CUTARWA COMPLT BY AYSHERCOOL

Author :  AYSHERCOOL Category :  African Stories & Novels

Chapter   7 / 74

18K to 21K   out of 219.4K words

""Ina kwana"""

"""Lafiya ™alau, ya makarantar?"""

"Ta ce ""Lafiya lau, to ina maman take?"""

"""Mama tana lafiya, ta ce; a gaishe ki"""

"Ummi ta sake kallonsa ta ce ""To zaka kai ni wurinta?"""

"""Ke wuce ki je ki cire uniform, ki yi salla"" Iya tayi mata tsawa. Yayi shiru ransa a matu™ar Sace, bai taSa tunanin ganin ummi a cikin wannan mummunan yanayin ba."

"Ta fito kanta babu Wan kwali, gashin nan a cukurkuWe, sai soshe-soshe take yi, saboda yadda ya addaba mata da"

™ai™ayi.

"Ya dubi iya ya ce ""Shikenan, tun da kun ce cikin ba naku bane ba, baku san da shi ba, ni ba dan wani abun hannunku"

"ya sanya muka zo muka sanar da akwai cikin ba, saboda a cika umarnin Ubangiji, amma tun da abun haka ne, Allah ya kyauta, mu mun ji mun gani, mun karSa. Amma dan Allah ku bani ´ar ta in kai mata, mariya ta kasa zaune ta kasa tsaye, hankalinta ya™i kwanciya, ku bata ´ar ta dan Allah"""

"""Ba rashin ummi ne ya hanata nutsuwa ba, mugun abun ta ne yake koma mata kanta, hakkina da na Wa na ba zai taSa barinta ba, ya din ga bibiyar ta kenan"""

"Ganin idan ya cigaba da zama, wannan jayayyar zata kai su ga maganar banza, ya sanya ya tashi tsam, ya ce"

"""Shikenan babu laifi, Allah ya kyauta"""

"Jin ya ce zai tafi, ya sanya ummi fitowa da gudu daga Waki, ta ce ""Ba zaka tafi da ni, ka kai ni wurin maman ba?"""

"Ya dur™usa ya shafa kanta ya ce ""Ki yi ha™uri, in sha Allah nan gaba kaWan, zaki koma wurin mamanki, Allah ya yi miki albarka"" ya ciro kuWi dubu biyar, ya bawa iya ya ce ""Dan Allah a canza mata uniform, a saya mata wasu ´an"

"kayan bu™ata"""

"Ba kunya iya ta amshe, tana harare-harare."

Ummi ta tsaya tabi bayansa da kallo har ya fice.

"Dukan da aka yi mata a kanta ne, ya sanya ta dawowa hayyacinta, ta firgita ta kalli Iya."

"""Duk wanda ya sake zuwa gidan nan, ki ka ce ya kai ki wurin uwarki, sai na saka idris ya zane miki jikinki, wato salon"

"ace ba a kula da ke, saboda ™warewa a munafunci kin tsotsa a nono ko?"" Tayi shiru ta sunkuyar da kanta ™asa."

"""Munafuka, ga muni ga kinibibi, tashi ki wanke kwanukan nan na safe"" sumi-sumi ta nufi wurin tara kwanukan"

"wanke wanke, ta haWa ta fara wankewa."

***

"Bayan sallar magariba, yaya garba ya je ya samu mahaifinsu ya sanar da shi cewa iya ta ce ba su san da ciki ba, dan haka a nemi ubansa."

"Malam yayi shiru, lamarin ya girmame shi ya ce ""Haka suka ce?"""

"""Wallahi, matar nan ba ta da mutunci ba ta da imani ko kaWan, ba ka ga Yarinyar nan a halin da na baro bata ba,"

"kamar ´ar jari bola saboda azabar datti da ™azanta"""

"""˜yalesu, yarinya kullum muna yi mata addu'a, in sha Allah babu wanda zai sake bi ta kansu, ita kuma Allah ya raba"

"ta da ciki lafiya"""

"Ya amsa masa da ""Amin"""

***

"Na'ima kuwa ummi na ranta, amma babarta ta ce mata ba ita ba ummi, dan kakarta ba mutunci ne da ita ba, kar ta yi mata wani sharrin."

"Sai dai ta kan ™ulle abinci wasu lokutan, ta tafi da shi makaranta ta bawa ummi."

"Yanzu babu mai yi wa ummi wanki balle guga, dan haka dauWa kamar ka kankarota a jikinta."

"Ummi na iya ™o™arin ta wurin kaucewa haWuwa da idiris, ga bala'in tsoronsa da take ji, saboda dukan da yake yi"

mata idan tayi laifi babu tausayi babu imani.

"Allah ya taimake ta, wasu lokutan magaji na taka masa burki a kan wasu abubuwan."

"Tsabar rashin gyara, ya sanya kwarkwata cika wa ummi gashi, kayan ta duk suka cukurkuWe suka yi mata kaWan, tana zaune har sakkowa kwarkwata suke yi daga kanta, suna bin ta, sai dai ta Suya tayi ta kashewa, ba ta son a gani."

"Ga wasu irin manyan ™uraje da suka din ga fitowa a cikin gashin kan nata, suna Wurar ruwa, suka ™ara bawa kwarkwatar nan damar hayayyafa babu ji babu gani."

"Banda zarnin fitsari da warin datti, babu abun da take yi, dan kuwa da kanta take yi wa kanta wankin kayanta,"

"wando sai ya fi kwana uku a jikinta, ba ruwan iya balle ta ce cire ki wanke."

"Sa'adatu ce babar auwwalu, ta fara lura da wannan ™urajen na kan ummi, ta kamata ta buWe kan, ta ga ™azantar da"

take cikin gashin.

"Ta nuna wa iya, Iya ta yamutse fuska ta ce ""TaS gaskiya ba zan iya taSa wannan kan ba, to gashi ne ba kaWan ba, gaba"

"Waya ba irin namu ba, kalar na mutanen ™etare, shiyasa nake cewa anya ma kuwa tamun ce, duk zuriyar mu, babu irin wannan gashin, yanzu meye abun yi kar kan ya ruSe ace ni ce ina kallonta, na bari ya ruSe ji yadda wani mugun ruwa yake tsatstsafowa da ™wayayen kwarkwata a ciki""."

"""Aikuwa sai dai a aske kan nan, dan ban ga yadda za ayi maganin abun nan ba"""

"Cikin ™yan™yami, sa'adatu ta sauke wa ummi gashin nan tsaf, ta koma sai ka ce namiji, ga hudar kunnenta ma, tana"

"ruwa saboda tsufan Wan kunne a kunnenta, ba a taSa cirewa ba."

"Iya ta saka aka haWa kanwa da gishiri, da omo aka wanke kan nan, ummi ta din ga wani irin masifaffen kuka, saboda azabar raWaWi, da bal'in zafi haka nan da ruwan sanyi aka tuSe ta, aka wanketa a tsakar gidan, iya har tana cewa"

"wannan ba™ar fatar ba da dutsen goge faso za a wanketa ba kuwa?. Wata irin annakiyar dauWa ta din ga zuba daga jikin yarinyar. Yara suka cika sashin dan™am suna kallon ummi, da tana ta ™o™arin rufe jikinta, amma azabar wahala da zafi ya sanya ta manta da tsiraicinta."

"Ummi na ji na gani, aka Waure gashinta a leda kaya guda da shi aka zubar, iya ta ce a sakawa kan ummi fiya-fiya, idan"

"ba haka ba, sauran ™wan zai ™yan™yashe kansa."

"Ba tare da tunanin wane hali zata shiga ba, suka shafe ™wallon kan da suka saukewa sumarta da fiya-fiya, hakan ya"

"sa ta din ga tari da atishawa, gaba Waya kanta ya juye, ta din ga jiri, kan dare zazzaSi ya rufe ta da ciwon kai."

"Ba wanda ya kula ya saya mata magani, haka ta kwana tana rawar sanyi, da ta yin™ura ta tashi, sai ta tafi luuu zata"

faWi.

"Da safe gwaggo ta bata, koko da ™osai, sai dai ta kasa ci, ta cigaba da kwanciya tana burgima a ™asa, kanta yana"

"ciwo, ga tari da take ta faman yi."

"Cikin barccin wahala, ummi ta ji wani ™amshin turare mai daWi, ta ji magana sama-sama kamar muryar babanta."

"Da sauri ta buWe ido, ta yi ™uri da ido tana kallonsa, ga iya a gefe suna magana da shi."

"Yayi murmushi ya ce ""Uwata ta kaina, kin tashi? ˜araso mu gaisa"" sai yanzu ta lura ba baba bane ba, mutumin nan"

ne mai kama da shi.

"Tasowa ta yi da sauri, sai dai ta faWi, saboda jirin da take ji."

"Da sauri ya tashi, ya ce ""Iya ba ta da lafiya ne?"" Iya ta taSe baki, mussaman jin ya kirata da uwassa ta kansa ta ce ""Eh"

"zazzaSi take""."

"""Subhanallah, kuma ba a kaita asibiti ba?"""

"Ya zaunar da ummi, ya sinsuna kanta ya ce ""Ya na ji kamar kina warin fiya-fiya? Ya cire hular kanta, sai ga kai sol ba"

"gashi, ga dagwalon gyambo a kan, ciwon duk yayi ba™i saboda fiya-fiya."

"A razane ya ce ""Meye wannan? Iya meya sameta a kanta?"""

"""Kwarkwata ce, da wasu ™uraje, shi ne aka aske kan aka shafa mata fiya-fiya"""

"""Innalillahi wa Innalillahi raji'un, iya wannan ai ganganci ne, ina laifin a kaita asibiti, wannan ™aramar yarinyar a saka mata fiya-fiya a ka, ai shi ya sanya mata zazzaSi""."

"""To ban da kai yahaya, ana ta abun da za a ci, waye yake ta wani asibiti, wa zai bayar da kuWin kai ta wani asibiti?"""

"Mi™ewa yayi ya ce ""Wannan abun kunya da yawa yake"""

"Cak ya saSa ummi a kafaWarsa, yayi waje da ita, iya ta biyo shi tana tambayar ina zai kai ta?."

"""Asibiti zan kai ta, idan ta mutu ba makawa ku ne ku ka kasheta"" yayi waje da ita."

"A mota ya kwantar da ita, ya ja suka tafi."

"Sosai likitoci suka din ga faWa, dan ma asibitin kuWi ne, aka sake wanke kan ummi, da magunguna, aka saka mata"

"ruwa saboda zazzaSin da ya rufeta, take ta rawar sanyi."

"Ya fita ya sayo kayan marmari, da ta farfaWo zazzaSin ya sauka, ya din ga bata da kansa."

"""Kana kama da baba"" ta faWa a lokacin da za™in kankana ya ratsa kwanyarta, wanda rabon da ta sha har ta manta."

"Yayi mata murmushi ya ce ""Ai nima baba ne"""

"""Ai an ce baba ba zai dawo ba, ya mutu yana cikin kabari""."

"""Haka ne mamana, kina yi masa addu'a ko?"" Ta gyaWa kai alamar eh."

"""Yanzu me ki ke son na saya miki?"""

"""Littafi"" ta bashi amsa."

"""Littafin makaranta?"" Ta jinjina masa kai alamar eh."

"Ya ce ""To shikenan, zan sai miki in sayo miki kifi ko nama, wanne zaki ci?"""

"""Nama"" ta faWa tana murmushi."

"Yayi mata murmushi shi ma, ya ce ""To bari su sallame mu, sai na saya miki mu tafi gida"""

"Har ummi ta Wan murmuro, ya saya mata tsire a hanya, da babbar robar youghurt, ya sai mata litattafai, da sabuwar"

"jakar makaranta. Babban abun da ya burgeta da shi, shi ne yadda take ta ce masa ta gode, a yanayin tattaunawar da yayi da ita, ya san ba™ar azaba kawai take sha, bai ga dalilin da ya sanya iya ri™e ummi ba, kuma shi ma idan ya ce zai tafi da ita can gidansa, faWa za suyi da Fauziyya matarsa, dan ya san ba zata karSi ummi ba."

"Gashi shi bai san a ina mahaifiyarta take a Maiduguri ba, dan lokacin da balarabe yayi aure, yana kudu karatu."

"A mota ya sanya ummi ta ci, har ta ™oshi, wani irin daWi take ji, yau ta ci kayan daWi, wataran tana kallo ake kawo wa"

"Iya, bata sammata."

"A ™ofar gidan yayi parking, ya buWewa ummi ta fito, ya ri™o ledar maganinta, ya ri™e hannunta suka shiga cikin"

gidan.

"""Ba™ar randa, ba™in zunubi, an dawo jinsinmu na maza"" Alhassan ya faWa yana ™ya™yata dariya""."

"Yahaya ya tsaya cak, ya kalle shi ya ce ""Alhassan, wa ka ke cewa ba™in zunubi? Ummi ba ™anwarka ba ce ba? Dan me zaku din ga aibata ta?"""

Alhassan ya yi shiru ya sunkuyar da kai.

"""Kai da ubanka na halitta, da zai halittoka da wannan kunnuwan kan kamar zomo na zikiri, ga ™aton kai kamar"

"marmara?"""

"Ya girgiza kai alamar a'a, nan yayi ta yi masa faWa, ya shiga cikin gida nan ma ya Wora, tare da yi wa iya ™orafi a kan"

"lallai ta sanya ido, a daina ci wa ummi zarafi, idan ba haka ba, zata dashi ba ta karsashi a cikin al'umma, saboda gudun kar a aibanta halittarta."

"Jin sa kawai Iya take yi, amma ba dan ta ji zata iya hana wani aibata ummi ba, dan ita ma aibata tan take yi."

"Yahaya ya kawo kuWi ja bawa iya nata, kamar yadda ya saba yi mata alkhairi, ya sanya a ka kira masa magaji, ya bashi"

"dubu goma ya ce ""Ga dubu goma, dan Allah duk abun da Yarinyar nan take bu™ata, ko na rashin lafiya, ko na makaranta ka cira ka saya mata, idan da damuwa zan rubuta lambar wayata, a kira ni a sanar da ni duk abun da take bu™ata, zan biya."

"Zumunci bai ce haka ba, mahaifinta ya rasu, an rabata da mahaifiyarta, kuma a™i tsayawa a kula da ita, dan Allah a kula da marainiya""."

"Hashim ya ce ""Ina sha Allah kawu, za ayi duk abun da ya dace"" ya dubi ummi ya ce ""Sannu ummi"""

"Ta ce ""Yauwwa"""

"Yahaya ya mi™e ya ce ""To iya, sai wani lokacin kuma, ayi ta ha™uri, Allah ya rufa mana asiri"""

Iya ta kwaSe baki ta amsa da Amin.

"Da sauri ummi ta ri™e rigarsa ta ce ""Baba yaushe zaka dawo?"""

"""Da wuri in sha Allah ummi""."

"""To ka ce ina gaishe da mama"""

"Ya kalli iya, iya ta kawar da kanta gefe, ya ce ""Iya yakamata a sanya lokaci a kaita ta ga mahaifiyarta, bai kamata idan"

"ma wani abu ne a tsakanin ku da mahaifiyarta ya shafe ta ba"""

"Iya ba dan Wan abun duniyar da ya bata ba, da babu abun da zai hana, ta Wura masa ashar. Sai dai ta yi masa shiru, ya"

™araci maganarsa ya tafi.

"Hashim ya tafi raka shi, suna tafe yana sake jaddada masa, dan Allah a kula da ummi, babu wanda yafi ™arfin Allah"

ya jarrabe shi da irin abun da ya jarrabe ta.

"Suka Wan yi hira a kan karatun Hashim, yake gaya masa ai yayi jamb, ya ce duk yadda ake ciki, idan yana bu™atar"

wani taimako yayi masa magana.

"Suka yi sallama ya dawo sashin Iya, sai dai fa iya nata jibgar ummi da kara, Idris na tsaye yana kallonsu."

"Da sauri ya ™arasa ya ™wace ummi, ya ce ""Iya daga asibiti fa aka dawo da yarinyar nan"""

"""A'a daga mutuware aka dawo da ita, duk yadda nake ™o™ari a kan yarinyar nan, bata da wani buri da ya wuce ta"

"tozarta ni, ta nunawa duniya azabtar da ita nake yi"""

"""To yanzu iya me tayi miki?"""

"""Ban sani ba, tun da makaho ne kai, baka gani, munafukar yarinya, wallahi duk ranar da wani ya kuma zuwa gidan"

"nan, ki ka yi masa zancen uwarki, sai mai shirin tafiya kabari ya fiki kwanciyar hankali, sai na casa ki, shegiya mai idon munafukai"""

Ummi ta cukuikuye rigar hashim tana kuka.

"Iya ta kalli Hashim ta ce ""Kai ma Waya munafukin, bani kuWin da ya baka, ai ba ita kaWai ce ´a a gidan ba, kuma idan"

"bayarwar ne, ai ni yakamata ya bawa"""

"Cikin takaici ya ce ""Amma iya..."

"""Rufe mini baki, ka bani na ce kan na Sata maka rai"" ya ciro kuWin ya ajiye mata, ya fice."

"Ummi da sauri ita ma ta fita, jikinta na ciwo, ga zazzaSi na sake son rufe ta."

"Ta koma ™ofar gida, ta samu in da rana take da saura, Wumin yana ratsata."

"Auwwalu ya taho da tawagar abokansa, har ya wuce ta ya dawo ya ce ""Yara ba™ar randa ta koma ba™in namiji, aski"

"aka yi mata fa"""

"Šaya daga cikin yaran ya ce ""Haba dai"""

"Ya ce ""Bari ku ga"" ya tunkari ummi, yana zuwa ya fara ™o™arin ja mata hijjabi, ta rirri™e hijjabin ta fara kuka."

"˜arasawa yaran suka yi, suka taya shi, kasancewar maza ne, gashi ba ta da ™wari ga rashin lafiya, suka kayar da ita,"

suka yage hijjabin.

"Ta saka hannu bibbiyu ta rufe kanta, tana kiran mama."

"Saboda mugunta irin ta yara, daga haka suka din ga kai mata duka a ka, wai sun ci ladan aski."

"Suka tuburbuWata a cikin ™asa, duk ta kurje jikinta, kan da aka yi wa dressing, duk suka cika shi da ™asa."

"Mariya daga alhinin mutuwar miji da rabuwa da Ummi, mariya ta zarce da damuwa, ba ta hira ba ta walwala, sai dai"

"kullum cikin wuni a Waki, duk lokacin da ta kwanta, ba ta da wani aiki sai mafarkin ummi, da kuma marigayin mijinta. Asibiti da maryam ke kaita awo, suka ce da zarar ta fara na™uda, a kai ta asibiti ta haihu a can, saboda hawan da jininta yayi."

"Sai dai kusan kwanaki uku kenan, tana jin ciwo, kuma sai ta yi ta mafarkin gata ta haifi ummi tan jaririya, amma tayi shiru da bakinta, ta™i faWa."

"Mama ta shiga Wakin, da niyyar tashin mariya ta yi salla, ta tarar da ita tana jijjiga, sai datse harshenta take yi, tana"

mimmi™ewa ga kuma haWe da jini na fita daga bakinta.

Ayshercool

08081012143

*CUTARWA!*

BRIGHT PENS

(FREE BATCH)

arewabooks ayshercool7724

Watpad ayshercool7724

Subscribe my YouTube channel https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

P7

"A guje mama ta koma tsakar gida, tana ™walawa malam kira, a kan ya zo ya ga abun da mariya take yi."

"Suka dawo a tare, ya tarar da yadda jikinta yake ta rawa tana jijjiga, ya fita da sauri, aka nemo ma™wabcin su, kasancewar yana da abun hawa, aka saka mariya a mota suka tafi asibiti."

"Can kuma hashim ne ya fito zai fita titi, ya hango yara sun yi dandazo, har zai wuce ya hango ™afar ummi, ya ™arasa"

"da sauri, ya tarar da ita a kwance, yara sun yage mata hajjabi, ta sanya hannayenta biyu ta rufe kanta, sai kuka take yi."

"Wani irin ba™in ciki ya turnu™e masa zuciya, ya rasa dalilin da ya sanya yara suka tsani ummi haka, kodayeke"

"iyayensu suka gani suna yi, da sun tsawatar musu da tarbiyantar da su a kan girmama halittar Wan Adam komai muninta, da ba su yi mata wani abun ba."

"Kai tsaye ya je ya tarwatsa yaran, yayi nasarar kama auwwalu, ya din ga kifa masa mari, yana ball da shi, yayi masa"

"dukan tsiya, sannan ya Waukko ummi ya shiga da ita gida."

"Gaban iya ne ya faWi ganin yadda ya shigo da ummi, ta mi™e tana faWin lafiya?."

"""Wallahi auwwalu ne ya tara yara, suka cire mata hijjabi suka yi ta dukanta a waje"""

"""Saboda iskanci, me tayi masa?"""

"""Oho masa"""

"""Kema uban waye ya ce ki fita?"" Tayi maganar tana kallon ummi, da take ta zirarar da hawaye."

"Ya ce ""Dan Allah iya ki yi ha™uri, a jigace take, jikinta zafi rau da zazzaSi"""

"Ya karkaWe mata ™asar nan, ya samu ruwa ya din ga shashshafa mata a jikinta, ya kaita Wakin gwaggo ya kwantar da"

ita.

"Iya kuwa mita take tana ""Na rasa wannan ba™in jini na yarinyar nan, ´a sai ka ce mujiya, ´an uwanki yara ma"

"gudunki suke yi, kodayeke ai dole a guje ki, wannan munin gaba Waya kalarki ba irin ta mutane ba"" Hashim bai kula iya ba ya fice, saboda haushinta da yake ji, dan ya fara tsinkewa da lamarin son zuciyarta, gashi babu wanda zai iya tarar ta ya gaya mata gaskiya kowa

7 / 74