CUTARWA COMPLT BY AYSHERCOOL

Author :  AYSHERCOOL Category :  African Stories & Novels

Chapter   71 / 74

210K to 213K   out of 219.4K words

aka fara fito da jarirai, mace da"

namiji.

"Sai dai hankalinsa ba a kansu yake ba, Ummi yake jira a fito da ita."

"Yana nan tsaye aka turo ta a kan gado idonta a rufe, an rufeta da green Win yadi."

"""Salma"" ya kira sunanta da Wan ™arfi."

"Ta buWe ido tare da ri™e hannunsa ta ce ""Ka yi magana a hankali mana, ban mutu ba"" yayi dariya ya dur™usa ya"

"sumbaci goshinta ya ce ""Thank you very much sweetheart, Allah ya baki lafiya"""

"Can waje kuwa ana ta murna an fito da jarirai, mami ta kallesu ta ce ""TaS, wannan wane irin yara ne, mu kaf"

"danginmu babu wannan kalar, meye wannan?"""

Ayshercool

8081012143.

CUTARWA!

AYSHERCOOL

(BRIGHT PENS)

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION

https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g

49

PAID ADVERT

"*Hajiya ina zaki? Saurin me ki ke yi haka? Šan bani aron mintuna biyu kacal, na gaya miki albishir Win da na zo miki da shi. Shin ko kin san sirrin she™in fatar ummi, da ya sanya ta kama zuciyar MD raihan ta hana shi sukuni? Kai ba ma"

"skin care ba, har da sirrin gyaran gashi, ina masu fama da amosani, karyewar gashi ko kuma san™o, jan gashi ne da ke? Ko taurin gashi kamar soson ™arfe. Idan matsalar ki budurwar fata, tare da rashin glowing, Annur skin scrub da hair bliss sun shirya tsaf domin magance muku kukanku, me ku ke jira ku tuntuSe su a kan lambar wayar su dan ™arin bayani 07045971194 ko 08140450950*"

49

"Tsit kowa ya yi ya zuba wa mami ido, tana wani yatsune fuska."

"Hajiya ta ce ""Amma meyasa zaki ce haka? Wannan ai ba magana ba ce ba"""

"""Eh na faWa, ko a dangina kin taSa ganin irin wannan?, kalli kalar uwarsu ki kalli raihan ki kalli yaran""."

"Jajawur yaran, haskensu ya wuce ace hasken raihan kawai suka Waukko, gasu manya sosai, kuma kansu ™wal babu gashi, kuma ba su da gashin gira ko kaWan sai alamarta."

"Mariya cikin jin kunya ta ce wa Hajiya ""Bari na gansu"""

"Aka mi™a mata yaran, ta zuba musu ido tana murmushi sannan ta kalli mami ta ce ""Hajiya, ai yaran nan da babansu"

"su ke kama, haka na haifi ummi, Iya ta din ga ce mata aljana, sai dai kwana biyu kanta ya cika da gashi ko anty maryam, sai dai ummi tun tana jaririya ba™a ce""."

"Wani mugun kallo ta yi wa mariya ta ce ""To ni danginmu babu irin wannan abubuwan, ni ban taSa ganin jarirai a"

"haka ba, danginmu dai kaf babu mai wannan farin"""

"Nan da nan Maryam ta harzu™a ta ce ""To mu namu akwai, duk tsiya dai ai na Wanki ne ba wani ba"""

"""Ba ni da tabbas, ni Wa na ma ba shi da cikakkiyar lafiya"""

"Hajiya da ta fara fusata ta ce ""Ke dai ya rainawa hankali, dan ya tsallake son zuciyarki"""

Mariya ce ta din ga basu ha™uri.

"Raihan kuwa yana can Wakin da aka kai ummi, sai zuba yake yi yana yi mata kalamai masu kwantar da hankali da"

™warin gwiwa.

"Likitan da yake yi mata allura ya ce ""Maman twins ai ba Kya bu™atar maganinmu, wannan kalaman sun ishe ki"

"warkewa"" suka din ga dariya, sai da bacci ya Wauke ta sannan ya tafi Wakin da su Hajiya suke."

"Noor ji take kamar ta kwaWawa mamin raihan mari, ko karar ganin idon mariya bai saka ta yi alkunya ba."

"Abdul da yake Wakin ya tashi ya fita, Salim ma surutun ya ishe shi, ransa ya fara Saci."

"Mariya ta kalli Salim ta ce ""Salim, dan Allah jariran nan ba da babansu suke kama ba, dan Allah kar ki saka zargi a"

"kansu tun suna jarirai, su sha wahala kamar ummi, idan ta tashi ta ji, ba za ta ji daWi ba""."

"Salim ya ce ""Mama, muna murna muna fatan Allah ya bawa ummi lafiya, mun gode wa Allah kyautar da ya bamu"""

ya ™arasa maganar yana yi wa mami mugun kallo.

"Kamar daga sama raihan ya shigo ya ce ""Hajiya ba ni su na gansu"""

"Hajiya ta maze kamar babu abun da yake faruwa ta ce ""Tun yanzu ka fara nuna wariya, ka tafi wurin matarka ko"

"Waukar su ba ka yi ba"" cikin washe baki ya ce ""Tuba nake, dole in fara zuwa kanta, saboda su an yanka mini mata"" yayi maganar ko a jikinsa yana Waukar su, wanda hakan ya sake ™ular da mami."

"Ya ce ""Tubarkallah, Hajiya irin idon ummi ne da su, brown masu kyau masha Allah, yaya ka ga namijin kallesu duk"

"farare. Alhamdilillah"" yayi maganar yana kallon Salim."

"Farincikin da mariya ta gani a fuskar raihan, sai ya mantar da ita takaicin abun da mami ta yi musu."

"Sauran mutanen maiduguri da suka zo ganin gidan mariya, suka cika asibitin. Ana jimawa ma sai ga dr. Ga Alhaji."

Raihan ya din ga sanar da ´an uwa batun haihuwar.

"Tsabar takaicin yadda raihan yake rawar ™afa, ya sanya ta tashi ta bar asibitin."

"Sai da ummi ta yi awa shida tana bacci, sannan nurses suka tasheta, suka Wagata aka wanke ta, sannan aka bata"

abinci.

"Ta saka kaya tayi kyau, kamar ba ita ba, sannan aka turo ta a kan gado aka mayar da ita main Wakin da take."

Suka din ga murna ganin an fito da ummi ras da ita.

"Sai jerawa ummi sannu ake yi, aka mi™o mata yaran dan ta shayar da su, amma ta kasa saboda yadda ido ya yi yawa."

"Hajiya tare da Salim suka koma gida, ta yi wanka ta yo girki, suka dawo da Alhaji."

"Shi ma Alhaji baki buWe yake ta murna, yana yi wa jariran addu'a, duk da babu wanda ya gaya masa abun da matarsa"

ta yi.

"Sai dai noor ta gaya wa ummi, abun da mamin ta ce, wanda ba ™aramin ciwo yayi mata ba, sai dai ta basar saboda"

tana cikin murnar kyautar da Allah ya bata.

"Ummi ta ce ""Mama, jikin yaran nan kamar jariran mage, basu da gashi kwata-kwata""."

"""Me ki ke ci na baka na zuba? Zai fito in sha Allah"""

"Dr. Ma da daddare ya zo ganin jariran, tare da yi mata sannu."

"Kusan kwanaki uku, ana ta shigowa ana fita duba ummi, a kwanaki ukun nan gashi ya cika kan yaran nan fal."

"Kwanan ummi biyar, aka sallame su daga asibiti, raihan ya ce bai yadda a Wauki hoton yaransa ba a saka a waya."

"Saboda masha Allah kai ba zaka ce ummi ce ta haife su ba, dan sun fi kama da larabawa sosai."

"Su Hajiya Aishan bauchi, da sauran jama'arta, duk suna kano, sai da ummi ta yi kwana goma da haihuwa, sannan aka"

shirya gagarumin taron suna a wani katafaren event center.

"Sai ranar suna ´an gagarawa suka zo, aka ci aka sha, ummi sun samu kyaututtuka sosai da sosai ita da yaran,"

"manyan mutane abokan hulWar Alhaji Tahir, da abokan aikin Raihan, ban da ´an uwa da abokan arziki."

"Sai dai kan ranar sunan nan, yaran nan sun juye kalar larabawa sosai da sosai, gashi ya cika kansu da girarsu, kuma"

"dukkansu brown eyes ne da su, namijin mai ba™in gashi, macen kuma irin na ummi."

"Sai dai sunan da aka sakawa yaran ya yamutsa hazo, dan kuwa raihan sunan ummi ya saka wa macen Salma, namijin"

"ya saka masa Muhammad, wai ya yi wa kansa takwara, ya yi wa Alhajin su, kuma ya yi wa mahaifin Ummi, tun da duk sunansu Muhammad la™anin ne daban-daban, aka yi musu la™ani da Iman da kuma Ayman."

"Ba yadda ummi ba ta yi da raihan ba, a kan ya canzawa macen suna, kar ya janyo mata magana a cikin dangi."

"Amma ya ce ""Kome mutum zai ce ya ce, son da nake yi miki, dole na yi miki takwara dole duniya ta shaida ina son"

"matata""."

"Noor ta sha kwalliya, kamar amarya."

"Ta je ta saka salim a gaba, sai ya yi mata hotuna da iphone Win sa."

"Ya gama yi mata hotunan yana nuna mata, sai murmushi take yi, ya kalleta ya ce ""Kin yi kyau kamar ranar bikinmu"" a"

"razane ta kalleshi ta ce ""Bikinmu kuma?"""

"""Eh mana, ko ba kya so na?"""

"Ta Wan sosa kai ta ce ""Yarinya ce fa ni"""

"""Ba kya son tsoho ko?"""

"Ta girgiza kai ta ce ""A'a kai ba tsoho ba ne"""

"Ya ce ""Tsoho ne mana a kan ki, am 37 you are just 15, dama so nake bayan suna in yi wa Alhajinmu magana, amma"

"tun da kin ce haka shikenan, idan kin gama hotunan ki kawo mini wayar""sai kuma ta ji babu daWi."

"Mami kuwa a ranar sunan sai da ta kira raihan, ta ™are masa zagi da cin mutunci, wai ya ™are a gidin mace, saboda"

"asara har da saka wa ´ar sa sunanta, bayan uban kuWin da ya kashe mata ita da yaranta."

"Shi dai yayi shiru bai ce komai ba, dan ya san duk abun da ya yi wa ummi bai faWi ba, kuma ba zai yi hidimar da"

Alhajinsu yake yi wa iyalinsa ba.

"Da daddare ummi ta yi wanka ta saka kaya, Anty maryam ma ta wanke jariran, an samu sun yi bacci saboda sun gaji,"

sun sha kuka da jagwalgwalon ´an suna.

Raihan ya shigo yana yi wa ummi murmushi.

"""My MD, murmushin me ka ke yi ne?"""

"""Kallonki kawai yana sani murmushi, amma murmushin na yau na musamman ne, guess what?"""

"Ta girgiza masa kai ta ce ""I have no idea"""

"Ya kamo hannunta ya dan™a mata mukullin mota ya ce ""Gashi in ji Alhaji, ya ce a baki ya riga ni"""

"Ummi ta waro ido ta ce ""MD mota Alhaji ya bani"" ta rungume raihan tana murna, ta din ga zuba masa addu'a da shi"

da Alhaji.

"Da gudu ta fita falo, tana nuna wa su mama da ba su riga sun bar gidan ba, aka din ga yi mata murna."

"Noor ta ce ""Yaya ummi baki ji zuciyata ba, na taya ki murna, amma ina son mu yi magana"""

"Suka keSe da noor, ta gaya wa ummi abun da ya faru tsakaninta da Salim."

"""Noor meyasa baki da wayo ne? To meye aibun yayan?"""

"Noor ta ce ""To ai ni yarinya ce, kuma ni bana son ayi ta yi mini surutu kamar yadda aka yi miki"""

"""To sai me? Wata™ila da ina nan a gida ban yi auren ba, ai yanzu ki samu mai sonki tsakani da Allah shi ne. Shi da ake"

"son ya yi auren ma, kin san da manyan ´an mata nawa aka haWa shi, duk ya ce ba ya so dan ya ce yana sonki zaki wula™anta mini yaya, to kin yi wa kanki"""

"Noor ta ce ""Dan Allah ki yi ha™uri"""

"""Kin fi son ki koma gida kina jerawa da kausar kuna faWa kenan? Ke ba kya son ki ganki kema a gidanki?"""

"""To ai yanzu ba a gida nake ba, gidan mama zan koma, ni ba zan koma gidanmu ba, maama haushina take ji kamar"

"ba ta son ganina ma"""

"""A'a ba sonki ne ba ta yi ba, amma dai yaya Salim dai kin yi wa kanki"""

"""Na shiga uku, yanzu ya zan yi?"""

"""Ki Wauki waya ki bashi ha™uri"""

"Noor ta tura baki ta ta ce ""Salon ajina ya zube"" ummi ta ™are mata kallo kawai tayi tsaki ta bar Wakin."

"Ummi na komawa Waki ta kira Salim, suka gaisa sannan ta ce ""Yaya ka ji Alhaji ya bani mota?"""

"Yayi murmushi ya ce ""Na riga ki sani ai, ina taya ki murna ™anwata"""

"""Na gode sosai yaya salim, Allah ya saka muku da mafificin alkhairi"""

"""Amin ™anwata, Allah ya raya mana su Iman"""

"""Amin yaya. Yauwwa noor ta gaya mini shirmen da ta yi maka, abun duk ya dame ta, dan Allah ka rabu da ita, Alhaji"

"ya samu dr. Da maganar""."

"Yayi murmushi ya ce ""Kin je kin takura mata ko? Bana son takura ta, daga baya nake ganin kamar na yi wauta nayi"

"mata tsufa"""

"""Dan Allah ka bar wannan maganar, tana sonka, duk ta damu fa"""

"""Amma, kina ganin dr. Zai bani noor kuwa? Kin san ni ina da case"""

"""A'a yaya me zai hana? Kuma dan kana da case sai a ™yamace ka? Ai yanzu ka shiryu a kan yadda na sanka a da, dan"

"Allah ka ™yale shirmen noor yaya"""

"Yayi murmushi ya ce ""Auta danger, shikenan zan yi tunani, a bata lokaci"""

"""Dan Allah yaya ka ™yaleta, mun yi magana da ita fa"""

"""To shikenan, sai da safe"""

"""Yauwwa yaya, a yi wa su hajiya bangajiya"""

"Suka yi sallama, ta din ga addu'a, Allah ya tabattar da alkhairi, dan tana fatan noor ta yi aure da wuri, tun kan farida"

"ta ™wace ta, ta siffantu da miyagun halayenta."

"Har dr. Ummi ta kira, ta sanar masa da abun alkhairin da Alhaji ya yi mata."

"³an gagarawa sai da suka kwana uku a gidan ummi, da zasu tafi ta haWa kayan suna ta basu suka tafi da shi."

"Ummi ta saka noor a gaba, ta bata waya ta kira Salim."

"Sai dai da ya Waga wayar ya ji murayarta, bai kashe ba suka gaisa."

"""First born"""

"""Mmmm auta"""

"""Fushi ka ke da ni ko?"""

"""Me ki ka yi mini zan yi fushi da ke?"""

"Ta Wan sosa kai ta ce ""Maganar da muka yi ranar suna""."

"""Ai ta wuce auta"""

"""Ba ka so na yanzu?"""

"Yayi murmushi ya ce ""Ke dai ba kya so na, an bar maganar bana son takura miki"""

"""To yanzu na canza shawara ka yi ha™uri"""

"""To"" ta Sata rai saboda yadda yake bata amsa a ta™aice da izza."

"Ummi ta girgiza mata kai, alamar kar ta yi fushi."

"""Yaya Salim"""

"""Noor"""

"""Idan muka yi auren zaka bar ni in yi makaranta, ka ga yaya inteesar mijinta hanata yayi daga baya""."

"""Zan barki in sha Allah"""

"""A'a rantse da Allah, kar ka canza shawara"" yayi mata shiru, ummi ta dafe kai, saboda wautar da noor Win ke yi."

"Bayan sun gama wayar, ummi ta ce ""Eh lallai akwai jan aiki a gabana, noor babban mutum yayi magana ki ce ya"

"rantse? Ke fa baki da kai"""

"""To ba ki ji yadda yake yi mini magana da gadara ba, da fa ba haka yake yi mini ba"""

"""Ba aurenki zai yi ba yanzu? Dole yayi miki izza. Ke fa miji ba abun wasa bane ba"" ta din ga yi mata faWa."

"Ummi ta ™ara Waura aniyar, raba noor da Farida har zuwa lokacin da za a saka auren noor Win, saboda kar ta Worata a"

kan mummunar Wabi'arta na raina miji da yin asiri.

"Ummi ta kira Alhaji a waya, ta din ga yi masa godiya, tare da yi masa adduo'i masu daWi."

"Ummi ta tara kuWi da suturu, da sauran abubuwa."

"Farida kuwa tayi watsi da dr., Shi ma yayi watsi da ita ya daina shiga sabgarta kausar ma ta biye mata ba sa kula shi."

"Yau yana gidanta, tana ta cika tana batsewa, ta same shi a fall ta tsaya a kansa ta ce ""Malam yaushe za ka dawo mini"

"da ´a ta ne?"""

"Ya Waga kai ya kalleta ya ce ""Ke da noor, sai lokacin aurenta, ta bar gidan nan kenan na bawa mariya ita"""

"""Wallahi ba ka isa ba, ai ba ita ta haifa mini ita ba, da zaka bayar mini da ´a"""

"""Ni ban isa na ™wace miki ´a ba, halinki da ki ke nuna mata ne, ya sanya ta guje ki ita ma"" za ta yi magana wayarta ta fara ringing."

Ta Waga wayar ta yi sallama.

"""Farida kina ina, ki yi maza ki zo asibitin murtala emergency, Rahama mijinta ya ™onata da ruwan zafi da ita da ´ar"

"da take goyo"""

"Farida ta dafe ™irji ta ce ""Ruwan zafi me tayi masa?"""

"""Wai faWa suka yi, ta tafi tsakar gida tana girki, ya zageta ta rama, ya fito yayi balla da kurfotin gabanta da"

"tafasasshen ruwa a kai, da garwashin duk ya watse musu a jiki ita da ´ar"""

"""Innalillahi na shiga uku"" tayi jifa da wayar tayi Waki tana salati."

"Kiran sallar la'asar ake yi dama, dr. Ya fice sallar isha'i, dan bai san me aka ce mata a wayar ba."

"Daga sallar isha'i, ya tafi gidan mariya."

Ya tarar ta idar da salla tana zaune ta yi shiru.

"""Ya dai, na ganki sai a hankali, ina noor ne?"""

"""Tana gidan ummi, ai noor ta gujeni saboda sun yi jarirai"""

"Yayi murmushi ya ce ""Noor an kusa girma, Alhaji Tahir ne yayi mini magana, wai su na ri™o Salim yana so, na ce zai sha shiririta"""

"Mariya ta ce ""A'a kar ka ce haka, abu namu ´a ta wa Wa na wa, za ta yi hankali in sha Allah kan lokacin"""

"""Wane lokaci kuma, shekara Waya ne kawai fa, tana gama secondary school ne suke so"""

"Mariya ta yi dariya ta ce ""Allah ya sa zamu gani"""

"Ya Wan kalleta ya ce ""Kamar akwai magana ko?"" Ta jinjina masa kai alamar eh."

"""To ya aka yi?"""

"""Dr. Tun muna waccan ™asar kamar ban kuma al'ada ba fa"""

"Yayi dariya ya ce ""To me ki ke so in ce?"""

"""Koma meye ka ce mana"""

"Dr. Yayi dariya ya ce ""Maman ummi rigima, kin fi ni sanin meyake faruwa ai"""

"""Innalillahi wa Innalillahi raji'un, wai ciki ne da ni?"""

"Dr. Ya kashingiWa yana dariya, gaba Waya ta ruWe ""Haba dr. Ummi na jego nima a ganni da ciki, na shige su"""

"""To laifina ne? Ni dai ina so ina murna Allah ya raba lafiya, kowa ya kalle ki fa zai gane kin ™ara haske sosai"" gaba"

"Waya ta rikice, wai abun kunya ne, shi kuma ya din ga yi mata dariya. Gaba Waya ya manta da a gidan farida."

"Ummi na Waki tana ta yi wa noor nasiha, a kan maganar salim, ta ce mata ita tana son sa amma tsoron auren take yi,"

"ummi tana ta lallaSata, dan sun yi magana da dr. Kuma ta san zai kira noor Win ya tambaye ta."

"Anty Maryam ta shigo Wakin ta ce ""Ummi, kin yi ba™uwa, sai wani harare-harare take yi, ban san me aka yi mata ba,"

"amma da alama ´ar uwar mai gidan ce, suna kama da shi"""

"Ummi ta yi murmushi ta ce ""Anty ki ce ta shigo""."

Mintuna kaWan sai ga Maryam ta shigo.

"Ummi ta ce ""Sannu da zuwa, yanzu ki ke tafe?"""

Ta ja tsaki ta zauna.

"Noor ta ce ""To, ikon Allah"""

"""Noor kawo mata ruwa da yaran ta gansu"""

"""Ai fa, an samu abun da ake so, an samu daular da ake kwaWayi tashin farko an zubo yara biyu, yaran da aka ce babu"

"kalarsu a danginmu"""

"Ummi ta yi dariya ta ce ""Ai abun alfaharinku ne, kun samu iri a dangi. Kuma ´a´a biyu sai matar so ba kwaWayayyi"

"ba, abun alfaharinku ne, ™aninki akwai himma, ko kuma maybe daga ni ce"""

"""Ummi ni ki ke

71 / 74