CUTARWA COMPLT BY AYSHERCOOL

Author :  AYSHERCOOL Category :  African Stories & Novels

Chapter   2 / 74

3K to 6K   out of 219.4K words

babanta, yaushe za a kaita makaranta."

"Ganin ta Wan tasa, kuma idan tana tare da mahaifinta, ko mahaifiyarta, ta kan yi hira da su. Sai dai da tayi yin™urin"

"gaya musu, abun da su Idris ke yi mata, sai ta kasa ta tsorata idan ta tuna suna cewa za su yankata."

"Babanta yana bata lokacin sa, yayi wasanni da ita, har da ´ar tsere a tsakar gida. Da iya ta ganshi kuwa ranar ya shiga"

"uku, da masifa da gori."

"Kasancewar garin sun Wan samu cigaba da wayewa, yanzu ana yin karatu sosai, akwai makarantu, ya sanya balarabe ya kai Ummi makarantar gwamnati, aka saka ta a ECC."

"Ta din ga murna ganin an saka mata sabon uniform, fari da kore, ga jakarta baba na gode, an saya mata sababbin"

"litattafai, sai washe fararen ha™oranta take yi cike da yarinta."

"Tun sha Waya da rabi, mariya ta cewa iya zata je Waukar ummi a makaranta, iya ta ce ""Mariya wai meyasa ba ki da ta"

"ido ne? Ni zan ™arasa girkin kenan, ki bari ta biyo yara, ko idan su Auwwalu sun dawo sa Waukkota. Ni kaita makarantar ma, Allah ya sa ba asarar kuWi ba ne ba, kar aje yadda fuskarta take haka ™wa™walwar take, ayi biyu babu""."

"Wani abu mai Waci ummi ta haWiye, ta cigaba da kaiwa tana komowa, ta faki idon iya, ta Wau mayafi ta fice Waukko ummi, duk da babu tazara sosai, amma yarinya ce ™arama, ba ta san hanya ba."

"Sai dai da ta je Waukar ta, ba ta ganta tana wannan murnar kamar lokacin da za a kaita makarantar ba."

"Tayi zaton kawai ta gaji ne, dan da yawa yara na Wokin makaranta, sai an kai su kuma, su ga ba abun da suke so ba,"

su ce ba sa so daga baya.

"Mariya tana cire mata uniform ta ce ""Mamana, me aka koya miki a makarantar yau?"""

"Cike da yarinta ta ce ""Lemo aka zana mana"""

"Tayi murmushi ta ce ""sai kuma me?""."

"""Bana son makaranta, ba zan sake zuwa ba?"""

"""Subhanallah, ummina meyasa?"" Ta yi maganar cikin kulawa."

"""Yala cu na ce mini baka"" (Yara suna ce mini ba™a)"

"Mariya ta yi ajiyar zuciya ta ce ""Kar ki kula su Yarinyar kirki, ki din ga mayar da hankali a kan abun da malama take"

"koya muku"""

"""Ni bana son ana cewa baka"""

"""Za su daina Ummi, yarinta ce take damun su"""

"Ummi ta ce ""To"""

"Hargowar iya ta jiyo a tsakar gida""Sai ka ce mayya, kamar a duniya babu wanda ya taSa haihuwa sai ke, ai ba a banza ba wannan kalar idon na ´ar ki, na fara zargin akwai masu lashe-lashe a danginku, dan ba™ar masifa, sai da ki ka tafi"

"yawon Waukotta, shafaffiya da mai"" Mariya ta yi shiru ba ta ce komai ba."

"Sa'adatu matar Sagir, da tayi sallama a sashin ta tarar da iya tana ta zuba tijara, ta ce ""Iya ke da wa kuma a tsakar"

"ranar nan?"""

"""Wacece idan ba mariya ba? Duniya kamar babu wani mai Wa sai ita, in dai aka wannan mummunar yarinya ce, ba ta ji ba ta gani""."

"""Iya kenan, mutum da Wan sa ai sai Allah, sauran kunu na zo idan akwai in bawa yaro, ya fara yi mini kukan yunwa"""

"""Shiga ciki ki duba, ni fita zan yi"" tayi maganar tana saSa mayafinta a kafaWa ta fice."

"Sai da iya ta fita, sannan ta lallaSa, ta fito yi wa ummi wanka."

"""Maman ummi, ashe ummi kuma an shiga makaranta"""

"Mariya ta ce ""Wallahi kuwa, ummi an shiga Ecc"""

"""Masha Allah, Ubangiji Allah ya yi jagora, ya sa an shiga a sa'a"""

"Mariya ta amsa da ""Amin"""

"Ummi ta Wan samu sassauci, daga laluben da samarin gidan suke yi mata, saboda shigarta makarantar boko, tun safe"

"sai sha biyu na rana, daga nan kuma ta kwanta tayi ta bacci, wasu lokutan yaran gidan da ´an sa'anninta, su zo su tafi da ita makarantar allo."

"Duk da kuka wasu lokutan kuka take ba ta so, haka mariya ke tursasa mata ta tafi, saboda shi ilimi, dole a tsayawa yaro yayi shi, ko da kuwa ba ya so, mussaman ma na addini."

"Duk da a hakan wasu lokutan ba ta tsira ba, ba ya hana azo har sashin su a Wauke ta, idan mariya zata hana, iya tayi"

ta masifa.

***

"Yau Mariya ta yi yamma wurin girki, tana ta aiki a tsakar gida, iya tana zaune a kan kujera ´ar tsuguno, ta kasa ta tsare, sai wa™e-wa™enta take yi na mutanen da, wa™o™in daSe wasu kamar na batsa,wasu kamar habaici."

"Wata mata ce tayi sallama, suka amsa baki Waya, matar ta gaida iya, Iya ta amsa mata cikin sakin fuska har da yi wa"

Wan matar wasa.

"Mariya ta ce ""Mai koko ke ce da yammacin nan? Bari na baki abun zama"""

"Mai koko ta ce ""Wallahi kuwa, haja na kawo miki"""

"Mariya ta shimfiWa mata tabarma ta ce ""Haja kuma, to Allah ya sa ba ta fi ™arfin talaka irin mu ba""."

"Mai koko ta kwance kaya, kayan yari da sar™a ne da mayafai a ta™aice dai kayan koli ne."

"Mariya ta yi ta WaWWagawa, kayan sun yi mata kyau sosai, ta san idan ta Wauka baban ummi ba zai ce komai ba,"

"amma ba ta son takura shi, dan haka ta ce ""Mai koko muna da Wan kunne, maWaurin gashi na so saya wa ummi, sai dai wannan sun yi ™anana ba zai ri™e gashinta ba, sai dai idan muna bu™ata zan yi miki magana da yardar Allah"""

"Ita ta ce ""Ke ma dai mai koko, ke da ki ke neman arziki, ina ke ina kawo wa wannan kaya, ba su da komai sai tsiya da"

"babu, ki kai sashin Sagir, ko gidan iliya, wannan ai da kin taSa su babu""."

"""Na ga alama kam, ban taSa kawo kaya mariya ta saya ba, kullum sai aukin idan tana bu™ata ta aiko ta saya""."

"""Kema tun da aka yi Waya biyu, ai ba kya bari ayi uku ba, da dai hidimar ´ar ta ce, nan tafi kauri, ta kanainaye mini Wa ta hana shi arziki"""

"Tuni mariya ta tashi, ta koma kan aikinta."

"Mai koko ta Waure kayanta ta ce ""Aikuwa iya ki dage da nema masa magani, ´an uwansa duk suna da rufin asiri ban"

"da shi, sa anjima"""

"""Yawwa ki gaida gida"""

"Ba ta sake bi ta kansu ba, kamar kullum yau da wuri ummi tayi bacci, bayan mariya ta kammala girki, ta Webi gawayi,"

"ta goge wa ummi uniform Win ta, ta gama komai, tana jiran dawowar baban ummi."

"Kamar mai kiran kurma, Iya ta ™wala mata kira, ta fito da sauri a Wan razane ta ce ""Iya gani"""

"""Maza yafo mayafinki, ´aron wurin iliyasu ne, ™aramin ya haWiye ™aya, ku Wauki yaron ki raka Sa'adatu ku je gidan sarkin suu, ya bashi magani"""

"Šan jimmm mariya tayi, so take ta huta, tun safe take aiki a gidan kamar jaka, yanzu kuma iya ta tsiro da wani abun."

"Ba yadda ta iya, ta ce ""To, bari na goya ummi, dan tayi bacci"""

"""Wai ke wace irin mace ce, har yaron ya mutu baki gama goyon wannan buhun sumuntin yarinyar ba, ban da rashin"

"kara, ai ke yakamata ki goya mata yaron, dan Allah ki hanzarta ku tafi, ina nan me zai samu ummin, hanzarta maza""."

"Haka nan mariya ta ji gabanta yana faWuwa, kamar wani abu zai faru idan ta tafi, ga Iya sai Waga mata murya take a"

kan tayi sauri.

"""Iya zan iya goya ummin, sai in Wauki yaron a hannu"""

"""Wai mariya meyasa baki da kunya, ina faWa kina faWa? Salon ki je ki kayar da yaron, ga wannan uwar ´ar ta ki, kaya guda a haka zaki Wauki, yaron ba zaki hanzar ta ba, ko dan ba Wan ki bane ba, ko da yake ina mai Wa Waya ya san"

"ciwon Wa ma"""

"Ta ce ""To ko in kawo ta Wakin ki, sai in kwantar da ita, idan na dawo na Wauke ta?"""

"""A'a ba zaki kawo mini ita ta yi mini fitsari ba, wannan samgartacciyar yarinyar, Wuwawunta ba shi da saiti. Uban"

"meye ma zai kamata a Wakin, ki wuce ku tafi"""

"Jiki a sanyaye mariya ta shiga Waki, ta Wakko mayafinta, ta na ta kallon ummi, tana fatan Allah ya sa babanta ya shigo"

da wuri.

"Ta fito tsakar gida wasu daga cikin jikokin iya suka shigo, shigowar su bai sanya iya yin shiru ba, ta cigaba da yi wa"

mariya masifa.

"Duk mutanen da ke cikin gidan, iya ta rasa wanda zata saka yayi rakiyar kai yaron sai ita, saboda dai kar ta huta,"

kuma kar ta zauna lafiya.

"Suna tafe a hanya tana goye da yaron, sai kakari yake yi, saboda yadda ™ayar take sukansa. Ga gidan sarkin su da"

"nisa sosai, haka suke tafe da fitila."

"Sai dai zuciyarta sai harbawa take yi da sauri, hankalinta ya™i kwanciya, ji take tamkar ta juya da gudu, ta koma"

wurin ´ar ta.

"Sai wajen tara da rabi suka dawo, gudu-gudu sauri-sauri ta nufi sashin su, ba ta bi ta kan iya ba, ta nufi Wakinta."

"Sai dai ta kai kai zata shiga Wakin, shi kuma ya fito da sauri, jikinsa yana tsuma."

"""Me ka ke yi mini a Waki yanzu? Me ka yi?"" Shiru yayi yana tsuma tare da kallon ta, ta hasken farin wata."

"""Me ka yi mini a Waki i yanzu? Me ya kai ka Wakina?"" Tayi maganar cikin ™araji."

"Iya ta ce ""Wai lafiya kuwa? Kun dawo kenan ya jikin yaron?"" HankaWe shi ta yi daga gabanta, ta shiga Wakin da sauri,"

"tana kiran sunan ""Ummi"""

"""Innalillahi wa Innalillahi raji'un. Iya! Iya! Zo ki ga? Iya zo da sauri"""

"Da sauri iya ta taho da gudu tana cewa ""Wai meye ne?"""

"Ta shiga Wakin, ta tarar da ummi a kwance, tana ta numfarfashi, jikinta sai rawa yake yi, an tura mata hularta a"

"bakinta, ga wandonta a yashe a gefe gabanta duk jini."

"Iya ta dafe ™irji ta ce ""Innalillahi wa Inna ilaihi raji'una, wace irin masifa ce wannan, me yaron nan ya zama, kar dai ki ce mini yaron nan ne?"""

"Cikin kuka mariya ta cirewa Ummi abun bakinta ta rungume ta, cikin Waga murya ta ce ""Haba iya, da idonki fa kin gani, kina gani fa, waye ya fita daga Wakin nan idan ba shi ba, na shiga uku na lalace an cuce ni, an cuci ´a ta"""

"""Dalla ki rufewa mutane baki, idan kuma kururwar zaki cigaba, ki tonawa kanki asiri shikenan, idan ba wata ™addara"

"ta Allah ba, waye ma zai aure ta, balle a san me ya faru da ita"" sororo mariya ta bi iya da kallo, wanda hakan yayi dai- dai da sallamar baban Ummi."

"Iya ce ta iya amsawa, ya shigo ya same su, mariya rungume da ummi tana kuka."

"""Maman ummi, Iya meyafaru ne? Ummin ce babu lafiya?"""

"Mariya ta Waga masa ™afar ummi, tana kuka ta sanar masa da abun da ya faru."

Salati ya saka ya dur™ushe a wurin.

"Iya ta ce ""Da ki ke Worarwa ke kin tabattar shi Win ne? Sai ki jirani in bincika in tabbatar ai"". Ta tashi ta fita daga Wakin."

"""Mariya, kina me? Garin yaya? Ya aka yi haka ta faru"""

"Cikin kuka mariya ta ce ""Wallahi iya ce baban ummi, iya ce na shiga uku an lalata mini rayuwar ´a ta, ina zan saka kai na"""

"Iya ce ta dawo ri™e da hannunsa, zuwa cikin Wakin ta kalleshi ta ce ""Uban wa ye ya yi wannan aikin? Me ka yi mata, ba sallama ka yi mini ka ce zaka tafi shagonku ba?"""

"Jiki a sanyaye ya ce ""Wallahi iya tsautsayi ne"""

"A fusace balarabe ya tashi ya sha™e shi, ya ce ""Tsautsayin ka kasa sauke shi a ko ina, sai kan ´a ta""."

"""Zaka cika shi ko sai na Wauke ka da mari? Ba Wa yake a wurin ka ba kai ma? Idan Wan ka ne ya aikata hakan, tona masa asiri zaka yi? Ko idan ka tayar da maganar wani abun hakan zai amfanar, aikin gama ya riga gama."

"Kuma bari ka ji in gaya maka, wallahi tallahi, muddin ku ka Waga maganar nan, wani ya ji ta, bayan mu Win nan, Allah ya isa ban yafe ba, kowaye sai na tsine masa. Ita dauWar gora ai ciki ka sha ta. Idan baku rufa musu asiri ba? Waye zai rufa musu ko salon zumunci ya lalace? ˜uruciya ce da ™addara da bai wuce kan kowa ba"""

"Da wani irin mugun sauri zuciyar mariya ke yi, ™uruciya ga yaron da har ya san, ya toshe mata baki da tsumma, ya"

"keta mata haddi, shi ake kira da ™uruciya."

"Jiki a sanyaye balarabe ya ce ""Shikenan iya, duk ba za ayi haka ba, in sha Allah hakan ba za ta sake faruwa ba, an bar"

"maganar da yardar Allah"""

"Ta kalli saurayin yaron ta ce ""Kai kuma wuce ka bani wuri, wallahi ka sake aikata makamancin haka, da kaina zan ci"

"ubanka na hukuntaka. Wuce ka bar Wakin nan"". Ya fice sumi-sumi ya ci bulus."

"""Ke kuma ki daina wannan kukan, ki tashi ki dafa ruwa, ki sakata a ciki, kiyi ha™uri, ko ki cigaba da kuka ba™in ciki ya"

"kashe ki"" daga haka ta juya ta fice."

"Tana fita mariya ta kuma rushewa da kuka ta ce ""Yanzu shikenan baban ummi, yaron nan ya ci bulus kenan? An"

"lalata mini rayuwar ´a, har iya na cewa wai babu lallai wani ya aureta, wane irin abu ne wannan?"""

"Zuciyar sa fal takaici da Sacin rai, saboda kar ya sake karya wa mariya gwiwa ya ce ""Dan Allah kiyi ha™uri mariya, ki"

"kwantar da hankalinki, kin ga iya uwata ce, ba yadda na iya, dan Allah ki yi ha™uri ki tayani yi mata biyayya, mu Soye sirrin nan, ko dan mutuncin ummi, kar abun yayi mata yawa. Dan Allah ki yi ha™uri mariya"""

"Tashi tayi ta kwantar da ummi, ta fita tsakar gida."

"Babanta ya rungume ta, jikinta ya Wau zafi, tana jin yadda hawayen sa ke Wiga a hannunta."

"""Ummina sannu kin ji? Meye yake miki ciwo?"" Tayi shiru ba ta yi magana ba, sai sheshshe™ar kuka."

"Mariya ta kawo ruwa a baho, ta fizge ummi daga hannun balarabe, ta saka ta a cikin ruwan Wumin. Sai a lokacin"

"ummi ta zabura ta fashe da kuka, ta ce ""Mama zafi""."

"Tana kuka ummi na kuka, ta yi mata wanka, ta saka mata kaya, ta nemi wuri ta kwanta, ta share balarabe."

"Kwana suka yi ummi na koke-koke, ko barci ya Wan Wauke ta, sai ta zabura tana turza ™afarta tana ihu."

"Haka mariya ta kwana kuka, da balarabe ya kai hannu zai taSa ummin, sai ta Wauke ´ar ta, ta juya masa baya."

"Wayewar garin Allah, mariya ta saba zuwa ta gaida Iya, amma a ranar ta™i kula kowa, ta ™i Wora girkin gidan."

"Yara masu tafiya makaranta, duk sashin ta suke zuwa karSar kunun safe, su sha su tafi makaranta, ranar shiru ba ta"

"Wora ba, kowa yazo sai ya koma."

"Balarabe ya din ga raragefe, ya rasa me zai cewa mariya, ya san ™arshen cuta an yi mata, ba ma ita kaWai ba, har da"

"shi, sai dai ba yadda ya iya sawun giwa ya take na ra™umi, iya mahaifiyarsa ce ba yadda ya iya, dole ya bi umarnin ta."

"Yayi shirin sa zai fita kasuwa, jiki a sanyaye ya ce ""Mariya, ko asibiti zamu kaita, na ga kamar da zazzaSi ta kwana""."

"""Dan Allah ka ™yale ni da abun da ya dame ni, ka ™yale ni bashir ka ™yale mini ´a ta, duk muninta daga jikina ta fito,"

"ni na damu da ita, tun da a gurin kai da mahaifiyar ka, ba ´a ba ce. Tun da baban sa yana da kuWi dole ta ce dauWar"

"gora ciki ka sha ta, nayi imani da Allah da Wan ka ne, yayi laifin nan, kowa sai ya ji"" tayi maganar cikin matsanancin"

kuka.

Lallai mariya ta kai ™arshe a Waukar zafi.

"""Ki yi ha™uri mariya, ke kin san ina ™aunar ´a ta, ba yadda na iya ne, wallahi mariya ba ki fi ni shiga damuwa da tashin hankali ba, ki yi ha™uri dan Allah"""

"Ba ta kuma kula shi ba, ta cigaba da shafa kan ummi, da ta Wan samu bacci, tana zubar da hawaye."

"Da son ransa ne, ya wuni tare da su, ya cigaba da rarrashin ta, amma ya san idan ya ™i fita, wani tashin hankalin zasu"

fuskanta daga Iya.

"Gaba Waya girkin ma ta™i yi, ummi kawai ta samawa abun da za ta ci, da ta tuna a yadda ta tarar da ummi, sai ta sake"

fashewa da kuka.

"Iya na son yin tijara, amma tana tsoron kar abun da ya faru ya tonu, dan sun haWu da mariya a tsakar gida,ta hango tsantsar rashin mutunci da tashin hankali a idon mariya, wanda ba ta taSa gani ba, dan haka ta ™udurce a kan"

balarabe za ta juye.

"Haka kuwa aka yi, ana idar da sallar magariba, ya dawo, ya je gaishe ta, ta dira masa bala'i, tamkar ba ita ta haife shi"

"ba, tare da jaddada masa muddin ko shi ko matarsa suka bari zancen nan ya fito, sai ta tsine masa kuma babu ita babu shi."

"Yayi ta bata ha™uri, sannan ya nufi Wakin su, ya tarar da mariya tana goye da ummi kamar jaririya, tana jijjigata tayi bacci."

"Sallamarsa kawai ta iya amsawa, daga haka ba ta sake kula shi ba."

"""Ya jikin ummin?"""

"""Ba sau™i"" ta faWa kai tsaye. Ta je ta kwantar da ummi a kan katifarta da ke ™asa, ta koma falo kan kujerar da ke"

"Wakin ta zauna. Da yake Wakin babba ne sosai, suka raba shi biyu da labule ya zama kamar ciki da falo."

"""Ba sau™i fa ki ka ce maman ummi?"""

"""Ina sau™in yake bashir? An yi wa ´a ta rauni na har abada, waye zai auri ummi ya ri™e ta da amana, alhalin an binne"

"gaskiyar abun da ya same ta tun a lokacin da ya faru, Wan gata ya ci bulus, koda yake dama an ce ba zata auru ba, saboda muninta, da wanne ummi za ta ji? Wallahi Waukar ´a ta zan yi na bar gidan nan, garinmu zan koma, ko kare Allah ya bani ina so, balle Wan adam"" Ta ™arasa tana sheshshe™ar kuka."

"Ya ™arasa ya zauna a kusa da ita, ya ri™e hannunta, idon sa ya tara hawaye ya ce ""Haba maman ummi, ya zan yi, iya"

"uwata ce, dole na yi mata biyayya, idan ki ka tafi da ummi ku ka bar ni, in zauna da wa? Ina son ku wallahi dan Allah kar ki yi mini haka, ummi kuma ba abun da zai hanata auruwa in sha Allah, dan Allah kar ki tafi ki bar ni"""

"Kallonsa ta yi, har cikin zuciyarsa yake

2 / 74