CUTARWA COMPLT BY AYSHERCOOL

Author :  AYSHERCOOL Category :  African Stories & Novels

Chapter   23 / 74

66K to 69K   out of 219.4K words

ke kuka, har ki ke nema ki kafirta"

"ni? To ki arata ummi, amma zaki ce na gaya miki, wallahi babu wanda zai aureki da wannan bain da gidadancin"""

"Ummi tayi murmushi mai ciwo hawayen na zubowa ta ce ""Ba ke ki ka fara faWar haka ba maryam, an daWe da gaya"

"mini ba zan auru ba ni mummuna ce, dan haka ban sa aure a ka ba dama, nima na san maza farare suke so masu kyau, in dai ubangijina yana sona shikenan maryam"" tayi maganar cikin sanyin halinta."

"Sai kuma jikin maryam yayi sanyi, ta ce ""Am sorry please, ba ina nufin na Sata miki rai ba ummi, mafita nake nema"

"miki"""

"Kawai ummi ta tashi ta bar ajin, domin kuwa an kaWa ararrawar tashi."

"Kai tsaye gida ta nufa, tana tafe tana hawaye ta cikin niabinta."

***

"Babban mutum ne zaune mai cike da nutsuwa da kamala,kallo Waya zaka yi masa ka san a cikin hutu yake, falon da yake zaune kawai ya awatu dai-dai gwargwado."

"A hankali yake zuar tea Win da yake hannunsa, yana kallon atuwar plasma tv da ke manne a jikin bango, sai dai kana gani ka san ba kallon yake yi ba, zancen zuci yake yi."

"""Alhaji ya dai?"""

Wata mata tayi maganar tana oarin zama a kusa da shi.

"""Bakomai"" yayi maganar yana murmushi."

"""A'a da komai mana, zancen zuci ka ke yi, shekaru sun ja, yakamata a din ga rangwatawa kai, kar wani ciwon ya"

"kama ka"""

"Ya ajiye cup Win hannunsa ya ce ""Da ciwo zai shigeni saboda tunani, da tuni ya shige ni hajiya. Lokaci yayi da"

"yakamata na huta, huta nake buata amma ki duba ki ga haryanzu ban huta ba, ni nake fama da harkar kasuwancina, gaba Waya yaran nan basu saka komai a gaba sai shashasha. Na tara dukiya, suna ta bushashasha, gaba Waya babu hankali ko nutsuwa a cikinsu da zai tallafe ni yanzu, su karSi ragamar kasuwancin ni na huta."

"Ko kartun kirki babu wanda ya tsaya ya kammala a cikinsu, duk da tarin kuWin da na kashe musu da sun yi karatu,"

"amma kalli duk shashanci suke yi, suna manya amma duk babu mai saiti a cikin su."

"Matan ne kawai nutsatsu a cikin su, su kuma duk matan wasu ne, ragamar babban kasuwanci irin wannan ma ai ba"

na mace bane ba.

"Jiki a sanyaye ta ce ""Na sani Alhaji, ka yi hauri, ka Wan ara musu lokaci, mu cigaba da addu'a, kuma a cigaba da jan"

"su cikin harkar kasuwancin"""

"""Eh su arasa ni ba. Wane lokaci zan ara musu? Salim na da shekara talatin da ku san biyar, dukkansu babu yaro a"

"cikinsu, wane lokaci zan basu banda wanda na basu a baya. Zan yanke hukuncin da nake ganin ya dace kawai""."

"Ta Wan gyara zamanta ta dube shi ta ce ""Wane hukuncin kenan?"""

"""Zaki gani idan na yanke"" yayi maganar yana sauya channel da remote."

***

"Ummi kuwa tsaye take a gaban mudubin Wakinta, tana Waure da zani kasancewar daga wanka ta fito, ta shiga are wa kanta kallo a jikin madubin."

"Ta saki gashin nan a bayanta, ta din ga kallon wayar idonta, da take brown sosai, cikin idon kuma fari al, ta gangaro kan fatarta da take jie da ruwa, baa mai Waukar ido."

"Ta kalli gashin ta, ta Wan shafa shi a hankali, tana tambayar kanta wace irin halitta ce ita haka. Ita kanta ta san ba ta taSa ganin mai irin halittarta ba, a asar hausa duk wanda take haWuwa da su, ba ta taSa ganin mai irin gashin kanta da kuma wayar idonta ba."

"A hankali ta murza fatar jikinta, tana tuna maganganun su kausar masu sosa rai, wai wankan bai asarar ruwa. Baar mace bolar maza, irinta kuma bolar da ko recycling ba za a iya yi ba."

"""Da gaske ba zan yi aure ba, saboda maza ba sa son baar mace mai duhu kamar ni? To haka zan cigaba da zama a"

"gidan kamar baiwa? Ko kuma zasu mayar da ni auye daga baya, saboda ban samu miji ba? Dama Iya ta ce babu wanda zai aureni, saboda munina. Idan ma na yi aure zai iya ara aure ya daina kula ni, saboda ni bani da kyau, to wa ma zai ce yana so na?."

"Ko dai maryam da gaske take hijjabin da nake sakawa, da kuma munina ba zai bari a aureni ba?"""

"Ta dubi irjinta, da tudunsu ya Waga sosai."

"Ta girgiza kai ta ce ""Ni ba zan iya bari a ga jikina ba, kuma ba zan saSawa Allah ba, idan na yi bleaching na raina"

"halittar da yayi mini kenan. Ya bani lafiya bani da wani mummunan ciwo da yake hanani sukuni, sai jarrabawar rayuwa da tsananinta bai sanya na rabu da rai na ba"""

"Istigfari ta hau yi, duk hawayen idonta ya kasa daina zuba."

"""Yaya ummi"" ta jiyo muryar noor."

"Tayi saurin share hawayenta ta ce ""Na'am ar gidan anty ummi"""

"""Ki Wora ni a kan mudubin na taSa gashinki"""

"Ummi ta yi murmushi, ta Wora noor a kan mudubinta, noor ta saka hannu biyu ta kama gashin tana dariya."

"Can sai ta urawa ummi ido, ta ce ""Kuka ki ke yi?"""

"Ummi ta girgiza kai ta ce ""A'a mama""."

"Noor ta kai hannunta ta shafo sauran hawayen ta ce ""Kuka ki ke yi, maama ce ta dake ki? Ko su anty intee ne?"""

"Ummi ta ce ""A'a mura nake yi ne, zauna a kan katifata na saka kaya"" tayi maganar tana ajiye noor a kan katifar."

Noor ta din ga tsalle a kan katifar tana wae-waenta na yarinta.

***

"Iya da idris fa sun haWu da wanda suka fi su tashanci, dan mussaman uwar hindu ta din ga tatsarsu kuWi, wai hindu ba ta da lafiya, za a saya mata magani, yadda ake kula da kowacce mace mai ciki, dole a kula da Hindu, tun da da bai yi abun da yayi ba, da hindu ba ta samu ciki ba."

"Dama akuyancin sa ne ya hana su bashi hindu, dan haka tun da ya hilaceta ya Sata ta dole ya kula da ita, saboda sun san ar su ba lalatacciya ba ce ba a baya."

"Yadda baban hindu yayi alawari, sai da ta haihu, ta haifi santaleleliyar jaririya, cibiya kawai aka yanke, aka naWo jaririyar a zani, har da mahaifarta suka kai suka direwa Iya a tsakar Wakinta, sai tsala ihu take yarinyar."

"Mutane kuma suka taru a gidan, arshen tonon asirin dai da asiri ya tonu, domin kuwa rana tsaka anwar babar"

"hindu suka zo suka kawo jaririyar, sannan suka sanar da iya cewa, sun saka yara sun kama wani aton rago da iya ke kiwo a waje, an kai shi can gidan za a yankawa mai jego bayan kwana bakwai na auri an sakawa jaririya sunan Iya wato Hajara."

Ayshercool

8081012143.

*CUTARWA!*

*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*

P19

FOLLOW ME ON WATPAD VIA THIS LINK.

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefr

iends

"Masu neman free books Wina, da free pages duk akwai a kan watpad account Wina. Irinsu"

Abduljalal

Wata kissar sai mata Wuta a masaa Cutarwa

anwar maza

Gaba da gabanta

Aidata

RuWin uruciya

Zaku iya samun paid pages Win a Arewabooks @ayshercool7724. Ko ku tuntuSe ni kai tsaye ta lambar wayata.

8081012143.

And also don't forget to subscribe my YouTube channel via this link.

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Ayshercool.

PAID ADVERT!.

"Ina uwargida, amare, har ma da an mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini,"

masu daWi da amshi.

"Mafaka gidan amshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku"

Oll types of Turaran wuta

Sandal Halut Irik Difur Gab Gab Kajiji Habil Nabak Humra

Kulakcha Dilke da kalta Kayan

Garan jiki Muna turara Kaya

Kujerar garan jiki Kannada

Madarorin turare masu kamshi Man garan gashi

Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche Ku nememu a wan nan no 08065728702 08025453921

*TALLA!TALLA!TALLA!*

"*INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA AN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON AWATA GIDAJENSU DA HAAUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAAUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*."

"*BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAAUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU*"

"*MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ARIN BAYANI, KU TUNTUE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUI GIDA*"

"BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUI."

P19

"Tun da Iya take, ba ta taSa cin karo da tashin hankali irin na yau ba, gida ya cika da mutane, ana ta salallami, yayin da"

Idris ya kulle kansa a Waki ya kasa fitowa saboda kunya.

"Tabbas da yana da kuWi babu abun da zai hana shi guduwa, kodayake yayan Hindu yayi masa kashedin muddin ya"

gudu sai ya Waure babansa.

"Yarinya ta din ga tsanyara ihu, a tsakiyar Wakin Iya."

"Su kuma suka wanda suka kawota suka gama tijararsu da rashin mutunci, suka fice suka bar gidan."

"Iya ta ce a Wauki ar a kai wa babar Idris, dan ita ba ta san ya za ta yi da jaririya Wanyen goyo haka ba, ita ko nonon"

"ma yanzu babu sun suWe sai fata, dan haka sai dai uwarsa."

"Babar Idiris kuwa ta ce ""Iya ke yakamata ki rie wannan a ba ni ba, tun da dama sunanki suka sawa yarinyar, ba yadda ban yi ba na bawa yarona tarbiyar da ta dace, amma ki ka i saboda yana da sunan mahaifinki, kin Wau son"

"duniya kin Wora masa. Ko laifi yayi na yi masa faWa, sai ki ci mini mutunci."

"Dan haka Iya ke zaki kashe wannan wutar, wallahi ki ka bani jaririya ban san yadda zan yi da ita ba""."

"Cikin fusata Iya ta ce ""Ni ki ke gayasa haka lami?"""

"""Iya ba rashin kunya ba ce gaskiya ce, da kin bari na bawa Wa na tarbiyya da haka ba ta faru ba""."

"""Rufe mini baki, har wata tarbiyya ce da ke da zaki bawa wani? Ke Win a yaya ki ke? Ki zo ki Wauke yarinyar nan ki san"

"yadda zaki yi da ita"""

"Lami ta ce ""Ban gane ba iya, ni na yi mata cikin, wallahi ba zan Wauka ba"""

"""Lami uwata ce take faWa kina faWa?"""

"Lami ta ce ""Maganar gaskiya ce fa, in Wauki a in yi yaya da ita? Ta in da aka hau ta nan za a sauka ai"""

"Iya ta ce ""Rabu da ita, na san maganinta, yanzu abun da ya fi dacewa shi ne ka je, ka ce musu mun amince a Waura"

"auren nan su karSi ar nan. Amma wallahi Idiris ya cuce mu, ya janyo mana masifa da abun kunya, ga ragona da nake son sayarwa lokacin sallar layya, sun tafi da shi, ku san yadda zaku yi ku karSo mini ragona""."

"Ilyasu ya ce ""Iya yanzu waye yake ta rago, muntuncinmu ya gama zubewa"""

"Baban su Idris ya ce ""Ina ga kawai mu je mu samu iyayen nata, ina sa'adatu ta zo ta yi wa yarinyar wanka, a saka"

"mata sutura, mu je gidan su Hindun"""

"Sa'adatu ta ce ""TaS ar gaba da fatihar? Wallahi ba zan taSa azanta ba, sai dai uwarsa ta wanketa, haka kurum in"

"taSa masifa"""

"Sakin baki Iya tayi tana cewa ""Wai me yake damun matan nan ne? addara ce fa, kowa zata iya faWa a ka"""

"Sa'adatu ta ce ""A'a irin wannan addarar Allah ya tsayar da ita a kan wanda ta sama"""

"Haka dai gida ya yamutse, kamar ayi yai."

Da yar babar Idris ta yi wa yarinyar wanka.

***

"Yau lahadi, ummi sun yi hutun makarantar islamiyya, sai dai ta kasa zama wuri Waya ta hutawa ranta, dan kuwa ta san babu wanda ya bata wannan damar."

"Dan haka wuni tayi tana kaiwa tare da komowa, wurin yin kwalema da tsabtace ko ina na gidan."

"Tana sanye da dogon hijjabinta, da ya zame mata tamkar uniform, duk zafi ko sanyi, ko a cikin gida, da hijjbi take"

"yawo, dan ko da ta fara irgar dangi, tsananta rufe jikinta tayi, balle yanzu da take aji biyar na sakandare ta ara cika sosai."

"Dan idan tana girki, wuta ta sha kamo mata hijjabin, ko ta yi Sarna a kitchen, farida ta ci mata mutunci, amma hakan bai sanya ta daina sawa ba."

"Hijjabin jikin nata ya sha jiki ya koWe, sai dai kasancewar a goge yake, muninsa ya ragu."

"Tana mopping noor na biye da ita suna hira, ta saki jiki tana biyewa noor, suna shiririta."

"amshin turaren da ya cika falon ne, ya sanya ummi Waga kai, aikuwa tayi tozali da intee ta fito, sai taku take Waya- Waya."

"Ta sha doguwar rigar abaya, amshin kansa ummi ta kasa tantance wane iri inteesar take yi."

"Tayi light make up, sai wani yatsuna fuska take yi."

"Ummi a ranta ta ce ""Tubarkallah masha Allah, kyau yana in da yake"" ba iya kyan da inteesar tayi ne ya burge ummi"

"ba, doguwar rigar jikinta ma ta tafi da ita, ta ji ina ma ita ma tana da ita ta saka, taga ya zata yi a ciki, dogayen riguna irin haka suna burgeta""."

"""Ke! Kalli gabanta kar ki kama mini kurwar a"" farida tayi maganar cikin tsawa."

"an zabura ummi tayi, ta cigaba da aikin gabanta."

"Kausar kuwa ta kwashe da dariya, yadda ummin ta Wan shagala da kallon yayarta kamar shashasha."

"Farida ta yi murmushi ta ce ""Farar mace...."

"Caraf kausar ta ce ""Alkyabbar mata"""

"""Farar mace kalar kyau, kalar babban gida da manyan motoci, kalar hutu da jin daWi farar mace mowar mata"""

"Inteesar kamar kanta ya fashe, saboda kirarin da mamanta ke yi mata."

"Ta dubi ummi ta ce ""Baar mace borar gida""."

"Farida ta amsa da ""Idan ta samu mijin ba"""

"""Idan ba ta samu ba kuma ta dauwwama ar wanke-wanke"""

"Ummi tayi burus, ta cigaba da hirarta da noor, tana jin zuciyarta na wani irin zafi."

"Intee ta yamutsa fuska ta ce ""Maama bari na je, ya kirani a waya, ya zo""."

"""To shikenan, a kula sosai, a iya karairaya da jan hankali"""

"""Kar ki damu maama, ammm ummi kin kammala girkin da na saki?"""

"""Na gama"""

"""Ok, ki shirya mini komai a tray, in the next few minutes ki kawo mana"""

"Kallon asan ido ummi tayi mata, ta yi mata girkin tarar saurayi, kuma ita za ta kai musu."

"Tayi ajiyar zuciya, tare da Wan girgiza kanta."

"Farida ta ce ""Ke ummi in tambayeki mana"""

Ummi ta Wago tana kallonta.

"""Wai dan Allah ina babarki ne?"""

"Ummi ta Wan yi jimm, dan ba ta zaci wannan tambayar ba."

"""Ban san in da take ba"""

"""Kamar yaya baki san in da take ba?"""

"Ummi ta ce ""Ai tun ranar da ta tafi, Iya ta hana a tafi da ni, ban sake ganinta ba, sau kusan uku an uwanta na zuwa"

"su tafi da ni, amma ta i bayar da ni""."

"""Kuma saboda rashin lissafi, ba ta sake neman in da ki ke ba, daga ita har an uwanta, yau shekarar ki nawa a gidan nan, ko kare daga dangin majaifiyarki ba wanda ya nemi in da ki ke, wace irin uwa ce wannan? Ko suma ba sa"

"buatar ki ne, an rasa mai rie ki, aka lia mana, anya babu lauje cikin naWi a game da ke, ta hanyar aure aka same ki kowa yake gudunki?"""

"Tuni idon ummi ya fara tara hawaye, cikin oarin kare mahaifiyarta ta ce ""Ai an ce ba ta da lafiya, tun da aka wace"

"ni, ta haihu Wan babu rai, ta samu matsalar wawalwa"""

"""Mahaukaciya ce kenan?"" Kausar ta faWa kai tsaye."

"Farida ta ce ""To ai mahaukaci ya san Wan sa, jahilci kawai da rashin sanin ciwon kai, idan ita ba ta da hankali, an"

"uwanta fa?"""

"Ummi ta yi shiru, ta kasa magana."

"Farida ta shigo falon a fusace ta ce ""Wai ke ummi me ki ke taama da shi ne? Cewa fa na yi ki kawo mana abinci,"

"amma dan wulaanci kin shanya ni, bana son rashin mutunci"""

"Ummi ta jingine mopper ba tare da ta ce komai ba, ta je ta Wauki tray, ta kai wa saurayin intee. Kallo Waya ummi ta yi masa ta sunkuyar da kai, gaba Waya bai yi kalar mutane masu Wa'a ba."

"Tunanin abun da farida ta faWa ya Warsu a ran ummi, idan an ce mamanta ta samu matsalar wawalwa, to an"

"uwanta fa, yakamata ace sun nemeta, ta san da a hannunsu take, ba za su wahalar da ita sosai ba."

"Sakawa tayi a ranta a wannan karon idan kawu ya zo gida, za ta tuna masa alawarin da yayi mata na binciko maata"

"in da mamanta take, dan ita ba ta taSa jin ko sunan garinsu wani ya faWa ba."

***

"Can gida gagarawa kuwa, an samu da yar da siWin goshi, su hindu sun karSi jaririya, babanta ya ce idan ta yi arba'in,"

"su zo su kawo kuWin aure, kuma yadda ake auren budurwa komai da komai, haka za a haWo mata, kuma shayarwa da hindu, za ta yi, sai an biyata kuWin shayarwa ko su dawo musu da jaririyar."

"Kan su dawo gida, sai da babanta ya caje su kuWi masu yawa, sannan suka dawo, suka sanar da Iya abun da babanta"

ya faWa.

"Iya ta ce ""Innalillahi wa Innalillahi raji'un, wannan wane irin matsiyatam mutane ne? Sai an yi mata komai kamar"

"auren budurwa ba ta riga ta haihu ba, har wani kuWin shyarwa suke nema, a gidan ubanwa aka taSa haka, ai da an dawo da ar a din ga bata nonon akuya""."

"""A'a iya, a samu a lallaSa mu rabu da mutanen nan lafiya, kowa ya Webo da zafi ai bakinsa, gobe ba ya ara ba""."

"Da labari ya iske idiris kuwa, masifa ya fara yi, yana balooon shi fa ba ya son Hindu, ban da zalunci yarinyar da har"

"haihuwa ta yi, tayaya za a ce wai ayi mata kaya kamar budurwa, saboda son zuciya."

"Cikin tsananin fusata mahaifinsa ya ce ""Rufe mini baki, ko na turmushe ka a wurin, mara mutunci, muna zaman"

"zamanmu ka janyo mana masifa, ka sanya kowa a tashin hankali, kuma wallahi ko

23 / 74