CUTARWA COMPLT BY AYSHERCOOL

Author :  AYSHERCOOL Category :  African Stories & Novels

Chapter   15 / 74

42K to 45K   out of 219.4K words

karkarwa saboda sanyi."

"Ruwan, bai gama Waukewa ba, ta fara takawa a hankali ta na ™an™ame jikinta saboda ™yan™yamin ruwan da ya kwaso dagwalon unguwar ya shigo ya taru a gidan."

"Šaya Wakin ta nufa, sai dai kasancewar ba taga babu ™ofa, a buWe yake, shima ta tarar ya malale da ruwa, babu in da za ta zauna, ta samu wuri Waya ta raSe tana cigaba da kuka."

"Har garin Allah ya waye ummi na tsaye, babu wurin da zata raSa ta zauna, saboda an yi ruwa ba Wan kaWan ba."

"Gari ya fara haske tana sanya ran ya buWe ™ofa ta suturta jikinta, amma bai buWe ba, ta din ga fargabar kar a zo gidan"

a tarar da ita jikinta babu sutura.

"Sai da gari yayi haske tar, sannan ya zare sakata ya fito ya shiga banWaki, tana hangen sa ta taga, ganin ya shiga"

"banWaki, ya sanya ta fita ta shiga Wakin, ta kwashi kayanta da duk ya yayyaga, ta saka, jikinta sai wata irin tsuma yake yi, saboda sanyi, ga ciwo da jikinta yake yi mata da ™afafuwan ta."

"A gurguje ta yi alwala, ta koma Wakin yin sallar asuba, duk a Warare take cikin tsoro take yin ta."

"Aikuwa a raka'a ta biyu ya dawo Wakin, bai damu da salla take yi ba, ya hankaWeta, saboda wata irin tsanarta da yake ji a cikin zuciyarsa."

"Ta mi™e ta cigaba da sallar, ya tsaya a kanta yana kallon ta yana huci, da ta idar da sallar, ta mi™e zata bar masa"

"Wakin, amma ya janyota ta baya, ya sake hankaWata ™asa."

"Wata irin ashar da yayi mata sai da ta kalleshi a firgice, ya din ga Wura mata ashar yana cin mutuncin ta da na"

"iyayenta, har da mahaifinta da ba ya raye a duniyar, har da kiranta da ´ar iska lalatacciya."

"Ummi ta yi shiru ta sunkuyar da kanta ™asa, ta nemi hawayen ma gaba Waya ta rasa."

"Har zai fita ya dawo, ya din ga dukanta hannu da ™afa, cike da tsana da jin haushin ta."

"Ya gama rashin mutuncinsa ya fita, ta tashi a hankali, ta koma gefe tayi zuru da ido."

"Sai a lokacin kuma ta samu damar yin kuka, jikinta sai ciwo yake yi, ga yunwa tana ji, gashi haryanzu sanyi take ji, ta"

"kwanta a wurin, ta hau bacci."

"Sallamar da Iya take kwaWawa a tsakar gida ne, ya sanya ummi farkawa, ta fito da sauri, ta ga Iya tare da yaya, mahaifiyar su Idris."

"Murmushi ummi ta yi ta ce ""Iya sannu da zuwa, yaya ina kwana"""

"""Ai kya bari mu shigo mu zauna ko"""

"Ta basu hanya suka shiga Wakin, suka zauna, yaya tayi ™uri tana kallon ummi, Iya ta ce ""Ke lafiya na ga kayanki a"

"yayyage?"""

"""Ba komai"""

"""Kamar yaya ba komai, kamar wadda ta yi dambe"" hawaye ne ke shirin taruwa a idon ummi."

"""Kuma dan ™azanta tun da aka kawo ki baki canza kaya ba, yau wurin kwana biyar""."

"Ummi ta buWe baki za ta yi magana, ta kasa hawaye suka riga maganar fita."

"Yaya ta ce ""Menene na kuka kuma ummi?"""

"Iya ta ce ""Sangarta mana, idan zaki yi wa kanki ™iyamullaili ki zauna ki daina wannan kukan shikenan, idan ba zaki"

"daina ba, sai ki yi ta yi, ga kaya nan na Webo miki a kayan auren da aka kaiwa waccan, abun bai yiwu ba, sauran an sayar an bashi kuWin yayi muku cefane, sadakin ki kuma, na bayar a sayo akuya a bayar da kiwo""."

"""Dan Allah iya ki mayar da ni gida, bana son zaman nan"""

"""Ki kiyayeni ummi, tun kan na Sata miki rai, bana son shashanci, ki tashi ki yi wanka ki canza wannan kayan"""

"Tashi ummi ta yi tana kuka, ta fita tsakar gida, suma fitowar suka yi, wai har tafiya za su yi."

"Ummi ta tsaya tana kallonsu, suka fice, wai wata unguwar zasu je, to da me za ta yi wankan, ko ruwa ba ta da shi? Ta"

"koma Waki ta zazzage lesar vivar da Iya ta kawo mata, atamfa ce kala uku, sai sabulun wanka uku, man shafawa Waya da soson wanka."

"Sai kuma 'yar tsala, a ™ulle a leda, ummi ta ture kayan ta kwanta, wani irin zazzafan zazzaSi ya rufeta, saboda dukan"

ruwan sama.

"Sai da ummi ta kwana biyu tana zazzaSin nan, babu abun da ya shafi Idris, da ya dawo zai koreta daga Wakin, bayan"

"ya gama ci mata mutunci da zaginta, wasu lokutan sai yayi mata dukan tsiya ma, duka na cin mutunci, haka take kwana a Waya Wakin da babu ko ™ofa a ciki, idan aka yi ruwan sama, haka zai sameta a Wakin nan."

"˜arshe ma ya watso mata kayanta da ga Wakin da katifa take, ya ce ta koma Waya Wakin."

"Da ya tuna ™arin da ya ji tana yi, da kuma yadda suka din ga lalubeta tana yarinya, sai ya ji ya ™ara tsanarta, da ganin an bashi saura."

"Dama abinci ba a magana, ba bata yake yi ba, wasu lokutan ne idan yaran gidan su za su zo, babar Idiris Win kan zuba"

mata abinci a kwano a kawo mata.

"Tana kwance a Waki tana numfarfashi, zazzaSi da ciwon kai sun ™i sauka, fitsari ya dameta, ta tashi da ™yar, ta je ta"

"yi, tana shirin komawa Wakin, ta ji an ce ""Ummi"""

"Tana waiwayawa taga Na'ima, ai sai ta nemi ciwon ta rasa, cikin wani irin zafin nama, ta rungume Na'ima ta fashe da"

kuka.

"Ita ma Na'iman kuka take yi, ta Wago ummi ta kalleta ta ce ""Ummi ba ki da lafiya ne? Na ji jikinki zafi?"" Ta jinjinawa"

na'ima kai.

"""Innalillahi wa Innalillahi raji'un, yanzu ummi a rasa wanda za a aura miki sai wannan Wan iskan, dukan ki yake yi kenan? Kalli shaidar yatsu a fuskarki"" Ummi dai ta yi shiru, daga baya ta ce ""Mu shiga Waki"""

Saroro na'ima ta bi Wakin da kallo.

"""Ummi kar ki ce ba su yi miki kayan Waki ba?"""

"""Suna can Wakin, koro ni yayi nan shi ne yake kwana a Wakin"""

"Na'ima ta zauna tayi kuka mai isarta sannan ta kalli ummi ta ce ""Wai ke ba ki san in da mamanki take ba? Anya ma"

"kuwa sun san halin da ake ciki?"""

"""Yaya Na'ima nifa tun da aka tafi da mama ban sake ganinta ba, dan Allah idan kin san in da take ki kaini, na gaji,"

"wallahi yaya Idris dukana yake yi, duk jikina ciwo yake zai kasheni"""

"Ta rungume ummi, ta din ga rarrashin ta, ta ce ""Kiyi ha™uri ummi, ban ma san an yi miki aure ba, mama ce ta aika"

"™anin mijina ya gaya mini, Allah yana sane da ke ummi, bari na je gida na kawo miki abubuwan da na kawo miki, sai na kawo miki tabarma da labule, a kafa a Wakin, tabarmar ki din ga kwana a kai"""

"Ummi ta yi ta mata godiya, ta bata abinci, ta aika ™annenta suka sayo mata magani, aka kafa labule, ta shimfiWa"

"tabarma, sai Wakin ya Wan yi kyan gani."

"""Yaya na'ima, dan Allah idan Allah ya yassare miki, ki saya mini wando, nawa ya ™arasa lalacewa, ba zai saku ba"""

"""Ummi meyasa ba zaki din ga zuwa wurin mama kina gaya mata ba? Ya za ayi ki rayu da wando guda Waya, abun da a"

"™alla a rana ana so ki canza biyu"""

"Ummi ta yi shiru, tana wasa da yatsun hannunta, yanzu ma dan ta ™ure ne ta nemi alfarmar na'ima, dan idris ya"

"™arasa shi, wandon har da in da ta kama take ™ullewa."

"Ta ji daWin zuwan na'ima, ta bata abubuwa da yawa, har da kuWi, sai bayan la'asar ta tafi, kuma Allah ya taimake ta,"

Idiris bai dawo ba a lokacin.

"Duk yadda ummi ta so ta yi wa naima bayanin halin da take ciki, kasawa ta yi, ta ji abun yayi mata girma ta faWa, dan"

"haka ta yi shiru da bakinta, ta samu ta saya mata wanduna guda huWu, har da ribbon."

"Duk in da idris ya haWu da abokansa, suka yi masa kirarin ango, da tambayarsa yaushe za su cin girkin amarya, sai ya"

"hau masifa yana basu labarin halin da ummi ke ciki, na mummunan ciwon sanyi da yadda take bugawa, da ™azanta tare da ™orafin ragowa ce aka haWa shi da ita, su yi ta masa dariya, suna ce masa angon WoWWoya."

"Tare da tabattar masa, idan bai yi da gaske ba, sai ya kwashi ciwon."

"Sai dai ko sun tambaye shi dalilin fasa auren sa da Hindu, sai ya Soye musu gaskiyar zancen."

"Haryanzu kuma bai rabu da hindu ba, yana lallaSawa su haWu a wani wurin na daban, duk da tarin kashedi da"

mahaifinta yayi mata a kan idiris.

"Na'ima kuwa a ranar zata koma gidanta, suka haWu da magaji a hanya, suka haWu suka gaisa."

"Ta ce ""Yaya magaji ashe aure aka yi wa ummi babu labari?"""

"Hashim ya ce ""Ke dai bari na'ima, abun ne yazo babu shiri, ni kaina ban san da zancen ba sai ana gobe Waurin aure""."

"Na'ima ta gyaWa kai ta ce ""Amma, ka yi ha™uri da abun da zan ce, wallahi ku din ga gaya wa kakarku da Wan uwanka"

"gaskiya, ya za a katsewa ummi karatunta, kuma a haWata aure da wanda baya ™aunarta, dama ita ba bi ta kanta za ayi, aji ko tana son sa ba, gaba Waya a firgice take a cikin gidan nan, jikinta duk shaidar duka, ya korota daga Waki, Wakin da na tarar da ita, ba ™ofa babu taga, babu abun zama, ba ya bata abinci, wace irin rayuwa ce haka? A gidanku ba ta huta ba, an aurar da ita, ta buWe sabon babi na ™alubale, sai yaushe za ta huta kenan? Meyasa Iya ta tsani ummi ne, kamar ba a cikin jikokinta take ba?"""

"Hashim ya numfasa, cike da damuwa da takaici ya ce ""Biyayyar da iyayenmu ke yi wa Iya, ta samo asali ne ga"

"wasiyyar mahaifinmu, na lallai su yi mata biyayya. Bayan haka ban san dalilin da ya sanya bayan biyayyar suke rufe idonsu a kan gaskiya ba, su kasa nuna mata hanyar da ta dace ba."

"Nayi iya yi na a kan auren nan, sai dai sun fi ™arfina, ni dama ba wani shiri muke yi ba, saboda bani da kuWi, Idris kuma sunan mahaifinta ne da shi. ˜iyayyar ummi kuma, dama ba ta son mahaifiyar ummi, saboda kawu Magaji yana matu™ar son ta, har wasu lokutan baya iya Soye son da yake yi mata, bugu da ™ari, baban ummi ba shi da komai, bai mutu ya bar komai ba, duk da haka dai, ban san dalilin da ya sanya ta tsananta ™iyayyar ummi haka ba."

"Zan cigaba da yi wa idiris nasiha, duk da ba jin shawara yake yi ba, zan kuma biya ta gidan yanzu, in ga halin da take ciki""."

"Jiki a sanyaye na'ima ta ce ""Yakamata kam, ummi na bu™atar kulawa da jaba jiki, har ga Allah ina jin tausayinta sosai"

"da sosai, dan Allah yaya magaji ka din ga zagayata""."

"""Kar ki damu, in sha Allah, ba zai gagara ba, ina godiya sosai da gudunmawar da ki ke bawa ummi""."

"""Bakomai yaya magaji, ummi ™anwata ce, ba zan manta karamcin iyayenta a gare ni ba, da yadda suke girmama"

"iyayena ba"""

"""Haka ne, ki gaida gida, da maigidan"""

"Suka yi sallama, kowa ya tafi."

"Kasa wucewa gida magaji yayi, ya wuce gidan Idris da bai taSa zuwa ba."

"Sallama yayi ya tsaya a waje, ummi ta le™o, tana ganinsa tayi murmushi ta ce ""Laa yaya magaji, shigo baka zo ba sai"

"yau"""

"Ya kalleta duk da tana da duhu, amma ga shaidar mari nan a gefen idonta."

"Ta yi gaba ta ce masa ya shigo, ya ce ""A'a bani abun zama, na zauna a nan"""

"Ta shiga ta Waukko masa tabarma, ta shimfiWa masa ta ce ""Yaya yaya na'ima ta zo fa"""

"Ya ce ""Haba?"""

"""Wallahi, duk ta sai mini kayayyaki ta bani, ita ta bani tabar nan ma"""

"""Masha Allah, Allah ya saka mata da alkhairi"""

"Ta ce ""Amin"""

"Ya Wan dube ta, ya ce ""Ummi babu wata matsala? Komai lafiya ™alau?"""

"Ta jinjina masa kai ta ce ""Eh""."

"""Na san ko baki faWa ba, akwai matsala ummi, amma dan Allah ki kwantar da hankalinki, komai zai wuce in sha"

"Allah"""

"""Yaushe zai wuce yaya? Gobe ko jibi?"" Tayi maganar idanunta na tara hawaye."

"""Lokaci ne ummi, zai zama tarihi"""

Tuni idanuwanta suka fara zubar da hawaye.

"""Ki dake ummi, ki ™arfafi zuciyarki, na san a cikin matsala ki ke, ki yi ha™uri ummi, ki share hawayenki, zai zama"

"murmushi wataran"" goge hawaye take yi, sai dai tana gogewa wasu suna zubowa."

"Idiris ne ya bankaWo babu ko sallama, yadda ummi ta zabura kawai ya isa ya baka tausayi."

"Ko kallonsu bai yi ba, ya shige ya buWe Wakin da yake kwana, ya shiga."

"Hashim ya tashi ya bi bayansa, ummi ta karkaWe tabarmar, ta Waukko tsintsiyar da na'ima ta bata, ta yi shara,"

"hayaniyar hashim ta din ga ji, da idris."

"Hashim yana ce masa ""Ka ji tsoron Allah wallahi, idan ka cigaba da biye wa Iya, wallahi Allah ba zai barku ba, kuna ta"

"azabtar da marainiyar Allah ba gaira babu dalili""."

"""An azabtar da ita Win, ni na ce a aura mini ita? Ko na ce ina son ta ne, kai meya hana a aura maka ita? An bani saura"

"™azama mummuna, Wallahi ba zan zauna da ita ba, sai ta gudu da ™afarta""."

"""Amma ita ma ai ba cewa tayi tana sonka ba, haWin Iya ne, ita tayi ha™uri, kai me zai hana ka yi ha™urin?"""

"Idris ya ce ""ba zan yi ha™urin ba, ka fita daga harkata, ko kai ma na karta maka rashin mutunci"""

"Haka suka yi baran-baran, hashim ya fito, ummi tana ce masa kai gaida gida, kai kawai ya jinjina mata ya tafi."

"Yana fita, Idris ya dirar mata da duka da zagi da cin mutunci kamar yadda ya saba, yana i™rarin ™ararsa ta kai wurin magaji."

"Ma™wabciyar su da ta kasance dattijuwa, yau ta kasa jure ihun ummi, ta shigo kawo mata Wauki, ta din ga bashi"

"ha™uri, amma mursisi ya ce ta fita ta bar masa gida, ganin idiris bai yi kalar mutunci ba, ya sanya ta fita ta bar gidan tana tausaya wa ummi."

"Tun daga ranar ya ™ara tsananta azabtarwar da yake yi mata, gashi ya tula mata wankinsa, ya ce tayi masa, idan tayi"

"bai fita ba, ya kamata ya zane ta, ban da zagi da cin mutunci."

"Abinci kuwa ko tumatir bai taSa kawowa ba, sai dai ta aika wa iya, Wataran ta bata, wataran ta ce ba ta da shi."

"˜arshe sai da iya tayi ta mata faWa, wai ba zata iya rufawa Idris asiri ba, ta san dai ba wata cikakkiyar sana'a ce da shi"

"ba, ranar da ya kawo su ci, idan ba shi da shi ta din ga ha™uri."

"Dattijuwar matar nan ta fuskanci halin da ummi take ciki, ta Wauki ragamar ciyar da ita, idan ta cewa ummi ta gudu ta je gida ta kai ™arar abun da yake yi mata, sai ummi ta ce ko ta je dawo da ita za ayi."

"Da ya kalli ummi, ya tuna a yanayin da ya sameta, sai ya ™ara ™aimi wurin cutar da ita, haWi da zaluntar ta."

"Idan aka zo ana sallama da shi abokansa, sai ta jiyo suna kiransa da angon WoWWoya, ba ta kawo komai a ranta ba, sai"

"ranar da ta jiyo suna tambayarsa ina amaryarsa WoWWoya, ya ce musu kar su sake haWa shi da wannan jakar yarinyar."

"Duk da ™arancin shekarun ummi, a lokacin ta fuskanci asiri ya tona mata a wurin abokansa, hakan ya sanya ta yin"

kuka da har kanta ya yi ciwo.

"A haka a wannan ba™ar azabar, tayi wata guda cir a gidan sa, tun tana tsoronsa har ta fara dakewa da duk abun da zai yi mata yayi mata."

"Yau ta tashi da wani irin zazzaSi mai zafin gaske, wanda baya rasa nasaba da dukan ruwa da kuma azababben sauron"

da yake cizonta a wannan Wakin.

"Ga gudawa da take zugawa babu ™a™™autawa, jikinta duk yayi weak."

"BankaWa labulen yayi, ya tarar da ita a kwance, ya watsa mata kayansa ya ce ta wanke masa. Shiru tayi ba ta motsa ba, ya daka mata tsawa ta ce ""Yaya bani da lafiya"""

"""Ina ruwana, dalla fito"""

"Ta janyo jikinta ta kwaso kayan ta fito, ya fita sayen omo, ta kwanta a kan kayan, tana jin Wumin ranar dake ratsata,"

wanda hakan ya sa zazzaSi ™ara rufeta.

"Azabar zafin dukan da yayi mata da ™afarsa yasa ta tashi da sauri, tana ri™e hannunta."

"""Bacci na ce ki yi?"" Shiru tayi tana sunkuyar da kai."

"Wani irin yawu ya haWiye, yana ™are wa ummi kallo, duk ba™in fatar nan ta ta fatar tana da Waukar ido."

"A wurin yayi yin™urin sake afka mata, sai dai ba ta sauya zani ba, duk da ta samu sassauci, na ciwon saboda yanzu"

"sau biyu take sauya wando a rana, kamar yadda Na'ima ta gaya mata."

"Amma duk da haka tana wannan ™arin mara daWi, duk da jikinta baya wari yanzu, saboda ta samu sabulun wanka."

"Zura masa ido kawai tayi, saboda a galabaice take da ciwo"

"Wata mummunar ashar yayi mata, yana zubar da yawu, ya Wagota ya din ga kifa mata mari."

"Kukan ma ba ya iya fita, saboda azaba da masifar idiris, da yake abu kamar dabba ba Wan adam ba."

"Ya din ga tsine mata albarka, da ita da iyayenta, dan har Iya sai da ya zaga."

˜arshe ma ya dan™ara mata saki a wurin.

"˜afarta ko takalmi babu, ta gyara suturar jikinta ta fice daga gidan a haka, ta tafi gida ga hannunta Waya kamar ba a"

"jikinta yake ba, saboda takata yayi a hannun."

"Iya da ke iza wuta ta mi™e tana faWin ""Ke lafiya?"""

"Kan ummi ta yi magana, jiri ya Webe ta ta faWi ™asa."

"Da sauri Iya ta ™arasa kanta ta ce ""Ke, menene wai?""."

"""Iya zan mutu, yaya idris zai kashe ni, dan Allah kar ki mayar da ni, ya ce ya sake ni"" tayi maganar cikin gunjin kuka."

"Ta taSa jikin ummi ta ji zafi, ga fuskarta shaidar yatsun Idris kwance a fuskar ta har idonta yayi taruwar jini."

"""LallaSa ki tashi ki shiga Waki ki zauna, daga yin aure ba a kashe shi ba, bari dai ya zo mu ji me ki ka yi masa"" Iya ta"

tashi ta fita.

"Kuka ummi ta din ga yi, tana jin dama ta mutu ta huta, idan aka mayar da ita gidan idris ta san sai ya

15 / 74