ta saki ta kankame jabir ta baya tana faman shassheka irinta wanda ya tsorata,
"Wasa nake anty" har lokacin bata saki jabir ba tana rike da rigarsa ta baya, ahaka suka shiga dakinta ya dudduba ko ina tana makale dashi har ya gama caje dakin ya dawo falo nanma baiga komai ba, kofar falon ta Baya yaja ya rufe ya jiyo yana kallonta yanda ta wani rikeshi tamau kamar wacce za akwace mata shi,
"To ki sake ni mana tunda kinga babu komai ai aciki dama na fada miki bazai zauna ba ya dade da ficewa, kuma ki daina barin kofar baya a bude kina rufeta dan ta nan zai rinka shigowa"
"Yes Sir" ta fada tana mai sake rike rigarshi al'amin kuma yana binsu yana yi mata dariya,
Bata sakeshi ba har suka fita daga falon duk ta yamutsa masa rigar sa, sashensa suka koma gaba dayansu, a falo ya barsu ya shiga bedroom dinsa yayi wanka ya sake kayan jikinsa daga shaddar dazu zuwa doguwar jallabiya fara, kansa babu hula ya dawo falon ya hau kan dining ya fara cin abinci jalop din shinkafa da kifi, yana ci yana kallon su sunata kiriniya suna yin puzzle game, sai da ya kammala sannan ya dawo inda suke,
"Goodness ki fara hadawa al'amin kayanshi domin nan da sati biyu zan kaishi wurin ummunshi"
Kanta ta dago zuciyarta babu dadi tace "to sir"
Shi kansa al'amin din yayi wani irin sabo sosai da goodness din wanda ya haifar da shakuwa sosai a tsakaninsu, kamar wadanda aka zarewa laka ajiki haka suka dawo.
Tun daga lokacin ta wankewa al'amin kayansa gaba daya ta harhada masa dukkan abubuwan da tasan nasa ne sa'arta daya mamanta ta kirata a waya tace ta sanar da mijinta zasu tafi okene nan da