CUTARWA COMPLT BY AYSHERCOOL

Author :  AYSHERCOOL Category :  African Stories & Novels

Chapter   14 / 74

39K to 42K   out of 219.4K words

hankali, haka kowa yayi maganganun sa ™asa-™asa."

"A hankali kowa ya watse aka bar ummi, ´an matasan yaran da aka bar ta da su, suka gaji da zama, ango bai shigo ba,"

suka watse suka bar ummi ko fitila babu.

"Wani irin tsoro ya mamaye ta, da ta ji motsi kaWan sai ta razana, shiru-shiru babu idiris babu dalilinsa."

"Ji ta din ga yi a ranta, kamar ta tashi ta koma gida, dan wani irin tsoro take ji, kamar ace kyat ta zura da gudu, saboda"

duhun da ya mamaye ilahirin gidan.

"Dare ya cigaba da yi, duhu ya sake mamaye ko ina da ko ina, ta yadda ko tafin hannunta ba ta iya gani, tun tana jin"

"motsin mutane sama-sama, har gari ya koma yayi tsit, sai kukan ™anan ™wari. Cigaba da kuka ta yi cikin firgici, ta tashi a hankali ta le™a tsakar gida, ta hango ™ofar gidan a buWe, tsakar gidan kuma sai ta yi ta ganin abubuwa na yi mata gizo, saboda a tsorace take, kuma ga duhu."

"Da sauri ta koma can ™uryar Wakin ta takure, bacci take ji sosai da sosai ga gajiyar aiki, ga ta biki, ga tashin hankali ga kuma dukan da ta ci jiya da daddare a wurin Iya."

"Babu tsammani ta ji rugugin hadari, da wal™iyya ko ta ko ina, fashewa tayi da kuka, tana son tashi ta fita da gudu ta koma gida, amma tsoro ya hanata."

"Tana nan zaune ruwa ya kece ya din ga zuba kamar da bakin ™warya, ta tashi da nufin ta rufe ™ofar Wakin, amma"

"™arfin zubar ruwan, da kuma tsawar da ake yi, ya sanya ta koma ta zauna tana cigaba da kuka."

"Ruwa ya din ga feshi cikin Wakin, wani irin sanyi ya mamaye garin."

"Ruwa ya shigo Wakin sosai ya ji™e, sai dai bai kai kan katifarta ba."

"Kasancewar bacci Sarawo ne, ya kwashe ummi a nan zaune ba tare da ta shirya hakan ba."

"sai da gari ya waye ya fara haske, sannan ta tashi a razane."

"Ruwan da aka yi duk ™asa ta shanye, ta zama taSo, wani kofi ta gani a tsakar gida, ya cika da ruwan da aka yi, tayi"

"alwala da shi, ta koma Wakin tayi sallar asuba."

"Tana nan zaune cikin zullumi da fargaba, aka yi sallama, wasu daga cikin ´an biki ne suka zo, hakan ya sanya ta ji daWi."

"Suka din ga rafsa guWa, ummi dai da ido kawai take bin su."

"Suka kawo mata abun karyawa, ake tambayarta ina angon? Tayi shiru ba ta ce komai ba, dan kuwa ba ta san me za"

ta ce Win ba.

"Suka ™ara yi mata ´an gyare-gyaren da zasu yi mata, suna ta hira suna yi mata nasiha, da azahar suka ce za su tafi."

Ummi ta Wau hijjabinta ta ce za ta bi su.

"""Ki bi mu ina? Ai ko ™ofar gida ki ka fita babu iznin mijinki, Allah zai ™ona ki a wuta, ki koma ki zauna, shima yana"

"ango amma safiyar fari ya fice, har azahar bai dawo ba?"" Cewar wata dattijuwa."

"˜anwar Iya ta ce ""Bar mara mutunci, ai da alama ba son auren nan yake yi ba, haWin Iya ne kawai, kodayeke ai ma"

"ya furta, tun da hama ta yi masa Allah ya sanya alkhairi, ya ce ba amin ba, ba ya so"""

"""Too ikon Allah, ai dama idiris ba mutunci ya cika ba, har ta bani tausayi, sannu kin ji ummi, Allah ya baku zaman"

"lafiya ya baki juriya"" suka gama salallaminsu suka tafi."

"Ta dawo tsakar gida, ta haWa takalmanta ta zauna, ta zubawa hanyar ™ofar gida ido, in da Allah ya taimaketa, ba™in da suka zo, sun saka yara su je gida, sun Waukko bokiti, an cika mata shi da ruwa, da haka ta samu na alwala."

"Da la'asar aka turo ™anin idris ya kawo wa ummi, abinci ta karSa ta ce masa dan Allah ya tayata zama kar ya tafi,"

tsoro take ji.

"Cikin ikon Allah bai tafin ba, ya tayata zama, har suka ci abinci tare, sai magariba ya tafi ya bar ta ita Waya ™wal kamar"

mayya.

"Hashim ya rasa in da zai sanya ransa, damuwa ta din ga sassa™ar zuciyarsa, gashi tun da aka Waura aure, bai saka"

"idiris a idonsa ba, yana son zuwa gidan ummi, amma yana tsoron yaje ya tarar da abun da ba shikenan ba, da zai"

Waga masa hankali.

"Baban su Idris ya samu Iya yake tambayarta, ya za ayi da dangin mahaifiyar Ummi, yakamata a sanar musu."

"Iya ta ce ""Rabu da su, gayyar tsiya ko an gaya musu uwar mai za su tsinana, talakawan banza, ba su ajiye komai ba"

"sai buzu da tawwada sai allo, ai a haka aka tsaface mini Wa, aka shanye shi ba ya moruwa sai abun da take so, yanzu idan suka sani tsaf za su yi wata ™ulla-™ullar, a bari sai komai ya lafa, an kwana biyu sai a aika musu da goro da alewa ace na aurar da jikata, shikenan"""

"Saminu ya ce ""Amma Iya za su ga kamar ba a kyauta musu ba fa"""

"""Ita abubuwan da tayi mini kyautawar ta yi? Can su ™arata yarinya ce dai na aurar da ita"""

"Saminu ya jinjina kai, amma dai ya san abun da aka yi ba a kyauta ba, ko ba komai suna da hakki a kan ummi, tun da"

´ar su ce ta haifeta.

"Ummi haka ta sake kwana a gidan nan, ita kaWai babu idris babu alamarsa, haka ta sake yin kwanan tsoro da tashin"

hankali.

"Sai dai wayewar garin Allah, babu wanda ya tuna da ita balle ya aiko mata da abinci."

"Babar idiris ta fara ™orafin, tun da aka kai ummi, Idiris bai zo ya ko gaishe su ba, har maganar ta je kunnen iya, ita ma"

"tayi maganar a ranta, amma kasancewar sai a ranar ba™i suka gama watsewa, abun ya dawo kanta."

"Rai a Sace ta aika Alhassan, ta ce ya je gidan ummi, ya ce Idris ya zo tana nemansa."

"A hanyar ™ofar fita, ya tarar da ita a zaune, tana kallon masu wucewa."

"""Ke ummi, kina amarya kina zama a hanyar ™ofar gida kina le™e?"""

"Duk da ba shiri suke yi ba, ummi ta ce ""Tsoro nake ji, nikaWai ce a gidan"""

"Ya ce ""TaS, ina yaya idiris, Iya ta ce yaje tana nemansa"""

"Ummi ta ce ""To ai bai taSa zuwa gidan nan ba, ni tun da aka kawo ni ban ganshi ba"""

"Ya waro ido ya ce ""Ke da gaske!? Ke kaWai ki ke kwana a gidan nan?"""

Ta Waga masa kai alamar eh.

"Ya ce ""Sannu da ™o™ari, kuma ki ka zauna? Kodayeke idan ma ki ka ™i zama kin san sauran, bari na je na gaya wa"

"Iyan"""

"Hankalin iya ba ™aramin tashi yayi ba, da jin cewar wai tun da aka kai ummi bai taSa kwana a gida ba."

"Ta Wau mayafi ta tafi gidan ummi, a nan tsakar gida suka tarar da ita a zaune."

"""Ke ummi, ashe tun da aka kawo ki, Idiris bai kwana a gidan nan ba?"""

Ummi ta Waga mata kai alamar eh.

"""Kuma dan ubanki ki ka ja baki ki ka yi shiru baki faWa ba? Har sai da na aiko, ke da na nemeki na rasa haka na yi"

"miki, ba yawon nemanki na tafi ba? Wato baki damu da shi ba ko?"" Ummi dai ta yi shiru ba ta ce komai ba."

"Iya ta yi ta mata masifa, sannan ta fita, daga gidan, ta saka aka tafi kasuwa aka kirawo babansa, da sagir aka ce"

"musu, ba a ga idiris ba."

"Iya ba ta damu da tsawon kwanakin nan, ya ummi take ba, ta ci abinci ko ba ta ci ba, bata bi ta kan hakan ba."

"Aka din ga yawon nemansa, wurin abokansa da sauransu, da ™yar aka gano shi, can wurin wani abokinsa ya koma, a"

can yake kwana.

"Iya ta same shi ta din ga zaginsa, ta in da ta shiga ba ta nan take fita ba, mahaifinsu ma kamar zai kai masa duka,"

saboda takaici da Sacin rai.

"Hashim kallon su Iya yake yi, yana tausaya musu ranar da hakkin ummi zai kama su baki Wayan su, babban abun da yake ™ara bashi mamaki, irin yadda ba wanda yake iya yi wa musu a kan duk wani son zuciyarta."

"Ummi ba ta san me yake faruwa ba, sai ma tunanin Allah ya sa Idris yana lafiya, tun da an ce tun ranar Waurin aure"

ba a sake ganinsa ba.

"Da ™yar tayi sallar la'asar, saboda yunwar da take ji, cikinta sai ™ugi yake yi, har wani jiri take ji idan ta tashi, ban da"

"ruwa ba abun da ta sha, tana son fita nemawa kanta mafita, amma an ce idan ta fita ba da izinin Idris ba, Allah zai"

"™onata, gashi kuma tana son komawa makaranta, amma ba ta ganshi ba balle ta tambaye shi."

"Sallamar yaro ta ji, tayi sauri ta fito daga Wakin, wani yaro ta gani da kwano, ya ce mata ""Gashi in ji mamanmu"""

"saboda ™uruciya da yarinta, ummi ba ta tambayi daga ina ba, ta karSa ta ce ta gode."

"Dafaffen rogo ne, da ™uli-™uli, ko wanke hannu ba ta yi ba, ta hau rogon nan da ci, saboda yunwar da take ji."

"Ta gode wa Allah bayan ta kammala, duk da ba ™oshi tayi ba, saboda Wan kaWan ne aka zubo shi a kwano."

"Ta fito da kwanon tsakar gida, ta saka ruwa tana girgijewa, dan ba ta da ko omo."

"Kamar wanda aka cillo, ta ga idiris ya shigo, babu ko sallama, hannunsa ri™e da jakar kayansa, wata irin nannauyar"

"ajiyar zuciya ta yi, saboda faWuwar gaba da tsorata."

"Babansa da yake bayan sa yayi sallama, ummi ta amsa ta tsuguna ™asa ta ce ""Baba ina wuni?"""

"""Lafiya ™alau, ya gidan?"""

"Kai a ™asa ta amsa masa da ""Lafiya lau""."

"""Gashi nan, duk ranar da bai kwana a gidan nan ba, da safe ki je gida ki sanar da ni, zaka ga yadda zan yi da kai,"

"mutumin banza wanda bai san abun da yake yi masa ciwo ba, an lallaSa abun nan a rufawa juna asiri, ka daina"

"Waukko mana magana, amma kana ™o™arin tona mana asiri"" mahaifinsa yayi masa kaca-kaca, sannan ya tafi."

"Ummi ji ta yi kamar tabi bayan sa, dan ta wani fannin zamanta ita kaWai babu Idris shi ne rufin asirin ta."

"Ta ajiye kwanon da take Waurayewa, ta nemi wuri can a tsakar gida ta zauna, tana ta addu'a a zuciyarta."

"Idris kuwa ya cika yayi fam! Kamar ya fashe saboda tsabar ba™in ciki da takaici, fuskar ummi kawai idan ya kalla, ji"

"yake kamar ya sha™eta ta mutu, me zai yi da wata ummi, mummuna kamar ba bil'adama ba, aba kamar bayan garwa."

"Tsaki yayi ya fito zai sake fita, aikuwa ta sake razana, kai tsaye inda take ya nufa, ta fara ™o™arin mi™ewa tsaye, ya"

sanya ™afarsa ya tankaWata ta faWi ™asa.

"""Shine ki ke je ki ka gaya musu bana kwana a gidan nan ko? Idan na kwana a gidan uwar me zan yi miki?"""

"Da sauri ta girgiza kai ta ce ""A..aA'a iya ce ya aiko nemanka, wallahi ba faWa na yi ba"" tayi maganar cikin rawar"

murya.

"""Rufe mini baki"" yayi maganar yana dukanta a ka da hannunsa."

"Ta saka hannu bibbiyu ta dafe kanta, saboda jin zafin dukan da tayi, dan ma Allah ya taimaketa, tudun gashinta bai"

bari ta ji zafin sosai ba.

"""Idan ki ka kuskura ko da wasa, ki kai ™arata, sai na yanka ki, kuma azabar da zan gana miki, sai kin gudu da ™afarki,"

"ke baki san yadda na tsaneki ba ko? Zaki gani yanzu ai, banza mai kama da dabbobi"""

"Kame jikinta take sake yi, saboda gudun kar ya kuma dukanta, aikuwa sai da ya sake takata da ™afarsa, sannan ya"

fita.

"Sai da ta tabattar ya fita, sannan ta iya Wagowa a hankali, ta bi hanyar da ya fita da kallo."

"Ta kalli jikinta, da ya Sata mata da ™asar takalminsa, tun da tazo gidan sau Waya tayi wanka, shi ma ba soso babu sabulu. Kayan jikinta tun wanda ta zo da su ranar da aka kawota, Iya ta ce za a aiko mata da kaya, amma shiru."

"A hankali ta saka hannu ta karkaWe ™asar, tana takaicin yadda ya ™as™antar da ita ta hanyar takata da takalminsa mai"

datti da taSo.

"Tayi shiru tana ta sa™e-sa™e a zuciyarta, ta haWe gwiwoyinta, ta kifa kanta, ta nemi hawayen ma ta rasa, sai zafi da"

™unar zuciya.

"Yaya Hashim bai zo ya ganta ba, maman na'ima ba ta zo ba, tayi ta lissafin mutanen da take sanya ran su zo su ganta,"

amma basu zo ba.

***

"A Sangaren mariya kuwa, tuburan depression ya zame mata hauka, ga ta dai a nutse, sai dai babu cikekken hankali, wasu lokutan sai hankalin ya dawo, ta yi ta harkokinta, amma da abun ya juyo, sai daina cin abinci, ta daina magana."

"Duk wanda ya shigo da ™aramin Wa gidan, sai ta ce sai an bata umminta, ko ta Wauki fulo tana yi masa wasa, ta ce"

ummi ce.

"Idan ´an yara mata suka shigo gidan, suma sai tayi ta kiransu da sunan ummi. Ta ce ""Yaya Wanlami, kalli yadda ummina tayi wayo ta girma""."

"Ya amsa mata da ""Tubarkallah, ki yi ta yi mata addu'a, Allah ya ™ara rayata"""

"Ta Wan yi shiru sannan ta ce ""Ba ummi ba ce, ummina ba™a ce mai kyau, bari in tashi in zuba ruwa in yi mata wanka,"

"na goyata garin nan da sanyi"""

"Yayi saurin tashi, ganin da gaske tana ™o™arin kama ´ar mutane ta yi mata wanka, ya ce ""Ki yi ha™uri in anjima sai ki"

"yi mata wankan""."

"""To ai bana son babanta ya dawo ya tarar da mu, ba mu yi wanka mun yi kwalliya ba, kaga yana son turare da lallen"

"da nake yi masa, baban ummina har kayan kasuwa yake sayo mana"" haka tayi ta gwamutsa masa zantuka."

"Yayi shiru yana kallonta, ba zai manta zuwan ™arshe da yayi gidan Iya ba, da yaje da maganar neman alfarmar"

"Waukar ummi, ko na ´an kwanaki ne, dan hankalin mariya ya kwanta, ta fara samun matsala a ™wa™walwa, amma ta kada baki ta ce Allah ya ™ara, hauka yanzu ta fara da yardar Allah sai ta din ga bi bola-bola hakkin ran Wan ta ne."

Tun daga nan yayi alwashin ummi ko ´ar gwal ce ba zai kuma zuwa da niyyar a bashi ba.

"Mama ta fito ta taya shi lallaSa mariya, suka mayar da ita Waki, sai surutai take, tana basu labarin baban ummi da"

"kuma ummi, sai dai ko da wasa ba ta zancen Iya, ko sauran mutanen gidan sai ummi da babanta."

"Ummi ta sakankance idiris ba zai kwana a gidan ba, dan haka har ta hau kan tsurar katifar ta kwanta, sai dai ta kasa"

"rufe idonta tayi bacci, saboda tana jin tsoro, ga gari hadari na ta haWuwa, sai addu'a take Allah ya sa kar ayi ruwan sama."

"Sai da hadarin ya haWo gaba Waya tare da iska, kawai ta ga hasken tochlight a tsakar gida, inuwar Idris ta hango, ya"

"tunkaro Wakin. Ta runtse idanunta, tana fatan Allah yasa ba shi bane ba, sai dai ta ji ya mayar da ™ofa ya rufe, hakan ya tsananta bugun zuciyarta."

"Ba ta san me yake yi ba, saboda ta rufe idonta, ™afafuwanta ya taka ya ce ""Ke dalla tashi"" yayi maganar a matu™ar"

"kausashe cikin rawar jiki ta motsa, ta tashi zaune, me zata gani Idris a tsaye a kanta tsirara kamar mahaukaci."

"Ihu ta saki, ta runtse idanunta ta dafe kanta da hannayen ta."

"""Dalla malama rufe mini baki, ki tashi na ce, uban meye baki sani ba? Munafukar banza da ta wofi, ma™aryaciya an cuceni an haWani da saura, har da zuwa ki gaya musu bana kwana a gida, ai na san kin san komai kin saba""."

"Kyarma ta fara yi, ta™i motsawa, aka kece da wani irin ruwan sama mai ™arfin gaske, ba ka jin komai, sai sautin"

zubarsa da ™arfin gaske a kan kwano.

"Ganin za ta Sata masa lokaci, ya sanya ya jefar da fitilar hannunsa yayi kanta, kamar zararre."

Ayshercool

08081012143

*CUTARWA!*

*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*

BRIGHT PENS

(FREE BATCH)

P12

"Kamar mai shirin tarayya da dabba, haka yayi kan ummi, ya fara yage suturar jikinta, yana ja tana ja, tana ihu tana"

bashi ha™uri.

"""Ba zaki rufe mini baki ba?"" Yayi maganar cikin fusata."

"Warin bakinsa ya daki hancin ummi, kai ka ce an buWe masai."

"Sai dai ba ta gama sha™e warin bakinsa ba, warin gashin kanta ya daki hancinsa, gashi ne fal Allah ya bata shi, sai dai"

"kasancewar babu gyara babu tsafta, ya sanya yake wani irin tsami mara daWin sha™a."

"Sai da ya ware gashin ya sauka bayanta, warin ya ™aru har wani gafi gashi gashin yake yi, saboda tururin warin dauWa"

da ™azanta.

"˜yale gashin yayi, ya cigaba da ™o™arin rabata da suturar jikinta, sai dai nan ma jikin ummi, warin dauWa yake yi, da"

"tsamin gumi, saboda rashin wanka da kula."

"Har Wauke numfashin sa yake yi, ita kanta ummin warin hammatar idiris Win ya hanata sukuni, yafi ™arfinta nesa ba kusa ba, amma ba ta gaza ba wurin ™o™arin kare kanta."

"Duk da a duhu ne bai hana shi, kifa wa ummi mari ba da dukkan ™arfinsa, Allah ya sa hannunta ya samu ba fuskar"

"ba, amma sai da ta gigice."

"Marin da yayi mata ya sanya ta saka kataSus, har ya cimma in da yake burin zuwa, sai dai wari da ™arni mai haWe da"

"zarni ya bugi hancinsa sai da yayi baya, take ya ji cikinsa ya yamutsa masa, kamar zai yi amai, nan da nan zuciyarsa ta fara tashi."

"Duk yadda ya so Wauke numfashin sa ya kasa, wani irin ba™in ciki da takaici ya ninku a zuciyarsa, ya laluba ya Waukko"

"fitilarsa ya hasketa, ta kare jikinta sai kuka take yi."

"Ya tashi ya rufeta da duka, abun da ta fi tsana, ya din ga takata da ™afarsa, sannan ya janyota ya hankaWata waje ana"

"wannan ruwan saman, ba tare da imani ko tausayi ba. Kuka take iya ™arfinta, tana danna ™ofar Wakin, amma ya saka sakata ta ciki."

"Tsakar gidan ya sha™e da ruwa, saboda rashin magudanan ruwa a unguwar."

"Jikinta duk ya yage mata sutura, kuma a haka tsirara ya hankaWota waje cikin ruwan sama."

"Ga wani irin tsoro take ji, balle ta tafi Waya Wakin, haka ruwa ya din ga dukanta tana kuka. Tun tana saka ran ruwan"

"zai Wauke, har ta zubawa sarautar Allah ido, ™afafuwanta suka gaji saboda tsayuwa, ruwan saman nan ya ™arasa zuba a kanta."

"Ta din ga buga ™ofar Wakin a hankali ta na cewa ""Dan Allah yaya idiris ka buWe mini na Wauki kayana, sanyi nake ji dan Allah"" tayi bugun har ta gaji, jikinta ya din ga wata irin

14 / 74