CUTARWA COMPLT BY AYSHERCOOL

Author :  AYSHERCOOL Category :  African Stories & Novels

Chapter   18 / 74

51K to 54K   out of 219.4K words

tun yana faWa har ya gaji ya daina yi."

"Ummi kuwa tun daga kama ruwan da tayi, ta ji daWin jikinta, ta tsiyayi maganinta ta sha bayan ta ci gurasar nan, ta"

Wauki sabon phanta ta canza.

"Wani irin daWi take ji da nishaWi, ta sake bubbuWe kayan da ya saya mata tana jin daWin hakan."

"Ko da wasa ba ta yi gangancin fitowa daga Wakin nan ba, dan ta fuskanci ´an gidan ba ™aunar ganinta suke yi ba."

"Ana kiran sallar la'asar ta yi salla, ta cigaba da zamanta a Wakin."

"Kamar an watso su, taga farida da rahama a Wakin, hakan ya sanya ta tashi a razane."

"Farida ta ce ""Tashi munafuka, ai ba zama ki ka zo yi ba"" a zabure ummi ta tashi tana rarraba ido."

"""Ba dai kawo ki aka yi le™en asiri da saka mini ido ba, zaki ci ubanki sai kin bar mini gida da ™afarki"" idonta ya sauka a kan ™atuwar ghana must go sabuwa fil."

"Ta ce ""Rahama janyo mini jakar nan ki zazzageta, wato zuwa yayi ya kashe mata kuWi, wallahi ba zai yiwu ba ya daidaita da ´a´ana, kar ta san kar ai""."

"Rahama ta janyo jaka, suka zazzageta, farida har da ashar, farida ta saka farida ta tsitstsince mata kayan, phants Win"

"ma duk ta kwashe ta bar mata uku, Allah ya taimaketa, tana da sauran wanda ta zo da su, da na'ima ta saya mata."

"Cikin ikon Allah, Allah ya taimaketa basu lura da ™ullin kayan maganin da ke bayan katifar Wakin ba, heater da flask"

Win kuma suna cikin banWaki.

"Hatta omo da sabulun da ya saya mata, sai da suka kwashe ta bar mata Wai Wai."

"Sannan ta sake dubanta a wula™ance ta ce ""Ki buWe kunnenki da kyau ki saurareni, nan gidana ne, abun da na dama"

"shi ake sha, shima kwana biyu na sarara masa ne, amma tun da haka ya zaSa zan yi maganinku duka. Ki saka a ranki ke ´ar aiki ce kawai a gidan nan. Kullum da yamma idan yara suka taso daga makaranta, zaki wanke musu uniform ki goge musu shi tas, wanke-wanke da duk wani aiki a gidan nan ke zaki din ga yin sa, idan ki ga dama ki gaya masa babu abun da zai iya yi a kai, bari in gaya miki ™iri-™iri idan ki ka sake kiransa da Abba sai kin bar gidan nan, dan bai haife ki ba."

"Kuma wanki ba na yara kawai ba, kaya ko na waye sai kin wanke a gidan nan, tashi mu je ma ki fara aikin ki daga yanzu. mummunar banza kawai""."

"Rahama ta kwashe da dariya ta ce ""Ni wallahi fuskarta ma dariya take bani, wannan ba™i kamar a dangwala""."

"""Rabu da ita tashi ki wuce"" ummi kaf maganganun su babu wanda ya Sata wa ummi rai, dan ba yanzu aka fara yi"

"mata ba, ™wace mata kaya yafi komai Sata rai."

Sai dai wata zuciyar ta ce da kin san zaki samu ne?.

"Saboda tsabar mugunta akwai injin wanki a gidan, kuma akwai mai guga, amma farida ta tula wa ummi kayan"

"makarantar su Abdul, na boko da islamiyyar su, kusan kowanne nasa set uku, daga na makarantar boko har na islamiyya."

"Ummi ko a jikinta, ta dur™usa ta fara wankin kayan nan."

"Tas ummi ta wanke su, kasancewar ta riga ta saba da wahala tun a gaban Iya."

"Bayan ta gama cike da mugunta, rahama ta ja ta kitchen, ta sakata sassauke kwanukan da sun fi wata shida ba a"

"saukko su an yi amfani da su ba, ta ce ummi ta wanke. Babu ™yuya ko ™osawa ummi ta wanke su."

"Duk yadda suka wahalar da ummi a yammacin nan har zuwa bayan isha'i, ko da wasa bata nuna musu gazawarta ba."

"Kwanaki uku da zuwanta gidan, rashin mutunci da kyara, haka babar su Abdul suke yi mata, da yaranta da ™anwarta,"

kuma wasu lokutan a hana ummin abincin.

"Sai dai lokaci Waya kawun nata ya rage bata wannan kulawar da yake bata da farko, hakan sam bai damu ummin ba,"

"dan gani take duk wahalar da zata sha, ba zata kai ta gidan Iya da idris ba."

"Ranar lahadi suka koma ganin likita, sai dai ummi ta ji daWin amfani da magungunan nan, dan kuwa sosai yayi mata"

sau™i ba kamar da ba.

"Likita ya dubata, ya rubuta mata magunguna, Allah ya sa kawu yahaya bai yi ™wauron baki ba, ya sanar masa"

"magungunan da take sha, likitan ya ce ta ajiye su ta gama shan na asibiti, idan suka ™are ta cigaba da waccan."

"Yayi masa godiya suka tafi gida, suna tafe yana rarrashin ummi, yana yi mata nasiha."

"Sai da ummi ta yi sati biyu cif a gidan, baban su Abdul ya cewa farida zai kai ummi makarantar su Abdul, amma ta ce"

"ba ta yadda ba, sai dai ya nemi wata mai arha ya kai ummi, dan ba zai dai-daita ta da yaranta ba."

"Staff school ya saka ummi, ta nan makarantar da yake lecturing, makarantar islamiyya ma, wata daban ya saka"

"ummi, sai dai makaranta ce mai kyau sosai ana karatu, dan akwai ´a´an manya a makarantar."

"Duk wanda ya shigo gidan nan ya ga ummi, sai farida ta ce musu ummi sabuwar ´ar aiki ta yi, su yi ta yaba ™o™arin"

"ummi, yarinya ™arama amma ba ta jin jikinta."

"Ko da ummi ta fara zuwa makaranta, a nan Win ma bata sauya zani ba, saboda ba ta tsira daga cin zarafi daga Walibai"

"ba, saboda launin fatarta da ta idonta."

"Wahala ta ™ara ™aruwar mata a ka, ga zuwa makaranta, ga kuma aikin gida tamkar jakarsu."

"Hatta rahama idan ta dawo daga makaranta, har wankin phant da brezia haka take watsowa ummi, ™arewar"

"wula™anci har da wando mai jini, sai ta cire ta bawa ummi ta wanke mata."

"Iya shege da rashin kunya kuwa a wurin su intee, ba a magana, sai ta gyara wuri su Sata, idan suka ci abinci sai ta bi"

"ta Wauke musu kwanuka, sai dai kawu yahaya baya iya magana, yana ji yana gani farida da ™anwarta suka mayar da ummi baiwa, ban da cin mutunci da wula™anci da muzanta halittarta. Dan har haramta mata zaman kan kujerar falo aka yi, wai kar ta shafa ba™i a jikin kujerar."

"Abdul ne ma ruwansa da ita, dama shi ba wani magana ya cika yi ba sosai."

"Yau ma farida ta tafi gida wai suna biki, ga tsohon ciki, amma kamar akuya saboda gantali, gashi tana cikin watanta"

na haihuwa.

"Daga ummi sai Abdul, sai kuma kawu yahaya da yake gida."

"Tana ta aikace-aikace, cikin tausayawa kawu yahaya ya ce ""Sannu da aiki ummina, ki samu ki je ki kwanta ki huta""."

"Tayi murmushi ta ce ""Kawu na kusa gamawa ai"""

"""Ummi kin daina kirana da Abba dai sai kawu ko?"" Tayi shiru tana murmushin ya™e."

"Bayan ta koma kitchen, ya numfasa ya ce ""Yaya"" Abdul ya Wago ya ce ""Na'am Abba""."

"""Yanzu muna tare muna rayuwarmu, gwanin sha'awa kuna rayuwa tsakaninmu cikin jin daWi, hakan yana yi muku"

"daWi ko?"""

"Yayi murmushi ya ce ""Sosai makuwa Abba""."

"""Allah sarki, kamar haka idan Allah ya so, a kowane lokaci zai iya raba mu, muna raye ba tare da wani ya mutu ba,"

"amma zai iya rabamu, kamar yadda ya Wauke mahaifin ummi, ya rabata da mahaifiyarta, ya kawota zama a cikinmu. Ina kallon duk abun da mamanku take yi wa yarinyar nan, da ita da ™annenka, ko ban ce komai ba, Allah yana kallon komai, dan Allah ko daga Sangaren ka ne ta samu sassauci, ba dan Allah baya son ta ya Wauki mahaifinta ba, ya kawota cikinmu ba, zaka so ayi treating Win ™annenka kamar yadda ake treating Win ummi?""."

Jiki a sanyaye Abdul ya girgiza kai.

"""To dan Allah ka din ga nunawa ´an uwanka, ummi mutum ce, kuma ´a ce kamar ku, muzanta ta da bautar da ita,"

"ba shi da wata fa'ida"" ya din ga yi wa Abdul nasiha, sai duk jikinsa yayi sanyi."

"Sai dare sannan suka dawo, suna dawo gidan kamar sun dawo da dauWa, suka cire kaya suka zubar, suka ci abinci suka baje kwanuka."

"Abdul ya tarar da ita a kitchen, tana ta wanke kwanukan da suka ci abinci, ya kalli ummi ya ce ""Ki je ki kwanta,"

"yakamata ki huta""."

"Ummi ta ce ""Kwanukan nan zan ™arasa wankewa"""

"Ya ce ""Bari na tayaki"""

"""Maza basa wanke-wanke"""

"Tun da ta zo gidan nan, maganar kirki bata taSa haWa su ba, ba ruwansa da ita, dan haka yau tayi mamakin cewa da"

yayi zai taya ta aiki.

"Shi dai tun da Abba yayi masa wannan nasihar Wazu, gaba Waya sai tausayin ummi ya kama shi."

"Kallonsa take yi tana mamaki, yadda yake kikkife mata kwanukan, ummi sai cewa take yi ka bar shi fa yaya Abdul."

"""Uban me ka ke yi a kitchen Win nan?"" Rahama tayi maganar tana shigowa hannunta ri™e da indomie."

"""Aiki nake taya ta""."

"Ta watsawa ummi indomie, ta ce idan ta gama, ta dafa mata guda biyu."

"Ko da wasa ummi babu alamar gazawa a fuskarta, ta dafa mata indomie, Abdul yana biye da ita, ta gama yayi zaton"

"kwanciya ummi za ta yi, amma ta kwaso uwar guga ta hau yi, kayan su na babarsu da na rahama."

"Abdul ya zuba mata ido, tana ta sauri ta kammala gugar, dan tana da assignment, tana yi yana ™o™arin yi mata hira, amma kasancewar ba sabawa suka yi ba, ya kasa ya saukko ya ce bari ya taya ta."

"Ba iya gugar yayi ba, ummi tana nuna masa yadda zai yi, sai dai bisa tsautsayi Abdul ya ™ona rigar babarsa, ta lace babban lace ba ™arami ba."

"Hakan yayi dai-dai da fitowar rahama, ta gansu a tare Abdul da dutsen guga. Ta buWe murya ta ce ""Anty farida, zo ki"

"ga bariki, aikin da ake sakata take rabawa da ´a´an gida""."

"Abdul ya ce ""Ni ne na ce zan tayata fa"""

"Farida da ™yar ta ™araso falon, saboda ciwon baya da mara da take yi."

"""Uban me ka ke yi a nan a wannan daren?""."

"Ya ce ""Bakomai""."

"""Tashi ka wuce ka je ka kwanta"" ya tashi ya nufi hanyar Wakinsa."

"Idonta ya sauka a kan rigar leshinta, da sawarta uku an ™ona rigar."

"Ashar ta lailayo, ta Wago rigar ta ce ""Rigar ta wa ki ka ™ona mini? Dan ubanki dan baki da mutunci ba ki da hankali?"""

"""Anty dan Allah ki yi ha™uri, tsautsayi ne, ban san zata ™one ba"""

"""Wallahi sai na ™ona ki da iron Win nan, ke wallahi sai na fanshe rigata, kut lallai baki da hankali"""

"Mi™ews ummi tayi, ta fara kuka tana bata ha™uri, amma rahama ta dan™ota, ta danne ta farida ta sake jona iron Win ya Wau zafi, ta nufo ummi."

"(*Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ina amfani da wannan dama wurin mi™a sa™on ta'aziyyata, ga Waukacin marubuta,"

"na rashin ´ar uwa marubuciya, maryam nasir marsad, dan girman Allah duk wanda ya karanta page Win nan, muna"

"barar ™ulhiwallahu ™afa uku, Ubangiji Allah ya yi mata rahama, ya kai haske kabarinta ya sanya bakin wahalarta"

"kenan, idan ta mu ta zo ya sanya mu cika da kyau da imani Amin*)"

"(MASU NEMA DAGA FARKO, KU DUBA A WATPAD PLEASE )"

Ayshercool

What's app only please 08081012143.

*CUTARWA!*

*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*

BRIGHT PENS

FREE BATCH

P15

"Ihu ummi take yi, tana yi musu magiya su yi ha™uri, amma cike da mugunta da zalunci, rahama ta danne ummi a"

"™asa, ta cusa mata Wan kwali a baki, ta yadda sautin ihunta ba zai fita sosai ba, ta Wage wa ummi riga, farida ta din ga nana mata iron Win nan a cikinta da zafinsa da komai."

"Wata irin mi™a ummi take, saboda azabar da ta ratsata, take ta saki fitsari, saboda azabar zafi da ya ratsa ta."

"Abdul har ya je Wakinsa ya tuna ya ™ona rigar maama, kuma ™ila ummi zata hukunta, dan haka ya juyo da sauri, ya dawo falon."

"A gigice ya ™arasa wurin, ganin bala'i da izayar da ake yi wa ummi."

"""Maama dan Allah ku bari, ba a yi wa mutum azaba da wuta""."

"Fitsarin da ummi ta saki, ya sanya rahama cikata, ta rufeta da duka, saboda ta Sata mata jiki da fitsari, ta fizge hijjabi da hular kan ummi, a take dogon gashin ta mai matu™ar santsi ya zubo har fuskarta."

"Rahama ta ce ""Kut, wannan gashi ko attach"" tayi maganar tana jan gashin ummi da ™arfin gaske, ummi jikinta ya din"

"ga rawa, ta kasa ihun saboda azaba, ta ri™e gashinta da rahama ta cika hannu da shi."

"Abdul ya fara ™o™arin ture rahama daga kan ummi, farida ta kai ™afa zata daki ummi, ta zame da ruwan fitsarin da"

"ummi tayi, ta faWi."

"Wani irin ihu ta kurma, rahama ta Waga ummi, ta nufeta a gigice, ummi ta samu ta lallaSa ta tashi da gudu, ta tafi"

Wakinta.

"BanWaki ta shiga, ta cire rigarta ta din ga zuba ruwan famfo a cikinta, tana jin tamakar wurin ci yake yi da wuta, ga"

"wani irin azaba da kanta yake yi, har wani jiri take ji."

"Kan ka ce kwabo jini ya fara zuba daga jikin faruda, jikinta ya fara kakkafewa, rahama ta ce ""Abdul yi sauri ka je ka"

"taso abbanku"" Abdul ya tafi da gudu Wakin da mahaifinsa yake ta bacci, saboda a gajiye yake sosai, duk wainar da ake toyawa bai sani ba."

"""Abba, Abba ka tashi maama ta faWi ™asa"""

"Da ™yar ya buWe ido, ya kalli Abdul ya ce ""Meyafaru?"""

"""Maama ce ta faWi a falo"" agogo ya kalla, Waya saura na dare, me ta je yi falo a yanzu?"". Ya saukko daga kan gadon,"

"suka fito falon tare, falon sai ™auri yake yi saboda iron da aka bari a jone."

"Jini take zubarwa sosai cikin gushewar hankali, da sauri kawu yahaya ya Waukko mukullin motarsa, da ™yar suka Waga"

"farida, saboda nauyin cikin ta suka bar Abdul a gida suka tafi asibiti."

"Ummi ba ta san abun da ake ciki ba, tana can tana jinyar cikinta da suka ™ona da dutsen guga."

"Ta zauna ta yi shiru tana ta tunanin, me ta aikata da ya sanya kowa ba ya son ta ji daWi, kowa babban burinsa shi ne ya ga ya cutar da ita ta yi kuka?"

"Ta Wauki vasaline ta shafawa wurin, duk da haka sai da ya fara Wurar ruwa, duk fatar cikin ta tashi."

***

"Idiris a tunaninsa tafiyar ummi, shi ne samun sassauci a gare shi, ya yar da ™wallon mangwaro ya huta da ™uda."

"Hashim kuma Iya ta sako shi gaba da cin mutunci, ko gaisuwarsa ta daina amsawa, saboda haushin gayawa kawu"

"yahaya abun da ake ciki da yayi, ya sanya yahayan yana yi musu kallon azzalumai."

"Idiris ya lallaSa ya cigaba da zuwa wurin hindu, yana son ya hilace ta su aikata alfasha, tun da iyayenta sun ™i ya aureta."

"Gulmace-gulmace suka din ga yawo, a kan azabtarwar da Iya ta yi wa ummi, da wanda idris ya yi wa ummin, tare da"

"™o™arin bankaWa asirin dalilin da ya sanya aka fasa auren idiris da hindu, ana ta zaginsu a unguwa, aure wata Waya ya mutu."

"Haka nan sai ummi ta din ga yi wa Idris gizo, idan ya je gidan da suka zauna."

"Ko kuma yayi ta mafarkinta tana yi masa mugun kallo tana kuka. Gashi duk wannan abun da ya faru, ya kasa daina"

"jin sha'awar ummi, ya kuma kasa manta yadda jikinta ke da matu™ar taushi kamar auduga."

"Tun da yake le™e-le™nsa, bai taSa taSa mace mai laushin fatar ummi ba, gashi dai ko man shafawar kirki ba ta da shi,"

amma fatarta har wani irin santsi take yi.

"Ya din ga tuhumar kansa, da ganin wautar sa na kasa daurewa ya sauke abun da yake damunsa game da ummin kan"

"su rabu, amma da ya tuna annakiyar dauWar da ke jikinta, da kuma warin da take yi sai yayi tsaki."

"A rashin ummi ya cigaba da ™o™arin hilatar hindu, yayi lalata da ita, hindu yarinya ce ´ar shekara goma sha shida, gidan su suna da tarbiyya sosai, dan haka sai wahalar da Idiris take, ta™i bashi haWin kai, sai dai tana matu™ar ™aunar"

idiris.

***

"Likitoci suka rufu a kan farida, ana ta ™o™arin ceto ranta, sai dai jini ya™i tsayawa, ™arshe aka ce tiyata za a shiga da ita da gaggawa a cire mata cikin, dan ta fara jijjiga ga jini ya Salle."

"A daren aka shiga da ita tiyata, aka ciro ´a mace, sai dai ba ta san in da kanta yake ba, har aka fito da ita."

"Ita kanta yarinyar ta™i yin kuka, aka yi ta fama, sai dai tayi kaWan tayi shiru, ga rashin isashiyar oxygen a jikinta sai da"

aka saka mata oxygen.

"Rahama ta din ga kuka, tare da Wora zargin hakan a kan ummi, sai dai ta yi shiru ba ta gaya wa baban su Abdul abun"

da ya faru ba.

"Abdul kuwa a gida aka bar shi, ya kasa zaune ya kasa tsaye, mussaman yadda ya kasa manta ganin jini na zuba a"

jikin.

"Ummi bacci sai Sarawo ya kwasheta, shi ma a rigingine ta kwana."

"Da asuba ta tashi tayi salla, fatar cikinta duk ta Waga tayi wani iri, saboda ™una."

"Bayan ta idar da sallar, ta lallaSa ta fito falon, ta tarar da wurin duk jini, ga kayan gugar duk a watse a wurin, tsaf ta"

"gyara wurin ta kwashe kayan gugar, ta shiga kitchen, ta Wora ruwan shayi, sai lallaSa jikinta take yi, saboda raWaWin da take ji a cikinta."

"Ta sake fitowa falo, ta tarar da Abdul a tsaye yana kallonta."

"Ta kalleshi ta ce ""Yaya Abdul""."

"""Na'am, ya jikin wurin ya ™one?"""

"Ta ce ""Eh, amma ba sosai ba""."

"Ya ce ""Maama fa a asibiti ta kwana"""

"Zaro ido ummi tayi ta ce ""Meya sameta?""."

"""FaWuwa tayi"" yayi maganar cikin damuwa."

"Sai a lokacin ummi ta tuna taga farida ta zame ta faWi, ta ce ""Innalillahi wa Innalillahi raji'un, to yanzu ya jikinta?""."

"""Nima ban sani ba, tun da suka tafi basu dawo ba""."

"Ummi ta ce ""Allah ya sa tana lafiya""."

Ya amsa da amin.

"Suna tsaye suna jajantawa, sai ga Abba yayi sallama, duk suka zura masa ido suna yi masa sannu da zuwa."

"""An yi wa mamanku aiki, an ciro baby girl, sai dai dukkannin su, they are under special care, duk basu da lafiya"""

"Ummi ta ce ""Subhanallah, Allah ya basu lafiya""."

"Ya amsa da ""Amin, ummina na san kin yi breakfast, ki zuba wani a flask a kai musu asibiti, ku shirya na ajiye ku a"

"makaranta, ina su kausar?"""

"""Ba su tashi

18 / 74