CUTARWA COMPLT BY AYSHERCOOL

Author :  AYSHERCOOL Category :  African Stories & Novels

Chapter   3 / 74

6K to 9K   out of 219.4K words

maganar, wani irin tausayin sa ya kamata, har ga Allah yana iya ™o™arin sa a"

"kan su, mahaifiyar sa ce ta hana su zama cikin kwanciyar hankali."

"Ta kwanta a jikinsa tana kuka, rarrashinta ya din ga yi, yana yi mata magiyar, ta taya shi ya yi wa iya biyayya, ya san"

"ba zasu taSe ba, kuma rayuwar ummi ba zata wula™anta ba."

"Abun ka da mata da miji, haka ya lallaSata ta janye batun yin yajin, har ya fara ™o™arin shiga wani abun daban."

"Iya ce ta faWo Wakin tana faWin ""Wai balarabe ba ka ji ana kiran salla bane, ka shige ka ™ule a Waka da mace"" a razane"

"mariya ta yi gefe, tana kare jikinta."

"""Eh iya yanzu zan tafi masallacin ma dama, dam..dama... Yanzu aka kira sallar"""

Ayshercool.

08081012143

*CUTARWA!*

Watpad ayshercool7724

Arewabooks ayshercool7724 YouTube Cool hausa novels What's app 08081012143

BRIGHT PENS

(FREE BATCH)

3

"Yanayin da suke ciki, bai sanya iya ja da baya ba, mussaman yadda suka rikice tamkar marasa gaskiya."

"""Ina jin duk abun da ku ke faWa ai, idan ta tafi ta barka ka yi yaya, tun da ta fini a wurinka, kar Allah ya sa ta zauna Win mana, ta ™ara gaba, wata™ila dama ita ce ™ashin tsiyar da ta tokare maka ™ofofin arziknka, har ni zan gindaya"

"umarni, ka zo kana lallaSata? Ki tafin mana waye ya ri™e ki? Ke idan ´ar mutunci ce ina uwarsa har sai ya nemi shawarar ki sannan zai bi umarnina?. To ke idan ban isa da ke ba, na isa da Wa na, dan haka ki san abun da yake yi miki ciwo, idan ™abilar ku kun saba asiri ku mallake mazaje, to ni na yi wa kaina da ´a´ana dafa'i, asirinku bai isa ya kama ni ba"""

"Ba yau iya ta saba yi musu laSe ba, dan haka yanzun ma mariya ba ta yi mamaki ba, dan idan da sabo ta saba."

"Iya ta sake jaddada musu duk wanda ya fasa abun da ta ce a rufe, bata yafe ba."

"Baban ummi ne ya yi ta bata ha™uri, mariya kuwa ta haWe rai, wani abu mai Wacin gaske na kaiwa da komowa a"

"™irjinta, ji take kamar ta tashi ta Wurawa Iya ashar, wanna ai shi ake kira da ga mari ga tsinka jaka, gaba Waya tsohuwar nan ba ta da imani, ba ta da mutunci, abu Waya take girmamawa a rayuwarta shi ne kuWi."

"Bayan sun samu ta fita, ya le™a ya tabbatar ta tafi, sannan ya dawo ya cigaba da rarrashin mariya, ganin ya shiga tsaka mai wuya, ya sanya mariya ce masa ""Ka kwantar da hankalinka baban ummi, ba wanda zai ji maganar nan, ina"

"fatan Allah ya yi wa ummi sakayya, ba wanda zan bari ya sani"""

"Ya ce ""Yauwwa, Allah ya yi miki albarka, in sha Allah zan san abun yi, zan yi ™o™arin neman fili a garin nan, na gina"

"mana ko Waki Waya ne da makewayi, mu koma can, ko kema kya samu sassauci."

"Kallonsa kawai take yi, cike da tausayawa dan kuwa ta san tun da iya ta gama raina masa wayo ba shi da abun"

"duniya, ba zata taSa barin sa ya bar gidan ba, ko dan kar ta huta."

"A zahiri kuma ta ce ""To Allah ya yassare"" ya amsa da amin sannan ya tashi ya fita."

***

"Jujjuyar lokaci ya sanya abubuwa cigaba da gudana, wasu da daWi wasu marasa daWi, sai dai lokaci ya wuce ba tare da Waci da raWaWin abun da ya faru da ummi ya bar zukatan iyayenta ba."

"Kuma babu kunya, wanda yayi laifin ya cigaba da sabgoginsa hankali a kwance."

"Mariya ta ™ara tsananta kula da jan ummi a jiki, babanta ya kaita makaranta, ita kuma ta je ta Waukkota, ta daina"

barin kowa ya raSi ummi.

"Mariya na zaune na ™o™arin koyawa ummi assignment a tsakar gida, kasancewar tana aji na uku a sakandare aka yi"

"mata aure, ta iya karatu da rubutu. Iya na zaune suna hira da babarsu magaji da idris."

"Ummi ta™i mayar da hankali a kan karatun da mariya take koya mata, sai soshe-soshe take yi, tana Sata fuska."

"""Mamana, wai ba zaki mayar da hankali ba, so ki ke anty ta zane ki?"""

"""Mama ni bana son makarantar"" tayi maganar hawaye na taruwa a idonta."

"Cikin damuwa haWi da kulawa ta ce ""Saboda me ummina"""

"Cike da ™uriciya ummi ta ce ""Tsokanata ake yi, mama dan Allah ki mayar da ni fara, kuma ki rage mini ™ibata"""

"Mariya ta Wan yi shiru sannan ta ce ""Ummina, ke fa kyakywar yarinya ce, ai kin san sahabban manzon Allah"

"Sallallahu alaihi Wasallam, da nake yi miki tarihi ko?"" Ummi ta jinjina kai ta ce ""Eh, Ina son tarihi"""

"""Yauwwa ummina, mai kiran salla a zamanin Annabi Sallallahu alaihi Wasallam, sayyiduna Bilal radiyallahu an hu,"

"ba™i ne, kuma Annabi bai taSa ™yamarsa ba, haka sahabbai ma"""

"Ummi ta yi shiru ta ce ""To mama kin ce in din ga son annabi, to masu tsokanata ba sa son annabi ko?"""

"Shiru mariya ta yi, tana tunanin wane bayani za ta yi wa ummi, dan duk da rashin sakewarta da mutane, idan tana"

"tare da mamanta, akwai surutu."

"Iya ta ce ""Kin ga kar ki sakawa yarinya wani tunani daban, ki gaya mata gaskiya kawai, mummuna ce ko ki so ko ki ™i"""

"Babar su magaji ta kwashe da dariya ta ce ""Iya wannan jika taki, ai tun yanzu yakamata a fara nema mata maganin"

"farin jini, dan za ayi gwagwarmaya kan a samu mai so, dan ina jin Alhassan ranar yana cewa; da zai samu igiya da ya zargawa ummi, ya tafi tashe da ita a matsayin Wan biri"" tayi maganar tana SaSSaka dariya ita da iya, ba tare da tunanin, ya mariya zata ji a zuciyarta ba ko ita yarinyar, ummi tayi ™uri tana kallonsu, duk da yarinya ce, ta san cin mutunci."

"Mariya ta ce ""Biri kuma, ummin za a yi wasan biri da ita, kuma ki ke dariya, shikenan bakomai"" tayi maganar cikin"

"™unar rai, ta kama hannun ummi suka tafi Waki."

"""Mama, da gaske ni biri ce? M, for monkey na bayan littafina?"""

"Mariya ta goge hawaye, ta ce ""Ummina ke mutum ce, mai kyau sosai da sosai, kar ki sake haWa kanki da biri kin ji ko?"

"Kina da kyau sosai, kalli gashinki fa, duk garin nan kin ga mai irin gashinki?"""

Ummi ta girgiza kai alamar a'a.

"""Yauwwa ummi, idonki ma mai kyau ne, ina son idonki, duk garin nan babu mai irin idonki""."

"Ummi ta taSa idonta ta ce ""Sai akuya ko?"""

"""Akuya kuma?"""

"""Eh, malamarmu ce ta faWa, ta ce ni da akuya irin idonmu Waya, eyes sunan ido da turanci in ji anty"""

"Mariya ta yi shiru tana kallon ummi, yarinyar na cikin taskun ™alubale, daban-daban, har a kai ga malamarta na kamanta ta da akuya."

"Iya kuwa ta cigaba da hurawa balarabe wuta, da shi da mariya, cin kashin yau daban na gobe daban, har ´an uwansa ma, ware shi suke a wasu abubuwan saboda ba shi da kuWi, haka zalika mariya ta cigaba da yi wa iyalan gidan bauta,"

"idan anjima su yi mata rashin mutunci, ko a ci zarafin ´ar ta a gabanta ba."

"Kusan kullum sai ummi ta ce ba ta son makaranta, dan kuwa abun da mariya ta fuskanta, ba iya Waliban ne ke tsokanarta ba har da malamansu a ciki."

"Dan idan ummi ta zo da aikin gida, tayi a gida, sai ta ce ba zata nuna wa malamarsu ba, idan ta tambayeta dalili sai"

"ta ce ""Malamarmu cewa take yi in fito gaban Allo, a tafawa ´ar ba™a saran daddawa, ayi mini dariya, ni kuma in yi ta kuka sosai, bana son ana tsokanata"""

"Ba ™aramin Saci ran mariya yayi ba, Dan haka da kanta ta je makarantar, ta ro™i headmaster, a kan ya taimaka ya tsawatar a kan abun da ake yi wa yarinyar, kar son karatun ya fita daga kanta gaba Waya."

"Yayi mata al™awarin yin hakan, sai dai ba ta canza zani ba."

"Ummi na ta kaiwa tana komowa a tsakiyar Wakinsu da safe, kasancewar yau ba makaranta, sai fama take da uban"

"gashinta, ta™i tsayawa a gyara, mariya sai fama take da ita ta nemi wuri ta zauna."

"Ta kalli babanta da yake cin abinci ta ce ""Baba kafi mama loma"" tayi maganar tana dariya."

"""Eh mana, baki ga na fita girma ba?"""

"Ummi tayi dariya ta ce ""To ni kuma gaba Waya ´an gidan nan, na fi su loma"""

"Mariya ta ce ""Ke Win, sai ka ce abinci ki ke ci"""

"""Mama nafi duk ´an yara girma fa"""

"Babanta ya ce ""Kin fi su lafiya ne, kuma kin fi su kyau shalelena"""

"Ta kama kumatunta ta ce ""Iya ta ce bani da kyau ai"""

"""A'a ke kyakywa ce sosai"" mi™ewa ummi ta yi ta fita daga Wakin, tana le™a ba™on Wan magen da yake wasa a tsakar gida."

"Mariya ta yi ajiyar zuciya ta ce ""Baban ummi, kana ganin ummi zata iya samun miji tayi aure?"""

"Ya kalle ta ya ce ""Meyasa zaki faWi haka? Kina mahaifiyar ta, kema kin fara biyewa surutun mutane na cewar ´armu"

"ba ta da kyau mummuna ce?"""

"""Ba haka bane ba, abun yana taSa ni sosai da sosai, har malaman su ummi su da zasu tsawatar wai har da su a cikin tsokanarta, babar su magaji wai har da cewa Alhassan ya na kiran ummi da biri, kuma ta faWa suna dariya"""

"Jiki a sanyaye ya ce ""Biri kuma? Cin mutuncin ya kai haka? Wallahi mariya ummi ba mummuna ba ce ba, tana dai da"

"duhu ne, kuma ™wayar idonta ce da ba irin tamu ba, amma ba mummuna ba ce ba"""

"Mariya ta numfasa ta ce ""Ni ba wannan ba, duk wanda ya ci zarafin ummi, na san bani na halicceta ba, amma abun"

"da yake damuna, a zamanin nan yarinya ta kai mutuncinta Wakin aure, ya ta ™are ina ga idan ummi ta samu miji, gaya"

masa zamu yi ga abun da ya same ta? Idan muna gaya masa waye shaida babu tabbacin a lokacin dukkaninmu da

"muka sani muna raye. Idan kuma muka rufa, zai yi mata kallon mutuniyar banza, ummi ta san abun da ya faru da ita mummunan abu ne."

"Ina tausayawa yarinyar nan abubuwan da suka baibaye rayuwarta, ina tausayawa ™alubalen da zata fuskanta wata™ila bana nan a lokacin balle na tayata kwasar raWaWin, amma ina tausayawa ummi, idan ba ta samu miji mai tawakalli ba, za ta fuskanci wula™anci, wa zai so mini ummi tsakani da Allah, ya karSi ™addarar da ta same ta? Wallahi baban ummi ba zan yafe wa yaron nan ba, ya cuce ni ya cutar da rayuwar ummi, ko idan ta ™ara girma zata manta oho, haryanzu bata yadda na bar ta a Waki ita Waya, an cuce ni"" tayi maganar kuka mai ™arfi yana ™wace mata."

"Balarabe yayi ajiyar zuciya, yana jin Waci a zuciyarsa ya ce ""Wallahi mariya ni kaina abun nan yana ci mini zuciya, ba yadda na iya, mahaifiyata ta riga ta yi mini kandagarki, ™etare maganar ta na iya shafar mu baki Waya, amma in sha"

"Allah, ina sanya ran Allah ba zai wula™anta ummi ba, dan Allah kiyi ha™uri mariya, wallahi idan kina kukan nan, sai na ji kamar na bijirewa umarnin iya, na Wau matakin abun da aka yi wa ummi""."

"Ta share hawayen ta, ta ce ""Kar ka yi haka, aikin gama ya riga ya gama, ko ka Wau mataki, wannan wani miki ne a"

"zukatanmu da ba zai taSa warkewa ba""."

"Yayi shiru ya zubawa mariya ido, shi kansa ya san mariya ba ™aramin ha™uri take yi ba, zama da shi. Tsakaninta da shi"

"babu wata matsala, amma azabar wahalar da take a gidan, duk ta rame ta yi duhu, soyayar kirki ba sa samun sakewa su nunawa juna, saboda azabar iya."

"Ihun Ummi suka ji, hakan ya sanya su yin rige-rigen fita tsakar gida da gudu."

"Ummi suka tarar da Alhassan Wan wurin saminu, ya tattara gashin ummi, ya murWe shi a hannunsa, jijiyoyin kanta"

"sun mimmi™e, duk ta gigice."

"A guje mariya ta ™arasa, ta hankaWe shi, ta ™wace ummi da ke kuka."

"""Alhassan me ummi tayi maka ka murWe mata gashi haka?"""

"Cikin fitsara yaron ya ce ""Šan magenmu take mana wasa da shi"""

"A fusace mariya ta ce ""Kuma saboda zalunci ka rasa me zaka yi mata, sai izaya da gashinta?"""

"""To waye ya ce ta taSa mana magenmu, ana ta nemansa?"""

"Cikin zafin rai, mariya ta Wauke Alhassan da mari."

Sai da balarabe ya waro ido.

"""Tura ta fara kaiwa bango, wane irin zalunci ne haka? Ummi fa ´a ce ba baiwa ba, wallahi duk wanda ya kuma dokar"

"mini ´a sai na ci ubansa. Dama a ciki nake da kai, na samu labarin kana ce mata matashiyar buranya, uwarka ce mai kama da buranya ba ita ba"""

"""Wayyo Allahana iya, a taimake ni ta kashe mini ido"" Alhassan ya wage baki yana kwarmato"""

"Bakomai ya hana balarabe taSuka komai ba, face sanin idan iya ta fito ba ™aramar tijara zata yi ba, kuma ™arshe su zata Worawa laifin""."

"Buje a hannu iya ta fito daga banWaki tana faWin ""Menene haka? Kashe yaron zaki yi me yayi miki?"""

Alhassan ya kwashe ™arya da gaskiya ya gaya mata.

"Ta kuwa hau sababi ""Balarabe kana tsaye take neman yin kisan kai, shikenan an taSa ´ar gwal sai tayi yin™urin cire"

"masa ido. Duk Wawainiyar da ubansa yake yi a gidan nan? Wace irin Wawainiya ce ba yayi da ku, wasu lokutan ba har ciyar da kai yake ba da iyalin naka, da baka ganin kowa da mutunci sai su, saboda zuciyarka ta riga ta mutu, baka da amfani ka kashe zuciyarka ka auri mai ™ashin tsiya, baka da komai sai sokonci da son mace, wadda maganarta ta fi tawa, tun da tana baka abun da bana baka, to kayi ™o™ari ta kashe masa Wa, wallahi duk matakin da ya Wauka a kanku, babu ruwana ko da kuwa wurin hukuma zai kai ku"""

"Cikin takaici mariya ta ce ""Wato iya saboda baban Alhassan yana da kuWi shi ne Wa, da idan aka Waukar masa mataki"

"ba zaki hana ba, ummi ce da aka ketawa haddi ba ´a ba? Iya Allah fa"" cikin hanzari balarabe ya girgiza mata kai. Cikin"

Wacin zuciya ta koma Wakinta.

"""Ai da ka bar ta ta cigaba da gaya mini magana, ta tabbatar mini da bata da tarbiyya, kai ban da ina tsoron Allah da"

"wallahi tuni na saka ka saketa, ko Allah ya sa ™ofar arzkin ka ta buWe, idan ya so ka auro falla-fallan mata, mu samu ta haifa mana masu kyau, kadara irin arziki"""

"Bai cewa iya komai ba, ya shiga Waki, ya tarar mariya ta rungume ummi, tana aikin kuka. Zai yi magana ta Waga masa"

"hannu, ta yi masa alamar ya rabu da ita, haka ya ™yaleta ya fice."

"Har ya tafi kasuwa tunani yake yi? Ko haya zai nema ya tashi ya bar gidan, ya san ba iya ce kaWai ke da hakki a kan sa"

"ba, iyalansa ma na da hakki a kan sa, kuma suna bu™atar walwala, amma iya ta takura su da yawa, kuma ya san ba zai iya biyan haya ba, kuma duniya zata zage shi, ya kasa zama da matarsa ya fifita iyalansa a kanta, haka yayi ta tunani, ba tare da samun mafita ba."

"Mariya ma wuni tayi tunani da zancen zuci, ita kanta ta san bata isa ta tafi gida ba, ta ce tayi yaji saboda takurar"

"uwar miji ba, ba babanta ba yayyenta maza kawai sun ishe ta, babu mai goya mata baya, dan ko hirar take musu, idan ta je ganin gida, sai ace uwa ce a wurinta idan da kara da tarbiyya."

"Gidansu irin iyayen nan ne masu kashe ´a´ansu su raya na wani a gidan aure, saboda dattaku dan gidansu gidan malamai ne."

"Kuma ko kusa ba zata iya gaya musu cewar an yi wa ummi fyaWe ba, saboda ita kanta da take ta hayagagar rashin bi wa ummi hakkinta, tana yi ne saboda abun yana damunta, mussaman nuna wa da ake yi ´ar kamar ba ta da amfani, saboda babanta ba shi da kuWi."

"""In sha Allah ummi sai ahalin nan sun kwanta a kafaWarki, Allah ya nesanta ki da talauci, ya baki ikon cin jarrabawar"

"nan da ni da ke baki Waya. Allah shi ya san dalilin da ya sanya yayi ki a haka, kuma ya jarrabeki Allah ya baki mai kula da ke, ko bana raye"" haka ta wuni cikin kuka da damuwa."

"***"""

"Rayuwa ta cigaba da tafiya, umma ta cika shekaru shida a duniya, sai dai bata sauya zani ba, domin kuwa gorin yau daban na gobe daban, haka iya ke yi, a kan cewa balarabe ba ya iya tsinana komai, a gidan komai shi ne koma baya."

"Haka zalika balarabe, ya fara tunanin mi™ewa ya nemi kuWi, ko dan samawa iyalin sa farinciki da kwanciyar hankali,"

"mussaman ´ar ™aramar yarinyar nan, da aka mayar da ita tamkar wata halitta daban."

"Yau suna kwance da daddare tare da mariya ya ce ""Maman Ummi kin san wani abu?"""

"Ta ce ""A'a"""

"""Ina ga ´an kuWaWena da nake tarawa, zan je birni in ga abun da zan iya yi, ko Allah ya sa na samo arziki"""

"Mariya ta kalle shi ta ce ""Baban ummi baka yadda da yadda Allah ya ajiye mu ba? Na san babu daWi abun da iya take yi maka, amma dai ka yi ha™uri da barin garin nan, ka tafi yawon neman kuWi, raba bawa da arziki sai mutuwa, dan"

"Allah kayi ha™uri"""

"Ya gyara kwanciyarsa ya ce ""Maman ummi, tun da abun nan ya faru da ummi, ji nake tamkar ina kan wuta, gidan"

"galibi duk maza ne tana cikin haWari, sannan ki duba ki ga yadda ake yi mata a gidan nan, Wazu fa suna tafe da yarinyar nan da take Waukarta ta tafi da ita islamiyya, yara suna tsokanarta ba™ar tukunya mai ™yalli, ba ki ji zuciyata ba, wallahi yanzu haka bani da burin da ya wuce tashi na bar gidan nan."

"Da nayi tunanin ko kano zan je wurin yaya hashimu idan da wata hanya da zai Wora ni a kan kasuwanci, to kuma bana son na je na Wora

3 / 74