CUTARWA COMPLT BY AYSHERCOOL

Author :  AYSHERCOOL Category :  African Stories & Novels

Chapter   57 / 74

168K to 171K   out of 219.4K words

albarka sosai daga"

wurin dr.

Ya Wauki matarsa suka tafi.

***

"Watannin ummi huWu a gidan raihan, mami ta matsa lamba a kan lallai sai ya auri safiyya. Sai dai juyin duniya, fafur raihan ya nuna mata ba zai iya auren Safiyya ba."

"Ta je ta samu Alhaji da maganar, ya ce ta bari, za su yi maganar da Raihan."

"Raihan ya amsa kiran da Alhaji yake yi masa, ba tare da sanin dalilin sa ba."

"Bayan Alhaji ya sanar masa da bu™atar mami, sai ya ga ya Sata fuska."

"""Babban mutum ba ka ce komai ba"""

"""Alhaji me zan ce? Kwata-kwata yaushe na yi auren da zan ™ara wani? Ni wallahi ummi ta isheni, mami ba za ta iya"

"samo mini mace mai qualities Win ummi ba, ni dai dan Allah ka bata ha™uri, ka san plan Wina Alhaji wallahi ina son ummi, yayi wuri in yi mata kishiya, kuma wallahi idan na auri wata ba zan iya adalci ba, na fi son ummi"""

"Alhaji ya yi murmushi irin nasu na dattawa ya ce ""Shikenan, jeka ba sai ka je wurinta ba, tafi gida abun ka""."

"Sai da daddare da mami ta zo wurin Alhaji, tayi masa maganar ya ake ciki, yaushe za a kai kuWin auren Safiyya"""

"Alhaji ya ce ""Bilkisu, ina son ki fuskanci wani abu, ki ™yale yaron nan da matarsa hankalinki da na su su kwanta, kar ki"

"saka ´ar mutane a wahala, idan ba ki bi a hankali ba yaron nan zai iya gaya miki abun da zaki gaza haWa ido da shi, ya ce ba zaki iya samo masa mace irin matarsa ba, ko ya auri wata ba zai yi musu adalci ba, idan kin gane shikenan idan kuma sai ranar da yayi miki hansfree shikenan."

"Na manta ban gaya miki ba, this coming Friday, za su tafi China tare da matarsa maganar auren nan ki bar ta for now."

Ayshercool

08081012143

"*Alhamdilillah, sai kuma Allah ya kaimu salla da rai da lafiya, Ubangiji Allah ya karSi ibadunmu, ya sanya mu cikin"

´antatun bayinsa*

*CUTARWA*

*BRIGHT PENS*

(FREE BATCH)

*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*

40

"MASU BU˜ATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ŠINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO"

IN SHA ALLAH.

Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp:

https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g

"Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan"

abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe.

FOLLOW AND SHARE

AYSHERCOOL 08081012143

"MASU BU˜ATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ŠINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO"

IN SHA ALLAH.

Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp:

https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g

"Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan"

abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe.

40

"Kamar ya gaya mata ranar mutuwarta, ta ce ""Ban gane ba, da ita zai tafi china, a kan me?"""

"""A kan matarsa ce, kuma ya isa"""

"A fusace ta ce ""Wai meyasa ka ke haka ne? Wallahi ko bangon duniya zai je, sai an yi maganar aurensa da safiyya""."

"Alhaji ya yi murmushi yayi shiru, ya ™yaleta ya cigaba da abun da yake gabansa."

"Ummi da raihan Kuwa suna zaune a toilet, yana ta murza mata dilka a bayanta, ita kuma tana shafawa a fuskarta."

"""Salma"" ta Waga kai ta kalleshi ta ce ""Salma kuma?"""

"""Ba ke ki ka ce in din ga kiranki da sunanki ba?"""

"Cikin shagwaSa ta ce ""To ba da ba ne?"""

"Yayi murmushi ya ce ""Lokacin ba kya so na ko? Yanzunma ina doubting"""

"Shiru ta yi masa ta mintsine shi a gashin ™afarsa, ya janye ™afar yana dariya."

"""Wai wannan abun ba zafi da nake murza miki kuwa?"" Yayi maganar yana le™a fuskarta."

"""Ai ba ka murzawa ma sosai fa"""

"""To ai gani nake zai ji miki ciwo, meye amfaninsa ne?"""

"""Laushin fata yake ™arawa"" ta bashi amsa."

"""Ban da wannan laushin wanne ki ke nema kuma, idan ba so ki ke a ji miki ciwo ba?"""

"Ta tashi ta ce ""Zauna saura kai, kai ma yi maka zan yi"""

"""A'a ni ba na so, ba zaki bani wahala ba"""

"Ta ri™e hannunsa tana shafa masa a fuskar sa, tana murza masa tana dariya ta ce ""Sonake kai ma ka yi kyau, in ga ka"

"na glowing"""

"""Duk wannan kyan bai yi miki ba"" dariya take yi duk ta shafa masa a jiki."

"Ta gama ta Waukko wata roba, an rubuta annur glowing scrub, ya kalleta ya ce ""Wannan fa?"""

"""Scrub ne, homemade, na saya zan gwada, ka san mutanenmu suna da skills, amma mun fi son sayen na ™asashen"

"™etare, amma yana da kyau sosai komai na ciki natural ne"""

"(Ga mai bu™atar mallakar scrub Win nan, domin su yi glowing tare da ummi, mijinta ya zame mata kamar raihan GA ANNUR GLOWING SCRUB, kuma ku saya ku jarraba, ba iya nan suka tsaya ba, har da maganin gyaran gashi, wanda"

"amosani, karyewar gashi, ko ™arfin gashi ya dama, sun tanadar muku maganin matsalar da ingantattun kayan haWi natural, kuna iya tuntubar su kai tsaye a wannan lambar wayar 0907 820 9905)"

"Raihan kallon ummi yake yi, yadda take yi masa bayani, yayi murmushi ya ce ""Ki wanke mini fuskata, wannan abun"

"ya dameni, duk ya ma™ale mini a gemu"""

"Ta wanke masa fuskar, ya tsaya yana kallon mudubin toilet Win ya ce ""Kamar na fara glowing Win ko?"""

"Tayi dariya ta ce ""Daga yi sau Waya, sai ka kwana biyu kana yi sannan zan fara tantance? to ka tafi zan yi wanka,"

"dilkata ta bushe"""

"Yayi mata wani irin kallo ya ce ""Ban gane in fita ba?"""

"Ta Wan kwaSe fuska ta ce ""Eh wanka zan yi"""

"""Ina zamana ki ka ce na zo na shafa miki abu, yanzu kuma ki ke korata?"""

"Ummi ta ce ""To ai dama iya shafa mini nake son ka yi, hannuna ba ya kaiwa tsakiyar bayana""."

"Raihan ya ce ""Tun da na shafa miki ni zan Wauraye ki, nima kalli yadda ki ka Sata mini jikina da wannan abun, sai na"

"sake wanka"" yayi maganar yana cire vest Win jikinsa, da duk tayi yellow."

"Raihan a rayuwar sa yana matu™ar son soyayya da kulawa, sai da ya auri ummi ma ja gane hakan, dan shi da duk"

"hakan ba ya gabansa, kuma a hankali ummi na rage wannan kunyar ta sa da take ji."

"Bayan sun fito daga wankan, ya zaunar da ita a gaban mudubi, yana shafa mata mai, ya jona hand dryer, zai busar"

mata da gashi.

"Ta cikin mudubi ya kashe mata ido ya ce ""Ya dai? Wanka da miji ya fi lada fa, sai wani Sata rai ki ke yi, kuma kin fi fita fa da na wanke ki?"" Yayi maganar yana murza fatarta yana murmushi."

"""Au da bana fita?"""

"""Gaskiya dai, ki din ga biyana ina yi miki wankan, na shafa miki kayan shafe-shafen naki, kuma in yi miki wanka, ki"

"din ga biyana, idan ina yi miki sai kin fi fita"""

"Ummi ta ce ""Hmm kalli agogo, sai makara ka ke yi, kuma sai na kira Alhaji na gaya masa wasa ka ke yi da aiki, ba ka"

"fita da wuri"""

"Yayi dariya ya ce ""Sai in ce masa ke ki hana ni fita, ki ka tsare ni da soyayya, na kasa fitowa"" mi™ewa tayi ta ce ""Kai ba"

"ka jin kunya fa ko?"""

"Kamar ba za su rabu ba, haka ya shirya suka fita falo, ta raka shi har gaban motarsa ya tafi."

"Ta koma ciki tayi ta fama da aiki, dan kaf Wakunan gidan nan, kullum sai ta shiga kowanne ta gyara."

"Wajen ™arfe sha biyu ta kammala aikinta, ba ta karya ba sai a lokacin ta yi farfesun kifi da dankali, ta koma falo ta"

"zauna tana karyawa, ga ™amshin turaren wuta yana tashi, ga Tv tana yi."

"Ta ™arewa falon kallo, ta kalli kwanon hannunta, ta yi murmushi ta ce ""Dukkan yabo da godiya da kirari sun tabatta"

"gareka, tsarkakken sarkin da babu wani kafinsa kuma babu a bayinsa, Sarkin da ni'imarsa da yalwarsa ba su da iyaka"" ta furta hawaye na taruwa a idonta, ba ta taSa tunanin irin wannan rayuwar ta ´anci ba."

"Ta Waga wayarta ta kira maiduguri, sun daWe suna gaisawa, bayan sun gama ta kira raihan."

"Sun daWe suna waya, suna hira sai da ya ce mata zai shiga meeting sannan ta katse wayar."

"Kasancewar kifin da ta Wiba tayi farfesu da yawa raihan ya kawo, dan haka ta tsiri yin girki da kifin, a cewarta a kai wa"

"dr. Wani wani kuma a kai gidan su raihan. Dan raihan ya riga ya bata damar duk lokacin da take son yin alkhairi, ya baga dama ba sai ta tambaye shi ba."

"Tun la'asar da raihan ya dawo gida ya ci abinci, take lallaSa shi ya kai abincin nan, amma sai yawo yake yi mata da"

hankali.

"""Dan Allah MD ka kai abincin nan kar yayi sanyi"""

"Ya ce ""Zan kai, yauwwa tafiyarmu fa sai next week in Allah ya kaimu"""

"Jiki a sanyaye ummi ta ce ""Ka gaya wa mamin zancen tafiyar ne?"""

"""Meyasa ki ka damu ne? Zan gaya mata in sha Allah, kar ki damu ba wata matsala in sha Allah, zan kai abinci da"

"daddare yanzu so nake na kasance da ke, wuni muka yi fa ba ma tare"""

"Ta yi shiru ba ta ce komai ba, ya fuskanci ta na tsoron abun da ka iya biyo baya idan ya sanarwa da mami zai tafi da"

"ita china, dan ita a so samunta kawai ya ™yaleta shi yayi tafiyar sa."

"A booth Win mota ya tafi da abincin sallar magariba, bayan ya idar ya fara zuwa gidan su ummi, sannan ya tafi"

gidansu.

"Bai san Alhaji ya gaya wa mami zancen tafiyar ba, ya fara shiga sashen hajiya, suka gaisa ya ajiye mata abincin, dan"

"ya san idan ya kai wa mami, ba burgeta zai yi ba ™arshe ta ci zarafin Abincin ma."

"Bayan sun gama gaisawa, ya shiga sashen mami, sai dai yanayin fuskarta ya nuna masa akwai matsala."

"""Ina wuni mami?"""

"""Nemi wuri ka zauna"" tayi maganar ba tare da ta amsa masa ba."

Ya zauna yana satar kallonta.

"""Ni na haifeka ko waccan mummunar yarinyar?"""

"""Wace irin tambaya ce haka mami, me kuma tayi?"""

"""Yanzu raihan ka yi ri™ar da zaka tsallake maganata ka ce zaka Wauketa ka tafi china, tawa maganar ka banzantar da"

"ita ko?"""

"Raihan ya ce ""Wallahi mami Alhaji ne ya shirya tafiyar, ba laif...."

"""Rufe mini baki ina magana kana magana, na kusa kawo ™arshen auren nan, na fuskanci ba haka suka ™yaleka ba, tun da ka fara bijire mini, kama aure kai da Safiyya babu fashi, umarni nake baka ba shawara ba, na soke tafiyar"

"nan"" yayi mata shiru, ta ci masa mutunci daga shi har ummi, tare da aibata ummi yadda take so, tayi ta gama bai tanka mata ba, ya tashi ya bar falon."

"Bayan fitarsa Nihal ta fito ta ce ""Mami, dan Allah ki din ga sassauta adawa da auren nan, kina gani fa kin gama"

"banbamin ki, ko amsa bai baki ba ya tafi"""

"Mami ta ce ""Shi ya isa, ban haifi Wan da zai bijire mini ba a kan mace wallahi"""

"Nihal ta kalli mami ta ce ""Idan kuma safiyyan ma yayi mata haka fa, ya so ta kamar yadda yake yi wa wannan? Tun"

"da kin ga yanayin halinsa Waya da Alhaji"""

"Mami ta ce ""Gara safiyya wannan ai tawa ce, ba wani abu"""

"Nihal ta numfasa ta ce ""Mhmm to mu kuma fa? Wasu fa zamu aura, mu ma ayi mana yadda ki ke yi mata kenan?"""

"Cikin mamaki ta ce ""Au goyon bayan sa ki ka fara kenan ya wula™anta ni?"""

"Nihal ta yi murmushi ta ce ""Ahh haba dai, kawai dai wani hasashe nake yi ne, Allah ya kyauta"""

"Ummi kuwa ta sha kwalliyar dare, tana jiran dawowar raihan, amma yanayin yadda ya shigo ya tabattar mata da"

"akwai matsala, ko kallon in da take bai yi ba, ya wuce wani bedroom Win."

"Jikin ummi yayi sanyi sosai, ta shiga tunanin ko ta yi wa raihan wani laifin, amma ta ga lafiya ™alau suka rabu, hakan ya tabattar mata da ba ita ta yi laifin ba."

"Bayan mintuna talatin, ta je ta le™a Wakin da ya shiga, ya kwanta yayi ruf da ciki, ta na son shiga amma idan yayi irin wannan burkicewar tsoronsa take ji, dan haka ta ™yale shi."

"Da safe ma ko karyawa bai yi ba, dan tana kitchen ya tayar da motarsa ya fice, sai ta ji gaba Waya duniyar ta yi mata zafi, kamar ta Wora hannu a ka tayi ihu."

"Raihan kuwa ga damuwar abun da mami tayi masa, ga tausayin ummi yake ji, har cikin ransa yake jin idan ya auri"

"Safiyya ba zai yi mata adalci ba, dan jin ummi yake yi a kowanne sashi na zuciyarsa, haka zalika ma yaushe ya auri ummi, da har za ace ya kawo wata?."

"Ya ji ba zai iya cewa ummi ya janye tafiyar su ba, hakan kamar zubar da kimarsa ne tare da kimar ita kanta mamin da"

"ta kasa gane hakan, dan haka ya ji bai zai iya cewa ya fasa tafiyar nan ba da ummi, ya san duk abu Alhaji zai tsaya masa."

"Sai ™arfe huWu na yamma ya dawo gida, ya kwaso gajiya sosai da sosai, sai dai kamar mai aljanu ya koma normal har yana ce mata gajiyar da ya yi kamar yayi gudun kwana biyar."

"Ta biye masa ya gama cin abinci, ya koma falo zai yi kallo, amma ta bar falon ta koma bedroom."

Ya bita Wakin ya tarar da ita ta fito da kayan wardrobe tana gyarawa.

"A Wan shagwaSe ya ce ""Yanzu fisabilillahi ba ki yi aikin bana nan ba, sai yanzu da na dawo, sonake ki zauna a kusa da ni mu yi hira"" ta Wago da idanunta ta kalleshi, ta kawar da kanta tana tura baki ta cigaba da aikinta."

"Ya ™arasa gabanta yana cewa ""Wai madam ya ne? Me na yi miki ne?"""

"Cikin rauni ta ce ""Kai zan tambaya me na yi maka? Kawai ka share ni, har da canza Waki kuma ni ban san me na yi"

"maka ba, sai yanzu zaka din ga yi mini wasa ba zan yi hirar ba"" tayi maganar har muryarta na rawa saboda shagwaSa."

"""Ohhh sorry kairun nisa'i, ba ki yi mini laifi ba, ba na son laifin da ba naki ba ya shafe ki ba ne, kin san idan ina fushi"

"sai a hankali yanzu ba gashi na saukko da kaina ba, ai idan ke ki ka yi mini laifi ke zan yi wa, bana son in Sata miki rai ne alhalin ba ke ki ka yi laifin ba""."

"""Ni ba ruwana da kai, har da wani canza Waki, to ka tafi kenan kwaso maka kayanka zan yi na mayar maka Wakin da"

"ka kwana, nima na huta"""

"Ya kwashe da dariya ya rungumota jikinsa ya ce ""Ke idan wani ya gaya miki wannan tatsuniyar zaki yarda? Raba Waki"

"da ke, ke ko a baki ya yi miki ma'ana? Iya wuya muna tare sai dai ki yi ta ha™uri. For now dai a yafe mini laifina"""

"Ta Waga kai ta kalleshi ta ce ""Bribe me tukuna"""

"""Da me?"""

"Cikin nutsuwa ta ce ""Ka fasa tafiya da ni, saboda hankalin mami ya kwanta bana son ta yi mini fushi da kai"""

"Yayi saroro yana kallonta, ya maze ya ce ""Ba na ce miki zan kula da komai ba? ba zata ™i ba ai"""

"Tayi murmushi ta ce ""Na san a kan maganar ne ka yi fushi jiya, idan damuwarka ta wurin aiki ce ina ganewa, haka"

"idan da mami ne dan Allah ka yi ha™uri, wallahi ba wani abu ka je ka dawo""."

"Raihan ya ce ""Ba yadda ki ke tunani ba ne, za ta amince fa, honeymoon zamu je"""

"Ta waro ido ta ce ""Wane honeymoon kuma? Me ya rage kuma wani honeymoon zamu je, ai ka gama honeymoon"

"Winka a nan"""

"""A'a fa, ga aiki ga stress, gara muje mu samu cikakken lokacin cin soyayyarmu ba hayaniya"" yayi maganar yana"

sumbatar bakinta.

***

"An kai ruwa rana sosai da mami a kan tafiyar nan, Alhaji ne ya tsaya tsayin daka a kan tafiyar, ya ce idan raihan ya dawo ayi zancen auren safiyya."

"Duk da farida ta san sirikar ummi ba ta sonta, amma ba ta zaci ummi za ta samu kwanciyar hankali da nutsuwa haka"

"ba, Ummi ta je ta yi musu sallama a kan tafiyar su china. Duk wanda ya san ummi a baya ya ganta yanzu ya san a cikin ni'ima take, iya kyan da fatarta tayi ka san tana samun kulawa."

"Noor ta din ga murna, jin ummi za ta je china har da cewa ta gaisar mata da su bursuli."

"Kwanciyar hankalin ummi ya tsayewa farida a rai, tare da jin cewar kausar ce yakamata ace a cikin wannan"

"kwanciyar hankalin, inteesar dai ga ta a cikin daular, amma mijinta ba ya SanSaruwa, gashi ya juya mata baya. Ashe tun kan aure ya kai ta aka yi mata allurar family planning, wai yafi son su gama cin amarci kan su tara yara, babu"

"wanda ta gaya wa daga baya kuma abun ya bata matsala ciki ya™i zama, wadda ya auro kuma ta samu ciki sai"

wula™anci take fuskanta iri-iri. Ga kausar ba makaranta ba mijin aure duk

57 / 74